TATTAUNAWA KAN SALLA

 

Yanzu ga mu nan a tattaunawar mu mun iso ga sallah. Sai Babana ya ce: “Salla kuwa kamar yadda aka ruwaito a hadisin Annabi (s) ita ce ginshikin addini in an karbe ta to an karbi sauran ayyuka in kuwa an jefar da ita an jefar da sauran ayyuka”. Kana Ya ci gaba da cewa: itace tabbatacciyar hanya ta saduwa tsakanin Ubangiji da bayinsa, Allah Ta’ala ya tsara lokutanta masu albarka, da hanyoyinta, suranta da yadda ake yin ta ga bayinsa…ta hanyarta ne kake tsayuwa gaba gare shi, kana fuskantarsa da hankalinka, zuciyarka da gabobinka, kana ganawa da magana da shi, ta hanyar wannan ganawa kana samun kwanciyar hankali da nisuwa, da kuma tsarkakan rai da ake samu ta hanyar wannan kyakkyawar ganawar kuma za ka rabauta da kauna da bege da arziki da karfin gwiwa da kuma jin dadin wannan saduwa.

Hakika lokacin da kakanka Amirul Muminina (a.s.) ya shagaltu cikin ibada ga ubangijinsa sai ya zamanto kyakkyawan zarafi na cire masa kibiya daga jikinsa a yakin siffin ba tare da jin zafi ba saboda yana ganawa da Ubangijinsa.

Haka ma Imaminka Zainul Abidin idan yana alwala don sallah sai ka ga fuskarsa ta canza, lokacin da iyalansa suka tambaye shi: Mene ne yake damun ka lokacin da kake alwala? Sai ya ce musu: “shin ba ku san a gaban waye nake so in tsaya ba ne?” Haka nan lokacin da ya tsaya don salla, sai ka ga jikinsa yana bari (ko da aka tambaye shi dalili) Sai ya amsa wa wanda ya tambaye shi “lna so in tsaya ne gaba ga Ubangijina kana in gana da shi, don haka ne wannan abu ya same ni”.

Haka ma Imaminka al-Kazim (a.s.) ya kasance idan ya tsaya don sallah kana ya kebanta da Ubangiji ya kan yi kuka kuma jikinsa ya kadu saboda girmama Ubangiji.

Lokacin da (Haruna) Rashid ya sanya shi a kurkuku sai ya sami dama na ibada ga ubangiji, yana mai gode wa ubangijinsa da wannan kyakkyawan dama abin kauna gare shi, yana cewa wa ubangijinsa: “Ya Allah na gode maka tun da dai na roke ka ka ba ni dama don in bauta maka sannan ga shi ka karbi addu’ata, to ina mai gode maka a kan hakan.”

Babana ya ci gaba da cewa: “salla bayyana wani abu ne da ke suturce wato abin da ake so na cikin zuciya, lta ce kuma hanyar komawa ga Allah mai girma da daukaka da kuma alaka da ubangijin halittu, mai iko kan komai, madaukakin shugaba. Kana lokacin da kake cewa (Allahu Akbar) don fara salla kamar kana kore dukkan wani abin da ya shafi duniya da tsare-tsarenta da kyalkyalinta kana za su karanta a zuciyarka watakila ma su bace gaba daya saboda kana tsaye ne gaba ga mahaliccin komai mai juya komai yadda ya so, kana shi ne sama da komai kana komai a hannunsa suke.

Lokacin da kake cewa yayin da kake karanta fatiha: “kai muke bautawa kana kai muke neman taimakonka”, kamar ka wanke kanka ne da jikinka daga dukkan wani irin nau’i na neman taimako daga wanin Allah mai iko kan komai mai hikima.

Ta wannan hanya ta kauna da kaskantar da kai ne kake tsarkake kanka sau biyar a kowace rana: wato lokacin asuba, azahar, la’asar , Magriba da isha. Idan ma ka so ka kara a kan haka sai ka kara da mustahabbai daga cikinsu.

T: Ma’anar haka wato akwai salloli wajibai da mustahabbai kenan?

A: Na’am, akwai salloli da suke wajibai akwai kuma mustahabbai.

T: Sallolin wajibai kan na san su …su ne sallolin da muke yin su kowace rana sune sallar asuba, azahar, la’asar, Magriba da isha.

A: Ba wadannan ne kawai wajibai ba, face ma dai akwai wasu sallolin na wajibai da ba wadannan ba, su ne:

1-     Salatul Ayat (dubi Tattaunawa kan salla ta biyu).

2-     Sallar Dawafi na wajibi a Umra ko Hajj (dubi Tattaunawa kan Hajj).

3-     Sallar mamaci (dubi Tattaunawa kan Mutuwa).

4-     Sallar da mahaifin mutum ya rasu ya bari (inda ya zama wajibi kan babban dansa ya rama masa) (dubi Tattaunawa kan Sallah ta biyu).

5-     Sallar da ta zama wajiba don ijara ko kuma ta hanyar bakance ko rantsuwa da sauransu. Wanda tana sabawa saboda bambamcin yanayi.

6-     Kana kuma sallolin nan biyar na rana suna da sharudda guda biyar su ne:

1-     Lokacin Salla

2-     Al-kibla.

3-     Wurin da za’a yi sallar

4-     Tufafin mai salla

5-     Tsarki yayin sallar.

Sai Babana ya ce: ya kamata kada ka zaci cewa wadannan sharudda guda biyar ba lallai ba ne a same su a sallolin da ba guda biyar dinnan ba -wato na daga sallolin wajibi da na mustahabbi - domin dole a sami wadannan sharudda amma banda na farko a cikinsu daga baya abubuwan za su bayyana maka in Allah ya yarda.

A halin yanzu zan koma da baya dai in yi maka cikakken bayani kan daya bayan daya na daga wadannan sharudda guda biyar:

T: Wato yanzu za ka fara da lokacin sallah kenan?

A: Na’am da na farkonsu.

1-     Lokacin sallah: kowani daya daga cikin sallolin rana yana da takamaimen lokaci nasa baya halatta a saba masa, lokacin sallar asuba daga fitowar alfijir zuwa fitowar rana. Kana lokacin sallar “Zuhrain” (Azahar da la’asar) daga lokacin da rana ta gota tsakiya (zawal) zuwa faduwarta, sannan farkon lokacin ya kebanta ga azahar ne kawai kana karshensa ga la’asar kawai gwargwadon yadda mutum zai iya yin su.

T: Yaya ne zan iya gane rana ta gota tsakiya, wato wannan lokaci da shi ne farkon lokacin “zuhrain”?

A: Shi ne rabin lokaci tsakanin fitowar rana da faduwarta.

Amma lokacin sallar “lsha’ain” (magriba da lsha) shi ne daga farkon faduwar rana har zuwa tsakiyar dare, kana farkon lokacin ya kebanta ne da sallar magrib kana karshensa da sallar lsha gwargwadon yadda mutum zai yi ta.

[Ba za ka fara sallar magriba ba sai bayan jaja-jajan da ke gabas dinnan ya bace).

T: Mene ne jaja-jajan dake gabas kuma?

A: Shi ne launi ja dinnan da ke sama ta bangaren gabas lokacin da yake bacewa shi ne bayan faduwar rana.

T: Yaya zan iya gane tsakiyar dare, wannan lokaci da shi ne lokacin da sallar lsha take karewa?

A: Shi ne tsakiyan lokacin da ke tsakanin faduwar rana da fifowar alfijir.

T: Idan har dare ya zo tsakiya har ma ya wuce ban yi sallar magriba da lsha ba da gangan fa?

A: [Wajibi ne gare ka da ka gaggauta ka sallace su kafin ketowar alfijir da niyyar kusanci wato ba tare da yin niyyar yin su akan lokaci ko ramuwa ba]

Dole ka lura da wannan abu wato cewa dole ka tabbatar da shigan lokaci kafin ka fara salla shin sallar asuba ce ko azahar ko la’asar ko magriba ko lsha.

2-     Al-kibla: Dole ne ka fuskanci al-kibla lokacin da kake sallah, al-kibla kuwa- kamar yadda dai ka sani- ita ce gurbin da dakin ka’aba madaukakiya yake a birnin Makka.

T: To idan na gagara gano al-kibla fa bayan na yi dukkanin iyakacin kokarina amma na gagara samo wata hujja da zan dogaro da ita don gano al-kibla?

A: Sai ka yi salla ta jihar da kake zaton al-kiblar tana ta gurin.

T: To idan kuma babu wani bangare da ya rinjayi dan’uwansa fa?

A: To sai ka yi salla ta dukkan jihar da kake tsammanin samuwar al-kiblar ta gurin.

T: To idan na kudure cewa wata jihar shi ne inda al-kiblar take sai na yi salla ta gurin, sai daga baya sai na gane ashe kuskure ne fa?

A: Idan har kuskurenka daga al-kibla yana tsakanin dama da hagun ne, to sallarka ta inganta… amma idan juyawan naka ya wuce haka ko kuma sallar taka ta akasin al-kibla din ka yi kuma lokacin sallar bai fita ba sai ka sake sallar, to amma idan lokacin nata ya fita to ba wajibi ne ka rama ba.

3-     Wurin mai salla: [Ya kamata ka gane cewa wurin da za ka yi salla dole ya zama na halal, domin salla a wurin kwace ba ya halatta]

Sannan ana kirga abu a cikin abin kwace duk wani abin da ya wajaba a cire “khumsi” a cikinsa amma ba’a cire ba shin wannan abu gida ne ko kuma abin shimfidawa da sauransu, zan maka cikakken bayani kan abubuwan da ake cire “khumsi” a cikinsu a (Tattaunawa kan khumsi) nan gaba, kawai a nan na kawo shi ne don in yi gargadi kan fadawa cikin ramin gafala, neman sauki da rashin damuwa, wannan rami da dayawa suka fada ciki kana suka ki fitar da hakkin Allah daga cikin dukiyoyinsu.

T: Mu dauka cewa kasa ko wurin (da za’a yi salla a kai) ba na kwace ba ne amma abin da aka shimfida a wurin na kwace ne fa?

A: Shi ma dai [Sallarka bata inganta ba a kan wannan shimfida]

Sai Babana ya ci gaba da cewa:

- Kana dole ne wurin sujadarka ya zamanto tsarkakakke ba mai najasa ba.

T: Shin abin da kake nufi da wurin sujada shi ne wurin ajiye goshi?

A: Na’am, tsarkin wurin sujada kawai, wato “Turba” da makantansu wanda ake sujada a kansu.

T: To sauran wuraren sallar, misali wurin kafafu da wuraren da sauran jiki suke fa?

A: Ba’a shardanta tsarkinsu ba. Idan da suna da najasa amma najasar tasu bata damfaruwa jikin mutum to sallah a gurin ya halatta.

 Sannan abin da ya saura shi ne wasu abubuwa da suka shafi wurin mai salla, zan yi maka bayani a kansu.

A-    Ba ya halatta a cikin salla ko kuma a waninta juya baya wa kabarin ma’asumai (a.s) in har a hakan akwai wani nau’i na sabawa ladabi.

B-    [ Sallar dukkan namiji da macen da suka yi salla kurkusa a gefen juna ko kuma macen tana gaba bata inganta] sai dai idan ratan dake tsakanin inda yake sallar da inda take yi ya fi zira’i goma na hannu ko kuma a tsakaninsu akwai wani abin da ya kare su kamar katanga misali.

C-    Mustahabi ne yin salla a masallaci, masallatai da suka fi saura su ne masallacin ka’aba da masallacin Annabi (S.A.W.A.) da masallacin kufa da masallacin kudus (al-Aksa). Kamar yadda mustahabi ne salla a Hubbaren ma’asumai (a.s).

- Abin da ya fi ga mace ta zabi: gurin da ya fi kowanne suturcewa don yin salla hatta a cikin gidanta.

A . Tufafin Mai salla: tana da sharudda kamar haka:

a-        Ya kasance mai tsarki [kana ba na kwace ba] ko da yake sharadin halaccin tufafi ga abin da ake rufe al’aura ne kawai, ko da yake haka din ma ya bambanta tsakanin namiji da mace domin ga namiji halaccin musamman tufafin da yake ciki kamar gajeren wando ya kan wadatar amma hakan ba ya wadatarwa ga mace saboda fadin abin da ya kamata ta rufa a salla shi ne dukkan jikinta in banda abin da aka kebance.

b-       Kada ya kasance daga bangarorin mushe da rai ke sauka kamar fatar dabbar da aka yanka yankan da ya saba wa shari’a [ko da kuwa shi kadai ba ya wadatarwa ya kasance abin rufe al’aura].

T: Shin salla tana inganta da bel na fata da aka samu a hannun musulmi ko kuma wadda aka yi a kasashen musulmi koda yake ba’a san tsarkinsa ba?

A: Na’am salla tana inganta da shi.

T: To bel na fata da aka samu a hannun kafirai ko kuma wadda aka yi a kasashen kafirai fa?

A: Salla tana inganta da shi [sai dai in ka san cewa an ciro shi ne daga dabbar da ba’a yanka ta ba].

T: To idan ban tabbatar kan cewa wannan bel na fata misali an yi shi ne daga fata na al’ada ko kuma daga sana’antacciyar fata ba ce fa (wato na kamfani)?

A: Salla tana halatta da shi a kowani irin hali ne.

c-        Kada tufafin mai salla ya kasance daga bangarorin muggan namun daji idan har za’a rufe al’aura da shi [har ma da wasunsu wadanda ba’a cin namansu]

d-       Kada ya zamanto na siliki (harir) ne ga maza amma ga mata kan yana halatta.

e-        Kada ya zamanto na zallan zinari ko wanda aka hada shi da wani abu in dai har za’a iya kiransa da zinare, amma banda wanda aka kwai kwaya, ko da yake wannan hukumcin ya shafi maza ne kawai.

T: Ko da zoben hannu ko kuma munduwan aure ne?

A: Ko da zoben hannu ko munduwan aure ne, sallar bata inganta da shi ga maza, kamar yadda yake haramun ne ga namiji sanya zinare a kowani irin hali.

T: Ko da lokacin da ba na salla ba?

A: Ko da yaushe,…ko da yaushe hatta lokacin da ba na salla ba.

T: To hakwaran zinaren da ke cikin baki wanda ake kerawa wa wadansu mazajen, da kuma agogo na zinare wanda wadansu suke sanyawa a cikin aljihunsu fa? 

A: Waddannan sun halatta wa mazaje, salla tana inganta tare da su.

T: Idan mutum bai san cewa zobensa na zinare ba ne sai ya yi salla da shi, ko kuma ya san na zinare ne amma sai ya mance ya yi salla da shi sannan sai bayan ya idar da sallar sai ya sani ko kuma ya tuna fa?

A: Sallarsa ingantacciya ce.

T: To mata fa…?

A: Ya halatta gare su su sanya zinare a kowani hali kuma sallarsu tana inganta da shi.

·        Abin da kawai ya saura mai muhimmaci a al’amarin tufafin mai salla shi ne cewa wajibi ne ga mazaje su rufe al’aurarsu ya yi n sallah su ne zakari,da ‘ya’yan marena da duburarsa kawai.

Kana yana wajaba ga mace da ta rufe dukkan jikinta ya yi n salla hakan ya hada har da gashinta ko da kuwa ita kadai ce babu mai ganinta in banda fuskarta gwargwadon inda rufin kai baya rufe shi, da tafin hannu zuwa gabobinsu da kafafunta zuwa farkon kwabri.

Waddanan su ne abubuwan lura a salla-inji Babana amma ita salla da kanta wani aiki ne wanda ya kumshi wasu abubuwa da kuma wajibai, su ne: Niyya, kabbarar harama, tsayuwa, karatu, zikr, ruku’u, sujada, tahiya da sallama inda ake lura da jerantawa da gaggautawa a cikinta kamar yadda za ka gani nan gaba.

T: Me yasa baka fara da kiran salla da lkama ba?

A: Kafin in amsa maka wannan tambaya taka zan so in tunatar da kai cewa wasu daga cikin wadannan ayyuka ana kiransu da “Rukuni” ne, su ne: Niyya, kabbarar, harama, tsayuwa, ruku’u da sujada.

Hakika wadannan suna da wata kebantuwa ta musamman daga sauran ayyukan wajibi ta inda salla takan baci idan aka bar su da gangan ko da mantuwa.

To yanzu zan komo kan amsar tambyarka:

Kiran salla da ikama a sallolin kowace rana na wajibi suna daga cikin mustahabai da aka karfafa wadda yana da kyau mai salla ya zo da su, ko da yake kuma yana halatta a gare shi da ya bar su.

Sai Babana ya ci gaba da cewa:

Ina fatan ba za ka bar kiran salla da ikama a cikin sallolinka na wajibai ba a kowace rana domin kada ka rasa ladansu.

T: To idan ina so in kira sallah, yaya zan yi kiran sallar?

A: Sai ka ce:

Allahu Akbar                                                                                                          sau hudu

Ash-hadu An-lailaha illallah                                                                                      sau biyu

Ashhadu Anna Muhammadar rasulullah                                                                    sau biyu

Hayya alas-salah                                                                                                      sau biyu

Hayya alal falah                                                                                                        sau biyu

Hayya ala-khairil Amal                                                                                             sau biyu

Allahu Akbar                                                                                                           sau biyu

Lailaha illallah                                                                                                           sau biyu.

T: To ikama fa?

A: A ikama sai ka ce:

Allahu Akbar                                                                                                           sau biyu

Ashhadu An-lailaha illallah                                                                                       sau biyu

Ashhadu Anna Muhammadar rasulullah                                                                    sau biyu

Hayya alas-salah                                                                                                      sau biyu

Hayya alal-falah                                                                                                       sau biyu

Hayya ala khairil Amal                                                                                             sau biyu

Kad- kamatis salah                                                                                                  sau biyu

Allahu Akbar                                                                                                           sau biyu

La ilaha illallah                                                                                                         sau daya.

T: To shahada kan wilayar Imam Ali, Amirul muminina fa?

A: To ita cikon shaida ce kan sako kuma mustahabi ce, sai dai ita ba bangare ne na kiran salla ko lkama ba.

T: Wato abu na farko a salla kamar yadda ka ambata ita ce Niyya ko?

A: Na’am

T: To mece ce niyya ko kuma yaya ake yin niyyar?

A: Shi ne ka kudurta yin salla wato da jingina ta ga Ubangiji mai girma jinginawa irin ta kaskantar da kai.

T: Ina son karin bayani kan kalmar (jinginawa irin ta kaskantar da kai)?

A: Anan ana nufin wani aiki ne da mutum zai yi tare da jingina shi da ibada ga Allah ta yadda da wannan aiki mutum zai ji cewa shi kaskantaccen bawa ne gaba ga Ubangijinsa madaukaki.

T: To shin niyya tana da wata takamaimiyar lafazi ne?

A: A’a, ita kawai wani aiki ne na cikin zuciyar dan’adam, ba na harshe ba don haka ba ta da wani takamaimen lafazi matukar dai inda ake yin ta shi ne zuciya. Ko da yake idan baka kudurta yin salla don neman kusanci da kuma kaskantar da kai ga Allah ba ta hanyar ayyukanka da kake yi to sallarka bataccyia ce.

Abu na biyunsu : wato kabbaran harama.

T: Mece ce kabbarar harama?

A: Ita ce ka ce: Allahu Akbar, a halin kana tsaye akan kafafunka a tabbace kana kuma kana fuskantar al-kibla…za ka fade ta ne da larabci kana ka bayyana sautin harafin “al-hamza dinnan na kalmar (Akbar) haka ma sauran haruffan. Abin da ya fi shi ne ka bambance tsakanin kabbarar harama da farkon suratul fatiha da dan shiru kadan don kada ka hada kabbarar haraman da farkon suratul Hamd (fatiha).

T: Ka gaya min cewa dole ka yi kabbara alhali kana tsaye a kafafunka, to kamar misali idan ba ni da lafiya ta yadda ba zan iya tsayawa a kan kafafuna ba ko da da dogaro a kan sanda ko a jikin ganuwa da makamancinsu, to yaya zan yi salla?

A: Sai ka yi salla a zaune, idan hakan ma ba za ka iya ba sai ka yi a kwance ta bangarenka na dama ko hagu fuskanka yana fuskantar al-kibla [wajibi ne ka gabatar da bangaren dama kan hagu idan har hakan zai yiwu].

T: Idan kuma ba zan iya ba fa ?

A: Sai ka yi a rigingine kafafunka suna fuskantar al-kibla.

T: To idan kawai zan iya tsayuwa ne lokacin kabbarar harama amma ba zan iya ci gaba da tsayuwar ba fa?

A: To ya wajaba gare ka ka yi kabbarar a tsaye kana ka ci gaba da sallarka a zaune ko a kwance kamar yadda na yi maka bayani.

Abu na ukunsu: karatu.

 Tana zuwa ne bayan kabbarar harama inda za ka karanta fatiha [da wata cikakkiyar sura bayanta] lngantacciyar karatu ba tare da kura -kurai ba kuma kada ka mance fa da karanta bismilla a farkon kowace sura banda suratut Tauba kamar yadda za ka tarar a Al-kur’ani.

T: To idan babu lokacin da zan karanta sura ta biyun fa wato waccan surar nan da ake karanta ta bayan fafiha?

A: Sai ka bar karanta surar ka karanta fatiha ita kadai…haka ma za ka aikata idan ba za ka iya karanta sura ta biyu ba bayan suratul Hamd saboda rashin lafiya, ko kuma kana halin gaggawa ko tsoro.

T: To yaya zan karata wadannan surori guda biyu?

A: [Wajibi ne ga namiji ya karanta wadannan surori a bayyane a sallolin asuba, magrib da lsha wato biyu na farko kana kuma a sallolin azahar da la’asar ya karanta su a boye].

T: To mata fa?

A: Babu bayyanawa ga mata sai dai [wajibi ne gare ta da ta boye a sallolin azahar da la’asar.].

T: Idan na jahilci hukuncin bayyanawa ko boyewa a cikin salla ko kuma na mance na karanta wadannan surori guda biyu ko kuma wani bangare nasu a boye alhali ni kuma ina sallar asuba ko magriba ko isha ne, ko kuma na karanta su ko wani bangare nasu a bayyane alhali ina sallar azahar ne ko la’asar wato akasin abin da ake so?

A: Sallarka ta inganta.

T: To wannan shi ne abin da zan karanta a raka’oin farko da na biyu, to me zan karanta a raka’a ta uku da ta hudu?

A: Kana da zabi a raka’oi na uku da hudu ko ka karanta fatiha ita kadai ko kuma ka karanta “Tasbihat” [ko da yake a dukkan halayen guda biyu a boye za ka karanta] in banda bismilla domin ita kana da hakki ka bayyana ta shin kana limanci ne ko kuma kana salla kai kadanka ne.

T: Idan na zabi “tasbihi” to me zan fada a ciki?

A: Ya wadatar in ka ce a boye: subhanallah, wal-hamdu lillah, wa lailaha illallah, wallahu Akbar sau daya ko mafi kyau sau uku.

T: To shin akwai wasu abubuwan lura kuma a bangaren karatu?

A: Na’am, ya yi n da kake karatunka a tsanaki to abin da ya fi fasaha shi ne ka dinga sa wasali a karshen kalmomin kowanne gwargwadon li’irabinsa, amma idan karshen kalmomin a daure suke to ba’a yin musu wasali, idan ka zo tsayawa a kan kalma, abin da ya fi fasaha shi ne ka daure haruffan karshen.

Kana bayan haka wajibi ne gare ka ka ja harafin “Alif” takaitaccen ja lokacin da kake karanta kalmar (al-Dwalin) na karshen suratul Hamd don ka kiyaye shaddar da ke gurin da kuma alifin a ingantaccen yanayi.

T: To bayan haka fa?

A: Idan “hamzatul wasl” ta fado a tsakiyar kalma a karatunka sai ka shafe ta amma banda farkonta kana kuma ka bayyanar da “hamzatul kad’I” ta yadda zai bayyana sosai akan harshenka lokacin da ka tsaya.

T: Ba ni misalin “hamzatul wasl” da “hamzatul kad’I”.

A: Hamzar da misali take cikin wadannan kalmomi:

(Çááå¡ ÇáÑÍãä¡ ÇáÑÍíã¡ ÇåÏäÇ)  

“hamzatul wasl” ce kada ka bayyana su a harshenka ya yi n da kake sadar da karatu kana ci gaba da yin sa sannan kuma hamzar da misali take cikin kalmomin (ÇíÇß¡ ÇäÚãÊ) hamzatul Kad’I ne za ka bayyanar da su don su fito fili a kan harshe lokacin da kake ambatonsu, sannan

T: Sannan me?

A: Sannan idan kana so ka karanta suratul Tauhid bayan fatiha wato idan ka zabe ta tsakanin sauran surori to abin da ya fi maka sauki lokacin da ka zo wajen kalmar “Ahad” ya yi n da kake karanta ayar nan mai girma ta (Þá åæ Çááå ÇÍÏ) sai ka dan tsaya, kuma ka yi dauri a karshen ayar wato ka dan tsaya kadan kafin ka karanta ayar da take biye mata wato (Çááå ÇáÕãÏ) .

Kana babana ya ci gaba da cewa:

Saboda ka kyautata karatunka lokacin da kake salla, ina maka nasiha da ka dinga salla a bayan wanda yake kyautata sallarsa don ya tsara maka karatunka da sallarka, idan hakan kuwa zai yi maka wahala to alal akalla ka yi kokari ka iya karanta surorin nan guda biyu (fatiha da surar da take biye mata) dai-dai da karatun daya daga cikin mutanen da aka shaida sun iya karatu, ka dinga karantawa tare da su don ka kyautata karatunka ta hanyar tasu.

A wannan lokacin ne za ka iya gane kura -kurenka- idan har akwai su-don ka gyara su. Hakan shi ya fi maka da ka ci gaba da karatu cikin kuskure wanda yake tare da kai tun daga yaranta ta yadda in har ka gano kuskuren naka daga baya zai zama kenan ka yi shekaru da dama kana salla da karatun da yake da kura-kurai.

Abu na hudunsu : Tsayuwa, ma’anarsa a fili yake amma zan so in yi nuni da cewa shi tsayuwa shi ne kadai bangare daga cikin bangarorin salla da yake da siffofi biyu, su ne, ya kan iya zama rukuni misali tsayuwa lokacin kabbarar harama da tsayuwa gabannin ruku’u wanda ake bayyana shi da tsayuwar da ke haduwa da ruku’u wanda yake da hukuncin rukuni, kana tsayuwa yana kuma iya zama wajibin da ba rukuni ba kamar tsayuwa ya yi n karatu ko “tasbihi” da tsayuwa bayan ruku’u inda a wannan halin hukuncin wajibi ne yake gudana a gare shi banda na rukuni.

Abu na biyar dinsu: Ruku’u.

Bayan karatun surorin nan guda biyu dole ne ka yi ruku’u.

T: Yaya ne zan yi ruku’un?

A: Ka sunkuya har kan yatsun hannunka su isa ga gwiwoyinka, kana lokacin da ka daidaita a ruku’u sai kuma ka ce: (subhana rabbiyal azim wa bi hamdihi) sau daya, ko kuma ka ce: (subhanallah) sau uku ko (Allahu Akbar) sau uku ko (Alhamdu lillah) sau uku da dai sauransu wadanda za’a iya kiran su zikiri kamar hailala (lailaha illallah) sau uku.

Sannan ka mike daga ruku’unka, kana ka tsaya, ya yi n da ka tsaya kyam sai ka sauka zuwa sujada.

Na shidansu: Sujada.

Wajibi ne a kowace raka’a ka yi sujada guda biyu.

T: Yaya zan yi sujadar?

A: Shi ne ka sanya goshinka da tafukan hannunka da gwiwoyinka da manyan yatsun kafarka a kasa.

Sannan an shardanta a abin da za ka yi sujada akai wato abin da za ka sanya goshinka akai ya zamanto daga kasa yake, ko kuma daga tsirrai da ba’a ci kana kuma ba’a sawa (wato ba’a yin tufafi da shi).

T: Ban misalin abubuwa da ba’a sujada a kansu don saboda abinci ne ko abin sawa?

A: Nau’in abinci da ake tonowa kamar dankali ko doya da ‘ya‘yan itatuwa ba ya halatta ayi sujada a kansu  don suna daga abin da ake ci, kana kuma auduga da kittani bai halatta ayi sujada a kansu  ba don su abubuwa da ake sawa ne.

T: To a kan mene ne zan yi sujada?

A: Za ka yi sujada ne akan turbaya ko yashi ko tsakuwa ko dutse ko katako (ko ko ice) abin da ba’a ci na daga ganyen bishiya…sannan kana iya sujada akan takardar da ake amfani da ita wajen rubutu idan an yi ta ne da katako ko auduga ko kittani sannan za ka iya sujada akan buntu da sauransu.

Amma ba za ka iya yin sujada akan alkama ko shinkafa ko auduga ko gashin dabba ko kwalta ko kwalba ko gilashi ba amma abin da ya fi kyau ka yi sujada akai shi ne kasa (turbaya) kana kasar da ta fi ita ce “Turbatul Husainiyya”, amincin Allah ya tabbata ga ma abucinta.

T: To idan ba zan iya sujada akan abin da ya inganta ayi akansa ba saboda rashinsa misali ko kuma saboda tsoro kamar a halin “takiyya”?

A: Idan ba ka da abin da ya inganta ayi sujada akai sai ka yi sujada akan kwalta to idan hakan bai samu ba sai ka yi abin da ya sauwaka…ko akan tufafinka ko akan tafin hannunka. Idan kuma kana halin “takiyya” ne to sai ka yi sujada akan abin da “takiyya” ta tanadar.

Babana ya ce haka kana ya ci gaba:

Amma kada ka mance fa cewa lalle ne inda za ka yi sujada ya zamanto dai-dai da inda gwiwoyinka da babbar yatsar kafafunka suke kada dayansu ya yi sama da daya fiye da tsawon yatsu hudu a hade [haka ma wurin sujadarka da wajen tsayuwarka] su ma su zama daidai.

T: To idan na sanya goshina da tafukana da kuma manyan yatsun kafafuna da gwiwoyina akan kasa, to me zan yi kuma?

A: Bayan ka daidaita a sujada sai ka ce:(subhana rabbiyal Aala wa bi hamdihi) sau daya, ko kuma ka ce: (subhanallah) sau uku, ko kuma (Allahu Akbar) sau uku ko (Alhamdu lillah) sau uku ko kuma makamancin wadannan na daga zikirori.

Sannan sai ka dago daga sujada ka zauna, in bayan ka zauna ka nitsu, sai ka koma ga sujada ta biyu ka karanta abin da ka zaba na daga zikirorin da suka gabata, na sujada.

T: To idan ba na iya sujada sosai saboda rashin lafiya misali?

A: Ka yi kokarin kaga ka sunkuya sosai gwargwadon iyawarka, sannan sai ka sanya abin da za ka yi sujada akai akan wani abu mai tudu kana sai ka sanya goshinka akai amma tare da la’akari da sauran gabobin sujada a wurarensu.

T: Idan hakan ma ba zan iya ba fa?

A: Sai ka yi nuni da kanka zuwa wajen sujada, idan hakan ma ba zai yiwu ba, sai ka yi nuni da idanunka rufe idanu ya zan shi ne sujjada bude su kuma dagowa.

Na Bakwai dinsu: Tahiya.

Yana wajaba ne bayan sujada ta biyu na daga raka’a ta biyu na kowace salla, kana da kuma raka’a ta karshe na sallolin magriba, azahar, la’asar da isha.

T: To me zan ce a cikinta?

A: Ka ce: [Ashhadu An-lailaha illallah wahdahu la-sharika lahu, wa ash hadu anna muhammadan abduhu wa rasuluhu Allahumma salli ala Muhammadin wa ali muhammadin] za ka fadi haka ne da siga ingantacciya kana a zaune cikin nitsuwa.

Na Takwas dinsu: sallama

Shi wajibi ne a kowace raka’a ta karshe na kowace salla, za ka yi sallaman ne bayan tahiya alhali kana zaune cikin nitsuwa.

T: Me zan ce yayin sallama?

A: Ya wadatar in ka ce: (Assalamu Alaikum) amma abin da ya fi ka kara: (Wa rahmatullah wa barakatuhu) ko da yake duk abin da ya fi ka ce gabanninsa, (wato sallamar): (Assalamu Alaika ayyuhan Nabiyyu wa rahmatullahi wa barakatuhu, Assalamu alaina wa ala ibadillahis Salihin).

Wadannan su ne juzu’oin salla, za ka yi su ne daya bayan daya a jere kamar yadda na fasalta maka, ba tare da ka kawo wani jinkiri a tsakaninsu ba ta yadda za ka bata siffar da hadewanta.

T: To amma ai ba ka ambata min “kunuti” ba ga shi kuwa ina ganin kana daga hannayenka don “kunut” a kowace sallarka?

A: “Kunut” ai mustahabi ne ana yin ta sau daya ne a sallolin rana da ma waninta (in banda sallar shafa’I) za ka daga hannayenka don yin “kunut” bayan karatun surorin nan guda biyu a raka’a ta biyu kafin yin ruku’u idan ka so aikata mustahabbi.

T: Shin akwai wata addua ta musamman ne da zan fada?

A: A’a, za ka iya karanto duk wata ayar al-kur’ani da a cikinta akwai neman wani abu daga wajen ubangiji (du’a), ko kuma za ka iya karanta duk wata adduan da ka ga dama.

T: Hakika yanzu na koyi yadda zan yi salla daga wajenka, da kuma abin da zan ce ko aikata yayin kowani juz’i na salla yanzu. Zan so tambayarka abubuwan da suke bata salla. Shin akwai abubuwan da suke bata salla wadanda idan na aikata su sai na sake sallar?

A: Na’am, yanzu zan kirga maka su:

  1. Barin daya daga cikin juzu’in salla da suka gabata da gan-gan kamar: niyya ko kabbarar harama ko ruku’u ko sujada da sauransu.
  2. Mutum ya yi “hadasi” ya yi n sallarsa [ko da kuwa da rafkanwa ko ala tilas ne bayan sujada ta karshe].
  3. Juyawa da dukkan fuska ko jiki daga al-kibla da gangan.

T: To idan juyawan nasa daga kibla bai kai wannan haddin ba fa kamar idan juyawan kadan ne ta yadda bai cutar da fuskantarsa ga al-kibla ba?

A: Hakan ba ya cutar da salla amma dai abin ki ne.

  1. Yin dariya da karfi da gangan.
  2. [Yin kuka da gangan kan al’amarin duniya shin da karfi ne ko kuma a’a] amma kuka kan al’amarin lahira ba ya cutarwa.
  3. Yin magana da gangan a cikin sallah ko da kuwa da harafi daya ne in dai har za’a iya fahimtansa shin yana so ya fahimtar da ma’anarsa ne kamar ya ce (Þ) fi’ilin umurnin na kalmar (æÞì) ko kuma ba ma’anarsa yake nufi ya fahimtar ba kamar da za’a tambayi mene ne harafi na biyu na haruffan larabci sai yace (È) to amma an fıtar da amsa sallama da misalinsa daga cikin abubuwan da suke bata salla shi kan ma wajibi ne, bai bata salla.
  4. Mai salla ya yi wani abin da zai tafiyar da surar salla din ko yanayinta kamar dinki ko saka.
  5. Mai salla ya ci abinci ko ya sha abin sha a cikin salla [ko da hakan ba zaı tafıyar da sifar sallar ba]
  6. [Mutum ya sanya hannunsa akan daya da gangan lokacın da yake tsaye ba kuma a halin takiyya ba] abin da ake kıra da Takfır” (wato kabalu)
  7. Ganganta fadin kalmar “Amin” da “mamu” zai fada bayan liman ya kare karatun fatiha [ko kuma mutum in yana salla shi kadai] ba’a halin takiyya ba kuma.

Sannan bayan haka akwai wani al’amari da na ga yana da kyau in yi ishara gare shi, shi ne “Shakka” a cikin salla.

T: Shin shakka a salla yana bata ta ne?

A: Ba’a kowani lokaci ba ne shakka yake bata salla, wasu shakkokin ne suke bata salla. Wasu kuwa ana iya gyara su kana wasu kuwa ma ba’a damuwa da su.

Yanzu bari in gaya maka wasu kaidoji gamammu wadanda za su magance maka wasu halaye na shakka.

Kaida Ta farko: Duk wanda ya yi shakka kan ingancin sallarsa bayan ya kare sallar to sallar lngantacciya ce.

T: Ba ni misali?

A: Misali idan ka yi shakka bayan ka kare sallar asuba shin raka’a biyun kuwa ka yi ko fiye ko kuma kasa da haka ka yi? To ka dauka sallarka dai-dai ka yi ta.

Kaida Ta Biyu: Duk wanda ya yi shakka kan wani juz’I daga juzuoin salla bayan ya riga ya yi shi, to ya dauki wannan juz’in da ya yi shakka akai ingantacce kana sallarsa ta inganta.

T: Ba ni misali?

A: Misali idan ka yi shakka kan ingancin karatunka, ko ingancin ruku’unka ko sujadarka bayan ka gama karatun ko ruku’un ko sujadar, to ka dauka karatunka ko ruku’un naka ko sujadar taka ingantacciya ce…kana kuma sallarka ta inganta.

Kaida Ta uku: Duk wanda ya yi shakka kan aikata wani juz’i daga cikin juzuoin salla bayan ya shiga wani aiki da ke biye masa, to sai ya dauka cewa ya riga ya aikata wannan juz’i da yake shakka a kansa sannan sallarsa ta inganta, kai ya kan wadatar ma akan hakan kawai shiga wani aikin salla da gangan wanda a shar’ance bai kamata ya shiga ba idan da ya bar wani juzu’i da ke gaba.

T: Ban misali akan hakan?

A: Misali, idan ka yi shakka lokacin da kake karanta sura ta biyu shin ka karanta fatiha kuwa ko kuma ka mance baka karanta ta ba, to sai ka dauka ka karanta ta kana ka ci gaba da sallarka, ko kuma idan ka yi shakka lokacin da kake sauka zuwa ga ruku’u shin ka karanta sura ko ba ka karanta ba? Sai ka dauka ka karanta kana ka ci gaba da sallarka, sallar ta inganta.

 Kaida Ta Hudu Mai yawan shakka da har shakkar tasa ta wuce haddi da aka saba, to sai ya mance da shakkar kada ya damu da ita. Kana sallarsa da ya yi shakkar a ciki ta inganta

T: Ba ni misali?

A: Misali, idan kana yawan shakka misali a sallar asuba kan adadin rakaointa to kada ka damu da wannan shakkar ka dauki sallar taka a matsayin ingantacciya.

Ko kuma kana yawan shakka kan shin sujada daya ka yi ko dukkansu biyun, to ka dauka sujada biyu ka yi kada ka damu da shakkar face ma dai sallarka ingantacciya ce, da dai sauransu A koda yaushe mai yawan shakka kada ya damu da shakkar tasa… koda yaushe…koda yaushe.

T: Yaya zan yi in san cewa ni mai yawan shakka ne?

A: Cikin sauki mai yawan shakka zai gane kansa…ya isa ace shakkarsa ta wuce ta mutane irinsa ko kuma babu yadda zai yi ya yi salloli guda uku face sai ya yi shakka a daya daga cikinsu.

Kaida Ta Biyar: Duk wanda ya yi  shakka cikin adadin raka’oin sallar asuba ko kuma sallar magriba ko rakaoi biyu na farkon duk wata salla mai raka’a hudu, sannan a cikin zuciyarsa daya bangare bai rinjayi dayan ba, kana kuma wani adadin raka’a bai zo masa cikin zuciyarsa ba, ya dai tabbata akan wannan shakka tasa bai san yawan raka’oin da ya yi  ba to sallarsa ta baci.

T: Ba ni misali?

A: Misali, idan yana sallar asuba sai ya yi  shakka shin a halin yanzu yana raka’a ta farko ne ko ta biyu, sai ya dan yi tunani, to idan bai isa ga wani takamaimen sakamako ba kana kuma zuciyarsa ba ta tafi kan cewa raka’a ta farko ce ko kuma raka’a ta biyu ba to sallarsa ta baci.

T: To idan zuciyarsa ta fifita daya bangare kamar ta tafi akan raka’a ta farko ce fa?

A: Idan har zuciyarsa ta tafi akan wani adadi ayyananne to sai ya yi  aiki gwargwadon abin da wannan tsammani ya tanadar, misali idan har zuciyarsa ta tafi akan abin da ka tambaya wato raka’a ta farko ce, to sai ya zo da ta biyu kana ya cika sallar , sallarsa ta inganta.

Haka al’amarin yake a sallar magriba da kuma rakaoin farko da na biyu na kowace salla mai raka’a hudu.

T: A halin yanzu na san hukumcin shakka cikin sallar asuba da magriba da kuma rakaoin farko da na biyu na salloli masu rakaoi hudu na daga sallolin azahar, la’asar da isha, to amma mene ne hukuncin shakka cikin rakaoi guda biyu na karshe wato na uku da na hudu na salloli masu rakaoi hudu?

A: To idan har zuciyarsa ta fifita wani takamaimen adadi na raka’a to sai ya yi  aiki da abin da ya dace da zatonsa, da kuma gwargwadon abin da zuciyarsa ta tafi akai.

T: To idan ya ci gaba da kasancewa cikin demuwa da shakka fa?

A: A wannan hali yana bukatuwa da bayani mai yawa, domin kowani hali yana da hukuncin da ya kebantu da shi, zan kawo maka wasu a takaice ba zan tsawaita ba:

       1.  Duk wanda ya yi  shakka tsakanin raka’a ta uku da ta hudu a ko ina shakkar ta faru, to sai ya dauke ta a matsayin raka’a ta hudu ce kana ya cika sallarsa, sannan sai ya zo da rakaoi gudu biyu a zaune ko kuma raka’a daya a tsaye, ana kiran wannan salla da “salatul lhtiyat”.

       2.  Wanda ya yi  shakka tsakanin raka’a ta hudu da ta biyar bayan ya shiga sujada ta biyu (ko da daga sanya goshinsa akan abin sujada ne ba tare da ya fara tasbihi ba) to sai ya dauka raka’a ta hudu ne kana ya cika sallarsa sannan sai ya yi  sujadar rafkanwa guda biyu bayan sallar.

       3.  Wanda ya yi  shakka tsakanin raka’a ta biyu da ta uku bayan ya shiga sujada ta biyu sai ya dauke ta a raka’a ta uku ce kana sai ya zo da raka’a ta hudu bayanta, sannan bayan ya idar da sallarsa sai ya zo da “salatul ihtiyat” [amma a nan raka’a daya zai yi a tsaye].

T: Yaya ake yin “salatul ihtiyat” din?

A: Bayan mutum ya idar da sallarsa ba tare da juyawa ta dama ko hagu ba kana ba tare da aikata wani abin da yake bata salla ba sai ya fara “salatul ihtiyat”, sai ya yi  kabbara ya karanta fatiha [a boye] ba wajibi ba ne a karanta wata sura daban, sannan sai ya yi  ruku’u ya yi  sujada ya yi  tahiya kana ya yi  sallama idan “salatul ihtiyat” din mai raka’a daya ce, idan kuwa mai raka’a biyu ce sai ya zo da ta biyu kamar yadda ya yi  ta farko.

T: To yaya ake sujadar rafkanwar nan da ka ambata?

A: Bayan sallar sai ka yi niyya kana ka yi sujada amma abin da ya fi ka fara da kabbara, sai ka ce a cikin sujadarka: Bismillshi wa billahi Assalamu Alaika ayyuhan nabiyyu wa rahmatullahi wa barakatuhu, sannan sai ka daga kanka daga ruku’u kana ka zauna sannan ka koma ga sujada ta biyu kana ka daga sannan ka yi tahiyya kana ka sallame da haka ka kawo karshen sujadar rafkanwa.

Babana ya ci gaba da cewa:

Amma ko da yake ba wai kawai a shakka tsakanin raka’a ta hudu da ta biyar bayan sujadu guda biyu ne ake sujadar rafkanwa ba kawai, akwai wasu wuraren ma kamar haka:

A- [Idan ka yi magana bisa mantuwa da rafkanwa a cikin salla].

B-  [Idan ka yi sallama a wajen da ba na sallama ba wato idan ka ce: (Assalamu alaikum) ko kuma ka ce: (Assalamu alaina wa ala ibadillahis salihin) alhali kuwa ba ka idar da sallar ba].

C- Idan ka mance ba ka yi tahiyya ba sai ka yi sujadar rafkanwa amma duk da haka abin da ya fi shi ne ka rama tahiyar.

D- [Idan ka san cewa -bayan idar da sallarka-ka yi kari ko ragi a cikinta tare da kasantuwar ingancin sallar taka, to a wannan hali wajibi ne ka yi sujadar rafkanwa] kana abin da ya fi kyau ka yi sujadar rafkanwa a cikin sallarka idan ka mance sujada guda daya (amma bayan ka rama ta bayan sallar) ko kuma idan ka mike a wajen da ake zama ko kuma akasin haka, da rafkanwa kai abin da ma yafi shi ne ka yi sujadar rafkanwa a duk wani kari ko ragin da ka yi a cikin sallarka.

E-  Ana maimaita sujadar rafkanwa dai-dai adadin abin da ya wajabta ta wato sau biyu ko ma fiye da haka.

Lokacin da muka kawo wannan wuri a cikin al’amarin salla na so in bukaci Babana da ya koya min yadda ake yin salla mai raka’a hudu kasantuwa ita ce sallar rana mafi tsayi don in gano yadda babana yake kabbara, da karatu, ruku’u, sujada, tahiya da kuma sallama amma daga baya sai na dawo daga wannan bukata tawa lokacin da na yi tunanin cewa ai kowace rana yana sallar isha kuma ita ai mai raka’a hudu ce kuma a bayyane ake yin ta, sai na ce a zuciyata ai zan kula da shi lokacin da yake salla.

Lokacin da Babana ya zo zai fara wannan sallar mai raka’a hudu da ake yin ta a bayyane, sai na kasance cikin nitsuwa da lura kan duk wani motsi na sallarsa, bari in siffanta muku yadda babana ya yi  sallarsa:

Da farko dai ya fara da kyautata alwala.

Kana sai ya tsaya a wajen da yake yin salla yana mai fuskantar al-kibla cikin kaskantar da kai, ya kira salla (da ikama). Sannan sai ya fara sallarsa, ya yi  kabbara yana mai cewa (Allahu Akbar) kana ya karanta fatiha da suratul “Qadr”.

Lokacin da ya gama karanta ta alhali yana tsaye sai ya yi  ruku’u, lokacin da ya daidaita a cikin ruku’u sai ya fara tasbihi yana mai cewa: (Subhana rabbiyal azimi wa bi hamdihi).

Lokacin da ya gama tasbihinsa a halin ruku’u sai ya mike tsaye.

Lokacin da ya daidaita a tsayuwarsa sai ya tafi zuwa ga sujadda, lokacin da ya daidaita a sujadarsa sai yace: (Subhana rabbiyal aala wa bi hamdihi) lokacin da ya gama tasbihinsa sai ya daga daga sujada kana ya zauna, lokacin da ya daidaita a zaune sai ya tafi zuwa ga ta biyu, sai ya karanta abin da ya karanta a ‘yar’uwanta sujjda ta farko, wato: (subhana rabbiyal a’ala wa bi hamdihi).

Sannan sai ya daga kansa daga sujadarsa, ya zauna daga nan sai ya mike tsaye saboda raka’a ta biyu. Lokacin da ya daidata a tsayuwarsa, sai ya karanta fatiha kana ya biyo ta a wannan karon da suratul Tauhid, lokacin da ya gama karatunsa sai ya daga hannunsa don yin “kunut”, a “kunutin” nasa ya karanta wannan aya ta al-kur’ani mai girma ne, wato”

(ÑÈ ÇÛÝÑ áí æáæÇáÏí æáãä ÏÎá ÈÈÊí ãÄãäÇ æááãÄãäíä æÇáãÄãäÇÊ æáÇ ÊÒÏ ÇáÙÇáãíä ÇáÇ ÊÈÇÑÇ) 

Sannan sai ya sauke hannunsa daga “kunut”, kana ya tafi zuwa ga ruku’u, lokacin da ya daidaita a ruku’unsa sai ya karanta: (subhana rabbiyal azimi wa bi hamdihi).

Kana sai ya mike tsaye don tafiya zuwa sujada, lokacin da ya yi  sujada sai ya karanta: (subhana rabbiyal A’ala wa bi hamdihi), sai ya dago daga sujadarsa ya zauna don tafiya ga sujada ta biyu, lokacin da ya yi  sujada ta biyu sai ya karanta: (subhana rabbiyal A’ala wa bi hamdihi) kana sai ya dago daga sujadarsa ya zauna.

Yayin da ya zauna sosai sai ya fara tahiyya yana mai cewa: (Ashhadu an lailaha illallah wahdahu la sharika lahu wa ashhadu anna muhammadan abduhu wa rasuluhu. Allahumma salli ala Muhammad wa aali Muhammad).

Lokacin da ya gama tahiyarsa sai ya mike tsaye don raka’a ta uku, bayan ya daidaita sai ya fara da tasbihi yana mai cewa: (subhanallah wal hamdu lillah wa lailaha illallah wallahu Akbar) sau uku a boye.

Daga nan sai ya tafi zuwa ruku’u ya karanta kamar yadda ya karanta a ruku’oinsa da suka gabata (subhana rabbiyal azimi wa bi hamdihi), kana sai ya dago daga ruku’unsa ya tafi zuwa sujada, ya karanta abin da ya karanta a sujadun da suka gabata wato (subhana rabbiyal aala wa bi hamdihi) kana ya dago ya zauna don komawa ga sujada ta biyu kana ya karanta (subhana rabbiyal aala wa bi hamdihi).

Lokacin da ya gama sai ya mike tsaye don raka’a ta hudu kana ta karshe, a ita ma ya fara da tasbihi kamar yadda ya yi  a wadda ta gabata, yana mai cewa: (subhanallah wal hamdu lillah wa lailaha laillah wallahu Akbar) sau uku.

Kana sai ya tafi zuwa ga ruku’u yana mai cewa: (subhana rabbiyal azimi wa bi hamdihi)

Sai ya dago don tafiya zuwa sujada yana mai cewa a cikinta (subhana rabbiyal aala wa bi hamdihi), sannan sai ya dago daga sujadar ya zauna don tafiya ga sujada ta biyu kana kuma ta karshe a wannan salla yana mai karantawa a cikinta-kamar yadda ya saba (subhana rabbiyal aala wa bi hamdihi).

Daga nan sai ya zauna a nutse don tahiyya yana mai karanta kamar yadda ya karanta a tahiyarsa ta farko: (Ashhadu an lailaha illallah wahdahu la sharika lahu, wa Ashhadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu, Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad).

Lokacin da ya gama tahiyarsa sai ya yi  sallama ga manzon Allah (S.A.W.A.) yana mai cewa: (Assalamu alaika ayyuhan nabiyyu wa rahmatullahi wa barakatuhu) sai ya cika sallarsa da cewa: (Assalamu alaina wa ala ibadillahis salihin), (Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu).

Haka dai babana ya yi  sallar isha, haka ma ya yi  sallar azahar da la’asar-domin su ma masu rakaoi hudu ne koda yake a boye ya karanta su.

Kana kuma na lura da shi, lokacin da yake sallar magariba, sai na ga ya yi  ta kamar yadda yake a sallar isha lokacin da ya gama sujada ta biyu ta raka’a ta uku, sai ya zauna ya yi  tahiyya kana ya yi  sallama, ya idar da sallarsa (don sallar magriba raka’a uku take da shi)

Sannan kuma na sake lura da shi ya yi n da yake sallar asuba, sai na ga yana yinta kamar yadda yake sallar isha, ko da yake lokacin da ya gama sujada ta biyu ta raka’a ta biyu, sai ya yi  tahiya kana ya yi  sallama, da haka ya gama sallarsa (don sallar asuba raka’a biyu take da shi).

Haka babana ya yi  sallolinsa na rana, ko da yake na lura da shi sosai, zan kawo muku wasu abubuwa da salla ta kebantu da su, kamar yadda na ga babana yana yi:

1-        Ya kasance yana kiyayewa sosai kan yin salla a farkon lokacinta, misali ya kasance ya kan sallaci sallar azahar ya yi n da lokacinta ya shiga wato ( gotawar rana daga tsakiya (zawal), kana yana sallar magriba akan lokacinta, da dai sauransu. Lokacin da na tambaye shi dalilin wannan gaggawa na yin sallar a farkon lokacinta, sai ya min bayani da hadisin Imam sadik (a.s) inda yake cewa: (fifikon farkon lokacin (salla) akan karshensa kamar fifikon lahira ne a kan duniya)

2-        Ya kasance ya yi n da ya tsaya gaba ga ubangijinsa don salla, za ka ga alamun tsoro da kaskantar da kai, kafin ya fara sallah ya kan karanta wannan aya:

 (ÞÏ ÃÝáÍ ÇáãÄãäæä ÇáÐíä åã Ýí ÕáÇÊåã ÎÇÔÚæä)

 da sauti da za’a iya ji, kamar yana kintsa kansa kafin ya fara salla don ya tunatar da zuciyar muhimmancin kaskantar da kai cikin salla.

3-        Ya kasance kafin ya yi sallar asuba ya kan yi raka’a biyu kana ya kan yi rakaoi takwas-rakaoi biyu-biyu kamar sallar asuba--gabannin sallar azahar da la’asar, sannan ya kan yi rakaoi hudu -biyu -biyu kamar sallar asuba--bayan sallar magriba kana ya kan yi rakaoi biyu a zaune bayan sallar isha.

Na sake tambayayarsa kan wadannan salloli:

Sai ya ce: Wadannan Su ne nafiloli, wadannan da aka ruwaito Imam Askari (a.s) yana cewa: (Wadannan suna daya daga alamomin mumini).

4-        To sabili da cewa wannan “al-hamza” da take kalmar (Akbar) na jumlar (Allahu Akbar) “hamzatul kad’I” ce, wato wajibi ne ka bayyana ta a fili akan harshenka lokacin da kake kabbara, haka babana ya ce.

Wani lokaci na tambaye shi cewa: Wasu mutane sukan ambaci wannan “hamza” kamar “wawun” kamar jumlar “Allahu wakbar” ce.

Sai ya ce: ina horonka da kada ka fadi kamar yadda suke fadi, domin kuskure ne suke yi. Sai ya ci gaba da cewa: al’amarin haka yake a cikin “hamzar” da take kalmar (ÇäÚãÊ) da take suratul fatiha (ÕÑÇØ ÇáÐíä ÇäÚãÊ Úáíåã) , ita ma “hamzatul kad’I” ce, wajibi ne ka bayyanar da ita a fili lokacin da kake ambatonta.

Misalinta iri daya ne da “hamzar” da take (ÇáÇÚáì)

 Na cikin (ÓÈÍÇä ÑÈí ÇáÇÚáì æÈÍãÏå) wadda ake yi a cikin sujada, ita ma “hamzatul kat’I” ce wajibi ne ka bayyana ta a fili lokacin da kake ambatonta

5-        Kana sai babana ya ce: ka yi kokari ka tsaya a harafin “Dal” da take kalmar (Qul huwallahu ahad).

Sai ka dan tsaya kadan kafin ka ci gaba da ayar da take biye mata wato (Allahus samad) hakan shi ya fi maka sauki da walwala.

6-        Babana ya kasance ya kan ambaci wasalin karshen kalmomi a sallarsa idan yana son ya ci gaba da su amma ya kan daure harfofin karshe na daga kalmomin da yake so ya tsaya a kansu.

7-        Wani lokaci na tambayi babana: Na ji ka lokacin da kake karanta inda Allah yake cewa: (Bismillahir rahmanir rahim) ka kan yi kisira wa harafin “Nun” na kalmar (ÇáÑÍãä ) da kuma harafin “min” na kalmar (ÇáÑÍíã )  Haka ma kake yin kisira ya yi n da kake karanta (ÇáÑÍãä ÇáÑÍíã ãÇáß íæã ÇáÏíä ) na suratul Hamd, Tattare da cewa na kan ji da yawa daga cikin mutane ya yi n da suke salla sukan karanta su da rufu’a ne?

Kamar yadda nake jin ka in kana karanta ayar nan ta suratu Hamd: (ÇíÇß äÚÈÏ)  ka kan yi rufu’a wa harafin “Ba’un” na kalmar (äÚÈÏ ) duk da kuwa wasu mutane kisira suke mata lokacin da suke sallah.

Sai ya ce: shin ba ka karanci “Nahwu” ba ne tukuna domin ka san kaidojinsa?

Sai na ce: Na karanta. Ko da yake ban zurfafa a cikinsa ba.

Sai ya ce: Me malaman “Nahwu” suke cewa kan wasalin kalmomin(ÇáÑÍãä ÇáÑÍíã )

Sai na ce: Kisira kamar yadda kake karantawa.

Sai ya ce: Kawo min Al-kur’ani.

Sai na kawo masa wannan littafi na Ubangiji daman yana kusa da ni.

Sai ya ce ciro suratul Hamd ka duba ta.

Hokacin da na ciro ta sai na ga kisira a karshen kalmomin  (ÇáÑÍãä ÇáÑÍíã ) kana kuma na ga harafin “Ba’un” na kalmar (äÚÈÏ )  na fadin Allah: (ÇíÇß äÚÈÏ)  tana da rufu’a ce ba kisira ba.

Sai na ce masa: Na same su ne kamar yadda kake karantawa sai ya ce: To karanta kamar yadda wasalinsu yake a littafin Allah, sannan ka lura da irin kura-kure masu yawa da masu karatu suke yi, don kada ka yi su.

8-        Babana ya kasance ba ya fara karanta zikrin da ke cikin ruku’u ko sujada sai bayan ya nitsu a cikin ruku’unsa ko sujadarsa kana ba ya dagowa har sai bayan ya gama zikirinsa alhali yana mai ruku’u ko sujada.

9-        Ya kasance idan ya dago kansa daga sujada ta farko sai ya dan dakata kadan alhali yana zaune kafin ya tafi zuwa sujada ta biyu, haka ma yake yi bayan ya dago kansa daga sujada ta biyu, ya kan zauna kafin ya mike don raka’ar da take biye mata.

10-    Wani lokaci na tambaye shi: Na kan gan ka bayan ka idar da salla ba tare da bata lokaci ba kana addua wa kanka da iyayenka da ‘yan’uwanka muminai?

Sai ya ce: Naam, Abul Hasan (a.s.) ya kasance yana cewa: (Duk wanda ya yi  addua wa’yan uwansa muminai maza da muminai mata, musulmai maza da musulmai mata Allah ya kan wakilta masa ga kowane mumini malaika don ya yi  masa addua).

11-    Na tambaye shi: Na ga bayan kowace sallar farilla kana tasbihi (Jan carbi)?

Sai ya ce! Wannan shi ne “Tasbihuz-Zahra (a.s) wanda manzon Allah (S.A.W.A.) ya koya mata. Ga yadda ake yi: (Allahu Akbar) sau talatin da hudu (34) sannan (Alamdu lillah) sau talatin da uku (33) kana (subhanallah) sau talatin da uku (33) in ka hada su za su ba ka tasbihi guda dari kenan.

T: Shin wannan tasbihi na zahra yana da wata falala ce?

A: Na’am, hakika an ruwaito daga Imam sadik (a.s) yana gaya wa Abi Harun al-makfuf cewa: Ya Aba Harun, mun kasance muna umurtan ‘ya‘yanmu da yin “Tasbihuz-zahra (a.s) kamar yadda muke umurtansu da salla, don haka ka lizimce shi, domin bawa ba ya lizimtarsa sannan ya tabe.

An ruwaito daga wajensa (a.s) yana cewa: “yin Tasbihuz-zahra kowace rana bayan idar da salla shi ya fi soyuwa a gare ni daga salla raka’a dubu kowace rana”.

Da ace akwai wani abin da ya fi shi da manzon Allah (S.A.W.A.) ya koya wa Fatima shi saboda matsayinta a wajensa, kamar yadda aka ruwaito a wajen Imamai (a.s).

12-    Wani lokaci babana ya kasance ya kan yi sallar azahar ba tare da bata lokaci ba ya biyo ta da la’asar, ko kuma ya kan yi sallar magriba kana ba bata lokaci ya biyo ta da lsha, tattare da wani lokacin kuma ya kan bambanta tsakanin sallolin biyu, ya kan sallaci azahar sannan ya ci gaba da wasu ayyukansa har sai lokacin sallar la’asar ya yi  sai ya sallaci la’asar, haka ma yake yi wa sallolin magriba da isha.

Lokacin da na tambaye shi kan haka sai ya amsa min da cewa: Kana da zabi kan ko ka raba su ko kuma ka hadu su.

13-    Na ce wa babana: lna jin ka lokacin da kake karanta suratul Qadr kana bayyana harafin “lamun” lokacin da kake karanta ayar (ÇäÇ ÇäÒáäÇ Ýí áíáÉ ÇáÞÏÑ ) alhali ina jin wasu mutane basa bayyana shi hatta kamar babu wannan harafin, kamar haka ake karanta shi: (lnna anzanahu) sannan kuma ina jin ka kana karanta (subhana rabbiyal azimi wa bi hamdihi) kana yin rufu’a wa harafin “sinun” na “subhana” sannan kana bayyana fatahar da take (rabbiyal) alhali ina jin wadansu ba haka suke fadi ba?

-            Ashe ban ce maka ka lura da karatunka ba.

 

* * * * * * * *

عنوان الکتاب