MUHAWARA KAN KASUWANCI

 

Babana ya ce: shin kana so ka yi kasuwanci kamar yadda ya kamata cikin addininka? Ya kuma kara da cewa “duk wanda ya so yin kasuwanci ya zama lallai ya nemi iliminsa cikin addini, domin ya san abin da yake haram kana kuma ya san abin da yake halas, domin duk wanda yake kasuwanci ba tare da ya san halas da haram ba to lallai ya sanya kansa cikin shubuhai.”

Wannan muhimmiyar tattaunwar tana karfafa da wannan nassin da aka ruwaito daga wajen lmam Ja’afar (A.S) sai dai babana ya fara muhawarar ne da yin magana kan ciniki, domin ya yi nuni da irin muhimmancinsa, kana kuma ya fadakar da wayanda suka rafkana suka afka cikin shubuha. To saboda na gaza fahimtar hakikanin sirrin da ke cikin shigar da masa’alar kasuwanci da fikhu.

Sai na tambaye shi cewa mene ne abin da ya hada kasuwanci da fikihu?

- Sai ya fara min jawabi, yana mai motsi da hannuwansa, yana cewa hakika sharaar musulunci tana dauke da magance abubuwan da ke cikin bangaorin rayuwa daban daban, har ma da bangaren yin taltali, wanda yake cike da adalci, yake kuma da hanya mai kyau domin yalwata dukiya, da kuma raba ta a tsakanin mutane daban daban, masu kuma matsayi daban daban don yin hakan cikin alumma shi zai kawo gyara da azurtar mutane gabaki daya.

Don haka ya zamana shari’ar musulunci ta tanadi wasu dokoki dangane da tattalin arziki domin ta samu ta isa ga manufarta na tabbatar da adalci. Dokoki ne wadanda ke halattawa ko kuma haramta wasu hakoki na kasuwanci, take kuma tsukewa a wasu bangarori ta kuma yalwata a wasu daban.

Yana zamowa lallai ga mutumin da shari’a ta hau kansa (baligi) ya yi kokari don ya nema wa kansa abin da zai rayu, don kuma ya kubutar da rayuwar wayanda suke wajibi ne ya ciyar da su, kamar matarsa, da ”ya”yansa, da mahaifansa lokacin da ya zamo suna da bukatuwa in har ya zamo shi bai da shi, To a daidai wannan lokaci da ya wajaba mutum balagagge ya nemi abinci wa kansa da iyalansa, shari’a ba ta bar shi sagaga ba.

Domin kuwa akwai wasu harkokin kasuwanci wadanda suke haramun ne mutum ya aikata su.

T: Ina misali?

A: Yana daga ciki sayar da giya da tsimin da ke da maye.

Yana daga ciki sai da kare amma banda karen da a ka sanar da shi farauta.

Yana daga ciki sai da alade.

Yana daga ciki sayar da mushe wanda yake najasa ne. Haka na nama da fatar dabba wadda ba a yanka ta a tafarki na sharia ba.  Kana kwacen dukiya daga bisani cinikinsa bai halatta ba.

Hakanan sai’da abin da bai yiwuwa ayi amfani da shi sai ta hanyar haramci misalin:- abubuwan da ake caca da su ko abubuwan da ake yin wasanni na haram da su. Algus cikin kasuwanci bai halatta ba, haka ma riba, kana kuma boye abinci abin nufi shi ne abincin da mafi yawan la’umma take da bukatarsa ko kuma a boye abin da abinci ba zai hadu ba sai da shi kamar fetur da kananzir, ko kuma kamar makamashi, ko kuma a boye abin da abinci yake kyautata da shi kamar gishiri, ko mai, don jiran sai ya yi tsada a kasuwa bayan kuma musulmi suna cike da bukatarsa,

Ko sauran al’umma suna da bukatarsa matsawar ba’a samu mutumin da ke sayar da wadannan  kayan a kasuwa ba.

Haka nan karbar cin hanci domin yin hukumci bai halatta ba yin hukunci ga mai gaskiya da kuma wanda ba shi da gaskiya.

Kana yin wasa da abubuwan caca kamar ludo ko kuma chess (dara dan china) tare da ba da jingina wato wasu kudi kai hasali ma wasan ludo ko cas ko makamancinsu bai halatta ba koda kuwa ba wani kudi mutum ya ajiye. ba matsawar sun zama kayan caca

Kana mutum ya kara wa wani abu kudi wanda a hakika shi ba saye zai yi ba kawai don wanda zai saya ya ji ya kara farashin wannan abin shi ma yin hakan bai halatta ba ko da kuwa bai yi nasarar rudar mai saye din ba.

Sayen abin da dan caca ya ciwo ko abin da barawo ya sato ko makamancin haka bai halatta ba.

Gaba dayan wayannan abubuwan da aka haramta ne.

T: Shin kuma akwai abubuwan da aka karhanta?

A: Iallai akwai daga cikin ciniki wanda yake abin kyama ga musulunci ko da yake barinsa ko nisantar sa bai zama lallai ba domin yana matsayi ne na makaruhi ba na haram ba abokin muhawara ya ce ina misali?

- Misalin sayar da kayaiyakin ba su da ciruwa kamar yankin kasa sai in har zai sayi wani yankin kasa ne da kudin kana cinikin zinari da zinari ko kuwa azurfa da azurfa ba tare da wani dadi ba makaruhi ne amma in har da kari ya zama haram.

Kana neman bashi a wajen mtumin da yake sabon samun arziki makaruhi ne.

Hakan nan kuma karahiya ne mutum ya mai da sanaarsa yankan dabba, ko kuma yin kaho, ko sai da likkafani da makamantansu.

Babana ya ci gaba da cewa:- akwai wasu ma amaloli da wasu harkakokin kasuwanci wayanda suke makaruhi, a musulunce.

T: Ina misali?

A: Karahiya ne mutum ya boye aibin abin sayarwarsa, in yin hakan bai kai ga (algus ba) amma in ya kai ga yin algus to ya zama haram kana kuma an karhanta yin rantsuwa a cikin cinki, in har mutun yana da gaskiya, amma in bai da gaskiya bai halarta ba, kana kuma an karhanta kara riba a kan mumini, in har an kara ta fiye da yanda’ake da bukata.

An karhanta neman ragi bayan an yi ciniki an karhanta yin ciniki a cikin duhun da ba a ganin aibin abin da za a saya.

Karahiya ne mutum yake yabon abin da yake sayarwa, kana kuma karahiya ne mutumin da zai sai wani abu yake kushe shi, ko kuma abin da ya yi kama da wannan.

T: Wannan gaba daya makaruhi ne in ji abokin muhawara, shin ko akwai mustahabi?

A: Hakika akwai mustahabi a cikin harkar kasuwanci wanda shara a take kwadaitarwa da a’aikata shi kana take son yin sa, sai dai ba lallai ba ne ga wanda shara’a ta hau kansa yaaikata, kana ba wajibi ba ne, yana matsayin mustahabi ne kawai.

T: Ina misali?

A: Yana daga mustahabi ba wa mumini bashi ba tare da neman ya dada wani abu ba kana sayan kayan da ba su daukuwa kamar yankin kasa  mustahabi ne, kuma dai yana daga mustahabi ba da dukiya ga wanda zai kasuwanci da nufin su dinga raba ribar a tsakaninsu.

Kamar dai yanda yake cewa akwai wasu hanyoyi na kasuwanci wanda Manzon Allah ya yi bayani cewa Allah na son mai kasuwanci ya yi su. Misali shi ne a daidaita farashi a tsakanin masu sayen kaya, sai dai in akwai wani dalili kamar talauci, kana yana da kyau kada mai sayarwa ya banbanta farashi tsakanin mai nacin- neman ragi da wanda bai da naci.

Kuma mustahabi ne mai sai da kaya ya karbi hanzarin mutumin da ya dawo masa da kayan da ya saya domin ya mayar masa da kudinsa.

Mustahabi ne ya karbi wanda bai cika ba in kuma zai bayar ya ba da wanda yake cikakke.

An kuma so saukakawa cikin farashi.

An so kyautatawa cikin kaswanci da kuma yin sauki.

An kuma so neman arziki da tashi dominsa.

An so yin zabe da sayan mai kyau da sai da shi. Kana an so yin balaguro dan neman arziki da kuma yin sammako.

        ·          Babana ya ci gaba da cewa wasu hanyoyin na kasuwanci suna matsayin halas kamar in muka dubi kasuwancimu na yau sai mu samu halas na da yawa.

Ya ci gaba da fadin cewa:- babana bayan ya gama yi mini wannan bayanin sai kuma ya ce:- Ubangjin da ya shar’anta musulunci ya shardanta wadansu sharadai cikin abin da ake sayarwa kana da wasu sharadan cikin kasuwanci ya kuma kara shardanta wasu sharadan ga mutumin da zai saya ko kuma zai sayar.

T: wayanne sharadai ne aka shardanta ga abin da za a sayar?

A: Sharaduddukan suna da yawa yana daga cikinsu mutum ya san yawan abin da zai sayar ko awunsa ko kuma adadinsa ko kuma fadinsa gwargwadon sabanin abin sayarwar.

Na biyu mai sayarwar ya zama yana da damar ba da abin da ya sayar domin haka ba ya halatta a yi cinikin kifi aruwa ko cinikin tsuntsu a sama, amma ya kan iya sayar da abin da bai da damar ba da shi kamar dabbar da ta gudu in har wanda ya saya din zai iya kama ta.

Sharadi na uku:- dan kasuwa ya zamo kwararre wajen sanin abin da yake jawo mai saye ya ji kwadayin kaya kamar sanin launi da amincin kaya ko rashinsa ko kuma sanin dandano idan abin da ake dandana ne kana da makamantansu na daga abubuwan da suke janyo wa kaya bambancin kima cikin kasuwa ga abin sayarwa.

Abu na hudu:- kada abin da za a sayar ya zama akwai hakkin wani a cikinsa wanda ba’a biya ba ba ya halatta a sayar da kayan jingina ba tare da an nemi yardar wanda ya jinginar ba,

Ko kuma a sayar da abin da aka sanya shi wakafi ga musulmi in har ba su daina amfani da shi ba da suna n wakafi ko kuma ya kasance cikin wurin da sharadin wakafi yake saraya a tare da shi.

Sharadi na biyar:- abin da za a sayar ya kasance wanda ake iya gani ne kamar gida ko littafi ko kuma kayayyaki, amma bai halatta a sayar da amfanin da gida ke kawowa ba.

Daga nan ne mahaifina ya ci gaba da cewa:- abin da ake sayar da shi da awu na sikeli a cikin wani gari to ba ya kyautuwa a wannan garin a sayar da shi ba da awun sikeli ba.

Hakana abin da ake sayar da shi da awun kwano ba ya halatta a sayar da shi a wannan garin ba da awun kwano ba. Hakan kuwa an guje shi ne domin kada a sami duhu a lamarin ciniki (dole ne abu ya zama filla-filla).

Sai abokin muhawara ya ce da mahaifinsa ba ni misali a kan haka sai ya ce misali shi ne:- kayan marmarin da a wani garin ake sayar da su da awu na sikeli ba ya halatta a sayar da su a wannan garin ba da awon sikeli ba. Kana madarar da ake sayar da ita a wani gari da awon lita bai halatta ba a sayar da ita ba a wannan garin sai da awon lita.

Hakan kuwa don kada lamarin ya zama cikin duhu ne. Wannan su ne sharaduddukan da suke wajibi a cika su cikin abin da ake saye ko kuma ake sayarwa, kana kuma akwai wasu daga sharaduddukan ciniki, yana daga ciki cewa bai halatta rataya ciniki da almarin da yake bai faru ba a lokacin ciniki.

T: Ina misali?

A: Sai mahaifinsa ya ce da shi misali shi ne:- bai halatta ka ce da mai saye na sayar maka da wannan gidan nawa idan jinjirin wata ya fito, ko kuma ka ce da shi na siayar maka da wannan mota tawa idan aka haifa min da namiji ko abin da yai kama da haka.

Lallai ba makawa a sabunta ciniki bayan fitowar wata ko kuma haihuwar.

Mene ne sharaduddukan da suke wajibi mai saye ko mai sayarwa ya cika su wayanda kai nuni da su cikin maganarka? Sai ya ce:- an shardanta ga mutumin da zai saya ko kuma zai sayar ya zamo mai cikakken hankali wanda shara’a ta hau kansa baligi kana yana mai nufin sayarwar bisa zabinsa ba wanda aka yi wa dole ba ya zamto kuma wanda yake da iko bisa sarrafa abin da zai sayar din abin nasa ne ko wakili aka nada shi ko izinin sayarwa aka ba shi. ko waliyyi. 

T: Da za a yi wa mai kaya dole bisa kan sayar da kayansa? Shin ya inganta?

A: Ciniki ba ya halatta in har ya sayar da umarnin azzalumi ta inda mai kayan bai yarda ba sai dai kawai yana tsoron in har ya saba umarnin azzalumin to zai iya cutar da shi ko ya cutar da dukiyar ko kuma ya cutar da wanda yake tare da shi.

T: Wani lokaci yana zamowa dole mutum ya sayar da wasu kayansa idan wani azzalumi ya sabbaba masa canjin wuri irin wannan ciniki ya inganta?

A: E ya inganta. Ka ce da ni yana zamowa sharadi ga mai sayarwa ya kasance abinsa ne ko wakili ko waliyyi ko wanda aka yi wa izini, to da wasun wayannan kamar aboki ko makoci ko makusanci za su sayar yaya kenan?

Sai ya amsa masa da cewa:- ciniki ba ya inganta har sai idan mai abun ya yarda ko wakili ko waliyyi ko wanda aka yi wa izini da sayarwa, amma in har daya daga cikin wadannan bai yarda maka ba to wannan ciniki batacce ne.

T: Da za’a sayar da dukiyar kwace daga baya sai mai dukiyar ya yarda da cinikin meye hukumcin?

A: - Wannan cinikin ya inganta.

        ·          Ka gayan cewa sharadi ne ga wanda zai saya ko zai sayar ya zamo baligi to yaya dukiyar yaro kenan wanda bai balaga ba idan ya nufi sayar da ita?:- sayarwarsa tana inganta cikin abubuwan da ba su kai sun kawo ba wayanda a al’ada yaron da yake rarrabewa yana mu’amala da ita amma wanin wannan bai inganta yaro shi shi kadai ba tare da wani ba ya sayar da shi.

T: Wane ne yake inganta ya sayar da kayan yaro kankane?

A: Shi ne waliyyin yaro wato uba ko kaka na wajen uba ko wasiyyin daya daga cikinsu ko shugaba na shari’a in har babu daya daga cikin wayanda aka ambata don haka yana halatta ga uba ya sayar da dukiyar yaronsa tare da rashin barna a ciki kamar yadda yake halatta ga shugaba na shari’a ya sayar da dukiyar yaro in har uba ba ya nan ko kaka ko wasiyyinsu tare da lura da masalahar yaron.

T: Shin yaro yana da dama ya wakilta wani akan sai da dukiyarsa kamar yarnda babansa ko kakansa suke da dama.

A: I yana da damar haka.

T: Da za’a yi ciniki daidai da sharadan da suka gabata. Shin yana  yiwuwa ga mai saye ya mayar da abin da ya saya a ba shi kudinsa?

Haka kuma wanda ya sayar zai iya mai da kudi a ba shi abinsa?

A: Akan iya ba ta ciniki cikin halaye daban daban

Na daya:- in wanda ya saya din da wanda ya sayar din ba su bar gurin cinikin ba ko kuma suna hanya daya ba su rabu ba bisa irin wannan yanayi yana yiwuwa ga kowanne daya daga cikinsu ya ba ta cinikin.

T: Idan suka rabu fa? Ko wannensu yai tafiyarsa ya kama gabansa ya shiga sha’aninsa.

A: A wannan lokacin ciniki ya riga ya tabbata kuma ya lizimta.

Na biyu:- idan mai saye ko mai sayarwa ya zama ya yi yaudara cikin cinikinsa [kamunga] to yana cancanta a ba ta cinikin misali:- da dan kasuwa zai sai da abin sayarwasa da farashin da bai kai na kasuwa ba wanda yake akwai ban banci mai yawa a tsakani ba tare da ya sani ba daga baya sai ya gano yana da hakkin da zai ba ta cinikin, haka nan kuma idan mutum ya sayi abu bisa farashi mai yawa fiye da na kasuwa a halin bai sani ba daga baya sai ya gano, hakkinsa ne ya mayar da abun a ba shi kudinsa.

Abu na uku:- in mutum ya sai wata haja bisa siffata masa ita da aka yi ko kuma labari da aka ba shi sai daga baya ya gan ta ba yadda aka siffata masa ita ba hakkinsa ne ya mai da ita a ba shi kudinsa.

Abu na hudu in mai sayarwa ko mai saye ya sanya sharadi kan ba ta cinki a cikin wani lokaci ayyananne to hakkinsa ne in ya ga dama ya ba ta cikin lokacin.

Abu na biyar in har daya daga cikin abokan ciniki ya yi alkawarin wani aiki, bisa wata fuska muayyana, sai kuma bai aikata ba kamar yadda ya kamata ko kuma wanda zai saya sai ya ambaci wata sifa wacce yake so ga wata haja sai kuma ya zama hajar ba ta da wannan sifar, to shi ma ya samu ya ba ta cinikin.

Abu na shida:- idan mai saye ya sayi abu sai kuma ya ga aibu a cikinsa, to shi ma yana da hakkin ba ta ciniki, kamar mai sayarwa in ya sami aibi a cikin kudi yana da damar mai da su, kana kuma a mai da masa da kayansa.

Abu na bakwai idan ya bayyana cewa abin da mai saye ya saya ba mallakar wanda ya sayar masa da shi ba ne to shi ma ya samu ya mai da shi a ba shi kudinsa, in har mai kayan bai yarda ba.

Abu na takwas in har mai sayarwa bai da damar mika abin da ya sayar, to mai saye ya samu ya karbi kudinsa.

Abu na tara in abin da aka sayar dabba ne mai saye yana da damar mai da ita a mayar masa da kudinsa a cikin kwana uku, haka kuma da a ce dabba ce aka ba da ita a maimakon kudin abin da aka sayar to wanda ya sayar da kaya yana da hakkin bata wannan ciniki ya mayar da dabbar ga mai ita a tsayin kwana uku.

Abu na Goma: idan mai sayar da abu ya nuna wa mai saye abin sayarwa ta yanda mai saye ya zamanto ya ga abin sayen da wata fuska wadda ba ta gaskiyan lamari ba, har hakan ya kwadaitar da shi ga sayen abin ko kuma ya kara son abin, to a wannan hali idan hakikanin (gaskiyan) abin ya bayyana gare shi daga bayan ya saya to yana da hakki ya mayar da abin ya karbi kudinsa.

Abu na goma sha daya: in mai sayarwa ya sai da wani abu sai dai bai karbi kudinsa ba kuma bai ba da abin sayarwar ba a kan sai mai saye ya kawo kudin to ciniki ya lizimta amma mai sayarwar ya samu ya sayar bayan kwana uku, kuma mai sayarwar ya samu ya bata cinikin in wanda ya saya bai kawo kudin ba, bayan kwana uku amma wannan yana faruwa ne in har ba su yi wani wa adi ba, wanda zai jira shi amma in sun yi wa’adi to wajibi ne ya jira shi zuwa wa’adin, ko da ya fi kwana uku amma in ba wata maganar saurara ko jira to mai sayarwa ya samu ya sai da abinsa daga lokacin da bai ba da kudinsa ba.

T: Idan a kai ciniki bashi ya halarta?

A: E ya halarta amma da sharadin an kayyade masa lokacin biya, wanda ba dadi ba ragi amma ba’a yin wa’adin bashi da lokaci wanda yake bai fita sarari ba, kamar a sanya lokacin girbin amfanin gona shi ne lokacin biyan bashi, to idan aka yi haka ciniki ya baci, domin wannan wa’adin bai da iyaka sananniya.

T: Idan lokacin biyan bashi ya yi amma sai kuma suka yi yarjejeniya kan su kara masa lokaci tare da karin wani kudi a bakin hakan shin yin hakan ya halarta.

A: Bai halarta ba domin ba kari ba ne (wato kudin ruwa).

Kuma riba haramce, kamar yadda ya zo a cikin Alkur’ani mai girma.

“ALLAH YA HALA-TA KASUWANCI YA KUMA HARAMTA RIBA”:- Wani lokacin mai saye da mai sayarwa sukan yi yarjejeniya daya ya ba da alkama kilo dari [100] dayan shi kuma ya saya da alkama kilo dari da hamsin [150] ya matsayin wannan ciniki yake?

- Wannan yana daga nau’i na riba don haka haram ne.

T: wani lokacin kuma su kan yi yarjejeniya a kan daya daga cikinsu ya sai alkama kilo dari [100] dayan kuma ya ba da alkama kilo dari da dinare hamsin?

Ya matsayin wannan yake?

A: Shi ma dai kuma wannan cinikin riba ne kamar yadda ka sani kuma riba haram ce.

Sai idan an kara a kan daya alkamar wani abin kudi kamar tawul da nufin cewa alkama da ke bari daya yana bakin tawul, sannan dinare hamsin yana bakin sauran alkama da ke bari na biyun- to a nan babu riba kuma ciniki ya inaganta.

T: Ta wacce hanya nake iya gane wannan muamalar riba ce domin in nisace ta?

A: An shardanta wasu abubuwa guda biyu kafin riba ta tabbata cikin mu’alar da za a biya take ba bashi ba.

Na daya:- abin da za a yi musanyen nasa ya zamanto wanda za a auna ne da kwano ko da mizani kamar alkama ko sha’ir ko adas ko shinkafa ko kayan marmari ko zinare da azurfa kai da dukkanin abin da ake iya aunawa da sikeli ko kwano.

Abu na biyu:- abin da za a yi musanyen nasa su zamanto daga jinsi guda yake.

T: Idan mu’amala ta kasance bisa bashi shin wayan nan abubuwa guda biyu da suka gabata sai sun tabbata kana muamala ta zamo riba?

A: Sam sam ba haka ba ne riba takan iya tabbata ba da su ba kamar yadda yake cikin wurare guda biyu masu zuwa.

Na daya:- abubuwan da za a yi musanyen nasu ya zamanto wanda za’a iya aunawa ne da kwano ko da sikeli sai dai kuma ba jinsun su daya ba kamar sayar da kilo dari na shinkafa da kilo dari na alkama amma sai karshen wata za’a ba da alkamar.

Abu na biyu:- musanyen ya kasance ba daga abin da ake aunawa ba ne sai dai kuma jinsinsu daya tare da kari a ciki kamar sayar da goruba goma da goruba goma sha biyar sai karshen wata za’a karba.

T: To yaya wannan musanyen idan ya kasance cikin abun da ake sayar da shi da kirge ne ba da awu ba kamar kwai ko kuma wanda ake sayarwa da awo na fadi kamar yadi da makamantansu yana halatta a yi cinikinsu da kari in har za a yi cinikinsu take?

A: Ya halarta a sayar da su da kari kamar a sayar da yadi mita talatin a ba da yadi mita arba’in in har take za’a yi cinikin kamar yadda ya halatta a sayar da kwai guda talatin da kwai guda arba’in in har take za’a bayar.

T: Yaya aikata haka cikin cinikin zinare?

A: Yin haka bai halatta ba domin zinare yana daga abin da ake aunawa.

T: Yaya cinikin zinaren da aka kera shi a saye shi da kari fiye da zinaren da ba a kera ba kamar yadda ake yi a yau.

A: Wannan haram ne domin kuwa riba ne, sai dai inda aka kara wani abu a kan zinaren da kyansa ya gaza na dayan  kamar yadda ya gabata?

T: Da nau’in alkama zai saba kamar a sayar da alkama kilo dari mara kyau da kilo casa in mai kyau ko a sayar da  shinkafa kilo dari mai kyau da shinkafa kilo dari da ashirin mara kyau mene ne hukumci?

A: Hakan bai halatta ba domin kuwa riba ne sai dai idan aka hada da wani abu kamar inda ya gabata.

T: Da za a sayar da kilo dari na alkama a bakin kilo sabain na shinkafa yaya hukuncinsa?

A: Ya halatta idan a take za a biya wato ba bashi ba.

Saboda jinsunsu ba daya ba ne. A nan yana da kyau a gane cewa alkama da sha’ir dukkaninsu jinsi daya suke a babin riba. Don haka bai halatta a sayar da kilo dari na alkama a bakin kilo dari da hamsin na sha’ir ba idan dai shi kadai ne. Hakana dabino dukkaninsa jinsi daya ne ko da wani iri ne. Saannan alkama da garin alkama da burodi da aka yi da alkama dukkansu jinsi daya ne. Haka kuma kindirmo da madara da cuku su ma daga jinsi daya suke idan daga nauin dabba guda ne. Danyan dabino da busasshe da abincin da aka yi daga dabino su ma jinsi daya suke, domin kuwa duk abincin da aka yi shi daga wani abu to yana jinsi daya da asalin abin da aka yi shi daga gare shi, wannan ka ida ce ta dindindin.

- To akwai wani naui kuma na riba da ake kira ribar bashi.

T: Ya kuma ake gane ribar bashi?

A: Rubar bashi ana gane ta ne inda mai ba da bashi yake dada wani abu ga mai karbar bashi kamar ya ba da bashin dinare dubu bayan wani lokaci a dawo masa da dinare dubu da dari daya yin hakan haram ne bai halatta ba ga mai karbar bashin da kuma mai bayarwa.

T: Ribar bashi shi ne a ba da bashi da ruwa to idan kuma ba ruwa a kan bashi fa?

A: Ba wa mumini bashi ba tare da yi masa kari ba yana daga cikin muhimman abubuwan da ake so na gaya maka wannan in ba ka manta ba musamman ba da bashi ga mabukata an samo hadisi daga Manzon Allah (S.A.W.A) yana cewa:” dukkanin mutumin da ya ba wa mumini bashi ya kuma saurare shi har zuwa lokacin da ya sami damar biya dukiyarsa za ta kasance cikin karuwa kuma mala’iku za su dinga yi masa salati har zuwa lokacin da za’a dawo masa da kudinsa.”

An karbo daga Imam sadik (A.S) yana cewa:- an rubuta a kofar aljanna sadaka tana da lada goma amma bashi yana da lada goma sha takwas.

T: Wannan shi ne magana kan bashi madalla da abin da ka fada kuma zan yi farin ciki da za ka gaya min wani bangare daga cikin hukumcin kamfani na hadin gwiwa domin dan uwana yana so su bude kamfani na hadin gwiwa da shi da abokinsa cikin harkar kasuwancinsu.

A: Bude kamfanin hadin gwiwa halas ne tsakanin mutane guda biyu masu hankali wayanda suka balaga bisa zabinsu ba wayanda aka yi wa dole ba muddin siffa ta wauta ko dabaibayi na bashi bai katangaye daya daga cikinsu ba.

Bayan haka sai babana ya ci gaba da cewa:- harka ta kamfani ana iya kulla ta ta bangarori daban daban kamar irin kamfanin da ake yi wa take a yanzu da [kamfanin izini] to irin wannan kamfani dukiyar da take kashin bayansa tana fitowa ne daga bangarurruka guda biyu ko fiye da suka hada gwiwa din saidai kuma dukiyar a gwame take wato an hada ta a wuri guda babu wanda ya ware nasa a ayyane, to irin wannan kamfani a kan iya fita daga cikinsa duk lokacin da aka so muddun ba zai janyo cutuwa ba. Idan dayansu ya fita to bai halatta ga sauran su yi amfani da wannan dukiya da aka yi tarayya a kaiba. Sannan akan raba riba da hasarar irin wannan ne kowannen su gwargwadon kudinsa.

T: Da abokan kasuwanci za su yi yarjejeniya akan ribar daya daga cikinsu ta fi yawa domin shi yake yin aikin ko kuma domin aikinsa ya fi yawa ko kuma don wani abu daban yin hakan ya halasta?

A: Irin wannan yarjejeniyar ta halarta.

T: Da wani abu zai bata a hannun wanda yake yin aikin yaya kenan?

A: Abokin aiki amini ne ba ya biyan abin da ya ba ta a hannunsa muddin bai yi zalunci ko sakaci ba.

T: A yanzu akwai wata irin mu’amala da mutane ke yi wacce take kama da’a kira ta hadin gwiwa mutum ya dauki kudi ya ba wa wani don ya yi kasuwanci su raba ribar ya matsayinta yake?

A: Irin wannan mu’amala ta inganta in har akwai yarjejeniya a tsakaninsu kana kuma suna da cikakken hankali kuma sun balaga sun kuma yi hakan bisa zabinsu da sharadin mai dukiyar bashi bai dabaibaye shi ba ta inda dukiyarsa ma ta zamo rabon wasu ba tasa ba, wannan ma’amala ita ake kira mudaraba.

T: Yaya kuma shi wanda zai yi aiki in bashi ya dabaibaye shi?

A: Ya halatta ya yi aikin ko da yana dabaibaye da bashi ne in har yarjejeniyar aikin ba ta lizimta masa yin amfani da dukiyarsa wadda bashi ya dabaibaye ba.

Yana kuma halatta ga mai dukiyar da kuma wanda zai yi aikin su ba ta yarjejeniyar kafin fara aikin ko kuma bayan fara shi hakanan kuma kafin tabbatar ribar ko bayan tabbatar ta, mai aiki ba ya biyan asara muddin bai yi zalunci ba ko sakaci.

T: To ya hukumci yake in mai dukiyar ya kafa sharadin cewa dukkanin asara tana kan mai aiki?

A: Wannan sharadi ingantacce ne idan har mai dukiyar ya yarda dukkanin ribar da aka samu ta mai aiki ce shi bai da wani kaso a cikinta.

T: Yaya kuma idan suka sa sharadin su raba asara?

A: Irin wannan sharadin batacce ne sai inda aka kafa sharadi ga shi mai aikin cewar idan an yi asara zai mai da wata daga cikin dukiyarsa ko kuma zai biya duka daga kudinsa to bisa wannan sharadi ya zama wajibi ya cika abin da suka yi yarjejeniya a kansa.

T: Yaya idan suka sami sabani daga baya a kan yawan kason da mai aiki zai dauka shi mai dukiya ya ambaci kason da bai kai wanda mai aiki zai dauka ba kana shi mai aiki din bai da sheda?

A: Fadin mai dukiyar shi ne abin dauka don haka shugaba na musulunci zai yi amfani ne da fadin mai dukiya yayin da aka kai masa kara muddin dai mai dukiyar ya rantse kana wani bakon abu bai bayyana ba wanda yake sabanin zahiri.

T: Yaya za a yi wani abu ya baiyana wanda yake sabanin zahiri?

A: Misalinsa shi ne da mai dukiyar zai yi da’awar ladan aikin mai aikin kasa da yanda aka saba kamar ya ce ladansa shi ne ya dauki kaso daya cikin kaso dubu [1000] na ribar da aka samu shi kuma mai aiki ya yi da awar abin da ya fi haka bisa yanda aka saba bayarwa.

T: To yaya idan mai aiki ya ce dilar da ya sayo ta ba ta ko kuma ya yi asara ko kuma bai ci riba ba mai dukiyar ya musanta haka a nan fadin wa za’a dauka?

A: Za a yi amfani da fadin mai aiki ne bayan an kai kara wurin hakimin musulunci muddin dai bayanin nasa bai saba wa zahiri ba kamar ya ce gobara ta cinye dilar amma ba ta ci sauran kayan da suke daure ba tare da dilar.

T: Da mai dukiya zai yi da’awar mai aiki ya ha’ince shi ko kuma ya yi sakaci  maganar wa za’a dauka?

A: A nan ma maganar mai aiki za’a yi amfani da ita lokacin da aka kai kara wurin hakimi na musulunci shi ma da irin sharadin da ya gabata.

T: A wani lokaci mutum ya kan wakilta wani ya tsaya a matsayinsa kan wani aiki da ya kamata a ce shi ya yi kamar ya wakilta shi sayar da gidansa ko filinsa ko abin da yai kama da haka shin irin hakan na da wani sharadi nasa daban?

A: E sharadi ne ga wakili da kuma wanda ya wakilta shi su zamo masu hankali masu kuma nufin aiwatar da wakilcin bisa zabinsu ba wayanda aka yi wa dole ba kamar yanda yake ga wanda zai wakilta waninsa ya kasance baligi ne shi sai dai cikin abubuwan da yaro mai hankali ma ya kan iya yi.

T: Shin akwai wani lafazi kebantacce wanda aka ware domin kulla wakilci?

A: Sam sam ba wani lafazi da aka ware ko wata siga wacce aka sanya domin yin wakilci don haka dukkanin abin da aka aiwatar na daga fadi ko aiki ko rubutu yake nuni zuwa wakilci sun isa kana wakilci yana baci da zaran wani daga cikin biyun ya mutu.

T: Wani lokaci mutum ya kan ba da hayar gidansa ko kantinsa ko makamantansu ko kuma ma ya ba da hayar kansa ga leburanci ko kwadago ko dinkin tela to mene ne hukumcin wannan haya?

A: A karbi haya daga mamallakin gida ko wakili ko waliyyi ta inganta amma ingancinta yana tabbata ga wanin wadannan lokacin da wani daga cikin wadannan ya ba shi dama daga ba ya. Abin da ake lura da shi ga mai karbar haya da wanda zai bayar su kasance wayanda suka balaga kuma masu hankali kana bisa zabinsu ba wayanda aka yi wa dole ba muddin dai bashi bai dabaibaye dukiyar daya daga cikinsu ba amma yana halatta mutumin da bashi ya dabaibaye shi ya sanya kansa cikin aikin leburanci kana ana lura cikin abin da za a bayar da hayarsa kamar guri ya kasance an yi masa iyaka kana wanda zai karbi hayar sai ya gan shi ko kuma ya san shi ta hanyar siffata wasu alamunsa kana ya zamo wanda ya ba da hayar yana da damar mika shi ga wanda ya karbi hayar kuma kasantuwarsa karkashin wanda ya karbi haya ya gamsar kuma ya  kasance wanda ya karbi hayar zai iya amfani da shi bisa manufar hayar tare da wanzuwar abin  kuma amfanin ya zamo na halas domin bai halatta’a karbi hayar guri don sayar da giya ba ko kuma makamanciyarta na daga abubuwan haram.

T: Shin akwai wani lafazi da aka aje domin bayar da haya?

A: Ba wani lafazi da aka sanya don bayar da haya don haka duk wani abu da aka aikata wanda yake nuni da karbar haya ya isa, don haka nuni wanda yake fahimtar da karbar haya ko bayarwa ya isa ga mutumin da yake kurma.

T: Idan mutum ya karbi hayar gida ko wani wuri sai mamallakin wurin ya kafa masa sharadin cewa shi kadai ya yarda ya zauna a gidan ko ya yi amfani da shi to ya halatta ya ba da hayar wurin ga wani?

A: Sam bai halatta ba.

T: To yaya kuma idan bai kafa masa sharadin komai ba?

A: In har bai kafa masa sharadin komai ba yana da damar da zai bayar da shi haya ga waninsa da sharadin kada ya bayar da hayar sama da yadda ya karba sai in har yai masa wasu gyare gyare kamar fenti wannan fa in abin da ya kar bi hayar tasa gida ne ko ko jirgin ruwa ko shago ko makamancinsu na daga gundarin abin da ake karba haya haka ma guraren noma. Daga nan ne babana ya ci gaba da cewa haya ba ta inganta har sai an iyakance mata lokaci don haka duk wanda ya ba da hayar gida ya zama lallai ya iyakance masa lokaci hakanan wanda ya ba da hayar wuri da sauransu.

T: Ba ni musali kan hayar da ba’a yi wa iyaka ba kana ita ba ta inganta ba?

A: Da mai gida zai ce da wanda ya ba wa haya na ba ka hayar gidana kan dinari dari [100] ko wanne wata Izuwa shekarun da za kai, irin wannan hayar ba ta halatta ba. Hakanan da mai gida zai ce da dan haya na ba ka hayar wurina kan dinare hamsin wannan watan dukkan iya zaman da kuma za ka yi bisa wannan lissafin yake.

- To watan farko ya inganta amma ragowar zama bai inganta ba.

Hakan in mu amalar tasu ta kasane da sunan haya suka yi ta amma su kan iya warware wannan matsalar da wani yanayi daban wanda ya halatta, wanda nan wajen ba wajen ambatonsa ba ne.

T: Mene ne abin yi lokacin da mai gida ya ba da gidansa ga dan haya?

A: Ya zama lallai ga dan haya ya mika wa mai gida kudin hayarsa.

T: Mene ne hukumci in gida ya rushe a hannun dan haya?

A: In har dan hayar bai yi sakaci ba wajen kare gidan bai kuma yi wata barna wacce za ta kawo faduwar gidan ba to bai da wani laifi.

T: Yaya kuma idan mutum ya ba wa wani motarsa haya?

A: A nan ya zama lallai ne su iyakance hanyoyin da zai dinga amfani da ita, motar ta daukan kaya ce ko ta hawa ce ko kuma dukkansu ce ya zama lallai su iyakance hanyar yin amfani da ita, hakanan kuma cikin ragowar abubuwa lallai ne a tabbatar da yadda za’a dinga amfani da su.

T: Yaya hukumci yake idan mutum ya ba da hayar motarsa domin daukar naman da ba a yanka a kan hanya ta shari a ba domin a sayar da shi ga wayanda suke ganin halas ne a tare da su?

A: Ashe ban gaya maka ba kan cewar bai halatta a ba da hayar wuri ba domin sayar da giya to haka ma wannan ba ya halatta.

T: Da mai gida zai wakilta wani mutum ya samo masa leburori don su yi masa wani aiki bisa wani lada da ya ayyana musu sai wakilin ya dauke su aiki kasa da kudin da mai gidan ya bayar ya halaccinsa yake?

A: Bai halatta ga wakilin ya ci yan kan ba ya zama lallai ya mayar wa da mai gidan ragowar kudinsa.

T: Da mai gida zai dauki mai fenti domin ya fente masa gidansa ya kuma gaya masa kalar irin fentin da yake so da siffarsa amma sai mai fentin ya fente masa da wani daban to mene ne hukumcin wannan?

A: Sam sam wannan mai aikin bai cancanci ladan aikin ba.

        ·          Abin da ya rage in tambaye ka  haya da ake kira sarkufliyya.

- Ita irin wannan haya ana yin ta kan abubuwa daban daban, misali mamallakin abu ya ba da hayar wurinsa amma ya karbi wata dukiya a hannun dan hayar shi kuma dan hayar ya ci gaba da amfani da wurin yana samun kudi da shi, bayan cikar lokacin hayarsa bisa wasu kudi da zai dinga biya, duk shekara  ko kuma bisa daidai kudin da wurin ya cancanta, wato yanda aka saba ba da hayarsa a tsawon shekara.

-         To idan suka yi irin wannan yarjejeniya ta (sarkufliyya), a yayin nan ya halatta ga dan haya ya ci gaba da zama a gurin bayan cikar lokacin hayar, amma kuma zai ba wa mai gidan kudin da suka yi yarjejeniya a kai. Hakana ya halatta ga dan hayan ya ba da wannan hakkin nasa ga wani mutum daban, a bisa wani kudi da suka daidaita akai, kuma a cikin wadannan halaye biyu ba’a shardanta izinin mamallakin wurin ba ko kuma yardarsa, domin tun farko ya riga ya daidaita da dan haya kan cewa yana da hakkin ya ci gaba da amfani da wurin da kuma rike wurin bayan cikar lokacin hayarsa.

T: Da mutum zai ba wa wani mutum wani abu da sunan kyauta shin hakan yana da wasu sharadai na musamman cikin musulunci?

A: I akwai sharadai ana lura da cewa wanda zai ba da kyautar ya kasance mai hankali wanda yake ya balaga wanda kuma yake nufin ba da kyautar bisa son ransa ba wanda aka yi wa dole ba to in har haka ta samu wannan kyauta ta inganta haka nan ma kyautar mutumin da bai da lafiya cikin rashin lafiyar da ya mutu a cikinta tana inganta muddin dai yawanta bai wuce kaso daya cikin kaso ukun dukiyar da ya mallaka ba amma in har ta fi haka ba ta inganta sai da yardar magada, ita kyauta wani abu ne wanda ake kulla shi da fadin cewa ya bayar ga mai kyautar da kuma karba ga wanda aka yi wa kyautar amma dukkanin irin abin da yake yin nuni zuwa ga bayarwa da karba na daga aiki ko fadi ya gamsar, kana kuma yana daga sharadinta wanda aka ba din ya zama ya karbi abinsa in har dama can ba tana wurinsa ba ne.

T: Yaya idan kyautar tana wajen wanda ya yi ta wanda aka ba din bai karba ba?

A: Tana nan karkashin mulkin wanda ya ba da ita har zuwa lokacin da wanda aka ba zai karba matsawar wanda ya bayar din yana  raye daga lokacin da wanda aka ba ya karba ta zamo mulkinsa.

T: Yaya ake karbar gida idan aka ba da shi.

A: Daga lokacin da mai gida ya dauke hannunsa daga gidan ko kuma ya kwashe kayansa daga cikinsa kana ya danka shi a hannun wanda ya ba wa daga wannan lokaci karbar gida ya tabbata kyauta kuma ta inganta.

T: Yaya hukumci yake idan da mai kyauta ko wanda aka ba ya mutu kafin karbar ta?

A: Wannan kyauta ta baci za ta koma karkashin magadan wanda ya bayar.

T: Wani lokaci mutum ya kan sami wata haja ko wata dukiya wacce ba’a san mai ita ba sai ya tsince ta mene ne hukumcin wannan?

A: Akwai halaye daban daban a cikin irin haka.

Na daya:- ya zamo dukiyar da aka tsinta ba ta da wata alama wacce mai dukiyar zai iya siffata ta da ita to a wannan lokaci wanda ya yi tsintuwa din yana iya rike abin tsintuwa din don ya yi amfanin kansa da shi. na biyu:- wani lokaci abin da aka tsinta din yana da alama kana bai da tsada wato ya gaza dirhami na sharia wato kwaya 12.6 na azurfa to a wannan hali ba lallai ne ga wanda yai tsintuwa ba ya yi cigiya, sai dai kuma duk da haka ba zai ci ba sai yai sadaka da ita ga mabukaci.

Abu na uku dukiyar da aka tsinta din ya zamo tana da alama kana kuma kimarta ta kai dirhami guda ko sama da haka to a cikin irin wannan hali ya zama lallai ga wanda ya yi tsintuwa yai gaggawa zuwa ga cigiya daga ranar da ya tsince ta har zuwa shekara kuma yana zamowa lallai wuraren da mutane suke taruwa kamar kasuwa da dandali a nan ne zai yi cigiya domin a nan ne ake iya ganin za’a iya  samun mai ita.

T: Da kuma duk za a yi hakan sai a rasa mai ita?

A: Idan har wanda yai tsintuwar bai samu mai ita ba to idan ya tsince ta ne a cikin haramin Makka ne sai ya ba da ita sadaka da niyyar mai ita idan kuwa ya tsince ta ne a wani wuri daban a nan mai tsintuwar yana da zabi imma ya ci gaba da ajiyarta ga mai ita wanda in yai hakan yana da damar da zai yi amfani da ita idan an sami mai ita daga baya ya mayar masa wa imma yai sadaka da ita da niyyar mai ita, a ko wanne hali dai bai da damar ya mallake ta ta zama nasa.

T: Da abin da aka tsinta zai zamo kamar kudi yaya kenan?

A: In har za’a iya gane mai ita sabili da wata alama da take da ita na adadin kudin ko zamanin da aka tsince shi ko kuma wurin da aka tsince shi to ya zama lallai a yi cikiya da wannan alamar.

T: Da wani zai yi da a war wannan tsintuwa tasa ce mene ne abin yi?

A: Da za’a gano gaskiyarsa ya zama lallai a ba shi haka kuma in an siffata ta sannan sifar ta zamo dai dai da yadda tsintuwar take kana aka sami nutsuwa da maganarsa ya zama lallai a ba shi.

T: In har ba’a sami nutsuwar gaskiyarsa ba sai dai kawai ana zaton mai gasikiya ne mene ne abin yi?

A: Zaton yana da gaskiya ba zai sa a ba shi ba.

T: Wannan magana kenan kan hukumcin kudin tsintuwa yaya hukumcin kayan da aka kwata ko kuma dukiyar da aka kwata da zalinci?

A: Shi dai kwace yana daga cikin manya manyan zunubai wanda aka hana kuma ma’abucinsa ranar kiyama za a yi masa horo da mafi tsananin azaba an ruwaito hadisi daga Manzon Allah (S.A.W.A.) yana cewa dukkanin mutumin da ya yi kwacen taki guda na kasa ranar kiyama Ubangiji zai dora masa nauyin kasashe bakwai,” sannan ya zama wajibi wanda ya yi kwace ya mayar da abin da ya kwata zuwa mai shi gida ne ya kwata ko kuma kudi ne ko wani abu daban.

T: Idan ya mai da gidan ga mai gidan shi kenan bai da sauran zunubi?

A: Ina sai ya biya shi gwargwadon kudin hayar tsawon zaman gidan a hannunsa.

T: Ko da bai zauna a gidan ba?

A: Zai biya kudin hayar ko da bai zauna a gidan ba cikin wannan lokaci, domin kuwa ya yi wa mai gidan asarar wannan lokaci, da haka dole ne ya rama masa ita.

T: Yaya kuma in mutum ya kwaci gona kana ya shuke ta?

A: Ya zama dole ga wanda ya kwata ya kau da abin da ya shuka, cikin gaggawa tare kuma da biyan ladan iyakar zamanta a wajansa, gwargwadan yanda ake karbar hayar wuri, banda ma haka da a wajen kau da abin da ya shuka zai lalata kasar ta yanda zai rage mata kima to sai ya mayar da wannan kimar da ya rage mata, amma hakan sai in mai kasar bai yarda ba.

- Amma idan mai kasa ya yarda ya bar shukan da ya yi a bakin wani kudi da zai biya ko kuma kyauta to ba laifi. 

T: yaya kuma in abin da ya kwata ya bata ba dan ya yi ganganci ba?

A: Ya zam dole ya biya mai shi abinsa ya kuma mayar masa da madadin amfanin da ya yi da shi a wannan lokacin. Da kuma amfanin da ya hana mai kaya ya samu a jikin kayansa.

T: Ta wace hanya ake iya biyan?

A: Abin kwace naui biyu ne: na daya wanda yake da wahalar samun kamarsa, sai dai a mai da kimarsa wato kudinsa kamar saniya ko kuma tunkiya, na biyu wanda bai da wahalar samun kamarsa, kamar alkama ko shair, irin wannan ya zama wajibi ga wanda ya kwace su ya mayar da misalin su da sharadin kwatankwacinsa ne zai bayar, bai halarta ya ba da mara kyau ba, in har mai kyau ya karba.

T: Idan ka karbi kwacen wata dila daga hannun wanda ya fara kwatarta kana sai dilar ta bata yaya kenan?

A: Mai dilar zai nemi kowane daya ya so daga wadannan da su biya shi wanda ya kwace ta na farkon da na biyun da su mayar masa da kayan shi ko kuma  su biya kima amma da mai dilar zai nemi wanda ya kwata da farko da ya biya to wanda ya fara kwatar yana da damar da zai nemi na biyun da ya biya shi daidai kimarta da kuma mai dilar zai karbi hakkinsa wajen na biyun to shi ba dama ya koma wajen na farko ya karbi wani abu.

T: Idan mai dukiya ya san dukiyarsa na hannun wanda ya kwata mene ne abin yi?

A: Yana da hakkin da zai karbi kayansa daga gurin wanda ya kwata ko da ko da karfi ne sai ya ci gaba da fadin cewa da dukiyar mai kwace za ta fada  hannun wanda ya yi wa kwace ya hallatta ya rike ta madadin dukiyarsa muddun dai kimarsu daya ne.

T: To yaya idan kuma dukiyar wanda ya yi kwacen ta fi yawan kima (kudin) wanda aka yi wa kwace fa?

A: Duk da haka ya halatta ga wanda aka yi wa kwacen ya debi daidai dukiyarsa.

Daga nan ne abokin muhawara ya ce kafin muhawararmu ta kare a yau ina so na yi maka tambaya guda daya!.

Sai mahaifinsa ya ce:- ya tambayarka.

T: Sau da yawa na ga kana yin sadaka?

A: Haka ne sai dai ya’a kai ka gan ni duk da kokarin da nake na kada wani ya gan ni domin ita sadaka ta mustahabbi duk lokacin da aka ba da ita a boye ta fi falala a kan a ba da ita a sarari kan idon mutane, domin Imamu Ali bin Hussain (A.S) yana cewa: “sadakar da aka yi ta a boye tana kau da fushin Ubangiji”

T: Shin akwai wani abu da ake lura da shi cikin ba da sadaka?

A: Ana lura da nufin kusanci zuwa ga Allah a lokacin da ake ba da sadaka.

T: Shin tana da wani lokaci ne kebantacce?

A: Sam sam ba ta da wani lokaci kebantacce sai dai an so a ba da ita da duku duku domin hakan yana kau da sharrin wannan rana kana kuma an so a ba da ita farkon dare don shi ma yana kau da sharrin dare.  [Mualla ibn khanis] yana cewa Abu Abdullah (A.S) ya fito cikin wani dare lokacin an yi ruwan sama a lokacin yana neman masaukin Banu sa’ida sai na bi shi can sai wani abu ya fado masa sai ya ce bismillahi Ubangiji ka dawo mana da shi sai na je wurinsa na yi masa sallama sai ya ce da ni kai ne Mu’alla?

Sai na ce I Allah ya kara ma girma sai ya ce da ni yi lalube da hannunka duk abin da ka samu ka miko min shi ko da na laluba sai na sami burodi a zube sai na ci gaba da miko masa shi can sai na sami jaka guda ta biredi daga nan ne sai na ce da shi Allah ya sanya ni fansa gare ka in daukar maka mana sai ya ce a’a ni na fi ka cancantar dauka sai dai kawai ka biyo ni sai muka isa wurin da Bani sa’ida  suke sai muka sami wayansu mutane suna barci sai ya dinga sanya waina daya zuwa biyu cikin kayan kowannensu har muka kai kan na karshe kana sai muka juyo daga nan ne sai na ce da shi Allah ya kara maka nasara wayannan sun san gaskiya ne sai ya ce da ni da sun san gaskiya da sai mun hada musu da gishiri ai domin ubangiji bai halicci wani abu ba face yana da wani mai kula da shi wanda shi ne kuma yake ajiye shi sai dai sadaka kawai domin ita sadaka ubangiji ne da kansa yake bin al’amarinta kuma ya ce mahaifina ya kasance idan ya yi sadaka da wani abu sai ya sanya shi a hannun wanda ya roke shi kana sai ya dawo da shi ya sumbace shi ya sansane shi sannan sai ya mai da shi hannun wanda zai ba wa domin ita sadaka tana fara zuwa ne tafin ubangiji kafin ta kai ga hannun wanda za’a ba wa.

T: Da wannan kissar zan fahimci sadaka na da falala mai girma ne?

A: I akwai ruwayuyyuka daban daban wayanda suka kwadaitar kan sadaka ya zo cewa:- sadaka magani ce ga mara lafiya kana tana ture bala’i wanda ya nufo mutum tana kawo arziki da ita ne kuma ake biyan bashi tana kau da mummunar cikawa da cuta kai har zuwa inda ya ambaci abubuwa guda saba’in munana wanda sadaka take karewa. Sai dai kuma duk da haka da irin wannan falala da sadaka take da shi yalwata wa iyali ya fi ta falala kamar yanda yin sadaka ga makusanci wanda yake mabukaci shi ya fi a bisa waninsa kamar yanda kuma sadakar da ta fi ko wacce falala ita ce sadaka ta dan uwa na zumunci. Wanda ya nuna maka gaba.

T: Dan uwa na zumunci wanda nake gaba da shi?

A: I man ta fi sai dai abin da ya fi sadaka falala ba da bashi hakika ba da bashi ya fi sadaka falala kamar yanda ka ji cikin ruwayar da ta gabata.              

 

عنوان الکتاب