TATTAUNAWA KAN ZAKKA |
||
|
Babana ya fara da cewa: Zakka daya ce daga cikin rukunan nan guda biyar da aka gina musulunci akai, kana tana daga cikin wajiban addini wanda ba a taklidi a kansu, saboda muhimmanci mai girma da take da shi ne aka ruwaito a hadisi cewa: (Ba’a karban sallar mai hana zakka). Kana ya ci gaba da cewa: “Lokacin da aka saukar da ayar zakka wato, Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai (KA KARBI SADAKA DAGA DUKIYOYINSU KA TSARKAKE SU, KUMA KA TABBATAR DA KIRKINSU DA ITA) Sai manzon Allah (SAWA) ya umurci mai shelarsa da ya gaya wa mutane cewa: (Hakika Allah madaukakin sarki ya wajabta muku zakka kamar yadda ya wajabta muku salla) ya yi n da shekara ta zagayo sai Manzon Allah ya umarci mai shelan da ya gaya wa musulmai cewa: (Ya ku musulmai ku ba da (zakkar) dukiyarku kana a karbi sallarku). Daga nan sai ya umurci ma’aikata (masu karban zakka) don su karbo ta daga hannun mutane. Kana babana ya sake cewa: Wata rana manzon Allah yana cikin masallacinsa sai aka ji ya ce: “Tashi wane, tashi wane” har sai da ya fitar da mutane biyar, sai ya ce: “ku fita daga masallacinmu, ba za ku yi salla a ciki ba, don kuwa ba kwa fidda zakka”. Sannan babana ya ci gaba yana mai karanto min wani hadisi daga Imam Abi Ja’afar (a.s), alhali fuskarsa tana murtuke, inda hadisi yake cewa “Hakika Allah zai tashi wasu mutane daga kabarinsu ranar lahira, alhali hannayensu suna daure a wuyansu, ba za su iya aikata komai da hannayen ba, kana malaiku suna bin su suna aibata su aibatawa mai tsanani, kana suna cewa wadannan su ne suka hana alheri kadan daga alheri mai yawa, wadannan su ne wadanda Allah ya ba su… amma suka hana hakkin Allah Ta’ala daga cikin dukiyo-yinsu”. Sannan babana ya kara da cewa: Daga cikin abubuwan da na lura da su ya yi n da nake karanta littafin Allah madaukakin sarki shi ne cewa sau da yawa al-kur’ani ya kan gwama zakka da salla a cikin ayoyinsa masu girma, wanda haka yana nuna muhimmancinta ne a shariar musulunci. · Yayin da na tambayi babana dalilin zakka, sai ya amsa min da wannan hadisi na Imam sadik (a.s) inda yake cewa: “Lalle an sanya zakka ne jarabawa ga masu abin hannu kana kuma taimako ga fakirai. Da a ce mutane za su dinga fidda zakkar dukiyoyinsu da babu wani musulmin da zai zauna da talauci kuma da zai wadatu da abin da Allah ya wajaba a ba shi, da mutane ba su zama fakirai ba da ba su zamo mabukata ba, da ba su ji yunwa ba, kuma da ba su rasa tufafi ba face sai saboda zunuban masu dukiya, lalle hakkin Allah ne ya hana rahamarsa isa ga mai hana zakka… daga abin da ya mallaka”. Sai na tambaye shi: shin zakka wajiba ce a kan kowace irin dukiya? Sai ya amsa cewa: Zakka tana wajaba ne a kan wadannan abubuwa masu zuwa: Na Farko: cikin kudi wato zinare da azurfa amma da sharudda. Na Biyu: cikin alkama, sha’ir, dabino da zabibi shi ma da sharudda. Na Uku: cikin rakumma shanu, da tumaki da awaki suna da nasu sharuddan. Na Hudu: [cikin dukiyar kasuwanci] shi ma da nasa sharudda. T: To wadanne ne wadannan sharudda na kudi wato zinare da azurfa da ka ambata a cikin maganarka? A: Sharuddan su ne: 1- Yawan. Zinaren ya kasance ya kai miskali goma sha biyar to zakkansa shi ne (2.5%) kana duk lokacin daya karu da miskali uku to wajibi ne a cire 2.5% daga ciki a matsayin zakka. Amma azurfa kuwa dole ne sai ta kai miskali dari da biyar kana a cire 2.5% nata a matsayin zakka. Kana duk lokacin da ta karu da miskali ashirin da daya to wajibi ne a cire 2.5% daga cikinta a matsayin zakka. T: To idan yawan zinaren ko azurfan ya gaza wannan haddi da aka ambata fa? A: To zakka ba ta wajaba. 2- Su kasance sun shafe watanni goma sha daya sun shiga na sha biyu alhali suna cikin mallakar mutum. 3- Zinaren ko azufan su kasamce an buga musu kan sarki wato wadanda ake amfani da su wajen saye da sayarwa a halin yanzu. T: To ababen da ake yin su na zinare da azurfa da kuma kayan adon mata (warwaro, abin wuya etc) da aka yi daga zinare ko azurfa ko kuma wani yanki na zinare ko azurfa fa? A: Zakka ba ta wajaba a kansu . 4- Mai dukiya ya zama yana da ikon sarrafa dukiyan duk tsawon shekara guda cikakkiya, don haka zakka bata wajaba a dukiya da ba ta cika haka ba kamar wanda ya bata na wani lokaci. 5- Kamalar mai dukiyar na daga balaga da hankali, zakkar kudi bata wajaba ga dukiyar yaro ko mahaukaci. (Abu na biyu) na daga abubuwan da zakka ta wajaba a kansu su ne: Alkama, shair, dabino da zabibi, Zakka tana wajaba a kansu idan bayan bushewarsu suka kai sa’i dari uku wanda ya kusan yin dai-dai - kamar yadda aka ce-da kilogram 847 a takaice, to abin da ya wajaba a cire shi ne kamar haka: A- Idan har ka shayar da su ne da ruwan sama ko na kogi ko makamancinsu ta yadda shayar da shukan bata bukatan wata wahala, to a wannan hali zakkanta ita ce (10 %) kashi goma daga cikin dari. B- Idan ka shayar da su da hannu ko kuma wani abin ban ruwa kamar injin ban ruwa ko makamancin haka, to zakkarsu shi ne (5 %) kashi biyar cikin dari. C- Idan ka shayar da su a wani lokaci da ruwan sama kana a wani lokacin kuma da hannu ko wani inji to zakkarsu a wannan hali shi ne (7.5 %), sai dai idan daya daga cikin hanyoyin shayar da ruwa ya karanta ainun ta yadda ba a dagaro akai to a wannan hali sai ayi aiki da hanyar shayarwa da ya yi galaba. T: To idan abin da aka samu ya gaza sa’i dari uku bayan bushewarsa fa? A: Idan har ya gaza haddin da aka fada to babu zakka a kansu . T: Shin akwai wasu sharuddan kuma? A: Na’am… abin da aka samu din ya zamanto mallakar mutum ya yi n ratayar abin ga zakka, da ace zai mallaki abin bayan wannan lokaci ne to zakka bata wajaba akan wannan abu. T: To yaushe zakka take rataya akan wadannan kayan gona guda hudu? A: Zakka tana rataya ne a gare su duk lokacin da sunayensu ya tabbata a kansu wato duk lokacin da aka ce ya zama alkama ko sha’ir, ko dabino ko inabi. (Abu Na Uku) da Zakka ta wajaba a cikinsu su ne: tumaki da awakai, rakumma, shanu da bijimi maras kaho. An shardanta wadannan abubuwa wajen wajibcin zakkarsu: 1- Ya kasance adadinsu ya kai “nisabi”, shi ne kuwa wani takamaimen adadi da idan har suka kai shi to zakka tana wajaba a cikinsu. A rakumma shi ne: idan adadinsu ya kai guda biyar, to zakkarsu itace tinkiya, idan kuwa suka kai goma to zakkarsu ita ce tumaki guda biyu, idan suka kai goma sha biyar, to zakkansu ita ce tumaki guda uku, idan suka kai ashirin zakkarsu ita ce tumaki hudu, idan suka kai ashirin da biyar zakkarsu ita ce tumaki biyar, idan suka kai ashirin da shida zakkansu itace rakumar da ta shiga shekara ta biyu a rayuwarta, idan kuwa suka kai talatin da shida, Zakkarsu ita ce rakumar da ta shiga shekara ta uku na rayuwarta. Akwai wasu adadin da ba wadannan ba amma ba mu da lokacin ambatonsu a nan. A dabbobi (wato Tumaki da awaki): idan adadinsu ya kai arba’in to zakkar ita ce tinkiya daya, idan suka kai dari da ashirin da daya kuwa zakkarsu ita ce tumaki guda biyu, idan suka kai dari biyu da daya to zakkarsu ita ce tumaki uku, idan suka kai dari uku da daya to zakkarsu ita ce tumaki hudu, kana idan suka kai dari hudu ko fiye to zakkarsu ita ce a kowani guda dari za’a cire tinkiya guda daya, komai yawan da adadin ya kai. A shanu da bijimi kuwa idan adadinsu ya kai talatin to zakkarsu ita ce “tabi’a” wato maraki da ya shiga shekara ta biyu na rayuwarsa, idan adadinsu ya kai arba’in to zakkarsu ita ce “Musinna” wato wacce ta shiga shekara ta uku na rayuwarta na daga shanu ko bijimi. Babu zakka tsakanin nisabai guda biyu ko adadi guda biyu cikin rakumma, shanu da tumaki da awaki, idan har adadi ya karu akan “nisabi” to babu zakka a kansu har sai ya kai wani sabon nisabi. 2- Dabbobin su kasance sakakku wadanda suna kiwo ne a kasar Allah, amma idan daurarru ne wadanda mai su yake ba su abinci ko da kuwa na wasu lokuta ne a shekara to babu zakka a cikinsu [kana ba sharadi ba ne dabbobin su kasance wadanda ba a aiki da su, kenan zakka tana wajaba a kansu koda kuwa ana amfani da su wajen ban ruwa ko daukan kaya da dai, Sauransu na wani lokaci] da za a iya dogaro a kai. 3- Ikon mai su ko waliyinsa wajen sarrafa su cikin tsawon shekara cikakkiya, da za’a sace su na wani lokaci abin dogaro to zakka ba ta wajaba a kansu . 4- Su kasance sun shafe watanni goma sha daya suna mallakarsa har sun shiga na sha biyu. (Abu na Hudu) na daga abubuwa da [zakka ta wajaba a cikinsu shi ne: kudin kasuwanci]: wato dukiyar da mutum ya mallaka don niyyar kasuwanci don neman riba. To zakkarsu shi ne (2.5 %) idan sun cika waddannan sharudda masu zuwa: 1- Balagan mai su da hankalinsa. 2- Kaiwar dukiyan nisabi shi ne kuwa daya daga cikin nisaban zinare da azurfa, (koma ga nisabin kudi don karin haske). 3- Cikan dukiyan shekara cikakkiya daga lokacin da aka yi nufin neman riban ko kasuwanci. 4- Dauwaman niyyar neman riban tsawon shekarar, da a ce zai juya ya yi niyyar mallakarsu ko kuma ya kashe su don bukatun yau da kullum a cikin shekarar, to zakka bata wajaba a cikinsa. 5- Ikon mai abin wajen sarrafa su cikin shekara cikakkiya. 6- Ya yi neman da uwar kudin ko kari a kansa tsawon shekara. T: To idan na fidda zakkar a wa zan bayar? A: Za ka ba da zakka ne ga wadanda suka cancance ta su ne mutane kashi takwas amma da sharudda Allah yana cewa: (ABIN SANI KAWAI, DUKIYOYIN SADAKA NA FAKIRAI NE DA MISKINAI DA MASU AIKI A KANSU DA WADANDA AKE LALLASHIN ZUKATANSU, KUMA A CIKIN FANSAR WUYOYI DA WANDA AKE BI BASHI DA CIKIN TAFARKIN ALLAH DA DAN HANYA (MATAFIYI). FARILLA DAGA ALLAH KUMA ALLAH NE MASANI, MAI HIKIMA) T: Mene ne bambanci tsakanin fakiri da miskini? A: Fakiri da misikini su ne wadanda ba su mallaki abin da za su ci su da iyalansu na shekara guda ba kana kuma basu da wata sana’a da za ta kawo musu abincinsu da na iyalansu, amma halin miskini ya fi na fakiri muni. T: Su wane ne masu aikin zakka? A: Masu aikin zakka su ne: Wadanda Annabi (S.A.W.A.) ko Imam , ko shugaba, na shari’a (“Hakim al-shar’i”) ko naibinsa suka ayyana don karbo zakka da lissafinta kana da isar da su gare su ko wadanda suka cancance ta. T: Su wane ne “Mu’allafatu Qulubuhum”? A: “Mu’allafatu Qulubuhum”: su ne musulman da ake karfafa musuluncinsu ta hanyar ba su kudi, ko kuma kafirai don jawo su zuwa ga musulunci, ko kuma don taimakon da musulmai za su yi musu don kare kansu. A nan yana da kyau ayi nuni da cewa mai dukiya ba shi da iko wajen sarrafa zakka kan kashi biyun nan da suka gabata wannan aiki ne na Imam (a.s) ko na’ibinsa. T: To mene ne maanar cikin fansar wuya? A: Fansar wuya: yana nufin bayin da ake saye kana a ‘yantar da su. T: Su wane ne “al-Garimun”? A: “Al-Garimun”: su ne wadanda bashi ya yi musu yawa kana kuma ba za su iya biyan bashin ba, amma bashi da shari a ta yadda da shi. T: To Fi, sabilillahi fa? A: Fi, Sabilillahi, shi ne duk abin da aka sarrafa a hanyar alheri kamar ginin masallatai da gadoji da makamantansu [kana sarrafa wannan kashi ma yana bukatan izini daga “Hakim, al-shar’i”]. T: To “dan tafarki” fa? A: Dan Tafarki: shi ne matafiyi wanda kudinsa ya kare ba shi da hanyar samun bashin kudin dawowa ko kuma samunsa matsi ne gare shi [kana kuma ba zai iya sayar da wasu kaddarorinsa da suke garinsu ba ko ba da hayansu don samun abin da zai ishe shi komawa garin] to za’a ba shi abin da zai ishe shi komawa amma da sharadin cewa tafiyar ba ta sabon Allah bace. Wannan shi ne raba-raben wadanda suka cancanci zakka, koda yake an shardanta ga wanda za’a ba shi zakka daga cikin wadannan ya kasance mumini [kana kada ya zamanto mai barin salla ko mashayin giya ko kuma mai bayyanar da munanan ayyuka] kana kada ya zamanto daga cikin masu sarrafa zakkar cikin sabon Allah [kai kada ba shi zakkar ya zamo taimako ne ga sabo da kuma sa masa kwadayi kan mummunan abu ko da kuwa ba zai sarrafa ta wajen sabon Allah ba] Kana kuma an shardanta cewa kada ya zamanto daga cikin wadanda ciyar da su ya wajaba akan mai ba da zakkar kamar matansa, kana kuma kada wanda za’a ba wa din ya zamanto bahashime wato daga Banu Hashim. Domin yana halarta ne ga bahashime ya ba da zakkarsa ga bahashime dan’uwansa kawai. * * * * * |
||