MUHAWARA KAN AURE

 

An gayyace mu da ni da mahaifina zuwa walimar auren dan makocinmu baban Ali sai ya zamo mana lallai ne mu yi shirin halartar wannan walima ranar juma’a misalin karfe biyar na yamma domin mu taya wannan makwabci namu mai girma farin cikin wannan abu.

Wai baikon wa za a yi ne ya tambayi babansa?

Baikon dansa Ali.

Amma Ali ai yaro ne har yanzu domin kuwa’a yanzu zancen da muke yi shekararsa ishirin har yanzu bai isa aure ba.

Mahaifinsa ya ce:- ya yi shekara ishirin din amma kake cewa bai isa aure ba bayan a yanzu ne yake kan ganiyar samartakarsa karfinsa yake kara karuwa hankalinsa yake cika kana kuma sha’awarsa take kara yawa. Kana ya kara da cewa tun da sha’awa ta zamo tana karfafa kuma tana motsawa cikin irin wannan shekaru don haka sai ya zamo abin da ya fi kyau ga saurayi ya yi aure a cikin farkon samartakarsa don ya kare kansa daga afkawa cikin mummunan aikin da aka haramta domin ita rai aba ce mai umarni da mummunan aiki ya zo a cikin ayar Alqur’ani mai girma cewa:- (ba zan kubutar da kaina ba domin rai mai yawan umarni ne da mummunan aiki)

Ya ce:- ko da na ji irin wannan hali na sha’awa take sai na ji kunya domin mutumin da yake cikin shekaru kamar nawa ya kan ji kunyar yai zance ko ya ji wani abu na game da magana kan sha’awa duk da cewa yana cike da shauki da bukatar hakan.lokacin da babana ya fahimci irin halin da nake ciki na kunya wanda ya bayyana a fuskata sai ya tambaye ni cewa:- kunya kake ji?

Sai na amsa masa:- I domin magana kan sha’awa abu ne mai sa kunya.

Mahaifina ya ce:- sai dai ita sha’awa wata bukata ce wacce take hade da lafiyar mutum wanda dukkanin mutum madaidaici yake da ita kuma tana matsayin abinci ne ko abin sha ga dan adam kana tana yin dai dai da sauran wasu bukatu na jiki, kamar yanda kake tsananin bukatar abinci don ka ci ko kuma kake tsananin bukatar ruwa don ka sha to haka na kake da bukata ta sha’awa Izuwa yin aure.

Amma shi Ali har yanzu saurayi ne?

Wani lokaci yana zamowa wajibi ga dan adam yai aure

Ka ce wani lokaci yana zamowa wajibi mutum yai aure kana nufin wajibci na shara’a?

I wajibi na shara’a in har mutum ba zai iya kame shaawarsa ba ya hana kansa afkawa cikin haram saboda rashin aure.

Ashe kenan Ali ya nuna jarunta saboda daura aniya da ya yi dangane da aure.

I ya nuna jarunta kwarai da kuma kare kai domin kuwa yayin da ya sami kansa cikin lokaci na sha’wa ya ga rudi na sha’awa yana bujuro masa ya kuma gano in yai wasa wannan hali zai zamar da kafafensa.

Wannan shi ne irin halin da yake tare da shi kowanne lokaci yake neman jansa yake kuma yi masa kai kawo, to a cikin irin wannan hali ne mai girgiza dan Adam da razana shi Ali ya ga mafi kyau shi ne ya zantar da babansa irin bukatar da yake da ita ta yin aure domin ya kare rabin addininsa kamar yadda fadin hakan ya gudana a harshen Manzo (S.A.W.A.) [cewa duk mutumin da ya yi aure ya kare rabin addininsa sai ya ji tsoron Ubangiji a cikin ragowar.]

Haka nan ya ce ya ci gaba kuma yana mai fadin:- aure wani aiki ne wanda ubangiji madaukakin sarki yake so domin kuwa Allah madaukakin sarki ya fada a cikin littafinsa mai girma  (yana daga ayarsa ya halicce maku daga rai naku mata domin ku sami nutsuwa kana kuma ya sanya soyaiya da tausayawa a tsakaninku).

Haka kuma a wani wuri daban cikin littafinsa mai girma yana cewa:- [shi ne wanda ya halicce ku daga rai guda kana ya sanya mata a gare ta domin samun nutsuwa]

Kuma an ruwaito cewa lmam Bakir [A.S] ya ruwaito daga kakansa [S.A.W.A] ya ce “ba’a gina wani gini ba a cikin musulunci wanda ya fi soyuwa zuwa ga Allah sama da aure.”

Kana Manzon Allah ya ce:- ku yi aure kuma ku aurar ga wasu.

Littattafan hadisi sun ciro mana hadisi daga imamu Ali [A.S] ya ce:- ku yi aure domin yin aure sunna ce ta manzo, manzon Allah ya kasance yana cewa:- duk wanda yake so ya bi sunnata sunnata ita ce aure.

An samo wani hadisin daga lmamu Ja’afaru sadiq ya ce:- “yana daga dabi’un annabawa son mata.”

An kara karbowa daga gare shi cewa:- raka’a guda biyu da mai aure yake sallatarta ta fi raka’a saba’in wacce gwauro ya sallata.

An hakaito cewa:-na ruwaito daga mahaifinsa lmamu Bakir [A.S] cewa:- ba zan taba son a ce ina da duniya da abin da yake cikinta domin na kwana dare daya ban yi aure ba.

An ruwaito wani hadisi kuma daga lmamu kazim [A.S] ya ce:- mutane guda uku Allah yana sanya su a cikin inuwar al’arshinsa ranar da ba wata inuwa sai ita.

Na daya:- mutumin da ya aurar wa dan uwansa musulmi ko ya yi masa hidima ko ya boye masa sirri.

Akwai wasu hadisai ban da wannan wanda suke nuni zuwa ga mustahabbancin yin aure da karhancin zama ba aure ga namiji ko mace.

Ya mahaifina ka ce namiji ko mace.

I karahiya ne zama ba aure ga namiji ko mace akwai hadisai wanda suke kira zuwa ga mace ta yi aure suke kuma kwadaitar da ita yin sa.

An ruwaito daga wajen lmamu sadik [A.S] ya ce:- manzon Allah [S.A.W.A] ya hana mata su zabi rayuwar su su kadai su haramta wa kansu aure.

Ban da ma haka akwai wasu hadisai da dama wanda suke kira zuwa ga a gaggauta aurad da yarinya kada a jinkirta aurad da ita, ya zo daga Manzon Allah [S.A.W.A] yana cewa yana daga albarkar mace gaggauta aurar da ita.

Ashe yin auren wuri abu ne mai kyau? Sai dai wahalhalun auren yana da yawa ya mahaifina a’ina matashi saurayi zai samu irin wannan dukiya don ya yi aure ga shi kuma yana da tsananin bukatarsa?

Shi dai musulunci yana kira ne zuwa ga saukaka aure da rage wahalhalunsa.

Wahalhalun aure kamar yaya?

Lallai musulunci yana kira zuwa ga rage wahalhalun aure.

Sadaki a yanzu yana da tsananin tsada wanda shi ne abin da yawancin mutane suke kuka da shi to yaya haka ta faru?

Shi dai sadaki an so a sanya shi kadan kuma an ki a sa shi ya yi yawa.

T: Ya mahaifina ashe yanzu an ki yawaita sadaki?

A: I an ki yawaita sadaki kuma an so a rage shi an ruwaito daga Manzon Allah yana cewa:- mafifitan mata cikin al’ummata mafi kyaun fuskarsu mafi kuma karancinsu sadaki.

An kuma ruwaito daga wajen lmamu Bakir yana cewa:- muna zaune tare da mahaifina sai aka sa hira a kan rashin al’barka sai ya ce:- rashin albarkar mace ta kasance mai yawan sadaki kuma mara haihuwa.

Ya zo daga hadisai masu girma cewa:- yana daga albarkar mace karancin sadaki, yana daga rashin albarkarta yawancinsa.

Haka mahaifina ya ce:- kana sai ya sunkuyar da kansa kadan kamar mai yin tunani kana sai ya kara karfafa maganarsa da fadin:- Manzon Allah [S.A.W.A] ya aurad da Fatimatuz zahra [A.S] ga lmamu Ali a kan wata garkuwa na sadaki kadan bayan kuma ita ce shugabar dukkanin matan duniya.

Imamu sadiki [A.S] ya ce:- Mazon Allah ya aurad da Fatimatuz zahar ga lmamu Ali [A.S] wanda yake garkuwa ya bayar a matsayin sadaki.

Imamu Abu Ja’afar [A.S] an ruwaito daga gurinsa ya siffata shimfidar fatimatuz zahra [A.S] sai ya ce:- shimfidar fatimatuz zahra [A.S] buzun rago ne shi suke shimfidawa su yi bacci akai.

Na ce da mahaifina:- mushkilar rashin samun wuraren samun kudi tana daga cikin matsalar da take hana matashi rike iyali:- bayan ya yi aure, ko ko mu ce tsoron irin bukatun da za su biyo baya ko tsoron talauci?

Ko ko tsoron rashin samun abin da zai ci da iyali?

Sai mahaifina ya ce Allah madaukakin sarki cikin littafinsa mai girma yana cewa [ku auri zaurawa daga cikin wayanda suke salihai daga bayinku ko kuma kuyanginku idan matalauta ne Allah zai arzuta su”

A karkashin tafsirin wannan aya ne lmamu Jafar sadiki [A.S] cikin abun da aka ruwaito daga wurinsa yake cewa:- duk mutumin da ya ki yin aure don gudun talauci hakika ya munana zato ga ubangiji, bayan ko Allah madaukakin sarki yana cewa:- [in har sun kasance matalauta Allah zai azurta su daga cikin falalarsa].

Akwai wata mushkila da wasu daga cikin masu abin hannu ko ko masu matsayi suke kawowa.

Kadan daga cikin irin wayannan mushkila shi ne: ya kan ce ba zai ba da “yarsa ba sai ga mutumin da ya gan shi ya yi dai dai da wasu abubuwa da yake so kana zai ga shi ya dace da ita, sai kuma’a samu irin wannan mutumin da yake ganin ya dace bai samu ba,  bayan ko mutane da yawa sun nemi aurenta amma duk da haka sai ta ci gaba da zama ba miji.

Sai babana ya ce:- bara na ciro maka labarin irin mijin aure da musulunci yake ganin ya dace ake aura masa kamar yanda ya zo cikin wata wasika ga Imamu Bakir [A.S] wacce [Ali ibn asbat] ya rubuto masa yana mai cewa:- magana ce kan al’amarin “ya“yana mata domin har yanzu ban sami wani mutum kamata ba.

Sai lmamu Bakir [A.S] ya rubuta masa amsa yana mai cewa:- na fahimci zancenka cikin al’amarin “ya“yanka cewar har yanzu ba ka sami wani mutum kamarka ba to kada ka lura da haka Allah ya ji kanka. Domin Manzon Allah ya ce:- idan wanda kuka yarda da addininsa kana da dabi’unsa ya nemi auren “yarku to ku aura masa in ko har ba ku yi hakan ba fitina da barna mai girma za su afku a kasa.

Daga nan ne babana ya bar ni na ci gaba da lura da wannan lamari kana sai na kara bijuro da batunsa ina mai sukar al’adu wadanda suke cutar da al’umma wacce aka tsiro ta cikin gurbataccen zamani kana kuma ta dabaibaye al’umma da igiyarta.

Shi dai musulunci yana kira ne zuwa saukake aure amma al adu sun saba ma haka.

Shi dai musulunci yana kira ne zuwa ga rage Sadaki amma al adu sun saba ma haka.

Musulunci yana cewa ku yi aure kar ku ji tsoron talauci. Amma mu mun saba ma hakan. 

Musulunci ya sanya kyakkyawan dabi’a da riko da addini su zamo wasu ma’auni wayanda suka dace a kalla cikin mijin aure, amma sai ga shi rayuwarmu ta yau ta sanya ma’auninta daban, watakil ma muna iya ganin abubuwan da ake fara gabatarwa shi ne kudi da matsayi cikin abubuwa.

Ko da karfe biyar ta matso take ni da babana sai muka tafi wajen gaiyatar walimar da akai mana. Ya kuma dace in siffata muku irin abin da ya gudana a wurin daurin auren.

Haka muka isa zauren karbar baki cike da wayanda aka gaiyata suna kuma ta yi wa junansu lale barka suna sanye da kyawawan tufafi masu kuma kyau da gani fuskar mazauna wurin cike da annashuwa, sai haske kake ta gani yana tashi a saman zauren saboda kendira da suke ci ta wani bangaren kake ganin haske ko ta ina ta wani bangaren ko kanshi kake ji.

Kana shi kuma Ali yana zaune a jikin garun zauren kusa da kofar ta ciki wacce take a rufe a kusa da shi akwai wani dattijo mai cike da kwarjini yana zaune wanda kai daga ganinsa za ka ga alamar kyawawan dabi’u da nutsuwa a tare da shi kana fuskarsa tana cike da kwarjini wannan dattijo sai ya tunfari kofar wannan zaure yana kwan kwasawa da ma kuma mutane duka an yi tsit daga nan da ya kwankwasa kofa da sauti mai karfi yana magana da amarya ta jikin kofar da take rufe bayan ya karanta musu ayoyin al’kur’ani da hadisi sai ya ce fatima kin yarda na zamo wakilinki na aurad da ke ga Ali dan Muhammad kan sadaki dirhami dari biyar wanda za’a bayar take in har kin yarda ki ce ni wakilinki ne.

Sai amarya ta amsa bisa sauti kasa kasa wanda yake cike da kunya wanda ba ya fitowa sosai, ta ce da shi ka zama wakilina.

Ko da fadarta wannan kalma wannan dattijo sai ya karbi wakilci sai tashin guda kake ji cikin gida kamar karar kararrawa ce ake ta bugawa.

Kana kuma  fuskoki sai annashuwa ce take fita daga cikinsu daga nan ne sai wannan dattijo ya tunfaro wajen Ali yana mai ce masa na aura maka fatima “yar Ahmad wacce nake yi wa wakilci bisa sadaki dirhami dari biyar sai ango Ali ya amsa take ba tare da wata nawa ba yana mai cewa na karbi wannan auren

T: Don me wannan sadaki aka sanya ya zamo dan kadan baba?

A: Irin wannan shi ne sadakin sunna hakika manzon Allah [S.A.W.A] ya sunnata sadakin mata muminai dirhami dari biyar na azurfa a waccen lokacin.

Sai na ce da babana yana yiwuwa amarya fatima ta aurad da kanta ba tare da wani a tsakani ba?

I me zai hana yana yiwuwa ma’aura su aurad da kansu ba tare da wani a tsakani ba, kana kuma yana yiwuwa ga daya daga cikinsu ko dukkansu su wakilta wanda zai zamo na ibinsu. Ana rinjayar da fadin cewa amsawa ta yi dai dai da bayarwa.

T: Kamar yaya amsawa ta yi dai dai da karba?

A: Misali shi ne:- idan mace ta ce na aura maka kaina take miji ba tare da jinkiri ba sai ya ce:- na karbi wannan aurawar, ba zai ce na karbi ki zama mata ta ba wannan idan auren ya kasance aure ne na dindindin .

Har akwai wani aure wanda ba na dndindin ba?

I akwai aure Izuwa wani lokaci wanda ake aiyana masa lokaci da sadaki akan iya yi masa lokaci kamar kwana daya ko wata daya ko shekara ko abin da yai kama da haka muddun dai bai wuce tsayin rayuwar daya daga cikin su ba, irin abin da yake cancantar aure na dindindin to ya cancanci wayannan ma’aura din, kamar su daura wa kansu da kansu auren ko su sa wakili, amma da za a ce su ne za su daurawa kansu irin wannan aure wanda ba na dindindin ba in matar ta ce da mijin na aura maka kaina zuwa shekara daya bisa dinare dari sai mijin shi kuma ya ce:- ba tare da wani jinkiri ba na karbi wannan aure to auren ya inganta.

T: In aka yi haka sai kuma yaya?

A: In har suka yi haka ta zama matarsa ita kuma ta halatta ga mijinta har zuwa tsayin wannan lokaci sai dai ba gado a tsakaninsu kuma ba dole ba ne ya ciyar da ita ko kuma ya rika kwana a gurinta.

Idan lokacin da sukai yarjejeniya ya kare ta haramta a gare shi, sabanin auren dindindin wanda yake shi mace tana halatta ga mijinta har zuwa mutuwarsu muddun dai bai sake ta ba.

Wannan kenan ka sani daura aure yana da sharadudduka.

T: Mene ne sharaduddukan?

A: Su ne kamar haka.

Na daya:- bayarwa da karba a lafazi wato mace ta ce ta aurar shi kuma ya ce ya karba  wanda yarjejeniya tsakanin ma’aura ba ta isuwa sai da wannan lafazuzzukan shin auren na dundundun ne ko kuwa ba na dundundun ba saannan rubutu ba tare da lafazi ba ba ya isa. Cikin abin da ya wuce ka ga yanda lafazin daure aure yake.

Na biyu:- nufin haifar da aure da wannan sigar ma’ana shi ne ma’aura ko wakilansu su nufi tabbatar da aure da wannan sigar don haka lokacin da mace take cewa:- na aura maka kaina ta mai da kanta ne matarsa kamar yanda miji ya nufi cewa:- fadinsa na karbi auren to ya mai da ita matarsa hakanan hukumcin yake kan wakilai.

Na uku: yardar maaura muhimmi a nan shi ne su samu dacewarsa a zuciya.

T: Wani lokaci mace tana yarda amma sai ta nuna ba ta yarda ba a fili don kunya ko kuma don rauni to yaya kenan?

A: In har yarda ta samu to ya isa don haka abin da za ta bayyana a sarari na rashin yarda ba zai cutar ba, haka kuma da za a ce ba ta yarda ba amma a sarari ta nuna ta yarda, to bai isa ba.

Na hudu ayyana miji ko matar ta yadda za a iya gane su sabili da sifatawa ko nunawa ko suna amma ba ya halarta a daura auren wace ba’a sani ba, kamar mutum ya ce na aura ma daya daga cikin ‘ya‘yana, wannan bai yi ba.

Na biyar: a daura auren da harshen larabci in har da akwai damar yin hakan,: in kuma babu dama to yaya kenan?

Amsa: wanin larabci ya isa wacce za’a iya fahintar aure da ita, ko kuma ya wakilta wanda ya iya larabci ya yi da larabci:.

Na shida: balaga da hankali ga wanda zai daura auren.idan wadannan sharadudduka sun cika aure ya yiwu, kuma matar ta halarta, ga mijinta.

T: Bayan auren take ta halarta ga mijinta ba sai an yi biki ba?

A: I daga inda aka daura aure ta halarta ga mijinta, sai dai ya kamata ka san cewa auren yarinya karama sai da yardar mahaifinta ko kuma kakanta na wajen uba ko da kuwa yarinyar ta kai matsayin budurwar da take yi wa kanta komai na harkar rayuwa.

T: To yaya in ba budurwa ba ce?

A: In ba budurwa ba ce tana da hakkin aurar da kanta.

T: Idan mutum ya auri mace akan cewa budurwa ce, sai daga baya ya baiyana cewa ba budurwa ba ce to yaya kenan?

A: Ya halarta ya ba ta auren.

T: In’bai ba ta ba kuma fa?

A: In bai ba ta ba sai ya rage mata sadaki gwargwadon banbancin sadakin budurwa da bazaura.

T: Shin mutum yana da damar ya auri duk irin matar da ya so?

A: I yana da dama ya auri duk matar da ya so ban da wacce aure ya haramta a tsakaninsu, yana daga cikin matan da aure ya harmta a tsakaninsu (1) mahaifiyarsa da kakarsa ko mahaifin mace, kana ya haramta (2) ya auri “yarsa, ko ‘ya‘yan dansa, (3) ya kuma haramta ya auri ‘yar uwarsa, ko ‘ya‘yanta ko ‘ya‘yan ya yanta ya kuma haramta (4) ya auri ‘ya‘yan kaninsa, ko wansa, ko kuma “ya“yansu, (5) kana ya haramta ya auri ‘yan uwan mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, mata kuma dai (6) ya haramta ya auri mahaifiyar matarsa, ko kakarta na uba da uwa, ko da ko bai kwanta da matar ba, (7) ya kuma haramta a gare shi ‘ya auri yar matarsa wadda ya kwanta da ita,  (8) kana ya haramta ya auri matar mahaifinsa, ko matar kakansa, (9) ya kuma haramta ya auri matar dansa, ko jikansa, (10) sannan dai yana haramta ya auri kanwar matarsa, muddun dai yana tare da matar tasa domin ba ya halatta a hada ya da kanwa lokaci guda.

T: Da matarsa za ta rasu a misali shin yana cancanta a gare shi ya auri kanwarta?

A: E yana cancanta a gare shi.

(11) Haka yana haramta ga mutum ya auri wacce ta shayar da shi, ko ‘ya‘ya matan da wacce ta shayar da shi ta haifa, yana kuma haramta a gare shi ta dalilin shayarwa dukkannin abin da yake haramta a gare shi ta dalilin nasaba.

A nan za mu ga cewa bai halatta ga baban dan da aka shayar ba ya auri ‘ya‘yan matar da ta shayar masa da da wacce kuma suka hada dangi da ita, ko kuma “ya“yan mutumin da dansa ya sha nonon matarsa, ko wayanda aka shayar da su tare ko na dangi yana da kyau a, sani cewa ba dukkannin shayarwa ce take janyo irin wannan haramci ba, lallai ne shayarwar ta zamo ta hado sharaduddukan shayarwa ta yanda wanda aka shayar zai samu tasirin shayarwas yana daga cikin irin wannan sharadan (1) shayarwar ta zamo ya sha nonon daga jikin maman wacce ta shayar da shi ne kai tsaye domin ba wani tasiri ga nonon mace idan dan jinjiri ya sha shi ta hanyar shayarwa ta zamani ba kai tsaye daga jikin mata mai shayarwar ba.

Sharadi na biyu:- ya zamo wanda aka shayar din bai wuce shekarun shayarwa ba wato shekara biyu, don haka da zai sha ko ya cika shayarwassa bayan shekara biyu ba wani tasiri da irin wannan shayarwa za ta yi.

Sharadi na uku:- ya zamo shayarwar ta kai yanda za ta tsirar da nama ga wanda aka shayar din ta kuma gina masa kashi.

Amma idan aka samu kokwanto, kan ganin ta gina masa nama da kashi ko ko ba ta gina masa ba, a’irin wannan hali shayarwar da aka yi ta wuni da kwana ta isa, ko kuma shayarwa goma sha biyar.

Amma idan har an yanke cewa wannan shayarwa ba wani abu da ta haifar masa da shi wato shayarwa na kwana guda da wuni ko kuma shayarwa sau goma sha biyar idan aka yanke cewa ba ta tsirar masa da nama ba bai kuma gina masa kashi ba to a nan sai a yi aiki da ihtiyat.

Za'a kiyaye cikin yin amfani da zamani -wato cewar sai ya sha nonon har tsayin wuni da kwana -ya kasance nonon kawai shi ne abincin yaron har zuwa tsayin wannan lokaci, ta inda kuma duk lokacin da ya nemi nonon tana ba shi ba ta hana shi, amma da zai nema ta hana shi ko ya ci wani abinci daban ko ya sha nonon wata mai shayarwa daban to wannan shayarwas tata ba tai tasiri ba in har daya daga cikin wadannan ya faru.

Ana kuma lura da cewa wanda za'a shayar din farkon lokacin da za'a shayar da shi ya zamo yana jin yinwa domin ya yi cikakken sha kana lokacin da zamanin shayar da shi din ya cika ya zamanto a koshe yake.

Amma bisa yin amfani da lissafi na adadi-wato cewa goma sha biyar-ya zamo ajere ne ya sha, yanda wata mace ba ta shayar da shi a tsakani ba, kana kuma ko wacce shayarwa ta zamo cikakkiyar shayarwa ya fara sha lokacin da yake jin yinwa ya gama ta yana koshe.

Akwai wasu hukumci daban daban na shayarwa wanda littattafan fikihu suka yi bayaninta ka iya duba su a can idan ka bukaci haka.

T: To yaya idan mutum ya yi aure dai dai da yanda shara'a ta tsara?

A: Matarsa ta halarta a gare shi kamar yadda na gaya maka kuma wajibi ne a gare ta ta yi masa biyayya kana ta ba shi kanta ko da yaushe ya so, ko kadan ba ya cancanta a tare da ita ta hana shi kanta sai in har da akwai wani uzuri na shara'a, kamar yanda kuma bai halatta ga matar da aka aura auren dindindin ba ta fita daga gidanta sai da izinin mijinta.

Ta wani bangaren yana zamowa wajibi ga miji ya ciyar da matarsa wacce ya aura auren dindindin kana ya sama mata gurin zama da tufafi kana ya samar mata abin da za ta ci ta sha ta rayu dai dai matsayinta gwargwadon halinsa.

Kamar yanda kuma bai cancanta ga miji ya ki saduwa da matarsa ba har tsayin wata hudu in ta kasance budurwa sai da yardarta ko kuma saboda wani uzuri wanda zai iya janyo jikkata ko cuta.

T: To yaya kuma idan miji bai ciyar da matarsa abin da ta cancanta ba?

A: Wannan ciyarwar tana nan a matsayin bashi a tare da shi don haka idan ya ki ba ta bayan ta nema ya halatta a tare da ita ta diba daga cikin dukiyarsa ba tare da izininsa ba.

Wannan kenan kana zan kara lissafa maka wasu daga cikin hukunce hukunce bisa wannan tsari da aka yi.

Na daya:- kallo ko shafa don nufin jin dadi haram ne namiji ya yi su ga wata mace ko da ko karamar yarinya ce ko kuma mace ta yi su ga wani namiji ko da ko karamin yaro ne amma ban da miji da mata kana ba su halatta tsakanin namiji da namiji ko da ko karamin yaro ne, haka ma tsakanin mace da mace ko da ko karamar yarinya ce na biyu:- kallon al'aurar wani namiji ko mace yana haramta ko da ko al'aurar yaron da ya mallaki hankalinsa ne, amma ban da al'aurar mata da miji.

Na uku:- ya haramta ga namiji ya yi duba zuwa jikin matar da ba tasa ba wacce take bare a tare da shi jikinta ko gashinta sai dai fuskarta da tafukan hannuwanta yana halatta a gare shi ya yi duba zuwa gare su ba da nufin jin dadi ba, kamar yanda yake haramta ga mace ta kalli jikin namiji wanda yake bare a tare da ita cikin wuraren da ba dole ba ne ya suturce su kamar kansa, hannuwansa, kafafuwansa ya halatta ta kalli wadannan wuraren ba da nufin jin dadi ba, na hudu:- ya halatta ga namiji ya kalli jikin dan uwansa namiji ba da nufin jin dadi ba, kana ya halatta ga mace ta kalli jikin yar uwarta mace ba da nufin jin dadi ba, kamar yadda ya halatta ga namiji ya kalli jikin matan da ya haramta ya aura shi ma ba da nufin jin dadi ba, kana yana halatta ga mace ta kalli jikin mazajen da ya haramta ta aura sai dai kuma ba da nufin jin dadi ba, sai dai kawai al'aura ne bai halatta a kalla ba cikin abubuwan da aka ambata.

Don haka yana halatta ga namiji ba da nufin jin dadi ba ya kalli jikin mahaifiyarsa, ko  ‘yar uwarsa, kanwar mahaifinsa, ko ‘yar uwar mahaifiyarsa, yar dan uwansa ko "yar kanwarsa, ko kakarsa.

Shin Ya halatta ya kalli jikin matar wansa, ko kaninsa, ko yar dan uwan mahaifinsa, ko ‘yar ‘yar uwar mahaifinsa ko ‘yar ‘yar uwar mahaifiyarsa, ko yar dan uwan, mahaifiyarsa?

Sam sam bai halatta ya kalli daya daga cikin wadannan ba, domin kuwa gabaki dayansu zai iya aurensu.

Na biyar:- yana zamowa wajibi a kan mace ta suturce jikinta ta rufe kanta gashinta da kuma jikinta ga dukkanin wanda bai halatta ya ga jikinta ba, daga mazajen da suke bare a tare da ita, har ma ga yaron da ya mallaki hankalinsa idan har hakan zai motsa sha‘awarsa, amma ban da fuskarta da hannuwanta ya halatta mace ta fito da su ko da ko a gaban mazajen da suke bare ne in har ba ta tsoron fadawa a cikin haram, kuma za ta yi haka ne ba da nutin jefa mutumin cikin kallo wanda ya haramta ba, idan kuwa ya zan haka to a wadannan halaye biyu ma wajibi ne ta yi lullubi gare su.

Na shida:- ya halatta ga namiji ya kalli jikin matan kafirai ba da nufin jin dadi ba da kuma matan da ba sa hijabi, wadanda suke fitsararru wayanda ba su yarda su kiyaye jikinsu da gashinsu ba lokacin da aka hana su yayewa ta inda ko an hana su hanin ma ba zai amfani ba.

Na bakwai:- idan mutum ya so auren wata mace ya halatta ya kalli wuraren da za su kayatar da shi nata kamar fuskarta da gashinta da wuyanta da tafukan hannunta da kwaurinta ba da nufin jin dadi ba.

T: Kafin a daura aure ya halatta a gare shi ya kalle ta?

A: I ya halatta ya kalle ta ya ma yi zance da ita kafin daura aure, kai kafin ma ya fara nemanta domin ya ga abubuwan da za su kayatar da shi kana daga baya ya sami karfin neman aurenta (idan an ga alamun gaskiya cikin neman yin hakan).

Na takwas:- ya halatta ga likita ya kalli jikin mace kana ya taba in maganin da za a yi mata ya kai da a taba ko a kalla wannan kuwa yana faruwa ne lokacin da mace ta bukatu zuwa magani kuma dokta namiji ya zamanto shi ya fi tausasawa a kan mace in ko ba haka ba to ta tafi wajen likita mace bai halatta ta je wajen namiji ba.

Na tara:- ya halatta ga namiji musulmi ya auri matar da take ahlul kitabi ina nufin kirista ko bayahudiya amma fa auren mutu'a.

T: To amma ita ai' ba musulma ba ce ba kuma mumina ba ce, kana kuma ba ta yi imani da auren mutu'ar ba to yaya kenan?

A: Duk da haka ya halatta a aure ta auren mutu'a ko da kuwa son kudi ne ya sa ta yi auren.

Na goma:- bai halatta namiji ya auri mace sama da hudu ba auren dindindin sai dai yana da "yancin ya saki matansa duk lokacin da ya so.

Abin ya zo dai dai kenan da ma ba kai min magana a kan saki ba.

Mahaifinsa ya ce:- zan yi maka magana kan saki cikin muhawararmu wacce za ta zo gaba insha Allah

Abin ya yi kyau Allah ya kai mu muhawara mai zuwa wacce ita ce muhawara a kan saki insha allah.

 

عنوان الکتاب