TATTAUNAWA KAN WANKA


Yau ga mu nan za mu tattauna kan wanka, nan ba da jimawa ba tattaunawar za ta kai karshe, ina mai alfahari da abin da na koya, mai tinkaho kan abin da na cimma, mai farin ciki kan abin da na samu, na samun iya tsarkake jiki daga dauda cikin sauki, watakila hakan ma zai kara min kaunar, ruwa, bugu da kari kuma dadin da nake ji irin wannan dadi ba za ta kasance ba da babu ruwa. Hakika wannan soyayya tawa ga ruwa dadadden abu ne, na kasance ina son sa tun ina karami, na kan yi wasa da shi da mahaifiyata, a duk lokacin da na samu daman wasa da shi, da kuma nitso cikinsa da kuma jin dadi da farin cikin wasa da shi. A duk lokacin da na samu daman koyon ninkaya a ruwa- domin babana ya gaya min cewa koyon nitso a cikin ruwa mustahabi ne- na zamanto mai tsanani kaunar ruwa a duk lokacin da aka nesanta ni daga gare shi, kaunan ruwan da watakila ma zai kusan irin na kifi a duk lokacin da aka nesanta shi daga ruwa abin kaunarsa.

Na’am na kasance mai kaunar ruwa, kana mai kusanci da shi, tun daga lokacin da na gane cewa shi din nan mai tsarkakewa da tsabtacewa ne- kuma tsabta ai tana daga imani ina wanke jikina kana kuma in wanke (abubuwa da shi).

Da sannu yau Babana zai yi min cikakken bayani kan yadda zan yi wanka.

Sai Babana ya ce: Wanka ya kasu kashi biyu: “Irtimasi”da “Tartibi”

T: Mene ne “Irtimasi”?

A: Shi ne ka nutsar da dukkan jikinka a lokaci guda a cikin ruwa, wannan shi ne takaitaccen ma’anarsa nan gaba hakikanin abin da ake nufi zai bayyana maka.

T: To “Tarteebi” fa?

A: Shi ne da farko ka wanke dukkanin kanka da wuyanka tare da wani sashi na abin da ya hadu da wuyan na daga jikinka, kada ka mance da wanke kunnenka (na daga abin da yake waje ban da wanda yake ciki) kana sai ka wanke jikinka ka fara da bangaren dama da wani sashi na abin da ya hadu da shi na daga wuya da kuma wani sashi na bangaren hagu sannan ka wanke bangaren hagu kamar yadda ka yi wa bangaren dama.

Sannan ya halatta ka wanke jikinka gaba daya bayan wanke kai da wuya ba tare da rarraba shi zuwa dama ko hagu ba.

T: Shin wanka yana da wasu sharudda ne?

A: Yana da sharudda kamar irin na alwala na daga niyya, tsarkin ruwa, halaccinsa da kasantuwansa “Mudlak”, tsarkin gabobin jiki, jerantawa wajen wanke gabobi, kana kuma mutum ya yi wankan da kansa in har zai iya yin hakan da kuma kasantuwan babu wani abin da zai hana amfani da ruwa a shar’ance kamar rashin lafiya (Duba tattaunawa kan alwala).

-         Koda yake ya bambamta da alwala a abubuwa guda biyu:

T: Mene ne su din?

A: Na farko: Ba sharadi ba ne a wanka wankewar kowace gaba ya kasance daga sama zuwa kasa kamar yadda yake a alwala.

-         Na biyu: Gaggautawa da kuma bibiya ba sharadi ba ne a wanka kamar yadda yake a alwala, za ka iya wanke kanka da wuyanka, kana bayan wani lokaci ka wanke sauran jikinka koda kuwa kan naka ya bushe misali a alwala lokacin da kake wanke fuska in ka isa gashi gira sai kawai ka wanke zahirinisa, ko kuma lokacin da kake shafan kai za ka shafi zahirin gashi ne, amma a wanka wajibi ne ka sadar da ruwa ga fatan kan, haka ma ga gashin gira, gashin baki da gemu, kana kuma sai…

T: Kana sai me?

A: Kana kuma wankan janaba yana wadatarwa daga alwala…

T: Haka yana nufin kenan idan na yi wanka lokacin da zan yi salla ba na bukatar yin alwala kenan?

A: Na’am, sai kawai ka yi sallarka ba tare da ka yi alwala ba. Kamar yadda idan wanka daban -daban suka taru maka kamar wankan janaba da juma’a misali, ya halatta maka ka yi wanka guda daya kawai da nufin gaba dayansu, sai ka yi niyyar wankan janaba to ya wadatar daga sauran [Na’am a wankan juma’a dole ne ka yi niyya koda niyya a dunkule domin wata wanka ba ta isar masa].

T: To misali idan mace tana da bukatar wankan janaba, haila da juma’a fa?

A: Za ta iya yin wanka guda daya da niyyar gaba dayansu, ko kuma ta yi niyyar wankan janaba ya isar mata daga sauran wanka amma ban da wankan juma’a kamar yadda ka sani.

Babana ya kara da cewa:

Zan gaya maka wasu abubuwa da za su amfane ka a wajen wankanka:

1-     Ka tabbatar cewa ka gusar da duk wata alama ta ruwan maniyyi daga jikinka kafin ka fara wankan.

2-     Ka fara da yin fitsari kafin ka fara yin wanka don ka fitar da duk wani abin da ya saura na daga ruwan maniyyi.

3-     Dole ne ka kawar da duk wani abin da zai hana isar ruwa ga jiki kamar fenti, amma idan har kawarwar ba zai yiyu ba ko kuma ya wahala to sai a koma ga taimama, amma idan abin da ke hana ruwan isa a wajen da ake yin taimama ne [sai ka hada tsakanin wankan da taimama].

4-     Dukkan wata shakka da za ta zo dangane da ingancin wankan bayan gama shi to ba ta da wani muhimmanci kuma ba abin lura ba ne.

Da a ce shakka za ta zo maka kan wanke kai da wuya alhali a lokacin kana wanke sauran jikinka ne, to [dole ne ka koma ka wanke gwargwadon wurin da kake shakkan].

T: Wankan janaba, haila, jinin haihuwa, istihala mutuwa, taba mamaci dukkansu wanka ne na wajibi kamar yadda ka min bayani amma wata wanka ta wuce a tattaunawarmu kan wanka da ka kira shi da sunan (Wankan Juma’a), to shin akwai wasu wanka ne da ba ka gaya min ba?

A: Na’am, akwai wasu wanka da yawa, amma mustahabbai ne ba wajibai ba, bari in ambata maka wasu daga cikinsu:

1-     Wankan Juma’a wadda take mustahabi ne mai karfi, lokacinta daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana amma abin da ya fi a yi ta kafin gotawar rana tsakiya (zawali).

2-     Wankan daura harami (ihram).

3-     Wankan ranar sallar nan gudu biyu (karama da babbar salla) lokutansu daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana amma an fi so a yi su kafin sallar idi

4-     Wankan ranakun takwas da tara na watan zul -Hajj, a ranar tara abin da ya fi shi ne ya kasance yayin da ranar ta kai tsakiya.

5-     Wankan daren farko da daren sha bakwai da daren sha tara da daren ashirin da daya da daren ashirin da uku da kuma daren ashirin da hudu na watan Ramalana mai albarka.

6-     Wankan (istikhara).

7-     Wankan rokon ruwa.

8-     Wankan shiga garin Makka.

9-     Wankan ziyarar dakin ka’aba.

10- Wankan shiga masallacin Annabi (S.A.W.A.).

Duk wadannan wankoki suna wadatarwa daga alwala.

Akwai wasu da dama da ba wadannan ba amma ba zai yiwu mu ambace su a dan wannan lokaci namu ba, wadansunsu sukan wadatar daga alwala su ne wadanda shari’a ta nuna mustahabbancinsu, kana wasunsu kuma basa wadatarwa su ne wadanda mustahabbancinsu bai tabbata ba a shari’a amma ana yin su ne don kwadayin samun lada.

T: Saura kawai in yi tanbayata ta karshe ita ce kuwa: idan ban yi istibra’I da fitsari ba bayan janaba, wato ban yi fitsari ba, sannan sai na yi wanka, sannan sai maniyyi ya fito min bayan haka koda kuwa digo daya ne fa?

A: Dole ne ka yi wanka na biyu koda kuwa ruwan maniyyin ya fita ne ba tare da wata sha’awa ko wasa ba.

Kamar yadda ya wajaba a gare ka ka sake wanka karo na biyu idan har ka san cewa wannan abin da ya fito maka yanzu maniyyi ne koda ba ta hanyar da ta gabata ba ne.

*  *  *  *  *

عنوان الکتاب