MUHAWARA KAN UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI GA MUMMUNA |
||
|
Babana ya ce yanzu dai ka san hukunce hukunce da dama kana ka koyi ababe da yawa da suka shafi lamurranka na shari’a. Yanzu haka ka san halal da haram , yanzu ka san abin da , da can ba ka sani ba . A halin yanzu ya kamata ka tuna lokacin da a da can kake cikin damuwa a yayin da kake cewa ya Allah ka dora min wajibai amma ban san su ba, ya Allah ta yaya ne zan samu in san halalinka domin in aikata ko kuma in san abin da ka haramta don in nesace su . A yanzu lokaci ya yi da ya kamata ka tuna cewa akwai yara matasa masu dunbin yawa kamar ka wadanda su ma a yau suke fama da irin matsalolin da ka fuskanta a baya suna cikin damuwa irin taka suna kuma neman sanin wajiban da ke kansu amma cikin wahala , shigen yanda kai ma da can ka karanta littattafan Fikihu amma ba ka gane ba . To yanzu tun da ka koyi lamurran da suka gabata kana tun da ka san hukuncen fikihu to lokaci ya yi da za ka yi aiki da fadin Allah Madaukakin sarki inda yake cewa : (kuma a sami wata jama’a daga cikinku suna kira zuwa ga aikin alheri kana suna umarni da kyakkyawan aiki suna kuma hani ga mummuna to wadannan su ne masu samun babban rabo) wato ka yi kira zuwa ga aikin alheri , ka yi umarni da kyakkyawan aiki kana ka yi hani ga mummuna. T: Da me zan yi umarni kana ga mene ne zan yi hani? A: Ka yi umurni da abin da ka sani na daga kyakkyawan aiki kana ka yi hani ga abin da ka sani daga munanan ayyuka. T: Ni kuma me ya hada ni da mutane ? ina ruwana da wanda ke mummunan aiki har da zan hana shi , kana tun da dai ni ina aikata kyakkyawan aiki ina kuma nesatan mummuna to wannan bai wadatar ba ? mene ne kuma zai kai ni ga shiga cikin sha’anonin mutane in rika musu umarni ko kuma in hane su ? A: Kada ka fadi haka kar kuma ka sake maimaita haka domin kuwa shi umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna a wasu marhalolinsa ya kan zama wajibin kifa’i ne don haka idan ba’a samu wani mutum guda wanda zai yi umarni da kyakkyawa ya yi hani ga mummuna ba wato ni ban yi ba kai ma ace ba ka yi ba kana wani mutum daban a cikin al’umma bai yi ba to a irin wannan hali dukkanmu mun aikata laifi kana dukkaninmu mun jawo fushin Allah madaukaki da azabarSa. Amma da za’a ce daya daga cikinmu zai yi umarni da kyakkyawa kana kuma ya yi hani ga mummuna to a wannan hali sai wajibcinsa ya zama ya kau daga kan sauran jama’a. Ka lura mana da fadin nan na Allah madaukaki inda yake cewa: ( kuma a sami wata jama’a daga cikinku tana kira zuwa ga aikin alheri tana umarni da kyakkyawa kana kuma tana hani ga mummuna to wadannan su ne masu samun babban rabo ). Wato ayar nan mai girma da na karanto maka ita dazu . Shin ba ka ji fadin Manzon tsira (s.a.w.a.) ba ne inda yake cewa : (al’ummata ba za ta gushe ba tana tare da alheri matsawar tana umarni da kyakkyawa kana kuma tana hani ga mummuna , kuma tana taimaka wa juna a kan aiki na kwarai , yayin da kuma suka bar aikata haka to za’a cire albarka daga gare su kana a dora sashensu a kan sashe suna addabarsu kuma babu mai taimaka musu adoron kasa ko asama ). Imam Ali (a.s) yana cewa : ( Kada ku bar yin umurni da kyakkyawa da hani ga mummuna ballantana a dora muku masu sharrin cikinku su shugabance ku sannan ku yi addu’a amma ba za’a karbi adduarku ba). Imam Bakir {a.s.} yana cewa : “ hakika umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna tafarkin Annabawa ne kana hanya ce ta salihai , farilla ce mai girma wacce da ita ake tsai da farillai kuma da ita ake aminta tafarkuna , da ita kasuwanci ke halatta kana da ita ake mai da zalunci , har wa yau da ita ake raya kasa a kuma dau fansa daga makiya al’amari ya daidaita”. A wata ruwayar kuma daga Imam Bakir {a.s.} yana cewa: “ umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna , halitta ne guda biyu daga halittun Allah duk wanda ya taimake su Allah zai daukaka shi , kana duk wanda ya ki taimaka musu to Allah ba zai taimake shi ba”. Shin ba ka karanta hadisin Manzon Allah [s.a.w.a.] ba ne inda yake cewa “ dukkanninku masu kiwo ne kana dukkanninku abin tambaya ne kan abin da yake kiwo” E na karanta. Don haka kai mai kiwo ne kana kuma kai abin tambaya ne kan ababen kiwonka .Shi makiyayi da ma akwai wajibai a kansa kana akwai hakkoki da suka rataya a wuyansa , to aikinsa mai nauyin gaske ne. To yanzu bayan wadannan bayanai har wa yau kana ganin cewa ba abin da ya hada ka da mutane ? To lallai umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna ba shiga sha’anonin mutane ba ne . Wannan abu ne wanda ya shafe ka , lallai ya shafe ka , domin kuwa wanda ya wajabta salla da azumi da haji da khumusi a kanka , shi ne ya wajabta maka yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna . T : Sai dai kuma ni ba malamin addini ba ne ballantana in yi umarni da kyakkyawa kana kuma na yi hani ga mummuna ? A : To da wane ne ya ce maka yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna abu ne wanda ya wajaba a kan malamin addini shi kadai ….. a’a wannan wajibi ne wanda ya rataya a kanka kamar yanda ya rataya a kaina haka kuma ya rataya a kan malamin addini da dalibi da malami da dan kasuwa da ma’aikaci da lebura da injiniya da soja da wanda yake shugabanci da talakawa da adali da fasiki da matalauci da mawadaci da namiji da mace …shi dai yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna abu ne da yake wajaba a kan kowa . Ka gayan cewa umarni da kyakkyawa hani da mummuna abubuwa ne wayanda suke wajibi, kuma a cikin misalin da ka ba ni na san wasu daga cikin wuraren da suke zamowa wajibi a kaina na yi umarni da kyakkyawa ko na yi hani da mummuna, sai dai yanzu ina son ka sanya min alamummuka wacce za ka ambata min iya al'amuran da suke wajaba a kaina in yi umarni da shi, ko kuma suke zamowa mustahabi in yi umarni da shi ka kuma iyakance min wuraren da suke zamowa wajibi a tare da ni na yi hani ga mummuna ban da wanda dazu dazu ka ambata, banda kuma wa''yanda suka wuce cikin muhawarar da muka yi. - A farko zan iyakance maka alamuran da za ka yi umarni da kyakkyawa a kansu kamar yanda ka nema, kana kuma na yi ma bayanin abubuwan da za ka yi hani da mummuna tare da sanya maka wani sharadi guda kafin na amsa. T: Wane abu ne wannan? A: Ina so ka yi aiki da ita idan na gaya maka tana matsayin mustahabi ko wajibi ne, kana kuma ka yi kira zuwa gare ta idan ta kasance kyakkyawa ka yi hani zuwa gare ta idan ta kasance mummuna. - Da farko zan fara da ambaton abubuwan da suke kyawawa bisa tsari wanda aka kayyade. · Da mahaifina ya fadi haka sai ya fara kididdige min wuraren yana mai amfani da haddansa wani lokaci da kuma littattafa dake gaba gare shi wani sa’i, daga cikin aiyuka na gari sai ya lissafa min su kamar haka- na farko- tawakkali ga Ubangiji domin Ubangiji madaukakin sarki ya fada cikin littafinsa mai girma [Duk wanda ya dogara da Ubangiji to Ya wadatar masa] an ruwaito cewa wani mai tambaya ya tambayi Imamu (A.S) a bisa wannan aya sai Imamu (A.S) ya ce masa tawakkali ga Allah hawa hawa ne yana daga ciki ka yi tawakkali ga Allah cikin dukkanin al amuranka, duk abin da ubangiji ya aikata a gare ka ya zamo ka yarda da shi, ka sani dukkanin abin da ya same ka na alheri ko kuma falala, ka san dukkannin hukumci cikin hakan na Allah ne sai ka yi tawakkali ga Allah cikin fauwala masa dukkannin abubuwa ka kuma amince da hukumcinsa cikin abubuwa na alheri da kishiyarsa na biyu:- riko da Ubangiji don Allah yana fade cikin littafinsa me girma . “Duk Wanda yai riko da Allah hakika ya shiriya zuwa tafarki madaidaici.” An karbo daga Imam Ja'afaru Sadik (A.S) ya ce ubangiji madaukakin sarki ya yo wahayi zuwa Annabi Dauda cewa:- Babu wani bawa daga cikin bayina da zai yi riko da ni ya ki yin riko da wani daga cikin bayina na san kuma niyyarsa ita ce ya yi riko da ni din, sannan a samu halittun sama da kasa su nufe shi da sharri face sai na sama masa mafita daga tsakanin sharrinsu. Kana ba'a sami wani bawa daga cikin bayina ba da zai yi riko da daya daga cikin halittuna na gane haka cikin niyyarsa, har sai na yanke arzikin sama daga hannunsa kana na yanke arzikin kasa ta karkashinsa ba tare da na damu da kwarin da zai je ya halaka ba: na uku:- yi wa Allah godiya bisa ni'imominsa wayanda suke zuwa ta koina Allah madaukakin sarki yana cewa cikin littafinsa mai girma [Ba wata ni'ima da kuke tare da ita face daga Allah take] Allah madaukakin sarki ya ce a wata ayar [ya ubangiji ka ba ni damar in gode maka bisa ni'imarka wacce ka ni'imce ni da ita, ka kuma ba ni damar na yi aiki na gari wanda ka yarda da shi”, an karbo daga Imam Jaafarus Sadik (A.S) yana cewa Allah bai yi wata ni'ima a bisa wani bawa ba ko yaya take, face idan ya yi godiya a kanta har sai godiyarsa ta zamo ta fi wannan ni'imar nauyi a mizani. Na hudu:- kyautata zato ga ubangiji an karbo daga Imam Bakir (A.S) ya ce:- mun samu cikin littafin Imamu Ali (A.S) Manzon Allah (S.A.W.A) ya fada a kan minbarinsa cewa nai rantsuwa da ubangiji da ba wani sai shi ba'a ba wa wani mumini alherin duniya da lahira ba sai sabida kyautata zatonsa ga Ubangiji da kyautata kaunarsa da kyakkyawar dabi'arsa. Na biyar-yin yakini da Allah kan cewar shi yake azurtawa shi yake rayawa, amfani ko cuta daga gare shi ne, an karbo daga Imamu Ali (A.S), yana cewa, ba yanda za'a yi wani bawa ya sami dandanon imani har sai ya san cewar duk abin da ya same shi daman bai kasance zai kuskure masa ba, kana abin da ya kuskure masa bai kasance zai same shi ba, kana mai amfanarwa mai cutarwa shi ne Ubangiji madaukaki. Na shida:- tsoron Ubangiji madaukaki, tare da kaunar rahamar, ubangiji, Allah madaukaki yana fade cikin littafinsa mai girma yana siffata muminai [su ne wayanda suke nesanta hakarkarinsu daga wurin kwanciya suna masu kiran Allah tare da tsoro da tsammani kana suke ciyarwa daga abin da muka azurta su da shi]. An samo hadisi daga Imam sadik (A.S) yana cewa: [wanda ya sami damar aikata wani zunubi sai ya ji tsoron Allah kana ya ji kunyar mala'lkun da suke tare da shi Ubangiji ya gafarta masa dukkannin zunubansa ko da ko sun kai misalin yawan zunuban mutane da aljanu.] Imam sadik (A.S) yana cewa :- [ka kaunaci Ubangiji cikakkiyar kauna wacce ba za ta ba ka tsaurin ido kan sabonsa ba sannan ka ji tsoron ubangiji tsoron da ba zai sa ka yanke kauna ga rahamarsa ba.] Na bakwai:- hakuri da hadiye fushi Allah yana fade cikin Al'Qur'ani [masu hakuri ne kadai ake cika musu ladansu ba tare da wani lissafi ba”. A wani wurin Allah na cewa:- [Allah yana tare da masu hakuri” kana a wani wurin yana fadin “da masu hadiye fushi, da masu yi wa mutane afuwa Ubangiji na son masu kyautatawa]. An samo daga Manzon Allah (S.A.W.A) yana cewa:- [Bawa bai hadiye wani abu mafi girman lada ba tankar hadiye fishi don Allah]. An karbo hadisi daga Manzon Allah (S.A.W.A) yana cewa:-[yana daga hanya mafi soyuwa zuwa ga Allah hadiye abubuwa guda biyu, hadiye fushi ta yin hakuri da hadiye musifa ta yin juriya. An karbo daga Imam Bakir (A.S) yana gayawa daya daga cikin ''ya''yansa [ya dana ba wani abu wanda ya fi faranta wa mahaifinka rai sama da hadiye fishi wanda yake karshensa hakuri]. Na takwas:- yin hakuri bisa abubuwan da Allah ya haramta. An karbo daga Imamu Ali (A.S) yana cewa:- [hakuri kala biyu ne yin hakuri lokacin musifa abu ne mai cikakken kyau sai dai wanda ya fi shi kyau yin hakuri da abubuwan da Allah ya haramta maka” An dai kuma karbo daga gare shi yana cewa ku ji tsoron sabon Ubangiji lokacin da kuke ku ku kadai domin wanda yake ganinku lokacin da kuke aikatawa shi ne mai hukumci. Na tara:- Adalci Allah yana fade cikin Al'Qur'ani mai girma [Allah yana yin umarni da adalci da kuma kyautatawa] An karbo daga Ja'afarsu sadik [A.S.] [mutane guda uku su ne mafi kusancin halitta zuwa ga Allah ranar alkiyama har zuwa lokacin da za a gama hisabi] mutumin da lokacin da yake cikin fushi karfinsa bai kai shi ga ya cutar da wanda yake karkashinsa ba, kana da mutumin da ya yi tafiya da mutane guda biyu bai karkata zuwa ga daya ba daga cikinsu kana bai fifita shi ba ko da ko da kwayar al kama, da kuma mutumin da ya fadi gaskiya kan hakkin da ake bin sa. Na goma:- hankali ya rinjayi sha'awa, Allah madaukaki yana fade cikin littafinsa mai girma [an kawata wa mutane son sha'awuwwuka daga mata da ''ya''ya da dukiyoyi wanda ake tarawa na zinare da azurfa da dawaki kiwatattu da dabbobin ci da kayan noma wannan shi ne dadin rayuwar duniya kuma a wurin Allah kyakkyawar makoma take]. An karbo hadisi daga manzon Allah (S.A.W.A) yana cewa:- [Aljanna na farin ciki ga mutumin da ya bar sha'awar da ta zo masa domin makomar da bai gan ta ba]. An karbo wani hadisin daga Imamu Ali (A.S) yana cewa:- [Da yawa sha'awa ta lokaci guda ta haifar da bakin ciki mai tsayi]. Na sha daya:- kaskantar da kai An karbo daga Manzon Allah (S.A.W.A) yana cewa:- [wanda na fi so daga gare ku, kana wanda ya fi kusanci da ni a gurin zama daga cikin ku ranar tashin alkiyama, shi ne wanda ya fi ku kyakkyawar dabi'a, ya fi ku tsananin kaskantar da kai”, An karbo hadisi daga Imam zainul Abidin (A.S) ya yi Add'a zuwa ga Ubangiji yana mai fadin [ya ubangiji ka yi tsira ga Annabi muhammadu da alayensa ina rokonka kar ka daukaka ni cikin mutane da wata daraja har sai ka sanya misalin ta ba abakin komai ba cikin raina kar ka fari wata daukaka mabaiyaniya a gare ni har sai ka haifar mini wani kaskanci makamanciyarta cikin raina]. Na goma sha biyu:- yin tattali cikin abinci ko abin sha, ko makamantansu don Allah madaukakin sarki cikin littafinsa mai girma yana cewa [ku ci ku sha kar ku yi barna domin Allah ba ya son mabarnata]. An karbo kuma daga Imam Sadik (A.S) yana cewa:- Manzon Allah ya ci abinci da maraicen ranar alhamis a masallacin kuba, sai ya ce akwai abin sha? sai [Ausu dan haula] ya zo masa da madara hade da ruwan zuma a ciki lokacin da manzo ya dora ta a bakinsa sai ya kawar da ita, kana ya ce:- abin sha iri biyu a hade kowane dayansu ya wadatar ni ba na sha ban kuma haramta a sha ba, sai dai ina mai kaskantar da kai zuwa ga Allah domin wanda ya kaskantar da kai Allah zai daga shi, wanda ya yi girman kai Allah zai kaskantar da shi wanda kuma ya yi tattali cikin rayuwa Allah zai azurta shi wanda yai almubazzaranci Allah zai hana shi, wanda ya yawaita tuna mutuwa Allah zai so shi]. Na sha uku:- yi wa mutane adalci ko da a kansa ne Manzon Allah (S.A.W.A.) yana cewa:- Wanda ya yalwata wa fakiri, ya kuma yi wa mutane adalci a kansa wannan shi ne mumini hakkan. An kuma karbo daga gare shi (S.A.W.A.) cewa “shugaba cikin ayyuka shi ne ka yi wa mutane adalci a kanka, kana ka yalwata wa dan uwanka na addini da kuma ambaton Allah cikin kowane hali”. An karbo wani hadisin daga Imam Ali (A.S) yana cewa: “ku saurara: wanda yake yi wa mutane adalci a kansa ba abin da Allah zai kara masa face daukaka.” Na sha hudu: kamewa: An karbo daga Imam Bakir (A.S.) yana cewa: “mafificiyar ibada ita ce kame ciki da kame farji” Na sha biyar:- mutum ya shagaltu da aibinsa ya bar aibukan mutane An karbo daga manzon Allah (S.A.W.A) yana cewa [Aljanna na farin ciki da mutumin da tsoron Allah ya shagaltar da shi ga tsoron mutane, kana Aljanna na farin ciki da wanda aibinsa ya shagaltar da shi ga aibukan muminai.] Na goma sha shida:- Dabiantuwa da kyawawan dabi'u Allah yana cewa:- cikin wurin da yake siffata annabinsa mai girma [lallai kai kana kan dabiu masu girma]. An kuma karbo daga Manzon Allah (S.A.W.A) [kyakkyawar dabi'a tana daga cikin halittun Allah mafi girma]. An dai karbo wani hadisin daga gare shi yana cewa:- shin in ba ku labarin wanda ya fi ku kama da ni?. Sai suka ce: E ya Maaikin Allah sai ya ce:- wanda ya fi ku kyakkyawar dabi'a mafi taushin ranku, mafi zaman lafiyarku ga makusantansa, wanda ya fi ku tsananin son yan uwansa na addini, wanda ya fi ku juriya a bisa gaskiya, wanda ya fi ku shanye fushi kana wanda ya fi ku yin rangwame, wanda ya fi ku tsananin adalci a kansa lokacin da yake cikin yarda ko fushi]. An ruwaito cewa maaiki (S.A.W.A.) an ce da shi wanne mumini ne ya fi muminai imani sai ya ce [wanda ya fi su kyakkyawar dabi'a]. An karbo kuma dai daga gare shi ya ce:- “mafi yawan abin da za'a shiga aljanna da shi tsoron Allah da kyakkyawar dabi'a.” Na sha bakwai:- hakuri an samo hadisi daga Manzon Allah S.A.W.A. ya ce Allah bai taba daukakawa da jahilci ba, kana bai taba kaskantarwa ba bisa hakuri]. An samo daga Imamu Rida [A.S.] yana cewa:- mutum ba ya zamowa mai bauta har sai ya kasance mai hakuri. Na sha takwas:- haddace al'Qur'ani mai girma, da aiki da shi, da kuma karanta shi Allah yana fadi cikin littafinsa mai girma [wayanda suke karanta littafin Allah kuma suka tsai da sallah suka kuma ciyar da abin da Allah ya azurta su da shi a boye da sarari, suna masu kaunar kasuwancin da ba asara]. An kuma karbo daga Manzon Allah (S.A.W.A.) ya ce:- [ma'a buta al'Qur'ani su suke kan mafi girman daraja daga cikin bani Adam in aka dauke annabawa da mursalai]. An karbo daga Imamu Sadik (A.S) ya ce:- [mahaddata al'Qur'ani wayanda suke aiki da shi suna tare da Mala'iku masu daraja da da'a” An karbo daga Imamu sadik (A.S) ya ce:- [wanda ya karanta al'Qur'ani yana mumini matashi al'Qur'ani zai cudanya da jininsa da namansa, sannan ubangiji zai sanya shi cikin mala'iku masu girma da da'a, al'Qur'ani kuma zai kasance hujjarsa ranar al kiyama]. Akwai wata falala ta musamman don karanta wasu kebantattun surori na al'Qur'ani wacce aka ambata cikin littattafan hadisi don haka in ka so sai ka je ka duba. Na sha tara:- ziyarar Manzo da Imam Ali da Fatimatuz zahra da Imam Hasan da Hussain da ragowar Imamai (A.S) an karbo daga imam Bakir (A.S) ya ce:- Imam Hussaini dan Ali (A.S) ya ce da Annabi muhammadu (S.A.W.A) ya babana mene ne sakamakon mutumin da ya ziyarce ka? Sai manzon Allah (S.A.W.A) ya ce da shi [wanda ya ziyarce ni ko ya ziyarci mahaifinka, ko ya ziyarce ka, ko kuma ya ziyarci dan uwanka ya zama hakki a kaina in ziyarce shi ranar tashin alkiyama har in kubutar da shi daga zunubansa, an kuma karbo daga Imamu sadik (A.S) cewa:- duk wanda ya ziyarci kabarin Imamu Husaini dan imamu Ali yana mai sane da hakkinsa za'a rubuta shi cikin wayanda suke'a aljanna madaukakiya,” an kara karbowa daga gare shi cewa “wanda ya ziyarci daya daga cikin mu kamar ya ziyarci Imam husaini ne]. Na ishirin:- gudun duniya an karbo daga Manzon Allah (S.A.W.A.) cewa [ka guji duniya sai Allah ya so ka] an kuma karbo daga gare shi ya ce:- [ku ji kunyar ubangiji cikakkiyar kunya sai suka ce ai muna jin kunyar Allah sai ya ce ba irin wanna kunyar ba domin kuna gina abubuwan da ba za ku zauna a cikinsu ba, kuna kuma tara abubuwan da ba za ku ci su ba] an karbo dai daga gare shi (S.A.W.A) ya ce:- [in Allah ya so alheri ga bawa sai ya sanya masa gudun duniya ya sanya masa son lahira kana ya sanya masa azancin gane aibinsa”] an karbo daga imamu Ali (A.S) ya ce:- yana daga abin da ya fi taimakawa kyawawan dabi'u cikin addini gudun duniya. An karbo dai daga gare shi ya ce:- alamar mai kwadayin ladan lahira ita ce gujewa kawace kawacen duniya] mai shudewa. An karbo daga Imam zainul abidin (A.S) ya ce:- [bayan sanin Allah da Maaiki ba wani aiki mafi falala sama da kin duniya]. An kuma ruwaito cewa:- wani mutum ya ce da Imamu sadik (A.S) ba mu gamuwa sai shekaru ka ba ni wasiyya kan wani abu wanda zan yi riko da shi, sai ya ce masa [ina yi maka wasiyya da tsoron Allah da tsentseni da kokari a hir dinka kake kwadayin wanda yake sama da kai abin da ubangiji madaukaki ya fadawa maaiki cikin al'Qur'ani mai girma cewa:- [karka mika idonka zuwa ga jin dadin da muka ba da shi ga wasu daga cikinsu na mata, wanda yake na kyale kyalen rayuwar duniya] a wani wurin yana cewa:- kada dukiyar su ko kuma ''ya''yansu su burge ka. [Idan ka ji tsoron irin wannan rayuwar ta gudun duniya to ka tuna rayuwar Manzo, ta yanda abincinsa daga sha’ir ne zakinsa dabino ne, kirarensa daga icen dabino don haka idan wata masifa ta same ka a kanka, ko dukiyarka, ko ''ya''yanka to ka tuna irin masifar da ta same ka dangane da Ma'aiki, domin halittu ba'a jarrabe su da masifa ba ko kadan kwatankwacin yanda aka jarabce su dangane da shi, an ruwaito cewa Imamu kazim (A.S) ya tsaya a kan wani kabari ya ce abin da haka ya zama karshensa to lallai a yi taka tsantsan cikin farkonsa, kuma abin da haka ya zama farkonsa to lallai a ji tsoron karshensa]. Na ishirin da daya:- taimakon mumini da kau masa da bakin cikinsa, da faranta masa rai, da ciyar da shi, da biya masa bukatunsa, an karbo daga Imamu Ja afar (A.S) ya ce:- [Ba wani mumini da zai taimaka wa wani mumini wanda aka zalunta sai taimakon ya kasance fiye da azuminsa na ramalana, da itikafinsa da yai a masallacin Makka, ba kuma wani mumini, da zai taimaka wa dan uwansa mumini alhali yana da ikon taimaka masa din, har sai Ubangiji ya taimaka masa duniya da lahira, kana ba wani mumini da zai ki taimakawa dan uwansa mumini, bayan yana da ikon taimaka masa, har sai Ubangiji shi ma ya ki taimaka masa duniya da lahira]. An samo wani hadisin daga gare shi ya ce:- [dukkannin muminin da ya yaye wa dan uwansa mumini wani bakin ciki, sai Ubangiji ya yaye masa bakin ciki saba'in na duniya da lahira]. An dai karbo daga gare shi ya ce:- [wanda ya saukakewa mumini lokacin da yake cikin tsanani Allah zai saukake masa bukatunsa duniya da lahira]. An karbo wani hadisin daga gare shi ya ce:- [Ubangiji madaukakin sarki yana cikin taimaka wa mumini muddun dai mumini yana taimakawa dan uwansa mumini]. An karbo wani hadisin daga gare shi cewa:- [wanda ya faranta wa wani mumini rai Allah zai faranta masa ranar alkiyama sai kuma a ce da shi ka nemi abin da kake so daga Allah don hakika ka kasance kana son farantawa masoyan sa a duniya]. An karbo wani hadisin daga gare shi [wanda ya shigar da farin ciki ga mumini kamar ya shigar wa da manzon Allah ne wanda ya shigar wa da manzo hakika hakan zai kai har zuwa ga Allah, haka nan kuma wanda ya bakanta masa rai]. An karbo daga gare shi [wanda ya ci da mumini daga yunwa Ubangiji madaukaki zai ciyar da shi daga ''ya''yan itaciyar aljanna, wanda kuma ya shayar da mumini daga kishin ruwa Allah zai shayar da shi daga ruwan lahira, wanda ya tufatar da mumini Allah zai tufatar da shi da tufafin aljanna”. An karbo wani hadisin daga gare shi “ba'a sami wani ya biya wa musulmi bukata ba har sai ubangiji madaukaki ya yi shela cewa:- ladanka na kaina kana ba wurin da na yardar maka da shi in ba aljanna ba]. Na ishirin da biyu:- yi wa kai hisabi ko wacce rana, an ruwaito cewa:- Manzon Allah (S.A.W.A) ya yiwa Abu zarril gifari wasiyya sai ya ce:- ya abu zar ka yi wa kanka hisabi tun kafin a yi maka don shi ya fi sauki da wanda za'a yi maka ranar al kiyama, ka auna ayyukanka tun kafin a'auna maka, kana ka yi tanadi ga mafi girman abin da zai bijiro ranar da ake bijiro da shi ba wani abu da yake buya wa Allah] an dai karbo daga gare shi (S.A.W.A.) ya ce ya aba zarri mutum ba ya kasancewa daga cikin masu tsoron Allah har sai ya yi wa kansa hisabi sama da yanda aboki yake yi ya san daga ina ne abincinsa da abin shansa yake zuwa, kana daga ina ne tufafinsa yake zuwa, shin ta hanyar halas ce ko haram, ya Aba zarri duk mutumin da bai lura da ta inda dukiya take zuwar masa ba to Allah ba zai lura da ta inda zai sa shi a wuta ba]. An samo hadisi daga Imam Zainul abidin (A.S) ya ce:[ya dan Adam ba za ka gushe ba kana tare da alheri muddun dai kana da mai yi maka wa'azi tare da kai cikin ranka, muddun kuma kana kulawa da yi wa kanka hisabi, ya dan adam za ka mutu, kuma za'a tashe ka, za'a tsai da kai gaban Ubangiji don haka ka tanadi amsa]. Na ishirin da uku:- kulawa da al'amarin musulmi, an karbo daga Manzon Allah (S.A.W.A.) ya ce:- [Duk wanda ya wayi gari ba ya kulawa da al'amarin musulmi, shi ba musulmi ba ne, an kuma karbo daga gare shi:- wanda ya wayi gari ba ya kulawa da al amarin musulmi wannan ba ya daga cikinsu wanda ya ji wani mutun yana kiran musulmi su taimaka masa bai amsa masa ba, ba musulmi ba ne shi]. An karbo hadisi daga Imamu Bakir: “Ba'a nemi bukata ga mumini ba wacce bai da ita, ya ji rashin dadi a ransa da damuwa, har sai ubangiji madaukakin sarki ya sanya shi a'ajanna sabili da damuwar]. Na ishirin da hudu:- kyauta da fifita wani a kanka, Ubangiji madaukaki yana fade cikin al'Qur'ani mai girma [suna masu zabin wasu a kan kansu ko da ko suna da tsananin larura] an ruwaito daga manzon Allah (S.A.W.A) ya ce:- [Allah bai sanya waliyyansa ba sai a kan kyauta da kyakkyawar dabi'a, ya kuma ce yana daga abin da yake wajabta yin gafara, kyautar abinci da yawaita sallama, da kyakkyawar magana”, an ruwaito ya ce:- [ku kau da kai ga zunubin mai kyauta domin duk lokacin da ya yi tuntube Allah na rike da hannunsa]. An ruwaito daga gare shi (A.S) [Aljanna gidan masu kyauta ne,] an kara ruwaitowa daga gare shi (S.A.W.A.) ya ce:- [wanda ya fi mutane imani shi ne wanda ya fi su kyauta]. Na ishirin da biyar:- ci da iyali an karbo daga Manzon Allah (S.A.W.A.) ya ce:- [wanda ke shan wahala sabili da ci da iyalinsa kamar mai jihadi ne fi sabilil lahi] [ya kuma ce mafificinku shi ne wanda ya fi ku alheri ga ahalinsa]. An karbo daga gare shi (S.A.W.A.) [Abin da mutum ya ciyar a bisa iyalinsa sadaka ne] An kuma karbo daga gare shi (S.A.W.A) ya ce:- [Dinaren da ka ciyar a bisa ahalinka da dinaren da ka ciyar fi sabilil lah da dinaren da ka ciyar cikin ‘yanta bayi da dinaren da ka yi sadaka da shi a bisa miskini wanda duk ya fi su lada shi ne dinaren da ka ciyar a bisa ahalinka]. Na ishirin da shida:- tuba daga Kananan zunubai da manya da kuma yin nadama. Ubangiji yana fade cikin littafinsa mai girma:- [ya ku wayanda ku ka yi imani ku tuba ga Allah tuban da ba za ku koma ba, watakil Ubangiji ya kankare muku munanan ayyukanku ya shigar da ku Aljanna wacce koramu suke gudana ta karkashinta]. A wani wurin Allah yana fade [ku tuba zuwa ga Allah dukkanninku ya ku muminai watakil ku rabauta]. A wata ayar yana cewa:- [Allah na son masu yawan tuba masu kuma yawan tsarki. A wata ayar yana cewa:- [shi ne wanda yake karbar tuban bayinsa, yake yin afuwa ga munanan ayyuka, yake kuma sanin abin da ku ke aikatawa]. A wata ayar Allah yana cewa:- [ka gaya musu ya ku bayina wadanda suka yi barna a bisa kayukansu, kada ku debe kauna daga rahamar Allah lallai Allah na gafarta zunubai baki daya kana shi ne mai yawan gafara mai jin kai]. An karbo daga Imam Bakir (A.S) ya ce:- da Muhammadu dan muslimu [ya muhammadu dan muslimu zunuban mumini idan ya tuba daga ita abar gafartawa ce a gare shi to mumini ya canja zuwa sabon aiki bayan tubansa da gafarta masa da aka yi, amma wallahi hakan ba ta kasancewa sai ga ma'abuta imani, sai na ce da shi ko da ya aikata ba sau daya ba ba sau biyu ba yana daukan zunubi ya tuba ya nemi gafarar Allah sai Imam ya ce:- ko da yaushe mumini ya koma yai istigifari (ya tuba) Ubangiji zai maimaita masa gafara]. An karbo daga gare shi (A.S) ya ce:- [mai tuba daga zunubi kamar wanda bai da zunibi yake, wanda kuma yake ci gaba da aikata zunubi yana mai neman tuba kamar mai izgili yake]. An karbo daga Imam Sadik (A.S) ya ce:- [ba wani bawa da zai aikata wani zunubi ya yi nadama akai har sai Ubangiji ya gafarta masa kafin ya tuba]. An dai karbo daga gare shi ya ce:- [Ubangiji madaukakin sarki yana farin ciki da tuban bawansa mumini idan ya tuba, kamar yanda daya daga cikinku yake farin ciki idan ya sami abinsa wanda ya bata]. Akwai wasu kyawawan ayyuka ban da wadannan wadanda littatafan fikihu da na hadisai suka tabbatar da su idan ka so dadi sai ka duba su. T: Sai na ce da mahaifina abin da aka lissafo wadanda suka wuce dukkanninsu suna nuni ne kan ayyuka na gari, to yaya munanan ayyuka ko ko wasu daga cikin wadanda aka lissafa? A: Abubuwan da ake lissafa su daga cikin munanan ayyuka suna da yawa zan lissafo maka wasu daga ciki amma bisa sharadin da ya gabata. T: Kana nufin nai maka alkawarin zan nesace su kana kuma zan hana aikata su? A: I haka nake nufi. :- Nai maka alkawarin haka. Sai ya ce yanzu zan gaya maka wasu daga cikin munanan ayyuka. Na daya:- zalunci Allah madaukakin sarki cikin littafinsa mai girma yana cewa:- [wayanda suka yi zalunci da sannu za su sani ga wacce makoma ce suke komawa]. An karbo daga Imamu Ali (A.S) [mafi girman kura kurai cirar dukiyar mutumin da yake musulmi ba tare da hakki ba]. An karbo daga Imamu Bakir (A.S) ya ce:- [lokacin da wafatin Imamu Ali bin Hussaini ya zo (A.S) sai ya hada ni da kirjinsa kana ya ce:- [ya dana zan yi maka wasiyyar abin da mahaifina yai min wasiyya da shi lokacin da wafatinsa ya zo, yana daga cikin abin da ya ambata wanda mahaifinsa yai masa wasiyya da shi cewa:- [ya dana ahir dinka da zaluntar wanda ba shi da wanda zai taimaka masa a kanka sai Allah]. An karbo daga Imam sadik (A.S) [wanda yai zalunci ko da guda daya tak za'a karbi abin da ya zalunta cikin jikinsa ko dukiyarsa ko ''ya''yansa]. An karbo daga gare shi ya ce:- [wanda ya ci dukiyar dan uwansa da zalunci bai mayar masa kuma da ita ba, ya ci garwashi ne na wuta gobe kiyama]. Na biyu:- taimakawa a yi zalunci da yarda da shi: An karbo daga Manzon Allah [S.A.WA.] [wanda ya tafi wajen azzalumi domin ya taimaka masa bayan ya san kuma azzalumi ne hakika ya fita daga musulunci, An kuma karbo daga gare shi cewa:- mafi sharrin mutane wanda ya sai da lahirarsa sabili da duniyarsa, wanda ya fi wannan sharri kuwa shi ne wanda ya sai da lahirarsa sabili da duniyar waninsa]. An karbo daga Imamu sadik (A.S) ya ce:- [mai aikata zalunci da mai taimakonsa da wanda ya yarda da shi dukkaninsu masu tarayya ne cikin zalunci. An karbo daga wurinsa [A.S.] ya ce:- wanda ya ba wa azzalumi uzuri akan zaluncinsa Allah madaukaki zai sallada wanda zai zalunce shi, idan ya yi addua ba za a karba ba. An kuma samo daga wajensa [A.S.] a cikin wasiyya da ya yi wa sahabansa yana cewa:- Ahir dinku, ku taimaka wa azzalumi a kan musulmi ya yi muku addua a amsa masa, cikin abin da ya yi muku addu'ar, hakika babanmu Manzo mai tsira ya kasance yana cewa:- [Adduar musulmi wanda aka zalunta abar amsawa ce]. An kuma karbo daga wajensa ya ce:- wanda ya taimaka ko da da yankin kalma aka kashe musulmi zai zo ranar tashin kiyama a tsakanin idonsa an rubuta mai debe kauna daga rahamar Allah]. An karbo daga gare shi wani mutum zai zo wajen wani mutum ranar tashin Alkiyama ya shashshafe shi da jini, sai ya ce da shi ya bawan Allah me ye tsakanina da kai, sai ya ce da shi ranar kaza da kaza ka taimaka da wata kalma aka kashe ni. Na uku:- mutum ya kasance cikin wadanda ake jin tsoron sharrinsu, manzon Allah (S.A.W.A) ya ce:- [sharrin mutane a wajen Allah ranar tashin Al kiyama su ne wadanda ake girmama su don tsoron sharrinsu]. An karbo daga Imamu sadik (A.S) ya ce:- [yana daga mafi kin halittun Allah bawan da mutane suka ji tsoron harshensa]. Na hudu:- yanke zumunci :Allah madaukaki ya fada cikin littafinsa Ashe baku kusata idan kuka ba da ba ya ku yi barna cikin kasa kana ku yanke zumuncinku]. An karbo daga manzon Allah (S.A.W.A)[kada ka yanke zumunci ko da ko kai an yanke maka]. AN karbo daga Imamu Bakir (A.S) ya ce:- a cikin littafin Ali [A.S.] cewa:- [Dabi'u guda uku har abada ma'abucinsu ba zai mutu ba har sai ya ga mummunan sakamakonsu, zalunci, yanke zumunci, rantsuwar karya wanda ya fuskanci Allah da ita]. An karbo daga Imam Ja’afar sadik (A.S) ya ce:- [wani mutum daga khas'am ya zo wurin Annabi muhammadu sai ya ce ya manzon Allah ka ba ni labarin abin da ya fi a musulunci sai Ma aiki ya ce:- imani da Allah, sai ya ce sannan sai me, sai Ma aiki ya ce sadar da zumunta, sai ya kara cewa:- kana sai me sai Ma aiki ya ce yin umarni da kyakkyawa, da hani da mummuna, sai ya ce ka ba ni labarin wanne aiki ne Allah ya fi ki, sai Ma aiki ya ce shirka da Allah, sai ya ce sannan sai me, sai Ma aiki ya ce yanke zumunci, sai ya ce sannan sai me, sai maaiki ya ce yin umarni da mummuna, da yin hani da kyakkyawa]. Na biyar:- fushi An karbo daga Imam Bakir (A.S) ya ce:- [mutum ba zai yi fushi ba ya ki hucewa har sai ya shiga wuta, dukkannin mutumin da ya yi fushi a bisa jama'arsa yana tsaye to ya zauna da sauri domin cewa daudar shaidan za ta tafi a tare da shi, dukkannin mutumin da ya yi fushi a bisa dan uwa na zumunci to ya kusance shi, ya shafe shi domin ita zumunta in an shafe ta sai ta sami nutsuwa, An karbo daga wajen Imam Sadik (A.S) ya ce:- fushi shi ne mabudin dukkannin sharri]. Na shida:- girman kai da takama [Allah madaukaki yana fada a cikin al'Qur'ani [ku shiga kofofin jahannama kuna masu dauwama a cikinta, tirkashi da munin makomar masu girman kai]. A wani wurin Allah madaukakin sarki yana cewa:- kada ka karkatar da kumatunka ga mutane, kar ka yi tafiya akan kasa kana mai nuna fadin rai don Ubangiji ba ya son dukkannin mai takama, mai Alfahari]. An karbo daga Manzon Allah (S.A.W.A) yana cewa:- [mafi yawan yan wutar jahannama masu girman kai ne]. An kuma karbo daga gare shi ya ce:- [wanda ya yi tafiya kan kasa yana mai takama da kasar da abin da ke samanta da kasanta za su tsine masa]. An kuma karbo daga gare shi (A.S) ya ce :- [wanda yake jin shi babba ne a cikin ransa, kana yai takama a tafiyarsa zai gamu da Allah yana fushi da shi]. An karbo daga Imam ja'afar sadik da Imam Bakir (A.S) sun ce [Duk wanda a cikin zuciyarsa akwai girman kai misalin kwayar zarra ba zai shiga Aljanna ba]. An karbo daga Imam sadik (A.S) ya ce:- [masu jin kansu da dagawa su suka fi mutane nisa da Allah ranar tashin Alkiyama.] Na bakwai:- cin dukiyar marayu bisa zalunci Allah madaukaki ya ce cikin littafinsa mai girma [wadanda suke cin dukiyoyin marayu da zalunci suna cin wuta ne a cikinsu, da sannu za su konu da wutar sa'ira]. Na takwas:- rantsuwar karya: An karbo daga Imamu Bakir (A.S) ya ce:- yana daga abin da ya zo cikin littafin Ali [A.S.] [Rantsuwar karya da yanke zumunci suna barin gidaje rusassu ga masu gidajen]. An karbo daga Imam sadik (A.S) ya ce:- [wanda ya rantse bayan kuma ya san karya yake yi hakika ya yi fito na fito da Allah]. Na tara:- shedar zur, wato shedar karya Allah na fadi cikin Al'Qur'ani mai girma [su ne wayanda ba sa shedar zur idan kuma suka wuce wuraren yasassar magana, sai su wuce suna masu kare girmansu]. An karbo daga Manzon Allah (S.A.W.A) ya ce:- [Ba wani mutum da zai yi shedar zur a kan dukiyar wani mutum don ya raba shi da ita, har sai Ubangiji ya rubuta masa masauki mai kunci cikin wuta]. Na goma:- makirci da yaudara Allah madaukaki yana fade a cikin Al'Qur'ani [mutanen da suka yi laifi da sannu kaskanci da azaba mai tsanani za ta same su daga wajen Allah saboda abin da suka kasance suna makircinsa]. An karbo daga manzon Allah ya ce:- [Ba ya daga cikinmu duk wanda ya yi wa wani musulmi makirci]. An karbo daga Imam Ali (A.S) ya ce:- [Ba don makirci da yaudara suna aiyukan wuta ba ne da na kasance wanda ya fi larabawa iya makirci]. Na sha daya:-[wulakanta mumini musamman ma fakiri, da nuna shi ba komai ba ne]. An karbo daga Imam Ja afarus sadik (A.S) [kada ku wulakanta mumini wanda yake fakiri don duk wanda ya wulakanta mumini ya nuna shi ba komai ba ne Allah madaukaki zai wulakanta shi, Ubangiji ba zai gushe ba yana mai fushi da shi har sai ya daina wukakanta shi ko ya tuba]. An kuma karbo daga gare shi [duk mutumin da ya kasakantar da mumini ya wulakanta shi saboda rashin abin hannunsa da talaucinsa Allah zai tozarta shi ranar tashin Al kiyama a idon jama'a]. Na sha biyu:- hassada Allah madaukaki yana cewa [Daga sharrin mai hassada idan ya yi hassada]. An ruwaito daga Imam sadik (A.S) ya ce:-[lallai hassada tana cin imani kamar yadda wuta take cin kirare]. An kuma karbo daga gare shi:- [shi mumini yana kaunar shi ma ya samu ne ba ya hassada munafiki kuma yana hassada ba yana burin shi ma ya samu ba ne]. An karbo daga gare shi [Asalin kafurci abu uku ne, kwadayi, girman kai, da hassada]. Na sha uku:- Giba wato yi da wani da sauraronsa, Allah madaukaki yana fadi a cikin Al'Qur'ani [kada ku yi leken asiri kada kuma sashenku su yi gibar sashe, shin daya daga cikinku yana so ya ci naman dan uwansa mushe lallai ba kwa so haka ba]. An karbo daga Imam sadik (A.S) [yi da mutum haram ne ga dukkannin musulmi domin yi da mutum lallai tana cin kyawawan aiyuka, kamar yanda wuta take cin kirare, An karbo da Manzon Allah (S.A.W.A.) ba wani wuri da za ake yi da mutane, face sai wurin ya rasa addini, ku toshe kunnuwanku daga jin yi da mutane domin mai fadin da mai jin suna tarayya cikin zunubi]. An karbo daga Imam Bakir (A.S) [wanda a ka yi da wani a gurinsa bai kare shi ba, bai kuma taimake shi ba, kana bai hana ayi, da shi ba, bayan kuma yana da ikon da zai taimaka masa Allah zai wulakanta shi duniya da lahira]. Na sha hudu:- son dukiya da kwadayin duniya Allah madaukaki yana fade cikin Al'Qur'ani [ya ku wadanda kuka yi imani kar dukiyoyinku da ''ya''yayenku su kau da ku ga zikirin Allah, duk wanda ya aikata haka, wadannan su ne asararru]. Ubangiji ya fada a wata aya daban [ku sani dukiyoyinku da ''ya''yanku fitina ne” An karbo daga Manzon Allah (S.A.W.A.)[wanda ya wayi gari duniya tana mafi girman bukatarsa, to a wajen Ubangiji shi ba'a bakin komai yake ba]. An kuma karbo daga gare shi [Wata Duniya za ta zo muku bayana tana mai cin imaninku kamar yanda wuta take cin kirare]. An karbo daga gare shi (S.A.W.A.) [ku bar duniya ga yan duniya duk wanda ya dauki wani abu daga gidan duniya sama da yanda zai ishe shi hakika ya dauki makashinsa bai sani ba]. An karbo kuma daga gare shi [Hakika Dinare da azurfa su suka halaka wa''yan da suke kafinku, kana kuma su masu halakar da ku ne”, ma aiki ya ce wanda ya so duniyarsa ya cutar da lahirarsa]. An ruwaito daga Imam sajjad [hakika na ga alheri gaba dayansa ya tattara ne cikin yanke tsammani daga abin da ke hannun mutane]. An karbo daga Imamu Bakir (A.S) [Tir da bawa bawan da tsammaninsa yake jansa tir da bawa, bawan da kwadayinsa yake wulakantar da shi]. An ruwaito daga Imam sadik (A.S) [son duniya shi ne shugaban dukkannin wani kure]. Na sha biyar:- Alfasha da kazafi da fitsara da zagi: An karbo daga Manzon Allah ya ce da Aisha [ya Aisha idan alfasha ta zama a misali ne to wannan misali ya yi muni.” An ruwaito daga gare shi [Allah yana kin mai alfasha fitsararre da maroki mai yawan naci]. An karbo kuma dai daga gare shi [yana daga cikin mafi sharin bayin Allah wanda ake kin zama da shi don alfasharsa”. An ruwaito yana cewa:- [zagin mumini fasikanci ne, yakarsa kafirci ne cin namansa sabo ne, haramcin dukiyarsa daidai yake da haramcin jininsa]. An ruwaito daga Amru ibn nu'uman AlJu'ufi ya ce :- Imam Ja'afarus Sadik (A.S) yana da wani aboki wanda ba ya rabuwa da shi, wata ran sai abokin ya ce da yaronsa, ya dan matar banza, sai Ja'afarus sadik ya daga hannun sa ya bugi goshinsa, kana sai ya ce:- subahanallah, yaya kake yi wa mahaifiyarsa kazafi, bayan ko ina ganinka mai hankali, lallai ka tabbata mara tsantseni, sai ya ce: in zama fansarka: babarsa mutuniyar [sindu] ce kuma mushrika ce sai Imam (A.S) ya ce:- Ashe ba ka san ko wacce Al'umma tana da irin nata auren ba, tafi ka ba ni wuri, Amru sai ya ce:- ban kara ganin su suna tafiya tare ba har mutuwa ta raba su]. Na sha shida:- saba wa iyaye Ubangiji madaukakin sarki ya ce:- [ubangijinka ya hukumta kada ku bauta wa kowa sai shi, kana ku kyautata wa iyaye]. An ruwaito daga manzo (S.A.W.A) [Ahir dinku da saba wa iyaye]. An karbo daga gare shi ( S.A.W.A.) [wanda ya wayi gari mahaifansa suna fushi da shi ya wayi gari yana da kofofi guda biyu budaddu zuwa wuta]. An karbo daga Imam Bakir (A.S) [mahaifina ya kalli wani mutum yana tafiya tare da dansa, dan ya jingina a jikin hannun mahaifinsa, daga nan mahaifina bai kuma yi masa magana ba, har ya rasu domin yana fushi da shi]. An karbo daga Imam sadik (A.S) [Duk wanda ya kalli iyayensa da duba na fushi, domin sun zalunce shi Allah ba zai karbi sallarsa ba]. Ya kuma ce:- [da akwai wata kalma kasa da uffi da Allah ya hana a fada wa iyaye ita, wannan kuma shi ne mafi kankantar saba wa iyaye, yana daga saba wa iyaye mutum ya kafa wa iyayensa ido]. Na sha bakwai :- yin karya Allah madaukaki yana fadi [kadai dai wayanda suke kirkirar karya su ne wa''dan da ba su yi imani ba].Allah yana kuma cewa: Sai ya biyar da su munafunci a zukatansu zuwa ranar saduwansu da shi saboda saba abin da suka yi alkawari ga Allah kuma saboda sun kasance suna karya.” An ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W.A) [ya isa girman hainci, ka yi magana da dan uwanka, shi yana mai gasgata ka kai kuma kana mai yi masa karya]. An karbo daga gare shi [karya tana rage arziki]. An karbo daga Imamu Ali (A.S) [dan adam ba zai samu dandanon imani ba har sai ya daina karya bisa wasa, ko da gaske]. An karbo daga Imam Sajjad (A.S): ku ji tsoron karya babbarta da karamarta, cikin wasa ko kuma da gaske, don mutum idan yai karya karama sai ya sami karfin yin babba]. An karbo daga Imamu Askari [An sanya dukkannin munanan abubuwa cikin daki, sai aka sanya karya ita ce mabudi]. Na goma sha takwas:- saba alkawari, Allah madaukaki yana cewa [sai ya biyar da munafinci a cikin zuciyarsu har zuwa ranar da za su gamu da shi, na daga abin da suka saba ma Allah na alka wari wanda suka yi]. An karbo daga manzo (S.A.W.A) ya ce:- wanda ya yi imani da Allah da ranar tashin Alkiyama to ya cika Alkawari duk lokacin da ya dauka]. An karbo daga gare shi [Abubuwa guda hudu wanda suka kasance a tare da shi ya kasance munafiki ne, wanda kuma daya ta kasance a gare shi yana da sifa daya ta munafunci har sai ya bar ta, in yai zance yai karya, idan yai Alkawari ya saba, in yai yarjejeniya ya yi yaudara, in an yi fada da shi yai fajirci]. Na sha tara:- zama cikin zunubi da maimaita aikata shi, da kin barinsa, da rashin yin nadama a bisa aikata shi:, Ubangiji madaukakin sarki ya ce:- [da wa''yan da idan suka aikata alfasha ko suka zalunci kansu sai su tuna Ubangiji su yi istigifari domin zunubinsu, kuma wane ne mai gafarta zunubai banda Ubangiji, kuma ba su ci gaba da zama cikin abin da suka aikata ba bayan ko suna sani, sakamakon wadannan gafara ce daga Ubangijinsu, da kuma Aljanna wacce koramai suke gudu a karkashinta, suna masu dauwama a ciki madalla da ladan masu aiki]. An karbo daga manzon Allah (S.A.W.A) yana daga cikin alamar rashin arzikin lahira ci gaba da zama cikin zunubi, An karbo daga imamu Ali (A.S) mafi girman zunubai, zunubin da ma abucinsa ya ki daina aikata shi, An karbo daga Imam sadik (A.S) [sam sam wallahi Ubangiji ba ya karbar wani abu daga biyayyar wanda yake ci gaba da aikata wani abu na sabo]. Na ishirin:- boye abinci da nufin yai tsada, An karbo daga Manzo Allah (S.A.W.A) [Dukkannin mutumin da ya sayi wani abinci ya ajiye shi tsayin kwana arba'in, da nufin ya yi tsada wa musulmi, kana sai ya sayar da shi yai sadaka da kudi ba za ta biya abin da ya aikata ba,” An karbo daga gare shi, [wanda ya boye abinci sama da kwana arba'in Allah zai haramta masa kanshin Aljanna, An karbo daga gare shi, wanda ya boye abinci tsayin kwana arba'in da nufin abinci yai tsada hakika ba ruwan Allah da shi, shi ma kuma ba ruwan shi da Allah]. Na ishirin da daya:- Algus an akrbo daga manzon Allah [wanda yai Al gus ga wani musulmi cikin saye, ko sayarwa, ba dan cikinmu ba ne], ya kuma ce[fadaki ka ji wanda yai mana algus ba ya daga cikinmu] ya fade ta har sau uku:- yana cewa [wanda yai wa dan uwansa musulmi algus, Allah zai debe albarkar arzikinsa, ya kuma ba ta rayuwarsa, kuma ya zamar da dogaronsa ba ga Allah ba.] An karbo daga Imam Bakir (A.S) ya ce:- [manzon Allah ya wuce wani abinci a cikin kasuwar madina, sai ya ce da mai abincin ban ga wani aibi a wannan abincin naka ba sai ya tambaye shi farashinsa sai Allah yai masa wahayi ya tura hannunsa cikin abincin sai ya cusa, sai ya fito da abinci mara kyau sai ya ce da mai abincin ba na ganinka sai a matsayin mutumin da ya hada hainci da algus ga musulmi]. Na ishirin da biyu:- barna da rashin tattali da almubazzaranci, ko da ko bai kai ya kawo ba, Allah madaukaki yana fade cikin Al'Qur'ani mai girma [ku ci ku sha kada ku yi barna, don Allah ba ya son mabarnata] A wani wurin yana cewa[lallai mabarnata su ne yan wuta] A wani wurin yana cewa [Masu almubazaranci sun kasance yan uwan shaidan, shi kuma shaidan ya kasance mai tsananin kafurce wa ubangijinsa ne]. An karbo daga Imam Ali (A.S) [idan ubangiji ya so Alheri ga bawa sai ya kimsa masa tattali da kyakkyawar tsari a rayuwa ya nesantar da shi, mummunar tsari a rayuwa, da barna]. An karbo daga Ja'afurus sadik (A.S) ya ce:- [Ashe kana ganin ubangiji ya yi kyauta ga wanda yai wa kyauta don ya girmama shi ne, ya kuma hana wanda ya hana don ya wulakanta shi ne? Sai dai dai dukiya ta ubangiji ce yana sanya ta ajiya ce ga mutumin da ya so, kana ya halatta musu, su ci cikin tattali su sha cikin tattali su aura cikin tattali su sayi abin hawa cikin tattali, abin da ya rage su ba wa talakawan muminai, don su kawar musu da barakarsu, duk wanda ya aikata haka ya kasance yana cin halas, yana hawan halas, yana auren halas, wanin wannan kuma haramun ne, kana sai ya ce:- [kada ku yi barna ubangiji ba ya son mabarnata]. An karbo daga gare shi [Tattali abu ne wanda Allah yake so barna kuma abu ne wanda Allah yake ki, ko da kuwa ta kwallon wani abu ne, domin za'a iya yin wani amfani da shi, ko da kuwa zub da ragowar ruwan da aka sha]. Na ishirin da uku:- barin daya daga cikin wajibai, kamar barin sallah, ko azumi, ko makamantansu na daga wajibai, manzon Allah ya ce:- [wanda ya bar sallah da gan gan hakika ya warware igiyar alkawarin Ubangiji a tare da shi, da igiyar alkawarin Manzonsa]. An karbo daga Imam sadik A.S. cewa: “kuma Allah madaukaki ba zai kalli bawansa ba, ba kuma zai tsarkake shi ba, idan bawa ya bar wani farali daga cikin farillai, ko kuma ya aikata wani zunubi daga manyan zunubai.” An kuma karbo daga gare shi cewa: “Allah Ta ‘ala ya umarce shi da ya aikata abu, lbilis shi ma ya umarce shi da aikata wani abin, sai ya bar abin da Allah madaukaki ya umarce shi da shi kana ya aikata abin da Iblis ya umarce shi da aikatawa to irin wannan da shi da lbilis suna tare a kasa gidan wuta ta bakwai.” Akwai kuma wasu amma ba zan iya ambaton dukkansu a nan ba, sai dai ka duba su a littafan hadisai da littafan fikihu in ka zabi haka. · Mahaifina ya fadi haka ke nan sai ya kara da cewa amma a wannan hali ya fito fili sosai sannan muryarsa ta canja ta zama ta karfafa zancen sosai ta sa shi ya yi tasiri sai ya ce: Zan cika wannan zance tamu a kan wannan lamari da wata magana wanda daya daga cikin manyan mujtahidai ya fade ta, ga abin da ya ce: “Hakika yana daga cikin mafi girman umarni da kyakkyawa da hani da mummuna kuma wanda ya fi daukaka ya kuma fi muhimmanci, musamman ma ga shugabannin addini, ya zamanto sun sanya rigar yin umarni da kyakkyawa sawa’un wajibi ko mustahabbi, kuma su cire rigar mummunan aiki sawa’un haram ne ko makaruhi, su kammala ransu da dabi’u na gari, su kuma nesaci dabi’u miyagu, domin kuwa wannan zai zama cikakken dalili da zai sa mutane su aikata kyakkyawan aiki su kuma bar mummunan aiki hasali ma idan aka hada hakan da yin wa azi mai kyau wanda zai kwadaitar da mutane ga aiki na kwarai ya kuma tsoratar da su daga mummunan aiki, domin kuwa kowane guri yana da irin zancen da ya dace da shi, kuma kowace cuta tana da maganinta, sai a sami biyan bukata. Ai da ma warkar da cutar da ta shafi ran mutum ta fi tsanani a kan wadda ta shafi gangan jikin mutum, to idan suka aikata wannan za su zama sun aikata mafi girman umarni da kyakkya wa da kuma hani da mummuna.” To da wannan tattaunawa za mu kawo karshen dukan muhawarori sai dai gobe za mu sake zama domin mu amsa tambayoyi, duk wanda ka zaba, domin watakil na ba ka takaitattun amsoshi a abin da ya gabata ko kuma akwai abin da ban tabo ba. Ina kuma fatan wannan tattaunawa ya amfane ka da sauran yan uwanka muminai, ina kuma fatan ya zama da tsarkin niyya muka aiwatar da shi. |
||