TATTAUNAWA KAN AZUMI

 

Babana ya fara maganarsa ne kan watan Ramalana da sauti mai karfi cike da tsoro kana idonsa na cike da hawaye mai haskakawa, kana ruhinsa na cike da kauna da soyayyar da ba ta iya lissaftuwa. Sunan (watan) Ramalana yana bijiro masa da dukkan ma’anarsa kyakkyawa, madaukakiya mai cike da alheri, tausasawa, albarkoki, rahama, gafara da yardan Ubangiji.

Saboda ya tabbatar min da wannan kwanciyar hankali nasa sai ya jawo hankalina zuwa wani lamari na daukaka da mutunci…har zuwa inda manzon Allah (S.A.W.A.) ya tsaya yake gaya wa mutanen gidansa da sahabbansa wannan huduba, yana cewa: “Ya ku mutane hakika watan Ubangiji ya zo muku da albarkoki da rahama da gafara. Watan da a wajen Allah ya fi dukkan watanni, ranakunsa su ne mafifitan raneku darairansa su ne mafifitan darare kana sa’ointa sun fi sauran sa’oi. shi wata ne da aka kira ku zuwa liyafar Allah a cikinsa, aka sanya ku masu daukaka a cikinta, nunfashinku a cikinta tasbihi ne, kana barcinku a cikinta ibada ne ayyukanku kuwa a cikinta karbabbu ne, adduoinku a cikinta kuwa amsassu ne Don haka ku roki ubangijinku da tsarkakakkiyar niyya da kuma zuciya mai tsarki don ya taimake ku kan yin azuminsa da kuma karatun littafinsa. Hakika shakiyyi shi ne wanda aka haramta masa gafarar wannan wata ya ku mutane, hakika aljanna a bude suke a wannan wata, ku tambayi ubangijinku kada ya rufe su gareku. Kuma kofofin wuta a rufe suke, ku reki ubangijinku kada ya bude su a gareku, kuma shedanu a daure suke, ku roki ubangijinku kada ya sau su a kanku.”

Babana ya karanta wannan kenan sannan sai ya koma da ni wani barin daga hudubar Manzo (S.A.W.A.), kai ka ce yana so ne ya nuna mini irin abin da ya kamata in aikata shi a wannan wata mai alfarma, sai ya karanta mini maganar Manzo (S.A.W.A.) inda yake cewa: ya ku mutane wanda ya ciyar da mumini mai azumi (wato ya ba shi buda-baki) a wannan wata yana da ladan wanda ya ‘yanta bawa a wurin Allah kana da kuma gafarar zunubansa da suka gabata”.

Sai aka ce masa: “ya Rasulallah! ba kowannenmu ne zai iya haka ba. Sai ya ce musu: ku ji tsoron wuta ko da da tsagin dabino…“ku ji tsoron Allah ko da da shayarwa da ruwa ne. Domin Allah yana bayar da ladan ga wanda ya aikata wannan dan abin idan ba zai iya aikata sama da haka ba…

Ya ku mutane! Daga cikinku duk wanda ya kyautata dabi’unsa a wannan watan , Allah ya lamunce masa tsallake siradi ranar da kafafu za su zame (akansa). Duk wanda ya saukake wa abin da hannun damansa ya mallaka (bayi) Allah zai saukake masa hisabinsa. Duk wanda ya tsagaita sharrorinsa a cikin wannan wata Allah zai dage masa fushinsa ranar da zai sadu da shi. Kana duk wanda ya girmama maraya a cikinsa, Allah zai girmama shi ranar da za su sadu. Duk wanda ya sadar da zumunci a cikinsa Allah zai sadar masa da rahamarsa ranar da zai sadu da shi, kana duk wanda ya yanke zumunci a cikinsa Allah zai yanke rahamarsa gare shi ranar da zai sadu da shi.

Duk wanda ya karanta wata aya ta Al-kur'ani a cikinsa yana da ladan wanda ya sauke dukka Al-kur'ani a wani watan na daban".

Babana yana kaiwa ga wannan wuri sai ya fara zargin wasu daga cikin ayyukan wasu masu azumi wadanda suke zaton cewa azumi shi ne kamewa daga ci da sha kawai, inda ya kawo wannan hadisin na Imam Ali (a.s) inda yake cewa a cikinsa: "Mutane nawa ne suke azumi amma ba su amfana da komai ba daga azumin nasu face kishin ruwa, kana mutane nawa ne suke tsayuwa (da dare) amma ba su da komai daga tsayuwan tasu in banda wahala"

Daga nan sai babana ya ci gaba da wani hadisin daga Imam Sadik (a.s) inda yake cewa: "Idan ka wayi gari kana mai azumi, to jin ka, ganinka, gashinka, jikinka da dukkan gabobinka su ma su yi azumin". Kana a wani gurin kuma yana cewa: (a.s) "Shi azumin ba wai kamewa daga ci da sha ba ne kawai, idan har kuna azumi to ku kare harsunanku daga karya, ku runtse idanunku daga abubuwan da Allah ya haramta, kada ku yi jayayya, kada ku yi hassada, kada ku yi maganar wasu (alhalin ba sa nan), kada ku yi zagi da ashar, kada ku zalunci wani…ku nisanci shaidar zur, karya, ko husuma, mummunan zato, cin naman mutane, annamimanci, ku kasance masu tunanin lahira, masu dakon ranekunku, masu jiran abin da Allah ya yi  muku alkawari, masu guziri saboda saduwa da Allah, masu kwanciyar hankali da wadatuwar zuci, tsoro da kaskantar da kai da kuma durkusawa irin na bayi masu tsoro ga ubangijinsa yana mai tsoro da kuma sa rai".

Sannan ya gaya min wata kissa da ta faru ga Manzon Allah (S.A.W.A.) wata rana annabi (S.A.W.A.) ya ji wata mace tana zagin makwabciyarta alhali kuwa tana azumi, sai manzon Allah (S.A.W.A.) ya bukaci a kawo masa abinci ya ce mata: "ga shi ki ci". Sai ta ce: ya Manzo ina azumi sai ya ce"Yaya za ki zama mai azumi, bayan kin zagi makwabciyarki, ai azumi ba wai kamewa daga abinci ko abin sha ba ne kawai face dai Allah ya sanya hakan ne don ya zamanto wata katanga da zai kare mutum daga dukkan munanan abubuwa na daga aiki da magana, ya mamakin yadda azumi ya zama kadan, yunwa kuma tai yawa”.

T: Na ce wa babana, hakika tsoro ya fara kama ni (wato kamar watakila na balaga): a wannan hali ya wajaba a gare ni in azumci watan Ramalana ta wannan shekarar kenan, to amma yaya zan yi in san watan Ramalana ya kama domin in azumce shi?

A: Za ka gane hakan ne ta ganin watan Ramalana a garinku ko wani garin da ke kusa da ku da kuke da hanyar sararin samaniya guda (ufuki) wato ganin watan wancan garin matukar babu wani abin da zai hana ganin kamar hadari ko dutse ko makamantansu.

T: Da mene ne ganin wata yake tabbata?

A: Yana tabbata ne da wadannan abubuwa da za su zo:

1-     Ko kaga watan da kanka

2-     Ko mutane biyu adilai su gan ta tattare da rashin bayyanar kuskurensu kana kuma da rashin karo tsakanin maganganunsu.

3-     Cikan watan sha'aban kwanaki talatin, kenan a wannan hali za ka san cewa watan sha'aban ya kare kana watan Ramalana ya shigo.

4-     Yaduwar labarin ganin wata daga mutane da yawa, a nan za ka samu yakinin ganin ta.

T: To idan daga farkon lokaci ban san shin an ga watan Ramalana ne don gobe in dauki azumi ko kuma a'a, to shin zan yi azumin ne tattare da cewa ban san shin gobe karshen sha'abana ne ko farkon Ramalana ba?

A: Za ka azumce shi a matsayin cewa sha'aban ne, to idan daga baya, bayan gari ya waye sai ya bayyana maka cewa Ramalana ne sai ka canza niyyarka daga azumin sha'abana zuwa Ramalana, babu komai a kanka.

Ya halatta gare ka kada ka azumci ranar shakka.

T: To yaya zan yi in gane cewa watan Ramalana ya kare, wato watan shawwal ya kama don in sha ruwa?

A: Ta hanyar da ka riga ka sani wacce ta gabata lokacin farkon watan Ramalana, wato ko kaga watan shawwal din da kanka ko…ko…

T: Na'am…Na'am. To idan ya tabbata gare ni cewa watan Ramalana ya kama?

A: To wajibi ne gare ka da dukkan musulmi balagagge mai hankali, wanda azumi ba zai cutar da shi ba mazaunin gida ba matafiyi ba kana kuma wanda yake cikin hankalinsa da ya azumci wannan watan.

Dangane da mata kuwa azumi yana wajaba ga macen da take tsarkakekkiya daga jinin haila da jinin haihuwa, domin mai haila ko jinin haihuwa ba ta azumi, kana daga baya ta rama abin da ya tsere mata na daga watan Ramalana.

T: To idan mutum yana tsoro wa kansa yin azumi fa?

A: Duk wanda yake tsoro wa kansa kamuwa da wata cuta ko jinkirin warkewa ko tsanantar cutar ko kuma karuwar zafin ciwon saboda azumin to ba zai yi azumi ba, ko da yake hakan ya ta'allaka ne da wani gwargwado da zai yiwu a yi dogaro akai da kuma ciwon da dabi'ar mutum ba za ta iya jurewa ba.

T: To matafiyi fa?

A: Idan ya yi  tafiyar ne bayan "zawal" to [zai ci gaba da azuminsa], to in kuwa ya yi  tafiyar ne kafin fifowar alfijir sai ya sha ruwa.

T: To idan bayan alfijir ne fa?

A: Idan ya yi  tafiyar bayan alfijir ne azumi [ba ya inganta a gare shi shin yana da nufin tafiyar ne tun da daddare ko kuma ba shi da shi] amma zai rama azumin.

T: Idan ina so in yi azumi, to yaya zan yi?

A: Za ka yi niyyar yin azumin tun daga farkon alfijir har zuwa faduwar rana don neman kusanci ga Allah.

T: Shin azumi ba shi ne kamewa (daga barin abu ba)?

A: Na'am.

T: To idan na yi niyyar azumi daga mene ne zan yi kamewar kenan?

A: Za ka kame daga barin wasu abubuwa da suke karya azumi, su ne guda tara:

1-     Da na 2, Ganganta ci ko sha kadan ne ko da yawa.

T: To idan ba da gangan ba ne fa, mantuwa na yi cewa ina azumi sai na ci wani abu ko na sha?

A: Matukar dai ba da gangan ba ne, to aziminka ingantacce ne.

T: To shin zan iya kurkure baki na da ruwa kana in zubar da ruwa?

A: Na'am za ka iya yin hakan amma idan hakan don sanyaya baki ne sai -ruwan ya wuce har ya isa ga makogoro to wajibi ne ka rama azumin idan kuwa da mantuwa ne ka hadiye to babu ramuwa a kanka.

T: To shin zan iya nitsar da kaina cikin ruwa tare da tabbacin cewa ruwan ba zai wuce zuwa makogoro na ba?

A: Na'am, za ka iya yin hakan ko da yake hakan makaruhi ne mai karfi.

3- [Ganganta yin karya wa Allah ko manzonsa ko Imamai ma asumai (a.s).]

4- Ganganta yin jima'i ta gaba ko ta baya ga wanda ya yi  ko wanda aka yi masa.

T: To miji da matan da suke azumi fa?

A: Za su iya yin jima'i amma fa da daddare kawai banda rana.

5- Mutum ya fitar da mani da kansa ta kowace hanya ce na daga hanyoyin (fitar da maniyyi).

6- Ganganta zama da janaba har alfijir ya keto, idan mutum ya sami janaba cikin dare ta kowace hanya, to wajibi ne ya yi  wanka kafin ketowar alfijir, don alfijir ya keto masa a halin yana da tsarki don ya yi  azumi.

T: To da a ce zan sami janaba cikin dare amma ba zan iya wanka ba saboda rashin lafiya fa?

A: Sai ka yi taimama kafin ketowar alfijir.

T: To mata fa?

A: Idan jinin haila ko na haihuwa ya dauke wa mace da daddare to wajibi ne ta yi wanka kafin fitowar alfijir don ta sami daman yin azumi.

T: To idan na yi mafarki da rana har maniyyi ya zubo ga shi kuma ina azumi fa?

A: Mafarkin mai azumi baya karya masa azuminsa, idan ka sami janaba a kowani lokaci ne na rana, to hakan ba ya cutar da ingancin azuminka ko da kuwa ba ka yi wanka ba.

7- [Ganganta shigar da kura ko hayaki masu kauri zuwa makogoro]

8- Ganganta yin amai (hararwa)

T: To idan aman ba da gangan ba ne fa?

A: Hakan baya cutar da azuminsa.

9- Ganganta yin allura mai ruwa!

T: To idan mai azumi cikin ganganci ya aikata wadannan abubuwan da suke karya azumin fa?

A: Wajibi ne ya kame bakinsa bisa bayanin wadannan abubuwa da za su zo:

A-    Idan mutum ya zauna da gangan cikin janaba har alfijir ya keto zai kame baki da rana, [kuma kamewar tasa ta zama don neman kusanci ga Allah ne kawai wato da nufin ikata abin da yake kansa ba tare da ayyana cewa kamewar na azumin watan Ramalana ne ko saboda girmamawa ba]

B-     Idan ya ganganta yin karya wa Allah ko manzonsa ko kuma shakan hayaki ko kura mai kauri, to a nan [zai kame bakinsa na sauran lokacin da ya saura na wannan ranar da abin da aka neme shi ya yi  wato ya dauka cewa kamewar abu ne da shari'a ta bukace shi da ya yi  ko saboda umarni da azumin ko kuma saboda girmamawa]

C-    Idan kuwa da sauran abubuwan da suke karya azumin ne ya bata azumin nasa to [zai kame bakinsa na sauran lokacin da ya saura a ranar don girmamawa].

Bayan haka kuma wajibi ne ya rama azumin wannan rana da ya karya ta kana kuma ya yi  kaffara imma ya 'yanta baiwa ko kuma ciyar da miskinai sittin ko kuma ya yi  azumi na kwanaki sittin a jere ga kowace ranar da ya karya azuminsa a cikinta, shin da abin halal ya karya azumin kamar shan ruwa ko kuma da abin da yake haramun ne kamar giya ko kuma fitar da maniyyi da kansa.

T: To yaya ake ciyar da miskinai sittin din?

A: Wani lokaci ciyarwa zai kasance gaba da gaba ne kai tsaye, to a wannan halin an shardanta cewa dole ne a kosar da su waton basu shiryayyen abincin da zai iya kosar da su.

A wani lokacin kuwa ta hanyar ba su abincin da ba'a dafa ba ne, to a wannan hali dole ka ba su abin da bai gaza 3/4 kilogram kaso uku daga hudu na dabino ko alkama ko gari ko shinkafa da makamantansu na abubuwan da za'a iya kiransu abinci ga kowace rana.

Amma ka ba su kudi a madadin abincin ba ya halatta, abinci kawai za'a ba su banda wani abu ko ka wakilta shi ya sayo maka sannan ka mallaka masa.

T: To idan na sha ruwa a wata rana ta Ramalana saboda wani uzuri kamar rashin lafiya da yake hana azumi ko tafiya fa?

A: To wajibi ne a wannan hali ka rama azumin wato ka zabi wata rana a cikin ranakun shekara amma banda ranar sallar idi biyu sai ka yi azumi a madadin waccan ranar da ka yi rashin lafiyar ko tafiyar a cikinta.

T: To idan wannan ciwon da ya hana ni yin azumi ya ci gaba har zuwa watan Ramalana mai zuwa fa?

A: Ramako ya fadi a kanka a wannan hali, amma wajibi ne ka ciyar da abinci wato ka yi sadaka a maimakon kowace rana da misalin 3/4 kashi uku cikin hudu kilogram na abinci.

Kafin mu gama wannan tattaunawa tamu kan azumi, sai babana ya ce, "ina so in yi maka ishara da wadannan abubuwa masu zuwa":

1-     Yin azumi ranakun sallolin idin nan guda biyu ba ya halatta (wato babba da karamar salla) shin ramuwa ne ko waninsa.

2-     [Wajibi ne ga babban da ya rama wa mahaifinsa abin da ya tsere masa na daga azumi saboda wani dalili daga dalilan da suke sa ayi ramuwa kana kuma bai rama ba tattare da yana da halin yin hakan amma da sharadin cewa shi babban dan yana da daman hakan ya yi n rasuwar mahaifin nasa kana kuma ba'a haramta masa gadon mahaifin nasa ba].

3-     An yi rangwame ga wasu mutane da su sha azumin watan Ramalana, wato azumi ba wajibi ba ne a gare su:

A-    Tsoho da tsohuwan da ba za su iya azumi ba, ko kuma zai iya janyo musu wahalhalu, to a wannan hali-wato halin wahala-wajibi ne a gare su bayar da "fidiya" akan kowace ranar da ba su yi azumin ba, wato misalin 3/4 kilogram na alkama wacce itace tafi waninta. Kana ba wajibi ba ne su rama azumin.

B-    Mace mai cikin da yin azumin zai cutar da ita ko ga abin da take dauke da shi a cikinta amma wajibi ne ta rama azumin daga baya.

C-    Mace mai shayarwar da take da karancin nono idan har azumin zai cutar da ita ko dan nata [kana kuma babu wani da zai shayar da yaron] idan har akwai to baya halatta ta sha ruwa. A halin da ya halatta mace ta sha kuwa to daga baya za ta rama azumin, kamar yadda ya wajaba garesu-mai ciki da mai shayarwa-da su yi kaffara ga kowace ranar da suka sha ruwa da misalin 3/4 kilogram na abinci.

4-     Kamar yadda salla ta kasu kashi biyu wato wajiba da mustahabba. To haka shi ma azumi yake bil hasali mustahabbi mai karfi ne Hakika an ruwaito a ruwayoyi cewa azumi (Garkuwa ne daga wuta) kana shi kuma (zakkan jiki ne) kana kuma (da shi ne bawa yake shiga aljanna) kana kuma (barcin mai azumi ibada ce kana numfashinsa da shirunsa tasbihi ne, ayyukansa kuma karbabbu ne kana adduoinsa abin amsawa ne) kana (Mai azumi yana da farin ciki biyu, farin ciki ya yi n shan ruwa dayan kuwa lokacin da zai sadu da ubangijinsa)

Hakika ruwayoyi sun nuna mustahabbancin wadannan azumi:

A-      Azumin kwanaki uku na kowane wata, amma abin da ya fi shi ne azumi kowace alhamis na farkon wata da kuma alhamis din karshe na wannan watan, da ranar laraban farko na goma ta biyu na wannan watan.

B-      Azumin rana ta ashirin da biyar na watan zil- ki’ida.

C-      Azumin rana ta ashirin da hudu na zil-Hajji.

D-      Azumin dukkanin ranekun watan Rajab ko wasunsu.

E-       Azumin dukkanin ranakun watan sha'aban ko wasunsu.

F-       Da wasunsu masu yawa da ba za mu iya kawo su ba saboda karancin lokaci.

5-     Daga karshe sai babana ya karanto min wannan ruwaya daga Imam Sadik (a.s) cewa: (Abin da ke cika azumi shi ne ba da zakka) wato zakkar fidda kai.

Kana sai babana ya ci gaba da cewa wajibi ne ga dukkan baligi, mai hankali kana wanda ya mallaki abin da zai ci na shekara da ya fitar da "Zakkar fidda kai" ga kansa da duk wanda yake karkashinsa, (iyalansa) shin na kusa ne ko yana nesa, shin babba ne ko yaro har bakon da ya zo masa kafin shigan daren karamar salla ko kuma [bayan shigarsa] har ya shiga cikin iyalansa da suke karkashinsa aka kuma lisafta shi cikin iyalansa.

Mikdarin abin da za'a bayar na "Zakkar Fidda kai" na kowani mutum shi ne "kilogram uku" na daga alkama ko sha'ir ko dabino ko zabibi da makamantansu na daga abubuwan da ake kirga su a matsayin abinci galibi ko kuma a bayar da kwatankwacinsu na daga kudi. Zai bayar da su ko ya ware su daren salla ko kuma ranar sallar [gabannin sallar idi ga wanda ya sallace ta] har zuwa "zawal" ga wanda bai sallace ta ba.

Zai bayar da ita ne ga fakirai da miskinan da ya halatta a ba su zakkar kudi (Dubi "Tattau-nawa kan zakka").

Koda yake ya kamata ka san cewa zakkar wanda ba "Bahashime" ba ba ta halatta ga Bahashime, idan har mai bayarwar ba "Bahashime" ba ne, wato daga kabilar Banu Hashim. Mutum ba zai ba da zakkar fidda kai ga wanda ciyar da shi ya wajaba a gare shi ba kamar babansa, ko mahaifiyarsa ko matarsa ko kuma dansa.

* * * * *

عنوان الکتاب