TATTAUNAWA KAN ALWALA


Sai Babana ya ce: Yau zan maka bayani kan alwala ne kana bayansa in yi maka bayani kan wanka da taimama. Sai na ce a cikin zuciyata: kenan za mu fara da abu na farko da yake tsarkake jiki daga abin da ya same shi (na daga wani hadasi).

Cikin sauki da gaggawa sai na nemi tuna wasu abubuwa da idan suka faru sukan gusar da tsarkin da ke jiki bayan da ya kasance cikin tsarkinsa.

Lokacin da na gama wancan tunanin, kana ya yi dai-dai da wancan abu da ya wuce sai na sake tanbayar kaina… yaya aka yi alwala ya zama tsarki? To shin me ya sa ba zan tambayi Babana ba tun da dai ga shi nan a gaba na?

T: Me ya sa ne muke yin alwala?

A: Don mu yi sallah…misali.

Don lokacin da za mu yi dawafi a dakin ka’aba lokacin aikin Hajji ko umra, ko kuma don taba rubutun al-kur’ani mai girma [da sunayen Allah da siffofin da ya kebantu da su kaman ar-Rahman da al-khalik] don su halatta mana,da dai sauransu.

T: Sanannen abu ne cewa da ruwa ake alwala…

To shin ruwan da za mu yi alwala da shi yana da wasu sharudda ne?

A: Na’am.

1-     Dole ne ruwan ya kasance mai tsarki ne, kana dukkan gabobin alwalarka su zama suma masu tsarki ne.Wanke su lokacin alwala yakan wadatar a matsayin tsarkake su idan har ruwa “Mu’utasim”ne.

2-     Ya kasance na halal ne ba na kwace ba, haka ma wurin da za ka yi alwala a cikinsa.

A nan ya kamata ka gane cewa abin nufi da sharadin halaccin wurin shi ne idan babu wani wurin da za ka yi alwala sai na kwace to wajibcin alwala ta fadi a kanka, a nan abin da ya wajaba kanka shi ne ka yi taimama amma da za ka saba wa hakan ka yi alwala a wurin kwace to da alwalar taka ta inganta sai dai ka yi sabo.

3-     Ruwa ya zamanto “Mudlaki” ne ba “Mudaf” ba, kamar ruwa mai gudu ko ruwan da ke cikin kofi wadda kake sha ba kamar ruwan ruman ba.

T: To yaya zan yi alwalar…?

A: Bayan ka yi niyyar alwala don neman kusanci ga Allah, sai ka fara:

Da farko: sai ka wanke fuskarka daga mafitan gashi wato saman goshi zuwa haba, tsawon fuska kenan fadinsa kuwa shi ne abin da ke tsakanin babban yatsa da yatsar tsakiya.

Idan ka buda tafin hannunka kana ka sanya shi a fuskarka, to duk inda tafin hannun naka daga kan babban yatsa zuwa kan yatsar tsakiya ya mamaye to shi ne abin da za ka wanke a matsayin fadin fuskarka.

-         Amma dole ne ka gane cewa [wanke fuska ana fara shi ne daga sama zuwa kasa] ba tare da bukatar a tsettsefe gashin da yake da kauri ba.

Abu na biyu ka wanke hannunka daga gwiwan hannu zuwa kan yatsu za ka fara da hannun dama sannan na hagu, za ka wanke daga saman gwiwan hannu ka yiyo kasa har zuwa kan yatsu.

Abu na uku: Ka shafi gaban kanka amma an fi so ya kasance da cikin tafin hannunka na dama kana kuma ka fara shafan daga sama zuwa kasa, shafa a kan gashi da ke gaban kai din yana isarwa ba sai ka yi shafan akan fata ba.

Abu na hudu: sai ka shafi kafafunka tsakanin kan yatsu zuwa gaban da ya raba kwabri da tafin kafa, za ka shafi kafarka ta dama da sauran danshin da ke hannunka na dama haka ma na hagu da danshin hannun hagu amma bai halatta ka debi sabon ruwa ka yi shafa da shi ba [kamar yadda ba ya halatta ka gabatar da kafar hagu akan na dama].

A lokacin alwala dole ka lura da wadannan abubuwa:-

1-     Jerantawa, wato ka wanke fuskarka kafin hannunka na dama, hannunka na dama kafin hannun hagu, shafan kanka kafin shafan kafafu.

2-     Gaggautawa: A nan ana nufin bibiya wanda aka saba tsakanin ayyukan alwala, wato ya zamanto an aikata abu (wankewa ko shafa gaba) kafin gaban da ya riga ya gabata ya bushe, idan kuwa har dukansa ya bushe to alwala ta baci sai dai cewa bushewar da iska ko zafi ne sababinsa ba ya ba ta alwala idan har gaggautawar ta tabbata.

3-     Yi da kai, wato ka yi alwala da kanka in har hakan zai yiwu.

T: Idan kuma ba zan iya ba fa?

A: Idan ba za ka iya ba, ya hatatta wani ya yi maka, wato ya daga hannunka ya wanke maka fuskarka da shi, sannan ya wanke maka hannunka, kana ya shafi kanka da tafin hannunka na dama, sannan ya shafi kafafunka da danshin tafukanka.

4-     Kada ya kasance akwai wani abu da zai hana isar ruwa ga fata kamar fenti da “gam” (danko) ko jan farce ga mata da sauransu, koda yake ya kamata ka san cewa mai ba ya cutarwa kana ba ya hana (isar ruwa).

5-     Kuma kada ya kasance akwai wani dalilin da zai hana ka amfani da ruwa kamar rashin lafiya, in kuwa har akwai, to taimama ta wajaba a gare ka maimakon alwala

T: Da a ce zan yi alwala kafin lokacin wata sallah ya zo, to shin zan sake alwala ne?

A: A’a, matukar dai wannan alwalar ba ta baci ba.

T: Yaya kuma yaushe ne alwala take baci?

A: Abubuwan da suke ba ta alwala guda bakwai ne: fitan fitsari, da fitan bayan gida, tusa, barci, dukkan wani abin da yake kawar wa mutum da hankali kamar suma da maye, istihala “karama da matsakaiciya” (dubi Tattaunawa kan istihala) da kuma janaba.

Daga nan sai na ga idon babana yana haske sai na fara zaton cewa wadannan ka’ida ko kaidoji sun fara aikinsu a kwakwalwansa, sai na tabbatar da zatona.

Don kuwa ga shi Babana yana cewa: Zan karasa wannan tattaunawa nawa da gaya maka ka’idoji  gamammu kan alwala wadanda za su amfane ka.

Ka’ida ta farko: Duk wanda ya yi alwala sannan sai daga baya ya yi shakkan shin alwalarsa ta baci (da daya daga cikin abubuwa masu ba ta alwalan nan guda bakwai da suka gabata) ko kuma tana nan, to sai ya dauka yana nan da alwalarsa.

T: Ba ni misali…

A: Misali ka yi alwala da safe kuma kana da tabbacin cewa har yanzu tana nan, to sai lokacin salla ya yi sai ka yi niyyar salla, sai ka fara shakka shin bayan nan ka yi fitsari ko kuma ba ka yi ba, to a wannan hali ka dauka cewa kana da alwala, kuma ka je ka yi sallarka.

Kaida ta Biyu: Duk wanda bai yi alwala ba ko kuma ya yi alwalar amma ya bata ta, kana sai daga baya ya yi shakka shin ya sake yin wata alwala ko kuma bai yi ba? To a nan ba shi da alwala.

T: Ba ni misali…

A: Misali, ka farka daga barci da safe, kana sai lokacin sallar azahar ta yi kana so ka yi salla, sai ka fara shakka, shin na yi alwala bayan farkawata ko ban yi ba, sai ka yi alwala ka yi salla.

Kaida ta uku: Duk wanda ya kare alwalarsa, sai ya fara shakkar ingancin alwalar bayan ya kare, to alwalarsa ingantacciya ce.

T: Ba ni misali…

A: Misali, ka kare alwala, sai daga baya ka fara shakka, shin na wanke fuskata kuwa ko ban wanke ba? Ko kuma shin wanke fuskata da na yi dai-dai ne kuwa ko kuma ba dai-dai ba ne? To a wannan hali sai ka dauka alwalarka dai-dai ce.

T: To idan na yi shakka a kan shafan kafar hagu ne fa?

A: Sai ka sake shafarta, sai dai-idan har ka shiga wani aiki kamar ka fara salla ko kuma ka yi shakkar ce bayan tserewar gaggautawa to a nan kada ka damu da wannan shakkar.

*  *  *  *  *

عنوان الکتاب