TATTAUNAWA KAN JININ HAILA

 

A wannan rana ma Babana ya hau kujerarsa da a ka tanadar masa a dakin tattaunawa, yana dan murmushi wanda haka ya sanya na yi tsammanin cewa akwai wani bakon abu da zai fada, sai ya zauna don ya fara:

- Yau zan yi maka bayani ne a kan “Haila”.

Kafin wannan rana ban san me Haila take nufi ba, koda yake zan iya tunawa na taba jin wannan kalma kafin wannan lokaci…koda yake ban damu kaina in san ma’anarta ba…na taba jinta a wajen mata amma cikin kunya…ana anbatonta a sannu kana kuma cikin sauri kamar cewa akwai wani abin kunya a cikinta…koda na tabbatar cewa an fara bayani kan haila, sai na ji kunya ya kama ni kana sai na tanbayi kaina: me yasa ne ma kunya ke damu na har ma yake zuwa min…wannan tambayar ta ci gaba da zuwa min …matuka, me yasa ake kula da wannan kunyar har take zuwa nan.

Wannan tunanin ya ci gaba da zuwa min…idan da gaske magana kan haila abin kunya ne, to me ya sa Babana zai yi magana a kansa a wannan rana…. Kana me ya sa yake min bayani kan abin kunya…. Ai da zai yi kyau kada kowa ya yi magana a kansa.

Daga baya sai na tuna cewa fa….dukkan batutuwan da muke tattaunawa a kansu sun shafi hukumce-hukumcen shari’a ne, saboda haka kuwa to dole haila ta kasance wani al’amari ne da fikhun musulunci zai yi magana a kansa, in kuwa al’amarin haka yake, to ina amfanin mu ji kunyan magana kan al’amarin da al-kur’ani mai girma ya ambata kuma manzon Allah (S.A.W.A.) ya yi bayani akai sannan ma’asumai (a.s) suka yi bayani kan hukumce-hukumcensa ga sahabbansu, kana bayan haka mene ne amfanin jin kunyan al’amarin da wajibi ne mu kiyaye hukumce-hukumcensa don mu aikata

Sai na tsinkayi muryar Babana yana cewa:

- Abin da ke jawo haila shi ne, fitar jinin haila, shi ne kuwa wani jini da mata suka saba da shi kana kuma suka san shi, sau da dama yakan fito a wani lokaci na kowani wata ana siffanta shi da cewa launinsa “Ja” ne wani lokaci yana kama da (baki) yana da (dumi) mata suna jin (zafi yayin fitansa).

T: Shin akwai wani takamammen shekara ne da mace za ta kai kafin ta fara haila?

A: Na’am, sai ta cika shekara tara na rayuwarta sannan kada ta wuce shekara sittin wadda shi ne shekarar da mata suke daina haila.

T: Kenan tsakanin shekara 9 zuwa 60 kenan?

A: Na’am, duk wani jinin da yarinyar da ba ta kai shekara 9 ba za ta gani koda kuwa da kadan ne to ba jinin haila ba ne haka ma duk wani jinin da mace za ta gani bayan cikarta shekara 60 ba shi da hukumcin haila.

T: Jinin haila har zuwa kwana nawa yake yi yana zuba?

A: Mafi karancin kwanakin haila shi ne kwanaki uku wato da darare biyu a tsakaninsu kana mafi yawansa shi ne kwanaki goma.

T: Idan kuma bai kai kwanaki uku ba ya yanke?

A: To wannan jini ba jinin haila ba ne.

T:  To in kuma ya wuce kwanaki goma fa?

A: Ai haila ba ya wuce kwana goma.

T: Idan jini ya dauke wa mace har ta yi tsarki sai daga baya ya dawo bayan kwana tara fa?

A: Wannan jini (na biyu) ba haila ba ne domin kuwa dole ne kwanaki tsakanin haila da haila kada ya gaza kwanaki goma.

T: Yaushe ne mace za ta lissafa kanta a matsayin mai haila?

A: Idan jini ya zo mata a lokacin al’adanta na lokaci ko kuma gabannin lokacin al’adarta da dan karamin lokaci kamar kwana daya ko biyu.

T: Yaya mace take zama mai al’ada na lokaci?

A: Idan jini ya zubo mata sau biyu ko fiye a lokaci daya a watanni biyu ko fiye.

T: To idan mace ba ta kasance mai al’ada na lokaci ba fa, kamar yarinyar da jini ya fara zubo mata kenan ko kuma wacce ba ta da takamaimen al’ada (mudtariba), yaya za ta gane cewa tana haila?

A: Za ta lissafa kanta a matsayin mai haila ne idan wadannan abubuwa suka tabbata:

1-     Idan jinin yana da siffofin jinin haila wato launin ja ko baki-baki, dumi da kuma zafi yayin fita.

2-     Idan ta ga jini kana kuma tana da yakinin ci gaba da zubansa har zuwa kwanaki uku ko fiye.

T: Idan ta dauki kanta a matsayin mai haila saboda daya daga cikin wadannan abubuwa da suka gabata don haka sai ta bar sallah sai daga baya jinin ya yanke kafin cikan kwanaki uku kana ta tabbatar cewa ba haila take yi ba, to me ya kamata ta aikata?

A: Sai ta rama wadannan salloli da suka wuce ta.

T: Idan jinin ya yi kwanaki goma yana zuba ko ya gaza haka ko kuma ya wuce kwanakin al’adarta fa?

A: Za ta dauki kanta a matsayin mai haila duk tsawon wadannan kwanakin da jinin yake zuba koda kuwa wasu jinin sun rasa siffofin haila.

T: To idan jinin ya wuce kwanaki goma kana ita macen ta kasance mai takamammen al’ada ta lokaci da adadi ce fa?

A: Ana daukanta a matsayin mai haila ne a kwanakin al’adarta kawai ba tare da la’akari da abin da ya gabaci aladarta ko kuma ya biyo bayan kwanakin aladarta ba.

T: Mace mai takamaime al’ada idan ba ta ga jinin ba akan lokacin al’adarta sai bayan lokacin sai jinin ya zubo kana ya ci gaba har ya wuce kwanaki goma sannan wasu jinin na dauke da sifar haila wasu kuma basa dauke da shi, to wanne ne daga cikinsu haila?

A: Na farko daga cikinsu, amma ta lura da adadin al’adarta da ta gabata idan wanda yake da siffafin haila din ya gaza adadin kwanaki al’adarta to sai ta cika adadin da wanda ba shi da siffar hailar, idan kuwa wadda yake da siffar haila din ya wuce adadin kwanakin al’adarta to sai ta dauki adadin kwanakin al’adarta a matsayin hailar kawai.

T: Idan jinin ya wuce kwanaki goma kana ita macen kuma ba ta da takamaimen al’ada kamar wacce ta fara, ko wacce ba ta da takamammen al’ada ko kuma mai kokwanto to yaya za ta iya bambamce jinin haila da waninsa?

A: Za ta iya hakan ne ta hanyar banbancin siffa, idan jinin da ya zuba yana da siffar haila kana kuma yana tsakanin kwanaki uku zuwa goma ne sai ta dauke shi haila sauran kuma jinin istihala ne wannan zan maka bayani a kansa nan gaba.

T: To idan mace ta yi shakka kan daukewar jinin haila fa? Wato ta yi shakkar shin ta sami tsarki ko kuma har yanzu tana cikin haila?

A: Dole ne ta yi bincike.

T: Yaya za ta yi binciken?

A: Ta hanyar sanya auduga wurin fitan jini kana ta bar shi na wani lokaci sannan ta ciro shi idan ya kasance fari a bushe to ta samu tsarki sai ta yi wanka kana ta zo da ibadun da suke kanta kamar sallah, azumi misali…idan kuwa ya baci da jini to har yanzu dai tana cikin haila.

T: Idan mace ta san tana haila, me za ta yi? Kana wasu abubuwa ne za ta bari?

A: Ga hukumce -hukumcen mace yayin haila kamar haka:-

1-     Sallah ba ta inganta a gare ta…shin sallar wajibi ne ko na mustahabbi.

2-     Ba za ta rama abin da ya tsere mata na daga salloli lokacin da take haila ba.

3-     Azumi ba ya inganta a gare ta.

4-     Za ta rama abin da ya tsere mata na daga azumin watan Ramalana lokacin da take haila [haka ma azumin bakancen da yake da takamammen lokaci].

5-     Dawafi lokacin aikin hajji bai inganta a gare ta…shin na wajibi ne ko na mustahabi.

6-     Sakinta baya inganta lokacin da take haila sai dai a wasu lokuta kebantattu.

7-     Ba ya halatta a sadu da ita ta gaba lokacin da take haila, amma yana halatta bayan daukewansa gabannin wanka [bayan ta wanke farjinta].

8-     Yana haramta a gare ta duk abin da ya haramta ga mai janaba (dubi Tattauna kan Janaba).

9-     Yana wajaba a gare ta ta yi wanka saboda sallah idan jinin haila ya dauke mata (Zan maka cikakken bayani kan yadda ake wanka a tattaunawarmu ta gaba).

*  *  *  *  *

عنوان الکتاب