MUHAWARA AKAN SAKI


Da ina zaton ni ne kadai nake kin saki bayan na ji zancen da muka yi da babana daga sannan na san ba ni kadai ba ne nake kin saki.

Wannan shi ne yadda na sami babana kamar ni shi ma yana kin saki, wa"yannan mutane kamar mu ne su ma suna kin saki, sama ma da haka babana ya gaya min cewa Ubangiji madaukaki yana kin saki ya ma kara da ciro min nassusukan hadisai wanda take yin magana a kan haka, babana ya ruwaito min hadisin [Ja'afarus sadik] [A.S] yana cewa:- ba wani abu da Allah yake ki sama da saki. Ya kuma kara ruwaito min wani hadisin daga gare shi [A.S] yana cewa:- ba wani abu da Allah ya fi ki sama da gidan da aka rushe a musulunci da rabuwa, abin nufi saki.

Ya kuma kara ruwaito min daga [Hasan ibn fadl] daga [Ja afarus sadik [A.S] yana cewa:- ku yi aure amma kar ku yi saki, domin al'arshi yana girgiza saboda saki.

Hakika kin da ake yi wa saki kamar yadda ya zo cikin hadisi mai girma ya ketare sakin har ya kai ga mai yin sakin, don an ruwaito hadisi daga lmam Jafarus sadik [A.S] yana cewa:- na ji mahaifina yana cewa:- Ubangiji madaukakin sarki yana kin mutumin da yake yawaita saki.

Sai na ce ni kam ina kin saki amma duk da haka yana da kyau in san wasu daga cikin hukumce hukumcensa.

Sai babana yace:- haka ne sai ya fara muhawararsa kan hukumce hukumcen saki ya ce:- an shardanta cikin mutumin da zai yi saki ya zamo baligi, kana mai hankali, kuma bisa zabinsa, sakin yaro ba ya inganta, ko mahaukaci ko wanda aka yi wa dole, I ana ganin sakin yaron da ya kai shekara goma yana iya inganta, amma duk da haka ba makawa bisa aiki da ihtiyadi.

Kana sharadi ne mai sakin ya nufi rabuwa da fadinsa “na sake ki”, don haka sakin da ya yi shi da wasa, ko da rafkannuwa, ko don bai fahimci kalmar sakin ba bai inganta ba.

T: Wace kalma ce wacce ake yin amfani da ita don yin saki?

A: Saki ba ya yiwuwa sai in har an yi shi da wata siga ta musamman, da kuma harshen larabci, ga wanda ya iya larabcin kana kuma a gaban mutane guda biyu adalai, wanda suke jin yanda za'a yi sakin.

Misalin yanda ake yin saki  miji yana cewa “matata wance sakakkiya ce,” ko kuma ya ce da ita “ke sakakkiya ce,” ko kuma wakilin miji ya ce:- matar wanda ya sanya ni wakilci wance sakakkiya ce, idan haka ta faru saki ya afku a tsakanin ma'aura.

T: Shin dole ne a ambaci sunan matar lokacin da za'ai sakin?

A: Sam ba wajibi ba ne ya ambaci sunanta cikin kalmar sakin, in har'an riga an san ta, kamar ya zamo ba shi da wata mace sai ita.

Sai babana ya ce:- saki ba ya halatta muddun matar da za'a saka ba'a cikin tsarki take ba na haila ko biki sai in har ba'a kwanta da matar ba, ko cikin wasu halaye wanda mijinta ya yi tafiya, kamar yadda ba ya halatta miji ya saki matarsa a cikin tsarkin da ya kwanta da ita, lallai ne ya saurara har zuwa lokacin da ta yi haila ta kuma yi tsarki kana ya sake ta bayan ta yi tsarki.

Wannan kenan amma ba'a sakin matar da aka yi auren mutu'a da ita rabuwa tana tabbata ne a auren mutua bayan karewar lokacin da suka yi yarjejeniya a kanta, ko kuma ya yi mata kyautar ragowar kwanukan da suka rage, kamar mijin ya ce da matar “na baki kyautar lokacin da ta ragu,” daga nan alaka tsakaninsu ta kare ba'a lura da sheda cikin ingancin kyautar ragowar lokaci wacce aka yi ta cikin auren mutu'a, kana kuma tsarkakuwar mace daga haila ko biki ba sharadi ba ne.

Babana ya kara da cewa idan mutum ya saki matarsa wacce ya kwanta da ita bayan ta cika shekara tara kafin ta kai shekarar daina yin haila wajibi ne ta yi idda daga  lokacin da aka sake ta ba daga lokacin da ta san cewa ita yanzu sakakkiya ce ba: iddar saki ga mara ciki tsarki uku ne kana kuma ana kidanya tsarkin da ke tsakanin sakinta, da hailarta mai zuwa a matsayin tsarki guda ko da lokacin bai da yawa.

T: Ma anar wannan shi ne cewa iddarta tana karewa bayan ta ga jini na uku kenan?

A: E bayan ta ga jinin hailarta na uku iddarta ta kare.

T: Yaya kuma iddar mai ciki take wadda aka saka?

A: Iddar mai ciki shi ne zuwa ta haife cikinta don haka iddarta tana karewa ne bayan haihuwar, ta haife shi cikakke ne ko bari.

T: Da za ta haihu bayan sakinta da kwana daya shin ta kare iddarta kenan da wannan haihuwar da ta yi?

A: I ta kare idda ko da kuwa haihuwar ta yi ta ne bayan sakin da awa daya, ba ma rana guda ba, sharadin dan ya kasance ba na zina ba.

T: Shin matar da a kai auren mutu'a da ita tana yin idda bayan ta rabu da mijinta?

A: Idan har ta balaga kuma ya sadu da ita ba ta kuma kai shekarun daina haila ba kana kuma ba ta da ciki iddarta haila biyu ne ga wacce take haila, sannan kwana ar'ba in da biyar, ga wacce ba ta haila saboda wata cuta ko abin da ya yi kama da haka.

Bayan babana ya fadi wannan sai ya kara da cewa saki wani al'amari ne wanda yake hannun miji kana sakin kala biyu ne akwai wanda ake yin biko akwai wanda ba'a yi.

Sakin da ba'a yin biko “ba’in” shi ne sakin da miji bai da damar dawo da matarsa har sai an kara daura sabon aure. Kamar mutum ya sake matarsa kafin kwana da ita.

Sakin da ake yin biko “raj’iy’shi” ne sakin da miji yake da damar dawo da matarsa wacce ya saka muddin tana cikin idda, ba tare da sai ta yi sabon aure ba ko kuma wani sabon sadaki ba.

Yana daga irin sakin da ba a yi masa biko sakin da ake kira [khul'i] abin da ake nufi da wannan sakin shi ne matar da take kin mijinta ta fanshi kanta daga gare shi muddun kin da take yi masa ya kai matsayin da ba za ta kare hakkin aure ba, ko kuma ba za ta tsai da hakkokin Ubangiji ba muddun dai ba mijin ne ya ki ta ba, to a'irin wannan hali idan mace ta ce da mijinta na ba ka sadakina don ka yi mini sakin khul’i, shi kuma mijin ya ce da harshen larabci a gaban shedu guda biyu matata wance na yi mata sakin khul’i bisa abin da ta ba ni, ko kuma ya ce wance sakakkiya ce bisa kaza idan ya fadi haka hakika ya sake ta saki na [khul’i].

T: Shin ambaton sunan mace a nan wajibi ne?

A: In har an san ta ba lallai ba ne ya fadi sunanta.

T: Shin yana halatta dukiyar da aka ba wa mijin ta kasance ba sadaki ba domin ya yi sakin khul’i wa matarsa?

A: E haka yana halatta.

T: Shin yana cancanta ga mace da miji su wakilta wani ya tsaya a matsayinsu cikin ba da sadaki ko waninsa cikin sakin khul'i.

A: I hakan yana halatta a gare su.

T: Wani lokaci ana neman miji a rasa a kuma kasa samun labarin inda yake, kana ba'a sani ba yana raye ko kuwa ya rasu in haka ta faru mene ne abin yi?

A: Yana cancanta cikin irin wannan hali ta kai kara wajen alkali na shara'a, shi kuma ya yi umarni da a nemo shi cikin shekara hudu idan har ba a samo labarinsa ba kana kuma mijin ba shi da wata dukiya wacce za'a iya ciyar da matar da ita sannan waliyyinsa bai ciyar da ita da dukiyarsa ba, alkali sai ya umarci waliyinsa ya sake ta, in kuma waliyyin ya ki kana an gaza tilasta masa, ko kuma ma bai da waliyi sai  alkalin  ya sake ta da kansa idan har matar ta nemi ya yi haka.

T: To yaya kuma in aka yi wa miji daurin rai da rai kana kuma bai da damar ci da matarsa kuma ya ki yadda ya sake ta?

A: Cikin irin wannan hali ya halatta mace ta kai kara wurin alkali na shara'a, shi alkalin ya sami mijin ya yi masa umarni da ya sake ta idan ya ki yadda ya sake ta, kana kuma aka rasa hanyar da za a bi domin a sa shi ya sake ta to a nan alkali sai ya sake ta idan ta nemi haka daga gare shi.

عنوان الکتاب