TATTAUNAWA KAN JANABA |
||
|
Da farko Babana ya riga ni zuwa wannan zama namu na tattaunawa ba kamar yadda ya saba ba. Koda na iso Babana bai ma lura da zuwana ba… ya kasance shiru kansa a sunkuye yana tunani? Yadda zan fuskanto wa tambayoyi da za su bijiro da kuma yadda zai bullo wa wannan karamar zuciya ta yara. Ba’a jima ba sai ga idanunsa sun dawo da kyakkyawan sifofinsu, sai ya juyo gare ni yana mai cewa: Zan fara maganata ce da gabatarwa wadda za ta kai ni ga tattaunawarmu ta yau…zuwa tattaunawa kan Janaba. Sai ya dan sunkuya. - Na yi maka bayani cikin (Tattaunawa kan Najasa) dangane da najasosi, wadannan da suke kawar da tsarkin da ke jikimmu da kuma jikunan sauran abubuwa, wanda da suka kasance tare da shi. Sannan na yi maka bayani cikin (Tattaunawa kan abubuwa Masu Tsarkakewa) dangane da abubuwan da suke tsarkake najasa, wadannan da suke mayar wa jikunammu da jikunan abubuwa a karo na biyu da tsarkin da suka rasa. Da za ka yi dubi ga (najasosi) za ka ga cewa su din nan wasu abubuwa ne da suke bijiro wa jiki daga gare shi ko kuma daga wani abu. Kana kuma akwai wasu abubuwa na ma’ana wadanda ba’a iya riskarsu wadanda idan ka aikata su to suna iya tafiyar wa mutum da tsarkin da yake da shi, kuma daga nan yana bukatan wani abu da zai dawo masa da wannan tsarki nasa da ya gushe da kuma kyakkyawan yanayinsa da ya rasa. Wannan abu (Hadasi) ya kasu kashi biyu… babba da karami. Babban Hadasi: su ne kamar, janaba,Jinin haila da haihuwa, Jinin lstihala mai yawa, taba jikin mamaci da kuma mutuwa. Amma karamin Hadasi: su ne kamar, fitsari, bayan gida, tusa, barci, Jinin lstihalan da ba shi da yawa da dai sauransu. Shi “Babban Hadasi” (wanka ne yake gusar da shi ko kuma Taimama) Amma karamim Hadasi kuwa alwala ne yake gusar da shi ko kuma taimama shi ma. A tattaunawarmu da za su zo nan gaba za mu yi dubi cikin wadannan daya bayan daya, yau za mu fara da “Janaba” ne. Sai na ce wa Babana: T: Yaya ne Janaba take samuwa? Sai ya ce: A: Tana samuwa ne ta hanyar daya daga cikin wadannan al’amurra guda biyu: Na farko: fitar ruwan maniyyi shin ta hanyar jima’i ne ko ta mafarki ko kuma ta wata al’ada boyayyiya ko kuma ta wata hanya daban. T: Mene ne siffofin wannan ruwa na maniyyi? A: Ruwa ne mai kauri, warinsa kamar warin garin da aka kwaba, yana da launi na madara koda yake wani lokaci yakan karkata zuwa launin rawaya ko kuma kore-kore sau da yawa yakan fito ne lokacin da sha’awar mutum ta kai wani matsayi yakan fito da tunkudowa kana gajiya ya biyo baya. T: To me mutum zai yi idan yana shakkan cewa shin wannan ruwa mai kauri da ya fito masa maniyyi ne ko kuma wani ruwa ne daban? A: Bari in ba ka wasu alamomi guda uku: wadanda idan har ya hada su duka ukun to wannan ruwa maniyyi ne. Wadannan alamu kuwa su ne: Jin dadi, fitowa da tunkuda da kuma mutuwar jiki. Amma ga mara lafiya kuwa jin dadi kawai ya wadatar. T: To idan daya daga cikin alamun ne ko kuma biyu suka samu fa? A: To ba ruwan maniyyi ba ne amma ban da mara lafiya kamar yadda muka fada a baya. T: Shin mace ma tana da ruwan maniyyi kamar namiji? A: Na’am ruwan da yake fitowa daga farjinta yayin da sha’awarta ta kai wani matsayi lokacin jima’i ana hukumta shi da hukumcin ruwan maniyyi irin na maza shin tana barci ne ko kuma a farke. Abu na biyu: Jima’i koda kuwa bai kai ga fitan maniyyi ba. Jima’i yakan tabbata ne ta buyan kan za kari (hashafa) a cikin farjin mace ko bayanta. T: To idan ruwan maniyyi ya fito ko kuma aka sami tabbatuwar jima’i fa? A: To Janaba ta tabbata, ga wanda ya yi da kuma wanda aka yi masa ba tare da wani banbanci ba tsakanin yaro da babba, mai hankali da mahaukaci ko kuma rayayye da mahaukaci. T: To me mutum zai yi idan ya sami janaba? A: To wanka ya wajaba a gare ka don saboda yin sallah-misali-ko kuma yin dawafi lokacin aikin hajji. Domin kuwa ingancin sallah da dawafi ya ta’allaka ne da wannan wankan, nan gaba cikin (Tattaunawa kan Wanka) zan maka cikakken bayani yadda za ka yi wanka. Kana kuma matukar kana da janaba wadannan abubuwa sun haramta maka: 1- Shafan rubutun al-kur’ani mai girma. 2- Shafan sunan “Allah” mai girma [da sauran sunayensa da siffofinsa da ya kebantu da su kamar al-khalik”]. 3- Karanta aya da ake mata sujada na daga cikin surorin nan guda hudu masu girma wato (surorin lkra, an-Najm, as-sajdda al-fusilat). 4- Shiga cikin masallatai ko kuma zama a ciki, ko kuma daukan wani abu daga ciki ko kuma ajiye wani abu a ciki [koda kuwa daga waje ne ko kuma yayin wucewa a cikinta]. Ya halatta ga mai janaba ya wuce ta cikin masallaci misali ya shiga ta wata kofa kana ya fita ta daya kofar in ban da masallatan nan guda biyu masu girma wato masallacin ka’aba da ke Makka da kuma masallacin Annabi da ke madina [wannan hukumci na masallatai ya hada har makabartu masu tsarki na “ma’asumai” (a.s)] T: Shin wannan hukumci ya hada har gefe-gefe da harabar masallaci koda yake su din ba masallaci ba ne, wato haramun ne a shiga cikinsu. A: A’a ban da su. - Tambayi duk abin da kake so kada ka ji kunya domin babu kunya kan al’amarin addini, kamar yadda na sha gaya maka. T: Wani lokacin bayan sha’awa ta taso min na kan ga wani farin ruwa mara kauri yana fitowa daga za karina? A: Na’am wannan ruwan mai tsarki ne baya najasta tufafi ko jiki, kuma bai wajaba a gare ka ka yi alwala ko wanka ba lokacin da ya fita, sannan akwai wani ruwan ma da yake fitowa wani lokaci bayan fitsari, to shi ma mai tsarki ne baka bukatan wanka ko alwala in ya fito. T: To mutum ya fitar da maniyyi da kansa fa? A: Fitar da maniyyi da kanka haramun ne, wajibi ne ka nisance shi, an ruwaito daga Imam sadik (a.s.) cewa yin haka yana dai-dai da yin zina!! * * * * * |
||