TATTAUNAWA KAN MUTUWA |
||
|
A gaskiya ba zan boye muku ba cewa lokacin da babana ya fara maganarsa kan mutuwa na kasance farke cikin tsoro da damuwa mai tsanani ina mai dubin fuskarsa da yadda sautinsa yake sama da kasa yayin da yake maganarsa kan mutwa cikin nitsuwa da lura don ya nuna irin abin tsoron da ke cikinta. Haka ma ba zan boye muku ba cewa duk lokacin da babana ya ambaci kalmar “mutuwa” -wannan kalma mai firgitarwa wadda aka jahilta na kan ji wani irin hali da ya sabawa dabi’a, na bugun zuciya saboda tsoron da nake fama da shi, wadda yake rina min fuska da kunnuwa da wani irin gumi da yake taruwa da gudana a kan goshi da hancina. A lokacin da Babana ya lura da alamun tsoro a fuskata sai ya tambaye ni… - Shin ka tsorata ne…? - Shin kana tsoron mutuwa ne ko mamaci? Hakika tsoron da ya same ni yau ya kasance tsoro ne mai girma. Duk tsawon rayuwata ban taba ganin mutum a halin mutuwa ba kai ban ma taba sanin abin da ya kamata in aikata ba idan ya kasance a gabana ga mutumin da ya kai gargara ko wanda yake halin mutuwa. Kafin wannan rana na kasance a duk lokacin da na ga an dauko gawa, wani irin hali na bakin ciki, tsoro da kunci sukan same ni har na kan so in daga idona daga kanta don in yanke hanyar tunani Na sake fadin haka ne don in jaddada yakinina. - Shin kana tsoron mamaci sama da yadda kake tsoron mutuwa, da abin da ke bayan mutuwa? Sai Babana ya ci gaba da cewa: Shin kana tsoron wanda kafin mutuwarsa yana raye kamarka, yana ci yana sha, yana kuka yana dariya yana shakatawa yana mafarki kana yana barci. Kana… Kana wani abu ya bijiro masa wadda idan ya bijiro wa dukkan wani rayayye sai ya gurfanar da shi. Me yasa ba za ka fuskanci abin da ya fi fitowa fili ba, wato ka ji tsoron mutuwa sama da yadda kake tsoron mamaci? Shin ka tambayi kanka ina dukkan wadancan al’ummomin da suka gabata suka tafi (gidajensu sun zama kaburbura, dukiyoyinsu sun zama abin gado, basu san abin da ya rage a bayansu ba kana basa iya amsa kiran wanda ya kira su). Sun bar lambuna da koramu, sun bar shuke-shuke da mukami mai girma, sun bar ni’imomi da da suke ciki- Allah ya ba da su ga wasu. Kana, ina wadanda da ka san su suka tafi? Ina iyaye da kakanninka da suka wuce suke, ina wane…ina wane …ina wane? Hakika sun musanya doron kasa da cikinta, sun musanya yelwa da kunci sun yi musayen sabo da bakunta sun kuma musanya haske da duhu. Kana sai Babana ya rera wannan waka: Dukkammu mun kasance cikin gafala, ga mutuwa ta farka tana yawo. Ka farka ya kai miskini,idan kana farkawa. Ba za ka dauwama ba koda kuwa ka rayu kamar yadda Nuhu ya rayu. Daga nan sai ya yi shiru fuskarsa ta canza kamar yana kokarin ya nuna abin da ke cikin zuciyarsa ko kuma kamar yana kokarin ya tattaro abubuwan da suke nan da can zuwa kwakwalwarsa har lokacin da sautinsa ya katse wannan shiru yana mai cewa: Allah ya rahamshe ka ya Abal Hasan ya Amira muminin ranar da gabannin rasuwarka ka ce: Jiya na kasance tare da ku, ga shi yau na zama abin misali gare ku, gobe kuwa wanda zai rabu da ku. Ya shugabana: wata rana kuma ka ce: “Ya kamata ku sani cewa wannan fata mai taushi ba za ta iya jure wa wuta ba, don haka ku ji tausayin kawukanku domin kun riga kun dandana wahalolin duniya kun gani”. Shin baku ga wahalar da dayanku yake sha ba lokacin da kaya ta soke shi , ko kuma idan ya yi tuntube, ko kuma idan hamada mai zafi ta kone shi? To ina ga kuma idan yana tsakanin dabakoki guda biyu na wuta yana kwance kan duwatsu, ya zama abokin shaidan? Shin kun sani cewa idan Malaika daya ya yi fushi da wuta wani sashen wuta ya kan rikito kan sashe saboda bacin ransa, idan kuma ya yi mata tsawa takan rika tsalle tana faduwa tsakanin kofofinta saboda wanan tsawa tasa”! Sai babana ya ci gaba da cewa: Ka gane cewa hakika an sanya maka tsoron mutuwa ne saboda fargaban da ke nan bayan mutuwa. “RANAR DA KUKE GANINTA DUKKAN MAI SHAYAR DA MAMA TANA SHAGALA DAGA Abin Da TAKE SHAYARWA, KUMA DUKKAN MAI CIKI TANA HAIFAR DA ABIN da ke CIKINTA, KUMA KANA GANIN MUTANE SUNA MAYE ALHALI KUWA SU BA MASU MAYE BA NE, AMMA AZABAR ALLAH CE KAWAI MAI TSANANI” A RANAR DA KOWANE RAI YAKE SAMUN abin da YA AIKATA NA DAGA ALHERI, A HALARCE, DA KUMA ABIN DA YA AIKATA NA SHARRI ALHALIN YANA BURIN, DA DAI LALLE ACE AKWAI FAGE MAI NISA TSAKANINSA DA Abin Da YA AIKATA NA SHARRI! KUMA ALLAH YANA TSORATAR DA KU KANSA, KUMA ALLAH MAI TAUSAYI NE GA BAYINSA”. Amma ai mamaci ko wanda ya kai gargara yana tuna maka yadda makomarka take ne… kada ka samu damuwa. Babana ya fadi haka kana ya yi shiru, tun da ya fadi haka sai na fara dawo da tunanina kan wannan abin tsoro cikakken tunani har lokacin da babana ya katse min wannan tunani yana mai jaddada cewa: Idan har ka sami kanka a wajen da wani musulmi ya kai gargara, to ka ajiye tsoronka a gefe guda, [kana ka fuskantar da shi al-kibla]. T: To yaya zan fuskantar dashi? A: Ka kwantar da shi akan bayansa kana ka sanya cikin tafin kafansa zuwa alkibla. T: Wato in mike kafansa su fuskanci alkibla kenan ko. A: Na’am haka ne, ba wani banbanci shin mutumin da ya kawo gargarar namiji ne ko mace ce, yaro ne ko babba. Kuma an so ka dinga ambata masa kalmar shahada, da kuma gaskata annabi (S.A.W.A.) da A’imma (a.s) kana a dinga karanta masa suratus as-safat don saukake masa zafin fitan rai. Sannan an ki mai janaba ko mai haila ta matso gurin wanda ya kai gargara ko shafansa yayin fitan rai. T: To yaya za’a yi idan ya rasu? A: Idan ya cika mustahabi ne rufe masa idanunsa, sannan a rufe masa bakinsa, sannan a mike hannayensa zuwa gefukansa, kana a rufe shi da tufafi, kana a dinga karanta masa al-kur’ani, sannan kunna fitilu (wato a haskaka) gidan da yake zaune, sannan a sanar da muminai labarin rasuwarsa don su halarci jana’zarsa, kuma abin so ne a gaggauta kai shi kabari sai dai idan ana shakkar rasuwar tasa. T: To idan aka yi shakku a mutuwarsa fa? A: Ya wajaba a wannan hali a jinkirta har sai an san tabbacin mutuwarsa, idan aka tabbatar to ya wajaba ayi masa wanka, shin namiji ne ko mace, yaro ne ko babba. T: To wanda aka yi barinsa fa? A: Har wanda aka yi barin idan dai har ya cika watanni hudu [kai koda ma bai cika wata hudu ba matukar dai halittarsa ta cika] Sai dai yi masa sallah ba wajibi ba ne ko mustahabi. T: To waye ya cancanci ya yi wanka wa mamaci? A: Namiji ya wanke (dan’uwansa) namiji kana mace ta wanke mace ‘yar’uwarta, sai dai miji da matarsa ya halatta ga kowanne daga cikinsu ya wanke dan uwansa haka ma kananan yara masu rarrabewa mace ko namiji mace ko namiji su yi masu wanka Haka nan ma tsakanin muharramai (wanda babu aure tsakaninsu) nan ma ya halatta ga mutum ya wanke muharraminsa ba tare da lura cewa jinsinsu daya ne ba (wato namiji da namiji,mace da mace) [amma sai fa idan an rasa jinsi iri daya]. T: To yaya ake wanka wa mamaci? A: Ana masa wanka kala uku ne: Na farko: da ruwan magarya Kana na biyu: da ruwan kafur Sannan na uku: ruwa mutlaki da sakakken ruwan da ba komai a cikinsa. [kana wankan ya zamanto “Tartibi”] a jere wato a fara da wanke kai da wuya, kana gefen dama, sannan gefen hagu, sannan kuma dole ne ruwan da za’a yi amfani da shi ya zamanto na halal ne ba na kwace ba, kana ruwa “al’mutlak” ne ba “al-mudaf” ba, sannan kuma magaryar da kafur din su zama na halal ne su ma. T: Shin za’a cire wa mamaci kayansa ne lokacin da za’a yi masa wanka? A: Ya halatta a yi masa wanka da tufafinsa watakila ma hakan shi ya fi da ace an bar shi tsirara. T: Yaya za’a yi ruwa ya zamanto “mudlak” bayan an sa masa magarya ko kafur a cikinsa? A: Za’a sa masa magaryar ko kafur din ne ta yadda ba zai canza shi zuwa ruwa “al-mudaf” ba. T: To me ya kamata ayi idan jikin mamacin ya najastu daga wata najasa daga waje ko kuma ma daga jikin mamacin lokacin da ake masa wankan? A: To wajibi ne a tsarkake abin da ya najastu daga jikinsa, amma ba wajibi ba ne a sake wankan. T: Me za’a yi bayan an gama wankan? A: Wajibi ne ayi masa “al-Hanud” sannan kuma ayi masa likkafani. T: Mene ne “Al-Hanud”? A: Shi ne shafan wurare sujjadan nan guda bakwai da kafur wanda aka nika aka kuma kiyaye kanshinsa, kana na halal ba na kwace ba, kuma mai tsarki ba mai najasa ba [koda kuwa ba zai najasta jikin mamacin ba] kana an fi so “al-Hanud” din ya kasance da tafi hannu za’a yi kana a fara da goshi. T: To sauran gabobin sujadan fa? A: Babu jerantawa tsakaninsu. T: To yaya ake yin likkafani wa mamaci? A: Wajibi ne ayi likkafani wa mamaci da kyallaye guda uku:- 1- Fatari [dole ne ya rufe abin da ke tsakanin cibi da guiwoyi]. 2- Riga [dole ne ya rufe abin da ke tsakanin kafada da rabin kwabri]. 3- Mayafi dole ne ya rufe dukkan jiki- [kana ya kasance yana da tsawon da za’a iya kulle sama da kasansa]. T: Fadinsa fa? A: Fadinsa ya kasance [ta yadda daya bangarensa zai iya haduwa da dayan]. Ya hau kansa. T: Shin akwai wasu sharudda dangane da wadannan kyallaye kuma? A: Na’am, an shardanta cewa dole su kasance sun suturce jikin mamacin, kuma kada ya kasance na kwace ne, kuma ba na siliki (harir) ba, [kuma ba na zinare ba, kuma kada ya kasance daga wani bangare na dabbobin da ba’a cin namansu] kuma ba daga najasa ba, sai dai a halin lalura, inda a irin wannan hali yana halatta ayi likkafani da dukkan wadannan abubuwa amma ban da na kwace. T: To idan waddannan kyallaye uku basu samu ba fa? A: Sai ayi wa mamaci likkafani da abin da ya sauwaka daga cikinsu. T: To me ya saura kuma bayan wanke mamaci, yi masa “hanud” da kuma likkafani? A: Sai ayi masa sallah koda kuwa yaro ne. T: Yaya ake yi masa sallar? A: Sallar gawa ta bambanta da sallolin da ake kowace rana domin ita tana da kabbarori guda biyar ne, kuma ba’a karatun sura a cikinta, haka kuma ba ta da ruku’u ko sujada ko Tahiya ko sallama, abin yi kawai shi mai sallan zai yi addu’oi ne ga mamacin bayan daya daga cikin kabbarorin nan guda hudu na farko, amma a sauran an ba shi zab tsakanin salati ga annabi (S.A.W.A) da adduoi ga muminai da kuma daukaka ubangiji. T: To ko za ka gaya min a takaice yadda ake yin ta? A: Mutum zai fara da kabbara ta farko sai ya karanto kalmomin shahadar nan guda biyu, kana bayan kabbara ta biyu sai ya yi salati wa annabi (S.A.W.A.) da Ahlu Baitinsa (a.s), kana sai ya yi kabbara ta uku ya yi addu’a wa muminai maza da mata, kana bayan kabbara ta hudu sai ya yi addu’a wa mammacin, sannan sai ya yi kabbara ta biyar shi kenan. T: Shin akwai abubuwan da ake lura da su a sallar mamaci? A: Na’am, ana lura da wadannan abubuwa:- 1- Daura niyya tare da ayyana mamaci karara. 2- Tsayuwa- idan har mutum zai iya tsayuwar. 3- Kuma ya kasance bayan wanke mamacin da yi masa “hanud” da likkafani ne. 4- Fuskantar al-kibla idan har ba wata matsala. 5- Kuma mamacin ya zamanto a gaban masu salla. 6- Kuma kan mamaci ya kasance a bangaren daman masu salla sannan kafafunsa su kasance a bangaren hagunsu. 7- Kuma a kwantar da mamacin ta bayansa yayin sallar. 8- Kuma ya kasance babu wani abin da ya raba mamacin da masu salla kamar katanga etc, amma rabuwa kamar irin na akwatin da ake sa mamaci a ciki ko kuma wani mamacin daban ba ya cutarwa. 9- Kuma kada a bar fili mai tsawo tsakanin mamacin da masu salla, kuma kada dayansu ya yi sama da daya bambanci mai girma, yawan sahun masu sallah ko yawan gawawwaki ba ya cutarwa idan dai har an yi sallan lokaci guda ne. 10- Kuma waliyin mamacin kamar babansa ko dansa shi ne mai bada izinin ga wadda zai masa salla. 11- Kuma a samu gaggautawa a tsakanin kabbarori da addu’oin. T: Me ya sa ba ka ambaci sharadin tsarki ga mai sallar ba kamar ya kasance cikin alwala, ko wanka ko taimama? A: Domin kuwa a wannan sallar ba wajibi ba ne. T: To idan aka idar da sallar fa? A: To wajibi ne a binne shi kuma hakan yana tabbatuwa ne ta hanyar rufe shi a cikin kasa tare da lura da wadannan abubuwa guda biyu:- Na farko: kiyaye shi daga mugayen dabbobi idan har ana tsammanin akwai su a gurin. Na biyu: kiyaye warinsa daga cutar da mutane idan har ana jin akwai wadda zai cutu daga hakan. Za’a sanya ta bangaren damansa a cikin kabarinsa tare da fuskantar da fuskansa zuwa al-kibla. T: To mene ne sharudan wurin da za’a binne mamaci? A: Na’am… 1- Dole wurin ya zamanto na halal ba na kwace ba, ba kuma an bar shi don wani abu na musamman ba ne kamar makarantu ko masallaci da makamantansu ta yadda zai cutar da abin da aka bar shi dominsa [kai koda ba zai cutar ba kuma koda babu matsi ga masu wurin.] 2- Kuma kada wurin ya zamanto wuri ne da zai zubar da mutuncin mamacin kamar wuraren kazanta da juji. 3- Kuma kada a binne shi a makabartan kafirai. T: To bayan an binne shi fa? A: An ruwaito daga manzon Allah (S.A.W.A.) yana cewa: (Ba wani lokacin da ya fi tsanani wa mamaci kamar daren farko (na rasuwarsa), ku jikan mamatanku da sadaka, idan baku samu dama ba to ku yi sallah raka’a biyu dominsa, a raka’a ta farko ku karanta “Ayatul kursiyyu” bayan fatiha, a ta biyu kuma ku karanta “Suratul kadr” sau goma bayan fatiha, bayan kun yi sallama sai ku ce: (Ya Allah ka yi salati ga Muhammad da zuriyar Muhammad ka isar da ladan wannan sallah ga kabarin wane (sai ka ambaci sunan mamacin) T: A tattawnawarmu da ta wuce ka ambaci wani wanka mai suna wankan taba gawa? A: Na’am, wajibi ne ga wanda ya shafi jikin mamaci musulmi ne ko kafiri bayan ya yi sanyi kafin a gama masa wanka, da ya yi wanka. T: Shin sai jikinsa da danshi? A: Ko da danshi ko babu, shin an tilasta shi ne ya shafi gawan ko kuma ganin damansa ne. 1- Wajbcin wanka ga duk wani aikin da tsarki yana daga sharadin ingancinsa kamar salla, idan har yana so ya yi salla to wajibi ne sai ya yi waka tukun. 2- Haramcin taba rubutun al-kur’ani mai girma da kuma dukkan abin da ya haramta ga mara tsarki ya taba. Sai Babana ya yi shiru na dan lokci kana ya ce: Idan mijin mace ya rasu to idda ya wajaba ga matarsa koda kuwa yaya shekarunta suke, kuma koda ba a yi dukhuli da ita ba. Iddar mace wadda ba ta da ciki wata hudu ne da kwana goma kuma a yayin nan ya wajaba a gare ta idan balagaggiya ce mai hankali, to ya wajaba ta bar yin kwalliya da sa tufafi na kawa, kuma ya haramta a wannan lokaci, sa tozali da shafa turare da yin lalle da sa kawace-kawace, koda yake ya halatta gare ta yi tsabta a jiki da tufafi, kuma ya halatta ta yanke farcenta, ya halatta kuma ta yi wanka, sannan ya halatta ta fita waje musamman domin biyan wata bukata ko kuma ba da wani hakki, ko aiwatar da wani wajibi ko wata lalura. T: To mace mai ciki fa? A: Iddar mace mai cikin da mijinta ya rasu shi ne ta hakura har lokacin da ta haihu, sannan ta gani shin ta kai wata hudu da kwana goma daga rasuwar mijinta, in ta kai to iddarta ta kare in kuwa ba ta kai ba to sai ta ci gaba da idda har ta cika wadannan kwanaki.
* * * * * |
||