TATTAUNAWA KAN HAJJI |
||
|
Cikin tsohuwar kauna da ta ki warkewa, kana da kuma tsananin soyayya da ta damfare da zuciya wacce bata goguwa don jin dadin saduwa da abu mai daraja. A cikin irin wannan hali, babana ya fara ban labarin aikin hajjinsa na farko, kana kuma idonsa na cike da kasala mai girgizawa, sannan kuma harshensa na cike da tsantsaini (kan abin da zai fada), kuma bakinsa na cike da murmushin dake nuna soyayya wacce take kokarin nuna kanta amma-ga dukkan alamu-kunya mai tsanani da daukaka suna hana ta. Sai na ce wa babana (saboda hakika irin wannan hali ya burge ni): -Na ga kana magana kan hajjinka na farko kamar yadda mai bege yake yi lokacin da ya cimma burinsa. Sai ya ce (alhali muryarsa tana rawa kana ya raunana yayin da yake min wannan magana):- Yanzu zan ba ka kaset din tunawa da wannan al’amari na farin ciki da dadi, don dawo da shauki mai gudana da kuma annashuwa da gusar da hankali, wannan soyayya mai taba mutum soyayya wanda aka shuka ta a cikin zuciya… Shin ba ka karanta maganar Allah da yake cewa: BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM: “KUMA A LOKACIN DA MUKA SANYA DAKIN YA ZAMA MAKOMA GA MUTANE DA AMINCI” Kana da kuma maganarsa madaukakin sarki - A harshen annabinsa lbrahim (a.s)- Bismillahir Rahamanir Rahim “YA UBANGIJINMU! LALLE NE NI, NA ZAUNAR DA ZURIYATA GA RAFI WANDA BA MA’ABUCIN SHUKA BA, A WURIN DAKINKA, MAI ALFARMA, YA UBANGIJIMMU! DOMIN SU TSAYAR DA SALLA. SAI KA SANYA ZUKATA DAGA MUTANE SUNA GAGGAWAR BEGEN ZUWA GARE SU…” Ga shi nan zuciyata tana faduwa a karo na biyu kamar yadda ta fadi da farko ga waccan daki mai tsarki dake cikin kwari da babu tsiro a ciki, wurin da ake zaune a cikinsa saboda girman wahayi, mai ni’ima da haske, kanshi da tsarkakakkiyar kauna, kyau da soyayya. Babana ya fadi haka, kana sai ya yi shiru takaitacciyar shiru kana cikin dadaddiyar murya sai ya rera wadannan baitoci, yana mai cewa: ya gudan jinin raina, kwari na soyayyar (annabi) Muhammad. Wacce take da yabanyar kauna amma ba na tsiro ba. Nan ce fa ka’aba mai kyalkyali, a nan ne wajen da wahayi ya sauka Anan ne dukkan haske yake, don haka ki shiga cikin soyayya ki narke Ya ke gudan raina, wurin da ake kiran Hatimu da zamzam Na zubar da hawaye na don kaunar a yafe min zunubaina A nan ne kasa ta rufe abu bakwai kana ta sanya wa idona kayataccen kwalli Kamar boyayyun kyawawan abubuwan da suke cikin sama A cikin ka’aba mai haske aka kawata kaunata, nishina ya zamar da kofofin zinare. Sannan kuma kofofin da suke sama ta shigar da ni ina mai gunji don soyayya Kana sai ya dago kansa yana mai ce min: Haka zuciyata ta damfara da hajjin farko, kana duk lokacin da wannan yanayi na shekara-shekara ya kewayo sai na ji ina kaunarsa. Hakika na kasance ina mai rokon ubangijina da ya arzurta ni da arzikin yin aikin hajji a karo na biyu da uku da hudu. Cikin mamaki, sai na katse babana (ina mai cewa): T: Shin yin aikin hajji na farko, na biyu na uku da na hudu wajibi ne? A: Ko da wasa, abin da kawai ya wajaba gare ka shi ne yin aikin hajji sau daya in kana da dama. Domin Allah madaukakin sarki na cewa: (KUMA AKWAI HAJJIN DAKIN ALLAH AKAN MUTANE WANDA YA SAMI IKON ZUWA GARE SHI) Amma yin aikin hajji na biyu, na uku da na hudu mustahabi ne… T: To ka ban labarin wannan hajji naka na farko da ka yi mana? A: To bayan na isa (al-Juhfa) wato daya daga cikin wuraren da shariar musulunci ta ayyana a matsayin wuraren yin “ihrami” wanda ake kiransu da (“Mawakitul lhram” wato wuraren daura ihrami bayan da na isa gurin kana na yi niyyar haramin umrar Tamattu’i” na zuwa hajji don neman kusanci da Allah Ta’ala, sai na cire kayana na sanya tufafi biyu na lhrami su ne kuwa riga da zani (bante farare) kana sai na amsa na yi talbiya na fara fadin wadannan kalmomi da larabci: (Labbaikal lahumma labbaika, Labbaika La sharika laka labbaika, innal hamda wan niimata laka wal-mulk, La sharika Laka labbaika) Ko da na fara fadin (Labbaika) sai na ji gabobina suna kadawa, hakika na fuskanci wani irin hali na tsoro da kaskantar da kai da ban taba fuskantar irinsa ba, kana a wannan hali sai na tuna da yadda Imaminka (a.s) yake kaduwa saboda tsoro kana yanayinsa ya canja sannan harshensa na rawa yana daurewa lokacin da yake yin “Talbiyya” saboda tsoron Ubangiji madaukakin sarki. To daga lokacin da na sanya “lhrami” an haramta min jima’i da dukkan nau’oinsa da abubuwan da ke tattare da shi da, amfani da turare, dubin madubi saboda ado, da rufe kai da abu mai yin inuwa (kamar lema) saboda kare rana [ko ruwan sama], sanya dinkakken abu da abubuwan da suke da hukuncinsa, sanya safa da rufe kai, da sauransu wadanda littattafan fikhu suka kawo. T: To bayan ka yi harami fa ( ka daura ihrami)? A: Bayan na yi harami sai na nufi Makka alhali ina cikin tsarki, don in yi dawafi a dakin Allah sau bakwai ina mai farawa daga bakin dutsen nan (Hajarul Aswad) kana kuma in kare a gurin. Kana bayan kare dawafin sai in yi salla raka’a biyu kamar sallar asuba a bayan “Makamu lbrahim” (a.s) ina mai neman kusanci da Allah cikin dukkanin ayyukana na umrah da Hajj. Bayan haka sai na yi “sa’ayi” tsakanin safa da “Marwa” sau bakwai shi ma ina mai farawa daga safa kana in kare a Marwa. Lokacin da na gama “sa’ayin”a Marwa sai na rage wani abu daga gashin kaina. Da wannan aski ne na kare “Umrar Hajji”, daga nan sai na cire “ihrami”na ina mai jiran zuwan rana ta takwas na watan zul Hajj wato (Yaumul Tarwiyya) don in sake yin “harami” a karo na biyu daga Makka, amma “haramin”a wannan karon ba na Umra ba ne na hajji ne. Ko da wannan rana ta takwas ta cika sai na sanya zani da rigata (na harami) a karo na biyu kana na yi niyyar lhramin hajji, kana kuma na yi “talbiya”, daga nan sai na nufi Arafa a budaddiyar mota inda ya zama min wajibi in tsaya kana in kasance a can, daga farkon azahar din rana ta tara na watan “zil Hajj” har zuwa faduwar rana. Lokacin da rana ta fadi a ranar tara ga zulhaj alhali ina Arafa sai na nufi (Muzdalifa)kana na kwana a can wato daren goma na watan “zil hajji” inda ya zamanto min wajibi alfijir din ranar goma ya keto ina nan muzdalifa har kusan fitowar rana. Yayin da rana ta ran goma ta fito sai na bar Muzdalifa zuwa “Mina” ina mai dauke da wasu kananan tsakuwa da na tsine su daga Muzdalifa inda wasu wajiban guda uku suke jira na in aikata su a Mina, a wannan ranar su ne kuwa: 1. Jifan “Jamratul Akabah” da tsakuwoyi guda bakwai daya bayan daya. 2. Yanka ko hadaya a Mina. 3. Aski a Mina. ya yi n da na gama su sannan na yi aski komai ya halatta min in banda jin dadi da mata da shafa turare [da farauta], sannan sai na nufi Makka a karo na biyu don yin dawafin Hajji, kana in yi sallar dawafi, kuma in yi “sa ayi” tsakanin safa da Marwa kamar yadda na yi dawafi, na yi salla kana na yi “sa’ayi” farkon isowa ta garin Makka. Bayan na gama su sai na yi “Dawafun Nisa” kana nayi sallar dawafi, kana bayan duk wannan sai na koma Mina inda wajibi ne gare ni in kwana dararen goma sha daya da sha biyu a can, kana in zauna a Mina har bayan azahar din rana ta goma sha biyu, a tsakanin wannan lokaci ne na jefi jamrorin nan guda uku (jifan shaidan) wato Jamra ta farko da ta tsakiya da ta Akaba a jere a rana ta goma sha daya kana kuma sai na komo a rana ta sha biyu na jefe su a karo na biyu kamar yadda na jefe su a baya. Lokacin da azahar din rana ta sha biyu ya yi kana ya dan gota, alhali ina Mina sai na yi sallar azahar sannan na bar Mina a ya yi n nan duk wasu wajibai na hajji sun kare. Duk da tsananin cikowa da zafin rana da kasa mai kuna, kana duk da kokarin da na yi wa kaina -kamar yadda yake wajibi-don in ga cewa ina tsaye ne a Arafa ba’a wajen ta ba, kana in kasance a cikin Muzdalifa ba’a wajenta ba, kana a Mina ba’a wajenta ba, duk da haka din amma aikin hajji ya zamanto albarkataccen wuri ne na kama kafa da Allah madaukakin sarki da kuma kusanci gare shi da kuma ta’allaka da shi kana da tsayuwa gaba gare shi dare da rana kana mai kadaita da shi. Bayan haka sai na baro garin Makka-duk da irin kauna na gare ta, da bakin ciki mai tsanani saboda rabuwa da ita sai na tafi -zuwa Madinatul Munawwara inda na ziyarci kabarin Annabi Muhammadu (SAWA)da kabarin sayyidatuna fatimatuz Zahra (a.s) da sauran kabarurrakan “lmaman Baki’a” (a.s) (lmam Hasan (a.s.), Imam Aliyu lbn Husain (a.s), Imam Muhammad al-Bakir (a.s.) da Imam Ja’afar as-Sadik (a.s). Kana kuma da ziyarar masallatai da wurare masu tsarki da ke kewaye da birnin Madina da kuma ziyarar sayyidina Hamza baffan Annabi (SAWA). Wannan shi ne takaitaccen tarihin hajjina na farko kenan, don haka duk lokacin da ka samu kudi za ka iya zuwa hajji bayan ka tsarkake su da fitar da zakka ko khumsi daga cikinsu idan har zakkar ko khumsin sun rataya da shi, a wannan lokacin ne zan maka cikakken bayani kan abubuwan da ya kamata ka yi a can. Ina rokon Allah da ya yi maka muwafaka da ziyarar dakinsa mai girma don ka amfana a can don shi mai amsa addu’a ne, makusaci. T: Babana kafin mu kare wannan tattaunawa tamu, ina so in tambayeka kan (Tsarkake Dukiya) wato dangane da zakka ko khumsi wadannan da ka ambata a cikin maganarka. A: Ba yanzu ba, domin magana kan zakka ko khumsi zai dauki lokaci mai tsawo lnsha Allah za mu ajiye wa kowani daya lokacinsa na daban. T: Wato a zamanmu na gaba za ka min bayani kan zakka kenan, kana bayansa kuma a kan khumsi. A: Kamar yadda kake so lnsha Allah. · Insha Allah. * * * * * |
||