TATTAUNAWA KAN JININ ISTIHALA |
||
|
Babana ya fito ya zauna kamar yadda ya saba kowace rana a wurin da ya saba zama, kana ya fara da kalmar “lstihala” a tattaunawarmu ta yau. Ko kafin ya soma fadar wannan kalma na fara tunanin cewa haruffan wannan kalma su ne haruffan kalmar “haila”, wato an ciro daga cikinta ne. T: Sai na ce: Shin “lstihala” yana daga abubuwan da suka kebanta da mata ne kawai? A: Sai Babana ya ce: Na’am. T: To shin yoyon jini ne…? A: Na’am…sai dai…. T: Sai dai me? A: Sai dai da sharadin kada ya kasance jinin haila ne, kuma ba na haihuwa ba, kuma ba ciwo ba, kuma ba kurji ba kana kuma ba na kawar da budurcin budurwa ba. Sai na ce: Ma’anar haka kenan shi “lstihala” shi ne duk wani jinin da ba “haila” ba ne, kuma ba jinin haihuwa ba ne kuma ba ciwo ba kuma ba kurji ba kana kuma ba jinin kawar wa budurwa da budurcinta ba ne. Sai ya ce: Na’am Sai na ce: Wadannan jini ne masu yawa. Sai ya ce: Wasu daga cikinsu alama ce ta girman mace da budurkantakanta. Shin baka ga cewa idan mace ta tsufa kana jini ya tsaya mata ba ta haihuwa. Sai na ce: Jinin ciwo da kurji da na haihuwa sanannu ne. To amma yaya za’a iya gane cewa wannan jinin jinin “lstihala” ne ba haila ba? Sai ya ce: Shin ka tuna siffofin jinin haila? Sai na ce: Na’am. shi ne jan jinin nan ko baki, yana da ciwo yayin fitowa kana kuma yana da zafi. Sai ya ce: Mafi yawancin lokuta siffofin jinin Istihala akasin na haila galibi jinin Istihala yana da launin rawaya kana ba shi da kauri sannan yana fitowa ba tare da ciwo ba. Sai na ce: To yaya za ta bambance cewa wannan jinin ba jinin kawar da budurcin budurwa ba ne idan aka sami haka daidai lokacin da budurwa ta tare? Sai ya ce: Jinin kawar da budurci yakan kewaye audugan da aka sa ne kamar wata, bayan kuwa shi jinin Istihala yakan ratsa audugan ne har ma wani lokaci yakan wuce ya taba abin da aka daure auduga dashi. Sai na ce: Kenan jinin “Istihala” yakan mamaye dukkan audugan kenan? Sai ya ce: Na’am, koda yake ba dole ne ya mamaye shi ba, saboda haka “Istihala” ya kasu kashi uku: 1- Istihala Mai Yawa: ita ce wadda jinin yake ratsa cikin audugan har ya wuce ya bata tsumman da ake daure audugan da shi. 2- Istihala Matsakaiciya: ita ce wadda jinin ya ratsa audugan amma ya tsaya anan ne kawai ba tare daya wuce ya taba tsumman da aka daure ba. 3- Istihala Karama: ita ce wadda jinin yake bata audugan ba tare da ya ratsa shi ba saboda karancinsa. T: To mene ne hukumci kowanne daga cikinsu? A: A “Istihala” Mai Yawa, wajibi ne ga mace ta yi wanka sau uku (a kowace rana) wato, wanka don sallar safiya, wanka don sallolin Azahar da la’asar idan ta hada su, sannan da wanka don sallolin Magriba da isha idan ta hada su. T: To idan ta raba su fa? A: Sai ta yi wanka ga kowace sallah. T: Shin wannan hukumci nata a kowani irin hali ne? A: A’a, wannan hukumcin nata idan har jinin yana bayyana akan auduga ba yankewa ne amma idan yana yayyankewa ta yadda za ta iya yin wanka da yin salla guda daya ko fiye kafin sake zubowan jinin a karo na biyu [to abin da ya wajaba kanta shi ne sake wanka duk lokacin da jinin ya zuba, da a ce za ta yi wanka ta yi sallar azahar kana kafin ta yi sallar la’asar ko kuma a tsakiyansa sai jini ya bayyana to wajibi ne ta yi wanka don wannan salla ta la’asar], idan har lokacin tsakanin zuban jinin guda biyu zai ishe ta ta yi salloli guda biyu ko fiye da haka ya halatta gare ta ta aikata haka ba tare da bukatar sake wanka ba. Wannan ga Istihala Mai Yawa kenan. A “Istihala Matsakaiciya” kuwa ya wajaba gare ta ta yi alwala ga kowace salla [kana kuma a kowace rana ta yi wanka sau daya kawai]. T: Ba ni misali akan haka. A: Misali, idan mace kafin sallar asuba ta gano cewa Istihalanta Matsakaiciya ce[sai ta yi wanka] kana ta yi alwala don sallar asuba kuma wannan wanka ya ishe ta ga dukkan sallolin da za ta yi na wannan rana tare da yin alwala ga kowace salla, washe gari ma [sai ta yi wanka] kana ta yi alwala, ga kowace salla haka dai za ta ci gaba da yi matukar wannan siffa tata ba ta canza ba. A “Islihala Karama” kuwa abin da ya wajaba kanta kawai shi ne alwala ga kowace salla shin wajiba ce ko mustahaba. T: Shin Istihalar mace yakan canza daga wani kashi zuwa wani? A: Na’am takan canza daga “karama” zuwa “Mai yawa”, daga “Mai yawa” zuwa “karama” haka haka dai. T: Yaya mace za ta gane canzawan Istihalarta? A: [Ya wajaba gare ta da ta binciki kanta gabannin sallah don sanin haka] sannan ta yi aiki da sakamakon binciken nata. Idan ya bayyana mata cewa “Istihala Karama” take da shi sai ta yi aiki da abin da ya wajaba kan mai “Istihala karama” na hukumce-hukumce. Idan kuwa “Istihala Matsa-kaiciya” ce sai ta yi aiki da abin da ya wajaba kan mai Istihala Matsakaiciya” na hukumce -hukumce, da haka dai. T: To idan audugan da tasa da kuma tsumman da ta daure da shi ya shafi jinin fa? A: Yana da kyau a gare ta ta canza su ko ta tsarkake su ga kowace salla idan har Istihalarta Matsakaiciya ce, ko karama amma idan “Mai Yawa” ce [Ya wajaba kanta da ta aikata hakan in za ta iya] kana ta kiyaye fitan jinin na dan lokacin da ke tsakanin karshen wankan har zuwa karshen sallar, idan har wannan kiyayewan ba zai cutar da ita ba. T: Shin wajibi ne gare ta ta gaggauta yin salla bayan aikata abin da ya wajaba kanta na tsarki? A: [Na’am]. T: To shin me ya wajaba kan mai “Istihala” dangane da hukumce-hukumce? A: Na farko: Ya wajaba ga mai “Istihala” bayan daukewan jininta ta yi alwala dan salloli masu zuwa idan Istihalar tata “Karama” ce ko “Matsakaiciya” kana kuma ta yi wanka idan “Istihalar Mai yawa” ce. Na biyu: ya haramta ga mai Istihala da dukkanin rabe -rabenta guda uku taba rubutun al’kur’ani mai girma gabannin samun tsarkinta amma yana halatta bayansa gabannin idar da sallarta. Na uku: Abubuwan da suka wajaba kan mai haila basa wajaba kan mai istihala kamar haramcin jima’i, da haramcin shiga masallaci da zama a cikinsa, da ajiye wani abu a cikinsa da kuma karanta ayoyin sujada. Na biyar. Ingancin azumi yayin Istihala “Karama” ko “matsakaiciya” koda kuwa mace mai Istihalar ba ta aikata abubuwan da suka wajaba kanta na salla kamar alwala da wanka ba amma wasu daga cikin malaman fikhu, Allah ya kara masu yarda sun tafi kan cewa ingancin azumin mai “Istihala mai yawa” ya rataye kan aikata abubuwan da suka wajaba a gareta ne na daga wanka a daren da ya gabaci ranar azumin da kuma wankan rana. Amma abin da ya fi inganta shi ne ingancin azumim nata bai rataya ga haka ba. Na shida: Ba ya wajaba ga mai “Istihala Mai Yawa” da ta yi alwala tare da wanka amma alwala yana wajaba ga mai “Istihala Matsakaiciya” bayan wankan [da ya wajaba a gare ta]. * * * * * |
||