Mutumtakarsa |
||
|
Duk wanda ya zauna tare da Sidi Sistani ko kuma yana da wata sadarwa da shi zai ga irin mutumtaka da daukakar ruhin da yake da ita irin wadda zuriyar gidan Manzon Allah (SAWA) suka kwadaitar a kanta da ke sanya shi shi da makamantansa su zama malaman da ake cewa “Malaman Allah” da kuma fadin Imam (A.S.) cewa: “Magudanar al’amura na hannun Malamai aminan Allah a bayan kasa a kan halalinSa da haram dinSa.” Ga misalan wasu daga cikin abubuwan da na lura da su daga gare shi yayin da nake halartar karatu a gurinsa:- A) Insanfi da mutunta ra’ayiSidi Sistani, saboda shauki da yake da shi game da ilimi da neman sani da kwadayin isa ga hakika da kuma girmama’yancin ra’ayi sau da yawa zaka iske shi yana karanta littafan Malamai da marubuta dabam-daban hatta na abokan karatunsa kuma za ka iske shi yana ambato hatta ra’ayayin wadanda matsayinsu na ilimi bai kai nasa ba ko kuma ya kawo ra’ayinsu a yi muhawara a kai, wannan abu ne da ba a san malamanmu da irinsa ba. B) Ladubban MuhawaraMakarantun addinin Musulunci a garin Najaf sun shahahara da muhawara ta ilimi tsakanin malamai da dalibai wanda hakan kan sanya dalibi ya goge wajen al’amuran ilimi. Wasu lokutan ma har muhawar takan wuce iyaka ta zama jayayyar da ba ta da wata riba ta ilimi. Shi kuwa Sidi Sistani muhawararsa da Malamai ko da dalibansa yakan yi ta ne da wani hali da ladubba na musamman wajen kaiwa ga manufa ta amfanar ilimi koda kuma wani daga cikin dalibansa ya yi zarbabiyar zartar da muhawararar zuwa da’ira jayayya yakan yi kokarin maimaita amsarsa cikin natsuwa da ladubban magana idan kuwa dalibi ya cije a kan ra’ayinsa to shi ya fi zabin ya yi shiru maimakon ci gaba da muhawarar da ba ta da ribar ilimi. C) Halayyar TarbiyyaKoyarwa ba wani aiki ne da Sidi Sistani ke yi don a ba shi albashi. Don wannan kan nesanta malami daga daidaita dalibinsa da kulawa da shi da isar da shi ga matsayin ilimi da daukaka da fita sarari; kamar yadda koyarwar ba wai kawai don tarbiyyar dalibi da kuma kai shi ga matsayin ilimi ba kawai sai dai kawai don sauke muhimmin nauyin da yake bukatar ruhin soyayya da tausasawa ga dalibai kamar yadda Sidi Imam Khu’i ya kasance yana yi da dalibansa. Dimin da’iman bayan darasi yakan kwadaitar da dalibai su yi tambaya yana cewa ku yi tambaya mana koda game da lambar shafi; ko kuma wani darasi ayyananne ko kuma littafi ayyananne ko kwa saba da muhawara da malami, kamar kuma yadda ya kasance yana sa dalibansa kintata tsakanin abinda ke rubuce da kuma wanda ake ji a gurin darasi, yana kuma yin ta’akidi koyaushe a kan girmama malamai da kuma kiyaye ladubban magana da muhawara da tattaunawa yayin magana da malamai, akwai misalan wannan da dama da dabi’arsa. D) Wara’u, kankan da kaiBincike da bayanai a garin Najaf wata dama ce ta fitowa sarari a tsakamin Malamai kuma ta yi nesa da taso da fitina, koda yake wasu suna ganinsa a matsayin abu da bai dace ba amma kuma akwai Maslaharsa da fa’idarsa wani lokaci domin idan har aka samu wata karkata to lalle ne malamai su fito fili, idan bidi’a ta bayyana wajibi ne ga malamai su bayyana iliminsu idan kuwa ba su yi ba to an zare musu hasken imani, kamar yadda ya zo a hadisi. Sai dai kuma idan haka zai zama fitina da ka iya cutar wa ga mutuncin wani mai matsayin addini ayyananne ko kuma tafarki ayyananne ko kuma akwai yanayin yakayyar ra’ayi da maganganu kamar yadda yake aukuwa sau da yawa yadda har takan kai ga hassada da kullace juna, Malamai da dama cikinsu har da su Sidi Sistani kan lizimci natsuwa da wara’u, wato kau da kai kamar yadda ya auku zamanin rasuwar Sidi Burujurdi da Sidi Hakim (R.A.) kamar kuma yadda yake a wannan zamanin Sidi Sistani ya yi riko da tufafinsa na zuhudu da zamansa a karamin gidansa da babu wasu kayan alfahari a ciki. E) Auren MushirikaiKa’idar “Lizimtarwa” wadda yawancin malaman fikihu da na usul ke kawowa, wato kamar ka’idar hankali ko ta ma’abuta hankali tsantsa. Sidi Aliyu Sistani a karkashin ka’idar “Idhdirar” matsuwa wadda ke kaiwa ga ka’idar “tazahum” mai matsuwa da juna da kaiwa ga kunsa fahintar sanya ma’ana ta aiki. Wani lokaci kuma yakan kara fadada ka’idar kamar yadda yake a ka’idar “La tu’adu” wadda yawancin malamai sukan kebance ta ga salla kawai saboda nassi a kan haka amma shi kuwa Sidi Sistani sai ya kama ma’anar cewa “La tu’adu Salati illa min khamsatin”a farkon ruwayar don nuna cewa ta hada da salla ne da kuma abinda ba salla ba na daga wajibai da kuma cewa karshen hadisin na bayyana cewa “Sunna ba ta warware farilla” wato ma’ana ka’ida ita ce gabatar da farilla a kan sunna a salla da kuma watanta na daga ayyukan da ke tabbatar da gaskiyar wannan gabatarwar lokaci da kuma Alkibla da dai sauransu daga bangarorin salla da sharudanta domin lokaci da Alkibla suna daga farillan salla ne ba sunnoni ba. F) Nassi game da Halin Zaman Jama’aDaga cikin malaman fikihu akwai malaman harafi wanda kawai yana kankame ne a kan fahintar nassi kawai ba tare da kokarin fadada fahimta da yalwata ma’ana daga nassin ba, kazalika akwai daga cikin masanan fikihu wanda ke karanta yanayin nassi da sharudan da ke gewaye da shi domin ya kara gane al’amuran da ke da tasiri wajen kaiwa ga manufarsa. Alal misali ya zo daga Manzon Allah (SAWA) cewa yana haramta cin naman jakunan gida ranar Yakin Khaibar, don haka idan muka dauki ma’ana ta harafi to da mun ce ya haramta ko ya zama makaruhi game cin naman jakin gida. Idan kuwa muka duba bangaren halin zaman jama’a game da nassin za mu ga cewa yana duba tsanani da halin wahalar yaki ne da Yahudawa a Khaibara, yaki kuwa yana bukatar daukar makamai daga wani guri zuwa wani guri da kuma daukar kayan taimako kuma babu abin daukan kaya a lokacin sai dabbobi kuma jakin gida na daga cikinsu. Saboda haka alal hakika hanin na iya tafi da shugabanci saboda wata maslaha ko Ka’ida ayyananniya da yanayin da ake ciki ya haifar a wancan lokacin don haka ba za a dauke shi a matsayin haramcin Shari’a ko karhanci ba. Sidi Sistani na daga cikin masu ra’ayi na biyun da muka bayyana. G) Cikakkiyar kwarewa game da guraren tsamo hukunce-hukunceSidi Sistani a kodayaushe yana ta’akidi cewa lalle Masanin fikihu ba zai zamanto masanin fikihu na sosai ba har sai ya samu cikakkiyar kwarewa game da maganganun Larabawa da wake-wakensu da adabinsu kafin ya zamanto yana da karfin ayyana abinda nassi ke nufi filla-filla ba a dunkule ba, kazalika babu makawa ya zamanto ya lakanci lugga da kyau tare da sanin halayen marubutanta domin yin haka yana daga cikin abubuwan da ake dogaro da su a lugga ko kuma ke hana dogaro da su. Kazalika Lalle ne fakihi ya san hadisan Ahlul Bait (A.S.) da masu ruwaito su, dalla dalla domin ilimin sanin maruwaita yana daga abubuwan da babu Makawa Mujthidi ya zamanto yana da su domin ya zamato yana da tabbaci game da ingancin abinda ya dogara da shi. Shi Sidi Aliyu Sistani yana da ra’ayoyi da ya kebantu da su wadanda suka saba wa Jamhurin Malamai. Alal misali suka da rashin dogaro da Ibin Fadha’iri al’amari ne da yake mashahuri ko domin saboda yawan suka gare shi ko kuma saboda rashin dogara da shi wajen raunanawa da kuma tantance adalcin maruwaita, amma shi Sidi Sistani bai yarda da wannan Mashahurin ra’ayin ba yana ganin cewa littafin tabbatacce ne kuma shi Ibinul Fadha’iri ya fi Najjashi da Shaikh zama abin dogara a fannin suka da kuma tantance adalcin Maruwaita kazalika yana da ra’ayin dogaro da tafarkin at-Tabakat wajen ayyana mai ruwaya da tabbatar da gaskiyarsa, kuma wajen tabbatar da cewa hadisi mai cikakken Isnadi ne ko mai yankakken Isnadi yana bin tafarkin Sidi Burujurdi (R.A.) ne. Kazalikia Sidi Aliyu Sistani yana da ra’ayin lalle ne a san littafan hadisai da sababaninsu da kuma sanin halin marubucin hadisan ta bangaren tsari da ka’ida da tabbataccen tafarkin talifi, da kuma abinda yake ya yadu game da wannan kan cewa Shaikh Saduk ya fi Shaikh Tusi Ka’ida bai amince da shi, shi dai kawai yana ganin Shaikh Tusi a matsayin Mai daukar hadisi ne kawai Mai gaskiya saboda abinda ya gani a littafa da kuma alamomin da ya dogara da su. Wannan bangare game da hadisai ba kowa ba ne daga cikin malamai yake dogaro a kansa a wajen tsamo hukunci sai dai kawai su dogara da ayyanannen abinda ya bayyana ba tare da tattaro alamomi dabam daban da za su dogara a kai ba sai dai kawai su dogara a kan maganganun wasu daga cikin masana lugga ba tare da bincike game da marubucin da kuma tafarkinsa ba, wasu ma sam ba sa kasancewa suna da wata madogara game da ilimin sanin maruwaita ko kuma kwarewa game da littafan hadisai. H) Fa’idantarwa ta fuskar TunaniSidi Sistani ba wai kawai Malamin fikihu ba ne a’a yana sane ma da ilimi na zamani kuma yana da masaniya game da ra’ayoyi masana fannoni dabam-daban yana kuma da matsayinsa na ilimi game da tattalin arziki da siyasa da fahimtar sha’anin tafi da shugabanci da halin zamantakewa da fahintar halin da zamani ke ciki yadda fatawarsa za ta zama alheri ga al’ummar Musulmi.
|
||