TATTAUNAWA KAN NAJASA

 

Babana ya fara maganarsa ne yana cewa:

Bari in gaya maka wata ka'ida ta gaba daya wanda za ta taimake ka a duk rayuwarka, ita ce kuwa cewa "kowani abu mai tsarki ne" dukkan komai…koguna, ruwan sama, koramai, bishiyoyi, hamada, duwatsu, tituna da gine -gine da kayayyakin ayyuka, tufafi kala-kala da 'yan 'uwanka musulmai… da… kowani abu, mai tsarki ne…

Dukkan wani abu sai dai ya najastu, ban da…

T: Banda me?

A: Ban da abin da najasa ne a dabi arsa, a yanayinsa, a zatinsa (a asalinsa).

T: Wani abu ne najasa a dabi''arsa, a zatinsa?

A: Abubuwa guda goma ne, yanzu zan lissafa maka su a jere:

"1 da 2 " fitsarin dan'adam da bayan gidansa. Da kuma fitsari da bayan gidan duk wata dabban da aka haramta namanta, idan har wannan dabba "mai “nafsun sa’ila” ce kamar kyanwa.

[haka ma fitsarin dabbar da ba mai"nafsun sa'ila" ba ce amma tana da nama].

T: Mece ce "an- nafsus saila"?

A: Wannan wata kalma ce da za ka yi ta jinta a wannan tattaunawa, zai yi kyau in dan kara maka wani haske.

Muna cewa: Wannan dabba mai"nafsun saila ce…idan jininta yana fitowa da karfi lokacin da aka yanka ta, saboda hanyoyin jini da take da shi.

Kana muna cewa: Wannan dabba ba mai"nafsu saila" bace…idan jinin da yake fitowa lokacin yanka yana fitowa a hankali ne, haka kuwa saboda ba ta da manyan hanyoyin jini kamar, kifi.

1-     Mushen dabbar da take mai"nafsu saila" ce koda kuwa namanta halal ne, haka nan ma duk wani bangare na jikinta mai rai da aka yanke.

Shin mene ne mushe?

- Shi ne duk wata dabbar da ta mutu ba tare da an yanka ta ba yanka irin ta Shariar musulunci.

T: Kamar misalin?

A: Kamar misalin dabbar da ta mutu saboda rashin lafiya, ko kuma saboda wani abu, ko kuma an yanka ba ta hanyar da ya dace da shariar musulunci ba, duk wadannan mushe ne.

T: Idan mutum ya mutu shin jikinsa yana zama najasa ne?

A : Na'am sai dai shahidi da kuma wanda aka yi masa wanka bayan an tsayar da haddi a kansa ko kuma "kisasi" a gare shi.

T: Shin sauran (matattu) najasa ne kenan?

A: A'a, ana tsarkake jikin matacce musulmi da yi masa wankan nan guda uku wadanda zan yi maka bayaninsu a tattaunawarmu ta gaba.

2-     Maniyyin dan'adam, da kuma maniyyin duk wata dabba mai "nafsu saila" [koda kuwa wannan dabbar ana cin namanta a shar'ance].

3-     Jinin da ya fito daga jikin dan'adam da kuma duk wata dabba mai "nafsu saila".

T : To jinin dabbar da ba mai"nafsu saila" ba ce fa?.

A : Yana da tsarki kamar jinin kifi.

4-     Karen doron kasa tare da dukkan bangarorin jikinsa, shin yana raye ne ko bayan ya mutu.

5-     Aladen doron kasa da dukkan bangarori na jikinsa, yana raye ne ko bayan mutuwa.

T: Shin kare da aladen ruwa fa…?

A : Masu tsarki ne.

6-     Giya [ya hada har da burkutu]

7-     Kafiri, rayayye ko macacce amma ban da kirista, da bayahude da bamajuse.

8-      Gumin dabba "Jallala", ita ce dabbar da take cin bayan gidan mutum.

Wadannan abubuwa guda goma najasa ne a dabiarsu, kuma najasarsu tana komawa ga duk abin da ya shafe su ko kuma ya taba su ko ya goge su matukar dai akwai danshi a jikinsu.

T: To idan babu damshi a jikinsu fa?

A: Idan har babu danshi to najasar ba ta komawa ga wannan abu, domin kuwa najasa ba ta komawa ga wani, lokacin da take bushe ko kuma karamar danshi.

T: Shin fitsari ko bayan gidan dabbobin da namansu halal ne kamar saniya, tumaki, kaji, tsuntsaye daban-daban… najasa ne ko kuma ba najasa ba ne?

A : Ba najasa ba ne

T: To jemage…fa?

A : Ba najasa ba ne.

T: To gashi, faratu, kaho, kashi, hakwara na dabbobin da suka mutu fa?

A : Dukkansu masu tsarki ne.

T: To jinin da ke kan naman da muke saye don ci fa?

A: Wannan jinin ba najasa ba ne…duk jinin da ke saura daga baya, bayan yankan da aka yi a hanya ta shari'a ba najasa ba ne.

T: To bayan gidan gafiya da bera?

A: Najasa ne ba mai tsarki ba ne. Da ka yi dan tunani kadan kan abubuwan da na lissafa maka da ka iya amsa wannan tanbaya da kanka…gaskiya ne da ka iya amsawa da kanka, domin kuwa suna da babban hanyar jini wanda jini yake fitowa da karfi yayin yanka.

Sai babana ya koma da baya don ya dan taimaka min kan wannan haske da yake fuskanta ta a farkon tattaunawarmu, sai babana ya ci gaba da cewa:

- Tun farkon wannan tattawnawa na fara koya maka kaida ta gaba daya wadda take da tasiri a rayuwarka, to zan cika maka da wata kaidar ta gaba daya wadda ita ma za ta taimaka maka.

Ka'ida Ta farko: ko wani abu da daman can ya kasance mai tsarki ne a zamanin baya to yanzu ma mai tsarki ne ko da ka samu shakkun cewa shin bayan haka ya najastu ko kuma yana nan a kan tsarkinsa…to wannan abu mai tsarki ne.

T: Ban misali a kan hakan?

A: Misali idan mayafin barcinka da kasan yana da tsarki, sai daga baya ka fara shakka shin ya najastu ko a'a, to sai ka dauka mayafinka yana da tsarki.

Ka'ida Ta Biyu: Duk wani abu da daman najasa ne to najasa ne ko da ka samu shakkun cewa shin bayan haka ya tsarkaku ko kuma yana nan a najasarsa?

To wannan abin najasa ne.

T: Misali?…

A: Misali, kana da yakinin cewa hannunka ya najastu kafin wannan lokaci, sai daga baya ka fara shakkun cewa shin ka tsarkake hannun daga wannan najasa ko kuma baka tsarkake ba?

Sai ka dauka cewa: hannunka akwai najasa.

Ka'ida Ta Uku: Duk wani abin da baka da masaniya kan yanayinsa da ya wuce shin kafin wannan lokacin najasa ne ko kuma mai tsarki ne?

To mai tsarki ne.

T : Misali?

A : Misali ruwa ne a cikin kofi wanda ka jahilci yanayinsa da ya wuce, ba ka san shin ya najastu ko kuma mai tsarki ne, sai ka dauka cewa wannan ruwa mai tsarki ne.

Ka'ida Ta Hudu: Duk wani abin da kake shakka cewa, shin najasa ta shafe shi har ya najastu ko kuma ba ta shafe shi ba, to a wannan halin ba wajibi ba ne ka yi bincike don tabbatar da tsarkinsa. Kawai ka dauka cewa mai tsarki ne, ba tare da ka dami kanka wajen bincike da neman bayani ba, koda kuwa binciken yana da sauki a gare ka.

T : Misali?

A : Misali, kana da tabbacin tufafinka yana da tsarki, sai daga baya ka fara shakka shin fitsari ya shafe shi ya najasta shi ko kuma har yanzu yana nan da tsarkinsa?

A wannan hali…ba wajibi ba ne ka yi bincike kan tufafin naka, ko kuma neman ganin alaman fitsarin, koda kuwa binciken ba shi  da wahala a gare ka, kawai ka dauka tufafinka mai tsarki ne.

*  *  *  *  *

عنوان الکتاب