TATTAUNAWA KAN SALLAH TA BIYU

 

Kafin lokacin tattaunawarmu kan salla ta biyu ya yi  na yi kokari dan in tuna abubuwan da suka faru a tattaunawa kan salla ta daya don in gano karfin haddata kana kuma in yi tanbaya kan abin da ban haddace ba ko kuma ban mallake shi ba tun da dai ba mu yi ban kwana da tattaunawa kan salla ba.

Zuwan babana ke da wuya sai na fara bijiro masa da tambayar da na gagara samo mata amsa, na ce masa:

T: Shin zan iya yin sallar isha raka’a biyu kawai?

A: A’a…ashe ban gaya maka cewa ita mai raka’a hudu ba ce?

T: Amma ai wani lokaci na gan ka ka sallace ta raka’a biyu?

A: Shin lokacin muna halin tafiya ne?

·        Na’am

-         Haka ne, ya yi n tafiya wajibi ne ka rage salloli masu rakaoi hudu (sallolin azahar, la’asar da isha) zuwa raka’a biyu, idan har wadannan sharudda sun cika:

1-     Mutum ya yi  niyyar tafiya wadda nisanta ya kai kilomita 44 daga gidansa shin wannan nisan tafiya ne kawai ko kuma tafiya da dawowa.

T: Kara min bayani sosai.

A: Idan mutum ya yi  tafiya da nisanta ya kai kilomita 44 ko fiye daga gidansa, to wajibi ne ya yi  kasaru wato ya sallaci salla mai raka’a hudu raka’a biyu kawai.

Haka ma idan ya yi  tafıyar da ta kai kilomıta 22 daga gidansa kuma yana da niyyar dawowa garinsa a wannan ranar mısali.

T: To daga ina zai fara kirgen nisan tasa?

A: Zai fara kirgen nasa ne daga wurin da mutum zai iya a bisa al’ada idan mutum ya ketare shi za a kirga shi a cikin matafiya, sau da yawa dai ana fara shi ne daga karshen gidajen gari kuma ya zama na nisan kilomita 44.

2-     Niyyar tafiya din ta kasance tare da matafiyi, idan har ya canza ra’ayinsa ko kuma abu ya bijiro masa to zai cika sallarsa, sai dai idan ya kuduri aniyar dawowa garinsa kana kuma hanyarsa ta dawowa da tafiyar da ya yi  ta kai haddin kasaru (kilomita 44) to a wannan hali wajibi ne ya yi  kasaru .

3-     Tafiyar ta kasance ta halal ce, idan tafiyar ita kanta ta zamanto ta haram kamar tafiyar mace a wasu halaye ba tare da izinin mijinta ba ko kuma ya yi  niyyar aikata haramun din a cikin tafiyar tasa kamar ya yi  niyyar yin sata a tafiyyar tasa to wajibi ne ya cika sallarsa, wannan hukuncin ya hada har da tafıya don farautan jin dadi, a wannan halin ma zai cika sallarsa.

4-     Kada matafıyı ya wuce ta garinsu wato ya sauka a garin ko ya tsaya a wurın ya yi n tafıyarsa kana kada ya yi  niyyar zama na kwana goma ko fıye a garin da ya je, sannan kada ya kasance mai shakku bai san yaushe ne zaı bar wannan garin da yaje ba har na tsawon kwanakı talatın. To zai rage sallarsa (kasaru) tun daga farkon tafiyar tasa ba zai cika salla ba.

T: To idan matafiyi ya wuce ta garinsu ko kuma ya tsaya a wurin ya yi n wannan tafiyar tasa ko kuma ya yi  niyyar zama na kwana goma ko fiye a garin da ya je, ko kuma ya kasance mai shakku bai san yaushe zai tafi ba har na tsawon kwanaki talatin fa?

A: To a wannan hali sai ya cika sallarsa, mai shakku ma bayan cikan kwanaki talatin zai cika sallarsa matukar dai yana nan a wannan garin.

5-     Kada tafiya ta kasance aikinsa ne kamar direba, ko makiyaya ko kuma ya maimaita yin tafiye tafiye saboda ayyukansa ko kuma saboda wani dalili daban.

T: Wato ana nufin direba zai cika sallarsa kenan ya yi n tafiyarsa?

A: Na’am. Duk wanda aikinsa shi ne tukin da ya kai nisan kasaru to zai cika sallarsa lokacin da yake wannan aiki nasa.

T: To dan kasuwa ko dalibi ko ma’aikacin da yake zaune a wani gari amma wajen kasuwancinsa, ko makarantarsa ko ma’aikatarsa tana wani gari ne daban da  nisansa ya kai kilomita 22 ko fiye sannan kuma kowace rana ko kowane kwanaki biyu yake wannan tafiya tasa fa?

A: Zai cika sallarsa ba zai yi kasaru ba.

6-     Kada ya kasance daga cikin wadanda ba su da takamaimen wajen zama kamar wadanda gidajensu suke tare da su kamar yan yawon shakatawa wanda ba shi da gari ko kuma wani abu ya faru a garin nasu yana yawo daga gari zuwa gari ba shi da takamaimen matsuguni tsakaninsu.

T: Yaushe ne matafiyi zai fara kasaru?

A: Wajibi ne ya fara kasaru lokacin da ya buya daga ganin mutanen garinsu saboda nisantarsu da ya yi , alamar hakan kuwa shi ne ta yadda ba zai ga motsin mutanen garin ba, to daga nan sai ya fara kasaru.

T: Ka ce min idan matafiyi ya wuce ta garinsu kana ya sauka a gurin sai ya cika sallarsa, me kake nufi da garinsu?

A: Abin da nake nufi da garinsu shi ne.

A-    Garinsu na asali da ake jingina masa kana kuma inda iyayensa suke zaune kuma inda aka haife shi.

B-    Gurin da mutum ya zaba wa kansa ya zamanto mazauninsa har karshen rayuwarsa.

C-    Gurin da ya zaba zai zauna na lokaci mai tsawo ta yadda ba za’a iya ce masa matafiyi ba a wajen.

T: Ma’anar hakan shi ne:

1-     Idan matafiyi ya wuce ta garinsu kana ya sauka a gurin.

2-     Idan ya yi  nufin zama na kwana goma ko fiye a garin da ya je.

3-     Idan ya tafi wani gari kana ya zauna na tsawon kwanaki talatin yana mai shakku bai san yaushe ne zai dawo gida ba. To a wadannan halaye zai cika sallarsa ba zai yi kasaru ba.

A: Na’am

T: To in mutum ya yi tafiya amma wadannan abubuwa da suka gabata ba su bijiro masa ba fa?

A: Zai yi kasaru a sallarsa. Duk wanda ya yi  tafiyar da nisanta ya kai kilomita 44 ko fiye daga garinsu, hukuncinsa shi ne yin kasaru sai dai idan ya bi ta garinsu kuma ya sauka a garin ko ya yi  niyyar zama a wuri na kwana goma ko…

-         Na’am…Na’am…

T: Idan lokacin salla ya yi  alhali mutum yana halin tafiya amma bai yi sallar ba, kana ya dawo garinsu, to yaya zai yi sallar a garinsu?

A: Zai cika sallar, domin lokacin da ya yi  sallar yana garinsu ne.

T: To idan bai yi salla ba, sannan sai ya yi  tafiyar da ta kai kilomita 44 ko fiye fa?

A: Zai yi kasaru, domin lokacin da ya yi  sallar yana halin tafiya ne?

T: Wani lokacin ina ganin wasu jamaa suna salla tare suna ruku’u tare kana kuma suna sujada tare sannan suna mikewa gaba daya?

A: Wadannan suna salla cikin jama’a (Jam’i) ne ba daidaiku ba.

T: To yaya za mu yi sallarmu a jam’i?

A: Idan mutane biyu ko fiye suka hadu, kana daya daga cikinsu yana da sharuddan limanci, to ya halatta ya jagorance su don su yi salla tare, ta haka za su sami karin lada.

T: Wato sallar jam’i mustahabi ne kenan?

A: Na’am, tana da lada mai girma ta musamman idan aka yi ta a bayan masani kana kuma duk lokacin da jama’a suka karu ladanta yana karuwa.

T: To mene ne sharuddan limamin da zai jagoranci jama’a wacce ka yi nuni da ita?

A: Dole ne limamin jama’a ya kasance, baligi, mai hankali ba mahaukaci, ba, mumini, adili wanda baya sabon Allah, mai ingantaccen karatu, dan halal, namiji idan mabiyansa maza ne.

T: To yaya za mu gane cewa wannan mutumin mumini ne kuma adili ne har mu yi salla a bayansa?

A: Kyan halinsa na zahiri ya wadatar.

T: Shin akwai wasu sharuddan jam’i da liman kuma?

A: Na’am, [dole ne liman ya kasance ba’a taba tsayar masa da haddi na shari’a ba] kuma dole sallarsa ta kasance a tsaye idan mabiyansa a tsaye suke salla, dole ne ya kasance inda zai fuskanta inda mabiyansa suke fuskanta ne, ba ya halatta ga wanda yake da itikadin cewa al-kibla tana ta wata bangare ne ya bi wanda yake da imanin cewa wani bangare ne daban, kuma dole sallarsa a ganin mabiyansa ta kasance ingantacciya ce, da a ce liman zai yi alwala da ruwa mai najasa amma ba ya da masaniya kan najastuwansa amma mabiyansa suna da masaniya, to a wannan hali ba ya halatta gare su da su bi shi.

T: Yaya zan yi sallar jam’i?

A: Sai ka zabi wani mutum da yake da sharuddan limancin da muka ambata idan kai daya ne sai ka koma baya kadan ta hannun damansa ko kuma ku tsaya a bayansa in ku biyu ne ko fiye ba tare da wani abu ya shiga tsakaninku ba kamar katanga, kana ba tare da wajen tsayuwarsa ya yi  sama da naka ba fifiko mai girma, kana dole nisan da ke tsakaninka da liman ko kuma tsakaninka da sauran masu salla da suke gefenka ko wanda suke gabanka masu alaka da liman ya zamanto ba shi da yawa.

T: Wato za mu ce wa masu salla kenan kada su bar filin da ya fi mita guda tsakaninsu ko?

A: [Na’am] mai salla ya kan iya samun sadarwa da dan uwansa ko da ta bangare daya ne, ya kan iya samun sadarwa ta wanda yake gabansa, ko wanda yake damansa ko hagu, daya cikinsu ya wadatar.

T: Me ya rage bayan wannan?

A: Idan liman ya yi  kabbara don fara salla sai su ma mabiyansa su kabbara bayansa, idan liman ya karanta fatiha da wata sura su mabiya ba za su karanta komai ba (shiru za su yi) karatunsa ya wadatar musu wato ya dauke musu, idan ya yi  ruku’u su ma sai su yi a bayansa, idan ya yi  sujada sai su ma su yi bayansa, idan ya zauna su ma su zauna, abin da ya fi shi ne su yi tahiya bayan tahiyarsa sannan su yi sallama bayan sallamarsa.

T: Shin zan yi zikiri a cikin ruku’u, sujada da tahiyana, kana shin zan karanta “tasbihat” a raka’oi na uku da hudu, ko kuma shiru zan yi?

A: Za ka yi karatu ne kamar yadda kake yi ya yi n da kake salla kai kadai.. za ka karanta zikiri a cikin ruku’u, sujada da tahiya, za ka karanta tasbihat a rakaoi na uku da hudu kamar yadda ka saba. Karatun surori biyu ne kawai ya dauke maka, sannan wajibi ne a gare ka ka bi shi.

T: Me kake nufi da haka?

A: Wajibi ne gare ka ka yi koyi da liman a duk abin da ya yi, idan ya yi  ruku’u kai ma sai ka yi tare da shi, in ya yi  sujada sai ka yi tare da shi, idan ya daga kansa daga sujada sai kai ma ka dago da dai sauransu, kada ka gabace shi a dukkan ayyukan salla.

T: Yaushe ne ake iya riske liman?

A: Ana iya riskan liman ne lokacin da yake tsaye bayan ya yi  kabbara ko kuma lokacin da yake cikin ruku’u.

T: Idan na riske shi lokacin da yake karanta surorin nan guda biyu, kamar yadda ka ce, ya dauke min su, to amma idan yana halin ruku’u yaya zan riske shi?

A: Sai ka yi kabbara kana ba tare da bata lokaci ba ka yi ruku’u lokacin da liman ya gama ruku’unsa ya daga, sai kai ma ka dago bayansa.

T: To karatuna na surori guda biyun nan fa?

A: Sun fadi a kanka matukar ka riske shi yana ruku’u.

T: To idan na riske shi a tsaye ne yana tasbihi na raka’a ta uku ko ta hudu fa?

A: Sai ka yi kabbara ka karanta surorin nan guda biyu a boye.

T: Idan babu lokacin da zan karanta su duka fa?

A: Sai ka karanta fatiha kawai.

T: Shin zan iya koyi da liman don sallar azahar, alhali kuwa limamin sallar la’asar yake yi?

A: Na’am, ya halatta maka hakan, ya halatta maka ka bi liman ko da sallarka ta saba da tasa ta wajen bayyanawa ko boyewa, ko kuma kasaru da cikawa ko kuma salla kan lokaci da ramuwa.

T: Shin mata ma suna iya jam’i kamar maza?

A: Na’am, ya halatta ga mace ta yi sallar jam’i a bayan namijin da yake da sharuddan limanci kamar yadda muka ambata, kamar yadda ya halatta mace ta bi mace, amma idan mace ta limanci mata [wajibi ne ta tsaya a sahunsu ba tare da ta gabace su ba] kamar yadda liman namiji yake yi.

Amma idan mata suka yi salla tare da maza wajibi ne su yi salla a bayan maza, ko kuma su yi nasu sahun tare da wani abin kariya ko da katanga ne kuwa.

T: Wannan ita ce sallar jam’i, ko da yake ina jin wata salla da ake ce mata sallar juma’a, shin ita daban take?

A: Na’am, ita rakaoi biyu take da shi kamar sallar asuba ko da yake ita ana banbance ta ne da hudubobi guda biyu gabanninta inda liman a cikinsu zai tashi ya yi  jawabi wa mutane kan abubuwan da Allah ya yarda da su da abubuwa da za su amfani mutane.

Mafi karanci abin da ya wajaba a huduba ta farko shi ne godiya ga Allah da yabon Allah [da harshen larabci].

Kana ya yi  nasiha kan tsoron Allah sannan ya karanta gajeruwar sura daga al-kur’ani mai girma. Daga nan sai ya dan zauna kadan dan ya tashi a karo na biyu saboda huduba ta biyu, ya yi  godiya ga Allah ya yabe shi kana ya yi  salati wa manzon Allah da mutanen gidansa da kuma Imaman musulmai (a.s) sannan abin da ya fi ya nemi gafara wa muminai maza da muminai mata.

T: Shin akwai wasu sharudda na wajibcinta?

A: Na’am, daga cikin sharadin wajibcinta shi ne shigar lokacin sallar azahar, masu sallar kada su gaza mutane biyar har da liman kuma ta kasance tana da limamin da yake da sharuddan limanci kamar yadda muka ambata.

Idan aka tsaida sallar juma’a a wani wurin da ya cika sharudda, to idan wanda zai jagoranci sallar “lmami ma’asumi” ne ko kuma wanda yake wakiltansa to wajibi ne ga dukkan mutanen da suke wajen da kuma wadanda nisansu daga wajen bai wuce kilomita 11 ba kana kuma basu da wani lalura na ruwa, sanyi, mai tsanani kana basa da rashin lafiya ko makamanta kana ba tsoho ko matafiyi ba su halarci sallar.

Amma idan wanda zai jagoranci sallar ba Imami “ma’asumi” ko wakilinsa ba ne to halartarta ba wajibi ba ne, ya halatta ya yi  sallar azahar kawai.

Idan mutum ya yi  sallar juma’ar da ta cika sharudda ta wadatar masa daga sallar azahar, ta dauke masa ita.

Saura kawai in yi maka nuni da wasu abubuwa guda biyu:

Na farkonsu: cewa ita sallar juma’a wajiba ce da ake da zabi a cikinta, mutum yana da zabi imma ya zo da ita idan har sharuddan nata sun tabbata ko kuma ya sallaci azahar amma juma’a dai ita ta fi.

Na Biyunsu: kada nisa tsakanin sallar juma’a da wata sallar juma’a (masallaci) ya gaza kilomita biyar da digo biyar.

T: Ina so inyi wata tambaya amma ina jin kunya?

A: Tanbayi duk abin da kake so babu kunya a addini.

T: Me zan yi idan ban yi wasu salloli ba saboda bacci ko kuma wani lokacin saboda mantuwa ko kuma saboda nuna halin ko in kula da jahilci ko kuma na sallace ta ba daidai ba bayan lokacinta ya fita?

A: Wajibi ne ka rama ta, idan sallar da ake bayyanawa ne kamar sallar asuba, magriba ko isha, za ka rama ta ne a bayyane, idan kuwa wadda ake boyewa ne kamar azahar da la’asar za ka rama su ne a boye, idan kasaru ce sai ka rama ta a kasaru in kuma wadda ake cikawa ne sai ka rama a cike.

T: Shin zan rama sallar azahar ne lokacin da rana ta yi zawali ko kuma isha yayin da lokacinta ya yi da dai sauransu?

A: Ya halarta maka ka rama sallar da ta wuce maka duk lokacin da ka so, shin dare ne ko rana.

 Ya halatta maka ka rama sallar asuba da yamma da dai sauransu.

T: Idan ban san adadin sallar da suka wuce min ba, to salloli nawa zan rama?

A: Sai ka sallaci sallolin da kake da yakinin sun tsere maka, amma wadanda kake da shakku a kansu  sai ka bar su ba za ka rama su ba.

T: Ba ni misali akan hakan?

A: Misali idan ka tabbata ba ka yi sallar asuba ba na tsawon wata daya, to wajibi ne ka rama sallar tsawon wata daya, amma idan kana shakka sun fi haka ko basu fi ba to ba za ka rama fiye da wata guda ba.

Wani misali daban, idan ka san cewa ba ka yi sallar asuba ba na tsawon lokaci, al’amarin sai ya zamanto maka kana shakka tsakanin abubuwa biyu:

Imma dai abin da ake nema daga gare ka shi ne sallar wata guda ko kuma wata daya da kwana goma. To a wannan halin ya halatta maka ka sallaci wata guda kawai ba tare da sauran ‘yan kan ba.

T: Shin wajibi ne mu gaggauta rama sallar da ta wuce mana ba tare da wani jinkiri ba?

A: A’a, yana halarta ka jinkirta, amma ina horonka da ka rama duk wata sallar da ta tsere maka a daidai ranar da ta tsere maka, misali idan ba ka farka don sallar asuba ba to ka rama ta a wannan rana lokacin da za ka yi sallar azahar gabanninta ko bayanta don kada sallli su taru su yi maka yawa ramuwarsu ta zamanto maka da wahala.

Ina rokon Allah ya tsare ka daga kasala wajen ramuwar salla ya kuma arzurta ka da yin salla a kan lokacinta da aka tsara.

T: Bari mu dan koma da baya kadan, a farkon Tattaunawa kan salla ta farko, ya yi n da kake kirga sallolin da suke wajibi, ka ambaci sallar da ta tsere wa mahaifi bai rama ta ba har ya rasu inda ka ce wajibi ne ga babban dansa ya rama masa?

A: Na’am, [wajibi ne gababban da ya rama wa mahaifinsa salloli na wajibi] da suka tsere masa saboda wasu uzururruka bai samu rama su ba tare da iko kan ramawar har ya rasu kana kuma dan lafiyayye ne ya yi n mutuwarsa kuma ba’a hana dan gadonsa (uban) ba, kana yana da daman ya yi  hayan wani don ya rama sallar a madadinsa.

T: Sannan kuma ka ambaci wata salla mai suna “Salatul Ayat”?

A: Na’am, “Salatul Ayat” tana wajaba akan duk wani baligi banda mace mai jinin haila ko jinin haihuwa, yayin zazzabin rana ko wata (husufi) ko da kuwa kadan ne, wato husufin bai zama gamamme ba [ko kuma lokacin girgizan kasa] an so ka sallace ta duk lokacin da bakar iska ta taso da duk wani abin tsoro daga sama kamar tsawa da dai sauransu, ko kuma yayin da wani abin tsoro na kasa ya faru kamar tsagewar kasa ko rugujewa idan har hakan ya haifar da tsoro ga galibin jama’a. Za ka iya “salatul Ayat” kai kadai kamar yadda za ka iya yin ta a jam’i yayin zazzabin wata ko rana (husufi).

T: Yaushe ake yin “salatul Ayat”?

A: Ga husufin wata ko rana, tun daga farkon al’amari har zuwa lokacin da suka yi haske gaba daya.

T: To ga girgizan kasa ko tsawa da kuma duk wani abin tsoro na sama ko kasa fa?

A: Sallolinsu basu da wani takamaimen lokaci, kawai zai sallace su ne lokacin da suka faru, sai dai idan lokacin faruwan abin yana da tsawo sai ya zo da ita kafin lokacin faruwarsu ya wuce.

T: Yaya ne zan yi sallar “salatul Ayat”?

A: Tana da rakaoi biyu ne a kowace raka’a akwai ruku’u biyar.

T: Yaya zan yi hakan?

A: Da farko ka yi kabbara sannan sai ka karanta fatiha da wata cikakkiyar sura, sai ka yi ruku’u idan ka dago kanka daga ruku’u sai ka sake karanta fatiha da wata cikakkiyar sura, haka za ka ta yi har sai ka yi ruku’u na biyar.

Idan ka dago kanka daga ruku’u na biyar sai ka tafi zuwa ga sujada, ka yi sujada biyu kamar yadda kake yi a sauran sallolinka.

Kana sai ka mike don raka’a ta biyu, ita ma a cikinta ka aikata abin da ka aikata a ta farko.

Daga nan sai ka yi tahiya ka yi sallama, ta haka ne za ka kare sallarka, da haka ne zai bayyana maka cewa tana da rakaoi guda goma ne a cikin rakaoi guda biyu.

Akwai wata hanya ta daban ta wannan salla, babu bukatan a ambace ta a nan saboda karancin lokaci.

T: Idan wata ko rana ya kamu da zazzabi amma ban san da faruwarsa ba sai bayan karewarsa fa?

A: Idan har duk watan ko ranan ya kamu gaba daya to wajibi ne ya rama sallar. Idan kuwa ba dukkansa ba ne ya kamu wani sashe nasa ne to ba dole ne ka rama sallar ba.

T: To girgizar kasa da tsawa fa?

A: Idan har lokacin da ya sadu da aukuwarsu ya wuce ba ka yi sallar ba to sallar ta fadi a kanka.

T: Shin wajibi ne a gare ni in yi “Salatul Ayat” ya yi n da aka samu husufin rana ko wata a wata kasa daga kasashen duniya?

A: A’a, sallar kawai tana wajaba a gare ka ne a lokacin da aka samu rashin lafiyar a garinku da garurwan da suke da alaka da garinku wadanda za su iya riskan al’amarin idan ya faru. Sallar ba wajibi ba ne a gare ka idan abin ya faru a wani gurin da ke da nisa daga kasarku.

T: Ka ce min cewa cikin salloli akwai wajibai da mustahabai amma ba ka yi bayani kan mustahabban ba?

A: Ai suna da yawa ne babu lokacin da za mu ambace su a nan, don haka zan takaita ne a kan wadansu kawai:

1-     Sallar dare, lokacinta da ya fi dacewa shi ne sulusin karshe na dare kana duk lokacin da ya fi kusanci da fitowar alfijir shi ya fi, tana da rakaoi takwas ne mutum zai yi sallama a duk rakaoi biyu daga cikinta kamar sallar asuba, idan ya gama da wannan sai ya yi  sallar “shafa’i” tana da rakaoi biyu ne, kana sai ya yi  “Witr” ita kuma raka’a daya ce, dukkansu za su zama rakaoi goma sha daya kenan.

T: Koya min yadda ake sallar “witri” domin ita raka’a daya ce?

A: Da farko ka yi kabbarar sannan sai ka karanta fatiha sannan an so ka karanta suratul Tauhid sau uku bayanta da surorin “an-Nas da al-Falak” sannan ka daga hannunka don addu’a da dukkan wata addu’ar da ka ga dama.

 An so ka yi kuka don tsoron Allah, kana ka nemi gafara ga muminai guda arba’in za ka ambace su da sunayensu, kana ka ce sau saba’in” (Astagfirullaha rabbi wa a tubu ilaihi) da kuma  fadin Haza makamul aizi bika minan nar sau bakwai kana da kuma fadin (al-Afwa) sau dari uku, idan ka gama sai ka yi ruku’u kana ka yi sujada kamar yadda kake ruku’u ko sujada a sallolinka na raneku daga nan ka yi tahiya da sallama.

Za ka iya takaituwa da shafa’i da witri su kadai ko kuma da witr kawai musamman ma idan lokaci ya kure maka.

T: Mece ce falalar sallar dare?

A: Sallar dare tana da falala da yawa, an ruwaito daga Imam sadik (a.s) yana cewa:Manzon Allah (S.A.W.A.) cikin wasiyyarsa ga Aliyu (A.S.) ya ce: “Ka kula da sallar dare, ka kula da sallar dare ka kula da sallar dare). An sake ruwaitowa daga manzon Allah (S.A.W.A.) yana cewa: (salla raka’a biyu tsakiyar dare shi ya fi soyuwa a gare ni daga duniya da abin da yake cikinta). Sannan daga Abi Abdullahi (a.s) cewa wata rana wani mutum ya zo gurinsa da kuka kan wata bukata tasa, ya tsananta a kawo kukan nasa kamar zai yi masa kuka kan yunwa, sai Imam (a.s) ya ce masa: “Ya kai wannan (mutum) shin kana sallar dare”? sai mutumin yace masa: “Na’am: sai Abu Abdullah (a.s) ya dubi Sahibinsa ya ce “Yayi karya duk wanda yake ikrarin yana sallar dare kana ya ji yunwa da rana hakika Allah madaukakin sarki ya lamunce abincin rana da sallar dare”.

2-     “Salatul Wahshah”ko kuma sallar daren da aka binne mutum Lokacin yin ta shi ne daren farko na binne mamaci, a kowani lokacin da kaso, tana da rakaoi biyu, a ta farko za ka karanta fatiha da “ayatul kursiyyu” [har zuwa inda Allah ya ce] (åã ÝíåÇ ÎÇáÏæä) A raka’a ta biyu kuwa bayan fatiha za ka karanta suratul Qadr sau goma kana bayan tahiya da sallama sai ka ce: “Allahumma salli ala muhammad wa ali muhammad wab as sawabaha ila kabri…” sai ka ambaci sunan mamacin. Kana akwai wata hanya ga wannan sallar ka koma ga littattafan fikhu.

3-     Salatul Gufaila: Wannan salla tana da raka’oi, guda biyu ne tsakanin sallar magriba da isha, ake yin ta a raka’a ta farko za ka karanta fatiha da wannan aya mai girma:

(æÐÇ Çáäæä ÅÐ ÐåÈ ãÛÇÖÈÇð ÝÙä Ãä áä äÞÏÑ Úáíå ÝäÇÏì Ýí ÇáÙáãÇÊ Ãä áÇ Åáå ÅáÇ ÃäÊ ÓÈÍÇäß Åäí ßäÊ ãä ÇáÙÇáãíä ÝÇÓÊÌÈäÇ áå æäÌíäÇå ãä ÇáÛã æßÐáß ääÌí ÇáãÄãäíä)

A raka’a ta biyu kuwa bayan fatiha za ka karanta wannan aya mai girma:

(æÚäÏå ãÝÇÊÍ ÇáÛíÈ áÇ íÚáãåÇ ÅáÇ åæ æíÚáã ãÇ Ýí ÇáÈÑ æÇáÈÍÑ æãÇ ÊÓÞØ ãä æÑÞÉ ÅáÇ íÚáãåÇ æáÇ ÍÈÉ Ýí ÙáãÇÊ ÇáÃÑÖ æáÇ ÑØÈ æáÇ íÇÈÓ ÅáÇ Ýí ßÊÇÈ ãÈíä)

Kana sai ka daga hannayenka don addua ka ce:

(Çááåã Åäí ÃÓÃáß ÈãÝÇÊÍ ÇáÛíÈ ÇáÊí áÇ íÚáãåÇ ÅáÇ ÃäÊ Ãä ÊÕáí Úáì ãÍãÏ æÂá ãÍãÏ æÃä ÊÝÚá Èí…)

Sai ka ambaci bukatunka. Sannan sai ka ce:

(Çááåã ÃäÊ æáí äÚãÊí æÇáÞÇÏÑ Úáì ØáÈÊí ÊÚáã ÍÇÌÊí ÝÃÓÃáß ÈÍÞ ãÍãÏ æÂáå Úáíå æÚáíåã ÇáÓáÇã áãÜøÇ ÞÖíÊåÇ áí)

Daga nan saı ka roki bukatunka in Allah ya yarda za ka ga bıyan bukata.

4-     Sallar ranar farko na kowace wata: Tana da rakaoi guda biyu ne, a ta farko bayan fatiha za ka karanta suratul Tauhid sau talatin, a raka’a ta biyu kuwa bayan fatiha za ka karanta suratul Qadr sau talatin, sannan sai ka yi sadaka da abin da ya sauwaka, da hakan ne za ka sayi amincin watan. Sannan mustahabi ne ka karanta wasu ayoyin al-kur’ani na musamman bayanta.

5-     Sallar Imam Ali (a.s): Tana da rakaoi guda hudu za ka sallace ta ne rakaoi bibbiyu kamar sallar asuba. A duk rakaointa za ka karanta suratul Hamd sau daya da kuma suratul Tauhid sau hamsin.

Imam Ali (a.s) yana cewa: “Duk wanda ya yi  salla raka’a hudu a kowace raka’a ya karanta  (Þá åæ Çááå ÇÍÏ) sau hamsin, ba ya tashi daga gurin tsakaninsa da Ubangiji da zunubi”.

6- Salla don saukaka al’amari mai wahala: Tana da rakaoi guda biyu ne, Imam Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Idan al’amurra sun yi maka wahala to ka yi salla rakaoi biyu, a rakar farko za ka karanta fatiha da  (Þá åæ Çááå ÇÍÏ ) da (ÅöäøÇ ÝÊÍäÇ) har zuwa ında Allah yake cewa: (æíäÕÑß Çááå äÕÑà ÚÒíÒà ) a ta biyu kuma suratul fatiha da (Þá åæ Çááå ÇÍÏ ) da (Çáã äÔÑÍ áß ÕÏÑß) .

 

عنوان الکتاب