MUHAWARA KAN YANDA AKE YANKA DA FARAUTA

 

Ba zan boye muku ba cewa lokacin da na shiga dakin muhawara wacce taken ta shi ne [yanda ake yin yanka da farauta] ban taba tunani zan ji irin abin da na ji ba ko kuma a ce zan fito da irin abin da na fito da shi ba. Da na kasance ina mai zaton zan ji an ce yanka rashin tausayi ne wanda ake nuna wa abin yanka sai ga shi an shammace ni!!

 Jama’a ashe bisa irin wannan tausasawa ne ubangiji yai wasiyya ga mai yankan dabba ya yi wa dabba lokacin yanka ta!

Ya mutane da dukkan irin wannan kulawa da muhimmantarwa ga irin abin da dabba take ji da kuma irin furfuka da take na fitar rai ashe Ubangiji [S.W.T.]ya kwadaitar da mai yanka irin abin da zai aiwatar a kan abin yankansa?!

Ya ku jama’a ashe da duk irin wannan nuni ne na kada a azabtar da dabba ko a wahalar da ita Allah madaukakin sarki ya kira mai yanka ya kasance?!

:- Duk irin wadannan tunanunnuka su ne suka zo cikin kwakwalwata nan take tare da kuma cewa tunanin irin surar halin rashin tausayi wanda yake cike da ban tsoro na azabtarwa ga dabbar da za’a yanka ban gushe cikin haka ba ina mai sauraron mahaifina yana zantar da ni irin abubuwan da suke ababan so a cikin yanka.

Sai mahaifina ya ce:- an so ga wanda zai yanka dabba ya tafi da ita gurin yanka bisa tausasawa. Kuma an so ga mai yanka ya ba wa dabbarsa ruwa ta sha kafin ya yanka ta.

Kana an so ga mai yanka kada ya bar dabba ta ga abin da zai yanka ta da shi wato wukar.

Kuma dai an so ga mai yanka ya goga wukar da karfi a bisa abin yanka cikin lokaci kankani domin ya gama yankan cikin gaggawa.

An so dai ga mai yanka ya kyautata saurin goga abin da yake yin yanka da shi domin yankan nasa ya zamo cikin sauki.

An kuma so ga mai yankan dabba kar ya dauke dabbar daga wurin da ya yanka ta sai bayan ta mutu.

An karhanta yin yanka gaban ragowar dabbobi wadanda suke jinsi guda.

Kana an ki mutum ya yanka dabbar da yai kiwonta da hannunsa.

An karhanta fede dabba kafin ta gama mutuwa.

Wadannan su ne abubuwan da babana ya fada ya kuma kara karfafa maganarsa da hadisin da aka ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W.A.) ya zo cikin hadisin cewa Ubangiji madaukakin sarki ya rubuta kyautatawa cikin kowanne abu don haka idan za ku yi kisa ku kyautata kisanku kana idan za ku yi yanka ku kyautata yankanku dayanku ya wasa wukarsa domin ya hutar da abin yankawarsa.

Ya mahaifina ni ban san yanda zan yanka dabba ba yaya ake?

Idan ka so yanka dabba ka yanke jijiyoyin wuyanta guda hudu dukkansu.

T: Wadanne ne jijiyoyin wuyanta guda hudu?

A: Sune [jannaye] hanyar da abinci yake gudu da kuma makogwaro hanyar da nunfashi yake fita da manyan jijiyoyi guda biyu wayanda suke hade da makogwaro da jannaye.

T: Ya mahaifina ina so ka kara mani bayani.

A: Daga nan ne mahaifinsa ya ce:- masana yanka suna cewa duk lokacin da ka yanke jijyoyi guda hudu za ka ga wani kulilun nama daga ta bangaren kai wato zakaran wuya’amma idan ka sami wani bangaren yana tare da jikinta abin nufi a nan wadannan jijiyoyi guda hudu ba su yanku ba domin shi wannan kululun naman shi ne mahadar makogwaro da jannaye amma abin da yake sama shi ba makogwaro ba ne ba kuma jannaye ba ne.

T: Ma’anar wannan shi ne lokacin da nake yanka zan yi yankan ne ta kasan kululun naman “wato zakaran wuya” ba ta samansa ba kenan.

A: Haka ne ka fara yanka ta kasansa domin kada kululun naman ya saura ta jikin dabba ba bangaren kan ba.

T: Da zan yi kure sai na yanko ta saman kululun naman ba ta kasansa ba kana take sai na gano na yi ba daidai ba shin ina da damar na koma na yanko ta kasansa kafin dabbar ta mutu?

A: E kana da damar haka.

Sai mahaifina ya kara da cewa an kebance rakumi daga cikin dabbobi da a soke shi ba wai a yanka shi ba.

T: Yaya zan soke shi?

A: Idan ka so ka soke rakumi ka shigar da wuka ko mashi ko kuma abin da kake son yin sukan da shi wanda aka yi da karfe mai kaifi a cikin karenkarmarsa wato karshen makogwaro ta bangaren kirji.

T: Mene ne karenkarma?

A: Shi ne dan wani guri da ya fada a ta saman kirji wanda ya hada da wuya.

Ya ce:- yanzu na san yanda ake yanka tinkiya ko akuya saniya ko kaza ko tattabara  kana kuma na san yanda ake soke rakumi.

Sai mahaifinsa ya ce:- idan ka san wannan don cin naman dabbobi kamar tumaki saniya kaza ko tattabara ya zama lallai ka cika wasu sharadai cikin yankansu sharadan kuwa su ne:-

Na daya abin yankan ya zamo da karfe aka yi shi in har za’a iya samun na karfen amma in babu ya halatta a yi da wanda aka yi da jan karfe ko nuhasi ko darma ko gilashi ko dutse wanda suke da kaifi ko kuma makamantansu wadanda za’a iya yin yanka da su.

T: Yaya wukaken da aka yi su da ingantaccen bakin karfe?

A: Irin wadannan wukake akwai mushkila cikin a yi yanka da su domin an zuba (chrome) da yawa a cikinsa shi kuwa ba karfe ba ne.

Abu na biyu: mai yankan ya kasance musulmi namiji ko mace ko kuma yaro mai rarrabewa yankan kafiri shi ne ba ya halatta ko da kuwa kirista ne ko Bayahude kuma ko da kuwa sun ambaci Allah.

Abu na uku:- ya kalli Alkibla da abin yankan lokacin yanka shi shi ne ya sanya fuskar dabba da hannuwanta da cikinta da kafofinta su kalli Alkibla in a tsaye take, ko a tsugune yana mai fuskantar da ita gaba daya zuwa alkibla kamar yanda mutum yake fuskantar Alkibla lokacin sallah amma idan dabbar a kwance take a kasa fuskantar da ita Alkibla yana tabbata da kirjinta da kuma cikinta.

T: Da za’a ki fuskantar da dabba zuwa ga kibla lokacin yanka ta yaya kenan?

A: In har da gangan aka yi ba ta halarta a ci ba.

T: In ya zamana ba da gangan ba ne fa?

A: Idan dalilin da ya hana a fuskantar da ita alkibla bisa mantuwa ne ko kuskure ko rashin sanin alkibla ko rashin samun damar fuskantar da ita ko ko rashin sanin cewar kallon’alkibla din sharadi ne daga cikin sharadan da suke halattawa a ci abin yanka, to in har daya daga cikin wadannan shi ne dalili bai haramta ba saboda rashin kallon. Abu na hudu:- mai yanka ya ambaci sunan Allah shi shi kadai domin yankan sawa’un ya ambaci sunan Allah lokacin da ya fara yankan ne ko kafin ya fara yana mai sadar da shi da yankan duk daidai ne.

T: Me yake fadi cikin ambaton Ubangijin?

A: Fadin bismillahi ko Allahu akbar ko alhamdu lillahi ya isa.

T: Yaya idan mai yanka ya manta ambaton Ubangiji shin ta haramta?

A: Ba ta haramta ba.

Na ga wasu suna yanke kan abin yankan lokacin da suke yankan, mahaifinsa sai ya ce da shi da gangan kada ka yanke kan abin yankanka kada kuma ka zubar da lakarsa kafin ya mutu.

Abu na biyar:- jini ya fito kamar yanda aka saba bai halatta ba idan har jini bai fito ba daga jikin dabba ko kuma jinin da bai kai ya kawo ba dangane da irin dabbar sabili da sandarewarsa cikin jijiyoyinta, amma idan karancin nasa ya kasance saboda zubewarsa ne domin rauni da ta yi hakan bai cutar ba wajen halaccinta.

Wadannan su ne sharadai wayanda suke wajibai cikin yanka.

Sai baba ya ce abin da ya rage na nusashsheka wani hali wanda idan aka yi kokwanto cikin ran dabba lokacin da ake yanka ta sai ya zamo sharadi ne idan an yanka ta ta motsa ko da ko motsin da bai kai ya kawo ba ne kamar ta motsa jelarta ko kafarta ko idonta ko makamantansu domin yin hakan shi zai halatta mana cin namanta.

T: Idan da ma mun san tana da rai fa?

A: A wannan lokacin sai ya zama ba’a da bukatar ta yi motsi.

T: Ka gayan cewa rakumi dole a soke shi shin ko akwai wani sharadi bayan sokewar don cin namansa ya halatta?

A: An shardanta ga mai sokewar abubuwan da aka shardanta ga mai yanka kana an shardanta wa abin da za ai sukan da shi irin abin da aka shardanta wa abin da ake yin yanka da shi.

Yana zamowa wajibi a kalli Alkibla cikin suka da kuma ambaton Allah kana ya zamo yana raye lokacin da za a soke shi.

T: Yaya dan tayin da yake cikin dabba?

A: Idan ya fito daga cikin babar tasa da rai hukumcinsa hukuncin babarsa za’a yanka shi shi ma ko a soke shi.

T: Idan ya fito a mace fa?

A: In har an yanka uwarsa ko an soke ta daidai da sharaduddukan da suka gabata sai ya mutu a cikinta saannan ya zamo dukkanin halitarsa ta cika wato dogwayen gashi ko kanana duk sun tsiro masa to cin namansa ya halatta, a nan bai halatta a yi jinkirin fitar da dan tayi daga cikin mahaifiyarsa ba har ya mutu yana zamowa wajibi a gaggauta tsaga cikinta a fito da shi, don haka da mai yanka zai yi jinkirin fito da shi har ya mutu cin namansa bai halatta ba.

T: Idan uwar dan tayi da dan tayin suka mutu ba tare da an yanka su ba ko an soke su ba a halin dan tayin na cikinta za’a ci?

A: Haram ne ba za’a ci ba.

Babana yace: sharadudukan da aka ambata idan ta hadu cikin yankan dabba ko kuma soke ta muna kiran wannan dabba dabbar da aka yanka irin yanka na shari’a, daga nan ne ya ci gaba da sharhi yana mai cewa:- wasu daga cikin dabbobi ana cin namansu kamar tinkiya ko akuya ko saniya da makamantansu.

Wasu daga cikin dabbobin ba’a cinsu kamar zaki, damisa, dila, shaho, ko mikiya da wasu daga cikin kwari wanda suke zaune a cikin kasa.

Wasu kuma najasa ne ba yanda za a yi su tsarkaka kamar kare da alade.

Ana yanka dukkanin dabbar da ake cin namanta sai yankan ya zama ya tsarkake ta ya kuma halatta cin ta don haka yanka ba ya yiwuwa ga dabbar da take najasa wacce ba yanda za a yi ta tsarkaka kamar kare da alhanzar (alade).

T: To yaya kuma dabbobin da ba a cin namansu kamar dila, zaki da mikiya?

A: Su ma ana iya yanka su amma kwari su ne wanda ba’a yankawa wayanda suke kananan dabbobi masu zama cikin kasa kamar damo ko bera su ba’a yanka su amma wasunsu ana yanka su sai namansu ya tsarkaka da fatarsu ya kuma halatta a yi amfani da fatar tasu da abubuwan da yake yiwuwa a yi amfani da su daban daban har ma kamar yanda magabatanmu suka kasance suna yin jallo don zuba mai ko ruwa sai ya zamo duk abin da ya taba bai najastu ba ko da ko jallon ya kasance danyar fata ne domin dabbar an yanka ta.

T: Idan muka samu naman dabbar da ake iya yanka ta ko fatarta a hannun wani musulmi yana sayarwa ko yana sanye da ita mu kuma ba mu sani ba shin ya yanka ta ko kuwa bai yanka ba mene ne abin yi?

A: Ka ce wannan dabba yankakkiya ce kawai muddun dai ka same ta a hannun musulmi kana kuma yana yin amfani da ita irin amfanin da bai dace a yi ba sai an yanka, sai dai inda ya tabbata cewar ba yankakkiya ba ce.

Ya ce:- karin wani abu da babana ya fada shi ne cewa:- idan ka sami wani abu na dabbar da ake yankawa a hannun musulmi yana sayarwa wanda kafin ta zo hannunsa daga hannun kafiri take kana kuma ana raya cewa ya tabbatar an yanka ta a nan ma hukuncinta hukumcin yankakkiya ce, sai inda ya tabbata a gare ka cewar ba yankakkiya ba ce.

Bisa yin kyakkyawan wani tsokaci wanda yake shi ne cewa:- idan ka riga ka san cewa musulmin ya karbo ta ne daga wurin kafirin ba tare da yin binciken ko yankakkiya ce ba kuma ana ganin kamar an yanka to a nan sai ka tafi a kan mai tsarki ce amma dai bai halatta kai amfani da ita ba cikin abin da yanka ya zan sharadi ne a cikinsa kamar ci.

Haka kuma nama ko fata wacce aka samo ta daga hannun kafiri kai tsaye.

T: Ka ce min idan an sami naman dabbar da ake iya yankawa ko kuma fatarta a hannun musulmi sai dai kuma ba’a san cewa an yanka ta ko kuma ba’a yanka ta ba cikin irin wannan hali ka fadi cewa wannan dabba yankakkiya ce har sai ya tabbata cewa ba’a yanka ba ko ba haka ba ne?

A: E haka ne.

T: To kamar yanda ka sani cewa musulmi suna da sabani cikin mazhabobinsu da ma akidunsu to ya abin da aka samu a hannunsu?

A: I duk da haka kana yi mata hukunci da cewa yankakkiya ce shin musulmin mazhabarku daya ko kuwa ba mazahabarku daya ba.

T: Akwai daga cikin mazahabobin musulunci ko akidun musulunci wadanda ba su shardanta sharadan da ka ambata na yanka ba, misalin wayanda basa ganin kallon alkibla sharadi ne ko kuma ambaton sunan Allah ko mai yankan ya kasance musulmi, kai ba ma sa ganin yanke jijiyoyin nan guda hudu suna daga cikin sharadi to irin yankan wadannan yaya kenan?

A: Duk na san da wannan ba wani abu ba ne kai mata hukumci da cewa yankakkiya ce muddun yana amfani ne da namanta da fatarta irin na dabbar da aka yanka, kuma kana raya cewar ya yanka ta dai dai da sharadan da muka ambata ko da kuwa ba ya ganin wayannan sharadai dole ne a kiyaye su, kai bandama haka ko da kana da yakinin bai kiyaye sharadin kallon alkibla ba hakan bai cutar da halaccin abin da ya yanka ba in a akidarsa yin hakan ba lallai ba ne.

T: Yaya hukumcin dabbobin da ake yankawa a garuruwan musulmi da injuna?

A: Idan dukkanin sharaduddukan da aka ambata sun cika yanka ya yi wato ya kasance wanda yake jibintar lamarin yankan wanda ke motsa abin da wukar yankan take cikinsa musulmi ne kana ya kasance yana ambaton Allah a wurin yankan bayan haka kuma an kalli alkibla tare da cika sharaduddukan da suka gabata ya halatta a ci namanta, sam ba ta da wani bambanci da wacce aka yanka da hannu.

T: Yaya kifaye?

Ba ka zantar da ni yadda ake yanka su ba.

A: Yanda ake yanka kifaye sannan daga bisani halaccin cin namansu ya saba da yankan sauran dabbobi wanda aka ambata a baya, domin kifi ko da yaushe ya zo hannunka da rai kamar wanda ka ciro shi daga ruwa ka sa hannunka cikin ruwa ka fito da shi ko ka farauto shi da koma ko fatsa ko burgi ko ko a’a kifin ya fito waje bayan kafewar ruwa ko irin wanda ya yo tsalle zuwa gabar kogi ko cikin kwale kwale sai ka kama shi da rai, to duk wanda ya zo hannunka da rai to ya halatta ka ci wato yankarsa shi ne ka kama shi da rai.

T: Yaya idan kifi ya yi tsalle ya fito waje amma ba ka same shi ba sai bayan ya mutu?

A: Haram ne ka ci namansa ban da haka da za ka ga kifi yana wutsil a kan kasa ba ka san cewa mutum ne ya fito da shi daga ruwan ko ba mutum ba ne ba ka kai kansa ba har ya mutu shi ma ya haramta ka ci namansa.

T: Ya sharadin ambaton sunan Allah yake na ji ba ka ambace ta cikin halaccin kifi ba?

A: Ba sharadi ba ne a ambaci sunan Allah cikin halaccin kifi ba.

T: Shin sharadi ne mafaraucin ya kasance musulmi?

A: Shi ma ba sharadi ba ne cikin halaccin kifi mafaraucin nata ya kasance musulmi.

T: Kana nufin idan kafiri ya fito da kifi daga ruwa yana da rai ya halatta a ci?

A: I ya halatta ka ci a nan ba bambanci tsakanin musulmi da kafiri.

T: Idan na sami kifi a hannun musulmi yana sayarwa ban sani ba shin ya same shi da ransa ne domin cinsa ya halatta a gare ni ko kuma ya same shi matacce ne domin cinsa ya haramta?

A: Ka ce wannan kifin halattacce ne muddun dai a hannun musulmi yake kuma ya aiwatar da abin da yake nuna an yanka shi kamar ya sai da shi don ci ko abin da yai kama da haka.

T: Idan na sami kifi a hannun kafiri ban sani ba cewa shin ya kama shi ne a wajen ruwan da rai ko ko matacce abin da nake son cewa:- shi ne shin an yanka ko ba a yanka ba?

A: Ka yi hukumci da cewa ba halattacce ba ne, kai ban da ma haka ko da ya ba ka labarin cewa an kama da rai bai halatta ka ci ba muddun dai ba ka san cewar ya fito da shi daga ruwan ba kafin ya mutu ko kuma ya same shi a wajen ruwan kafin ya mutu ko kuma ya mutu a cikin komarsa ko tarkon da ya kafa a cikin ruwa.

T: Idan mai kamun kifi ya zuba guba a cikin ruwa sai kifi ya ci sai ya taso saman ruwan ya kasa gudu sai ya kama shi to menene hukumci?

A: Idan ka kama shi da rai ya halatta ka ci amma in ya mutu kafin ka kama shi bai halatta ka ci ba.

T: Idan dan su ya kafa shinge ko tarko domin kama kifi sai kifin ya shiga kana sai ruwan ya kafe sai kifin ya mutu a cikinta bayan kafewar ruwan shin za a ci?

A: I za’a iya cin namansa.

T: Wani lokaci dan su na jefa tarkonsa cikin ruwa sai ya fito da shi yana dauke da kifi ya mutu a cikin tarkon ya hukuncin cinsa yake?

A: Shi ma dai za’a ci.

T: Wani lokaci dan su yana fito da kifi da rai sai ya tsaga shi ko kuma ya doki kansa sai ya mutu, yaya wannan za’a ci?

A: Ya halatta ka ci domin ba sharadi ba ne don an fito da kifi daga ruwa a ce sai ya mutu da kansa, yana halatta a ci namansa ko da ko tsaga a kai ko gasa shi ko gunduwa gunduwa da shi har ya mutu.

T: Jinin da ya fito daga jikinsa fa kafin a gasa shi yana bukatuwa zuwa tsarkakewa?

A: Jinin kifi abu ne mai tsarki.

T: Na ce da mahaifina ka zantar da ni yanda ake farautar kifi amma ba ka zantar da ni yanda ake farautar dabbobin daji ba kamar barewa yayin da aka farauto ta da bindiga ya halaccin su yake?

A: An shardanta cikin yankan dabbar jeji wacce aka halatta cin namanta kamar barewa, bauna, tsuntsu da jakin jeji da makamantansu in har an farauto su da bindiga ko wani abu daban na daga makami akwai sharaduduka wanda idan suka hadu cin namansu ya halatta kuma ya tsarkaka kamar wacce aka yanka.

Wadannan su ne sharaduddukan.

Na daya:- mafaraucin ya zamo musulmi ko wanda ake wa hukumci da musulunci kamar yaron da ya mallaki hankalinsa kamar yanda ya riga ya gabata a cikin shara duddukan yanka.

Na biyu:- ya zamo yana mai nufin farauta a lokacin da yake amfani da makamin nasa amma da zai harba makaminsa da nufin wani abu sai ya sami wata dabba bisa kuskure sai ya kashe ta a nan bai halatta a ci ba.

Na uku:- ya ambaci sunan Allah lokacin da zai yi amfani da makamin nasa kan dabbar farauta ko kafin gamuwa da ita, ambaton bismillahi ko Allahu akbar ko alhamdu lillahi ya isa.

Na  hudu:- ya samu abin da ya farauto din makaminsa ne ya kashe shi ko ya same shi da rai sai dai kafin ya yanka shi ya mutu, amma da zai same shi da rai har ya zamo akwai lokacin da zai yanka shi bai yanka shi ba har ya mutu bai halatta a ci ba.

Na biyar:- a cikin farautar da ake yi da bindiga wajibi ne ya zamo harbin ne ya shigi jikin dabbar ya kashe ta wato harbin ne musabbabin mutuwarta.

T: Idan aka farauci dabbar daji wacce ta halatta a ci kamar barewa ko tsuntsu da karen farauta ba da makami ba ya halatta a ci?

A: Ya halatta a ci shi yana kuma tsarkaka bayan ya farauce shi in har wayannan sharaduddukan masu zuwa sun cika.

Sharadi na daya:- karen ya zamo an koyar da shi farauta yanda yana jin umarnin mai shi ko haninsa

Na biyu:- ya zamo mai shi ne ya sake shi domin ya kamo dabbar amma da ya zamo shi da kansa ne ya kamo ta bai gamsar ba matsawar ba mai shi ba ne ya sake shi.

Na uku:- kana mafaraucin ya zamo musulmi kamar yanda ya riga ya gabata a cikin sharadan yanka.

Na hudu wanda ya tura karen ya zamo ya ambaci sunan Allah lokacin da ya sake shi ya wadatar ya ce bismillah ko Allah Akbar ko alhamdu lillah.

Na biyar:- dabbar ta zamo ta mutu ne saboda raunin da karen ya yi mata ko cizonsa amma ba irin wadda ta mutu saboda makura ko gajiya yayin gudu ko makamantansu ba.

Na shida:- mai karen ya samu abin da ya farauta bayan ya mutu ko dab da zai yanka shi, amma da zai same shi da rai ya zamo akwai lokacin da zai iya yanka shi bai yanka ba har ya mutu bai halatta a ci ba, haka kuma hukuncin yake da zai yi nawar zuwa wurinsa har ya mutu kafin ya isa wurinsa ko kuma ya isa cikin lokacin da ba zai yiwu ya iya yanka shi ba har ya mutu.

T: Ya hukumcin dabbar da gaggafa ko shirwa ko shaho suka farauta ko waninsu?

A: Bai halatta a ci naman  dabbar da suka farauta ba sai wacce kare ya farauta kawai.

Kuma a san cewa dai dai wurin da karen ya gatsa najasa ne ya zama wajibi a wanke shi, kana bai halatta a ci dabbar ba kafin a wanke shi .

T: Wani lokacin shirwa ko makamanciyarta tana farautar dabba sai mai shirwar ya sami abin da aka farauta ya yanka shi kafin ya mutu ya hukumcin wannan yake?

A: Ya halatta ya ci namanta in har dabbar da ake cin namanta ne kuma mafaraucin ya yanka ta yanka na shari’a irin yanda ya gabata.

T: Wani lokaci ina ganin kana yin amfani da kalmar dabba da ta halatta a ci namanta ko wacce ba ta halatta a ci namanta ba ashe kana ganin akwai wata dabbar da sam sam bai halatta a ci namanta ba?

A: I akwai dabbar da ta haramta a ci namanta.

Hakanan mahaifina ya ce: bayan ya yi shiru kadan kamar yana hado tunaninsa wuri guda kana ya dago kansa zuwa gare ni ya ce min domin na sanya ka cikin yanayin da ya dace zan lissafa maka muhimman dabbobin da ya halatta a ci namanta da wanda bai halatta a ci namanta ba, ya ci gaba yana mai fadin yana daga dabbobin da suke doron kasa wanda ya halatta a ci namansu, kaza da dukkanin nau’inta tinkiya ko akuya saniya ko rakumi doki ko alfadari ko jaki da ragon kan dutse da bauna da jakin dawa da barewa.

Sai dai an karhanta cin naman doki, alfadari da jakin gida amma ba’a haramta ba.

An haramta cin dukkan dabbar da take da fika kamar zaki, dila da makamantansu kamar yanda aka haramta cin zomo, giwa da biri kana kuma an haramta cin damo da wasunsu bera da maciji da kwari, kana an haramta naman dabbar da mutum ya barbare ta an haramta nononta kana da “ya “yan da za ta haifa gaba.

Idan dabbar da aka barbara ta kasance wacce ake son namanta ne kamar rakumi, saniya, tinkiya, da makamantansu ya zama wajibi a yanka su da farko kana a kone su wanda ya barbare su kuma ya biya kudinsu in ba nasa ba ne idan ko dabbar da aka sadu da ita dabba ce wacce hawanta aka fi yi ya zama wajibi a raba ta da garin a kai ta wani gari daban a sayar da ita wanda kuma ya barbare ta ya mai da kudinta ni har ba tasa ba ce.

- Daga nan ne babana ya kara yana mai fadin cewa:- daga cikin dabbobin ruwa kifi ya halatta ka ci naman dukkanin irin nau insa da sharadin jikinsa yana da bawo (kambori).

Amma ya haramta ka ci mataccen kifin da yake yawo a kan ruwa kamar yadda ya haramta ka ci dabbar ruwa wacce ba kifi ba musamman yana haramta ka ci naman kaguwa, kwado, kunkuru, da kozo.

Yaya kuma krafish? Halas ne.

Mahaifina ya kara da cewa:- daga cikin dabbobin da suke tashi ya halatta ka ci dukkanin nau’in tattabara da tsada da bul bul, jimina, huda huda, dawisu.

Amma bai halatta ka ci naman hankaka ba da dukkanin nau’insa kamar yanda ya haramta ka ci naman zanzaro da waninsa na daga kwari masu tashi amma ban da fara kana ya haramta ka ci dukkanin wani tsuntsu mai fartuna kamar gaggafa, shaho, shirwa kana dukkanin tsuntsun da yakan baza fukafukinsa ne wajen tashi wanda ba ya yawaita motsa su.

T: Idan ba mu san yanayin yanda tsuntsu yake tashi ba yaya kenan?

A: Abin da ake lura da shi wajen halaccin naman tsuntsu a wannan lokacin ya zamo yana da makoshi (baroro) ko kundu ko idon sawu

T: Na ga wasu masu yankan lokacin da suka yanka dabba suka gutsutsura ta  suna fitar da wasu abubuwa suna jefarwa. Haka ne akwai wasu abubuwa wayanda ba’a ci a jikin dabbar da aka yanka idan aka same su, yana daga ciki jini, kashi, ala’ura, namiji ko mace da mahaifa da duk nau’i na kumburi da “ya “yan maraina, kwayar da take cikin kwakwalwa, laka, matsarmama, saifa, mafitsara, kwayar ido wacce ake gani da ita da kashe kara ita ce [manya manyan jijiyoyi da suke kwance a cikin kashin baya daga wuya zuwa jela]. Wannan dukkanninsa a jikin dabbar da’aka yanka ba’a cinsa amma tsuntsun da aka yanka jini da kashi shi yake haramta, a kan nesanci irin abubuwan da aka lissafa na dabba in har an same su a jikinsa.

lokacin da mahaifina ya kare lissafa wadannan abubuwa sai nai shiru na ce a raina muddun dai muna magana kan abin da ya halatta a ci namansa na daga dabbar da aka yanka da wanda bai halatta ba, to don me ba zan tambayi abubuwan da suka halatta a ci ko a yi amfani da su na daga sauran abubuwa ba me yasa ba zan tambaye shi abubuwan da suke mustahabi ne a ci ba?

Yayin da wannan tunani na tambaya ya taru a cikin kwakwalwata sai na ce da mahaifina ba ni izinin in dan fita daga wannan lamari kadan domin na yi wasu tambayoyi guda biyu wayanda suke kai kawo a raina.

T: Shin yanzu akwai wani abu da ya haramta a ci ko a yi amfani da shi ban da wanda aka ambata?

T: Muddun dai muna zama a wajen cin abinci kowacce rana sau uku to shin akwai wasu mustahabai cikin cin abinci?

Ya kara da cewa:- a nan ne mahaifina ya yi murmushi take kamar ya fadi wani abu kana sai ya daidaita zamansa domin ya ce:- zan amsa maka tambayarka ta farko kana na amsa maka daya tambayar.

A: Akwai wasu abubuwa da aka haramta amfani da su ban da wayanda aka ambata kana zan takaita kan ambaton wasu abubuwa guda biyu muhimmai.

Na farko:- ya haramta a sha giya da watanta na daga abubuwan da suke sa maye domin hakika al Qur’ani ya yi magana kan haramcin shan giya inda Ubangiji madaukaki yake cewa:- “abin sani kawai giya da caca da refu da kiban kuria, kazanta ne daga aikin shaidan sai ku nisace su”.

Haka kuma ya zo cikin wasu hadisai cewa yana daga mafi girman zunubai shan giya lmam sadiq [A.S] yana cewa:- giya ita ce uwar dukkanin wani mummunan aiki kuma shugabar dukkan wani sharri.

Fiye ma da haka ya haramta ka ci abinci a kan tebur din da ake shan giya ko ko wani abu mai sa maye kai ya haramta ka zauna a’irin wannan wuri.

Abu na biyu:- ya haramta mutum ya ci dukkan wani abu da zai iya cutar da shi cutarwar da za ta iya halaka shi ko kuma ta jiyata shi kamar guba wacce take kisa da makamanciyarta. Wannan shi ne abin da yake rataye ga tambayarka ta farko.

Amma abin da yake rataye ga tambayarka ta biyu, mustahabban da suke cikin cin abinci suna da yawa shin za ka iya yin aiki da su.

Ya ce:- zan yi kokarin aiki da su. Sai mahaifinsa ya ce:- na daya daga ciki wanke hannaye kafin cin abinci da bayan cin abinci kana da goge su da hankici.

Na biyu:- ambaton Allah lokacin farawa.

Na uku:- ci da hannun dama.

Na hudu:- yin kananan loma.

Na biyar:- kyautata tauna.

Na shida:- ci sannu sannu.

Na bakwai:- a fara da dandanar gishiri a gama da dandanarsa.

Na takwas:- a wanke “ya “yan itace kafin a ci.

Na tara:- kar’a ci sai ana jin yinwa.

Na goma:- kar’a ci abinci da zafi.

Na sha daya:- kar a busa abinci ko abin sha da baki.

Na sha biyu:- kada ya bare bawon ‘ya’yan itaciyar da ake cinsu da bawonsu.

Na sha uku:- kar ka jefar da dan itaciya kafin ka gama shansa ko cinsa.

Na sha hudu:- kar ya rika kallon fuskokin mutane lokacin da suke cin abinci.

Na sha biyar:- mai abinci ya zamo shi ya fara ci kana kuma kowa ya riga shi karewa.

Na sha shida:- kada ya sha ruwa a lokacin bayan cin abinci mai maiko.

Na sha bakwai:- ka ci gabanka kar ka ci gaban wasu.

Na sha ta kwas:- kar ka ci ya yi maka yawa.

Na sha tara:- kar ka yanka burodi da wuka.

Na ishirin:- kada ka ajiye burodi a karkashin kwano.

Banda ma wayannan akwai wasu mustahaban da ba lokacin da za mu ambace su.

A nan ne muhawara akan yanka da farauta ta zo karshe.

عنوان الکتاب