MUHAWARA KAN WASIYYA


        ·          Babana ya fara haskaka zaman muhawara da hadisin da aka ruwaito daga ABU JAAFAR (A.S) ya ce:- “wasiyya wani hakki ne da ya dace musulmi ya yi, domin Manzon Allah (S.A.W.A.) ya yi”.

T: Ya mahaifina ai wasu mutanen ba sa yi, domin su suna sauwara cewa wasiyya wani abu ne wanda ake yin sa dab da mutuwa don haka ma suka sanya shu'umanci cikinta?

A: Wasiyya abu ne wanda yake mustahabi kai ana ma cewa abu ne wanda yake tsawaita rayuwa, kana kin yin wasiyya makaruhi ne abu ne kuma mara kyau.

T: Bayan wadannan abubuwa duka  mutuwa ai gaskiya ce ko ba haka ba?

A: E mutuwa gaskiya ce domin ubangiji madaukaki ya fada cikin littafinsa mai girma [Dukkannin rai mai dandanar mutuwa ce] wannan wata aya ce wacce da yawa mutane suna maimaita ta, kana ni ma ina karanta ta a makabarta a hanya.

        ·          Na dan yi shiru kadan na ce mutuwa gaskiya ce cikin alamar tsoro da razani.

In har haka ne to don mene ne ake gudun abin da yake hakika dole kuma sai ya faru?

Ashe ba abu ne wanda ya kamace mu mu kasance masu riko da hakika ba mu kuma yi aiki da ita ba?

Ashe bai dace mu yi tanadi ga abin da ba makawa sai ya zo ba'a isa a guje masa ba?

Shin mun yi tsawon rai ko ma ba mu yi tsayin rai ba lallai za ta zo don haka  sai ta kasance hanyar wa azi da kuma abin lura.

T: Sai dai ni har yanzu ban sani ba yaya mutum zai yi wasiyya?

A: Mustahabi ne ka fara sanin irin wasiyyar da Manzon Allah (S.A.W.A.) ya sanar da lmam Ali (A.S) ita da kuma musulmi.

T: Wacce irin wasiyya ce?

A: Mahaifina ya zabura ya tafi dakin littattafansa can sai ga shi ya dawo tare da littafi wanda yake girmamawa yana kiran sa [AL'WASA'IL] sai ya karanta min nassin wasiyyar da Manzon Allah ya koya wa lmam Ali da musulmai ni kuma ina rubuta abin da yake karatawa ni kuma na rubuta to ga nassinta:

[Ya Allah mahaliccin sammai da kassai wanda yake masanin sarari da boye mai rahma da jin kai ya Ubangiji ina mai daukar maka alkawari tun a nan gidan duniya cewa na shaida babu wani sarki sai kai, kai kadai kake baka da abokin tarayya Annabi Muhammadu kuma bawanka ne Manzonka ne kana wuta da aljanna gaskiya ne tashin ma mata da hisabi gaskiya ne auna aiyukan bayi ma gaskiya ne kaddara da mizani ma gaskiya ne addini kuma shi ne kamar yadda ka siffata musulunci kuma shi ne kamar yanda ka shar' anta kuma zance, shi ne kamar yanda ka fada Al' qur'ani shi ne kamar yadda ka siffata kuma kai ne ubangijin gaskiya mabayyani ka sakanta wa Annabi Muhammadu da fiyayyen sakamako, kana Annabi Muhammadu da ahlul baitinsa ka daukaka darajarsu.

Ya ubangiji ya abin tanadina lokacin bakin cikina ya wanda yake tare da ni lokacin da nake cikin tsanani ya wanda yake majibincin ni'imata.

Ya mahaliccina mahaliccin iyayena kar ka bar ni da kaina iya tsayin rayuwata ko da da kiftawar ido domin in ka bar ni da kaina wannan shi ne mafi kusanci zuwa sharri mafi nisa daga alheri ka debe min kewa cikin kabari ka sanya min wani alkawari ran da zan gamu da kai] kana sai mutum ya yi wasiyya da abin da yake son yin wasiyyarsa.

T: Da me zai yi wasiyyar?

A: Zai wasiyya ga kula da 'ya'yansa kanana, da kuma iyalinsa ya kuma yi wasiyya ga sada zumunci, kana ya yi wasiyya da biyan bashin da ake binsa, ko ba da amanar da aka ba shi, ya kuma yi wasiyya da rama' abin da ya kufce masa na sallah da azumi da hajji, yai Wasiyya da ba da khumusin dukiyarsa ko zakka wacce bai bayar ba, ya kuma yi wasiyya da ciyar da talakawa don ya sami lada, kana yai wasiyya da wasu aiyukan alheri na musamman wanda za'a yi don shi bayan ya rasu, yana yin wasiyya da sadaka da kuma duk abin da ya so.

        ·          Mahaifina ya fadi wannan sai ya kara da cewa:- an shardanta ga wanda zai yi wasiyya ya kasance ya balaga kuma yana da hankali bisa zabinsa kana ya kasance mai nitsuwa domin wasiyyar wawa cikin dukiyarsa ba ta inganta ko wasiyyar mutum wanda aka tilasta masa, yaro wanda ya shekara goma in wasiyyar tasa ta zamo ta fuskar aikin alheri ne ko sada zumuncin makusantansa to ta inganta.

Kar me ba da wasiyyar ya kasance ya kai kansa ga halaka ne da gangan da cin guba ko yi wa kansa mummunan rauni, ko abin da ya yi kama da haka na daga abin da yake jawo masa mutuwa.

A irin wannan hali wasiyyarsa ba ta inganta ba, amma tana inganta cikin wasu abubuwa daban kamar abin da ya shafi kayan binne shi, ko kuma abin da ya rataya cikin "ya''yansa wanda ba su da hali ko abin da ya yi kama da haka.

Babana ya kara cewa:- ana ambaton mutumin da mai wasiyya ya zabe shi domin aiwatar da wasiyyarsa [Wasiyyi] Wasiyyi kuma ba shi da dama ya fauwala al'amarin wasiyyar ga wani daban ba shi ba abin nufi shine:- shi wasiyyi bai da dama ta fuskar shari a, ya tube kansa ya nada wani ya zama wasiyyi.

Amma yana da damar da zai wakilta wani da ya aminta da shi, domin ya tsaya masa ga wani alamarin wasiyyar in har mai wasiyyar ba yana nufin shi da kansa ne zai aikata ba.

T: Shin sharadi ne wasiyya ta kasance a rubuce aka yi ta?

A: Sam ba sharadi ba ne mutum zai iya yin wasiyya da lafazi ko ko da nuni wanda ake fahimtar abin da yake nufi da shi, kamar yanda rubutunsa yake gamsarwa ko sa hannunsa wanda ke nuna nufin a yi aiki da wannan abin bayan ya rasu [Abin nufi rubutun da yake da alamar cewar wasiyyarsa ce.

T: Shin mutum yana rubuta wasiyyarsa ne lokacin da yake rashin lafiya da zai rasu?

A: A'a mutum yana rubuta wasiyya cikin halayen guda biyu halin rashin lafiya, ko halin da yake da lafiya.

T: Yana iya yin wasiyya da dukkannin abin da ya so?

A: I yana iya yin wasiyya da dukkannin abin da ya so da sharadin in ba, sabo ba ne, kamar taimaka wa azzalumi ko makamancin haka.

T: Yana iya yin wasiyya da dukkannin abin da ya ga dama cikin abubuwan da zai bari ko ko kowane gwargwado na kudi?

A: Mutum yana da ''yancin ya yi wasiyya kadai da abin da bai fi kaso daya cikin kaso ukun kayan da zai bari ba kudi ko kuma abin da ba kudi ba wato sulusi kawai.

T: To yaya idan ya yi wasiyya da abin da ya fi kaso daya cikin kaso ukun abin da zai bari yaya kenan wato sulusi?

A: Wannan wasiyyar ta baci cikin abin da yake sama da kaso daya cikin kaso uku sai in har magada sun yarda su yafe abin da ya karu a kan kaso daya cikin uku (sulusi).

T: Idan na so aiwatar da wasiyya yaya zan yi?

A: Da farko kana fitar da hakkin dukiyar da ya rataya a wuyan mai wasiyyar daga cikin Jimlar abin da ya bari kamar biyan bashi da kudin kayayyakin da ya saya bai biya ba da makamantansu daga ciki akwai khumusi da zakka da hakkokin mutanen da suke wuyansa da hajji ta wajibi tun asali ko da ya yi wasiyya da hakan kuma ko da bai yi ba.

Wannan idan bai yi wasiyya da fitar da ita ba daga cikin kaso daya cikin kaso uku in ko ya yi wasiyya sai a fitar daga cikinsa,

Sannan sai a raba abin da ya bari uku, kashi daya ga abin da ya yi wasiya kaso biyu kuma na magada.

T: Wani lokaci mamaci yana yin wasiyyar a ba da wasu kudi ga wani mutum mu'ayyani ko a ba shi wani gida, ko wasu kaya ko fili, ko kuma ya yi umarni da a binne shi wani wuri na musamman, ko irin hanyar da za,a binne shi ta zamo wata hanya ce ta musamman ko abin da ya yi kama da haka to yaya irin wannan yake a shara'a?

A: Ya cancanci a yi masa dukkannin abubuwan da ya ambata in har ba su ketare kaso daya cikin kaso ukun da ya bari ba.

T: Yaya in wani abu daga cikin dukiyar mai wasiyya ya bata a hannun wanda aka yi wa wasiyyar?

A: Wanda aka ba wa wasiyya ba'a neman ya mayar da abin da ya bata a hannunsa sai inda ya yi sakaci ko ganganci, bayan mahaifina ya fadi haka sai ya kara da cewa:- idan alamar mutuwa ba ta bayyana ga mutum ba a wannan lokaci wasiyya mustahabbi ne idan alamun mutuwa ta bayyana to wajibi ne ya yi wasiyya kan wasu abubuwa kamar haka:-

(1)   Biyan bashin da lokacin biyansa ya yi in akwai damar biya din amma basukan da lokacin biyansu bai yi ba ko ko ya yi amma masu bashin ba su neme shi ya bayar ba ko kuma ma bai da ikon da zai biya bashin to cikin wa''yannan ya zama wajibi ya yi wasiyya da ita, ya kuma nemi shedu akansa in har mutane ba su sani ba.

(2)   Mai da amanar da aka ba shi ga masu ita ko ya sanar da masu ita cewar amanarsu na wurinsa ko ya yi wasiyyar a mayar da ita.

(3)   Ba da khumusi da zakka da hakkokin mutanen da yake kansa cikin gaggawa in har akwai wani hakki a kansa da ake binsa kuma yana da ikon bayar da shi.

(4)   Ya ba da wasiyya kan cewa a nemi wani a biya shi daga cikin kudinsa, domin ya yi sallah da azumi a madadinsa in har ana binsa, wajibi ne ma ya yi wasiyya ko da bashi da kudin da zai biya a yi masa in har akwai mutumin da yake ganin zai iya sadaukantar da kansa don ya yi masa, a wani lokaci ba da labari ya'isa a matsayin wasiyya, kamar a ce yana da babban da da yake jin tabbas zai rama masa salla da azumin da ake binsa.

(5)   Ya ba wa magada labarin dukiyar da yake da ita a wajen wasu ko kuma a wani wuri daban wanda ba wanda ya sani sai shi, domin kar hakkinsu ya salwanta bayan ya rasu.

T: Farkon muhawara ka ce min wasiyya mustahabi ce to yaya idan mutum bai yi ba?

A: Hakkin yai amfani da kaso daya cikin kaso ukun dukiyarsa kamar yadda yake so ya fadi, sai dai kawai a raba abin da ya bari ga magadansa dai dai da yadda yake a babin gado.

T: Yaya ake rabon?

A: Wannan shi ne abin da za mu tattauna a kansa cikin muhawararmu ta gado mai zuwa in sha Allah.

 

عنوان الکتاب