SHIMFIDA

 

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

Ga ni nan yau na cika shekara goma sha biyar na shekaruna, lokacin da na farka daga barci da safe ban san cewa wannan ranan za ta zo min da abubuwan mamaki,da   ba zata,da tsammani, alfahari da kuma faduwan gaba ba. Kana ga ta cike da jin dadi, kauna da soyayya da kuma jin dadin wannan sabon abu, rana ce da za ta daga ni daga wata marhala kana ta sanya ni a wata marhala ta daban.

A wannan rana na farka da sassafe kamar yadda na saba kowace rana, amma ban gama ayyukana na wajibi da na saba yi kowace rana.

- wato wadancan da suke bambance tsakanin farkawa ta da kuma zama na a gaban teburin cin abincin karyawa- sai na lura da cewa fuskar babana ta canza ba kamar yadda take kowace rana ba, wannan yanayi ya sanya ni tunanin cewa akwai wani abu da ya faru kana yake damunsa.

Idanuwansa a bubbude sama da yadda da suke, kamar suna dubin wani abu a sarari, lebukan (bakinsa) suna rufe kana suna motsi kamar suna kunshe da wata magana mai muhimmanci suna so su fitar da ita amma sun matse ta, hakan sai yake nuna min cewa lalle akwai wani abu mai muhimmanci a cikin zuciyarsa, kamar saura kadan ya fashe saboda cikansa.

Koda na zauna a gabansa ta bangare na biyu na teburin abinci sai ya fuskance ni fuskarsa cike da farin ciki yana mai cewa:

- Ya dana yau din nan ka yi bankwana da wata marhala daga rayuwarka, kana ka tarbi wata sabuwar marhala…Yau din nan ka wayi gari a idon shariar musulunci a matsayin cikakken mutum da yake da wasu abubuwan da wajibi ne ya kula da su …A wannan rana Allah ya niimta ka ya kuma ba ka wasu ayyuka (da dole ka kula da su), na daga umurni da hani.

Kana babana ya ci gaba da cewa:-

- Har zuwa jiya shari’ar musulunci tana ganinka ne a matsayin yaro ba ka kai matsayin mutum ba don haka shari’a ta bar ka da al’amurranka…Amma yau din nan komai ya canza…a yau din nan ka zama mutum kamar sauran mutane, ka zama cikakken mutum da ya cancanci wasu abubuwa, lokacin da aka kai ka wannan marhala kana aka isar da kai gare ta, sai Allah ya niimta ka da umurninsa da haninsa.

        ·          Yi hakuri, ban gane nufinka ba yaya za’a yi umurnin Allah ya zamanto ni’ima gare ni? Shin umurni yakan zama ni’ima? Yaya hakan zai yiyu?

- Bari in maka karin bayanin al’amari da wannan misali har ka gane yadda umurni zai zama maka ni’ima…a halin yanzu kai dalibi ne, kana nan tare da sauran ‘yan ‘uwanka dalibai, a cikinku akwai haziki, akwai mai kula da al’amurransa, akwai mai kokari, akwai mai damuwa da karatunsa kana kuma a cikinku akwai waninsu, to idan kuka tsaya don fuskantar wani aiki da ke gabanku, kana sai ga shugaban makarantarku ya zo zai wuce, koda kuka yi ido biyu da shi cikin murmushi sai ya yi maka albishir da ci gabanka zuwa wata marhala ya gaya maka cancantarka ga wannan sabuwar marhala, yana mai nusar da kai, yana mai bambance tsakanin ka da sauran ‘yan ‘uwanka da wani umurni da zai kai ka ga cimma wani buri naka.

Shin a wannan lokaci ba za ka ji wani irin nau’I na farin ciki ba saboda wannan umurni kana da kuma kauna ga abin da ya umurce ka da shi, da shiri, don abin da zai zo, da kuma nitsuwa saboda nusar da kai da ya yi ban da sauran ‘yan ‘uwanka sannan kana mai kokarin ganin cewa ka aikata abin da ya umurce ka da shi….

To wannan fa umurnin shugaban makarantarku ne, to yaya za ka ji idan da a ce wanda ya yi maka wannan umurnin shi ne shugaban makaranti gaba daya?! Kai ! shin yaya yanayinka zai kasance da mai umurnin shi ne shugaba na koli gaba daya?!

Shin yaya yanayinka zai kasance da a ce mai umurnin shi ne…

Daga nan sai babana ya ci gaba da bayani kan umurnin da ake yi daya bayan daya, kana a duk lokacin da ya yi sai ya dada fito min fili ba kamar yadda da yake cikin duhu ba.

        ·          Babana bai isa ga wannan umurni na Allah madaukakin sarki gare ni ba,da kuma ayyukansa a kaina ba face sai da na suma.

        ·             Allah yana magana da ni… yana umurta na… ni kaina.

- Na’am ya dana…Allah yana magana da kai ne…kai dan shekara goma sha biyar… ya wajabta maka wasu ayyuka… kai dan shekara goma sha biyar… yana umurtanka… yana hana ka.

        ·          Shin na cancanci dukkan irin wannan girmamawa… ubangijin dukkan halittu ya dinga lura da al’amurrana har ya sanya min abubuwan da zan dinga yi, mai kula da al’amurra a sammai da kassai ya tausaya min har ya umurce ni kana ya hane ni kan wasu abubuwa …Me ya fi wannan rana tawa ta yau dadi kana me ya fi shekara ta wannan  kyau…me ya fi muhimmanci kan kasantuwa na mutum baligi.

- Ya dana ina maka wasiyya da yin biyayya ga abubuwan da Allah ya umurce ka da su kana ya daukake ka da su.

        ·          Na’am zan yi kokari cikin so da kauna wajen aikata abin da ya dora min da kuma hukumce-hukumcensa abin kauna, sai dai…

A : Sai dai me…?

T: Sai dai mene ne wadannan abubuwa da ya dora min in aikata? Mene ne hukumce-hukumcensa da ya wajabta su gare ni?

A : Hukumce-hukumcen Sharia sun kasu kashi biyar…wajibai, haramtattu, mustahabbai, makaruhai da halattattu.

T : To wadan ne ne wajibai? Kana wadan ne ne haramtattu? Sannan wadanne ne mustahabbai? Kuma wadan ne ne makaruhai? Kana wadan ne ne halattattu?

- Duk wani abin da dole ne gareka ka aikata shi to yana daga cikin wajibai kamar salla, azumi, hajji, zakka, khumsi, umurni da kyakkyawa, hani da mummuna da dai sauransu masu yawa.

 Kana duk wani abin da dole ne a ,gareka ka bar aikata shi to yana daga cikin haramtattu kamar shan giya, zina, sata, almubazzaranci, karya da dai sauransu masu yawa.

Sa`nnan duk wani abin da aikata shi yana da kyau  amma ba tare da an wajabta ma mutum aikata shi ba idan har da nufin kusanci da Allah ne to yana daga cikin mustahabbai, kuma za a ba da lada a kai idan ka aikata kamar sadaka ga fakirai, tsabta, kyakkyawan dabi’u, biya wa mumini bukatarsa, sallar jam’I, shafa turare da dai sauransu masu yawa.

Sannan duk wani abin da kin aikata shi da kuma nesantarsa abu ne mai kyau amma ba tare da an wajabta wa mutum barin nasa ba kana kuma ya bar shi ne don neman kusanci ga Allah to yana daga cikin makaruhai za a ba da lada a kai idan ba ka aikata ba kamar jinkirta yin aure ga namiji ko mace, tsadar sadaki, kin ba da ba shi ga muminin da ya bukaci haka tare da halin yin hakan da dai sauransu masu yawa.

Amma abubuwan da aka bar maka zabi kansu imma ka aikata ko ka bari to suna daga cikin halattattu kamar ci da sha, barci, zama, tafiye-tafiye, shakatawa da dai sauransu masu yawa.

T: To yaya zan iya bambance wajibai daga mustahabbai, kana haramtattu daga makaruhai. Yaya zan iya sanin cewa wannan (aiki) wajibi ne don in aikata shi, kana wannan haramun ne don in nesance shi. Yaya zan iya sanin cewa wannan…

 Sai babana ya katse ni yana mai murmushi, kana sai ya dube ni dubi na rahama da kauna yana so ya fadi wata magana amma da wani abu ya bijiro masa sai ya  sa shi yin shiru, kana daga nan sai ya nutse cikin tunani mai zurfi.

Ban iya gano me ke gudana ba a cikin zuciyar mahaifina, tattare da cewa na kasance mai lura da irin abin da ke gudana a goshinsa kamar wani bakin hadari wanda yake gudana har ya rufe sauran bangarorin fuskarsa har zuwa lebbansa da ke fitar da karamar sauti mai tausasa abubuwa.

A: Za ka iya banbance tsakanin wajibai daga haramtattu kana mustahabbai daga makaruhai ne idan ka karanta littafan ilmin fikhun musulunci. Za ka ga cewa wadan sunsu suna da wasu rukunoni, juzuoi da sharudda, kana wasunsu kuwa suna da wasu halaye na musamman da wajibi ne ka aikata su, wasu kuwa suna da wasu abubuwa da ba zai yiwu ka tsere musu ba sannan wasu suna da…wasu suna da…

Ka koma ga littafan fikhun musulunci za ka sami  abin da kake nema a cikinsu…kana daga baya za ka gano cewa shi din nan ilmi ne mai fadi da daukaka, an rubuta darurrukan littafai kan wannan ilmi, malamai har sun fadada bincike sosai kan mas’alolin da ke cikinsu, kana ba shi da na biyu wajen fadi da zurfi cikin sauran ilimomin dan’adam.

T: To shin kafin in san abubuwan da ya wajaba a kaina in aikata, wajibi ne sai na karance dukkan wadannan littafa?

A: A’a ya ishe ka ka duba wadanda suka fi fahimta da kuma saukin samu daga cikinsu, da sannu za ka ga cewa an kasa su kashi biyu:

Bangaren lbadat da kuma bangaren mu’amalat.

T: Wadan ne ne lbadat? Kana wadan ne ne muamalat?

A : Saurara kadan, ldan ka duba littafan fikhun musulunci, da sannu za ka gano abubuwan da kake hanyar gano su a halin yanzu.

* * * * *

Bari in koma ga dakin karatu (library), ko watakila zan iya samun wadannan littattafan fikhun musuluncin da a ke magana a kai…don magance bukatata. ina sanya idona akan wadannan littattafa sai farin ciki mai tsanani ya kama ni ko kuma in ce haka nake tsammani.

        ·          Hakika daga karshe na samu isa ga wadannan littattafa na fikhun musulunci…da sannu zan karanta su, kana zan samu cikakken amsoshin tambayoyina a cikinsu…da sannu-sannu zan sami kwanciyar hankali.

Nan da nan sai na dawo dakina ina mai alfahari da abin da na samo, cikin sauri sai na bude kofa kana da sauri na shige cikin dakin sannan na bude littafina cikin gaggawa. Ban fara karanta littattafan ba face sai da fara ganin wasu sabin kalmomi, sai na samu kaina cikin mamaki.

Hakika na samu kaina ina mai karatu da yawa amma bana fahimtar wani abin a zo a gani.

Ya‘yan ‘uwana yaya zan yi ne wajen magance wannan matsala tawa, kuma wannan matsala tawa tana daga cikin nau’o,in da ba a saba da su ba.

Sai na ci gaba da karatuna ina mai cewa:

Hakika zan ci gaba da karantawa da kuma kokari wajen fahimta watakila daga karshe zan amfana.

A sannu-sannu lokaci yana wucewa, ga shi zuciyata tana faduwa karkashin wani abu mai nauyi, bai gushe ba yana damu na yana kuntata min, kana a hannayena kuwa ga littafin da nake karantawa,ina karantawa kana kuma ina dada maimaita abin da na karanta amma bana fahimtar komai.

Daga nan sai na fara jin kasala ta fara mamaye ni a hankali a hankali, kana farin cikin da ke tare da ni sai na ji a hankali a hankali ya fara komawa wani abin da yake kama da wani duhu na bakin ciki mai tsanani da ya bayyana a idona.

Hakika `na yi karatu mai yawa, amma ban fahimci wani abin a zo a gani ba daga abin da na karanta.

Hakika na fuskanci wasu kalmomi da kunnena bai taba jinsu ba…ban san mene ne ma’anonin kalmomin (an-Nisab, al-Hawl, albayyina, masafal mulaffaka, ma’una al-Dirhamul Bagli da kuma al-Zimmi) ba.

Kana haka ma na fuskanci wasu abubuwa da adabi da watakila wasu istilahohi ne da suka kebanta da wannan ilmin da ban taba karanta su ba, ban san me ake nufi da ((al-llmul ijmali, as-Shubhatul Mahsura, al-Hukumul Taklifi, al-Hukumul Wad’I, al-Shubhatul Maudu’iyya, al-Ahwat luzuman, at- tajazzi fil ljtihad da sidk’ul-urfi, al-Manad da kuma al-Mashakkatun Nau’iyya).

Kana bayan haka kuma na karanta wasu jumloli da suke da wani irin tsari na musamman, da ban saba da su ba kana da wasu jumloli kuma da suka magance wasu matsaloli da basu taba faruwa ba a rayuwarta ta yau, koda yake ban san dalilin da ya sa aka ambace su ba, kana wasu jumloli masu rudarwa kwarai da gaske da za su iya daukar ma’anoni kala-kala, da kuma jumloli da a ka rarrabe su aka kuma zurfafa a cikinsu hakika (wadannan jumloli) sun bar ni cikin tunani a kansu.

Misali, na gagara fahimtar maanar wannan jumla ((Idan mutum yana da masaniya kan isar (abin zakka) nisabi da ratayar zakka amma bai san wanne ne ya rigayi daya daga cikinsu ba to zakka ba ta wajaba ba, shin yana da masaniya kan lokacin ratayar amma ya jahilci lokacin isar (wato kaiwa nisabin zakka) ko kuma yana da masaniyya ne kan lokacin da abin ya kai na nisabi amma ya jahilci lokacin ratayar, ko kuma ma ya jahilci duka biyu, haka ma hukunci yake ga mahaukacin da haukan nasa ya rigayi hankali, amma idan hankalin nasa ya rigayi haukan, to idan ya san lokacin ratayar to zakka ta wajaba sabanin sauran halayen)).

Haka ma wannan jumlar: (Zato kan yin raka’oi kamar yakini ne, amma kasantuwan zato cikin ayyuka ya zamo haka akwai “lshkal” matsala, amma “al-Ahwat” idan zato cikin yin ayyukan a muhallinsa ne to sai ya ci gaba kana daga baya ya rama sallar, kana idan zaton kan rashin aikata aikin bayan ya riga da ya wuce muhallinsa ne to ya koma ya aikata shi sannan kuma ya sake sallar).

Haka ma jumlar: “Al-Akwa” shi ne cewa taimama tana dauke “hadasi” tauyayyan daukewa baya wadatarwa idan har mutum yana da zabi, amma niyyar daukewa ko niyyar halarci ga salla, misali). ba ta wajaba.

Kana na gagara gane maksudin cewa (Idan mutum ya yi alwala a halin kuncin  lokaci to idan ya yi nufin sallar da lokacinta ya kuntata to ta baci, amma idan nufinsa shi ne wani abu na daban-koda kuwa kasancewa cikin tsarki ne-to alwalarsa ta inganta).

Haka ma jumlar da ke cewa: (Idan mutum ya yi “hadasi” da “karamin hadasi” yayin wanka sai ya cika shi kana ya yi alwala (ta daban), amma kada ya bar “lhtiyat” wajen sakewa da niyyar abin da yake kansa na daga cikawa ko da nufin cikitawa kana ya yi alwala).

Ko kuma jumlar da ke cewa matsawar matafiyi yana nan akan niyyarsa dangane da tafiya to ta wadatar koda ya canza tafiyarsa ta farko.

Haka nan ma wannan jumla: (Mizanin bayyanawa da boyewa shi ne wanda  mutane za su ambace shi da cewa bayyanawa ne ko boyewa).

Da dai sauransu da dama da idanuwana suka fada a kai, amma ban san ma’anoninsu ba.

Daga nan duniya ta min zafi…kana ta sake yi min zafi a karo na biyu.

Ya ‘yan ‘uwa na: Yaya zan san abubuwan da Allah ya halatta don in aikata kana abubuwan da ya haramta don in nesanta?

Daga nan sai na daga kaina zuwa sama, kana idanuwana sun yi ja jawur saboda share hawaye mai tsanani,.

Ya ubangijina! Na san Ka dora min (wannan wajibi) amma ban san takamaiman abin da ka dora min ba…

Ya ubangijina! Ta yaya zan san abubuwan da kake bukata daga wajena, domin na cika abin da kake bukata daga wajena…

Ya Allah ka taimake ni kan fahimtar abin da nake karantawa.

Ya Allah ka taimaki littafan fikhu wajen fayyace abin da maganganunka suke nufi, don in gano abin da maganarka take bukata.

* * * * *

Daga nan sai na jira babana akan teburin cin abincin dare….

Amma lokacin da daren yayi, da farkon al’amarin sai na fara jin idanuwa na sun gaji, suna cikin damuwa da rudani. Kana ban zauna ba face sai da na ji su suna jujjuyawa suna walkiya kamar azurfa kana ga su sun hadu da damuwa saboda kalubalen da suke fuskanta.

Koda aka shirya mana abinci kana babana ya iso sai na ji zuciyata tana bugawa, kana kumatuna suna motsi, sannan yanayin zafin kunnena ya kara zama kamar wanda zazzabi ya kama shi, kana kuma sai na fara jin damuwa, kunya, fargaba da rudewa alhali ina mai tunanin kalmomi da jumlolin nan da suka gagare ni fahimta.

Daga nan sai na yi kokarin neman taimakon jarumtaka da kokarina domin in nuna gazawata, sai na ce wa babana:

        ·          Hakika na karanta wasu littattafan fikhu amma sun yi min wahalar (ganewa), na gaza fahimtarsu…Na yi matukar kokari don boye harafin karshe na kalmata ta karshe don in tsira daga idanuwan babana, wadanda-watakila-suka nitse cikin tunani mai tsanani, kana bayan dan lokaci kadan suka dawo cikin hayacinsu kamar wanda ya dawo daga wata tafiya mai tsawo, sannan suka kewaya tsakanin idanuwa na kamar suna so su fadi wani abu,      

koda yake lebbansa sun budu don fitar sauti mai taushi hade da bakin ciki mai tsanani:

hakika ni ma na taba fuskantar matsala irin taka, lokacin da nake matsayin shekarunka.

Hakika na karanta littattafan fikhu amma na gagara fahimtar wani abin a zo a gani a cikinsu…koda yake ni ban mallaki irin wannan jarumtaka taka na in bayyana gazawata wajen fahimtarsu ba.

Hakika tarbiyyata da jurewa kan kunyata mai tsanani ta shiga tsakanina da tambayar babana kan wadansu yanayi na musamman kan marhalan samartaka da balaga, na kasance ban san cewa balaga tana tabbata da wasu takamaiman shekaru ba har zuwa…sai na katse babana:

T: Shin balaga tana tabbatuwa da wanin haka? ne?

A: Na’am ya dana, balaga tana tabbata ga namiji idan har yana da daya daga cikin wadannan alamomi guda uku:

Na farkonsu: Ya kasance ya cika shekaru goma sha biyar na rayuwarsa.

Na Biyunsu: fitar maniyyi daga gare shi ta hanyar yin jima’i ko kuma mafarki ko kuma waninsu.

Na ukunsu: fitar kakkausan gashi a mararsa, na kira shi kakkausa ne mai kama da gashin kai don in banbanta shi da tattausan gashi da -sau da yawa-yake rufe wasu bangarori na jikin mutum misali kamar hannu.

T: Mene ne mara?

A: Mara ita ce wani wuri da yake karkashin ciki sama da wurin da tsiraici ya hadu da ciki.

T: Wadannan alamomin balagan maza ne, to na mata fa?

A: Balaga a wajen mace tana tabbata ne lokacin da ta kai shekaru tara na rayuwarta (wato shekarun hijiriyya).

        ·          To tun da yau na bayyana maka gazawata wajen fahintar littattafan fikihu, to ka ba ni dama mana in gaya maka abin da nake ganin ya kamata ayi-  Saboda bukatuwan da nake da shi-shi ne ka shirya min wasu darussa da a cikinsa za ka dinga yi min bayani kan abubuwan da fahimtarsu ya yi min wahala, wadanda kuma fahimtarsu da gane su ya zama min wajibi, don aikata abin da suka hau kaina na hukumce-hukumcen shari’a kamar yadda Allah madaukakin sarki ya tsara su kana ya umurce ni da aikata su.

        ·          Ina ma da wadannan darussa namu za’a tsara su ta hanyar tattaunawa da kuma tambayoyi.

- Kamar yadda kake so (za’a yi su)

T: To amma da me za mu fara tattaunawar tamu?

A: Za mu fara ta da “al-Taklid” domin shi ne asasin da zai iyakance mana hanyoyi da yanayin da za mu aikata fikihunmu.

        ·          Mun daidaita kan haka.

* * * * *

عنوان الکتاب