Salon Koyarwarsa

 

   Tafarkin koyarwarsa ya bambanta sosai da tafarkin da aka sani a makarantun addini. A fannin koyar da Usul ya kebantu da mafi muhimmancin kebabbun hanyoyi kamar haka:-

A) Bayanin tarihin fanni da asasinsa:

Mai yiwuwa yana iya zama na falsafa ne kamar matsalar “Basatatul Mushtak Wat Tarkibihi” ko kuma na akida ko na siyasa kamar misalin “Ta’adul Wat Tarâjih” wanda a ciki ya bayyana al’amarin sabanin hadisai wadanda arangamar ra’ayoyi da akidu ta jawo tare kuma da yanayin halin siyasa da ke kewaye da Imamai (A.S.) a wancan zamanin Wanda Kuwa abu ne a sarari cewa sanin tarihin irin wannan binciken zai fito mana da bangarorin al’amarin sarari ya kai mu ga hakikanin al’amarin ra’ayoyin da aka bayyana.

B) Kulla tsakanin tunanin makarantun addini da kuma ilimin

Zamani, a bayani game da “Ma’anil harfi” da “Ma’anil Ismi” kan cewa shin bambancinsu “Zati” ne ko Kuma “Lihazi” ne sai ya gina shi a kan fahimta irin ta falsafa ta zamani wadda ita ce fahimtar “Takathirul Idrâki” fi fa’aliyyatiz Zihni Bashari wa Khallakiyyatihi” Kuma abu ne mai yiwuwa ga hankalin dan Adam ya suranta abu guda ta fuska biyu. Wani lokaci kai tsaye kuma a bayyane wannan shi ake kira suna, wani lokaci da wasila da tsani a dunkule wannan shi ake kira harafi. Yayin kuwa da ya shiga bayani game da “Mushtak” a kan sabanin da ke tsakanin malamai game da sunan da ya kebantu da zamani “Ismuz Zaman” Sai ya bayyana “Zaman” din da fahinta irin ta falsafar yammaci wato ciro ma’anar “Zaman daga “Makan” abinda ake kira “Zamkan” saboda la’akari da bibiyar da ke tsakanin haske da duhu. Bayaninsa game da abinda sigar umarni ke nufi da kuma gundarinsa, da kuma bayani game da “tajarri” sai ya kawo ra’ayin malaman ilimin halin zaman jama’a dangane de kasafin bukatar abu ta hanyar bukata irin ta umarni da kuma ta roko da kuma ta tambaya saboda shisshigar juna da bangarorin bukata da roko da tambaya saboda kasancewar wanda ya bukatar na sama ne ko tsara madaidaici ko kuma na kasa da wanda aka bukatar daga gare shi.

Hakanan ya sanya Ka’idar sanya Ukuba a kan tsaurin kan bawa ga Ubangidansa wannan shi ma an assasa shi ne a bisa asasin halin zamantakewar dan Adam irin ta da can, wato kasancewa akwai Ubangida da kuma bawa, Madaukaka da kuma Makaskanci da makamancin wannan. Wannan ra’ayi ne da aka gina shi a bisa tunani irin na kasa al’umma dabaka - dabaka ba a bisa dokokin maslaha da amfani ‘yan Adamtaka ba.

C) Himmatuwa da Usulin da ke hade da fikihu

Sau da yawa dalibi zai ga cewa zurfafawa a karatun usuli ko koyarwarsa daga bangaren malamai da dama ba ya haifar da wani sakamako na aikace sai dai kawai a tunani da ra’ayi wato kamarsu bincike game da sanya sunaye da kasancewarsa al’amarin surantawa kawai ko kuma a halitta, ko kuma kasancewar kebewa ko kudara aniya, da kuma bayanansu game da abin binciken ilimi da dai makamantansu. Amma abin lura da darasin Sidi Aliyu Sistani shi ne zurfafawa da kokartawa wajen fitowa da ra’ayin bincike kakkarfa da ke hade da aikin tsamo hukumce-hukunce, kamar bayani game da Usulu Amaliyya da At- Ta’adul da At- Taraji da “Amun” da “Khassun”. Sauran al’amuran koyarwarsa ma daidai fada daidai aiki yake yin su.

D) Sabuntawa da Tajdidi

Daga cikin malaman makarantun addini akwai kwararru da dama wadanda ba su da kudurar sabuntawa da kawo canji sai dai kawai su mai da hankalinsu su dukufa a sharhi da karin bayani da takaituwa a kan kyawun wani bincike ko bayaninsa ba wai su kawo sabon ra’ayi a kan asasin ra’ayoyin da ke akwai ba ballantana ya yawata a cikin ra’ayoyi ya zabe na zabewa ba, sai dai kawai kara bayani a kan maganganu irinsu; “Ta’ammal” ka kuma “Fatham” wato yi tunani, ko kuma ka fahimta idan kuma ya taso da matsala sai ya tsaya a kan kawo mushkila daya ko biyu kana ya tsaya.

Shi Sidi Aliyu Sistani da Shahidi Sadir sun sha bamban da kowa a kan wannan tafarkin, kowa daga cikinsu yana kokari ne ya ba da sabuwar siga da ta dace da bukatar da ake da ita a kan binciken. Wato kamar yadda shi Sidi Sistani ya yi yayin da ya fara bayanin aiki da lafazi da ma’anoni dabam - daban. Domin su Malaman Usuli sun yi bayanansu ne ta bangaren, yiwuwa da kuma korewa, ta Imkan Wal Istihalah, a matsayin bincike na aikin hankali da kuma Falsafa Wanda ba shi da wata fa’ida ta aiki, shi kuwa sai ya bayyana shi ta fuskar aukuwa da kuma rashin aukuwa, Al-Wuku’u Wal adam domin ya fi “imkan” karfi kamar kuma yadda ya yi bayaninsa ta fuskar neman bayyanan -al- Istizhar.

A fannin “At- Ta’adul Wat Tarajih” kuwa gani ya yi cewa sirrin wannan “bahasin” La’alla yana komawa ne ga sabanin hadisai, saboda idan har muka bincika su muka kayyade dalilan sabanin nassosin shari’a to mushkilar mai tsanani ta warware ke nan wadda da’iman take ci wa mai bincike da mai amfana daga hadisan Ahlul Baiti (A.S.) tuwo a kwarya, wannan kuwa zai wadatar da mu ga barin ruwayoyin “tarjih wat tagyir” kamar yadda mai kifayah ya yi game da “Istishab” wato sashen tabbata a kan abinda ya kasance kana da tabbaci game da shi. Wannan irin bincike ma Shahid Sadir ya tabo shi, sai dai shi ya gina nasa ne a bisa asasin hankali zalla, shi kuwa Sidi Sistani ya taro hujjoji ne na tarihi da na zamani sai ya fito da muhimman ka’idojin warware sabanin sa’an nan kuma ya shiga koyar da su a darasin fikihu.

H) Gwama Tsakanin Ra’ayoyi Mabambanta

Abinda aka fi sani a gurin da dama daga cikin Malamai shi ne takaituwa da koyar da wani tafarki ayyananne ko kuma wata manufa ta musamman amma abinda aka sani daga Sidi Sistani shi ne hadowa da kuma gwama tsakanin ra’ayin karantarwar Mashhad da ra’ayin Makarantun Kum da Tafarkin Malaman Najaf. Yakan kawo ra’ayoyin Mirza Mahdi Isfahani (R.A.) da na Sidi Burujurdi daga Makarantun Mashhad, da ra’ayoyın manyan malaman uku da kuma na Sidi Khu’i (R.A.) da Shaikh Husain Hilli (R.A.) a matsayin makarantar Najaf, wadannan ra’ayoyin da tafarkunan kuwa taro su guri guda yana ba da wadatacciyar hanya gare mu da kuma mayalwaciyar manufar ilimi gare mu.

A fannin fikihu ma yana da tafarkin koyarwa na musamman da ya bambanta da da sauran hanyoyin, salon koyarwar tasa ya kebantu da abubuwa kamar haka:-

A) Auna tsakanin Mazhabar Shia da Sauran Mazhabobi da ba na Shi’a ba

Domin fahintar fikihun Mazhabar Ahlussunna da ya yi zamani da lokacin nassi kamar su Muwatta Malik da Kharraj Abi Yusuf da makamamtansu yana nuna mana munafar Imamai (A.S.) yayin kawo nassi.

B) Sabunta Abubuwan Kaddamarwa

Abu sananne a gurin mafi yawan manyan Malamanmu shi ne cewa suna karbar ka’idojin Fikihu ne kawai kamar yadda magabata suka kawo ba sa kara kome sai dai game da ingancin abinda aka dogara da shi ko kuma cewa babu wata madogarar ta dabam. Amma shi kuwa Sidi Sistani yakan yi karin sigar ka’idojin a wasu sassa. Alal misali dangane da Ka’idar “Ilzam” wadda wasun malamai suke ganin ta bangaren cewa Musulmi Mumini zai iya amfani da ita wajen cim ma manufarsa ko biyan bukatarsa ta kansa daga Ka’idojin wasu Mazhabobi na dabam koda kuwa shi ba ya bin wadannan mazhabobin. Shi kuwa Sidi Sistani yakan bullo ne ta fuskar girmama ra’ayi wato girmama ra’ayin wasu da dokokinsu, inda yakan zo da sigar cewa kowace al’umma akwai irin aurenta.

C) Amfani da dokokin zamani a wasu Bangarori na Fikihu

Kamar inda ya waiwaici dokokin Iraki, da Masar da na Faransa yayin da yake bincike game da cinikayya, da kuma kewayewa da dokokin zamani wajen fayyace ka’idojin fikihu da yalwata madogararsu da guraren aiki da su.

 

عنوان الکتاب