TAQLID |
||
|
Da farko - Bari in yi maka cikakken bayani kan ma'anar "Taqlid". "Taqlid": shi ne komawa ga wani fakihi (malamin fikhu) don aiki da fatawoyinsa, ka aikata abin da ya tsaya kan a aikata shi, kana kuma ka hanu da abin da ya hana, ba tare da wani tunani ko ka ce na ce ba, wato kamar ka sanya alhakin ayyukanka ne a wuyansa tsakanmka da Allah. T: To me ya sa za mu yi "Taqlid"? A: Daga abin da ya wuce ka fahimci cewa mai kafa dokoki (Allah) ya umurce ka kana kuma ya hana ka wasu abubuwa… ya umurce ka wasu abubuwa inda ya zama wajibi ka aikata su, kana kuma ya yi maka hani kan abubuwan da suke haramun inda ya zama wajibi ka nesance su, amma wasu abubuwa ne ya umurce ka da aikatawa kana wadanne ne ya hane ka? Hakika wasu abubuwan da ya umurce ka da su a fili suke a cikin sharia-watakila-za ka iya gano su daga abin da kake da shi, haka ma wasu abubuwan da ya hane ka a fili suke -watakila za ka iya gane su. Amma da yawa-da yawa tsakanin "wajibai" da "muharramai" za su saura a boye gare ka da kuma da yawa daga irinka. Babana ya ci gaba da cewa: - kai ka sani cewa shariar musulunci ya hade dukkan bangarorin rayuwa daban-daban, kana kuma ya sanya wa kowani al'amari hukumcinsa, yaya za ka iya gane hukum cinka kan al'amari lokacin da kake aikata abubuwa daban-daban na rayuwarka? Yaya za ka gane cewa wannan aiki shari'a ta halalta shi don ka aikata kana kuma wannan aikin shari'a ta haramta shi don ka nesance shi? Shin kana ganin za ka iya komawa ga Dalilan shari la (al-kur'ani da Hadisi) kan manyan al'amurra da kanana don ka ciro hukumce-hukumcensu?
- Ya dana, hakika zamaninka da zamanin da ake saukar da shari'a ya yi nisa, kuma wannan nisa dada karuwa yake, tattare da cewar da yawa daga wadannan nassosin" sun bata, ga kuma canje-canjen maganganu da kuma hanyar bayani, kana kuma ga samuwar masu sanya hadisan (karya)-su ne wadanda suka kirkiro hadisai masu yawa kana suka cakuda su da hadisan gaskiya wanda haka ya sa shari'a ta yi wahala. Kana wata mishikilan kuma ita ce amincin masu ruwaya wanda hakan ma ya zama wata katanga kan hanyar isa ga wannan manufa. Sannan mu dauka ma cewa ka samu daman iya tabbatar da hakan ta hanyar masu ruwayar nassi da gaskiyarsu, da kuma tsantsaninsu kan abubuwan da suka ruwaito da kuma haddarsu, sannan kuma ka iya ba ta lokaci don haddace abubuwan da suka shafi wannan al'amura shin za ka iya nitsawa cikin ilmi mai zurfi da fadi mai wahala wanda yake bukatuwa da mukaddimai masu yawa da kuma bincike mai zurfi, don ka gano wani abu daga gare shi ta hanyar ilminka kansa da kuma bincike a kansa da ka yi. T: To mene ne abin yi? A: Sai ka koma ga kwararru kan wannan ilmi wato (malaman fikihu) don karbo hukumcin -ka daga wajensu…(ka yi musu "Taqlid"). Hakan kuwa ba kawai a fagen ilmin fikhu ba ne, a'a a kowani ilmi ne. Hakika wayewa na wannan zamani ya kwadaita mana kwarewa kan ilmummuka, ta yadda aka wayi gari a kowani ilmi akwai ma'abutansu da kuma kwararru kansa waddanda ake komawa gare su a duk lokacin da bukatuwa ga wannan ilmi ya taso. Babana ya ci gaba yana cewa: T: Mu dauki ilmin likitanci a matsayin misali da a ce za ka yi rashin lafiya-Allah ya sauwake-to yaya za ka yi? A: Sai in nemi likita, in bayyana masa abin da ke damu na don ya gano ciwon kana kuma ya ba ni maganin da ya dace da wannan ciwo. T: Me ya sa kai da kanka ba za ka binciko ciwon ba kana ka ba wa kanka magani? A: Don ni ba likita ba ne. - To al'amarin haka yake kan al'amarin fikhu. Kana da bukatuwa da komawa ga kwararren "fakihi" don gano umurni da hanin ubangiji, ko kuma don bijiro da mishkilolinka na shari'a gare shi, dai-dai da yadda kake neman likita kwararre, don gano wani al'amarin da ya shafi likitanci ko kuma abin da ya shafi rashin lafiyarka. Kamar yadda kake bukatuwa da yin "Taklid" ga likita a inda yake da kwarewa haka kake bukatuwa da "Taqlidi" ga "fakihi" a inda yake da kwarewarsa. Haka kuma kamar yadda kake neman likitan da ya fi kowa, masani a bangaren kwarewansa musamman ma idan ciwon naka yana da hatsari, to haka neman kwararren fakihi kan abin da ya kware ya zama maka wajibi don ka yi "Taqlidi" da shi kana ka karbi hukumce-hukumcen shari'a daga wajensa a duk lokacin da wani hukumci ya shiga maka duhu. T: To yaya zan iya gane cewa wannan mutumin "fakihi" ne? ko kuma cewa wannan shi ne ya fi shahara? Sai Babana ya ce: A : Bari in tambaye ka…ta wace hanya kake gane cewa wannan likitan mashahuri ne ko kuma cewa shi ya fi dukkan likitoci kwarewa don ka je wurinsa, kana ka ba shi jikinka don ya aikata abin da ya ga ya dace da irin ciwonka? Sai na ce masa: - To ta haka din ne ma za ka iya sanin "fakihi" sai ka tambayi mutum wanda yake kula da wajibobinsa, kana mai nisantar abubuwan da aka hana, amintacce, wanda yake da iko, sani, ilmi, adili yana da kuma masaniya kan banbamce martabar ilmin mutane kan abubuwan da suka kware a kai. Ko kuma "fakihancin" mutum ko kuma fifikonsa tsakanin sauran "fukaha'u" ya watsu kana kuma ya yadu tsakanin jama'a ta yadda wannan bayyananniyar fifiko da kuma wannan yaduwarta tsakanin mutane zai dada tabbatar da "fakihancinsa" ko kuma fifikonsa. T: Shin akwai wasu sharudda kan wanda ya wajaba mu yi masa "Taqlid" ban da sharadin "fakihanci"? A: Dole wanda za ka yi masa "Taqlid" ya zamanto: namiji, baligi, mai hankali, mumini, adili, rayayye ba macacce ba, dan halal- kana kuma kada ya zamanto mai yawan kuskure, mantuwa da gafala. T: Da kyau, tun da ga shi yanzu na kai matsayin mutum, baligi kana kuma na gano wasu abubuwa daga wajenka kan "Taqlid", to yanzu mene ne ya zama wajibi in aikata? A: Sai ka yi "Taqlid" wa mafificin "fakihin" zamaninka, kana ka yi aiki da hukumcin da ya bayar kan abubuwan da suka shafe ka… misali kan al'amurran alwalanka, wankanka, taimamarka, sallarka, azuminka, aikin hajjinka, khumusinka, zakkarka da sauransu. Kamar kuma yadda za ka yi masa "Taqlidi" kan mu'amalolinka…kamar hukumce- hukumcen saye da sayarwarka, auratayyanka, aikin gonarka, ba da hayarka, jinginarka, wasiyarka, kyautarka…. Sai na ci gaba da kidayawa tare da babana… - A'a… imani da Allah da kadaita shi, da kuma imani da annabcin annabimmu Muhammad (S.A.W.A.) da imamancin imamai goma sha biyu (a.s) da ranar lahira… ba ya halatta a yi "Taqlidi" kan wadannan al'amura don kuwa su suna daga cikin "usulud-Deen" (Tushen addini) ne, kuma baya halatta a yi "Taqlidi" kan "usul-ud-Deen" sai dai wajibi ne kowani musulmi ya yi imani da su, karfafaffen imani da babu shakka a cikinsa, kana babu kokwanto ko fargaba ko taraddudi, kowa ya yi cikakken imani da Allah, zai iya yin haka ne ta hanyar kokarinsa da kuma ni'imar da Allah ya yi masa na ikon tunani wadda zai isar da shi ga cikakkiyar kwanciyar hankali da ba za ta taba girgizuwa ba… T: Da kyau… shin ya halatta in yi "Taqlidi" wa wani "fakihi" tattare da kasantuwan wanda ya fi shi a wannan bangaren? A: Za ka iya yin hakan amma da sharadin cewa ba ka san akwai banbanci ba tsakanin fatawar wanda kake yi masa "Taqlid" da fatawar "A'alam" (wanda ya fi fifiko) kan wannan al'amari da kake so ka aikata. T: Da a ce zan yi "Taqlidi" da A'alam, amma sai ya zamanto ba shi da fatawa kan abin da ya dame ni? Ko kuma yana da shi amma ba zan iya samun labari a kai ba, to yaya zan yi? A: Sai ka koma ga "A'alam" din da yake biye masa wato wanda yake biye masa wajen ilmi cikin "fukaha'u". T: To idan sauran (fukaha'u) dai-dai suke wajen ilmi fa, yaya zan yi? A: Sai ka koma ga wanda ya fi su tsantseni kan al'amura wato wanda ya fi tabbatuwa da kuma hangen nesa cikin ra'ayin da yake dauka da kuma fatowoyin da yake bayarwa. T: Idan kuma ya zamanto wasu ba su fi saura tsantseni ba fa? A: To za ka iya aikinka da fatawan ko wane daga cikinsu sai dai kawai a wasu ayyanannu lokuta ko hali inda ya zama wajibi ka yi amfani da "lhtiyad" a kansu koda yake lokaci ba zai bar ni inyi maka cikakken bayani ba. T: Da kyau… a fili yake cewa lokacin da na je wurin likita zan iya sanin ra'ayinsa kan lafiyata, to yaya zan iya gano fatawan wanda nake masa "Taqlid" akan al'amarin sharia? -Yaya zan iya isa ga fatawarsa don in aikata? Shin dole ne in koma gare shi kan kowace mas'ala? A: Za ka iya gano fatawarsa ne…ta hanyar tanbayarsa kai tsaye kan mas'ala, ko kuma ta hanyar tambayar wanda kake da tabbaci kan karbowarsa daga gare shi da saninsa kana kuma da gaskiyarsa wajen karbo wannan fatawa, ko kuma ta hanyar komawa ga littafinsa na fikhu kamar "Risalatul" Amaliyyarsa" (littafin fikhu kan al'amurran yau da kullum) idan har kana da kwanciyar hankali cewa babu kura-kurai a ciki. Sai Babana ya yi dan murmushi, kana ya dan gyara zama ko da yake fuskarsa tana ishara da zama na gaba. · Sai na ce: kan sallah za mu fara. - Sai ya ce: za mu fara da sallah. Ya kara da cewa: - Koda yake sallah tana bukatuwa da tsarkin mutum daga dukkan abin da yake bata tsarki. T: To mene ne abin da yake bata tsarkin mutum? A: Abubuwan da suke bata tsarkin mutum su ne: 1- Abubuwan da suke bijirowa saboda ayyukan gabobin dan 'adam kamar najasa. 2- Abubuwan da gabobi basa iya riskarsu in sun faru ta hanyar daya daga cikin dalilansu wadanda suke wajabta alwala, wanka ko kuma taimama kamar janaba, haila, istihala, jinin biki, shafan macacce, barci, fitar, fitsari ko bayan gida ko kuma tusa. Kafin mu juya akalan namu zuwa ga sallah za mu fara tattaunawar tamu kan al'amarin najasa, za mu fara da bayanin ma'anarta, kana bayan haka kuma mu gano abubuwa masu tsarkake najasa don mu tabbatar da tsarkin jiki daga dukkan wani abin da yake kawar da tsarki kuma ya kawar da tsabta. Kana kuma daga baya sai mu ci gaba da tattaunawa kan abubuwan da idan mutum ya yi "hadasi" abin da yake wajabta masa tsarki ta hanyar alwala ko kuma taimama, shin "hadasin" nan na daga fitsari ne ko bayan gida ko tusa ko barci ko lstihala kadan ko wanin ta. Kana kuma sai mu koma da baya, mu duba wani bangaren abubuwan da idan mutum ya yi "hadasi" za su wajabta masa tsarkake su da hanyar wanka ko taimama kamar in "hadasin" janaba ne ko haila ko lstihala ko jinin biki ko kuma taba gawa. Za mu daga duk wani abin da zai kawo mana cikas wajen kusanci da Allah madaukakin sarki daga hanyarmu ta hanyar sallah, bayan haka kuma mu samu babban rabon tsayawa gaba gare shi muna masu kabbara masu godiya masu samun nima da ambatansa da rokansa kuma masu kwadayin ya sanya mu daga cikin wadanda bishiyoyin kaunarsa za su girmama a gonakin zukatansu, kana kuma kaunarsa ta samu wajen zama a zukatanmu. Bayan sallah kuma mu yi dubi cikin abubuwan da tsarki na daga cikin sharadin aikata su kamar azumi, aikin Hajji da sauransu. - Na'am gobe za mu fara da ita lnsha Allah. * * * * * * * |
||