MUHAWARA KAN [WA KAFI] |
||
|
· Na ce da mahaifina bayan mun zauna ina mai fara magana a wannan ranar muhawarar, abin da na ce da shi shi ne:- ina ziyartar kabarurukar lmamai masu tsarki a garin NaJaf da Karbala da makamantansu, wani lokaci ina ganin an rubuta kalmar [wakafi] a jikin wasu al'kur'ani a cikin wannan kabarurruka masu tsarki ko kuma an rubuta a jikin abubuwan sa sanyi da fitilu na zamani da kuma sauran fitilu da makamantansu. Kamar yadda wasu lokuta ina ganin wannan kalmar ta [wakafi] a jikin wasu wurare, ko ginunnuka, ko fankoki ko fitilu na masallatai, ko wuraren karatu, ko Husainiya da yawa na kan ga wannan kalmar a rubuce a kan wasu ababan sanyaya ruwa gefen titinan Jama'a. Mahaifina sai ya ce:- yana kyautuwa ga mutum ya bar wasu abubuwa don amfanin musulmi saboda Allah, da sunan wakafi kamar wanda ka ambata da makamantansu bisa wasu kaidoji na musamman, idan wakafi ya cika sharadansa kamar yadda shara'a ta ajiye, to abin da akai wakafi da shi ya fita daga mulkin wanda ya yi wakafin, a wannan lokacin wakafin ya zama dukiyar da, ba'a kyautar da ita kana ba'a gadonta ba kuma a sayar da ita, sai bisa wasu kebantattun halaye wayanda littattafan fikihu suka yi bayani a kai. Mahaifina bayan ya fadi haka sai ya kara da cewa:- wani lokaci wakafi yana kasancewa karkashin wanda aka yi wakafi domin su kamar a ce mutum ya ba wa ‘ya ‘yansa wakafin wani abu ko makwabtansa , ko kuma abokansa, wani lokacin kuma wakafi yana kasancewa ba karkashin wanda aka yi wakafin dominsu ba, kamar mutum ya ba da wakafin wani abu da ya mallaka don ya zama masallaci. Wanda ya ba da wakafi wani lokaci kuma ya kan sanya wani mutum domin ya dinga kula da abin da ya ba da wakafinsa, sannan mutumin da aka sanya zai aiki daidai da yadda mai wakafin ya shardanta masa, wannan mutumin ana yi masa suna da mai kula da wakafi. T: Shin wakafi yana da wata siga wacce aka kebance masa? A: Bai da wata siga kana bai da wani yare wanda aka kebance masa don haka da wani mutum zai yi gini bisa shakalin masallaci da nufin ya zamo masallaci ya isa ya kasance masallaci. Sai babana ya ce:- zan gaya maka wasu daga cikin abubuwan da ake lura da su a cikin wakafi. (1) Dauwamar da amfani da shi don haka wakafi ba ya inganta in aka iyakance masa lokaci. T: Ba ni misali kan abin da ka fada. A: Misali shi ne:- idan mutum ya sanya gidansa wakafi ga talakawa tsayin shekara guda wannan wakafin bai inganta ba domin ba madauwami ba ne. (2) Kar abin da aka yi wakafinsa ya kasance mai wakafin ya bayar da abin ne ga shi kansa, koda kuwa ya sanya wakafin wa kansa ne amma tare da wasu mutane.. T: Ina misali? T: Misali:- shi ne idan mutum ya sanya wani fili ya zamo Wakafi a kan kansa don a binne shi a cikinsa bayan ya rasu to wannan wakafin bai inganta ba. T: To yaya idan mutum ya ba da gidansa wakafi ga wasu kebantattun mutane kamar ''ya ''yansa da makusantansa? A: Wannan wakafin ya inganta bayan sun karba domin wakafi na musamman kebantacce ba ya inganta in wanda aka ba wa wakafin bai karba ba ko waliyyinsa ko wakilinsa. T: Da yaya karbar gidan nasu ya ke tabbata? A: Yana tabbata lokacin da ya zamo karkashin wanda aka ba wakafinsa ko waliyyinsa ko wakilinsa. T: Wani lokaci dukiyar da ake so a bayar wakafi tana kasancewa a hannun wanda za a ba wa wakafin ne to a wannan hali yaya za a yi? A: Hakan ya isa ba ya bukatuwa ga wata sabuwar karbar daga wajen wanda ya sanya wakafin, wato ba sai ya karba ya sake mayar musu ba. T: Wakafin da aka bar shi na kowa da kowa waye mai karbarsa? A: Ba'a shardanta karba ba cikin ingantuwarsa. T: Ka gaya min cewa ci gaba da amfani da wakafi da dauwamarsa a matsayin wakafi sharadi ne cikinsa, don haka bai cancanta a yi wa wakafi iyaka ba wanda bayansa zai dawo mulkin mai shi. A: I haka ne amma yana da damar da zai bar abinsa a yi amfani da shi zuwa wani lokaci wato habsi in har bai so ya sanya shi wakafi ba, ya bar shi a yi amfani da shi ta wata fuska ta musamman ko hannun wani mutum wanda ya kebance zuwa wani lokaci da ya sanya, ba ya halatta a gare shi ya karbe shi kafin cikar lokacin, sai yai hakuri har zuwa karshen lokacin, bayan karewar lokacin sai abin ya dawo halinsa na farko karkashin mulkinsa, wannan shi ake kira habsi. Bayan babana ya fadi haka sai ya karkada kansa kadan sai ya nunfasa kamar wanda ya tuna abin bakin ciki, lokacin da ya gama maganarsa kan [HABSI] wato sanya dukiya hannun wasu don su yi amfani da ita zuwa wani lokaci, sai na ce da mahaifina domin na yanke tunanin da na ga yake yi ba ni misali a kan haka. - shi ne idan mai motar fasinja misali ya ce:- motata na bar ta matsayin habsi har tsayin shekara ishirin domin daukar alhazai zuwa dakin Allah, idan wannan lokaci da ya fada ya kare to motar ta dawo karkashin mulkinsa kamar yadda take da. T: Da za mu raya cewar wannan mutumin ya mutu kafin cikar lokacin da ya sanya, shin motar tana dawowa zuwa masu gado har ma su gaje ta? A: Idan wanda ya bar dukiyarsa a matsayin habsi ya rasu to tana nan a wannan matsayi har zuwa karshen lokacin da ya ambata, don haka idan lokacin ya kare sai ta komo karkashin magada kuma hakkinsu ne su yi amfani da ita. T: Shin yana kyautuwa mutum ya sanya wata dukiyarsa habsi ga wani mutum wanda ya kebance har zuwa mutuwarsa? A: I yana da damar ya yi haka sai dai bai halarta ya dawo da ita karkashin mulkinsa ba muddun yana raye, yayin da ya mutu kuma sai ta komo zuwa magada. T: Idan mai abu ya ce da wani mutum ga wannan gidan da kai da yayanka ku zauna ya hukumci yake? A: Bai hakatta ya dawo da gidan karkashin mulkinsa ba muddun dai wanda ya sa din yana nan tare da ''ya ''yansa, duk lokacin da suka mutu to sai gidan ya dawo karkashin mulkinsa ko ya dawo hanun magada. T: Idan mai gida ya ce:- ka zauna a gidana tsayin rayuwarka, sai mai gidan ya rasu kafin wanda ya sanya a gidan yaya kenan? A: Bai halatta ga magada su fitar da shi ba har sai ya mutu, idan ya mutu gidan ya komo na magada. T: Shin yana halatta ga miji ya ba da wasiyyar cewa kaso daya cikin kaso ukun lambunsa a ba da shi habsi ga matarsa har zuwa rasuwarta, domin ta rika samun amfani a jiki idan ta rasu ya dawo karkashin masu gadonsa? A: I yin hakan ya halarta. Shin ya halatta a bayar da aron shimfida da ke masallatai domin harkar aure ko taro alhali ita wannan shimfidar wakafi ne? A: In har wakafi ne kebabbe aka bar shi to ba ya halarta a yi wani amfani da shi sai dai ta fuskar wakafin. T: Shin ya halatta a ba da shi haya? A: Bai halarta ba. T: Masallacin da bai da bukatar dukiyar wakafin da aka kebance shi da ita shin yana halatta a sanya ta ga wani masallacin daban, wato kamar a gyara wani masallaci daban da dukiyar?. A: Idan har masallacin a wannan lokacin bai da bukatar wannan dukiyar tasa ko kuma cikin abin da zai zo nan gaba kadan kuma zai yi wahala a'iya ajiye ta zuwa lokacin da zai bukace ta sai ayi amfani da ita cikin abin da aka ga ya kamata na daga abubuwan da suka fi kusaci ga abin da mai wakafin yake nufi tare da duba irin bukatar da masallacin da aka ba wa wakafin yake da ita ko kuma a raya wani masallacin daban. |
||