Rubuce - Rubucensa |
||
|
Tun daga shekaru 34 da suka wuce ya fara koyar da Fikihu da Usul da Ilimin sanin masu ruwaito hadisai a marhalar tarbiyyantar da Mujtihidai yana ba da gudummawa mai amfani game da littafin Al-Makasib, da Tahara, As Salat da Alkhadha’u da Al-Khums kamar kuma yadda ya yi a kan Kawa’idul Fikhiyya banganren da ya shafi Riba, da Ka’idatut Takiyya, da Ka’idatul Ilzam. Kazalika ya koyar da Usulul Fikihi daga farko zuwa karshensa har sau uku kuma wasu bayanansa suna nan an tsara su daidai yadda za a iya buga su a matsayin Littafi kuma bayanansa a “Usulul Amaliyya” da “Ta’adul” da “Tarajihu” da kuma wasu bayanai na fikihu a babin Salla da kuma “Ka’idatul Takiyya” da “Ilzam”. Koyarwarsa ta tarbiyyantar da manyan dalibai wadanda hatta wasunsu sun kai ga koyar da darasin share fagen Ijtihadi; kamarsu Allama Shaikh Mahdi Marwarid da Allama Sidi Habib Husainani, da Allama Sidi Murtadha Isfahani, da Allama Shaikh Bakir Irawani da sauransu da dama da ke daga cikin manyan makarantun addini. A halin yana koyarwa da tarbiyyantar da dalibai har ila yau yana ta rubuce-rubuce domin wadata makarantun addini da littafan da ake bukata baicin kuma rubuce koyarwar malamansa da ya kasance yana karatu a gurinsu. Ga Sunayen wasu daga cikin rubuce-rubucensa kamar haka:- 1- Sharhul Urwatul Wuthka - Littafin fikihu mafi girman matsayi da ake karantawa. 2- Kitabul kadha 3- Al- Buhuthul Usuliyya 4- Kitabul Bai’i wal Khiyarat 5- Risalatun Fil Libasul Mashkukun Fihi 6- Risalatun Fil Ka’idatul Yadi. 7- Risalatun Fi Salatul Musafir 8- Risalatun Fi Ka’idati Tajawuz Wal Farag. 9- Risalatun Fil Kibla 10- Risalatun Fil Takiyya 11- Risalatun Fi Ka’idatul Ilzam 12- Risalatun Fil Ijtihadi Wat Taklid 13- Risalatun Fi Ka’idati La- Dharara 14- Risalatun Fir Riba 15- Risalatun Fi Hujjiyyati Marasilu bin Abi Umair. 16- Nakdi Risalata Tashihil Asanid Lil Ardabil 17- Sharhu Mashikhatut Tahzib 18- Risalatun Fi Masalikil Kudama Fi hujjiyyatul Akhbar. Wadannan duk kari ne a kan rubuce rubucensa a wasu fannonin da kuma Risala babbab a kan hukunce-hukuncen ayyukan ibada don masu yi masa takalidi suna bin hukunce-hukunce da fatawarsa.
|
||