TATTAUNAWA KAN JABIRA |
||
|
Yayin da lokacin tattaunawarmu ya yi sai na ce wa Babana: Jiya ka ambaci kalmar “aljabira” inda ka ce yau za ka yi min bayani. - Na’am, idan ka sanyo wani kyalle ko abin da ya yi kama da haka akan rauni ko miki ko karaya to wannan shi ake kira “Jabira” (wato Bandeji). T: Hakika na san rauni da karaya amma mene ne miki? A: Miki shi ne ciwo da ke fitowa a jiki. T: Yaya zan yi wanka ko taimama ko alwala tare da cewa akwai “Jabira” a jikina? A: Idan har za ka iya daga “Jabirar” ba tare da wata cutarwa ko wahalarwa ba to ka daga, kana sai ka wanke ko ka shafi kasarsa gwargwadon abin da ya wajaba kanka na wankewa ko shafawa, a wannan gurbi na alwala . T: To idan daga “Jabirar” ba zai yiwu ba saboda cutarwa ko wahala fa? A: Sai ka wanke abin da ya sauwaka maka na daga jikinka da ke gefen “Jabirar” kana ka yi shafa akan “Jabirar” a madadin bangaren da yake rufe da “Jabirar” shin “Jabirar” tana wajen da ake wankewa ne kamar akan hannu ko kuma inda ake shafa kamar idan yana kan kafa ne, tare da la’akari da wadannan abubuwa masu zuwa:- 1- Kan “Jabirar”- inda ake shafa da hannu mai danshi-dole ya kasance mai tsarki, kana kada najasarta da ke ta cikin “Jabeerar” da take manne da ciwon, ta dame ka. 2- [Kada “Jabirar” ta kasance ta kwace ce]. 3- Girman “Jabirar” ya kasance dai-dai da fadin ciwon kamar yadda aka saba daure ciwo ko rauni. T: To idan girman “Jabirar” ta fi girman ciwon fa? A: Sai ka daga dai -dai karin kana ka wanke abin da yake kasarsa ko kuma ka shafa gwargwadon abin da ya dace da shi, gurbin a alwala. T: To idan ba zai yiwu in daga shi ba ko kuma akwai cutarwa a daga shi din fa? A: To sai ka bar shi, kana ka yi alwala da shafa a kan “Jabirar”. T: To idan dage gwarwadon inda aka kara din yana wahala ko kuma zai cutar da wurin da ke da lafiya ba gurin da yake da ciwon ba fa? A: To sai ka yi taimama a maimakon alwala idan har “Jabeerar” ba awurin da ake taimama ba ne [in kuwa a gurin ne to sai a hada duka biyun]. T: To idan “Jabirar” ta rufe dukkan fuskata ko kuma dukkan daya daga cikin hannayena ko kafata fa, to yaya zan yi lokacin alwala? A: Sai ka yi alwala da shafa a kan “Jabirar”. T: To in kuma ta mamaye dukkan gabobi ko kuma mafi yawa daga cikinsu ne fa? A: [To sai ka hada tsakanin alwala tare da shafa akan “Jabira” da kuma taimama]. T: To idan a fuskata ko hannuna akwai rauni ko miki wanda ke bude kuma likita ya hana ni barin ruwa ya taba shi, to yaya zan yi wajen alwala? A: Sai ka wanke gefensa kana ka bar inda yake da ciwon. T: Idan a fuskata ko hannuna akwai budaddiyar karayar da ruwa ya kan cutar da shi amma babu rauni a jikinsa, to yaya zan yi alwala? A: To alwala ta fadi sai ka yi taimama. T: To idan wannan budadden raunin da ruwa yake cutar da shi yana daya daga cikin wuraren shafa ne, kamar misali in yana kafa ko kai ne, to yaya zan yi shafa a alwala? A: Sai ka koma ga taimama. T: To yaya zan yi in na so yin wanka amma a jikina akwai rauni ko miki budadde? A: A nan kana da zabi ko ka bar wanke raunin ko miki kana ka wanke gefensa ko kuma ka koma ga taimama. T: Idan a jikina akwai budadden karaya yaya zan yi wanka? A: Sai ka yi taimama a maimakon wanka. * * * * * |
||