MUHAWARA AKAN BAKANCE DA ALKAWARI DA RANTSUWA |
||
|
· A kan hanyata ta komawa gida na ji wata muhawara tsakanin da da mahaifiyarsa kamar haka:- mahaifiyar ta ce:- hakika na yi bakance ga ubangiji kan yanka rago in kaninka ya warke daga cutarsa, ga shi kuma yanzu Allah ya warkar da shi don haka ya zama wajibi in cika wannan bakance nawa. Sai dan ya ce:- ashe ban gaya miki ba mama cewa koda yaushe kina fifita kanina a kaina. Sai mahayiyarsa ta ce:- don me ka fadi haka, ashe kaninka bai yi mummunar rashin lafiya ba? Ashe baka ga yanda ya rinka suma ba, ashe dakta bai ce ba don kiyayewar Allah ba da bai warke ba? Yanzu ashe ka manta irin halin da ya shiga,? Ashe yanzu bai zamo wajibi mu gode wa Allah ba,? A bisa warkar da shi da yayi? Har ma na yanka rago don yin godiya ga Allah a bisa ni'imarsa ba?. Yanzu a ce bakancen da na yi wa Allah madaukaki domin kaunar ya warkar da kaninka daga mummunar rashin lafiyar da ya yi yana nufin kenan na fifita shi a kanka? Yanzu ka manta mun yanka maka ragon suna, kuma rago mai girma ranar bakwai ga haihuwarka ashe ba mu yi yanka domin ka ba? T: Mene ne yanka ragon suna mene ne kuma laiya? A: Sai babana ya ce:- ya dana yankan suna shi ne:- a yanka wa dan da aka haifa namiji ko mace rago ko saniya rana ta bakwai ga haihuwarsa. An ruwaito daga Imam Sadik (A.S) cewa:- ana rada wa yaro suna cikin rana ta bakwai kana ana yi masa yanka ana yi masa aski ayi sadaka da azurfa. Wacce take daidai da nauyin gashin nasa, ana aika kafa da cinya, ga unguzomar da ta taimaki mai ciki wajen haihuwa sauran a ciyar da ragowar mutane da shi a kuma yi sadaka da shi, karahiya ne ga uba ko daya daga cikin iyalansa musamman ma uwar yaron su ci naman ragon sunan dan. Yanka rago sunna ce mai karfi ga wanda yake da ikon yankawa an ruwaito daga lmam Bakir (A.S) cewa:- Manzon Allah [ S.A.W.A.] ya yi kiran sallah a kunnen Hasan da Husaini a ranar da aka haife su ya yanka musu ragon suna a rana ta bakwai. Mutumin da babansa bai yanka masa ragon suna ba ya halatta ya yanka wa kansa da kansa bayan ya girma domin Umar bin Yazidu ya tambayi lmam sadik (A.S) yana mai cewa wallahi ni ban sani ba shin babana ya yanka min ragon suna ko bai yanka min ba sai lmam (A.S) ya umarce shi da ya yanka sai ya yanka wa kansa a lokacin yana tsoho”. T: Wannan ragon suna kenan sai dai kuma mene ne laiya? A: Babana ya ce:- laiya ita ce mutum ya yanka rago a ranar idi, wato idin Baban Salla in yana da hali, madalla da zai kasance mai kiba, lta ko laiya sunna ce mai karfi, kuma yana halatta a yi layya ga wani yana da rai ko ya mutu ko da ko karamin yaro ne domin Manzon Allah (S.A.W.A) ya yi wa matayensa layya kana kuma ya yi wa Ahlin gidansa wanda bai sami damar yi ba, kana kuma ya yi wa al'ummarsa wanda ba su sami damar yi ba, kamar yanda lmam Ali (A.S) yake yi wa Manzon Allah (S.A.W.A) layya kowace shekara. T: Shin dole ne wannan matar ta cika bakancen da ta yi? Ko kuwa kamar ragon suna ne ko kuma layya wanda ba wajibi ba ne mustahabi ne? A: Bara na fara gaya maka ko mene ne bakance to bakance shi ne mutum ya lizimta wa kansa wani aiki ayyananne ko kuma ya lizinta wa kansa barin wani abu domin Allah, sai dai ba ko da yaushe ne cika bakance yake zama wajibi ba, sai in har wasu sharadai sun cika. T: Yaya sharadan suke wadanda in aka cika su yake zama wajibi? A: Sune kamar haka (1) ya yi bakancen da wata siga wacce take tattare da fadinsa “lillahi” ko kuma abin da yai kama da haka daga sunayen Allah wanda da Allah kadai ya kebanta, da mai yin bakance zai ce na yi wa Allah bakancen kaza to a nan bakancensa ya tabbata, kamar ya ce “idan dana ya warke na yi bakance ga Allah zan yanka rago na yi sadaka da namansa ga talakawa.” Ko kuma ya ce “na yi bakance ga Allah a kan in bar cutar da makwabcina” da abin da ya yi kama da haka, da larabci ko kuma wani yare duk daya ne ba banbanci. Abokin muhawar:- da a ce mai bakance ya yi bakance da wata kalma daban ba wacce mutane suka saba yin bakance da ita a yanzu ba wato yanda suke cewa:- na yi wa Allah bakance kan kaza ko na yi wa ubangijin rahma bakance kan kaza to shi bai fadi haka ba. Shin wannan yaya bakancensa yake? Idan shi bai ambaci sunan Allah ba. - Ba lallai ne ya cika bakancensa ba. (2) - Abin da aka yi bakancen yin sa ya zamo abu ne wanda shari'a ta yadda da shi wato abu mai kyau kuma abin so a shari’a. T: Idan abin da aka yi bakance ya zamo ba abu ne mai kyau ba kamar karahiya, ko mai cutarwa ko kuma abin da yake halas yaya kenan? A: Cikin abubuwa biyu na farko bai inganta a yi bakance a kansu ba, amma abin da yake halas in har yana nufin cewar ma'ana da aka so da shi ya halatta, kamar da zai yi bakancen shan ruwa yana mai nufin ya kara samun karfin yin ibada da shi, to bakancen ya inganta idan ko har ba haka ba to bakancensa bai yi ba. (3) Wanda ya yi bakancen ya kasance baligi, mai hankali, kuma ba dole aka sa shi ba kuma yana mai nufin bakancen, sannan ba wanda aka hana shi sarrafa dukiyan ba. (4) Abin da aka yi bakancen da shi ya kasance abu ne wanda mai bakance yake da damar aikatawa. T: Da mutum zai yi bakancen abin da bai da ikon aikatawa yaya ke nan? A: Wannan bakancen bai, inganta ba. T: Yaya idan mutum ya yi bakance daidai da sharadan da aka ambata? A: Wajibi ne ya cika wannan bakancen nasa, ya lizimta wa kansa abin da ya yi bakancensa shin ya kasance wani aiki ne wanda zai yi shi don Allah, ko zai bar shi don Allah, zai aikata shi cikin wani zamani da ya kebance ne, ko ko zai aikata shi muddun yana raye, shin wannan aikin sallah ne, ko azumi, ko sadaka, ko ziyara, ko hajji, ko kuma yin kyauta da wani abu, ko barin wani abu, ko wanin wadannan. T: Yaya idan mutum ya ki cika bakancensa da gangan? A: Wajibi ne ya yi kaffara, kaffarar ko ita ce "yanta bawa, ko baiwa, ko ciyar da miskini goma ko dinka musu tufafi. T: A misali da za a ce mutum ya kasa saboda talauci yaya kenan? A: Sai ya yi azumi uku a jere wajibi ne ya aikata hakan. T: Da mutum zai yi bakancen sanya dukiya ga wani wurin ziyara daga cikin wurare masu tsarki yaya wannan bakance yake? A: Sai ya sanya wannan dukiya domin gyara wurin ziyarar, ko sanya masa fitulu, ko shimfida, ko ababen sanya dumi, ko sanyi, ko kuma ma dai abin da ya yi kama da haka daga abubuwan da ake yi wa wuraren ziyara, in har shi mai bakancen bai nufi wani abu na musamman wanda zai yi ba cikin wadanda da aka ambata, ko wasunsu. T: To yaya kuma da zai yi bakancen musamman saboda wanda aka binne, kamar Annabi ko Imami ko kuma ‘ya‘yan daya daga cikinsu? A: Zai ciyar da abin bakancen nasa ga talakawan da suka kai ziyara, ko kuma ga wurin ziyarar da makamancinsu. T: Idan mutum ya yi cikaken zaton cewa ya yi wani bakance mu'ayyani shin wajibi ne ya cika shi? A: Idan har ya sami nitsuwar ganin cewa ya yi bakancen to ya zama wajibi ya cika shi, in ko ba haka ba ba wajibi ba ne ya cika shi. · Haka mahaifina ya fada sai ya kara da cewa mutum yana yi wa Allah madaukakin sarki alkawari a wani lokaci, kamar ya ce:- na yi wa Allah alkawarin zan aikata kaza ko da yaushe na samu kaza idan har ya fadi haka wajibi ne ya lizimta wa kansa cika wannan alkawar. T: Ma'anar wannan shi ne cewa yin alkawari kamar bakance yake, shi ma ba ya inganta sai da wani lafazi kebantacce? A: E haka yake sannan kuma ba ya inganta sai in har ya daukar wa Allah al'kawarin kan abin da shara'a ta ba shi fifiko ko da ko al amarin da ya shafe shi ne na duniya, da sharadin dai kar ya kasance shara'a ba ta ba shi fifiko ba, kana kuma an shardanta wa alkawari irin abin da aka shardanta wa bakance, kuma na yi maka bayaninsa. T: To yaya idan mutum ya saba alkawarin da ya yi wa Allah? A: Kaffara ta zamo masa wajibi ita ce "yanta bawa ko ciyar da miskini sittin ko azumin wata biyu a jere. · Haka baba na ya fada ya kuma kara da cewa wajibi ne a cika rantsuwa kuma da mutum zai saba da gangan kaffara ta wajaba a gare shi wato kaffarar rantsuwa ita ce 'yanta bawa, ko ci da miskini goma, ko yi musu tufafi idan ko har ba zai iya daya daga wadannan ba sai ya yi azumin kwana uku ajere. An shardanta cikin rantsuwa ta zama da lafazinta kuma ya kasance da Allah ne madaukakin sarki aka yi rantsuwar sannan abin da aka yi rantsuwa a kansa ya kasance ana da damar cika shi kuma shara'a ta ba shi fifiko kuma yana isa da zai yi rantsuwa kan abin da yake halas idan ya yi rantsuwa kan aikata shi ko da kuwa kan abin da ya shafi maslaharsa ta duniya ne, sai dai an shardanta wanda zai yi rantsuwa ya kasance baligi kuma yana da hankali, kuma yana mai nufin rantsuwa bisa zabinsa wato ba a sa shi dole ba. T: Ina misalin irin rantsuwar da yake wajibi ne a cikata? A: Idan mutum ya ce wallahi sai na aikata kaza, ko ya ce na rantse da Allah zan aikata kaza, ko fadin na rantse da Ubangijin al'kur'ani ko abin da ya yi kama da haka. T: To yaya da kuma mutum zai gaya wa wani mutum daban cewa wallahi sai ka aikata kaza? A: Rantsuwa ba ta da alaka da aikin wani mutum daban ko kuma zamanin da ya riga ya wuce don haka ba wani tasiri akan irin wannan rantsuwa. Kamar yanda rantsuwar yaro ba ta yiwuwa in har babansa ya hana shi, haka nan rantsuwar mace idan mijinta ya hana ta. Idan da ya yi rantsuwa ba da izinin babansa ba ko mace ta yi rantsuwa ba da izinin mijinta ba a nan uba ko miji suna da damar warware wannan rantsuwar. T: Wani lokaci mutum yana yin rantsuwa a kan cewa zancensa gaskiya ne kuma a hakika ya yi gaskiya a zancen nasa ko kuma kan wani abu mu'ayyani, kuma yana da gaskiya a rantsuwar tasa to irin wannan rantsuwar ya hukumcinta yake? A: Rantsuwa kan gaskiya ba'a haramta ta ba sai dai an karhanta. Amma rantsuwa a kan karya an haramta ta banda ma haka ana ganinta daga cikin manyan zunubai, sai dai in larura ce ta sa aka yi ta. T: Wacce irin larura? A: Idan mutum yai nufin kubutar da kansa ko muminai daga azzalumi to wannan rantsuwar ta halatta ta kan iya zamowa wajibi kamar inda azzalumin ya yi barazana cikin salwantar ran muminin ko mutuncinsa, ko wani muminin daban, ko kuma mutumcinsa sai dai duk da haka zai duba cikin kalmomi masu harshen damo don yin amfani da su in har ya san su kuma cikin sauki zai iya amfani da su to lallai ne sai yai amfani da su. T: Me kake nufi da ya zo da kalmomi masu harshen damo a cikin maganarsa “tauriya”? A: Kalma mai harshen damo wato tauriya ita ce mai magana yai nufin wata ma'ana wacce ba ita zahirin kalmar ke nunawa ba, ba kuma tare da yin bayani ba, misali shi ne da azzalumi zai tambaye ka ko ka ga wane, wanda yake mumini ne sai ka ji tsoron kar ya cutar da shi sai ka ce da azzalumin ban gan shi ba bayan kuma ka gan shi kafin awa daya da maganarka sai dai kana nufin a nan tun mintuna da suka gabata baka gan shi ba wannan ita ce kalma mai harshen damo ko kuma tauriya. |
||