TATTAUNAWA KAN TSARKI

Kafin mahaifina ya isa wurin wannan tattawnawa namu, na kasance cikin tunani mai zurfi ina kokarin in aikata abubuwan da na karanta ….wadancan abubuwan da suka wuce cikin "Tattawnawarmu kan najasa"-kan abubuwan da suke wanzuwa a wannan rayuwa da muke ciki, kana da kokarin gyara kura- kuren da ake yi kan najasa ta wannan hanya, ina mai kwadayin cewa zamanmu na yau zai yi magana kan yadda za'a iya dawo wa abu da tsarkinsa bayan najasa ta shafe shi kana kuma taba ta shi.

Koda mahaifina ya iso sai na fara da:

T : Jiya ka ce min abubuwa masu tsarki su kan rasa tsarkinsu lokacin da suka shafi najasa. To yaya wadannan abubuwa za su iya dawowa da wannan tsarki da suka rasa?

A : Abin da ya fi dawo ga abubuwan da suka najastu da tsarkinsu na farko da suka rasa, shi ne "ruwa" wato ko ka wanke inda ya najastu daga jikinka ko kuma ka wanke abin da ya najastu da shi, don haka za mu fara da… "al-Mutahhir" (Mai tsarkakewa) na farko: Ruwa.

Babana ya ci gaba da cewa:

-         Ruwa: "al- Mutlak" da "Mudaf".

T: Mene ne ruwa "al- Mutlak"?

A: Ruwa: " al-Mutlak"…shi ne wannan ruwa da muke sha, kuma dabbobi ma suke sha kana kuma ake shayar da tsirrai…ruwan da ke kewaye da mu, koguna, koramai da rijiyoyi.

Ruwan sama, ruwan fanfo wanda yake isowa gare mu daga rumbunan da ake tara ruwa a birane da alkaryu, kana kuma ruwa yana tabbata akan "mudlak" dinsa koda kuwa ya dan hadu da tabo ko laka kamar ruwar koramai da masu gudu.

T: To ruwa "al-mudaf"fa?

A: Zaka iya gane ruwa "al-mudaf"daga karin wata kalma da ake yi wa kalmar ruwa a duk lokacin da ake so a ambace shi, misali, ruwan furanni, ruwan ruman, ruwan inabi, ruwan karas, ruwan kankana da sauransu. Koda yake idan da za ka lura wadannan misalai ba sune abin da suka dame mu ba a nan,mu dai a nan muna magana ne kan wancan ruwan da za mu iya tsarkake abu da shi kana kuma mu sha, muna magana ne kan ruwa ba wai akan ruwan ruman ko ruwan inabi da makamancinsu ba.

Kana ruwa ko kuma ruwa "al-mutlak" ya kasu kashi biyu: "al-mu'utasim" da "gairu mu'utasim.

T: To me ruwa"al-mu'utasim" yake nufi?

A: Ruwa"al-mu'utasim" shi ne ruwan da baya najastuwa daga saduwarsa da najasa sai dai in daya cikin launi, dandano ko kanrshinsa ya jirkita Amma ruwa "gairu mu'utasim" kuwa shi ne ruwan da yake najastuwa da saduwarsa da  najasa koda kuwa daya daga cikin siffofinsan nan guda uku bai canza ba.

T: To wasu ruwa ne "mu'utasimai"?

A: Su ne:-

1-     Ruwa mai yawa: shi ne duk ruwan da ya kai gwargwadon "al-kur" wato ruwan da zai cika tankin da fadinsa da sama da kasansa yakai taki (na hannu) 36, kamar ruwan famfo wanda yake isowa ga gidajemmu daga manya -manyan rumbunan ruwa da ake samu a birane, ko kuma dam- dam, da kuma ruwan tankunan da ake dorawa a kan gidajemmu in har ya kai matsayin "al-kur", da kuma ruwan kananan rumbunan (ruwa) in har sun hadu da ruwa mai gudu kana kuma babu wani abin da ya raba su.

2-     Ruwan rijiya

3-     Ruwa mai gudu: kamar ruwan koramai, koguna da sauran idanuwan ruwa.

4-     Ruwan sama lokacin da yake sauka

 Waddannan su ne ruwa "mu'utasimai".

T: To waddanne ne ruwa waddanda ba "mu'utasimai ba?

A: Su ne ruwa da ke cikin wajen tara ruwa karami, kwanuka, kofuna da makamantansu na ruwa da suke tsaye guri guda amma ban da rijiya, wadanda basu kai gwarwadon "al-kur" ba ana kiransu da sunan "al-maul kalil" (Ruwan da ba shi da yawa).

Sannan daman mun riga mun san cewa suna najastuwa da zarar saduwarsu da najasa.

T: To ruwa "al-mudaf" fa?

A: Hukumcinsa daya yake da hukumcin Ruwan da ba shi da yawa wato yana najastuwa matukar ya shafi najasa shin yana da yawa ko ba shi da shi kamar ruwan shayi. Wannan hukumci ya hada har da sauran abubuwa masu ruwa-ruwa kamar madara, fetur, ruwan magani da sauransu wato sukan najastu da zarar sun taba najasa.

Sai Babana ya ci gaba da cewa:

Duk wani "maul-kalil"da ya hadu da ruwa mai yawa to ya zama ruwa mai yawa kana ya zama"mu'utasim" matukar haduwar tasu ba ta yanke ba, kenan karamin wajen ajiye ruwa ya kan zama "Ruwa mai yawa" idan ya hadu da idanuwan ruwa masu gudu hakanan dan ruwan da ake sanyawa a wajen wanki idan aka bude masa ruwan da ke hade da "al-kur" wato wannan ruwa ya hadu da wannan ruwa to yakan zama "Ruwa mai yawa, amma hakan yana yiyuwa ne idan har wannan haduwa yana nan.

T: Da kyau…to me zai faru idan digon jini ya digu a cikin ma'ajiyin ruwan da yake tsaye wanda ya kai gwargwadon "kur"?

A: Baya najastuwa sai idan digon jinin ya yi yawa ta yadda har ya canza launin ruwa saboda yawan jinin.

T: To in kuma a cikin karamin kwano ne ya diga fa?

A: To a nan kan kwanon ya najastu.

T: To idan muka hada shi da ruwa mai yawa har ya koma launinsa na asali fa?

A: To a nan ruwan kwanon ya kan tsarkaka [amma ya kan komo ya najastu idan ya rabu da wannan ruwa mai yawa kamar yadda za ka zo ka gani cewa idan kwano ya najastu to ba ya tsarkaka kuwa sai an wanke shi sau uku].

T: Da za mu bude ruwan buta a kan wani abin da ya najastu, shin ruwan butar ya najastu?

A: A'a, domin najasar ba ta tashi zuwa hanyar butar da ruwan yake zubowa kasa, babu daya daga cikin hanyar butar ko ruwan butar da ya najastu.

T: To yaya ruwan sama yake tsarkake abubuwa?

A: Idan ya zuba a kansu. Shin wannan abu mai najasa kasa ne, ko tufafi ko taburmai (abin shimfidawa a tsakar daki, da sharadin ya ratsa cikinsa ko kuma kwanuka da makamancinsu da sharadin cewa za'a iya kiran wannan abin da yake saukowa da sunan ruwan sama ban da irin yayyafin da ba za'a kira shi ruwan sama ba.

T: Shin zuban ruwan sama sau daya ya kan wadatar wajen tsarkaka abu?

A: Na'am ya kan wadatar amma ban da jiki ko tufafi wadanda suka najastu da fitsari domin su wajibi ne a wanke sama da sau daya [haka ma a kwanuka].

T: Shin ruwan sama yana tsarkake ruwan da ya najastu?

A: Na'am idan har ya cakuda da shi.

T: Yaya za mu tsarkkake abubuwan da suka najastu da "Ruwa kadan ko mai yawa?

A: Zamu iya tsarkake duk wani abin da ya najastu…duk wani abu ta hanyar wanke shi da ruwa kadan ko mai yawa sau daya amma da ruwa kadan an wajabta raba ruwan tsarkin da abin da yake da najasa.

T: Shin duk abubuwan da suka najastu ta haka ne ake tsarkake su?

A: Na'am amma ban da wadannan abubuwan:

1-     Kayayyakin girki da cin abinci kamar kwanuka da kofuna da sauransu da suka najastu da giya,to wadannan za mu wanke su ne da ruwa sau uku.

2-     Kayayyakin girki da cin abinci da bera ya mutu a ciki ko kuma alade ya ci abinci a ciki ko ya lasa, to anan za mu wanke su sau bakwai.

3-     Abubuwan da suka najastu da fitsarin jariri ko jaririyar da basu fara cin abinci ba, to a nan za mu zuba masu ruwa ne ta yadda zai mamaye ko ina, ba bukatar wani abu sama da haka.

Ba lalle ne sai an matse ba idan abin da ya najastu tufafi ne ko makamancinsa.

4-     Kayayyakin girki da cin abincin da kare ya yi lallaga a ciki koya lasa da harshensa, da farko za ka goge su da kasa kana ka wanke sau biyu da ruwa. Amma idan yawun bakinsa ya zuba a ciki ko kuma ya shafe su da sauran gabobinsa [ya wajaba da farko a goge su da kasa kana a wanke da ruwa sau uku.]

T: Mene ne lallagar kare?

A: Shi ne yadda yake shan abu da kan harshensa a cikin kwano.

5-     Tufafin da ya najastu da fitsari, za ka wanke su sau daya in "Ruwa mai gudu" ne, ko kuma sau biyu in ruwan ya kai "al-kur" ko ruwan famfo ne, haka ma in ruwan "maul kalil" ne shi ma sau biyu kana kuma a matse su. Amma tufafin da suka najastu da abin da ba fitsari ba, imma ka wanke su da "al-maul kalil" sau daya kana ka matse ko kuma ka wanke da "Ruwa mai yawa" ba tare da lalle sai ka matse ba.

6-     Jikin da ya najastu da fitsari za ka wanke shi ne kamar yadda ya gabata, amma idan wankin da "al-maul kalil" ne to dole ne a kawar da ruwan da aka yi tsarkin da shi daga jiki ta hanyar da aka sani.

7-     Cikin kwanuka, idan ya najastu ne da abin da ba giya ba ko lallagar kare ko zubar yawunsa a ciki ko kuma shafansu da sauran gabobinsa ko kuma mutuwar bera ko kuma lallagar alade, to za mu wanke su ne sau uku idan da "al-maul kalil" ne haka ma idan da "Ruwa mai yawa" ko mai gudu ko ruwan sama [shi ma sau uku].

T: To bayan kwano fa?

A: Ana tsarkake shi ne ta hanyan wankewa sau daya koda kuwa da "al-maul kalil" ne.

T: To yaya zan yi wajen tsarkake tafin hannuna da ya najastu alhali kuwa ruwan da ke wajena "maul kalil" ne?

A: Idan hannun naka ba da fitsari ya najastu ba, to in ka zuba masa ruwa sau daya ya wadatar matukar ruwan tsarkin ya bar hannunka.

MAI TSARKAKEEWA NA BIYU: Rana.

T: Me take tsarkakewa?

A: Tana tsarkake kasa da dukkan abubuwan da aka tsayar a kanta na daga gine-gine da katangu, da tabarmai saidai ban da zare-zarensu.

[Amma hukumcin bai hada har da kofofi da katakai da bishiyoyi da ganyayenta, da tsirrai, da 'ya'yan itatuwa kafin a tsinke su da sauran abubuwan da suke tabbace akan kasa].ba

T: Yaya ne rana take tsarkake kasa da gine-gine?

A: To hanyar saukan haskenta a kanta (kasa da gine-gine etc) har ta bushe saboda hasken ranar da sharadin gushewar asalin najasan daga gare ta.

T: To yaya za mu tsarkake bushasshiyar kasa (mai najasa) da rana?

A: Sai mu zuba mata ruwa idan rana ya busar da ita to ta tsarkaka.

T: To ldan hasken rana ya sauka akan kasar da ta najastu da fitsari har ta bushe fa?

A: Ta tsarkaka matukar dai babu abin da ya saura na daga fitsarin.

T: To tsakuwa da turbaya ko laka, ko duwatsu wadanda akan kidaya su a matsayin wani bari na kasa, idan suka najastu da fitsari kana rana ta busar da su fa?

A: Sun tsarkaka.

T: To kusoshin da suke kafe a cikin kasa ko gini fa…?

A: [Hukumcinsa ba hukumcin kasa ba ne,don haka rana ba ta tsarkake shi].

  MAI TSARKAKEWA NA UKU: Gushewar asalin najasa daga cikin jikin mutum da kuma jikin dabbobi.

T: Ba ni misali akan hakan.?

A: Misali gushewar jini daga cikin baki, ko cikin hanci, ko cikin kunne, gushewa ne na asalin najasar.

Daga lokacin da jini ya gushe to bakin mutum ya tsarkaka, haka ma hanci da kunne da ido da sauransu ba tare da bukatuwa kan sai an wanke su da ruwa ba.

T: To jikin dabba…fa?

A: Suma haka nan ne, daga lokacin da jini ya gushe a bakin kaza to bakinta ya  tsarkaka, haka ma daga lokacin da jini ya gushe a bakin kyanwa to ya tsarkaka, da dai sauransu.

T: To shin allura (alluran da ake wa mara lafiya) tana najastuwa idan ta taba jinin jikin mutum ko dabba lokacin da aka tura ta cikin jikinsa?

A: A'a, ba ta najastuwa idan aka cira ta ba tare da ta baci da jinin ba, don kasancewar gamuwarta da jini kawai ba ta najastuwa.

MAI TSARKAKEWA NA HUDU: kasa…duk wani abin da za'a kira shi kasa to yana tsarkakewa, kamar dutse, tsakuwa, turbaya, da inda aka yi masa dabe da blok ko siminti amma ban da kwalta da makamancinsa, sannan dole ne kasar ta zamanto [busasshiya] kuma mai tsarki.

T: To yaya zan iya ganewa cewa tana da tsarki?

A: Matukar dai ba ka san cewa ta najastu ba to tana da tsarki, don haka tana tsarkakewa.

T: To me kasa take tsarkakewa?

A: Tana tsarkake cikin tafukan kafafu da takalma ta hanyar tafiya a kanta ko kuma gogewa da ita amma da sharadin cewa najasar da ke kafan ko takalmin ta gushe ne saboda tafiyar da aka yi a kanta ko kuma gogewan da a ka yi, wannan kenan idan dai an sami najasar ce daga kasa mai najasa ta hanyar tafiya a kanta ko kuma ta wani yanayi [Amma idan an samo najasar ce ta wani hali daban ba daga kasa ba to a wannan hali kasa ba ta tsarkake ta].

MAI TSARKAKEWA NA BIYAR: Bibiya.

T: Bani misali kan bibiya.

A: Misali kafirin da ake masa hukumci da najasa idan ya musulunta to ya tsarkaka, haka ma dansa karami ya tsarkaka (saboda bibiya) wanda da najasa ne saboda bibiya ga ubansa. Haka ma kakanni da uwa kafirai idan suka musulunta sun tsarkaka, haka ma yayayensu kanana (saboda biye musu) wadanda da najasa ne saboda bibiya ga najastuwan iyayensu, koda yake hakan yana yiyuwa ne idan shi karamin yaron yana tare da wanda ya musulunta din ne kana kuma yana karkashin kulawansa kana kuma ya zamanto babu wani kafirin da ya fi kusanci da yaron kamar shi.

Idan giya ta juya ta koma ruwan inabi to ta tsarkaka, kana (saboda bibiya) kwanon da giya yake ciki ma ya tsarkaka.

Mamaci bayan an yi masa wankan nan guda uku ya tsarkaka, da gadon da aka yi masa wanka dasu sun tsarkaka (saboda biye masa).

Tufafin da ya najastu idan misali aka wanke shi da "al-maul kalil" ya tsarkaka, kana (saboda bibiya gare shi) hannun da ya wanke shi ma ya tsarkaka.

MAI TSARKAKEWA NA SHIDA: Musulunci.

T: Shin yaya musulunci yake tsarkakewa? Kana kuma wa yake tsarkakawa?

A: Musulunci yana tsarkake kafirin da ake masa hukumci da najasa lokacin da ya musulunta, ya kan tsarkake shi kansa, kana kuma ya tsarkake (saboda bibiya gare shi) gashinsa, faratunsa da sauran gabobin jikinsa wadanda suka kasance najasa saboda kafircinsa.

MAI TSARKAKEWA NA BAKWAI: Buyan musulmi baligi ko yaro mai banbancewa.

T: Me ake nufi da buyan musulmi?

A: Shi ne hakikaninsa ya rabu da kai ta yadda idanuwanka su basu gan shi ba.

T: To idan ba ka ganinsa fa, sai mene?

A: In ba ka ganinsa ya tsarkaka, to kayayyakinsa sun tsarkaka tare da shi kamar tufafinsa haka ma abubuwan shimfidansa, da kayayyakin girki da cin abincinsa da sauran kayayyakinsa idan har kana da tsammanin cewa ya tsarkake su.

T: Bani misali a kan hakan?

A: Misali, tufafin' dan 'uwanka ya najastu shin ya sani ko bai sani ba amma kai dai ka san hakan, to shin shi mai kula da hukumce hukumcen shari'a ne ko kuma ba ya kula…kana bayan haka sai ya yi tafiya, daga baya sai ya dawo to in har kana da tsammanin cewa ya tsarkake tufafin nasa to a wannan hali sai ka dauka cewa tufafin dan'uwan naka masu tsarki ne.

Za ka kudure hakan ne ba tare da lalle sai ka tambaye shi ba.

MAI TSARKAKEWA NA TAKWAS: Ciruwa.

T: Misali?

A: Jinin mutum -misali-wanda kwarkwata da kudin cizo da sauran kananan kwarin da basu da jini suka sha kana ya zauna a cikinsu, kana yayin kashe wannan dabba sai wannan jinin ya zuba maka a jiki ko tufafi, to wannan jinin mai tsarki ne.

MAI TSARKAKEWA NA TARA: Al- lstihala

T: Mene ne al-lstihala?

A: Al- lstihala: Shi ne canjin wani abu zuwa wani abu daban da ba irinsa ba, juyawa ta sosai ba kawai  canjin sunansa ko siffansa ko kuma rarrabuwan shi ba.

T: Ba ni misali a kan haka.

A: Katako mai najasa-misali- idan aka kona shi ya koma toka, to wannan toka mai tsarki ne. Haka abubuwan da ya saura na daga dabbobi idan a ka kona shi da wuta, to tokansa da ya saura a murhu mai tsarki ne, da dai sauransu.

MAI TSARKAKEWA NA GOMA: Fitar jini gwarg-wadon da aka saba daga jikin dabban da aka yanka ta hanyar shari'a, a wannan lokacin saura jinin da ya saura a jikin dabbar za mu hukumta shi da tsarki.

MAI TSARKAKEWA NA SHA DAYA ! Juyawan giya zuwa ruwan inabi, domin kuwa yayin  girka ruwan inabi akwai wani lokacin da yake zama giya ya najastu kafin daga baya ya juya ya koma ruwan inabi ya tsarkaka.

MAI TSARKAKEWA NA SHA BIYU: lstibra'I (tsarkake) dabba mai cin kazanta:

Idan dabban da ake cin namanta ta saba cin bayan gidan mutum to namanta ya haramta, haka ma shan nononta, kana kuma fitsari da bayan gidanta da gumin jikinta najasa ne.

T: Yaya ake yin "istibra'I" ga dabba mai cin bayan gidan?

A: Ta hanyar hana ta cin najasa har na tsawon lokacin da za'a daina kiranta da dabba mai cin bayan gidan, inda za ta zama dabba yadda aka saba.

T: To daga nan fa?

A: Daga nan bayan "lstibra'I"za'a hukumta namanta, nononta da duk sauran abin da suka gabata a matsayin masu tsarki.

*  *  *  *  *

عنوان الکتاب