MUHAWARA KAN KHUMUSI |
||
|
A nan ne abokin muhawara ya ci gaba da cewa yau babana ya shiga dakin muhawara, yana dauke da al Qurani a hannunsa, fuskarsa kuma na cike da kwarjini da ya zo zai zauna a gabana sai ya sunkuyar da kansa kana ya sumbaci al qur ani mai girma kana sai ya miko min shi a lokacin da na karbe shi na rike shi da hannuwana na sumbace shi sai na ji nutsuwa a tare da ni, take sai babana ya ce dan: bude Al kur’anin ka karanta farkon juzu, i na goma in ji. · A nan ne sai na bude al qur'ani juzui na goma na karanta ta'awizi kana na karanta fadin Allah madaukaki: “kuma ku sani abin da kuka samu na ganima to lallai ne Allah yana da khumusinsa kuma da manzo da makusantansa da kuma marayu da wanda basu da shi da matafiyi idan kun kasance kun yi imani da Allah da abin da muka saukar akan bawanmu ranar rabewa ranar da jama a biyu suka hadu” A nan ne babana ya tsayar da ni ya ce maimaita min wannan ayar na ji sai na kara maimatawa. - zuwa wurin da Allah yake cewa: khumusinsa na ga Allah da ma aiki da makusanta da marayu da miskinai. · Sai ya ce da ni ya isa ya isa, kana sai na ji yana maimaitawa a cikin ransa :[ku sani abin da kuka samu na ganima daga wani abu to lallai Allah yana da khumusinsa] daga nan ne ya dago idonsa ya dube ni ya ce min Allah madaukakin sarki ya ce: [ku sani] shin ka san cewa khumusi wajibi ne? Take sai na ji nutsuwa ta kama ni tare da razani sai na ce masa, I na sani, na sani, daga nan ne sai na ga ya tashi ya dauko wani, littafi da ke kusa da shi wanda ake kira [al wasa'il]. Koda na duba bangonsa sai na ga sunan wanda ya yi shi [Muhammadu bn hasan al Hurri al amili] sai yace da ni budo babin khumusi ka karanta, sai na budo babun khumusi na karanto masa hadisan da aka ruwaito kan khumusi daga manzon Allah da Imamu Ali, Imamu Baqir da Imamu sadiq da Imamu kazim (A.S) dangane da khumusi, yana daga cikin hadisin da na karanta masa wanda wani mutum ake kira lmranu bn Musa ya ruwaito, yana cewa na karanta ayar khumusi gaban [Musa bn Ja'afar] (A.S) sai ya ce: [abin da yake na Allah ai na manzo ne abin da yake na manzo namu ne Ahlul Bait] sannan sai ya ce (A.S) ubangiji ya sanya sauki cikin arzikin muminai. A cikin kowanne dirhami guda biyar su sanya daya ga Ubangijinsu kana su ci kaso hudu halal a tare da su, a cikin wani hadisin da wani mutum ya ruwaito wanda ake kira da suma'a, ya ce na tambayi Abal Hasan akan khumusi sai Abul Hasan ya ce khumusi yana samuwa ne cikin dukkannin amfanin da suka samu mai yawa ko kadan. An samo wani hadisin daga muhammad ibn Hasan al ash’ari, ya ce wasu daga cikin abokanmu sun rubuta wa Abu Ja’afar cewa, ya ba su labari akan khumusi. Suka tambaye shi cewa ana fitar da khumusi ne akan dukkannin abu mai yawa ko kadan? Kuma kowane ma aikaci ne ke fitarwa? Yaya kuma ake fitar da shi? Sai abu Ja’afar ya rubuta musu yana cewa khumusi ana fitar da shi ne bayan abin da aka kashe, a lokacin da na kare karanta wannan hadisi sai na tambayi babana ina mai ce masa: cikin muhawarar da muka yi kan sallah ka ce kada na yi sallah cikin tufafin da khumusi ya rataya amma ba’a fitar ba, kana na kuma ce masa: ka ce min cikin muhawarar hajji cewa na tsarkake dukiyata da fidda khumusi da zakka muddin tana tattare da hakkin zakka ko khumusi kafin na yi aikin hajji da dukiyar, yanzu ya zama wajibi kenan kaina na fidda khumusi cikin dukkanin dukiyata ko kuwa? sai mahaifina ya kada baki ya ce khumusi yana wajaba ne cikin wayannan abubuwan, na daya ganimar da musulmi suka samo ta a yaki, daga dukiyar da ake iya daukarta ko wacce ba a iya daukarta kamar kasa a yakin da aka yi da kafirai wanda yakarsu ya halatta. Na biyu abin da aka samoshi daga ma’adanai misalin azurfa ko zinare ko karfe ko ashana da makamantansu haka kuma ana fitar da shi cikin fetir da kuza bayan an fitar da wahalhalun da aka sha wajen fitar da su kana kuma da sharadin kimar abin da aka samu ya kai nauyin tataccen zinare goma sha biyar ko sama da haka wanda ake hulda da shi. Na uku ana fitar da khumusi cikin tsuntuwar da aka yi a karkashin kasa da sharadin abin da aka tsinta din ya kai nauyin tsaftataccen zinare goma sha biyar, ko kuma nauyin azurfa dari da biyar, wanda ake hulda da su. Bayan an fitar da kudin da aka kashe wajen samo abin. Abu na hudu tsintuwar da’aka yi ta a kasan kogi ko kuma babbar korama, na daga lu’ulu’u ko murjani ko makamantansu in har sun kai kimar zinare. Abu na biyar dukiyar halal wadda take cude da ta haram, a wasu halaye. Abu na shida ribar da aka samu a shekara ta hanyar kasuwanci ko aikin hannu ko kyauta ko noma ko kuma dukkan wani aiki har ma cikin ladan leburanci ko kuma albashi. Karin bayani a kan haka, ma’a nar wannan shi ne cewa ya zama lallai a fitar da khumusi daga ribar da aka samu a kasuwanci? Amsa shi ne ba ribar da aka samu a kasuwanci kadai ake fitar wa da khumusi ba, har ma cikin dukkan amfanin da aka samu, koda waye ke samun amfanin. Tambaya ita ce yaya dan kasuwa zai iya lissafa ribarsa da ya ci wacce zai fitar wa da khumusi? Dan kasuwa yana lissafa dukkanin dukiyar da take tare da shi tare da kudin da ke hannunsa bayan cikan shekara da fara kasuwancinsa. Amma an yi rangwame kan wasu ababe. (1) Asalin uwar kudin. (2) Kuma abin da ya biya wutar lantarki da tarho da ladan da ya biya na sifiri da kuma abin da ya biya na hayar kanti da harajin kasuwa da makamantansu. (3) Kana kuma da abin da ya kashe, ma kansa da iyalansa tsawon shekara na harkar ci, da sha, da tufafi da mazauni da kayan da suke bukata, da magani da kuma bukatun yau’da gobe, wanda ya hado da biyan bashi da kyauta da wajibai, da harkar tafiya da biki da harkokin yau da kullum, wanda ya dace da shi muddin bai kai ga al mubazzaranci ba, idan duk ya cire wadannan kana abin da ya rage sai ya ba da khumusinsa. Wato ya ba da kashi ashirin daga cikin dari 20%. Misali in har dan kasuwa ya fahimci cewa yana da dinari dubu goma, wato kudin dake hannunsa ya kai wannan kimar, kana kuma dukiyar da yake da ita ta kai dinari dubu ishirin [20,000]. Don haka idan ya hada gaba daya zai zamo dinari dubu talatin [30,000], ya kuma san cewa jarinsa dinari dubu sha biyar ne a lokacin da ya fara kasuwancinsa kana ya yi amfani da dinari dubu wajen tarho da wuta da hayar kanti da sifiri kana ya kashe dinari dubu hudu a kansa da iyalinsa, cikin shekara, don haka ribar da za ta ragu bayan ya cire jarinsa wanda yake dai dai da dinari dubu goma sha biyar kana ya cire abin da ya kashe na tarho da kudin hayar kanti da sifiri sai ya samu abin da ya ragu shi ne dinari dubu goma wanda wannan shi zai fitar wa da khumusi, khumusinsa kuma shi ne dinari dubu biyu [2000], domin dubu goma idan an raba wa mutum biyar kowa zai sami dubu biyu shi ne gwargwadon abin da ya wajaba a bayar. 3000-2000=10000 ÷ 5=2,000. Tambaya daga wane lokaci ne ya kamata na lissafa ribar da na samu domin idan shekara ta yi na fitar mata da khumusi? Amsa daga ranar da ka sami riba in har ada ba wata sana’a da kake yi wadda kake rayuwa a kanta. Daga wannan rana ne za ka fara lissafi matsawar ba ka yi amfani da ita wajen harkar magani ko abinci ko tufafi ko tafiya, ba to bayan shekara ta zago. Sai ka fitar da khumusinsa. Amma idan ya zamo akwai wata sana;a ko aiki wanda kake rayuwa a kai to daga ranar da ka fara aikin za ka fara lissafin shekara. T: da zan sai tufafi na’ajiye shi ban sa ba har shekara ta yi zan fitar masa da khumusi? A: Za ka fidda khumusinsa. Kana ma dukkanin mai gida da mutumin da ya mallaki abu zai fidda khumusin kayai yakin da ya saya muddin bai yi amfani da su ba har shekara ta yi da kuma irin abin da ya yi saura na shinkafa da alkama ko gari da maiwa ko sukari ko fetir da gas ko shayi ko mayi da makamantansu. Ma’ana shi ne dukkanin abin da ya ragu bayan bukata wanda mutum bai yi amfani da shi ba shi ne zai fitar wa da khumusi? Amsa:- I wato tankade da rairaya zai yi don fitar da khumusin duk wasu kaya da suka ragu bayan bukatar ka ta shekara sai ka ba da khumusinsa ko kuma ka kimanta shi sai ka ba da kudi. T: Shin zan ba da kimarsa ne na ranar da zan fidda khumusinsa, ko kuwa kimarsa na lokacin da na saye shi? A: Kana fidda kimarsa ne ta kasuwa na lokacin da za ka fidda khumusinsa ba kimarsa ta lokacin da ka saye shi ba. T: Da za a ce ina da wani abin hannu wanda ban fidda khumusinsa ba shin wajibi ne in fitar masa da khumusi? A: Daga lokacin da ka ki fitar masa da khumusi bai halatta ka kara yin wani amfani da shi ba, sai in har shugaba na shari’a marja’I ya ga masalaha cikin ka yi amfani da shi to a nan ne za ka iya amfani da shi. T: Mutumin da ya rasu ana binsa khumusi bai ba da wasiya kan a fitar ba me magada ya kamata su yi? A: Ya zama lallai a kansu da su fidda khumusi daga cikin dukiyar da ya bari tun gabanin wasiyar da ya yi da kuma rabon gado, amma banda mai sabon Allah da ya mutu ba ya fidda khumusi, domin kayayyakin da ya bari yana halatta ga magajinsa mumini kuma magajinsa ba dole ba ne ya biya khumusin da ake bin sa.. Haka nan kuma dukkannin dukiyar da ta sami mumini daga mutumin da ba ya ba da khumusi kawai zai ci gaba da yin amfani ne da ita kamar yadda yake halatta gare shi ya yi amfani da dukiyar mutumin da ba ya fitar da khumusi muddin dai ya ba shi damar amfani da ita, domin cikin dukkanin wadannan muminin bai zamowa mai laifi laifin na kan wanda bai fidda khumusin ba muddin yana sane ya ki fitarwa. Kana sai babana ya yi shiru kadan cikin hanzari sai na ce:- dan kasuwa ko mutumin da ya mallaki gona ko ma aikata ko kuma ma aikaci ko mai leburanci ko dan makaranta ko makamancinsa mene ne abin da ya kamata ya yi in har ba ya fitar da khumusi? Ba ya kuma ganin kansa cikin wanda ya dace su fidda khumusi, bayan kuma shekara da shekaru yana samun riba da amfani daban daban, kana kuma ya mallaki gidaje ya sai kayai yaki da shimfidu kai da ma tufafi da kuma dukkanin abin da yake bukata, daga baya sai ya gano wajibi ne ya fidda khumusi daga cikin wannan dukiya da ya mallaka to irin wannan mutum yaya zai yi? - Ya zama wajibi a kansa ya fidda khumusin dukkanin wadannan abubuwa da ka ambata in har sun ragu bayan bukatunsa na shekara. Sai abokin muhawara ya ce da mahaifinsa ba ni misali akan abin da ka fada sai mahaifinsa ya ce duk gidan da mutum ya saya ba don ya zauna a cikinsa ba domin yana da wani gidan da ya dace da shi daban wanda yake zaune a ciki to lallai ne wancan gidan ya fitar masa da khumusi, haka nan kuma dukkanin wasu kaya na alatu da ya saya wadanda suke a zube ba ya amfani da su su ma wajibi ne a fitar musu da khumusi. Ya ci gaba da cewa ina kuma misalin gidan da ya saye shi cikin ribarsa ta shekara da nufin ya zauna a cikinsa ko kuma ya sai kayan alatu ya yi amfani da su ko abin da ya yi kama da haka. Da zai sai kaya ko gida da ribarsa ta shekara da nufin zama a gidan ko yin amfani da kayan to ba zai fitar musu da khumusi ba hakanan hukumci yake cikin makamantansu. Sai abokin muhawara ya kara cewa idan ya sai gida da ribarsa wacce ta taru shekara da shekaru kana ya hada da ribarsa ta wannan shekarar kamar yanda mutane da yawa suke aikata haka a zatona don haka sai ya zamo sun shigar da ribar wata shekarar cikin wata shekarar to yaya za’a fidda wannan khumusin bayan ya tare a wannan gidan? - Ya wajaba a kansa ya tambayi shugaba na shari’a wato marja’i ko kuma ya tambayi wanda yake a matsayinsa domin ya yi masa bayanin abin da ya fi kamata ya yi , amma abin da ya tabbata na ribar shekarun da suka gabata lallai ne ya fitar musu da khumusi cikin gaggawa. Idan ba zai iya bayar da khumusin ba tashi guda domin yin hakan zai iya sanya shi cikin tsanani ko kuma ba shi da damar fitarwa to me ya kamata ya yi? - Shugaba na sharia zai iya sarayar masa da shi ta hanyar ya dawo da khumusin kansa, wato mudawara, shi kuma ya dinga biya a sannu a sannu ba tare da yi masa lako lako ba ko barinsa kawai. Abokin muhawara ya kara da cewa yanzu dai ga shi muna zaune gida guda ni da kai bayan kai ka fidda khumusinka lallai ne ni ma sai na fidda khumusin? - I lallai ne ka fidda khumusi cikin ribar da ka samu ko da muna tare gida guda din muddin dai ka ci riba kana tare da ita har tsayin shekara ba ka bukaci yin amfani da ita ba. T: A matsayina na dalibi da zan yi aiki a cikin hutu na sami kudi kuma kai mahaifina ba ka karbe shi ba ka bar shi don na yi amfani da shi wajen sayen kaya da bukatuna shin lallai ne na fitar wa wannan ladan nawa khumusi? A: Idan ka yi amfani da shi cikin abin da ya dace da kai ya kuma kamace ka ba wani khumusi da za ka fitar amma da za ka sa shi gaba daya a banki ko wani sashinsa har zuwa shekara to lallai ne ka fitar wa da abin da ka ajiye khumusi. T: kwanukan da aka tanade su don ci da sha amma sai ga shi ana ajiye da su don ado to shin irin wannan amfani da ake yi da su don ado zai hana a fitar musu da khumusi? A: Idan har samuwarta a wajensa yana yin daidai da sauran jama’a makamantarsa abin nufi shi ne in har sauran jama’a ma suna yin haka kana rashin samuwarta tawaya ne a tare da shi to a wannan lokacin sai a sanya ta cikin abubuwan bukatarsa na shekara don haka ba zai fitar mata da khumusi ba. T: Kudin da mutum ya tara ya fitar masa da khumusi kana sai ya canja su zuwa wani kudi da nufin ajiya sai ga shi kimarsa ya nunku bayan shekara zai fitar masa da khumusi? A: Ba zai fidda khumusin kimar da ta dadu ba muddin yana nufin ajiye dukiyar ne. T: Wasu kayan abinci suna samun tallafi daga gwamnati domin haka farashinsu sai ya zama da sauki idan an kwatanta da irin yadda ake sayarwa a kasuwa to da mutum zai ajiye ta har tsayin shekara ba tare da ya yi amfani da ita ba idan ya tashi ba da khumusi shin zai lissafi kan farashin gwamnati ko kuma kan farashin kasuwa? A: Zai yi lissafi ne kan farashin kasuwa lokacin da zai fidda khumusi. T: wani yanki ne na kasa wani ya saye ta kamar yanda ya kamata har ma ya fara cin gajiyarta sai dai abin da yake rubuce a kan takarda sunan wani ne ta yadda wata rana zai iya da awar tasa ce har ya nemi raba shi da ita, to bisa wannan yanayi ya zama lallai ya fitar mata da khumusi ko kuma zai saurara ne har zuwa lokacin da ya zamo sunansa ne a rubuce a kan takardar mallakar wuri? A: Ya zama lallai ya fitar mata da khumusi a wannan lokacin in har sharadan khumusi ya tabbata a kanta, wato sharadan da muka ambata a baya. T: Kudin da hukuma take ba wa ma’aikaci bayan ya bar aiki [garatuti] shin zai fidda khumusinsa ne daga ranar da ya karbe shi ko kuwa zai saurara har sai ya shekara? A: Zai fidda khumusin abin da ya ragu bayan cikar shekara. T: To idan na fidda khumusi wa zan ba wa? A: Khumusi yanki biyu ne yanki guda na Imam Mahdi (A.S) ana yin amfani da ita cikin abin da yake tattare da yardar Imam tare kuma da samun izini daga marja’i mai cikakken sani ko kuma a ba da shi ga marja’in, daya yankin kuma ga talakawa da matafiya wadanda guzurinsu ya kare wadanda suke muminai dangin banu hashim kana kuma ana ba wa marayu wadanda iyayensu talakawa ne muminai na kwarai kana suna daga cikin muminai masu kiyaye addininsu da kyau. Abin da ake nufi da banu Hashim su ne mutanen da suke dangi da manzon Allah (S.A.W.A) ta bangaren uba har Izuwa ga [Hashim] kakan Annabi Muhmmad (S.A.W.A.). Wannan kenan, kuma lallai bai halatta a bayar da khumusi ba ga mutumin da wajibi ne ga ma abucin dukiyar ya ciyar da shi, kamar baba, maha ifiya, mata, da kuma ‘ya’ya, kamar yanda kuma ba ya halarta a ba da khumusi ga mutumin da zai yi amfani da shi ta hanyar da bai halatta ba, kai banda ma haka ana lura da cewar in an ba shi ba za a karfafa shi kan ya yi zunubi ba. Kamar yadda bai halatta a ba da khumusi ba ga mutumin da yake wasa da sallah ko yake shan giya ko aka san shi da aikin alfasha.
|
||