TATTAUNAWA KAN JININ HAIHUWA |
||
|
Da farko babana ya ce: Yau zan maka bayani kan jinin haihuwa. T: Mene ne jinin haihuwa? A: Jini ne da mace take gani yayin haihuwa ko bayansa saboda haihuwar da ta yi, to wannan lokacin mukan kira wannan mace da “mai Jinin haihuwa”. T: Kwana nawa jinin haihuwa yake yi? A: Mafi yawansa kwanaki goma ne. T: To mafi karancinsa fa? A: Ba shi da karanci, yakan iya yin minti daya ko ma abin da ya gaza haka. T: Shin jinin haihuwa yana banbanta ne tsakanin mata? A: Masu jinin haihuwa sun kasu uku kuma kowace akwai hukumcinta na musamman da ta kebu da shi. Na farko: Ita ce wacce zuban jinin a gurinta ba ya wuce kwana goma. T: To mene ne hukumcinta? A: Shi ne ta dauki duk kwanakin da jinin ya yi yana zuba a matsayin jinin haihuwa. Na biyu: Wacce jininta yakan wuce kwanaki goma yana zuba, kana kuma tana da al’ada ta adadi takamaime a haila kamar misali al’adarta ta haila ta kasance kwanaki biyar ne a kowani wata. T: To mene ne hukumcinta? A: Shi ne ta dauki adadin kwanakin al’adarta a matsayin jinin haihuwa, wato kwanaki biyar a misalin da muka kawo. T: To sauran kwanakin fa? A: Sai ta dauke su a matsayin jinin lstihala. Na uku: Wacce jininta yake wuce kwana goma yana zuba, kana kuma ba ta da takamaimen al’ada ta adadi a haila. T: To mene ne hukumcinta? A: Shi ne ta dauki kwanaki goma a matsayin ranakun jininta. T: Mene ne hukumcin mace mai jinin haihuwar da ta kasance tana da al’ada takamammiya a haila, kana sai kwanakin zuban jinin haihuwarta suka wuce kwanakin al’adar tata sannan kuma ba ta san shin jinin nan zai dauke kafin kwana goma ba ko kuma zai ketare kwana goman? A: Sai ta bar ibada har zuwa cikon kwanaki goma, idan har jinin ya dauke sai ta dauki duk wannan lokacin a matsayin jinin haihuwa, idan kuwa har ya wuce ran na goman to sai ta yi wanka kana ta aikata aikin mai jinin istihala. T: To wadannan kwanaki da ke tsakanin kwana goma da karshen al’adarta da ta bar lbada a cikinsa fa? A: Sai ta dauke su a matayin istihala, kana ta rama abin da ya tsera mata na ibada. T: To idan zuban jinin ya tsaya a ranar farko kana sai ya sake dawowa amma ya yanke a rana ta goma ko kuma wata rana gabannin (ranar goma) fa? A: To zuban jini na farko da na biyu dukkansu jinin haihuwa ne. T: To dan lokacin da jinin ya dauke tsakaninsu fa? A: [A wannan hali hukumcinta shi ne ta hada ayyukan wacce ta tsarkaka daga jinin haihuwa da kuma abubuwan da ya kamata mai jinin haihuwa ta bari]. T: To idan jini ya dauke sannan ya dawo kana ya sake daukewa sannan ya sake dawowa, haka dai… amma duka kwanakin basu wuce goma ba fa? A: To dukkan kwanakin da jinin yake zuba jinin haihuwa ne amma sauran kwanakin da ya tsaya [sai ta hada tsakanin ayyukan tsarkakakkiya (daga jinin haihuwa) da kuma abubuwan da mai jinin haihuwa za ta bari]. T: Idan mai jinin haihuwa ta kare kwanakin jininta, amma sai daga baya ta ga wani jini fa? A: Duk wani jini da mai haihuwa za ta gani bayan cikan jinin haihuwarta har zuwa kwanaki goma bayan haka to jinin lstihala ne, shin yana da siffofin jinin haila ko ba shi da shi, haka ma shin a cikin kwanakin al’adarta ne ko ba’a cikinsa ba ne. T: Shin wasu abubuwa ne suka wajaba kan mai jinin haihuwa na hukumce-hukumce? A: Dukkan abubuwan da suka wajaba kan mai haila na hukumce-hukumce ya wajaba kanta shin na wajibai ne ko mustahabai ko “makruhai” ko na haramun [har da haramcin karanta ayoyin da ake musu sujada na daga surorin sujjada, da shiga masallatan Makka da Madina ko da kuwa wucewa ne, da shiga sauran masallatai amma ban da wucewa ta cikinsu kana da kuma ajiye wani abu a cikin masallatai] Dubi Tattaunawa kan haila don karin bayani. * * * * * |
||