TATTAUNAWA KAN TAIMAMA |
||
|
Lokacin da Babana ya ce yau za mu tattauna ne kan “Taimama”, sai na ji cewa wannan kalma ba bakuwa ba ce gare ni face dai ma na sha jin ta, koda yake a wancan lokacin ba zan iya bayyana dalilin wannan sauki ba, da kuma ina wannan sauki ya fito ba. Kana da kuma sirrin wannan rashin wahala ba. Ba mu gama wannan tattaunawa ba har sai da dalilin wannan sauki ya bayyana min, domin wannan kalma ta taimama na sha karantawa da jin ta lokacin da nake karanta al-kur’ani mai girma, ko kuma ina saurarensa daga wani shahararren mai karatun al-kur’ani domin Babana ya kasance yana kwadaitar da ni kan in dinga karanta abin da ya sauwaka na daga al-kur’ani kowace rana, kuma hakika na kasance a kan wannan tafarki kowace rana…har ya zamanto bakina, zuciyata, kwakwalwata sun kyautata saboda karanta shi da nake yi. Na kasance mai tunani a kansa kana shiriyar da ke cikinsa ya taimaka min wajen samun kwanciyar hankali da daukaka, kuma a tafarkinsa dabi’una sun karfafa, haka ma alakata tsakanin al’umma, cikin dangina, wadanda na sansu, yan’uwana kana da abokaina. Koda yake duk da irin kwadayin da nake da shi na gano wannan al’amari, sai dai na gagara tuna ayar al-kur’ani mai girman nan da ta yi magana kan wannan al’amari ko kuma tuna surar da aka ambace ta a ciki, don haka ne ma na fara tattaunawarmu ta yau da wannan tanbaya: T: Baba… na yi kokari in tuna sunan surar da aka ruwaito kalmar “taimama” a cikinta amma na gagara. A: Ita ce suratun “-Nisa’I” inda Allah yake cewa: “…kuma idan kun kasance majinyata, ko kuwa akan tafiya ko kuwa wani daga cikinku, ya zo daga bayan gida ko kuwa kun shafi mata, ba ku sami ruwa ba to, ku nufi fuskar kasa mai kyau, ku yi shafa ga fuskokinku da hannuwanku lalle ne, Allah ya kasance mai yafewa mai gafara” Hakika -kamar yadda za ka gani-wannan aya ta yi bayanin, yaushe ne, da mene ne kana yaya ne ake yin taimama, za mu fara daya bayan daya. - Za ka yi taimama ne a madadin wanka, ko alwala, ko kuma a madadinsu su biyun, yayin da: 1- Idan baka samu ruwan da zai ishe ka wanka ko alwala ba kowanne a gurbinsa. 2- Kana da ruwa, amma ba za ka iya isa gare shi ba saboda wani gazawa –kamar shan inna- ko kuma aiki da shi din ya ta,allaka da aikata haram kamar yin alwala da ruwa na halal amma a kwanon kwace ko kuma saboda tsoron wata cutarwar da za ta same ka ko mutuncinka ko dukiyarka. 3- Saboda tsoron kishirwa ga kanka ko kuma duk wani wanda yake da alaka da kai ma’ana wanda hakkinka ne kulawa da al’amarinsa, kai hatta ma dabbobin da kulawa da su yana kanka ne, idan har ruwan da kake da shi ba zai ishe ka ka kawar da kishin ruwa sannan a dai-dai wannan lokacin ka yi alwalan ko wanka ba. 4- Idan lokaci ya kure ta yadda lokacin ba zai ishe ka ka yi wanka ko alwala tare da yin salla dukkanta a cikin lokaci ba. 5- Idan samun ruwan don wanka ko alwala ko kuma amfani da shi saboda su biyun zai haifar da matsi da wahalhalu masu yawa wadda ba za ka iya daurewa ba, kamar idan samuwar nasa zai haifar da zubar mutuncinka ko kuma ruwan ya canza ta yadda amfani da shi zai haifar maka da wahala mai tsanani. 6- Idan wani al’amari ya wajaba a gareka wadda zai sa ka yi amfani da ruwan dominsa kamar gusar da najasa daga masallaci. T: Menene “Jabira”…? A: Zan maka cikakken bayani kanta a tattaunawarmu ta gaba. T: To a halin yanzu na san yaushe ne zan yi taimama, to amma da me zan yi taimamar? A: Za ka yi taimama ne da duk wani abin da ke kan kasa na daga turbaya ko yashi ko dutse, ko tsakuwa da makamancinsu da sharadin cewa abin da za ka yi taimaman da shi ya kasance mai tsarki ne [tsaftacacce] kana kuma ba na kwace ba. T: To yaya ne zan yi taimamar? A: Zan yi taimama a gabanka don ka koya…(sai Babana ya fara)- da farko mutum zai cire zoben da yake hannunsa, sai ya bugi kasa da cikin tafin hannunsa gaba daya, sannan sai ya hada su waje guda don shafan abin da ke tsakanin wurin da gashin kai ya fara fitowa da saman kan hanci, yana mai shafan goshinsa [da kundukukinsa (wato saman kumatu)] daga inda gashi ya fara fitowa zuwa kan gira, to lokacin da ya iso da shafan zuwa saman kan hanci sai ya dakata a nan, sai ya daga hannunsa daga kan hanci kana ya shafi dukkan bayan hannunsa na dama (daga wuyan hannu zuwa kan yatsun hannu) da tafin hannunsa na hagu sannan ya shafi bayan hannunsa na hagu da tafin hannunsa na dama daga wuyan hannu zuwa kan yatsu. T: A! shin shi kenan ya gama taimama da irin wannan sauki da sauri? A: Na’am, ai ba taimama ce kawai take da sauki ba. Allah yana cewa: “ALLAH YANA NUFIN SAUKI NE A GARE KU KANA KUMA BAYA NUFIN TSANANTAWA GARE KU” T: Shin taimama tana da wasu sharudda ne? A: Na’am. 1- Dole ne ka kasance ba za ka iya yin wanka ko kuma alwala ba kamar yadda ya gabata. 2- Ka daura niyyar yin taimama don kusanci ga Allah. 3- Dole ne abin da za ka yi taimaman da shi ya zamanto mai tsarki, [kana tsabtacacce], kuma ba na kwace ba, kuma ba’a hada shi da wani abu da bai halatta a yi taimama da shi ba kamar tokan katako sai dai in abin da aka hada shi da shi din ya bace a cikinsa. 4- [Dole ne abin taimaman ya manne da hannunka taimama kan falale da babu kura akai baya wadatarwa.] 5- [Dole ne shafan fuskarka ta zama daga sama zuwa kasa] 6- Kar ka yi taimama sai ka yanke kauna daga gushewar uzurin naka cikin lokaci idan taimamar taka saboda salla ne ko kuma wani aiki na wajibin da yake da lokaci takamaime. 7- Ka yi taimama da kanka in za ka iya. 8- Ka gaggauta wajen shafan kada ka bar lokaci mai tsawo tsakanin ayyukan taimama ta yadda zai kawar da yanayinta. 9- Dole ne ya zamanto babu wani abin da ya raba tsakanin abin shafa da abin da ake shafan wato misali tsakanin tafin hannunka da fuskarka. 10- Ka shafi fuskarka kafin tafin hannunka na dama, kana hannunka na dama gabannin na hagu. T: To idan na kasance ina da uzuri wajen amfani da ruwa don wanka ko alwala saboda wani ciwo sai na yi taimama na yi salla, sai daga baya likita ya ce min zan iya amfani da ruwa kana kuma akwai sauran lokacin sallar? A: Sallarka ta inganta ba dole sai ka sake sallar ba matukar taimamar taka ta yi dai-dai da shari’a kamar idan ya kasance ka yi taimaman ne bayan ka yanke kauna daga gushewar uzurin cikin lokaci. T: Misali, idan likita ya hana ni amfani da ruwa na tsawon wasu ranaku saboda rashin lafiya, sai na yi taimama na yi salla, sai daga baya ya ba ni izinin amfani da ruwan bayan na warke, to shin zan rama wadannan sallolin da na yi su da taimaman ne? A: A’a, ba za ka sake ba. T: Idan na yi taimama bayan shigan lokacin salla sannan na yi salla, kana sai lokacin wata sallar ya shigo kuma wannan uzuri nawa bai gushe ba, to zan sake yin wata taimaman ne don wannan sallar? A: A’a, babu bukatan sake wata taimamar matukar uzurin naka bai gushe ba kana kuma baka tsammanin gushewar uzurin kana kuma ka kiyaye taimamar taka duk tsawon wannan lokacin. T: Idan na yi taimama a madadin wankan janaba, to shin zan yi alwala ne saboda salla? A: A’a, ya wadatar maka daga alwala da wanka gaba dayansu. T: Idan na yi taimama a maimakon wanka sai na shiga ban daki ko kuma na yi barci misali, to shin taimaman da zan yi nan gaba maimakon alwala ce ko kuma wanka? A: Sai ka yi alwala in za ka iya, in kuma ba za ka iya ba sai ka yi taimama maimakon alwala. T: To idan na yi shakka kan shafan fuska ko shafan tafin hannun dama sannan a lokacin ina kan shafan tafin hannun hagu ne fa? A: Kada ka ba wa wannan shakka taka wani muhimmanci. T: To idan kuma ka yi shakka a kansu su biyun ne bayan gama taimamar fa? A: Shi ma dai kada ka ba wa wannan shakka taka wani muhimmanci.
* * * * *
|
||