GABATARWA

 

DA SUNANSA MAI GIRMA

 

An gama dubawa da tabbatar da cewa wannan littafi ya yi dai-dai da fatawoyin Ayatullah al-Uzma as-Sayyid Aliyul Husainiyul Sistani (Allah ya tsawaita ransa) a ofishinsa da ke Najaf- al-Ashraf ran 4 ga Rabi’u Awwal 1416 Hijriyya.

 

OFISHIN

AYATULLAH AL-UZMA

AS-SYYID ALIYUL HUSAINIYUL SISTANI

QUM


 

GABATARWA

 

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI

(ÑÈ ÇÔÑÍ áí ÕÏÑí * æíÓÑ áí ÇãÑí * æÇÍáá ÚÞÏÉ ãä áÓÇäí * íÝÞåæÇ Þæáí)

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabammu Muhammad da tsarkakan mutanen gidansa, kana bayan haka:

Hakika na so kana na yi kokarin wannan rubutu nawa kan fatawoyi masu sauki ya zamanto cikin sauki don ya taimaka wajen tattaunawa a wannan zamani tsakanin marubuta da masu karatunsu, kana mun yi iyakacin kokari don magance abubuwan da suke da wahala na nassosin fikihu da abubuwan da basu fito fili ba don saboda masu karatunsa, masu bukatuwa da shi kana da masu aiki da shi.

Mun zabo hukumce-hukumcen da suke da muhimmanci kana kuma mutum yake da bukatuwa da su. Kana duk wanda yake son karin bayani sai ya koma ga littattafan da. Suka yi cikakken bayani na daga littattafan fikihun musulunci da kuma “Risalatul Amaliyya” (littattafan da marajiai Sukan rubuta kan hukumce-hukumcen fikhu don aiki da su).

(Kana mun yi) kokari nan da can don dinke barakar da ke zuciyar mai karatu na tsakanin ilmin fikhu da “al-Akhlaq”... kana tsakanin aikin da wajibi ne ya aikata da kuma ainihin ruhin aikin da ya wajaba ya aikata.

(Kana mun) rarraba wannan aiki zuwa kashi uku. Kashi na farko ya kunshi Ibadoji ne, muka sanya salla wacce ita ce «tushen addini wacce in an karbe ta to an karbi sauran ayyukan (mutun) ma kana idan an Jefar da ita to sauran ayyukan ma za’a Jefar da su» a matsayin mafificiyar ibada.

Domin (sallah ba ta yiyuwa sai da tsarki) don haka ne tushen bincike ya sanya kafin Isa zuwa ga Salla da in fara- bayan magana kan Taqlid- da abubuwan da suke kawar wa jiki da tsarkin da yake da shi na daga “najasosi”daban-daban, kana kuma in ambaci abubuwan da suke dawo wa jiki da tsarkin da ya rasa na daga (masu tsarkakewa- Mudahirat-) daban-daban ita ma, sannan in har na gama hakan sai in Isa zuwa ga Salla kana in Sallace ta kamar yadda ya kamata wanda yake tsaye gaba ga ubangijinsa cikin tsarki da Ikhlasi ya aikata.

Kana bayan Salla in wuce zuwa ga abubuwan da suke bukatuwa da tsarki kafin a aikata su kamar azumi ko hajji.

Kana kashi na biyu na kebe shi ne kan harkoki na kudi kamar saye da sayarwa, haya da kuma kasuwanci na hada gwuiwa da sauransu.

Kana na koma na kebe kashi na uku kan halayyan dan adam na daga aure, shika, bakance, alkawari, rantsuwa da sauransu.

Kana na ci gaba da tattaunawa kan al’amarin umurni da abu mai kyau da hani da munana, kana na cika wannan aiki da wasu maganganu guda biyu na gaba daya.

Don haka a bisa wannan tsari za’a iya tsara darussan kamar haka:

Tattaunawa kan Taqlid, Tattaunawa kan najasosi, Tattaunawa kan Tsarki, Tattaunawa kan Janaba, Tattaunawa kan Haila, Tattaunawa kan jinin Haihuwa, Tattaunawa kan Jinin Istihala, Tattaunawa kan Mutuwa, Tattaunawa kan alwala, Tattaunawa kan Wanka, Tattaunawa kan Taimama, Tattaunawa kan Jabeera, Tattaunawa kan Salla, Tattaunawa kan Salla ta biyu, Tattaunawa kan azumi, Tattaunawa kan Hajji, Tattaunawa kan Zakka, Tattaunawa kan Khumsi, Tattaunawa kan kasuwanci da abubuwan da suka rataya da shi, Tattaunawa kan yanka da Farauta, Tattaunawa kan Aure, Tattaunawa kan Shika, Tattaunawa kan Bakance, Alkawari da Rantsuwa, Tattaunawa kan Wasiyya, Tattaunawa kan gado, Tattaunawa kan Jingina, Tattaunawa kan Umurni da abubuwa masu kyau da hani da munana, kana da kuma Tattaunawa kan abubuwa na gaba daya.

Hakika na sami daman kammala wannan littafi ne ta hanyar ziyarar ofishin Mai girma Ayatullah al-Uzma as-Sayyid Aliyu al-Husaini yyu al-Sistani (Allah ya kara masa tsawon rai) da ke Najaf al- Ashraf don tabbatar daidaituwansa da fatawoyinsa, kana hakika ofishin nasa sun gudanar da ayyukan gyararrakin da suka wajaba don wannan littafi ya zamanto ya yi dai-dai da fatawoyinsa (Allah ya kara masa tsawon rai).

Na kasance mai kwadayin ya kasance na tabbatar da abin da nake kokari akansa, ina mai gode wa dukkanin wadanda suka taimaka min kan wannan hanya da na zaba, musamman ma dole in ambaci irin kokarin da ofishin shugabammu da ke Najaf al- Ashraf Saboda irin yadda suka ba da karfinsu wajen tsarkake wannan littafi, ina mai rokon Allah Ta’ala da ya sanya ni daga cikin wadanda -KA BAI WA LITTAFINSA A DAMANSA, SAI ya ce WA (MAKUSANTANSA) KU KARBA, KU KARANTA LITTAFINA- kana ya sanya wannan aiki nawa ya zamanto saboda SHI ne kawai (Ranar da dukiya ko ’ya’ya basa amfanarwa sai dai kawai wanda ya je wa Allah da tsarkakekkiyar zuciya) (ya ubangijimmu kada ka kama mu kan abin da muka yi mantuwa ko kuskure a kansa) (muna neman) gafararka, ya ubangijiimmu, kuma a gareka makoma take)

                                    Walhamdu lillahu Rabbil alamin.

Mawallafi


 

 

KARIN HASKE:

Hukumce – hukumcen sharia (da suke cikin wannan littafin) wadanda aka sanya su a cikin baka “Ihtiyat al-Wujubi” ne, kana da zabi Imma ka yi aiki da su ko kuma ka koma ga wani mujtahidi daban, amma tare da la’akari da mafi sani (A’alam) sannan mabiyinsa.

 

عنوان الکتاب