MUHAWARA TA FARKO WACCE TA HADO ABUBUWA DABAN DABAN

 

Abokin muhawara:- daga lokacin da mahaifina ya rabu da ni sai na taro shimfidaddun takardu dangane da umarni da kyakkyawa, da hani da mummuna na yi ban kwana, da su domin na cika muhawararmu ta fikihu, na abubuwa masu cin gashin kansu, kuma don na yi tanadin bude fagen muhawara ta musamman wacce za ta zo nan gaba, wacce kuma zan sanya wa muhawarar da tambayoyinta iyaka, da kuma inda muhawarar ta fuskanta kamar yanda mahaifina yai min alkawari.

Sa a daya ba ta karasa ba sai ga shi na tattara wasu tambayoyi, yankin farko na tambayar yana tattare da yin tambaya kan muhawara ta farko wacce ta hado abubuwa daban daban.

lokacin da waadin fara muhawara ya yi sai babana ya zo yai sallama ya fara da gode wa Allah da yabonsa, kana ya bude wannan muhawara wacce ta hado abubuwa daban, take na miko tambayoyina a gare shi da na nemi ya amsa su, tambayata ta farko a kan fatu wacce aka aikata ta aka zo da ita daga kasashen da ba na musulunci ba misali kamar kasashen turai, da makamantansu.

T: Wani mutum ya sa agogo wadda sarkar agogon ta fata ce wacce aka yi ta daga kasar da ba ta musulmi ba, wanda kuma yake sanye da ita bai sani ba, fatar ta kasance ne daga dabbar da aka yanka ta hanyar shara’a ko ko a’a, ko kuma bel na wandonsa wanda yake na fata shin wannan mutum wajibi ne a gare shi ya kwabe ta lokacin da zai sallah?

A: Sallarsa ta inganta muddun dai yana ganin cewa wannan fatar ko kuma bel din na fatar dabbar da ake ci ne wacce kuma aka yanka ta a hanyar shara’a.

T: To yaya kuma yar jakar da ake zuba kudi wacce ake sanya ta a cikin aljihu lokacin sallah idan ita ma fatarta daidai yake da fatar agogo wacce aka fada yanzu?

A: Sallah tana halatta da ita.

T: Mu dauka cewa mutum ya nutsu da ganin cewa fatar agogon ko bel din daga dabbar da aka yanka ba ta hanyar shara’a ba ne, sai dai kuma ya yi salla da ita da mantuwa kana sai ya tuna yana cikin sallar sai ya yi sauri ya cire yaya hukumci yake.

A: A irin wannan hali sallarsa ta inganta, sai dai in mantuwar tasa ta samo asali ne daga karancin kulawarsa, ko kuma rashin muhimmantar da abin, to a nan wa jibi ne ya mai da sallar.

T: Abin wanki na wutar lantarki yana busar da tufafi bayan an rufe ruwa bai zuwa masa, irin wannan busarwar tana faruwa ne saboda tsananin juyawa, amma badon wai an matse ba to shin hakan yana isa tufafi su tsarkaka?

A: I yana isa ta tsarkaka da haka.

T: Da yawa ina gaisawa da mutane a halin hannuna tana jike kana ban sani ba wanda muka gaisa da shi din musulmi ne ko kuwa kafiri ne wanda ba’a hukumta tsarki a tare da shi ba, shin yana wajaba a gare ni in tambaye shi domin na tabbatar?

A: Sam sam ba wajibi ba ne ka tambaye shi kana iya cewa kawai hannunka mai tsarki ce.

T: Dalibin jami’a ko dan kasuwa ko masu yawon shakatawa, ko makamantansu, suna zuwa kasashen da ba na musulunci ba, kamar kasashen turai wanda rayuwarsa ta yau da gobe ba yanda za ai ta kubuta daga cudanya da mazauna kasar, wato kiristoci da yahudawa, tare da danshin da ke isa zuwa gare shi, wajen mai shayi ko mai aski ko likita, ko mai gugar kaya, ko makamantansu, na daga wanda ba su lisaftuwa cikin sauki, to a nan meye abin yi?

A: Zai yi gini bisa tsarkakuwar jikinsu muddin bai tabbatar da najastuwar jikin da wata najasa daga waje ba.

T: Da zan shiga wani gida zuciyata ta sami nutsuwa cewar mutanen da ba ai musu hukumci da tsarki ba su ne da suke zaune a ciki shin yana cancanta na yi hukumci da tsarkakuwar kowanne abu?

A: E za ka yi hukumci da tsarkakuwar dukkanin wani abu da yake ciki, muddin ba ka sami nutsuwa kan cewar da najasa ba.

T: Bara kuma in koma sallah domin na yi tambaya kan mutumin da yake sallah kuma yana azumi sai dai kuma yana yawan yin wankan tsarki ba daidai ba, sai ga shi yanzu ya yi cikakkiyar tabbatawa kan cewa wasu daga cikin wankansa da ya yi ba daidai ba ne amma bai san ko nawa ba ne saboda dalilin haka ma bai san sallah nawa ce wacce ya yi ta ba daidai ba bai kuma san azumi nawa ne ya yi ba daidai ba to ya hukumci yake?

A: Azuminsa ya inganta amma wankansa batacce ne, sai dai ya wajaba a gare shi ya rama sallar da ya yi da wankan da ba daidai ba, idan kuma yai kokwanto kan sallar tsakanin adadi biyu, wanda daya adadin bai kai yawan dayan ba to ya halatta ya takaita ramakon a kan adadi kadan din.

T: Wani lokaci ina son yin sallah a cikin aljihuna akwai fararen takardu, shin ya halatta na yi sujuda a kai?

A: I ya halatta ka yi sujuda a kai in har takardar mai tsarki ce kuma an yi ta da itaciya ko abin da yai kama da ita wanda yake halatta a yi sujada a kai, haka kuma in an yi su da auduga ne ko kirtani.

T: Yaya yin sujada a kan siminti?

A: Shi ma ya halatta a yi sujada a kai.

T: A wani lokaci ina jin makarancin al’kur’ani a cikin rukoda, ko rediyo ko talabijin, yana karanta ayar da ake yin sujuda shin zan yi sujada?   

A: Bai wajaba ka yi sujuda ba sai in har ka ji ta daga bakin mai karatun ba karatunsa wanda aka dauka ba.

T: Wata mace tana sallah ba ta sani ba wani bangaren gashinta ya fito ta karkashin abin da ta boye gashinta da shi shin wajibi ne in gaya mata lokacin da take yin sallar ko kuma bayan ta gama?

A: Ba wajibi ba ne ka gaya mata ko da ko ba ta sani ba har ta gama sallarta, sallarta ta inganta haka kuma idan ta gano tana cikin yin sallar ta yi sauri ta boye shi shi ma sallarta ta inganta.

T: Mutumin da ya tashi kafin lokacin sallar asuba da mintuna shin yana cancanta a gare shi ya kara komawa barci, idan ya san ko kuma yake cikakken ganin ba zai tashi ba har sai rana ta fito?

A: Idan ya kasance don wulakantawa ne ga sallah, ko rashin daukanta da mihimmanci bai halatta ya koma ba.

T: dan makaranta, ko ma aikaci, wanda yake aiki ko yake karatu a wani gari, wanda yake tsakaninsa da garin da yake ya fi kilomita ishirin da biyu [22] kana ko wacce rana yana zuwa ya dawo domin aiki, tsayin shekara ko sama da haka yaya hukumcin sallarsa da azuminsa a wannan garin?

A: Zai yi sallarsa cikakkiya kana kuma ya yi azuminsa.

T: To yaya kuma da zai zamo cikin kowanne sati yana zuwa sau uku ko sau hudu har tsayin shekara domin wata bukata ba wai don sana’arsa ba, kamar a ce yana zuwa ne don shakatawa ko domin ziyarar makwancin lmamai da makamantan wadannan ya hukumcin sallarsa yake?

A: Zai cika sallarsa ya kuma yi azumi domin a al’ada ana lissafa shi mai yawan tafiya, amma da za’a ce a cikin sati yana yin tafiya sau biyu ne kwana biyar kuma yana zaune, a cikin garinsa, to wajibi ne a gare shi ya hada kasaru da cika sallah a cikin watan ramalana kuma yai azumi kana bayansa ya rama.

T: Tun da muna magana ne kan matafiyi to yaya hukuncin mutumin da yake azumi cikin watan ramalana kana ya yi tafiya bayan zawali?

A: Zai cika azuminsa ba ramuwa a gare shi.

T: To yaya kuma idan ya yi tafiyar kafin zawali wacce tun dare ya daura aniyar yin ta?

A: Ba zai azumi ba wannan ranar zai ci abinci lokacin da ya isa wurin da aka yarda a fara cin abinci wato haddut tarakkhus wajibi ne ya rama azumin daga baya.

T: To yaya kuma idan ya yi tafiya kafin zawali wanda bai da niyyar yin tafiyar tun dare?

A: Hukumcinsa hukumcin da ya gabata.

T: yaya matafiyin da ya dawo gida ko inda yake zaune cikin watan ramalana kafin zawali shin yana wajaba ya kame bakinsa har rana ta fadi?

A: Bai wajaba a gare shi ba, ko da yake ya kamata ya kame bakinsa.

T: To yaya idan ya dawo kafin zawali sai dai kuma ya ci abinci a tafiyar tasa?

A: Hukumcinsa irin hukumcin da ya gabata ne.

T: yaya idan ya dawo kafin zawali bai ci komai ba a tafiyar tasa? (tun lokacin alfijir).

A: Wajibi ne a tare da shi ya yi niyyar azumi, ya nesanci abubuwan ci a ragowar wunin, ba kuma ramuwa a tare da shi.

T: Yaya mutumin da yake yin azumin watan ramalana tsayin shekaru, sai dai bai san wankan janaba wajibi ba ne don haka ba ya wanka?

A: Azuminsa ingantacce ne kaffara kuma ba ta wajaba a gare shi ba.

T: Wasu marasa lafiyan suna yin amfani da wani abu wanda zai taimaka musu wajen numfashi wanda ake sanya shi a cikin baki, bayan sa shi idan an danna ya kan fitar da wani abu mai kama da gas a cikin baki, shin yin amfani da wannan abin tare da azumi zai yiwu?

A: I zai yiwu wanda yake amfani da wannan abu azuminsa na nan ingantacce ba abin da ya same shi.

T: Shin ya halatta a ba wa wadanda ba su yin azumi abinci cikin watan Ramalana a wurin sayar da abinci, ko kuma gida ga wadanda suke da uzuri na rashin yin azumi da kuma wadanda ma ba su da uzuri, in har ba su ba zai janyo wulakanta alfarmar watan Ramalana ba?

T: yana halatta a ba wa masu uzuri amma bai halatta a ba wa marasa uzuri ba.

T: Da za a ce in sami nutsuwa dangane da ingancin lissafin malaman taurari kan fitowar wata, shin zai yiwu in dogara da wannan nutsuwa da na samu bisa tabbatar da wata domin na yi azumi ko kuma na yi sallar idi?

A: Ba wani tasiri ga samun nutsuwa kan fitowar jinjirin wata, lallai ne ya zamo ka gan shi da ido ko wanda kuke tare da shi ya gan shi, ko da dai ganin watan wani gari yana isar wa wani gari in har sun hadu cikin sansani (wato ufuki), ta inda a ce ganin shi a waccen garin yana lizimta yiwuwar ganinsa a garin da kake idan ba don gajimare, ko dutse, ko kura, ko waninsu ya tsare shi ba.

T: Abin da ake yi shigen jaka ta roba kuma yake dauke da ruwa da sukari da wasu magunguna wanda ake ba wa mara lafiya ta hanyar allurar da take saduwa da jini kai tsaye, don rashin lafiya ko kuma ba tare da rashin lafiya ba, kamar a ba shi ita domun ciyarwa shin wajibi ne mai azumi ya nesanci irin wannan?

A: Ba wajibi ba ne ko da dai ya kamata ya nesanci haka.

T: Zan koma cikin aikin hajji na yi tambaya kan mutumin da ya sami damar zuwa aikin hajji ta mallakar kudin cikin wata shekara amma sai aka hana shi zuwa, don rashin samun biza a wannan shekarar sai ya bukaci amfani da wannan dukiyar saboda halin rayuwar yau da gobe, bayan an gama aikin hajji, kana kuma sai ya kasa samun wata dukiyar da za ta ishe shi yin aikin hajji?

A: idan ya samu dama cikin shekaru masu zuwa to hajji ta wajaba a gare shi, amma in da bai samu dama ba ba ta wajaba ba.

T: cikin muhawa rar da muka yi ta aikin hajji ka ce min lokacin da ka yi aikin hajji ka jefi [Jamratul akaba] amma ba ka gaya min ta wanne bangare ka jefe shi ba?

A: Na jefe shi ne ta inda yake fuskanta domin ba ya halatta a jefe shi ta bayansa.

T: Sai ka ce ka daura haramin hajji bayan zuwanka Jiddah a jirgin sama a wurin daura haramin da ake kiransa da [Juhufa], da wani mutum bisa rashin sani zai daura nasa haramin a Jiddah ba [Ju hufa] ba yaya kenan?

A: Idan da ma can ya yi bakance a kan zai daura ihrami daga Jidda to ya wadatar.

T: Ka kuma ce ma ni bayan ka yi dawafi da sa’ayi ka yanke gashinka, to da wani daga yan uwanka ya nemi ka yanke masa gashinsa tun gabannin ka yanke naka yaya hukuncinsa?

A: Ba ni da hakkin in yanke wa wani gabanin yanke nawa.

T: Da a ce a wannan shekara zan sami damar aikin hajji, ga shi kuma ni dalibin jami’a ne, ko kuma sakandare kuma lokacin tafiya hajjin ya yi daidai da lokacin jarabawata ta karshe, wanda idan na tafi zai janyo min maimaita shekara, da asarar kudi, da rashin kwanciyar hankali, a nan me ye abin yi?

A: Muddun dai tafiyarka aikin hajjin za ta janyo maka cikakkiyar takura kamar yanda ka fada ya halatta ka bar zuwa a wannan shekarar.

T: Yi min izini in fita daga wannan magana na haji don na yi tambaya kan wasu muhimman abubuwa, kan ciniki wanda zan fara da mu’amala da banki, don wasu mutane suna ajiye dukiyarsu a ciki da nufin karuwa, sai mahaifina ya ce min bara in fara tambayar ka, shin wannan bankunan daular musulunci ita ta kafa su ko ko daular da ba ta musulunci ba, kana kuma ana ajiye dukiyar ne da sharadin ba da kari ko ko a,a?

- to a nan mene ne bambanci?

A: Ajiya a cikin bankunan da suke ba’a daular musulunci ba halas ne cikin dukkan halaye ko da ko da sharadin ba da kari ne, amma ajiya cikin bankunan hukuma a kasashen musulmi idan ya zamo da sharadin samun kari to wannan riba ne kuma haram ne, idan ko ya zamo ba sharadin komai wannan ajiyar ta kubuta daga riba a wannan lokacin ta halatta sai dai ba ya halatta a yi amfani da dukiyar da aka karba daga bankin, har sai an sami izini daga shugaba na shara’a ko wakilinsa. Wato marja’i ko wakilinsa.

T: To shin akwai bambanci ne tsakanin gundarin kudin da ya ajiye da kuma karin da ya samu akai, a wannan hukunci da ka ambata?

A: A’a babu bambanci a tsakaninsu, bai halatta ba a yi amfani da wani abu cikin kudin face an tuntubi marja’i ko wakilinsa.

T: ka ce min bai halatta a yi ajiya cikin bankunan da suke daular musulunci ba tare da shardanta samun kari, to me kake nufi da shardantawa, kana nufin mai ajiya ya kudurce cikin ransa ba zai nemi banki da ya ba shi wani kari ba?

A: A’a ba haka nake nufi da sharadi ba, ma’anarsa shi ne kar ajiyar an rataya ta ne a kan lizimta wa banki ba da wannan karin kuma wannan ya sha bamban da ka kudurce cikin ranka cewa ba za ka nemi banki da ya ba ka kari ba domin kuwa kana iya kudurta haka amma ba ka yi sharadi ba, kamar yadda kuma za ka iya yin sharadi ba tare da ka kudurta wannan kuduri ba.

T: Da zan san cewa bankin zai ba ni kari ko da ban shardanta masa ba shin ya halatta na yi ajiya a wurin da nake ganin za’a lissafa amfani da ni?

A: Ya halatta muddin dai ba ka shardanta neman kari a tare da shi ba.

T: Wasu mutanen suna neman bashi daga bankuna amma sai bankuna su shardanta musu wani amfani don su ba su bashin, a wani lokacin kuma bashin yana zamowa hade da jingina yaya hukumci yake?

A: Bai halatta a nemi bashi daga banki ba idan har ya shardanta samun amfani cikin ba da bashin gare su, don haka riba ce shin ya ba da shi ne hadi da jingina ko ko a’a, sai dai yana halatta a gare su su karbi dukiya daga bankin ba da nufin bashi ba su yi amfani da ita da izinin shugaba na shara’a ko wakilinsa a wannan lokacin saninsu dangane da cewa bankin zai nemi amfani daga gare su ala tilas ba zai cutar ba da kuma zai neme su da su ba da kari a wannan hali ya halatta su bayar in har ba su da wata hanyar da za su ki ba wa bankin.

T: Mutumin da bai mallaki gidan da zai zauna ba, shin yana cancanta a gare shi ya nemi bashin bankin hukuma, tare da ba da amfani don ya gina gida da zai zauna?

A: Ba ya halatta a nemi bashi in an shardanta amfani kan kowacce irin bukata, sai dai yana halatta a karbi dukiya daga bankin ba da nufin bashi ba, kana daga bisani a kyautata yanda za a yi amfani da ita ta hanyar shugaban shara’a ko wakilinsa, kamar yanda na fada a baya a nan nake so na maimaita maka abin da na ambata maka shi, a farko cewa yin amfani da dukiyar bankunan hukuma a kasashen musulmi ba ya halatta sai da izinin shugaba na shara’a ko wakilinsa.

T: Ba ni labari kan bude asusu a banki domin fitar da kaya ko shigo da su, shin ya halatta.

A: I bude  asusu a bankuna abu ne wanda yake da kyau ta fuskar shigo masa da wani abu ko fitar masa da wani abu, haka kuma yana halatta ga banki mai zaman kansa ko na hukuma, yarjejeniyar karban lada daga wanda ya bude (asusu) din, Shin wannan ladan bankin zai karba ne a sabili da hidimomi da yake bayarwa – wanda suka shafi yin alkawarin biyan bashinsa, da kuma sadarwa a tsakanin banki da mai kaya, haka na karban takaddun kaya da kuma mika su gare shi da makamantansu – ko kuwa an karbi ladan ne a sabili da kudin da bankin ya biya daga asusun banki domin fitar da kaya, ga mai kaya, wanda bai zama daga kudin shi mai kayan ba.

T: Banki yana alkawari da daya daga ciki abokan mu’amalarsa (kostomomi) kan wani aiki na daban, ko kuma lamuni na dukiya wanda aka yi shi da hukuma ko ba da hukuma ba mene ne hukumcin yin hakan?

A: Wannan ya halatta ko da ko bankin ya karbi lada daga wajen kostoman nasa kan abin da ya sanya na alkawari ko lamuni.

T: Shin sayan hannun jari ko sai da shi ga wani kamfanin  mai hannun jari yana halatta?

A: Ya halatta a sai da hannun jari ko a saya ga kowanne irin kamfani muddun dai kamfanin ba ya ma’amalla ta haram, kamar cinikin giya ko ma’amala da kudin ruwa.

T: Wani lokaci kamfanin hannun jari yana sanya banki ya dau nauyin sayar masa da hannun jarin da yake da shi, sai bankin ya sayar masa bisa karbar wani lada na aikin da ya yi hakan ya halatta?

A: Yin hakan ma amala ce wacce take halas.

T: Yaya cinikin sai da cek na banki?

A: Bai halatta a sayar da cek ba kana kuma bai halatta Bankuna su zama tsani na sayar da shi ko sayen sa ba, haka kuma bai halatta a ci ladan aikin ba.

T: Yaya kuma aikawa da kudi a cikin kasa ko wajen kasa?

A: Ka fito min da tambayar taka a sarari don na sami damar amsa maka ita.

T: Banki ya kan ba da [Cek] na kudi ga wanda yake ma amala da shi, domin ya karbi masa kudi daga wakilinsa  a cikin kasa ko wajenta in har yana da asusu a banki, kana bankin ya karbi ladan aikin da ya yi yaya matsayin wannan yake?

A: Hakan ya halatta.

T: Mutum ya kan iya ajiye wasu kudi a wani banki cikin wani gari, kana sai ya karbi adadi na kudin ko abin da yake daidai da kudin daga wani  bankin a cikin kasa ko wajenta, kana sai bankin ya dauki ladan aikin da ya yi shin hakan ya halatta?

A: I ya halatta. 

T: Banki yana daukar nauyin sai da kudin kasashen waje ko kuma shi ya saye ta ya ba da kudi, tare da kara wani abu a ciki yaya halaccin wannan yake?

A: Hakan ya halatta.

T: Yaya kuma matsayin musanye na kudin ajiya, abin da nake nufi shi ne mutum, ya mai da wanda yake bin sa bashin zuwa ga banki, ko kuma banki ya mai da wanda yake bin sa bashi zuwa ga wani reshensa na waje don ya karba a can, ko kuma zuwa wani bankin daban?

A: Duk hakan ya halatta, yana kuma halatta banki ya karbi ladan irin wannan musanyen.

T: Yaya kuma matsayin yin inshora ta rai, ko kuma hatsari da annoba ko kan dukiya kamar jirgin sama ko jirgin ruwa, ko mota, ko gobara?

A: Dukkanta ta inganta.

T: A nan zan ajiye magana kan banki da mu, amala da shi, domin na yi tambaya kan cinikin awon nauyin abin da aka rina da zinare a sayar da shi da awon nauyi wanda ba’a rina da shi ba tare da karbar ladan rini?

A: Yin haka bai halatta ba kana haram ne duk da cewa hakan ya zamo gama gari a yanzu, ko da dai na amsa maka wannan tambayar to a yanzu zan kara karfafawa da cewa haram ne bai halatta ba.

T: Wasu daga cikin kayan ado na aure an rina su ne da farin zinare shin ya halatta maza su sa shi?

Kana nufin karfen platinum?

i shi nake nufi.

A: Sinadarin Platinum abu ne daban ba zinare ba ne kuma ya halatta maza su sa shi, domin abin da aka hana su sawa shi ne zinare da dukkannin nau’e’nau’ensa amma ba,a haramta musu abin da ba zinare ba.

T: Yaya mastayin yin ‘yar tsana da siffar mutum ko dabba shin ya halatta?

A: Sam sam bai halatta ba.

T: Yaya matsayin zana hoton mutum ko dabba ko waninsa?

A: Ya halatta.

T: Me ye matsayin saye ko sai da sassakakken dan adam ko kuwa dabba don yin ado da shi?

A: Shi ma ya halatta.

T: Wasu riguna marasa nauyi wadanda suke shara shara wanda ake cewa da siliki aka yi su, sai dai ni ban sani ba da silikin ne ko kuwa a’a, kana shin wajibi ne na yi bincike don in tabbatar?

A: Sam ba wajibi ba ne ka yi bincike don ka tabbatar kuma ya halatta ka sa.

T: Sayen kusumburwa da abubuwa na wake wake, da sayen kayan wasannin da aka haramta, haram ne sai dai akwai wasu abubuwan wasa wadanda aka yi don yara don nufin rarrashin su shin cinikin su ya halatta?

A: I ya halatta muddun dai ba ta zama an lissafa cikin abubuwan wasan da aka haramta ba.

T: Mai fili yana yin yarjejeniya da abokin yarjejeniya a kan cewa wanda ya yi yarjejeniyar da shi ya gina filin nasa kan wasu kudi da suka yi yarjejiniyar akai har ya kafa masa wani lokaci kamar she kara, don haka idan abokin yarjejiniyar bai gina ba cikin wannan lokaci to zai biya mai filin wani adadi na kudi a duk wata to yaya irin wannan sharadi yake, kana kuma abokin yarjejeniyar yana sanya wa mai wuri sharadi kan cewa shi abokin yarjejeniyar ne zai yi gini a tsayin shekara guda amma da sharadin cewa mai filin ne zai rika kawo masa kayan gini, idan kuma shekara ta cika amma ginin bai gamu ba, a dalilin cewa mai filin bai kawo kayan ginin a bisa lokaci ba, to shi sai ya biya abokin yaryejeniyar wani adadi na kudi, imma a karshen kowani wata, ko kuma sau daya. To shin ya halatta a karbi irin wannan kudi da aka shardanta a dukkan wadannan fuskoki biyu domin kuwa sun yi sharadin ne a cikin kullin yarjejeniya da ya zama lazimi.

A: I, ya halatta a ci cikin wannan fuskokin guda biyu.

A: Yaya matsayin lasisi da rejista don kafa kamfani ko wata masana’anta ko makamanciyarta a kan iya gadonta ko sayar da ita ko sayenta ko mai da mallakarta hannun wani daban, shin a shara’a muddun dai hukuma ba ta soke shi ba ma haka abin yake?

A: I muddun dai an karbi ci gaban halaccinta daga shugaba na shari’a.

A: To ya matsayin wasu kamfanin bugun littafi wadanda suke buga wasu litattafai don sayarwa, ba tare da izinin wanda ya dauki nauyin buga shi ko wallafa shi ba bayan kuma an rubuta ba’a yarda wani ya buga ba?

A: Ba wani tasiri ga wannan rubutu wanda ka ambata, sai in har ya zamo akwai wata doka wacce take kare hakkin masu buga littafi da watsawa, kuma ya zamto shugaba na shairi’a ya yarda da hakan..

T: Cusa abubuwa cikin fatun dabbobi da sanyasu a wuraren karbar baki ko wuraren zama domin ado ya halatta?

A: I ya halatta.

T: Sai da jini ko sayansa domin magani ya halatta?

A: I ya halatta.

T: Sai da abin da ba’a cin namansa kamar zomo ga mutumin da mazhabarsa ta yarje masa da ya ci ya halatta?

A: I ya halatta.

T: Ka ce min bai halatta in zauna a tebur din da ake shan giya ba, to shin ya halatta da ni da mai tebur din wanda yake sayar da giya a wurin da mushe tare da wasu abubuwa wayanda ya halatta a sayar ni da shi mu kulla yarjejeniya kan wani aiki wanda bai shafi sai da giya ba sai abubuwan da suka halatta?, kana kuma mene ne hukumcin dukiyar da mai wurin ya ba ni ita wacce ya ciro daga cikin akwatin kudinsa wadanda suke hade da kudin halal da haram?

A: Idan kun kulla cewa za ka rika sayar masa da abubuwan da ba na haram ba kawai to ba laifi cikin hakan, don haka albashinka wanda kake karba daga wurinsa yana matsayin halal a gurinka, muddun dai ba ka gano cewa daga gundarin haram ne ya dauko ya ba ka ba.

T: Shin ya halatta na yi aiki a wurin sayar da abinci wanda yake aikina shi ne na dafa naman dabbar da ba’a yanka ta yanka na shari’a ba, da sharadin ba zan rinka ba da ita ga masu saye ba, aikina kawai shi ne dafawa?

A: Hakan ya halatta.

T: Daga nan zan mai da tambayoyina kan abubuwan ci da sha, da farko zan yi tambaya kan halarcin ci, ko cinikin kazar da aka zo da ita daga kasar musulunci, kana a ka rubuta cewa an yanka ta kamar yanda musulunci ya nema?

A: Ya halatta ka ci ko ka saya ko ka sayar muddun dai ba ka gano cewa ba yankakkiya ba ce, shi ko wannan rubutu ba ruwanka da shi an rubuta ko ba,a rubuta ba za ka ci.

T: To yaya kuma wacce ta zo ba daga kasar musulunci ba amma an rubuta cewa an yanka ta kamar yanda musulunci ya nema?

A: Bai halatta ka ci ba in har ba ka sami nutsuwa ba kan cewa lallai an yi yanka na musulunci ba.

T: Yaya matsayin cuku wanda aka zo da shi daga kasar da ba ta musulunci ba, kana ban san yanda akai aka yi shi ba?

A: Ya halatta ka ci.

T: Wasu kifayen ba dukkannin bayansu ne yake da bawo (kambori) ba, shin ya halatta a ci su?

A: I ya halatta ka ci ko da ko bawon da ke jikin bayan nasa guda daya ne.

T: Yaya kuma matsayin kifin gwangwani wanda aka zo da shi daga kasashen Turai ko kuwa Amerika, shin ya halatta mu ci bayan kuma ba mu da yakini kan yankan sa ta fuska guda biyu:- fuskar farko shi ne ba mu san kifin yana daya daga cikin masu bawo a ba ya ba ko ko ba ya daga cikinsu, sai dai an rubuta a jikin gwangwanin cewa yana da bawo a baya, kana kuma an san kasar da ta yi shi da kiyaye doka kan abubuwan da ta rubuta a jikin abubuwan sayarwarta.

Fuska ta biyu shi ne:- sannan ba mu hakikance sun sami damar kama kifin a wajen ruwan da rai ba ko kuma ya riga ya mutu tun a cikin ruwan a cikin tarkon, sai dai kawai abin da yake a sarari shi ne an kamo ta ne da jiragen ruwan kamun kifi na zamani, wanda kuma ana fito da kifayen ne da ransu zai wahala a sami wani ya mutu, yaya matsayin wannan yake?

A: Idan har an sami nitsuwa ne bisa yin duba kan wadannan fuskoki guda biyu da ka kawo ya halatta a ci, in ko ba’a sami nitsuwa ba bai halatta ba.

T: Akwai wuraren cin abinci daban daban cikin kasuwannin musulmi wanda suke sanya nama cikin abincin wadanda suka saya to yaya matsayinsa yake?

A: Ya halatta ka ci wannan nama.

T: Ko da ko ban tambayi mai wurin abincin ba?

A: Ya halatta ka ci ba tare da bukatar tambayarsa ba, kamar yanda ba wata bukata kan ka tambayi lizimtan addinin wadanda suke aiki a wurin ba.

T: Shin wajibi ne mutum ya yi bincike kafin ya sha magani don ya tabbatar cewa maganin ba a yi shi da wani abu na haram ba?

A: Sam sam bincike ko neman tabbatarwa bai halatta ba.

T: Akwai magunguna da yawa wadanda a cikinsu akwai alkohol wanda bai taka kara ya karya ba, shin ya halatta na sha shin kuma ba najasa ba ne?

A: Ba najasa ba ne, ya kuma halatta ka sha.

Akwai tambayoyi da dama wadanda suka hado abubuwa daban, daban sababbi, tambayi duk abin da ka so.

T: Zan fara tambaya ta a farko kan kyauta shin ya halatta mutum mai rai ya yi kyautan idonsa ko kodarsa zuwa ga wani mutum mai rai?

A: Bai halatta a yi kyautar ido ba, amma yana halatta a yi kyautar koda idan mutum yana da wata kodar lafiyayya.

T: Wasu mutane suna ba da wasiyyar in sun mutu a ciri wani abu daga jikinsu don a sanya ta a jikin wani mabukacin shin irin wannan wasiyya ta inganta kana ya halatta a ciri wannan abun?

A: Sam sam bai halatta ba in har wanda ya yi wasiyyar musulmi ne sai in har ya zamo rayuwar wani musulmin za ta salwanta, domin rashin wani abu a jikinsa, to a nan ya halatta a cira a sa masa ko da ko mai abin bai yi wasiyyarsa ba, sai dai kuma za’a biya diyya in har an cira ba tare da wasiyyarsa ba, amma babu diyya in har ya yi wasiyya.

T: Wani lokaci ana daure hanyar daukan cikin mace wato bututun da koyaye suke bi a rufe shi in har daukan cikin nata yana hade da hadari ta yanda za’a iya bude shi daga baya ta hanyar tiyata, yin hakan ya halatta?

A: Yin hakan ya halatta ko da ma ba zai yiwu a kara bude shi ba.

T: Wasu kamfanoni su kan jarraba wani sabon maganin da su kai a jikin mara lafiya ba tare da saninsa ba, don ganin cewar maganin nasu ya yi, ko bai yi ba yaya matsayin wannan yake?

A: Bai halatta wani kamfani yai haka ba.

T: Yaya matsayin fede mutum bayan ya mutu tare da dalili na hankali kamar don binciken abin da ya kashe shi, ko makamancin haka?

A: Bai halatta a fede gawar musulmi ba don wadannan dalilai amma fede gawar kafirin da ba na amana ba ya halatta, ko kuma kafirin da ake shakkun ko kafirin amana ne, in har ba wata alama ta shara’a da take nuna cewa kafirin amana ne.

T: Da yawa rahoton likitoci yana bayanin cewa shan taba abu ne mai cutarwa domin kuwa yana daga cikin manya manyan dalilan da suke jawo ciwon zuciya ko ciwon matattarar jini da jijiyoyin da suke rabe da shi a jikin dan adam, da kuma ciwon huhu, kana da cutar kirji, ban da ma irin cutarwar da yake yi wa iyalin mai shan ta, da abokan zamansa, shin ya halatta ga wanda bai shan taba ya fara sha? Shin wanda ya saba ya halatta ya ci gaba da sha?

Kana shin ya halatta ga mace mai ciki ta sha?  bayan kuma likitoci sun ce jinjiri na tasirantuwa da shan tabar mahaifiyarsa?

A: In har shan taba zai janyo babbar cuta ga mai shanta, ko kuma ga jinjiri to ya haramta ga wanda zai fara, da kuma wanda ya saba wanda rashin shan nata ba zai jawo masa cikakkiyar cuta ba, amma wanda daina shan zai janyo masa cuta cikakkiya, to sai ya duba ya ga wanne ne wanda ya fi karancin cuta shin, ci gaba da shan ne ko ko dainawa  sai ya yi aiki da abin da ya fi, karancin cuta.

T: Ana ba da kyaututtuka ga wandanda aka yi wa haihuwa, wayanda kyaututtukan a bisa al’ada a kan yi su da kaya na zinare ko abinci ko kudi, to irin wayannan kyaututtuka na wanda aka haifa ne ko na iyayensa ne?

A: Kyaututtuka su kan saba a irin wannan wuri akwai wacce take dauke da abin da yake nuna ta wanda aka haifa ce to ta zama tasa akwai kuma wacce wanda aka haifa din ba zai iya amfani da ita ba kamar abubuwan ci da makamancinsu wannan na iyayensa ne, abin da yake a sarari kudin da aka sanya karkashin fulon abin da aka haifa ko kuma kayansa to wannan na wanda aka haifa ne.

T: Shin ya halatta iyaye su yi amfani da dukiyar dansu wanda bai balaga ba?

A: Ya halatta ga uba ya yi amfani da dukiyar dansa, muddun ba zai janyo illa ga yaron ba, amma uwa ba ta da damar yin amfani da dukiyarsa ba tare da izinin uba ko kaka ba, kuma ba zai janyo illa ga yaro ba amma in zai janyo illa ga yaron bai halatta ba gare su kai ya zamo wajibi ma su adana masa ita har ya girma.

T: Yaya matsayin kyakkyawan sihiri wanda ake yin sa don aikin alheri, sabanin mummunan sihiri wanda masharranta ke yin sa shin ya halatta?

A: Sihiri da dukkan kala kalarsa bai halatta ba, har ma wanda ake yin sa don bata sihiri da aka yi wa wani, sai in har akwai maslaha mai girma cikin yin sa, kamar kare ran da yake da mihimmanci.

T: Yaya matsayin kiran rayuka wadanda suka mutu don tambayar ma’abotansu da kuma tambayar su kan yanda barzahu yake ko wasu abubuwa daban?

A: Haram ne ya kira ran wanda kiran ransa zai cutar da shi daga cikin rayukan da suke masu alfarma ban da marasa alfarma.

T: Wasu suna da’awar yin amfani da Mala’iku shin gaskiya ne?

A: Wannan magana ce mara tushe.

T: Hotunan Annabi da na A’imma shin ya halatta a rataya su a cikin gida, kana shin ya halatta a yadda cewa hotunan nasu ne tsira da amincin Allah ya tabbata a gare su?

A: Ya halatta a sa su a gida amma a kudure cewar sun yi daidai da surarsu wannan kuduri ne wanda yake kure a sarari.

T: Wasu masu shirye shiryen fim suna shirya fim din tarihin [Annabi ko na A’imma A.S], shin ya halatta wani mutum ya fito gaban mutane a matsayin shi ne Annabi (S.A.W.A.) ko kuwa a matsayin wani daga cikin A’imma?

Idan amsar shi ne halacci to sharadi ne ya kasance mumini?

A: Ya halatta a fito a matsayinsu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare su, sai dai da sharadin ba zai jawo wani aibi, ko wulakanci ga surarsu, ko matsayinsu mai girma a cikin zukata ba, don watakila wanda zai yi kama da su din, ya zamo yana da wata siffa wacce za ta iya janyo haka a tare da su.

T: Mutane suna jefar da jaridu ko mujallai ko wasu yankin littattafai masu muhimmanci a wuraren da ake zubar da shara tare da cewa a cikinsu akwai ayoyin al kur’ani ko kuwa sunan Allah madaukaki?

A: Hakan bai halatta ba ya kuma zama wajibi a dauke su daga wannan wurare a kuma tsarkaka su in har najasa ta same su.

T: Lokacin da rikici na magana ya afku wasu suna magana cikin fushi da lafazuzzuka wanda ma’anarsu kafirce wa Allah ne kamar yanda suke yin wasu lafazuzzuka ga A’imma wayanda ba su dace ba wanda ba wai haka suke nufi ba da gaske shin wajibi ne ai musu haddi kan haka?

A: Muddun dai abin da suka fada ba haka ne hakikanin abin da suke nufi ba, ba za a yi musu haddin shara’a ba sai dai sun cancanci a yi musu ladabi.

T: Da za su kasance da gaske suke kuma bisa nufi cikin zagi da suka yi wa Allah madaukaki ko Annabi ko A’imma, ko addini ko mazhaba, ta yadda sun yi nufin haka suka rika maimaitawa mene ne hukumcinsu?

A: Hukumcinsu kisa.

T: Akwai wasu tambayoyin daban wadanda suka rage a kan wannan da kuma wasu abubuwa, sai dai kai min uzuri saboda tsawaitawa.

Shin ya halatta mace ta koyi tukin mota a wajen wani mutum daban wanda ba muhararraminta ba, wanda hakan zai lizimta kadaitarta da shi, ta tafi tare da shi zuwa wuraren koyo wanda a al’ada irin wadannan wuraren wurare ne wanda ba shi da mutane da yawa?

A: Hakan ya halatta, da sharadin kubuta daga fadawa haram.

T: Shin ya halatta ga mace ta dauki hotonta wanda ba hijabi don ta sanya shi a [fasfo] din ta?

A: In har ya zama lalura ta sa hoto mara hijabi a kan fasfo ko kuma wani kati na dabam ya halatta, sai dai wanda zai dauki hoton ya zamo mijinta ne ko muharraminta, in da larura ta iya zuwa gidan hoto ta dauka.

T: Shin ya halatta a yanka dabba ta keya?

A: I ya halatta.

T: Shin ya halatta a tona kabari, in har hakan ba zai janyo wulakanci ga ma’abucin kabarin ba?

A: Bai halatta ba sai a wasu wurare da littattafan fikihu suka yi bayani, yana daga ciki wuraren larura.

T: Yaya matsayin ba da fim wanda aka dauka na matan da suke yin hijabi, ga mutumin da yake ba muharraminsu ba domin ya wanke hoton?

A: Hakan ya halatta in har wanda zai wanke din bai san takamaimen matan da ke cikin hoton ba kana hoton matan wanda yake cikin fim din ba zai motsa sha’awa ba, kuma ba zai jawo fitina ba.

T: Yaya matsayin kudin da na tsince shi a bakin titi ko kasuwa, ko filin jirgi ko tashar jirgin kasa, ko tashar mota wuraren da ba sa rabuwa da mutane kana ina da yakini ba zai yiwu a samu mai shi ba?

A: Za ka yi wa  mai shi sadaka.

T: Yaya matsayin kudin da yaro ya tsinta misali a ce mai yawa?

A: Idan har bai dauke da wata siffa wacce zai iya gano mai shi ta hanyarta, to ya halatta ga waliyyin yaron ya karbi kudin ya mallaka masa shi, in ko har yana da siffa to ya zama wajibi a yi cigiya kamar yanda ya gabata,

T: Daga nan ne kuma zan koma tambaya kan abin da ya shafi akida, zan yi tambaya kan halaccin neman arziki ko da, ko kariya, ko taimako, daga ma’asumai kai tsaye?

Bara in fara tambayarka!

Za ka nemi haka ne a wurinsu domin su ne suke halitta ko suke azurtawa, ko suke karewa?

Sam ba da nufin haka ba ne illa kawai su zamo tsani ne zuwa ga Allah madaukaki kuma masu ceto kan biyan bukatu, kana su ba sa aikata komai sai da izininsa.

Kana nufin su ma suna rokon Ubangiji ne sai ya yi halitta, su roke shi kuma ya azurta, kana al’umma ne wadanda ake karbar cetonsu ba’a mai da abin da suka roka?

Kana saboda matsayinsu a wajen Allah madaukaki da kuma kasantuwarsu majibintan lamuranmu?

I haka nake nufi.

A: Haka ya halatta domin Allah madaukaki yana fadi cikin littafinsa mai girma [KU NEMI TSANI ZUWA GARE SHI]

Kuma su Ma’asumai su ne tsaninka zuwa ga Allah hakan ya halatta.

 

عنوان الکتاب