Matsayİnsa Na Marja’İ

 

 

    Wasu Malaman garin Najaf sun bayyana cewa bayan rasuwar Ayatullahi Sidi Nasrullahi Al- Mustambat, wasu daga cikin manyan malamai sun shawarci Imam Khu’i da cewa ya ayyana wani da za a iya dogaro da shi wajen karewa da kiyaye makarantun addinin garin Najaf, zabin wannan zamanin shi ne Sidi Sistani saboda falalar iliminsa da kyawun halinsa da tafarkinsa da kuma tsayuwarsa yana ba da salla a mumbarin Sidi Khu’i (R.A.) da yin bayanai a makarantarsa da kuma rubuta karin bayani a kan Risalar shi Sidi Khu’i din (R.A.). Bayan rasuwar Imam Sidi Khu’i yana daga cikin mutane shidan da suka raka gawarsa kamar kuma yadda ya kasance shi ne ya sallace shi. Daga bisani ne kuma ya dauki matsayin shugabancin makarantun addini na garin Najaf yana aikewa da izinin tara Khumusi da rarraba hakkoki, yi masa takalidi kuma ya fara yaduwa musamman ma a Iraki, da kasashen Yankin Tekun Parisa da sauran gurare kamarsu Indiya da Afirka da sauransu musamman ma a tsakanin Malaman Makarantun addini da kuma masana ilimin Zamani da matasa saboda saninsa da suka yi da ci gaban tunani da ra’ayi. Shi yana daga cikin ’yan kalilan din da ke daga cikin manyan malaman fikihu da ake ambatawa daga cikin mafifita a ilimi tare da shaidar da dama daga malamai masana ta kan ilimi da kuma masu koyarwa a makarantun addini a garin Najaf mai alfarma da birnin Kum mai tsarki.

 

 

 

 

Saboda Muhimmancin littafan addinin musulunci ne Ma’assasar Imam Ali (a.s) da ke nan birnin Kum-Iran ta dauki nauyi fassara littafan zuwa harsuna dabam-daban da kuma bugawa da yadawa domin wadanda ba sa jin harshen larabci su fahinci abinda suka kunsa kana su ji irin dadin da ke cikin fahintar ma’anarsu; daga bisani kuma su amfane su wajen kyautata dabi’arsu da fatan za su zama hanyar fa’idantuwa da su a duniya da kuma lahira.

 

Mu’assasar Imam Ali

عنوان الکتاب