MUHAWARA TA BIYU WACCE TA HADO ABUBUWA DABAN DABAN

 

 

Akwai tambayoyi da yawa wanda suke zuwa cikin tunanin mutane musammam ma matasa, ina mai fatan ka ba ni izini domin na yi tambaya a kan wasu mas aloli wayanda ina sane na ki yin tamba ya a kansu domin ina so na sanya su cikin babi daban a babuka masu zuwa, sai ga shi yanzu na ga mun yi muhawarori daban daban wanda kuma nake ganin ya dace a ce mun sami wani zama na musamman domin wasu muhawarorin, wanda yin hakan ina ganin abu ne mai kyau.

T: Yanzu ga shi na zauna ina mai nema a amsa min, ga kuma mahaifina ya zauna yana nema ya amsa min sai na ce a cikin raina lallai ne yau muhawararmu za ta kasance wahalhalun wasu dalibai lokacin neman iliminsu.

Saboda haka nake so ni kuma na san hukumcin musulunci a kai, don haka sai na ka da baki na ce da mahaifina wasu daga cikin dalibai masu karanta ilimin likita suna koyan darasi wanda yake zamowa lallai sai sun taba jikin mace mara lafiya sun kuma ci gaba da mu’amala da shi zuwa lokacin da rashin lafiyar tata ya bukaci rashin tabawar tasu, wanda kuma da dalibi zai ki da zai fadi a jarabawa shin ya halatta a karanta irin wannan darasi a kuma kware a cikinsa?

A: Ya halatta dalibi ya koyi irin wannan darasi, in ya sami nitsuwa ko kuma ya san cewa kwarewarsa kan wannan ilimin abu ne wanda zai ceto rayuka masu alfarma da shi ko da ko nan gaba ne, sai dai lokacin da yake ya zamo yana yin sa ba ta yanda zai motsa shaawa ba.

T: A makarantun koyan aikin likita yana zamowa dole ga dalibi ya duba matar da ba muharramarsa ba ko kuma namiji wanda ba makusancinsa ba, wanda wata rana dubawar sai ta kai ga al’aura ko kuma dubura shin irin wannan bincike yana halatta ga dalibin, kana shin hakan yana halatta ga likita in har akwai kare wani rai mai girma ko da ko nan gaba ne?

A: I hakan yana halatta ga dalibin da kuma likita in har hakan yana tattare da kare wani rai mai alfarma ko da ko nan gaba ne.

T: A cikin asibituttuka mata majiyyata su suke auna jini da wankin gyambo, da makamancin wadannan, shin namiji mara lafiya yana da damar da zai ki yarda su taba jikinsa?

A: Zai iya neman wani daga cikin maza don yin wannan aikin ko ya nema wannan macen da ta sanya safar hannu ko wani hankici, don ya kare hannunta daga  taba jikinsa.

T: Wani lokaci cutar tana da bukatar sai an taba jikinsa, kana kuma babu namiji ko kuma ya nemi hakan zai iya zamowa matsala, ko kuma macen ita ta fi kwarewa da tausasawa a kan namijin to in har hakan ta faru to yaya kenan?

A: Idan har lalura ta binciken cuta ko ko ta magani ta kai da sai an taba jiki to hakan ya halatta, kamar cikin wannan tambayar amma a takaita gwargwadon yawan larurar da za ta kai da’a taba jikin.

T: Wani lokaci miki yana kasancewa a kusa da al aura, kuma ya bukaci a wanke shi to yaya kenan?

A: Lallai kenan sai mara lafiya ya nemi mai wankin ciwon namiji ne ko mace da ya sa hannunsa cikin safa ko wani hankici don kar ya taba al’aurarsa, in kuma har hakan ba zai yiwu ba, ya halatta ya taba gwargwadon yanda lalurar wankin ciwon ta bukata.

T: Da za mu musanya wannan tambayar dangane da tabawa zuwa tambaya kan gani to mene ne hukumcin kallo?

A: Hukumcin kallon da aka haramta daidai yake da hukumcin shafar da aka haramta, don haka abin da ya gabata na bayani shi ne a tare da shi.

T: Cikin irin tambayoyin da na yi in mara lafiyar mace ce, mai duban mara lafiyar namiji shin hukumcin duk daya ne?

A: I daya ne.

T: Wasu daga cikin mazaje wadanda addini bai dame su ba, su kan nemi matarsu ta daina salla ko kuma ta daina hijabi, ko kuma ta kai wa baki giya, ko kuma ta shiga wasan caca ko gaisawa ta musafaha da bakin da suka zo, ya kuma yi mata dole kan haka in ta ki, shin yana cancanta ga matar ta ki zama a wurin don ta tsira da addininta, da abubuwan da suke wajibi a kanta na shara’a?

A: I yana kyautuwa da ita ta ki zama a wurin gwargwadon yanda larurar ta hukumta kana kuma duk da haka ta cancanci ya ciyar da ita kamar kullum.

T: Matar da take kula da hijabi sai dai kuma mjijnta yana hana ta, har ma yana ba ta zabi ko ta cire hijabi ko kuma ya sake ta yaya za ta yi?

A: Ba yadda za’ai ta rabu da hijabi ko da ko abin ya kai da ya sake ta.

T: Sai dai kuma sakin zai janyo wa wasu daga cikin mata kunci da takura mai tsanani yaya kenan za su yi?

A: Lallai ne su jure wa wannan takura da kuncin, su kuma tuna fadin Allah madaukaki [DUK WANDA YA JI TSORON UBANGIJI ZAI SAMA MASA MAFITA YA KUMA AZURTA SHI TA INDA BA YA ZATO].

T: abubuwan da suke hana daukan ciki sun yi yawa a wannan zamanin, da za a lizimci yin amfani da maganin gargajiya zai jawo cuta, don haka al’amarin sai ya kai da ba makawa sai an yi amfani da bude jiki a wurin likita namiji ko mace, shin hakan yana yiwuwa ga mace, bayan tana sane da cikin zai sabbaba mata cuta ko takura?

A: Yana halatta muddun dai tana fuskantar matsaloli guda biyu matuka matsalar shan magani da matsalar ciki, sai dai kuma idan har hakan zai kara janyo har sai an auna ta da abubuwan aunawa na mahaifa don a gano wasu wurare daban daga jikinta, kamar bangaren abin da ke sa haihuwa to ya, zama wajibi a tare da ita ta ga likita mace in har ba ta sami macen ba ta ga namiji.

T: Shin ya halatta ga mace ta dubi bangaren da ya kebanci tsakanin cibiya da gwiwa, na wata mace daban muddun dai ba ta ga gabanta ko dubararta ba?

A: I yana halatta in har ba zai motsa sha’awa ba.

T: Wasu mata suna kin haihuwa bayan kuma mazajensu suna son haihuwa, kamar yaya?

Ta yanda suke yin amfani da magani ko wankin mahaifa bayan saduwa, ko yin allura, ta haka ne suke kin haihuwar?

A: Wadannan abubuwa ne wadanda suka halatta muddun dai ba su kai ga cikakkiyar cutarwa ba.

T: Yaya matsayin [azlu] shi ne zubar da maniyyi a wajen farji, ta yanda mata suke hana mazajensu su zuba musu maniyyi cikin farjinsu a lokacin da suke saduwa?

A: Hakan bai halatta a gare su ba.

T: Shin miji yana da ikon da zai hana matarsa haihuwa bayan ita tana so?

Yaya zai yi mata dole kan haka?

Yana yi mata dolen ne ta hanyar allura ko shan kwayoyi?

A: Hakan bai halatta a tare da shi ba.

T: To yaya kuma idan shi ya yi mata [azlu] a lokacin da suke saduwa?

A: Hakan ya halatta a tare da shi.

T: Ya matsayin kwayoyin magani wanda mata ke sha don ya hana su haila?

A: Shansu yana halatta a tare da ita.

T: Farkon ciki abu ne mai sauki a’iya zubar da shi, shin yana halatta ga uwa ta zubar da shi?

A: Sam sam ba ya halatta ta zubar da shi sai in har za ta cutu da ci gaba da zamansa a cikin mahaifarta, koko ci gaba da zamansa zai wahalar da ita wahalarwar da ba a saba ba.

T: Yaya matsayin rungumar juna, ko sumbantar juna da wasu mata ke yi a filin jirgi ko a gefen titina ko kasuwa?

A: Rungumar juna ko sumbar mace zuwa mace ya halatta, da sharadin har a gama wani abu na haram bai shiga ba.

T: A yanzu mata suna fitowa bakin titina, suna bude da wasu wuraren da ya wajaba su rufe, shin yana halatta a kalle su ba tare da shaawa da jin dadi ba?

A: Yana halatta in har sun kasance in an hana su ba za su hanu ba.

T: Yana daga abin da aka saba da shi a yau, mace ta shafa kwalli ko hoda, ko ta sanya zobe ko abin wuya ko awarwaro domin ado, kana ta fito gaban mutane cikin kasuwa ko titi, mene ne hukumcin haka?

A: Hakan bai halatta a tare da ita ba sai kwalli da zobe kawai da sharadin za ta kubuta daga afkawa cikin haram, kuma ba ta nufin motsa sha’awar wasu mutane daban.

T: Tun da dai muna magana ne kan hijabi, ina so na yi tambaya a kan macen da take fitowa gaban mutane, saman kafarta yana bude, wanda ba muharraminta ba na kallo me ye hukumci?

A: Bai halatta ba.

T: Yaya matar da ta ke yin sallah saman kafarta a bude?

A: Wannan ya halatta, domin bayyanar saman kafa ko kasan kafa halal ne a cikin salla.

T: Yaya wasu mata suna hawa motar haya, ya zamo daga ita sai direba, ba wani a tare da su?

Shin hakan yana kaiwa ga motsa sha’awa ko aikata haram?

Sam sam bai kaiwa ga haka, ina tam baya ne kan halin da aka saba da shi a yanzu.

A: Muddun dai ta amince wa kanta rashin afkawa cikin haram idan ta hau ita kadai tare da shi ya halatta.

T: Yaya matsayin tunanin kan mata yake, wacce ba matarka ba da gangan, wanda hakan yana kaiwa da suranta mu’amala ta jinsi da ita a cikin tunani, ya kan kai maabocinsa al’aurassa ya mike ba tare da zubar da maniyyi ba?

A: Ba haram ba ne in har bai kai ga abin da aka haramta ba.

T: Cikin muhawararmu wacce ta wuce ka gaya min mutum ya buya ya fitar da maniyyi bai halatta ba, shin da namiji da mace cikin hakan ba bambanci?

A: I ba bambanci kamar yanda bai halatta ga namiji ya aikata abin da zai jawo maniyyi ba da al aurarsa, haka nan ba ya halatta ga mace ta aikata abin da za ta jawo maniyyi da al aurarta.

T: Halin rashin lafiya ya kai ta inda sai likita ya yi bincike kan magudanar maniyyinsa, bayan ya ki ya fita ta hanyar shara’a ta inda in zai fitar da maniyyin sai ya zamo lallai likita yana wurin yaya hukumci yake?

A: In har mara lafiya ya bukaci yin hakan don lalura ya halatta ya fito da maniyyin nasa.

T: Idan mutum ya so ya jarraba ya ga ko zai iya haihuwa, sai likita ya nemi ya fito da maniyyinsa don ya yi bincike yaya hukumci yake?

A: Muddun dai ba lalura ba ce to bai halatta a gare shi ya fito da maniyyi ba.

T: A wannan zamani ta hanyar abubuwan ilimi sababbi yana yiwuwa a san yanayin da jariri yake ciki, yana da lafiya ko kuwa yana da wata cuta, idan ya tabbata a ilimance kasantuwarsa akwai cututtuka a jikinsa ko kuma cuta ko tsarin gabbansa ba daidai ba ne ya halatta a zubar da shi?

A: Rashin kyan jariri bai kasance abin da zai janyo a zubar da shi ba, to sai dai in har ci gaba da zamansa a cikin mahaifar mahaifiyar zai iya cutar da lafiyarta, ko kuma zai sanya ta cikin tsanani mara iyaka, wanda a al’ada ba’a iya jure masa, a nan ya halatta ta zubar da shi, hakan kafin shigar rai jikinsa, amma bayan shigar rai bai halatta a zubar da shi ba ta ko wanne hali.

Abokin muhawara:- sanya maniyyi cikin mahaifa ta hanyar na’ura, wanda yanzu ya zama gama gari ana kuma yin sa ta hanya daban daban, na so in bijiro maka da tambaya a kansa domin na san irin fuskar da mai shara’a na musulunci ke kallonsa da ita.

Ana diban ruwan maniyyin miji a sanya shi cikin mahaifar matarsa, ta hanyar sirinji ko abin da ya yi kama da haka na wasu hanyoyin, mene ne hukumcinsu?

A: Kamar yanda dai ka fada yanzu a wannan tambaya ya halatta.

T: Shin ya halatta a zuba wa wata matar daban ba matarsa ba?

A: Bai halatta ba.

T: Ana diban “ya“yan kwan namiji da na matarsa a sanya su cikin kwalbar bincike a rene su kana a mai da su cikin mahaifar matar, yaya hukumci yake?

A: Shi ma dai wannan kamar yanda ka ambace shi haka ya halatta.

T: Kana ana diban ruwan namiji a debi kwan wata mace daban wacce ba matarsa ba a raine su kana a sanya shi cikin mahaifar matarsa ya hukumci yake?

A: Shi ma kamar yanda ka ambace shi ya halatta.

T: To a nan dan na wane ne shin na wacce aka debi kwan nata ne ko kuma na wacce ya girma a cikin mahaifarta ne, abin da na ke nufi wace ce za ta zamo mahaifiyarsa ta jini?

A: A cikin wannan masa’ala akwai fuskoki guda biyu ba makawa sai an yi taka tsan tsan a tsakaninsu, wato a yi ihtiyadi.

T: Yaya kuma idan aka debi kwan mace aka raine shi da ruwan namijin da ba nata ba, kana aka dawo da shi cikin mahaifarta?

A: Yana kamata a nesanci yin haka.

T: Zan komo magana kan dalibai da hukumce hukumcensu kuma, na yi tambaya kan yin bulala wa dalibi a makaranta, shin lallai ne sai an karbi izini daga waliyyinsa?

A: Ya halatta a bugi dalibi a lokacin da yake cutar wasu, ko kuma lokacin da ya aikata haram, ana yi masa bulala uku in har’an nemi izini daga waliyyinsa, ba’a yi masa sama da uku, dukan ya kasance a hankali ta yanda ba zai janyo jikinsa yai ja ba, in kuwa ba haka ba lallai diyya ta wajaba.

T: Shin yin algus cikin jarabawa ya halatta idan har wasu daga cikin malaman su za su taimaka wa dalibi kan yin ta?

A: Hakan ba ta halatta.

T: Wasu daga cikin daliban takanikal suna koyar zane zane da makamantansu na daga abubuwan da suke da jiki da rai, kana idan ba su yi ba hakan zai hana su cin jarabawa da gama makaranta din kuma zai hana su samun satifiket na makaranta, shin hakan yana halatta su yi?

A: Don kawai in ba su yi ba zai hana su cin jarabawa? Ba zai sanya su aikata abin da shara’a ta hana ba.

T: Yaya matsayin wasan kwallo yake ga dukkanin kala kalarsa, wanda ake yi ba tare da ba da wata jingina ba?

A: Ya halatta.

T: Yaya matsayin wasan kokawa da dambe wanda ake yi ba tare da ba da jingina ba?

A: Sun halatta muddun dai ba za su kai ga cutar da jiki ba mummunar cutarwa.

T: Yana daga cikin muhimman masa aloli ga mazaje, mas alar aske gemu don wasu daga cikin mazaje suna aske gemunsu su bar gashin haba shi kadai, shin hakan ya gamsar a shara’a?

A: Bai gamsar ba.

T: Yaya idan mutum kamar a yau ya aske gemunsa da aska, shin ya halatta a washegari ya sake aske wurin tun da gashin gemu bai fito ba?

A: Bai halatta ba.

T: Yi min izini in koma kan tambaya kan alakar da da uba, don na yi tambaya kan abubuwan da yake zamowa wajibi a kan da ya bi umurnin mahaifinsa?

A: Musulunci ya wajabta wa da ya yi kyakkyawar ma’amala da iyayensa.

T: Da kyau shin ya dace a shara’a a bi iyaye kan dukkannin abin da suka yi umarni da shi har ma cikin al amuran yau da gobe, har ma mahaifi ya ce da dansa ci wannan kayan marmarin, ko kuma ya ce yi bacci karfe goma, ko abin da ya yi kama da haka?

A: Hakan yana da kyau.

T: Yaya idan uba ya hana dansa aikata wani abu wanda yake zaton dan zai cutu idan ya aikata shi, bayan dan yana sane da cewar ba wani abu da zai same shi idan ya aikata?

A: Ba ya halatta a saba wa mahaifi cikin wannan halin ta yanda saba masa ya kan cutar da shi domin tausayinsa da yake yi..

T: Da mahaifi zai ce da dansa na san cewar ba wata cuta da za ta same ka a wannan tafiya taka, sai dai ya dana ka rabu da ni ka nesanta da ni abu ne mai wuya a tare da ni, kana zai iya cutar da ni don haka na hana ka wannan tafiya taka?

Kafin na amsa maka wannan tambayar bara in tambaye ka, shin da dan zai yi wa mahaifin nasa biyayya ya ki yin tafiyar, shin zai cutu saboda kin yin tafiyar tasa?

Ba wata cutuwa da zai yi, sai dai kawai bai samu abin da yake so ba.

A: Bai halatta yai wannan tafiyar ba muddun dai tafiyar za ta cutar da mahaifinsa.

T: Zan koma kan abin da zukatan mafi yawan matasa yake ta kai kawo a yanzu shi ne wasan shatranj (chess), amma ba tare da jingina ba wato dara ‘yar china.

A: Ba su halatta ba.

T: Wasu daga cikin matasa suna yin wasa ba da draft ba ba da chess ba da wasu abubuwa ne daban na wasan caca, amma ba tare da ba da wata jingina ba shin ya halatta?

A: Wasa da dukkannin irin abin da za a iya yin caca da shi ya haramta ko da ko an yi shi ba da jingina ba.

T: Wasu wasannin ana yin su ne da na’ura mai aiki da lantarki, wanda take fitowa a kan talabijin ta hanyar yin amfani da wani abu da ake kiran sa da “Atari” kana ana yin wasan ne ba tare da jingina ba, ya halatta?

A: Idan abin da yake fitowa a kan lebijin din abu ne wanda ake iya yin wasan caca da shi, wannan wasan bai halatta ba ta hanyar wannan na’ura, in ko ba haka ba ya halatta.

T: Daga tambaya kan abubuwan wasan da za’a iya yin caca da su zan koma kan tambaya kan rawa nai tambaya kan rawar mace ga mijinta domin ta kyautata masa ko ta motsa sha’awarsa?

A: Bai halatta tai rawa a gaban wani namiji ba wanda ba mijinta ba ne, ban da ma haka ba ya halatta tai rawa ko da’a gaban mata ne “yan uwanta.

T: Yaya rawar namiji a gaban maza, ko gaban mata wacce ba matarsa ba?

A: Bai halatta ba.

T: Lokacin aure ko wani abun farin ciki maza ko mata suna yin tafi yaya matsayinsa yake?

A: Hakan ya halatta a tare da su muddun dai bai hado da wani abu na haram ba.

T: Zan koma tambaya kan jin wakoki na addini?

Kana nufin kalmomi na addini wanda ma’abota wake suke kakkarya amma da lafazi irin na ma’abuta wargi da rangwada?

I shi nake nufi?

A: Irin wannan bai halatta a ji ba haka nan dukkanin zancen da ba wargi ba muddun dai za’a yi shi da siga ta karai rayawa, shin addu’a ne ko zikiri ko wani abu daban.

T: Yaya maganganu na wasa wanda ake yin su da irin wannan karairayawa na waka?

A: Irin wannan shi ne wakan da yake sananne wanda ba kokwanto cikin haramcinsa.

T: To yaya kuma abin da ake kira da miuzik a yanzu?

A: Ya kasu kashi biyu akwai wanda ake yi wajajen wasa (da batsa) da rangwada wannan jin sa ya haramta, akwai kuma wanda yake ba wa“yannan wuraren ba shi bai haramta ba.

T: Akwai wani kala na miuzik wanda ake sanya shi kafin karatun kur’ani ko kiran sallah, ko kafin wasu shirye shirye na addini, ko bayan an gama  sai a sa su shin ya halatta a ji?

A: Da yawa irin wadannan yana daga cikin yankin da ya halatta a ji.

T: To yaya matsayin miuzik din da ake sawa tsakanin wani shiri zuwa wani ko kuma kafin watsa labarai?

A: Shi ma ya halatta.

T: Wasu daga cikin agoguna suna dauke da sauti wanda yake da kara irin ta miuzik, don faranta wa wanda yake dauke da ita ko da yaushe ya so shin ya halatta a sayar da ita ko a saye ta ko kuma a ji irin miuzik din da take yi?

A: Ya halatta.

T: Yaya matsayin miuzik din da ake yi wa take da “klasikal” wanda ake cewa yana sanya wa jijiyoyin da suka motsa nutsuwa, wani lokaci ma ana cewa yana iya yin maganin cutar da ta shafi hankali, shin ya halatta na ji?

A: Miuzik din da bai dace da wuraren wasa (ko batsa) da rangwada ba ya halatta.

T: Yaya matsayin miuzik (waka) din da ake sa shi tare da hotuna cikin gidajen telebijin domin nufin fito da  darajar wani fim ga masu ganinsa?

A: Mafi yawansu yana daga cikin wanda aka halatta,

T: Waka wacce take tsuma jiki ko wacce ake yi wa kasa wani lokaci ana sanya ta tare da miuzik shin ya halatta?

A: Ita ma ana kiyaye abubuwan da suka gabata dangane da ita.

Ban izini in yi maka tambayoyi guda biyu na karshe yi tambayoyiyinka.

T: Shin ya halatta mace ta fita daga gidanta domin wasu sha’anoninta, tana sanye da turare mazaje wanda ba muharramanta ba suna shekar kamshin?

A: Bai kamata ta aikata haka ba, kai bai ma halatta ba in har zai jawo fitina ga mazajen ko kuma zai sabbaba musu motsawar sha’awa.

T: Idan wani mai girma ya mutu mata suna sanya bakaken tufafi domin bakin ciki, wani lokaci ma su kan bugi fuska da kirji, da makamantansu shin hakan ya halatta?

A: I ya halatta.

 GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN TALIKAI

عنوان الکتاب