MUHAWARA KAN GADO |
||
|
A farkon tattaunawarmu kan gado sai Babana ya ce: za mu iya raba darajar makusata zuwa uku dangane da lamarin gado. Daraja ta farko: uwa da uba da ‘ya ‘ya da ‘Ya ‘yan ‘ya ‘ya (jikoki)…da haka… Sai dai kuma idan akwai da na Tsatso to ya kan hana jika ya yi gado. T: Baba mene ne kake nufi da jika? A: Jika shi ne dan da ko dan diya. Daraja ta biyu: ‘yan uwa maza da ‘yan uwa Mata, idan babu su to ‘ya ‘yansu Da kakanni maza da kakanni mata, na gefen uwa Da na gefen uba ko da kuwa ba Kakanni na kurkusa ba ne (komai nisarsu) Idan kuma su ‘yan uwan suna da ‘ya ‘ya Da kuma jikoki, to ‘ya ‘yan dan’uwa sun fi Kusaci, bisa ga jikokin dan uwa. Kuma samuwar ‘ya y’an dan’uwa yana hana jikokin dan’uwa yin gado. T: Ba ni misali kan abin da ka fada. A: Misali shi ne dan dan’ uwa in yana nan To zai hana jikan dan’ uwa yin gado. Daraja ta uku: Baffanni da kawunni da ‘yan uwan Uba mata da ‘yan uwan uwa mata, Idan babu daya daga cikinsu to ‘ya ‘yansu. Sannan wanda ya fi su kusaci shi zai yi gado daga cikinsu-a yayin nan ‘ya ‘yansu ba za su yi gado ba, wato ‘ya ‘yan baffa ko ‘ya ‘yan kawu, ko ‘ya ‘yan ‘yan uwan uba mata ko ‘ya ‘yan ‘yan uwan uwa mata to duk wadannan da muka lisafito ba za su yi gado ba, matsawar baffa ko kawu ko ‘yan uwan uba mata ko ‘yan uwan uwa mata- suna nan, face a wani hali guda daya wanda littafan fikihu suka yi bayani a kai. - Shin mene ne ya sa ka raba makusata zuwa darajoji uku, ba ka raba su zuwa kashi uku kawai ba, ina nufin me ya sa ka ce ana raba makusata zuwa darajoji iri uku amma ba ka ce zuwa kashi uku ba? - Tambayarka mai maana ce, nan a wajen rabon gado wani makusaci daga daraja ta uku ko ta biyu ba zai yi gado ba matsawar akwai makusata daga daraja ta farko. Kana makusata daga daraja ta uku su ma ba za su yi gado ba matsawar akwai makusata daga daraja ta biyu, don hawa hawa ne. T: To idan mamaci ba shi da makusata daga wadannan darajoji da ka lisafta fa? A: A yayin nan baffannin babansa da baffannin mahaifiyarsa da kuma kawunnin uba da uwa, sa annan da ‘yan uwan kakanninsa maza da mata da kuma ‘ya ‘yansu su ne za su gaje shi. T: Idan wadannan su ma babu su fa? A: To a nan baffannin kakanninsa da kawunnin kakaninsa da kuma ‘yan uwan iyayen kakanninsa mata, bayansu kuma sai ‘ya ‘yansu komai nisan su, amma da sharadin cewa suna da dangataka da mamacin, kana kuma wanda ya fi su kusaci da mamacin shi za a kaddamar a kan wanda bai da kusaci da mamacin sosai. T: To maaura biyu fa wato miji da mata su ba ka ambace su a wata daga cikin wadannan darajoji uku ba? - Su su kan yi gado bisa wasu dokoki na musamman, amma kuma su kan yi gado tare da kowace daya daga wadannan darajoji. · Da farko ina ganin zan tambaye ka bisa masu gado daraja ta farko da ta biyu da ta uku. Tambayi abin da ka so. T: Idan mamaci ya kasance a cikin makusantansa ba masu cin gado na farko sai ''ya''ya kawai ya za'ayi rabon. A: Sai su gaje dukkanin dukiyarsa. T: In da namiji tilo ne ko ko ''ya mace kawai suka rage yaya za'a yi? Wato da namiji shi kadai ya rage. Ko kuma ya mace ita kadai ta saura? A: Sai ya gaje dukiyar gaba daya ko ta gaje dukiyar gaba daya.. T: In ko dukkanninsu maza ne fa ko kuma dukkaninsu mata ne yaya za'a yi? A: Sai su raba dukiyar a tsakaninsu daidai. T: Amma idan maza ne tare da mata fa? A: Namiji sai ya dauki kason mace biyu. T: Shin lafazin da ana amfani ne da shi kan namiji da mace koko ana amfani ne da shi kan da namiji ne kawai kamar yadda ya fi yaduwa a yanzu. A: Ana yin amfani da shi a kan da namiji ko mace, kamar yanda lafazin ya zo cikin al'kur'ani mai girma Allah madaukaki yana cewa [ALLAH YANA YI MUKU WASIYCI A CIKIN ''YAYA YENKU NAMIJI YANA DA RABON MACE BIYU]. T: Da za mu dauka cewar wani mutum ya mutu ya bar da daya namiji da ''ya daya mace to yaya za'a raba gado tsakanninsu? A: Za'a raba dukiyar mamaci uku a ba wa dansa kaso biyu ''yar kashi guda. T: Idan har mamaci bai da makusanta masu gado a daraja na farko sai iyayensa kana dayansu ya rasu yaya kenan? A: Wanda yake da rai din sai ya gaji dukiyar gabaki daya. T: Da kuma mahaifiya da mahaifi suna raye sai dai mahaifin bai da ''yan uwa a nan yaya rabon yake? A: Sai mahaifi ya dauki kaso biyu cikin kaso ukun dukiyar, mahaifiya kuma ta dauki kaso daya wanda ya rage. T: To yaya kuma idan mahaifi da mahaifiya suna raye, kana mamacin yana da ''ya guda daya sai dai ba shi da ''yan uwa yaya rabon yake? A: Sai mahaifi ya dauki kaso daya cikin kaso biyar din dukiyar, kana mahaifiya ma ta dauki kaso daya cikin biyar ragowar kaso uku cikin kaso biyar din dukiyar ''ya ta dauka. T: Idan mamaci ya zamanto daya daga cikin iyayensa na raye tare da ''ya''yansa maza da mata yaya za'ayi rabon? A: Kaso daya cikin kaso shidan dukiyar sai wanda yake rayen daga cikin mahaifansa ya dauka abin da ya rage sai a raba wa ''ya''ya dai dai da ka'idar da take cewa: [NAMIJI YANA DA MISALIN RABON MACE BIYU] T: Bara kuma mu koma ga masu cin gado daraja ta biyu zan iya tunawa ka ce min ''yan uwa suna daga masu cin gado daraja ta biyu ne. A: I haka ne na gaya maka. T: Yaya idan mutum ya bar dan uwa guda daya mace ko miji? A: Dan uwan ko ‘yar uwar suna daukar dukiyar ne gabaki daya. T: To yaya idan ya kasance yana da ''yan uwa da yawa wanda suke uwa daya uba daya? A: Za'a raba dukiyar daidai a tsakaninsu idan dukkanninsu maza ne, koko dukkaninsu mata ne amma idan ya zamanto wasunsu maza ne wasunsu mata ne sai a yi rabon namiji yana da misalin kason mace biyu, ana yin wannan ne idan babansu daya babarsu daya ko kuma duk babansu daya kawai, amma idan uwa suka hada za a raba musu dukiyar daidai ne koda ko maza da mata ne. T: Da kyau baffanni da kawunni ai ina ce suna daga cikin masu cin gado daraja ta uku ne? A: Haka ne ai har ma ‘yan uwan uwa mata ko maza suna daga cikin masu cin gado daraja ta uku. T: Da za mu dauka cewar mutum ya mutu bai da kowa sai dan uwan mahaifi mace ko namiji ya za a yi rabon? A: Dan uwan mahaifin ko ‘yar uwar mahaifin suna daukar dukiyar ne gabaki daya. T: To yaya kuma idan da ‘yan uwan mahaifin da yawa wayanda dukkanninsu maza ne ko kuma mata? A: Za'a raba dukiyar a tsakaninsu daidai da daidai. T: Ya hukumci yake in mamaci ya bar daya daga cikin dan uwan mahaifi namiji ko mace tare da daya daga cikin dan uwan mahaifiya namiji ko mace ko kuma sama da daya? A: Sai a raba dukiyar uku kaso biyu na "yan uwan mahaifi kaso daya kuma na yan uwan mahaifiya. T: Yaya kuma gadon mata da miji yake? A: Mace tana da wani hukumci na daban cikin gado, wasu daga cikin abubuwan da miji ya bari matarsa ba ta gadarsa kai tsaye ba ta gadon gundarun abun, kana ba ta gadon kudinsa, misali kasa kowace iri ne kuwa kamar kasa ta ginin gida, ko kasa ta noma, ko makamanciyarta, domin dukkannin kasar da miji ya bari mace ba ta da rabo a cikinta ko cikin kudinta. Haka kuma mace ba ta da rabo cikin gundarun wasu daga cikin dukiyar da ya bari saidai kawai tana da rabo ne cikin kimar wannan dukiyar, misalin bishiyoyi ko kayan gona, ko gini mace tana da kaso a cikin wannan kadara, na kimarsu a lokacin da aka bayar bayan yi musu kimar, kamar yadda aka saba, bai halatta ga ragowar magada su yi amfani da abin da mace take da gadonsa ba, koda ko wanda take da gadon kimarsa ne sai da izininta. T: Yaya kuma cikin abubuwan da miji ya bari wanda ba gini ba ba kasa ba ba bishiya ko kayan gona ba? A: Abin da ba wadannan ba mace tana gado kamar yanda kowa yake gado. T: Shin miji yana gadon matarsa? A: I miji yana gadon matarsa cikin dukkan abin da ta bari wanda ake iya daukarsa da wanda ma ba'a iya dauka kamar kasa da dukiya da bishiya da makamantansu. T: Idan mace ta mutu ta bar mijinta ba ta da da tare da shi, ko waninsa ya gadon yake? A: Mijin yana daukan rabin abin da ta bari ragowar magada kuma su dauki rabi. T: To yaya idan ta zamo tana da da? A: A nan miji zai dauki kaso daya cikin hudu abin da ya rage kuma na ragowar magada. T: Da za mu Juyo da tambayarmu mu ce idan miji ya mutu ya bar matarsa ba shi da da kaso nawa take gada daga dukiyar mijin nata? A: Tana daukan kaso daya cikin hudu abin da ya rage ragowar magada su dauka. T: Ya idan ya zamo yana da da da ita ko da watanta wato da wata mace? A: Za ta dauki kaso daya cikin takwas ragowar a bai wa magada. · Babana sai ya ce:- akwai wasu masa alolin na gado wanda littattafan fikihu suka yi cikakken bayani a kansu, in ka ga kana son karin bayani sai ka duba su. Duk da cewa yanzu mun gama zan yi maka nuni da wasu alamura: (1) A cikin kayan da mamaci ya bari ana ba wa babban da kyautar al'kur'aninsa, zobensa, da takobinsa, da kayansa wanda ya sa da wanda ya tanada domin ya sa, idan al'kur'anin ya zamo yana da yawa ko zoben ko takobin babban dan sai su yi sulhu da sauran magada, haka nan kuma misalin sirdi da bindiga da wuka, mai baki biyu da abin da ya yi kama da su na daga makami. (2) Wanda ya yi kisa ba ya gadon wanda aka kashe idan har kisan da gangan ne bisa zalunci, amma in ya kashe shi bisa kuskure ne zai gaje shi cikin abin da ya bari. (3) Musulmi yana gadon kafiri amma kafiri ba ya gadon musulmi.
|
||