FASALI NA UKU

 

HAQIQANIN RUHI DA MAKOMA A RANAR QIYAMA

 

bullet

Bahasi Na Farko: Haqiqanin Ruhi Da Tajarrudinsa

bullet

Ruhi Cikin Alqur'ani Da Hadisi

bullet

TAJARRUDIN RUHI

bullet

Dalilan Masu Aqidar Tajarrudi

bullet

Na Uku: Hujjojin Hankali

bullet

Na Huxu: Hujjojin Ilmin Kimiyya Na Gwaji

bullet

BAHASI NA BIYU: HAQIQANIN TASHIN QIYAMA

bullet

Na Farko – Tayarwa Ta Jiki

bullet

Haqiqanin Tayarwa Ta Jiki

bullet

Inkarin Tayarwa Ta Jiki

bullet

Shubuhohi Kan Tayarwa ta Jiki

bullet

Na Farko: Shubuhar Ma-Ciyi da Wanda Aka Ci

bullet

Na Biyu: Rashin Yiyuwar Dawowar Abin Da Ya Gushe:

bullet

Na Uku: Yawaituwar Jiki


 

HAQIQANIN RUHI DA MAKOMA A RANAR QIYAMA

Bahasi Na Farko: Haqiqanin Ruhi Da Tajarrudinsa([1])

 Haqiqanin Ruhi Ba A Sarari Yake Ba

 

Babu shakka ruhin mutum shi ne ya fi kusanci da shi kuma ya fi liqewa da shi, sai dai an jahilci haqiqaninsa kuma hankalin xan'Adam ya jahilci haqiqaninsa masaniya kan sirrinsa.

Don haka ne ma aka samu savanin ra'ayi tsakanin malaman falsafa da na aqida kan asalin yanayin ruhi. Shin shi arad ne ko kuma jauhar[2] ne; sannan kuma a vangaren samuwa ruhi shin shi tun fil azal yana nan ne ko kuma daga baya ne aka samar da shi, da kuma alaqar ruhi da jiki da kuma dangantakarsa da shi, sannan kuma da tabbatarsa bayan mutuwa, da kuma haqiqanin rabautarsa (a lahira) da rashin rabautarsa da dai sauran irin waxannan bahasi masu yawan gaske([3]).

Ba za mu ambaci ra'ayoyin waxannan masana ba, za mu taqaita ne kawai da bahasi kan ma'anonin ruhi da suka zo cikin Alqur'ani mai girma da tsarkakan Sunnoni da kuma abubuwan da aka faxi dangane da tajarradin ruhi da kuvutarsa daga haqiqanin abu mai jiki (madda) da siffofinsa da kuma tabbatarsa bayan mutuwa duk da lalacewar jiki. Za mu yi hakan ne saboda tasirin da wannan bahasi yake da shi wajen fahimtar haqiqanin makoma..

 

Ruhi Cikin Alqur'ani Da Hadisi:

Abin da aka faxi dangane da ruhi: Shi ne abin da jiki yake dogaro da shi, da shi yake sansancewa da motsi da nufi. An ambace shi da wannan ma'ana da kuma sauran ma'anoni cikin ayoyi daban-daban na Alqur'ani da suka sauka a Makka da Madina. Bari mu ambato wasu daga cikinsu kuma mu jera su daidai da ma'anonin da suka zo, kana mu haxa da hadisai:

 

1. Ruhin Da Shi Ne Musabbabin Rayuwa: Allah Ta'ala na cewa:

﴿æíóÓúÃóáõæäóßó Úóä ÇáÑøõæÍö Þõáö ÇáÑøõÍõ ãöäú ÃãúÑöÑÈøöí æóãóÇ ÃõæÊíÊõã ãäó ÇáúÚöáúãö ÅáÇøó ÞóáöíáÇð

"Suna tambayarka kan ruhi. Ka ce "Ruhi daga al'amarin Ubangijina ne, kuma ba a ba ku (kome) ba daga ilmi face kaxan"([4]).

 Malaman tafsiri sun yi maganganu daban-daban kan wannan aya([5]), mafi bayyana daga cikin waxannan maganganu shi ne cewa abin nufi ruhin da da shi ne jiki yake qarfafa. Abin da ke tabbatar da hakan kuwa shi ne dalilin saukar ayar([6]) da kuma wasu hadisai da suka zo daga Ahlulbaiti (a.s).

Daga cikinsu akwai hadisin da Abu Basir ya ruwaito daga Abu Ja'afar al-Baqir (a.s) ko kuma daga Abu Abdullah al-Sadiq (a.s) cewa: Na tambaye shi dangane da faxinSa Maxaukaki

 ﴿æóíóÓúÃóáõæäóßó Úóäö ÇáÑøõæÍ.ö  

"Suna tambayarka kan ruhi…"

 mene ne ma'anar ruhin? Sai ya ce: "Wanda ke cikin dabbobi da mutane", sai  na ce: mene ne shi? Sai ya ce: "Shi daga malakutu(¯) yake, daga qudura([7])"

Haka nan ana iya ganin ma'anoni daban-daban na faxin Allah Maxaukaki cewa:

 ﴿  Þõáö ÇáÑøõæÍõ ãöäú ÃóãúÑö ÑóÈøöí  

" Ka ce "Ruhi daga al'amarin Ubangijina ne…"

 cikin maganganun malaman tafsiri, mafi shahara daga cikinsu su ne:

Na Farko: An tambayi Ma'aikin Allah (s.a.w.a) dangane da haqiqanin na ruhi, sai ya amsa da wannan ayar da cewa ruhi na daga nau'in al'amari, daga nan kuma sai Allah Maxaukakin Sarki Ya bayyana al'amarin naSa da faxinsa Maxaukaki cewa:

﴿ÅöäøóãÇó ÃóãúÑõåõ ÅöÐÇ ÃÑóÇÏó ÔóíúÆÇð Ãóäú íóÞõæáó áóåõ ßõäú Ýóíóßõæäõ ! ÝóÓõÈúÍóÇäó ÇáøóÐöí ÈöíóÏöåö ãóáóßõæÊõ ßõáøö ÔóíÆò æÅöáóíåö ÊõÑÌóÚõæäó

"Al'amarinSa kawai, idan Ya yi nufin wani abu, sai Ya ce masa, 'Ka kasance', sai ya kasance. Saboda haka, tsarki ya tabbata ga Wanda mallakar kowane abu take ga HannayenSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku([8])".

 Wannan yana nuna mana cewa al'amarinsa Maxaukakin Sarki daga malakutu da kuma qudura yake, shi ne kuwa faxinsa ga abu "ka kasance", wanda hakan kalma ce ta samarwa da rayuwa wacce Yake jefa ta ga abubuwa sai su kasance da yardarSa ba tare da gittawar wasu sabubba na samuwa, ba tare da kuma sharaxin lokaci ko kuma waje ba. Ana iya ganin hakan cikin faxinSa Maxaukaki cewa:

 ﴿æóãóÇ ÃóãúÑõäóÇ ÅáÇøó æóÇÍöÏóÉõñ ßóáóãúÍò ÈöÇáúÈóÕóÑöó

"Kuma al'amarinMu bai zamo ba face da kalma xaya, kamar walqawar ido([9])".

 Daga nan za mu iya fahimtar cewar wannan ayar tana nuni ne da cewar haqiqanin ruhi yana daga cikin al'amurran da muka ambata ne([10]).

Na Biyu: Yayin da aka tambaye shi kan haqiqanin ruhi, sai ya amsa da ayar: "Ruhi daga al'amarin Ubangijina ne", wato na daga cikin abubuwan da Ubangiji ya bar wa kansa ilminsa babu wani wanda ya sanshi([11]).

Na Uku: Yayin da aka tambaye shi (s.a.w.a) kan ruhi, shin shi na tun fil azal (qadimi)ne ko kuma fararre, sai ya amsa da ayar "Ruhi daga al'amarin Ubangijina ne", wato na daga aikinSa da halittarSa, wato yana nufin cewa ruhi fararre ne, mai samuwa daga aikin Allah([12]).

Ma'anar ruhi cikin ayar da ta gabata ta yi daidai da faxin Allah Ta'ala dangane da halittar Annabi Adamu (a.s):

 ﴿ÝóÅöÐÇó ÓóæøóíúÊõåõ æóäóÝóÎúÊõ Ýöíåö ãä ÑøõæÍí  

"To, idan Na daidaita shi, kuma Na hura daga RuhiNa a cikinsa..([13])",

da kuma faxinSa Maxaukin Sarki dangane da halittar Annabi Isa (a.s) :

(ÝóäóÝóÎúäóÇ ÝöíåóÇ ãöäú ÑøõæÍöäóÇ æóÌóÚóáúäóÇåóÇæÇÈúäóåóÇ ÇóíóÉð áøöáúÚóÇáóãöíäóó  )

"Sai Muka hura a cikinta daga ruhinMu. Kuma Muka sanya ta ita da xanta wata aya ga duniya([14])"

, da kuma faxinSa cewa: 

   (öäøóãóÇ ÇáúãóÓíÍõ ÚöíÓì ÇÈúäõ ãóÑúíóãó ÑóÓõæáõ Çááåö æóßóáöãóÊõåõ ÃáúÞóÇåóÇ Åáì ãóÑúíóãó æÑõæÍñ ãöäúåõ)

"Abin da kawai aka sani, Masihu Isa xan Maryama Manzon Allah ne kuma kalmarSa ya jefa ta zuwa ga Maryama kuma ruhi ne daga gare Shi…([15])".

Ruhi a nan yana nuni ne da wani voyayyen qarfi wanda aka samar da rayuwa da shi da kuma sirrin Ruhin Ubangiji wanda yake canza abu maras rai zuwa ga mai rai. A nan Allah Ya keve ruhin Adamu da Isa (a.s) saboda halittarsu ta sava da yadda ya halicce sauran halittu, sannan kuma Allah Ya danganta ma kansa lafazin ruhi ne don nuna xaukaka da girmamawa da kuma kevance su da Ya yi kamar yadda Ya jingina kalma gida ga kanSa cikin faxinsa Maxaukaki cewa:

(óæóØóåøöÑú ÈóíúÊöí)([16])

“Kuma ka tsarkake XakiNa”.

 

2. Al-Ruh Da Ma'anar  Jibrilu:

Allah Ta'ala Na cewa:

 (ÝóÃóÑúÓóáúäóÇ ÅöáóíúåóÇ ÑõæÍóäóÇ ÝóÊóãóËøóáó áóåóÇ ÈóÔóÑðÇ ÓóæöíøÇðó )

"Sai muka aika ruhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaici([17])"

. Abin nufi a nan shi ne Mala'ika Jibrilu (a.s)([18]). Allah Ya siffanta shi da amana da kuma tsarki cikin faxinSa cewa:

 (äóÒóáó Èöåö ÇáÑøóæÍõ ÇáÃóãöíäõ Úóáóì ÞóáúÈößó )

"Ruhi amintacce ne ya sauka da shi([19])",

 da faxinSa Maxaukaki:

 (Þõáú äóÒøóáóåõ ÑõæÍõ ÇáúÞõÏõÓö ãöä ÑøóÈøößóòò )

"Ka ce, Ruhul Qudusi ne ya sassaukar da shi, daga Ubangijinka([20])".

Yayin da yake magana kan ma'anar wannan aya, Imam Abi Ja'afar al-Baqir (a.s) yana cewa: "Wanda ake nufi shi ne Mala'ika Jibrilu (a.s)([21])". Yana da kyau a fahimci cewa haxa sunan al-Ruh da Allah Maxaukakin Sarki Ya yi ga kanSa ba don komai ba ne face sai don girmamawa([22]).

 

3. Al-Ruh Da Ma'anar Halitta Wacce Ta Fi Mala'iku:

Idan muka duba wasu ayoyi da hadisai za mu ga suna nuni da cewa shi (Al-Ruh) wata halitta da take da maxaukakin matsayi a wajen Allah Maxaukakin Sarki kuma Allah xin Ya kan wakilta shi akan wasu ayyuka nasa masu muhimmanci da suke da alaqa da gaibu da kuma wahayi, shi kaxai xinsa ko kuma tare da sauran Mala'iku a duniya ne ko kuma a can lahira. Allah Ta’ala Na cewa:

 (íóæúãó íóÞõæãõ ÇáÑøõÍõ æÇáúãáÇÆößÉõ ÕóÝøðÇ áÇøóíóÊóßóáøóãõæäó)

"Ranar da Ruhi da mala'iku za su tsaya a cikin safu, ba su magana([23])".

 Sannan Yana cewa:

 (ÊóäóÒøóáõ ÇáãóáÇóÆößóÉõ æÇáÑøõÍõ ÝöíåóÇ ÈÅöÐúäö ÑóÈøöåöãú ãöäú ßõáøö ÃóãúÑò )

"Mala'iku da Ruhi suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu saboda kowane umurni([24])".

 Wasu ruwayoyi sun siffanta wannan halitta (al-Ruh) da cewa shi wata halitta ce da tafi Mala'ika([25]) - ko kuma wani mala'ika da yake sama da Jibrilu da Mika'ilu – yana tare da Manzon Allah (s.a.w.a) da kuma Imamai (a.s)([26]).

An ruwaito daga Abu Basir, daga Abu Abdullah al-Sadiq (a.s) yayin da yake magana kan faxin Allah Ta'ala cewa:

 (æóßóÐóáößó ÃóæúÍíúäóÇ Åöáóíúßó ÑõæÍðÇ ãöäú ÃóãúÑöäóÇ )

"Kuma kamar wancan , Mun aika wani ruhi zuwa gare ka daga gare Mu([27])"

 cewa: "Wata halitta ce daga halittun Allah, wanda ya fi Jibrilu da Mika'ilu xaukaka, ya kasance yana tare da Manzon Allah (s.a.w.a) yana ba shi labari kuma yana tabbatar da shi, kamar yadda kuma ya kasance da Imaman da suke bayansa([28])".

 

4. Al-Ruhi Da Ma'anar Imani:

 Allah Ta'ala na cewa:

 (æóÃóíøóÏóåõãú ÈöÑæÍò ãöäúåõ )

"Kuma Ya qarfafa su da wani ruhi([29])",

 an ruwaito daga Imam Baqir da Sadiq (a.s) suna cewa abin da ake nufi da al-Ruh cikin wannan aya shi ne imani([30]).

An ruwaito daga Abu Bukair yana cewa: wata rana na ce da Abu Ja'afar al-Baqir (a.s) game da faxin Manzon Allah (s.a.w.a): "Ruhin imani kan fita daga mai zina a lokacin da yake zina" sai ya ce: "Shi ne faxin Allah Ta'ala  

(æóÃóíøóÏóåõãú ÈöÑæÍò ãöäúåõ )

 wannan shi ne abin da zai rabu da shi([31])".

Haka nan an ruwaito irin wannan magana daga Imam Sadiq (a.s)([32]).

Wasu sun ce: zahirin maganar Allah Maxaukakin Sarki tana nuni ne da cewa, baya ga ruhinsa na xan'Adam wanda mumini da kafiri suke da shi, mumini yana da wani ruhi kuma na daban wanda yake ba shi wata sabuwar rayuwa ta daban kuma yake taimaka masa da wani sabon qarfi. Wannan shi ne abin da ake ishara da shi cikin faxinSa Mai girma da xaukakaka cewa:

)Ãóæóãóä ßóÇäó ãóíúÊðÇ ÝóÃóÍúíóíúäóÇåõ æóÌóÚóáúäóÇáóåõ äõæÑÇð íóãúÔöí Èöåö Ýöí ÇáäøóÇÓö ßóãóä ãóËóáõåõ Ýöí ÇáÙøõáõãóÇÊö áóíúÓó ÈöÎóÇÑöÌò ãöäúåóÇö(

 "Shin, kuma wanda ya kasance matacce, sa'an nan Muka rayar da shi, kuma Muka sanya wani haske dominsa, yana tafiya da shi, yana zama kamar wanda misalinsa yana cikin duffai, shi kuma ba mai fita ba daga gare su?...([33])".

 

5. Al-Ruh Da Ma'anar Littafi da Annabci:

 Allah Maxaukakin Sarki cikin LittafinSa mai tsarki na cewa:

(íõäóÒøöáõ ÇáúãáÇóÆößóÉó ÈöÇáÑøõæÍö ãäú ÃóãúÑöåö Úóáìãóä íóÔóÇÁõ ãäú ÚöÈÇÏöåö)

"Yana sassaukar da mala'iku da Ruhi daga umarninSa a kan wanda Yake so daga bayinSa([34])",

 da kuma faxinSa Maxaukakin Sarki:

 (íõáúÞöí ÇáÑøõæÍó ãäú ÃóãúÑöåö Úóáìãóä íóÔóÇÁõ ãäú ÚöÈÇÏöåö  )

"Yana jefa ruhi, daga al'amarinSa a kan wanda Ya so daga bayinsa([35])".

 An ruwaito Imam Baqir (a.s), yayin da yake magana kan aya ta farko, yana cewa: "Da Littafi da Annabci([36])".

Wasu suna cewa: An ambaci kalmar ruhi ne a nan akan annabci, addini, wahayi da sauran abubuwan da ruhi da hankali suke rayuwa da su saboda ta hanyarsu ne ake samun sanin Allah da Mala'iku da Littattafai da ManzanninSa. Kuma ruhi da waxannan ilmummuka yake rayuwa([37]).

  

TAJARRUDIN RUHI

Abin nufi da ruhi shi ne abin da mutum yake nuni gare shi yayin da yake cewa 'ni' ko kuma abin da ake ce masa 'al-nafs al-Naxiqa([38]) (rai mai hankali). Sannan abin nufi da tajarrudinsa (ruhi) kuma shi ne kasancewarsa ba jiki ba ne wanda yake iya rabuwa wanda yake da lokaci da wuri([39]). Yanayinsa da kuma yadda ake xaukarsa savanin yanayin jiki da sauran ababen da suka haxa jikin([40]).

Wannan mas’ala da ke da alaqa da dawwamar ruhi tana daga cikin manya-manyan mas’alolin falsafa da masana cikin qarnonin da suka gabata suka yi jayayya kanta saboda kasantuwarta daga cikin mas’alolin da suka fi shafan zuciyar xan’Adam da kuma al’amurransa saboda ita ce take ba shi natsuwa kan burinsa yayin da ya rabu da abin da ke zahiri. Tsananin jayayyar na nan tsakanin mabiya zahiri (madiyun), masu inkarin dawwamar ruhi da kuma masu ra’ayin tajarrudin ruhi da dawwamarsa. Yanzu bari mu kawo wasu sassa na maganganun vangarorin biyu da wasu dalilansu:

 

1- Al-Maddiyun([41]):

Zantuttukan masu wannan aqida sun sassava dangane da matsayin ruhi ga jiki da kuma rabe-rabensa([42]), sai dai dukkansu suna xaukar cewa xan’Adam shi ne wannan jiki na zahiri kuma babu wani samamme sama da (madda), wai shi ruhi. A ganinsu ruhi sifface ta jiki wacce take bin dukkan dokokin da suke gudanar da shi. Ta wata fuska kuma, ruhi wani gungu ne da ya tattara su hankali da shu’uri da nufi da kuma tunani. Wato ruhi ba komai ba ne face jumlar ayyuka irin na gavovi, ba shi da wani bambanci da sauran ayyukan da jiki ke gudanarwa.

Haka nan suna ganin cewa tunani da sani ba komai suke ba face sakamakon harakar motshin jijiyoyi da kuma sassauyawar sinadarin da ke cikin kwayoyin halitta na hanyar tunani. Dukkan waxannan tasirai da harakoki na ruhi suna bayyana ne bayan samuwar hankali da tsarin jijiyoyin kai saqo kuma suna macewa ne yayin da jiki ya mutu. Saboda haka idan mutum ya mutu to mutumtakarsa (shaksiyya) ta vace, jikinsa ya rududduge kuma duk wani abin da ya cimma a fagen aikin hankali da xaukaka da kamalar ruhi, sun gushe([43]).

Sabuwar falsafar maddiyya ta yi kunnen uwar shegu da siffofi da kuma tasiri irin na ruhi, waxanda ba sa bin qa’idar da madda take tafe a kai. Suna cewa ruhi da ma dukkanin alamominsa irin su shu’uri da ilmi ba su da wata samuwa daban da ta jikin madda na xan’Adam, wai su waxannan haqiqaninsu shi ne su aiki ne da jiki ke yi sakamakon dangantakarsa da duniya (waje da jikin). Wai tuntuntuni da ma’anoni ba su samuwa sai ta hanyar harkar madda, tamkar samuwar zafi yayin da aka goga wasu yankuna biyu na qarfe. Wato ilahirin siffofin da xan’Adam yake da su ba komai ba ne face karo da duniyar waje (waje da xan’Adam), kamar yadda Povlov ya ce a nazariyyarsa, wato waraka (wa’ayi) da dukkan alamominta, ba komai ba ne sai aikin madda wacce tsaruwarta ya kai matuqa, wato dai sanin aiki ne da kuma haraka ta qwaqwalwa.

Sun ci gaba da cewa: Tunani ta madiyyar ta bani in baka (al-maddiyya al-jadaliyya) tana kore tunanin cewa ruhi wani abu ne wanda ba ya dogara da madda; abin da ake danganta shi da ruhi aiki ne na madda yayin da take cikin mafi xaukakar yanayinta na aikin gava, sakamakon haraka da mu’amalar zamantakewa([44]).

Mabiya aqidar maddiyya suna kafa hujjar tabbatar da mazhabarsu wacce ta kafu bisa inkarin ruhi, ta hanyar riqo da wasu qaddare-qaddare waxanda ko kusa ba a sarari suke ba, da kuma wasu raunanan bayanan da ba za a iya tabbatar da su ba([45]).

 

2- Masu Ra’ayin Tajarrudin Ruhi:

 Galibin al’ummomin da suka gabata kamar su ‘yan Hindu da Misrawa da Sinawa da Farisawa da kuma Girkawa sun yi imani da samuwar ruhi da kuma wanzuwarsa. Haka nan malamansu na falsafa da mawaqansu. Misali Sokrat da Aflatun sun kasance suna ganin cewa ruhi wani jauhari ne mai wanzuwa, kuma samamme tun fil azal. Yayin da xan tayi ya kai matuqarsa sai ruhi ya liqe masa yana cikin ciki. Bayan mutum ya mutu kuma sai ruhi ya koma wurinsa na farko. Aflatun yana ganin cewa ruhi guda biyu ne: ruhin da yake hankaltawa (aikin hankali) shi ne dawwamamme kuma a qwaqwalwa yake. Xayan kuma baya dawwama kuma baya hankaltawa. Shi xin ma ya kasu kashi biyu: mai fushi da ke cikin zukata da kuma mai sha’awa da yake cikin ciki.

Arosto kuma yana ganin cewa ruhi yana faruwa ne tare da jiki. Yayin da jiki yake samun kamala sai ruhi ya  samu ba tare da can yana da wata rayuwa ba. A ganin wannan masanin falsafa, akwai ruhi iri uku da suke tsirowa daga jiki, su ne: ruhi mai hankaltawa – wato rai mai tunani – kuma ya xauke shi mujarradi; sai ruhin dabbantaka wato mai riska da kuma ruhi mai qoto. Guda biyun nan ba mujarradai ba ne a ganin Arosto([46]).

Dikat (Des Carte) (wanda ya mutu a shekarar 1560) ya bayar da muhimmanci ga bambancin ruhi da jiki da kuma ayyana siffofin ko wane guda. A ganinsa ruhi wani jauhari ne wanda siffar da tafi kevantarsa, ita ce tunani. Ba za a yi masa tunanin yiyuwar rabuwa yanki-yanki ko kuma rashin sajewar jinsi ba. Dikat ya xauki jiki a matsayin wani jauhari ne wanda mafi kevantar siffofinsa ita ce tsawo. Jiki yanda yanayin sura da kuma motsi, kuma bisa xabi’arsa yana iya kasuwa da canzawa([47]).

Maganganun masana falsafa na yammaci na zamanin da da na yanzu kan batun ruhi suna da yawa amma za mu taqaita kan waxanda muka ambata.

Su kuwa malamai da masana ilmin falsafa musulmi ra’ayinsu daban ne. Misali Sheikh Saduq yana cewa: “Abin da muka yi imani da shi, shi ne cewa ruhi ba ya daga jinsin jiki, shi wata halitta ce ta daban saboda faxin Allah cewa:

 ﴿Ëõãøó ÃóäÔóÃúäóÇåõ ÎóáúÞðÇ ÂÎóÑó ÝóÊóÈóÇÑóßó Çááøóåõ ÃóÍúÓóäõ ÇáúÎóÇáöÞöíäó

“Sannan kuma Muka mai da shi wata halitta daban. Saboda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun masu halittawa([48]).

 Idan rayuka suka bar jiki, zasu ci gaba da wanzuwa, waxansu za a ni’imartar da su waxansu kuma za a azabtar har lokacin da za a komar da su cikin jikkunan da suka kasance ciki([49]).

Nasiruddeen al-Tusi na cewa: “Rai jauhari ne mujarradi (wato mai tajarrudi). Allamah Hilli cikin sharhinsa na cewa: Akwai maganganu daban-daban kan haqiqanin rai da kuma shin shi jauhari ne ko a'a. Masu cewa shi jauhari ce su ma sun sassava kan shin shi mujarradi ne ko a'a. Abin da ya fi shahara a wajen malaman farko da kuma malaman aqida kamar su Bani Naubakht da Sheikh Mufid daga cikin malaman Imamiyya da Gazali daga cikin mabiya aqidar Asha’ira sun tafi kan cewa rai jauhari ne mujarradi, kuma shi ba jiki ba ne ba kuma siffar jiki ba([50]). Alaqarsa da jiki, alaqa ce ta gudanarwa…..

Waxansu malaman Asha’ira irinsu Raghib al-Isfahani da Fakhrurrazi da kuma Mu’ammar bn Ubbad al-Sulami daga cikin Mu’utazilawa sun yarda da wannan ra’ayin, haka nan ma Allamah Hilli da Sheikh al-Baha'i daga mabiya Imamiyya da wasunsu da yawa([51]). Waxansu (malamai) na baya-bayan nan kuma sun yi da'awar cewa ruwayoyi da yawa suna bayar da ma'anar tajarrudin rai([52]).

Ibn Sina ya yi imani ne da tajarrudin qarfin hankaltawa kawai, amma Sadrul Muta’allihin al-Shirazi ya yi imani da cewa dukkan qarfin xan’Adam na da fuska ta madda da fuska ta tajarrudi, da kuma cewa dukkanin qarfi na madda na xan’Adam yana tare da qarfi mujarradi, ta yadda yayin da mutum ya mutu, ba kawai hankali ne za a cire masa ba, a’a hankali, qwaqwalwa, gani da ji([53]).

 

Dalilan Masu Aqidar Tajarrudi

Da dama daga cikin masanan falsafar musulmi da aqidarsu sun kafa hujja da nassi da hankali kan cewa ruhi mujarradi ba shi da siffofin jiki, ba ya gushewa da mutuwa, a’a ya kan ci gaba da wanzuwa, ko dai cikin ni’ima ko kuma azaba. Ga wasu daga cikinsu:

 

Na Farko: Dalilai na Alqur’ani,

da suka qumshi waxannan bayanai masu zuwa:

1- Ayoyin Alqur’ani da suke nuni da cewa ruhin shahidai da siddiqai ba sa mutuwa saboda mutuwar jiki kuma ba sa gushewa da gushewarsa, sai dai za su ci gaba da rayuwa cikin ni’ima da kwanciyar hankali. Misali faxin Allah:

 ﴿æóáÇó ÊóÞõæáõæÇú áöãóäú íõÞúÊóáõ Ýöí ÓóÈíáö Çááøåö ÃóãúæóÇÊñ Èóáú ÃóÍúíóÇÁ æóáóßöä áÇøó ÊóÔúÚõÑõæäó

“Kada ku ce ga waxanda ake kashewa a cikin hanyar Allah: matattu ne. A’a rayayyu ne, kuma amma ba ku sansancewa([54]),

 da faxinSa Maxaukakin Sarki cewa: 

       ﴿æóáÇó ÊóÍúÓóÈóäøó ÇáøóÐöíäó ÞõÊöáõæÇú Ýöí ÓóÈöíáö Çááøåö ÃóãúæóÇÊðÇ Èóáú ÃóÍúíóÇÁ ÚöäÏó ÑóÈøöåöãú íõÑúÒóÞõæäó

“Kada ka yi zaton waxanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A’a, rayayyu ne su, a wajen Ubangijinsu. Ana ciyar da su([55]),

 da kuma faxinSa Maxaukakin Sarki cewa:

 ﴿íóÇ ÃóíøóÊõåóÇ ÇáäøóÝúÓõ ÇáúãõØúãóÆöäøóÉõ!ÇÑúÌöÚöí Åöáóì ÑóÈøößö ÑóÇÖöíóÉð ãøóÑúÖöíøóÉð! ÝóÇÏúÎõáöí Ýöí ÚöÈóÇÏöí ! æóÇÏúÎõáöí ÌóäøóÊöí

“Ya kai rai mai natsuwa. Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhali kana mai yarda (da abin da Ya qaddara maka a duniya) abar yardarwa (da sakamakon da za a baka a Lahira. Saboda haka, ka shiga cikin bayiNa Kuma ka shiga AljannaTa([56]).

Dukkan waxannan sun tabbatar da cewa abu ne mai yiyuwa mutum ya zamanto rayayye alhali jikinsa na cikin qasa, wanda hakan yana lizimta kasancewar haqiqanin mutum ya sava wa wannan jiki([57]).

2- Ayoyin da suke nuni da cewa ana azabtar da kafirai a wuta alhali jikinsu na kabari. Misali faxinSa Maxaukaki:

 ﴿æóÍóÇÞó ÈöÂáö ÝöÑúÚóæúäó ÓõæÁõ ÇáúÚóÐóÇÈö ! ÇáäøóÇÑõ íõÚúÑóÖõæäó ÚóáóíúåóÇ ÛõÏõæøðÇ æóÚóÔöíøðÇ æóíóæúãó ÊóÞõæãõ ÇáÓøóÇÚóÉõ

“….kuma mummunar azaba ta wajaba ga mutanen Fir’auna. Wuta, ana gitta su a kanta, safe da maraice, kuma a ranar da Sa’a take tsayuwa…([58])

 da kuma faxinSa:

﴿ãöãøóÇ ÎóØöíÆóÇÊöåöãú ÃõÛúÑöÞõæÇ ÝóÃõÏúÎöáõæÇ äóÇÑðÇ Ýóáóãú íóÌöÏõæÇ áóåõã ãøöä Ïõæäö Çááøóåö ÃóäÕóÇÑðÇ

“Saboda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa’an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sama wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba([59]),

 suna raye ana azabtar da su bayan mutuwar jikkunansu, wanda hakan na nuni da cewa haqiqanin mutum wani abu ne daban ba wannan jikin ba([60]).

3- Ayoyin da suka ambaci mataki-mataki na halittar jiki, kamar faxinSa Maxaukakin Sarki cewa:

﴿ æóáóÞóÏú ÎóáóÞúäóÇ ÇáúÅöäÓóÇäó ãöä ÓõáóÇáóÉò ãøöä Øöíäò ! Ëõãøó ÌóÚóáúäóÇåõ äõØúÝóÉð Ýöí ÞóÑóÇÑò ãøóßöíäò ! Ëõãøó ÎóáóÞúäóÇ ÇáäøõØúÝóÉó ÚóáóÞóÉð ÝóÎóáóÞúäóÇ ÇáúÚóáóÞóÉó ãõÖúÛóÉð ÝóÎóáóÞúäóÇ ÇáúãõÖúÛóÉó ÚöÙóÇãðÇ ÝóßóÓóæúäóÇ ÇáúÚöÙóÇãó áóÍúãðÇ

“Kuma lalle ne, haqiqa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga laka. Sa’an nan kuma Muka sanya shi, xigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya. Sa’an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa’an nan Muka halitta gudan jinin tsoka, sa’an nan nan Muka halitta tsokar ta zama qasusuwa, sa’an nan Muka tufatar da qasusuwan da wani nama….([61]).

 Wannan aya tana nuni da cewa mutum jiki ne da yake girma cikin yanayi daban-daban. Haka nan yayin da Yake magana kan busa rai Allah Maxaukaki na cewa:

    ﴿Ëõãøó ÃóäÔóÃúäóÇåõ ÎóáúÞðÇ ÂÎóÑó ÝóÊóÈóÇÑóßó Çááøóåõ ÃóÍúÓóäõ ÇáúÎóÇáöÞöíäó

“Sa’an nan kuma Muka qaga shi wata halitta daban. Saboda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun masu halittawa”.

 Wato ya samar da wannan tabbataccen jiki da wata halitta ma’abuciyar shu’uri, iko, tunani da hangen nesa da sauran siffofi da ayyuka da ba a samunsu daga sauran jikkuna. Hakan tabbatarwa ne cewa siffofin ruhi wani abu ne da ya sava da abin da muka ambata a baya na yanayin irin na jiki da ake samu cikin halayyar jiki, wanda hakan na nuni da cewa ruhi wani abu ne daban da jiki([62]).

4- Ayoyin da suka bambance tsakanin yankin xan’Adam da yake madda ne mai qarewa da kuma abin da ke tabbata kuma Allah Ya ke xaukansa zuwa gare shi, kamar faxinSa Maxaukaki cewa:

﴿Çááøóåõ íóÊóæóÝøóì ÇáúÃóäÝõÓó Íöíäó ãóæúÊöåóÇ æóÇáøóÊöí áóãú ÊóãõÊú Ýöí ãóäóÇãöåóÇ ÝóíõãúÓößõ ÇáøóÊöí ÞóÖóì ÚóáóíúåóÇ ÇáúãóæúÊó æóíõÑúÓöáõ ÇáúÃõÎúÑóì Åöáóì ÃóÌóáò ãõÓóãøðì

“Allah ne ke karvar rayuka a lokacin mutuwarsu, da waxannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sa’an nan Ya riqe wanda Ya hukumta mutuwa a kansa, kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce([63]).

 Wannan aya tana nuni da cewa xan’Adam ruhi da jiki ne, da kuma cewa ruhi shi ne ke juya jiki da tsara shi bisa umarnin Allah Maxaukakin Sarki, mutuwa kuma tana nufin yanke alaqar da ke tsakanin ruhi da jiki, da kuma cewa, bayan hakan shi zai koma zuwa ga Mahaliccinsa. Allah Maxaukakin Sarki Shi ne ke karvar rai lokacin mutuwar jiki da kuma barcinsa, wanda aka qaddara masa mutuwa sai ya ci gaba da zama wajen Ubangijinsa har zuwa ranar qiyama. Kuma Yana mayar da xayar ga jiki har lokacin da aka xiba masa ya yi.

Malamai suna cewa: Ran da yake mutuwa lokacin barci shi ne ran dake da hankali kuma yake iya bambancewa, idan ya gushe numfashi ba ya gushewa saboda da shi. Shi kuwa wanda ke mutuwa lokacin mutuwa shi ne ran da ke tattare da rayuwa wanda idan ya kawu, rai ma zai tafi tare da shi. Saboda haka xaukar rai yayin barci take kishiyar farkawa kuma ruhi yana kasancewa tare da ita. Ita kuwa xaukar rai yayin mutuwa kishiyar rayuwa ce, ruhi na fita daga jiki yayin xaukar rai([64]).

Saboda haka, a bisa mahangar Alqur’ani, abin da yake shi ne haqiqanin mutumtakar mutum zai ci gaba da wanzuwa, wanda shi ne ruhi, wato wannan haqiqa ma’abuciya iko da kuma fahimta alhali jiki kuma zai gushe([65]).

Abin da wannan aya ta qumsa na daga ‘xauka’ da ‘riqo’ da ‘aikawa’ na nuni da bambanci da ke tsakanin rai da jiki, domin waxannan siffofi sun kevanta ne da ruhi banda jiki. Idan har haqiqanin xan’Adam madda ce babu ma’ana ga ‘xauka’ da ‘aikawa’ da kuma ‘riqo’.

5- FaxinSa Ta’ala:

﴿æóíóÓúÃóáõæäóßó Úóäö ÇáÑøõæÍö Þõáö ÇáÑøõæÍõ ãöäú ÃóãúÑö ÑóÈøöí

“Suna tambayarka dangane da ruhi. Ka ce ruhi daga al’amarin Ubangijina ne…([66]).

 Wannan umarni (ko al’amari) shi ne faxin ‘kun’ da ke cikin Faxinsa Maxaukaki:

 ﴿ÅöäøóãóÇ ÃóãúÑõåõ ÅöÐóÇ ÃóÑóÇÏó ÔóíúÆðÇ Ãóäú íóÞõæáó áóåõ ßõäú Ýóíóßõæäõ

“UmarninSa, idan ya yi nufin wani abu, sai Ya ce kawai ‘Ka kasance’ sai ya kasance (kamar yadda Ya nufa)([67]).

 Wato umarni da ake aikata shi nan take ba na lokaci-lokaci ba, ba tare da sharaxi na lokaci ko bigire ba. Daga nan za mu iya fahimtar cewa wannan umarni tare da ruhi wani abu ne da ba irin na jiki ba kuma ba madda ba, saboda daga cikin hukumce-hukumce na gaba xaya dangane da halittu ma’abuta jiki, shi ne cewa su halittu ne da aka xaure su da lokaci da bigire kuma samuwarsu sannu-sannu ne, saboda haka ruhi ba jiki ne na madda ba([68]).

 

Na Biyu: Dalilai Daga Sunna.

 Suna da yawa, a nan za mu ambaci wasu ne kawai daga cikinsu:

1- Faxin Manzon Allah (s.a.w.a) cewa: Wanda ya yi mini salati wajen kabarina zan ji shi, wanda kuma ya yi mini salati daga nesa za a sanar da ni. Sannan yana cewa: Wanda ya mini salati sau guda zan masa sau goma, wanda kuma ya yi min salati sau goma, zan masa salati sau xari, to mutum ya yawaita yi mini salati…... Wannan hadisi na nuna mana cewa Manzon Allah (s.a.w.a) yana jin salatin da ake masa hatta bayan barinsa duniya, hakan kuwa ba zai faru ba har sai in ya kasance rayayye a wajen Allah Maxaukakin Sarki. Haka nan Imamai (a.s) suna jin sallmar mai musu sallama daga kusa, kuma ana sanar da su sallamar mai musu sallama daga nesa. Dangane da haka an samu ingantattun ruwayoyi daga gare su (a.s)([69]).

2- An ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a) cewa wata rana ya tsaya a Badar, yana ce ma mushirikan da aka kashe a yayin yaqin cewa: Kun kasance muggan maqwabta ga Manzon Allah, kun fitar da shi daga gidansa kuka kore shi, sannan kuma kuka taru kuka yaqe shi, haqiqa na samu abin da Ubangijina Ya yi mini alqawari gaskiya ne, shin kun sami abin da Ubangijinku Ya yi muku alqawarinsa gaskiya ne? Sai aka ce masa ya ya kake magana da su bayan sun mutu? Sai ya ce: Wallahi ba ku fi su ji ba, da na juya fuskata daga gare su Mala’iku za su kama su da qangi na qarfe([70]).

3- Da faxinsa (s.a.w.a) cikin wata doguwar huxuba cewa: Har lokacin da aka xauko mamaci a kan makararsa, ruhinsa zai taso kan makarar, ya ce: Ya ku dangina da ‘ya’yana, kada ku bari duniya ta yi wasa da ku kamar yadda ta yi wasa da ni, na tara dukiya ta hanyar halal da haram, dukiyar ta zamanto ta wani wahalar kuma a kaina, ku hankalta daga abin da ya same ni([71]).

4- Daga Amirul Muminina (a.s) cewa wata rana ya yi hawa, bayan yaqin Basra, har ya iso inda Ka’ab bn Surat yake yana kwance tsakanin gawawwaki sai ya ce: Ku zaunar da Ka’ab bn Surat, sai aka zaunar da shi, sai ya ce masa: Ya Ka’ab bn Surat, haqiqa na tarar da abin da Ubangijina ya yi min alqawarinsa, shin ka tarar da abin da Ubangijinka ya yi maka alqawari?. Daga nan sai ya ce: Ku kwantar da Ka’ab. Sannan ya aikata hakan ga Talha bn Abdullah. Sai wani daga cikin sahabbansa ya tambaye shi cewa: Ya Amiral Mumini, me ya sa kake magana da waxannan gawawwaki da ba sa jinka? Sai ya ce masa: Dakata ya kai wannan, wallahi sun ji maganata kamar yadda mutanen rijiya suka ji kalamin Manzon Allah (s.a.w.a)([72]).

5- Daga Habba al-Arni, yana cewa: Wata rana na fita tare da Amirul Muminina (a.s) sai ya tsaya a (maqabartar) Wadi’u al-Salam, tamkar yana magana da mutanen da ke wajen…sai na ce masa: Ya Amiral Muminin, lalle ni na damu da irin wannan doguwar tsayuwa da ka yi….sai ya ce min: Ya Habba, hakan ba wani abu ba ne face tattaunawa ce da mumini gami da xebe kewa, sai na ce: Ya Amiral Muminin, suma hakan suke? Sai ya ce: Na’am, da za a yaye maka shamaki da ka gansu a zaune suna magana, suna fuskantar juna ([73]).

6- Daga Abu Basir yana cewa: Ya tambayi Abu Abdullah (a.s) dangane da ruhin muminai, sai ya ce: Suna cikin xakuna a Aljanna, suna ci daga abincinta, suna kuma sha daga abin shanta, suna cewa: Ya Ubangijinmu Ka tayar da qiyama a gare mu, Ka cika mana alqawarin da Ka yi mana, Ka riskar da na qarshenmu da na farkonmu([74]).

7- Daga Abu Basir, daga Abu Abdullah (a.s) yana cewa: Na tambaye shi kan ruhin mushirikai, sai ya ce: Suna cikin wuta ana azabtar da su, suna cewa: Ya Ubangijinmu kada ka tsayar mana da qiyama, kuma Kada ka cika mana abin da Ka yi mana alqawarinsa, kuma Kada ka riskar da na qarshenmu da na farkonmu([75]).

 

Na Uku: Hujjojin Hankali

Akwai hujjoji da dama da masu cewa rai (ruhi) ya kuvuta daga siffofin madda suka dogara da su. A nan za mu ambaci wasunsu:

1- A sarari yake cewa bayanai da ilmomin xan’Adam kuvutattu ne daga madda, saboda haka ilmin da ya rataya da ita ba makawa yana dacewa da ita, wato ke nan mujarradi ne saboda tajarrudinta. Ashe ka ga gurin da sani yake – wato rai – lalle ne shi ma kazalika mujarradi ne domin koruwar shigar mujarradin abu cikin abin da yake madda.

2- Abubuwa da suke na madda ne suna kasuwa, alhali sani wanda yake rabe yake da rai baya kasuwa, domin haka gurin da yake raben ma baya kasuwa. Sannan kuma da a ce muhallin sani (ilmi) na game (wato waxanda ba filla-filla suke ba) jiki ne ko kuma abin da ya samo asali daga jiki, to da ilmin ya zamo masu kasuwa (rarrabuwa). Domin kuwa abin da yake sauka cikin abu mai kasuwa shi ma mai kasuwa ne; ga shi kuma kasuwar sani da ma’anoni na cikin zuciya mustahili ne.

3- Rayukan ‘yan Adam suna iya aikata ayyuka da riskar abubuwa ba tare da iyaka ba, tamkar hankaltar (tunanin) adadi mara iyaka alhali qarfi irin na jiki ba ya aikata abin da ba shi da iyaka. Ashe ran xan’Adam wani abu ne ban da jiki.

4- Da a ce jakar (maxaukin) ilmi qwaqwalwa ce ko kuma wata gavar hankalta da riskar abubuwa, to da duk lokacin da aka qara mata wani sani sai ya rufe wani bigire daga jikinta sannan yiyuwar xaukar sani ga xan’Adam sai zama mai iyaka, tun da dai yiyuwar karvar sani a wajen madda mai iyaka ce, kamar misalin farar takarda wacce take cika da rubutu ko kuma faifai (faifan garmaho ko kaset na radiyo ko bidiyo, ko kuma na sidi –CD-) wanda ya kan cika da sauti ko hoto. Abin da wannan yake nufi shi ne da a ce an ba wa mutum tsawon rai ta yadda zai cike dukkan jakarsa ta sani, da sai ya kai matakin da zai rasa shirin da yake da shi na samun ilmi. Wannan kuma mustahili ne.

Amirul Muminina (a.s) ya ce: Dukkan jaka tana quntata saboda abin da ake zuba wa cikinta, ban da jakar ilmi. Ita tana qara yalwa da hakan([76]). Don haka faxin jakar ilmi daidai yake da faxin ilmin shi kansa, kenan jakar ba madda ba ce.

5- Akwai wani sanin da yake a sarari (badihi) wanda wata haqiqa ce tabbatacciya – da mutum yake ji (shu’uri) da shi tsawon rayuwarsa har ma bayan tayarwa (ranar Lahira). Ana kiran wannan abu ‘ni’. Da dai mutum shi ne wannan jiki na zahiri da sauyawa da canzawa sun kama shi, kuma da dukkan tunane-tunanensa da saninsa sun gushe, kuma da jin ‘ni’ da yake da shi ya zama qarya da kusukure. Saboda yankunan jiki suna canzawa. A ko wace rana miliyoyin qwayoyin halitta suke mutuwa, wasu sababbi suna maye gurbinsu. Masana ilmin kimiyya sun buga lissafi sun gano cewa matsakaicin saurin canzawar qwayoyin halitta a jikin mutum shi ne a duk shekara goma dukkanin qwayoyin halittan jiki suna canzawa sau guda. Idan kuma aka mutu to jikin zai lalace gaba xaya ne, kuma abin da ya canza ba shi ne tabbatacce dawwamamme ba. Saboda waxannan dalilai za mu ga cewa abin da ya qumshi dangantakan mutumtakan xan’Adam wanda kuma shi ne tushen wanzuwar tuntuni da saninsa, duk da faruwar sauye-sauye cikin ginin jiki, shi ne ruhi.

6- Qarfin jiki yana raunana idan ayyuka suka masa yawa. Alal misali idan mutum ya dubi rana lokaci mai tsawo ba zai iya ganin ranar cikakken gani ba. Amma nau’oin qarfi na rai ba su raunana saboda yawan aiki, kai yayin yawaita nazari ma qarfin rai yana qara himma ne. Saboda haka, abin da yake faruwa ga ruhi yayin yawaita aiki shi ne kishiyar abin da yake faruwa ga qarfin jiki a yayin yawaita aiki. Ka ga ke nan dole ne qarfi na rai ya zama ba na jiki ba.

7- Saruwar kishiyoyi a nau’in qarfin ruhi da kuma rashin samuwar haka a nau’oin qarfi na jiki. Alal misali idan muka xauka fari da baqi kishiyoyi ne, to dole ne haqiqanin fari da haqiqanin baqi su haxu a cikin hankali alhali kuma a sarari yake cewa abubuwa kishiyoyin juna ba su haxuwa a wajen jikuna (wato ba dama wani jiki ya zama fari kuma baqi a lokaci guda). Tun da sun haxu a cikin nau’oin qarfi na rai to dole ne waxannan nau’oin qarfi su zama ba na jiki ba ne.

8- Idan wasu surori (ko hotuna) da zane-zane suka auku kan madda to jikin ba zai iya xaukar waxansu hotunan ko kuma zane-zane ba har sai an kawar da na farkon tukuna, alhali hankaltar zuci ko kuma tunani yana iya xaukar hotanni xaya bayan xaya, waxanda mutum ya kan iya kawo su a zuciya a lokaci guda, gwargwadon yadda suke a waje. Kuma wannan tunani da kawo surar abubuwa ba ya buqatar mataki mataki ko gushewar lokaci, sannan kuma muhallin (zuciyar) ba ya cika saboda su. Saboda haka ba makawa wannan muhallin ba na madda ba ne kuma ba mai bigire ba ne.

 

Na Huxu: Hujjojin Ilmin Kimiyya Na Gwaji

Masana ilmin kimiyya na qasashen yamma sun kai ga natija a sarari a fagen tabbatar da duniyar ruhi, da kuma ingancin cewa ruhi mai dawwama ne kuma mujarradi ne, ba shi da siffofin madda. Wannan nasara tasu ba ta hanyar falsafa mai dogaro da tunani da kafa hujja suka same ta ba, a’a, sun same ta ne ta hanyar kimiyyar gwaji. An cimma wannan ne ta hanyar ilmin kiran ruhi da kuma ilmin sa mutum barci. Waxannan ilmomi biyu sun bude sabbin qofofin fahimtar duniyar ruhi waxanda suka canza masana da suke da aqidar maddiyya masu inkarin duniyar ruhi sai ga su sun yarda da duniyar gaibi kuma sun yi yaqini kan dawwamar rai.

Waxannan ilmomi biyu an sansu tun da daxewa. Misrawa da Ashurawa da mutanen Hindu da Romawa sun san waxannan ilmomi sai dai sun taqaita ne da wuraren ibada kuma ba mai amfani da su sai masu kula da al’amurran addini. A qarshen qarni na goma sha tara miladiyya, waxannan ilmomi biyu sun sami yaxuwa a Amurka da Turai da ma sassa da yawa na duniya. An wayi gari malaman jami’a da kuma gogaggun masu gudanar da bincike mai zurfi sun karvesu hannu bibbiyu, sun ba su wani sabon matsayi na ilmin kimiyya. Yanzu za mu ambaci irin ayyukan da aka gudanar a dukkan ilmomin biyu:

 

Na Farko: Kiran Ruhi:

 Wannan shi ne ilmin da ke da alaqa da matattu ta hanyar kiran rayukansu su taho daga duniyar da suke. Sai rai ya bayyana a gaban mai kiran shi, ya yi masa magana ya tabbatar masa a sarari cewa shi ran wane ne. Ran yana amsa akasarin tambayoyin da za a yi masa, amsa bisa hankali da hikima. Wannan har ya kai matsayin da wasu masanan sun iya warware mas’aloli masu wahala tare da taimakon waxannan rayuka. Haka nan rai zai amsa in aka tambaye shi halin da yake ciki da makomarsa bayan mutuwa, ko yana cikin ni’ima ko azaba.

Wannan al’amari ya ba da mamaki ga masana xabi’a da likitoci da masa falsafa da ma sauransu. Sun ci gaba da bincike-binciken kimiyya a kai a kai, lamarin da ya ganar da su batutuwan da suka danganci duniyar ruhi masu jan hankali. Sun gane cewa ruhi yana wanzuwa, yana kuma halartowa bayan mutuwa. Duk wannan ta hanyar qididdigan ilmi wanda ya dogara kan bincike da gwaje-gwaje masu yawa. Hakan ya sanya masanan yarda da samuwar wannan ilmin bayan dalilai da hujjoji masu qarfi sun tabbata a gare su. Farid Wajdi ya ambata a cikin Da’irat al-Ma’arif jerin shahararru daga waxancan masanan([77]).

Waxannan bincike-bincike an gudanar da su ne qarqashin kulawa ta musamman. An kafa qungiya a Birtaniyya da Amurka qarqashin kulawar Dakta Hudson a Birtaniyya da Farfesa Heizlub a Amurka domin hakan, inda qungiyar ta ci gaba da bin diddigin lamarin tsawon shekara goma sha biyu. A shekarar 1899 sai ga shi ta bayar da sanarwar cewa ta gamsu da ingancin waxannan bincike-bincke, kuma sakamakonsu da aka gani, aikin ruhin mutanen da suka riga suka mutu ne.

Masana da yawa ‘yan mazhabar maddiyya daga qasashe daban-daban na duniya sun duqufa kan wannan aiki, kuma daga gwaje-gwajen da suka gudanar sun fitar da sakamakon cewa xan’Adam yana da wani qarfi na ruhi wanda ya kuvuta daga siffofin madda kuma ba ya qarewa saboda mutuwar jiki. Wannan qarfi yana iya motsi cikin nishaxi ba tare da buqatar wannan jiki na qasa ba. Saboda haka waxannan masana sai suka yi imani da dawwamar ruhi bayan da suna qaryata hakan. Daga cikinsu akwai: Alfred Russell Dallas, Farfesa Kurkes, shugaban Jam’iyyar Ilmin Kimiyya a Birtaniyya da Sir Oliver Ludge, masanin ilmin xabi’a kuma shugaban Jami’ar Birmingham da Farfesa Hudson da Dakta George Skiston na Birtaniyya da Dakta Shambir da Dakta James Jalli da Farfesa Heizlub na Amurka da shahararren masanin ilmin taurarin nan Kamiel Fulamriyon da masanin falsafan nan na Birtaniyya Sir John Kusk da Farfesan ilmin albarkatun cikin qasa Barkes da dai sauransu. Wannan qoqari bai yanke ba har yanzu ana ta gano bayanai da suka shafi duniyar ruhi.

 

Na Biyu: Sa Barci:

Wannan wata fasaha ce wacce da ita qwararrun masana suke iya sa mutum barci, sai barci mai zurfi ya xauki mutum ta yadda gavovin jikinsa ba sa motsi ba sa jin komai. Mutum ba zai ji komai ba sai sautin wanda ya sa shi barcin. Yana sallama masa yana bin nufinsa da kuma tunaninsa. Kana wanda aka sa barcin yana bin umarnin mai sa barci ba tare da wani taraddudi ba. Ta hanyar sarrafa shi da ake yi, abubuwan da suka savawa xabi’a sukan bayyana gare shi, wanda hakan yana tabbatar da cewa yana da ruhi wanda ya sha bamban da jikinsa. Ruhinsa yana iya tafiya wasu wurare masu nisa daga inda yake, kuma ya bayyana wasu sirrorin da bai sansu ba sanda yake farke. Wani lokacin ma ya kan yi magana da wasu yarukan da bai iya su ba, yana kuma ba da labarin abubuwan da ba shi da wata masaniya kansu.

Wasu gungun masana falsafa sun gudanar da bincike kan  haqiqanin barci suna masu amfani da sabon hasken da aka samu a fagen ilmin kimiyyar yanayin rai. Sakamakon wannan bincike sun hakaito al’amuran ruhi masu ban al’ajabi. Daga cikin waxannan masana falsafa akwai malami xan qasar Birtaniyya Meyesr, malami a Jami’ar Cambridge kuma marubucin littafin Mutumtakan xan’Adam. A cikin wannan littafi ya ambaci gwaje-gwaje da aka yi a ilmin sa barci, kuma ya xauke shi a matsayin mas’aloli ne na gwaji waxanda ba dama a danganta su da yanayi ko ayyukan gavovi. Waxancan gwaje-gwaje suna ma tabbatar da cewa shi mutum, baicin jiki na madda da yake da shi, yana da wani sirri wato ruhi, wanda samuwarsa ta samo asali ne daga duniyar ruhi da duniyar qasa. Wannan kuma shi ne haqiqanin mutum, haqiqanin mai xaukaka, kamar yadda wannan masanin yace.

Wannan ilmi ya ci zango mai nisa a fagen binciken duniyar ruhi mai faxin gaske. Wasu zavavvun masana waxanda suka qware kan batun sa barci sun samar da babban sakamako a kimiyance, wanda ya dogara kan tacewa da tantancewa. Mashahuran wannan fanni na sa barci sun haxa da masanin nan na Birtaniyya James Pride da Nowelz da Sharko da Philips Carth da sauransu([78]).

Daga hujjojin da muka jero ya bayyana cewa mutumtakar mutum wacce ake ce da ita ‘ni’ ba jiki ba ne ba kuma yanki ne daga wannan jikin ba, saboda wannan mutumtaka tana siffantuwa da sani da riska, kuma ba ta canzawa tare da canzawar jiki ko gavovinsa. Har ila yau ba ta bin qa’idojin lokaci da bigire irin yadda jiki yake yi, kuma tana kevanta da wasu siffofi da jiki da madda ba su da su, kamar yadda muka gabatar.

Idan muka koma kan batun alaqar da jiki da gavovinsa suke da ita da ruhi za mu ga cewa alaqa ce irin ta kayar aiki (ala) da mai aikin. Aikace-aikacen ruhi suna bayyana ne ta hanyar jiki da gavovi tare da cewa ruhi da jiki suna yi wa juna tasiri. Alal misali, tsoro da farin ciki suna da tasiri kan gavovin jiki, fatar jiki tana xamewa ko kuma launin fata ya canza saboda tsoro. Haka nan raunin kayan aiki (gavovi) ko tawayarsu yana yin tasiri kan harakar tunani da hankaltawa. Wannan alaqa da ke tsakanin ruhi da kayan aikinsa na jinsin madda zai ci gaba a ranar tashin qiyama yayin da za a dawo da ruhi ga jiki. Sai gavovi su zama shaidu kan aikin ruhi, kamar yadda ayoyin Alqur’ani mai girma suka nuna a sarari. Daga cikinsu akwai faxin Allah Maxaukakin Sarki cewa:

﴿ íóæúãó ÊóÔúåóÏõ Úóáóíúåöãú ÃóáúÓöäóÊõåõãú æóÃóíúÏöíåöãú æóÃóÑúÌõáõåõã ÈöãóÇ ßóÇäõæÇ íóÚúãóáõæäó

“Ranar da harsunansu da hannayensu da kuma qafufuwansu suke shaida a kansu da abin da suka kasance suna aikatawa([79])”.

Duk da haka, ba za a iya sanin tabbas yadda wannan alaqar ba ni in baka tsakanin ruhi da jiki take ba. Shin a cuxe suke da juna, ko su biyun abu guda ne, ko kuwa ko wani guda yana cin gashin kansa a mas’alar (da ya kevance shi)?. Wannan daga al’amarin Ubangiji na ne, kuma Shi Ya san haqiqanin lamarin.

 

BAHASI NA BIYU: HAQIQANIN TASHIN QIYAMA

Musulmi sun yi ittifaqi kan cewa tashin qiyama gaskiya ne da kuma za a tayar da mutane, kamar yadda malaman falsafa ma suka yi daidai da su a wannan ra'ayi. Bambancin da kawai suke da shi shi ne kan yadda hakan zai faru (wato yanayin tashin), don haka suka tafi kan maganganu guda biyu:

 

Na Farko – Tayarwa Ta Jiki

Abin nufi shi ne cewa Allah Maxaukakin Sarki zai ta da mutane ranar qiyama da jikin da suke da shi tun kafin mutuwarsu. Tashin qiyama da wannan ma'ana xaya daga cikin shika-shikan addini ne wanda dole ne a yi imani da shi, duk wanda ya yi inkarin hakan ya kafirta bisa ijma'in malamai. Dalilin tabbatansa kuwa shi ne cewa tashin qiyama da wannan ma'ana lamari ne mai yiyuwa sannan kuma samuwarsa ya fito daga tushe.

A fasalin da ya gabata mun tabbatar da yiyuwar hakan. Nassosi sun yi magana kan tabbaci da wajibcin hakan cikin addinan Annabawan da suka gabata, kamar yadda yake tabbace cikin addinin Manzonmu (s.a.w.a). Haqiqa Alqur'ani mai girma ya tabbatar da hakan cikin ayoyi masu yawa ya kuma bayyana cewa tashin qiyamar zai faru ne lokacin da mutane za su fito daga kaburburansu don fuskantar hisabi. Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

﴿ íóæúãó ÊõÈóÏøõáõ ÇáÇúóóÑúÖõ ÛóíúÑó ÇáÇúóóÑúÖö æóÇáÓøóãÇæóÇÊõ æóÈóÑóÒõæÇ ááåöö ÇáúæóÇÍöÏö ÇáúÞóåøóÇÑö! áöíóÌúÒöíó Çááåõ ßõáøó äóÝúÓò ãøóÇ ßóÓóÈóÊú[80]

"A ranar da ake musanya qasa, ba qasar nan ba, da sammai kuma su bayyana ga Allah Makaxaici, Mai tanqwasawa", har zuwa inda yake cewa: "Domin Allah Ya saka wa kowane rai da abin da ya aikata..",  na alheri ko sharri, kamar yadda kuma hadisai mutawattirai na Ma'aiki da na Ahlulbaiti (a.s) suka tabbatar da tayar da jiki. Daga cikin ayoyin akwai:

1-     FaxinSa Maxaukakin Sarki cewa:

﴿ÃóíóÍúÓóÈõ ÇáÅööäÓóÇäõ Ãóáøóä äóÌúãóÚó ÚöÙóÇãóåõ ! Èóáóì ÞóÇÏöÑöíäó Úóáóì Ãóä äøõÓóæøöíó ÈóäóÇäóåõ[81]

"Shin, mutum yana zaton cewa ba za Mu tara qasusuwansa ba? Na'am! Masu ikon yi Muke a kan Mu daidaita gavovin yatsunsa".

2- FaxinSa Maxaukaki cewa:

﴿æóÖóÑóÈó áóäóÇ ãóËóáðÇ æóäóÓöíó ÎóáúÞóåõ ÞóÇáó ãóäú íõÍúíöí ÇáúÚöÙóÇãó æóåöíó Ñóãöíãñ ! Þõáú íõÍúíöíåóÇ ÇáøóÐöí ÃóäÔóÃóåóÇ Ãóæøóáó ãóÑøóÉò æóåõæó Èößõáøö ÎóáúÞò Úóáöíãñ[82]

"Kuma ya buga Mana wani misali, kuma ya manta da halittarsa, ya ce "Wane ne zai rayar da qasusuwa alhali kuwa suna rududdugaggu? Ka ce, "Wanda ya qaga halittarsu a farkon lokaci, Shi ke rayar da su, kuma Shi, game da kowace halitta, Mai ilmi ne.

3- Akwai kuma wasu ayoyin da suke magana kan fitar da matattu daga qaburbura, kamar faxinSa cewa:

﴿æóäõÝöÎó Ýöí ÇáÕøõæÑö ÝóÅöÐóÇ åõã ãøöäó ÇáÇóÌúÏóÇËö Åöáóì ÑóÈøöåöãú íóäÓöáõæäó !ÞóÇáõæÇ íóÇ æóíúáóäóÇ ãóä ÈóÚóËóäóÇ ãöä ãøóÑúÞóÏöäóÇ åóÐóÇ ãóÇ æóÚóÏó ÇáÑøóÍúãóäõ æóÕóÏóÞó ÇáúãõÑúÓóáõæäó ! Åöä ßóÇäóÊú ÅöáÇøó ÕóíúÍóÉð æóÇÍöÏóÉð ÝóÅöÐóÇ åõãú ÌóãöíÚñ áøóÏóíúäóÇ ãõÍúÖóÑõæäó !ÝóÇáúíóæúãó áÇ ÊõÙúáóãõ äóÝúÓñ ÔóíúÆðÇ æóáÇ ÊõÌúÒóæúäó ÅöáÇøó ãóÇ ßõäÊõãú ÊóÚúãóáõæäó[83]

"Kuma aka yi busa a cikin qaho, to, sai ga su, daga kaburbura zuwa ga Ubangijinsu, suna ta gudu. Suka ce, "Ya bonenmu! Wane ne ya tayar da mu daga barcinmu?" "Wannan shi ne abin da Mai rahama ya yi wa'adi da shi, kuma Manzanni sun yi gaskiya". Ba ta kasance ba face wata tsawa ce guda, sai ga su duka, suna abin halartarwa a gare Mu. To, a yau, ba za a zalunci wani rai da kome ba. Kuma ba za a saka muku ba face da abin da kuka kasance kuna aikatawa". Da kuma faxinSa Ta'ala cewa:

﴿ãöäúåóÇ ÎóáóÞúäóÇßõãú æóÝöíåóÇ äõÚöíÏõßõãú æóãöäúåóÇ äõÎúÑöÌõßõãú ÊóÇÑóÉð ÃõÎúÑóì[84]

"Daga gare ta Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta Muke fitar da ku a wani lokaci na daban".

4- Ayoyin da suke magana kan cewa za a zo da mutum wajen hisabi da dukkan gavavunsa don su kasance shaidu kan ayyukan da ya aikata, kamar faxinSa:

﴿Çáúíóæúãó äóÎúÊöãõ Úóáóì ÃóÝúæóÇåöåöãú æóÊõßóáøöãõäóÇ ÃóíúÏöíåöãú æóÊóÔúåóÏõ ÃóÑúÌõáõåõãú ÈöãóÇ ßóÇäõæÇ íóßúÓöÈõæäó[85]

"A yau, Muna sanya hatimin rufi a kan bakunansu, kuma hannayensu su yi Mana magana, kuma qafafunsu su yi shaida kan abin da suka kasance suna aikatawa". Da kuma faxin Allah Maxaukakin Sarki cewa:

﴿ÍóÊøóì ÅöÐóÇ ãóÇ ÌóÇÄõæåóÇ ÔóåöÏó Úóáóíúåöãú ÓóãúÚõåõãú æóÃóÈúÕóÇÑõåõãú æóÌõáõæÏõåõãú ÈöãóÇ ßóÇäõæÇ íóÚúãóáõæäó[86]

“Har idan sun je mata, sai jinsu da ganinsu da fatunsu, su yi shaida a kansu a game da abin da suka kasance suna aikatawa”.

5- Ayoyin da suka kawo fitattun misali kan tashin qiyama na jiki([87]), kamar qissar rayar da Uzair da BaIsra'ilen da aka kashe, da Ashab al-Kafi (mutanen kogo), da kuma rayar da tsuntsaye ga Annabi Ibrahim (a.s). A baya mun kawo su yayin da muke kafa hujja kan tashin qiyama.

6- Ayoyin da suke magana kan abubuwan jin daxin da ke cikin aljanna da ba a jinsu sai ta hanyar jiki, da kuma irin azabobin da suke cikin wuta da suke samun wasu sassa na jiki da ake azabtarwa. Allah Ta'ala Ya siffanta 'yan Aljanna, da cewa:

﴿ Úóáóì ÓõÑõÑò ãøóæúÖõæäóÉò ! ãõÊøóßöÆöíäó ÚóáóíúåóÇ ãõÊóÞóÇÈöáöíäó ! íóØõæÝõ Úóáóíúåöãú æöáúÏóÇäñ ãøõÎóáøóÏõæäó ! ÈöÃóßúæóÇÈò æóÃóÈóÇÑöíÞó æóßóÃúÓò ãøöä ãøóÚöíäò ! áÇó íõÕóÏøóÚõæäó ÚóäúåóÇ æóáÇó íõäÒöÝõæäó ! æóÝóÇßöåóÉò ãøöãøóÇ íóÊóÎóíøóÑõæäó ! æóáóÍúãö ØóíúÑò ãøöãøóÇ íóÔúÊóåõæäó ! æóÍõæÑñ Úöíäñ ! ßóÃóãúËóÇáö ÇááøõÄúáõÄö Çáúãóßúäõæäö[88]

"(Suna) a kan wasu gadaje saqaqqu. Suna gincire a kansu, suna masu kallon juna. Wasu yara samari na dindindin gewaye a kansu. Da wasu kofuna da shantula da hinjalai daga (giya) mai vuvvuga. Ba a sanya musu ciwon jiri saboda ita, kuma ba su buguwa. Da wasu 'ya'yan itacen marmari daga irin waxanda suke zave. Da naman tsuntsaye daga wanda suke ganin sha'awa. Da wasu mata masu fararen idanu da girmansu. Kamar misalin lu'u-lu'u wanda aka voye", sannan yayin da kuma Yake siffanta 'yan wuta, Allah Maxaukaki Na cewa:

﴿Åöäøó ÇáøóÐöíäó ßóÝóÑõæÇú ÈöÂíóÇÊöäóÇ ÓóæúÝó äõÕúáöíåöãú äóÇÑðÇ ßõáøóãóÇ äóÖöÌóÊú ÌõáõæÏõåõãú ÈóÏøóáúäóÇåõãú ÌõáõæÏðÇ ÛóíúÑóåóÇ áöíóÐõæÞõæÇú ÇáúÚóÐóÇÈó[89]

"Lalle ne waxanda suka kafirta da ayoyinMu za Mu qone su da wuta, ko da yaushe fatunsu suka nuna, sai Mu musanya musu wasu fatun, domin su xanxani azaba".

Dangane da hadisai kuwa suna da yawa, daga ciki akwai faxin Amirul Muminina (a.s) cewa: "Har lokacin da al’amurra suka kusato, duniya ta qare kana tashin qiyama ta kusato, Allah Zai fitar da su daga kusurwoyin kaburburansu, daga sheqan tsuntsaye, kogon dabbobin daji da kuma wuraren mutuwa. Suna masu gaggawa zuwa ga UmarninSa da kuma makomarsu ta qarshe qungiya-qungiya, suna tsaye tsit a sahu…([90])".

Da kuma abin da Aliyu bn Ibrahim da Shaikh Saduq suka ruwaito daga Imam Sadiq (a.s) cewa: "Idan Allah Yana nufin tayar da halitta, sama za ta yi ruwa na ranaku (safiya) arba'in, sai a taro gavuvva, sai kuma nama su tsiro([91])".

 

Haqiqanin Tayarwa Ta Jiki:

Dukkan musulmi daga malaman fiqihu, aqida, hadisi da Irfani sun ittifaqi kan tayarwa ta jiki. Dukkansu  sun haxu a kan dawo da mutum da jikinsa ranar lahira kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki Ya faxi cikin littafinSa, abin da kawai suka samu savani kansa shi ne haqiqanin (ma'anar) ruhi. Wasu daga cikinsu, suna cewa ruhi shi ne wani jiki mai gudana cikin wannan jiki, tamkar yadda wuta take gudana cikin garwashi ko kuma ruwa cikin fure. Don haka su a wajensu tayarwar jiki da ruhi duka abu ne da ya shafi na jiki. Duk da cewa hakan ba wai yana nufin dawo da jikin da ya mutu ba tare da ruhi ba ne, a’a jikuna za su dawo da rayukansu da hankalinsu. Kai ruhi a ganinsu yana cikin sahun jikkuna.

Su kuwa waxanda suka yi imani da tajarrudin ruhi, suna ganin tayarwar za ta kasance ne ta jiki da ruhi, wato dawowar ruhi zuwa jiki yayin tayarwa. Waxanda suka yi imani da wannan aqida su ne da dama daga manyan malaman hikima da na irfani da kuma na aqida kamar su Al-Ghazali, Al-Ka'abi, al-Hulimi, Ragib Isfahani da kuma da dama daga cikin mabiya Shi'a Imamiyya irinsu Shaikh al-Mufid, Abu Ja'afar Tusi, Sayyid Murtadha, Al-Muhaqqiq al-Tusi da Allamah al-Hilli (yardar Allah ta tabbata a gare su) sun tafi a kan cewa rai mujarradi yana komawa jiki ranar qiyama([92]).

Ruwayoyi masu yawa sun zo kan cewa ruhi wani jauhari ne na haske mai taushi wanda ya sha bamban da jiki. Da kuma cewa, bayan rushewar jiki zai wanzu yana mai murna da farin ciki, yana raye kuma ana arzurta shi, ko kuma akasin haka([93]). A baya mun ambaci da yawa daga waxannan ruwayoyi a bahasi na farko. A nan za mu ambaci wani hadisin da aka ruwaito daga Imam Sadiq (a.s). Wannan hadisi ya tattara haqiqanin makoma (tashin qiyama) gaba xaya: Wani zindiqi ya tambayi Imam Sadiq (a.s) yana mai inkarin tayarwa (a ranar lahira) ya ce: “Ya ya Ubangiji zai tayar alhali jiki ya rududduge? Gavovi sun yayyanke, wata gava tana wani gari, dabbobi sun cinyeta wata kuma tana wani garin qwari suna kekketata, wata gavar kuma ta zama qasa an ma gina katanga da ita?”.

Sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa: Shi ruhi yana zaune ne a wurinsa, ruhin mai kyautata aiki yana cikin haske da yalwa, ruhin mai munanawa kuma yana cikin matsi da duhu. Shi kuma jiki zai zama qasa kamar yanda aka halicce shi daga ita. Toroson dabbobi da qwari dake fita daga jikkunansu daga abin da suka ci, duk yana cikin qasa amma a kiyaye yake wajen Wanda babu abin da zai vuya gare Shi a cikin duffan qasa kuma Yana sane da adadin abubuwa da kuma nauyinsu…Idan lokacin tayarwa ya yi za a yi wa qasa ruwan tashi sai ta xaga sannan a fitar da su kamar yadda siqa (wani tsuntsu mai kama da shamuwa) yake zuba qwai. Sai qasar ‘yan Adam ta zama tamkar zinare idan an wanke shi da ruwa, ko kuma kamar yanda mai yake fita daga madara yayin da aka kaxa shi. Sai qasar ko wani jiki ta taru, sannan ta tafi ta sami ruhin, da yardar Allah Mai iko. Sai surorin su dawo kamar siffansu (ta da), da izinin Mai surantawa. Sannan sai ruhi su shige su, har idan mutum ya daidaita zai xauki siffarsa ba bambanci([94]).

 

Na Biyu: Tayarwa Ta Ruhi:

Akasarin malaman falsafa sun tafi kan tayarwa ta ruhi, saboda ba su yarda da dawowar jiki ba, inda suke cewa: jiki ya kan qare gaba xayansa saboda katsewar alaqa tsakaninsa da rai, don haka ba za a dawo da shi ba saboda ba a dawo da abin da ya gushe. Nafs dai jawhari ne da zai saura ba tare da gushewa ba([95]). Don haka suke ganin tayarwa da dukkan abin da suka dangance shi a matsayin sha'anin ruhi shi kaxai saboda ba ya gushewa.

Wannan zance ya sava wa zahirin ayoyin Alqur'ani mai girma da sahihiyar Sunnar Ma'aiki (s.a.w.a) masu nuni da dawowar mutum da jikinsa ranar qiyama. Masu cewar tayarwa ta ruhi ce daga malaman falsafa musulmi suna ganin cewa lada da azaba a matsayin jin daxi ko raxaxin da rai zai gamu da shi, irin jin daxi ko raxaxin da hankali da ruhi suke iya gamuwa da su bayan sun rabu da jiki. Sai suka yi qoqarin tawilin dalilai na shari'a don su yi daidai da ra'ayinsu, suna masu tawilin ayoyin Alqur'ani masu yawa da suke magana kan jin daxi ko azaba da ake jinsu a jiki a Aljanna ko kuma a wuta. Suna ganinsu a matsayin aron abin da ake ji a zahiri ne saboda a misalta jin jin xaxi ko azaba na ruhi da hankali don kusanto da lamarin zuwa ga fahimtar sauran mutane da suka fi ba da muhimmanci ga abin da ake ji a jiki sama da na hankali.

An fi sanin Sheikh al-Ra'is Ibn Sina da inkarin tayarwa ta jiki, yana mai qarfafa tayarwa ta ruhi([96]), ta yadda hatta Al-Ghazali ya kafirta Ibn Sina da wasu masana falsafa sakamakon inkarin da suka yi wa tayarwa ta jiki([97]).

To sai dai gaskiyar lamarin ita cewa babu inda Ibn Sina ya fito ya yi inkarin tayarwa ta jiki a cikin sanannun litattafansa; kai muna iya gani cikin mafi girman littafinsa wato 'Al-Shifa' yana bayyana imaninsa da tayarwa ta jiki, da kuma nuna cewa hakan lamari ne da babu makawa cikinsa.

Al-Muhaqqiq al-Dawwani ya faxa cikin sharhinsa ga littafin Al-Aqa'id al-Adhudiyya cewa: Duk da inkarin da Abu Ali yake yi ga batun tayarwa ta jiki kamar yadda yazo cikin littafin Al-Ma'ad da kafa wasu hujjoji da yake gani suna inkarin wannan batu, sai dai duk da haka ya faxi cikin littafin 'Al-Najat wa al-Shifa' cewa: Ya wajaba a san cewa, akwai wasu abubuwa kan batun tashin qiyama da aka naqalto su daga shari'a (Musulunci) da babu yadda za a iya tabbatar da su sai ta hanyar shari'a da gaskata hadisai. Su ne abin da jiki yake samu, yayin tayarwa. Alherai da sharrorin da suka danganci jiki kuwa sanannu ne da babu buqatar saninsu. Shari'ar gaskiya da Manzonmu Muhammad (s.a.w.a) yazo mana da ita ta yi bayani filla-filla kan halin arziqin lahira da kuma tavewa (shiga wuta) irin wanda jiki ke iya xanxanawa. Akwai kuma batun tayarwa wanda ake iya gano shi da hankali, ta hanyar hujjar qiyasi wanda annabci ya gaskata, haka shi ne kuwa sa'ada da shaqawa tabbatattu ta hanyar qiyasi…….([98]).

Uztaz Fathullah Khalifa, yayin da yake bayani kan ra'ayin Ibn Sina kan rai (nafs), ya ce shi Ibn Sina yayi imani da tayarwa ta jiki babu wani shakka ko kokwanto cikinsa([99])".

Wasu suna da'awar cewa al-Ghazali ma yana inkarin tayarwa ta jiki, duk da cewa lamarin ba haka ba ne. Wanda yayi sharhi wa Al-Maqasid yana cewa: Irin yawan maganganun da Al-Ghazali ya yi kan tayarwa ta ruhi da kuma bayani kan nau'oi na lada (a lahira) da uquba da ke samun ruhi ya sanya da dama suke cewa yana inkarin tayarwa ta jiki, amma ya ya hakan zai kasance bayan ya ambaci wannan batu a wurare daban-daban cikin littafin Al-Ihya' da sauransu, har ma ya tafi kan cewa inkarin hakan kafirci ne. Bai yi qarin bayani sosai kan hakan cikin sharhin nasa ba ne saboda faxinsa cewar: Wannan lamari ne da ke a fili ba shi buqatan wani qarin bayani([100]).

 

Inkarin Tayarwa Ta Jiki:

Haqiqa Annabawa da Manzanni (a.s) sun fuskanci matsaloli na inkarin tashin qiyama da al'ummarsu suke yi, inda suka fuskanci wahalhalu masu yawa da zarge-zarge:

﴿æóÞóÇáó ÇáøóÐöíäó ßóÝóÑõæÇ åóáú äóÏõáøõßõãú Úóáóì ÑóÌõáò íõäóÈøöÆõßõãú ÅöÐóÇ ãõÒøöÞúÊõãú ßõáøó ãõãóÒøóÞò Åöäøóßõãú áóÝöí ÎóáúÞò ÌóÏöíÏò ! ÃóÝúÊóÑóì Úóáóì Çááåö ßóÐöÈÇð Ãóã Èöåö ÌöäøóÉñ [101]

“Kuma waxanda suka kafirta suka ce, ‘Shin, za mu nuna muku wani namiji wanda yake gaya muku wai idan an tsattsage ku, kowace irin tsattsagewa, lalle ku, tabbas, kuna a cikin wata halitta sabuwa? Ya qaga qarya ga Allah ne ko kuwa akwai wata hauka a gare shi?”.  Duk da cewa tashin qiyama na daga cikin ababen da hujjoji na nassi da hankali suka tabbatar da shi har Allah Maxaukaki a wajaje daban-daban na LittafinSa mai tsarki Ya siffanta shi da cewa:﴿áÇ ÑíÈ Ýíå  “Ba kokwanto gare shi”. Me tayar da tsuntsaye ga Annabi Ibrahim (a.s), rayar da BaIsra'ilen da aka kashe, Uzair, Ashabul Kahfi da sauransu yake nufi face misalai na tayar da matattu da Allah Maxakaki Ya yi a lokuta daban-daban don tabbatar da aqidar qiyama cikin zukatan mutane, wanda hakan na nuni da irin matsayin da wannan aqida take da shi da kuma yawan masu inkarinta.

Inkarin tashin qiyama da waxannan mutane ke yi lamari ne da bai dogara kan hujja ta sarari ko nassi ba, ya ginu ne kan zato da ba shi da wata qima, Allah Maxaukakin Sarki na cewa:

﴿ æóÞóÇáõæÇ ãóÇ åöíó ÅöáÇøó ÍóíóÇÊõäóÇ ÇáÏøõäúíóÇ äóãõæÊõ æóäóÍúíóÇ æóãóÇ íõåúáößõäóÇ ÅáÇøó ÇáÏøóåúÑõ æóãóÇ áóåõã ÈöÐáößó ãöäú Úöáúãò Åöäú åõãú ÅöáÇøó íóÙõäøõæäó

“Kuma suka ce, ‘Babu kome face rayuwarmu ta duniya; muna mutuwa kuma muna rayuwa (da haihuwa) kuma babu abin da ke halaka mu sai zamani’. Alhali kuwa (ko da suke faxar maganar) ba su da wani ilmi game da wannan, ba su bin kome face zato([102]).

  Haka nan yana dogara ne kan asasin korewa da ba shi da wata matsaya a tattaunawa ta ilmi, face dai gazawa ce wajen fahimtar hujja ta isa ga haqiqa.

Ummul aba'isin xin inkarin tashin qiyama gazawan xan'Adam da kutsawarsa cikin son duniya da bautan sha'auce-sha'aucen zuziyarsa, da ke fitar da shi daga da'irar taqawa da imani wacce aqidar tashin qiyama ta sanya shi ciki, da karkatarsa ga varna, fasadi da ja'irci 

 ﴿ íóÓúÃóáõ ÃóíøóÇäó íóæúãõ ÇáúÞöíóÇãóÉö  ! Èóáú íõÑöíÏõ ÇáÇúööäÓóÇäõ áöíóÝúÌõÑó ÃóãóÇãóåõ

“Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fajirci, ya qaryata abin da yake a gabansa. Yana tambaya, ‘Yaushe ne Ranar Qiyama([103]).

Don haka ne za mu ga ma'abuta girman kai da suka cika duniya da zalunci da fasadi, da kuma masu hannu da shuni waxanda suke bauta wa sha'auce-sha'aucen zukatansu sun tsananta wajen inkarin tashin qiyama ne saboda girman kai da neman xaukaka kansu. Daga cikinsu akwai al'ummar Annabi Hudu (a.s). Allah Maxaukakin Sarki na cewa:

﴿ ÞóÇáó ÇáúãóáÃóõ ãöä Þóæúãöåö ÇáøóÐöíäó ßóÝóÑõæÇ æóßóÐøóÈõæÇ ÈöáöÞóÇÁö ÇáÇúóÎöÑóÉö æóÃóÊúÑóÝúäóÇåõãú Ýöí ÇáúÍóíóÇÉö ÇáÏøõäúíóÇ ãóÇ åóÐÇ ÅöáÇøó ÈóÔóÑñ ãøöËúáõßõãú íóÃúßõáõ ãöãøóÇ ÊóÃúßõáõæäó ãöäúåõ æóíóÔúÑóÈõ ãöãøóÇ ÊóÔúÑóÈõæäó  ! æóáóÆöäú ÃóØóÚúÊõã ÈóÔóÑÇð ãöËúáóßõãú Åöäøóßõãú ÅöÐÇð áóÎóÇÓöÑõæäó    !ÃóíóÚöÏõßõãú Ãóäøóßõãú ÅöÐóÇ ãöÊøõãú æóßõäÊõãú ÊõÑóÇÈÇð æóÚöÙóÇãÇð Ãóäøóßõã ãõÎúÑóÌõæäó   ! åóíúåóÇÊó åóíúåóÇÊó áöãóÇ ÊõæÚóÏõæäó    ! Åöäú åöíó ÅöáÇøó ÍóíóÇÊõäóÇ ÇáÏøõäúíóÇ äóãõæÊõ æóäóÍúíóÇ æóãóÇ äóÍúäõ ÈöãóÈúÚõæËöíäó  ! Åöäú åõæó ÅöáÇøó ÑóÌõáñ ÇÝúÊóÑóì Úóáóì Çááåö ßóÐöÈÇð æóãóÇ äóÍúäõ áóåõ ÈöãõÄúãöäöíäó

“Mashawarta daga mutanensa, waxanda suka kafirta kuma suka qaryata game da haxuwa da Lahira, kuma Muka ni’imtar da su a cikin rayuwar duniya, suka ce, ‘Wannan ba kowa ba, face wani mutum ne kamarku, yana ci daga abin da kuke ci daga gare shi, kuma yana sha daga abin da kuke sha. Kuma lalle ne idan kun yi xa’a ga mutum misalinku, lalle ne, a lokacin nan, haqiqa, ku masu hasara ne. Shin yana yi muku wa’adin (cewa) lalle ku, idan kun mutu kuma kuka kasance turvaya da qasusuwa, lalle ne ku, waxanda ake fitarwa ne? Faufau faufau ga abin da ake yi muku wa’adi dashi. Rayuwa ba ta zama ba face rayuwarmu ta duniya, muna mutuwa kuma muna rayuwa, kuma ba mu zama waxanda ake tayarwa ba. Bai zama kowa ba face namiji, ya qirqira qarya ga Allah, kuma ba mu zama, saboda shi, masu imani ba([104])

. Sannan Allah Ya jaddada girman kansu ga barin miqa wuya ga gaskiya da hasken hujja cikin faxin Allah:

﴿ ÝóÇáøóÐöíäó áÇíõÄúãöäõæäó ÈöÇáÇúóÎöÑóÉö ÞõáõæÈõåõã ãõäßöÑóÉñ æóåõã ãõÓúÊóßúÈöÑõæäó  

“To, waxanda ba su yin imani da Lahira, zukatansu masu musu ne, kuma su makangara ne([105]).

Su ma masu inkarin tashin qiyama a lokacin Manzo ba su dogara da komai ba in ban da zato da korewa, ba tare da wani dalili ko hujja ba:

﴿ Èáú ÞóÇáõæÇ ãöËúáó ãóÇ ÞóÇáó ÇáÇúóóæøóáõæäó  ! ÞóÇáõæÇ ÃóÁöÐóÇ ãöÊúäóÇ æóßõäøóÇ ÊõÑóÇÈÇð æóÚöÙóÇãÇð ÃóÁöäøóÇ áóãóÈúÚõæËõæäó   !áóÞóÏú æõÚöÏúäóÇ äóÍúäõ æóÂÈóÇÄõäóÇ åÐóÇ ãöä ÞóÈúáõ Åöäú åÐÇ ÅöáÇøó ÃóÓóÇØöíÑõ ÇáÇúóóæøóáöíäó

“A’a, sun faxi misalin abin da na farko suka faxa. Suka ce, ‘Shin, idan mun mutu kuma muka kasance turvaya da qasusuwa, shin, lalle ne mu, haqiqa waxanda ake tayarwa ne. Lalle ne, haqiqa, an yi mana wa’adi, mu da ubanninmu ga wannan a gabani. Wannan abu bai zama kome ba, face tatsuniyoyin na farko([106]).

Don haka, ayoyin Alqur'ani suka mayar musu da martini da kuma amsa musu tambayoyin da suka gabatar ta fuskoki uku:

Ta Farko: Kafa hujjojin da suka dace da hankali da zuciyar xan'Adam dake tabbatar da wajibcin tashin qiyama da cika alqawarin Ubangiji. Daga cikin irin waxannan hujjoji har da hujjar tamka da ta iko da ta hikima da ta adalci da muka gabatar a baya.

Ta Biyu: Bayyana haqiqanin xan'Adam, saboda inkarin da mushirikan jahiliyya suke yi wa tayarwa ta jiki, kamar yadda Alqur'ani mai girma ya kawo irin bayanin inkarin nasu:

﴿ íóÞõæáõæäó ÃóÁöäøóÇ áóãóÑúÏõæÏæõäó Ýöí ÇáúÍóÇÝöÑóÉö ! æÃóÁöÐóÇ ßõäøóÇ ÚöÙóÇãÇð äóÎöÑóÉð   !ÞóÇáõæÇ Êöáúßó ÅöÐÇð ßóÑøóÉñ ÎóÇÓöÑóÉñ

“Suna cewa, ‘Ashe, lalle za a iya mayar da mu a kan sawunmu? Ashe, idan muka zama qasusuwa rududdu-gaggu? Suka ce, ‘Waccan kam komawa ce, tavavviya([107]),

﴿ óÞóÇáõæÇ ÃóÁöÐóÇ ßõäøóÇ ÚöÙóÇãÇð æóÑõÝóÇÊÇð ÃóÁöäøóÇ áóãóÈúÚõæËõæäó ÎóáúÞÇð ÌóÏöíÏÇð      

“Shin idan muka kasance qasusuwa da niqaqqun gavuvuwa, shin lalle mu, haqiqa, waxanda ake tayarwa ne a cikin wata halitta sabuwa([108])?”

﴿ æóÞóÇáõæÇ ÃóÁöÐóÇ ÖóáóáúäóÇ Ýí ÇáÇúóóÑúÖö ÃóÁöäøóÇ áóÝöí ÎóáúÞò ÌóÏöíÏò

Kuma suka ce, ‘Shin, idan mun vace a cikin qasa, shin, lalle mu, tabbas ne, muna zama a cikin wata halitta sabuwa([109])?”,

 Allah Ya amsa musu ta hanyar bayyana haqiqanin xan'Adam wanda shi ne ruhin da Mala'ikan mutuwa zai xauka

﴿ Þõáú íóÊóæóÝøóÇßõã ãóáóßõ ÇáúãóæúÊö ÇáøóÐöí æõßøöáó Èößõãú Ëõãøó Åöáóì ÑóÈøößõãú ÊõÑúÌóÚõæäó  

“Ka ce, ‘Mala’ikin mutuwa wanda aka wakkala a gare ku, shi ne ke karvar rayukanku. Sannan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku([110]),

wato ba za ku vace cikin qasa ko ku lalace sakamakon mutuwa ba, saboda Mala'ikan mutuwan ya kan xauki ruhinku ne, da zai ci gaba da zama a wajensa ba tare da ya vace ba. Idan kuma aka tayar da ku za ku koma wajen Allah inda za a sadar da jikinku da rayukanku sai su kasance ku ku xin ne([111]).

Ta Uku: Mayar da martini ga inkarin ranar lahira da kuma barazana ga masu inkari da azaba mai tsanani, Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

﴿ æóÅöä ÊóÚúÌóÈú ÝóÚóÌóÈñ Þóæúáõåõãú ÃóÁöÐóÇ ßõäøóÇ ÊõÑóÇÈÇð ÃóÁöäøóÇ áóÝöí ÎóáúÞò ÌóÏöíÏò ÃõæáÆößó ÇáøóÐöíäó ßóÝóÑõæÇ ÈöÑóÈøöåöãú æóÃõæáÆößó ÇáÇúóóÛúáÇáõ Ýöí ÃóÚúäóÇÞöåöãú æóÃõæáÆößó ÃóÕúÍóÇÈõ ÇáäøóÇÑö åõãú ÝöíåóÇ ÎóÇáöÏõæäó

“Kuma idan ka yi mamaki, to, mamakin kam shi ne maganarsu, ‘Shin, idan muka kasance turvaya, za mu zama a cikin wata halitta sabuwa? Waxancan ne, waxanda suka kafirta da Ubangijinsu, kuma waxanda akwai ququmai a cikin wuyoyinsu, kuma waxancan ne abokan wuta. Su a cikinta, masu dawwama ne([112]).

  Haka nan Yana cewa:

 ﴿ æóÃóäøó ÇáøóÐöíäó áà íõÄúãöäõæäó ÈöÇáÇúóÎöÑóÉö ÃóÚúÊóÏúäóÇ áóåõãú ÚóÐóÇÈÇð ÃóáöíãÇð      

“Kuma lalle ne waxanda ba su yin imani da Lahira, Mun yi musu tattalin wata azaba mai raxaxi([113]),

 kuma Maxaukakin Sarki Yana cewa:

﴿ æóíúáñ íóæúãóÆöÐò áöáúãõßóÐøöÈöíäó ! ÇáøóÐöíäó íõßóÐøöÈõæäó Èöíóæúãö ÇáÏøöíäö  !æóãóÇ íõßóÐøöÈõ Èöåö ÅöáÇøó ßõáøõ ãõÚúÊóÏò ÃóËöíãò

“Bone ya tabbata a ranar nan ga masu qaryatawa. Waxanda suke qaryatawa game da ranar sakamako. Babu mai qaryatawa gare shi face dukkan mai qetare haddi, mai yawan zunubi([114]).

 

Shubuhohi Kan Tayarwa ta Jiki:

Dubi cikin shubuhohin da malaman falsafa na da da na yanzu suke gabatarwa wajen inkarin tayarwa ta jiki, za a iya fahimtar cewa dukkansu suna komawa ne ko dai ga jahiltar siffofin Allah Maxaukaki, musamman a fagen ikonSa da ba shi da iyaka da kuma ilminSa da ya haxe komai, ko kuma jahiltar yanayin lahira da kuma siffofin da jikin da za a tayar a karo na biyu yake da shi. Don kuwa sukan kwatanta wancan duniya (lahira) da irin abubuwan da jikin wannan duniya yake da shi da qa’idojin da suke gudanar da wannan duniya da jikkunanta don kuwa hakan qiyasi ne a inda bai dace ba. Lahira dai ta bambanta da wannan duniya tamu da abubuwan da ta qumsa, don ita duniya da tsare-tsarenta za su canza a vangarori daban-daban, shi ma xan'Adam zai rayu ne wata irin rayuwa maras qarshe.

Bisa la'akari da bayanin da Alqur'ani mai girma da Sunna suka yi kan cewa jiki ba ya lalacewa, za a tayar da shi don ya haxu da ruhi, mutum ya zamanto xan'Adam, don ya samu lada ko uquba. Bayyanar  da wata shubuha kan hakan tamkar jahilci ne a gaban ilmi. Yanzu bari mu kawo wasu daga cikin shubuhohin da ake gabatarwa da qoqarin amsa su:

 

Na Farko: Shubuhar Ma-Ciyi da Wanda Aka Ci

Wannan tsohuwar shubuha ce, da Aplatun da makamantansa cikin masana falsafa na farko da ma na baya-bayan nan cikin musulmi da waxanda ba musulmi ba suka bayyana ta ta hanyoyi daban-daban, mafi muhimmanci ciki ita ce cewa: Da mutum zai yanka xan’uwansa mutum, ya cinye dukkan gavovinsa, to guda daga cikinsu ne za a tayar saboda babu abin da ya saura na guda daga cikinsu da za a sake halittar gavovinsa daga jiki. Don haka, da wani ruhi daga cikin biyu za a tayar da jikin da za a tayar xin? Idan har zai koma ga ruhin wanda ya ci (mutum) xin me, misali idan kafiri ne shi kuma wanda aka cinyen mumini ne, zai zamanto an azabtar da mumini kenan. Idan kuma aka sami akasin haka zai zamanto an saka wa kafiri kenan da alheri?

Amsa: Amsar wannan shubuha tana da fuskoki daban-daban:

1- Allah Maxaukakin Sarki Masani kan komai ne, ilminSa ya kewaye komai, Ya san komai, kome kashinsa, ciki kuwa har da gavovin wanda ya ci mutum da mutumin da aka cinyen, don haka zai iya taro su cikin hikima da ikonSa cikakkiya, Ya hura musu ruhi komai lalacewar da suka yi kuwa. Allah Maxaukakin Sarki na cewa:

 ﴿ Þõáú íõÍúíöíåóÇ ÇáøóÐöí ÃóäÔóÃóåóÇ Ãóæøóáó ãóÑøóÉò æóåõæó Èößõáøö ÎóáúÞò Úóáöíãñ

“Ka ce, ‘Wanda ya qaga halittarsu a farkon lokaci, Shi ke rayar da su, kuma Shi, game da kowace halitta, Mai ilmi ne([115]).

 Haka nan yayin da Ya ke mayar da martini ga shubuhar masu inkari, Allah Maxaukakin Sarki Yana cewa:

﴿ ÃóÆöÐóÇ ãöÊúäóÇ æóßõäøóÇ ÊõÑóÇÈðÇ Ðóáößó ÑóÌúÚñ ÈóÚöíÏñ  !ÞóÏú ÚóáöãúäóÇ ãóÇ ÊóäÞõÕõ ÇáÃóÑúÖõ ãöäúåõãú æóÚöäÏóäóÇ ßöÊóÇÈñ ÍóÝöíÙñ

“Shin, idan muka mutu, kuma muka kasance turvaya (za a komo da mu)? Wancan komowa ce mai nisa. Lalle ne, Mun san abin da qasa ke ragewa daga gare su, kuma wurinMu akwai wani littafi mai tsarewa([116]), kuma:

﴿ÞóÇáó ÝóãóÇ ÈóÇáõ ÇáúÞõÑõæäö ÇáÇõæáóì!ÞóÇáó ÚöáúãõåóÇ ÚöäÏó ÑóÈøöí Ýöí ßöÊóÇÈò áÇó íóÖöáøõ ÑóÈøöí æóáÇ óíóäÓóì

“Ya ce, ‘To mene ne halin qarnonin farko? Ya ce ‘Saninsu yana a wurin Ubangijina, Ubangijina ba Ya vacewa kuma ba Ya mantuwa([117])”.

Yayin da yake magana kan tayar da mamata, Amirul Muminina Ali (a.s) yana cewa: Har lokacin da al’amurra suka kusato, duniya ta qare kana tashin qiyama ta kusato, Allah Zai fitar da su daga kusurwoyin kaburburansu, daga sheqan tsuntsaye, kogon dabbobin daji da kuma wuraren mutuwa. Suna masu gaggawa zuwa ga UmarninSa da kuma makomarsu ta qarshe qungiya-qungiya, suna tsaye tsit a sahu….([118])”. A nan Amirul Muminina (a.s) yana nuni da cewa za a tayar da mutane ko da kuwa namun daji ko tsuntsaye ne suka cinye su.

2- Ya zo cikin wani hadisi daga Imam Sadiq (a.s) cewa: “(Wata rana) Annabi Ibrahim (a.s) ya kalli wata gawa da ke gavar rafi da namun daji da na ruwa suke ci, sai suka fara faxa tsakaninsu, suka cin junansu, hakan ya ba wa Ibrahim (a.s) mamaki, sai ya ce: Ya “Ubangijina Ka nuna min yadda kake rayar da matattu”? sai Allah Ta’ala Ya ce masa: “Shin ba ka yi imani ba ne, ya ce ‘Na’am! Kuma amma domin zuciyata, ta natsu’. Ya ce: ‘To ka riqi huxu daga tsuntsaye…”, har zuwa qarshen ayar[119]. Sai Ibrahim (a.s) ya xauko xawisu, zakara, kurciya da hankaka, sai Allah Ya ce masa: “Ka karkatar da su zuwa gare ka”, wato ka yayyanka su da rarraba namansu, sannan ka rarraba su kan duwatsu guda goma, sannan ka kira su za su zo maka a gudane. Sai Ibrahim (a.s) ya aikata hakan, ya raba su kana ya kira su….sai ga naman kowace guda na haxuwa da qashinta da kuma kanta, suka tashi suka nufo inda Ibrahim (a.s) yake, ganin haka sai ya ce: “Lalle, Allah Mabuwayi ne, Masani([120])”.

 Ana cewa: Cikin wannan ruwaya akwai ishara ga cewa Allah Maxaukakin Sarki yana kiyaye gavovin wanda aka ci cikin jikin wanda ya ci (mutum), inda za su dawo jikin wanda aka cin a lokacin tayarwa, kamar yadda aka rarraba da fitar da gavovin waxannan tsuntsaye daga junansu([121]).

3- Malaman aqida da na falsafa sun amsa wannan shubuha ta hanyar cewa tashin qiyama na faruwa ne kan sassa na asali ba wai dukkan sassa ba waxanda daga su ne aka fara halitta, waxanda za su ci gaba da wanzuwa tun farkon rayuwa har zuwa qarshenta. Don haka sassan asali na wanda aka cinye za su kasance marasa amfani ga wanda ya ci, don haka ba za a dawo da su ga wanda ya ci xin ba, amma za a dawo da su ga wanda aka cinyen ne([122]), saboda Allah Maxaukakin Sarki Zai kiyayesu, ba zai sanyasu yankin wani jiki ba.

Al-Muhaqqiq al-Tusi cikin Al-Tajrid yana cewa: Dawo da abubuwan da ba su ne asali ba a jikin mutum ba dole ba ne. Shi ma Allamah cikin sharhinsa na cewa: Mutane sun sassava kan wanda shari’a ta xorawa aiki (mukallafi) daga ciki akwai waxanda suke ganin rai mujarradi ne aka xora wa nauyin. Akwai kuma zancen wasu muhaqqiqai da suke ganin cewa nauyin aiki na bisa sassan asali na jiki waxanda ba su raguwa ko qaruwa. Abin da ke wajibi yayin tayarwa shi ne dawo da dukkan sassan asali ko kuma rai mujarradi tare da sassan asali. Amma sauran sassa da suke haxe da na asalin, ba dole ba ne a dawo da su([123]).

 

Na Biyu: Rashin Yiyuwar Dawowar Abin Da Ya Gushe:

Suna cewa: Dawo da abin da ya gushe ba zai tava yiyuwa ba saboda hakan zai tilasta kutsawar rashi cikin samuwa guda, sai abu guda ya zamanto biyu. Ko kuma ace mutuwa gushewa ce ga xan’Adam, to idan aka dawo masa da rayuwa a karo na biyu, zai kasance wani mutum ne na daban ba na farkon ba, wannan kuma zai zamanto wata sabuwar halitta ce bayan gushewa. Don haka babu dawowa a nana kuma babu wata alaqa tsakanin farkon (halittar farko) da tayarwa (wanda aka tayar ranar lahira).

 

Amsa:

1- Tayarwa bisa ra’ayin masana falsafa, imma dai tana nufin samar da samuwa bayan gushewa ko kuma dawowar sassan jiki bayan rarrabuwarsu. Malaman falsafa xin sun kore ma’anar farko, sai dai qa’idar madda da ake jinginata ga Lavosiya (wanda ya rasu a shekara ta 1793) ta yi watsi da wannan zance tun asali, saboda ra’ayinsa na cewa madda ba ta gushewa, tana nan ba ta canzawa sai dai idan wani abu ya bijiro mata. Kamar yadda a mahangar malaman falsafa gushewa ba ta aukawa samuwa, wasu malaman falsafa da na aqida su na ganin yiyuwar dawo da abin da ya gushe, yayin da suke cewa: Ba abin da zai hana samuwarsa ta biyu, ba zai hana hakan ba, sannan malizimta zatin ma ba za su hana ba. Don idan ba haka ba babu samuwa tun farko. Dawowa ta fi sauqi sama da fararwa. Su kuwa Mu’utazila suna da ra’ayin wanzuwar yanayin abubuwa da zatinsu; inda suke cewa: Shi rashi kansa abu ne, saboda haka idan aka gusar da samamme zatinsa da ya kevantu da shi zai wanzu, saboda haka akwai yiyuwar ya dawo, tun da yake zatin nasa zai ci gaba da wanzuwa ko da kuwa a halin gushewar ne.

Idan muka koma ga wata ma’anar tashin qiyamar kuma, wasu masanan falsafa musulmi masu imani da tayarwa ta jiki suna cewa: Tayarwa ta jiki ba tana nufin dawo da abin da ya gushe ba ne, a’a tara sassa ne da suka warwatse. Don kuwa gushewar jiki ba tana nufin lalacewarsa ba ne, abin da take nufi shi ne rarrabuwar sassa ne da cakuxuwarsu (da juna). Tattaro sassan da suka watse kuwa lamari ne mai yiyuwa saboda Allah Maxaukakin Sarki Masani ne kan waxannan sassa kuma Mai ikon iya tattaro da haxa su ne, saboda ilmi da quduran da Yake da su kan dukkan halittu([124]).

2- Yayin da muke amsa shubuhar da ta gabata mun ambaci ra’ayin wasu malaman aqida da falsafa na cewa jiki yana da wasu sassa na asali da qari ko ragi ko qarewa ba su shafansu. An ruwaito wani hadisi daga Imam Sadiq (a.s) dake tabbatar da hakan. Cikin Al-Kafi daga Ammar bn Musa daga Abu Abdillah al-Sadiq (a.s) yana cewa: An tambaye shi kan mamacin da jikinsa ya rududduge? Sai ya ce: “Na’am har namansa da qashinsa su qare su bar lakar da aka halicce shi daga ita, domin ita ba ta tsufa. Za ta wanzusaura cikin kabari har a sake halittar shi daga gare ta kamar yadda aka halicce shi tun farko([125]).

3- Koda ma abin mu yarda da qa’idar rashin yiyuwar dawowa da abin da ya gushe, to ai Allah Maxaukakin Sarki Wanda Ya halicci mutum tun farko, tun bai zama wani abu ba, Yana da ikon Ya sake dawo da shi ko da kuwa ba komai, kuma mun ambaci hakan a wajen hujjar qarfi (qudura) cikin dalilan hankali na tashin qiyama.

4- Abin da ke tsare tabbatuwar ko wane mutum shi ne ruhi, dake wajen Allah wanda ba zai tava gushewa ko lalacewa ba. Abu na biyu shi ne halittar jiki da sada shi da ruhi, sai ya zamanto shi shi xin ne ba tamkarsa ba, saboda haxuwar da suka yi ta mahiyya ce wato surar halitta.

 

Na Uku: Yawaituwar Jiki

Suna cewa: Qwayoyin halittar jikin mutum suna iya fuskantar canji a duniya. Ilmin kimiyya ya tabbatar da cewar dukkan abin da ya gina jikin xan’Adam na canzawa cikin shekaru goma, don haka da mutum zai mutu yana da shekaru sittin, to zai iya samun wannan canji har sau shida. Idan har abin da za a tayar ranar qiyama shi ne dukkan abubuwan da suka gina jikin mutum lokaci bayan lokaci, to hakan zai sa a tayar da jiki sama da xaya na mutum guda kenan. Idan kuwa abin da za a tayar jiki guda, to hakan ya sava wa adalcin Ubangiji don kuwa wannan jiki zai samu lada ko uqubu kan dukkan ayyukan da mutum ya yi kenan tsawon rayuwarsa.

Amsa: Yanayin xan’Adam a nan duniya yana nuni da warwarar wannan shubuha, don kuwa duk da yiyuwar ginin jiki da ake samu kamar yadda ilmi ya tabbatar, to amma mutum yana nan kamar yadda yake duk canza shi da lokaci da shekaru suka yi kuwa. Alal misali, da wani mai laifi zai aikata laifi lokacin samartakansa, amma sai aka masa hukumci lokacin tsufansa, ba za a ce hakan ya sava wa adalci ba ko kuma hukumci da aka yanke masa ba na wanda ya aikata laifin ba ne, haka lamarin yake ranar qiyama. Jiki dai jiki ne matuqar dai aka dawo masa da ruhi, sawa’un an tashe shi yana saurayi ne ko kuma tsoho.

Mulla Sadra yana cewa: A haqiqanin gaskiya abin da za a tayar lokacin tayarwa (ranar lahira) shi ne haqiqanin jikin mutum wanda ya mutu da sassansa, ba kamarsa ba, ta yadda da wani zai ganshi da ya ce: ai wannan wane ne da ya kasance a duniya. Duk wanda ya yi musun hakan ya qaryata shari’a, wanda kuwa ya qaryata shari’a bisa hukumcin hankali da shari’a, kafiri ne([126]).

Don haka, abin da ya wajaba kowani musulmi ya yi imani da shi, shi ne cewa a ranar lahira Allah Ta’ala zai dawo da mutane musamman mukallafai don hisabi, ko sakamako mai kyau ko maras kyau. Amma kan yadda za a dawo xin ko kuma yadda za a gudanar da hisabin, ko yanayin aljanna ko wuta da dai sauran siffofin ranar lahira…sun ce neman ilmi da imani da shi ba wajibi ba ne, imani na gaba xaya ya wadatar. Sai dai ababen da muka kawo na maganganu da hujjoji cikin littattafa daban-daban komai ba ne sai don kawai su taimaki mai karatu tunani don kuma su kasance mafarin bahasi da bincike.

 


([1]) . Tajarrudi shi ne kasancewar abu ba jiki ba, wato ba jiki ne da ake riska ta hanyoyin nan biyar ba, su ne: ji, gani, xanxano, sunsunawa da kuma shafawa. Misali fushi, qauna da qiyayya.

([2]) . Aradh: shi ne duk wani abin da samuwarsa yake buqatar wani abin da zai dogara da shi, Jauhar: kuma shi ne abin da ya tsaya da kansa, misali dutse ko bango jauhar ne amma launinsa ba jauhar ba ne domin babu launi kurum ba tare da abin da ya xauki launin ba.

([3]) , Dubi littafin Al-Ruh na Ibn al-Qayyim: 129, 158, 195 – Darul Qalam Beirut, Tafsir al-Razi 21: 40-53, Ruhul Ma'ani na Al-Allusi, 15: 155 – Darul Ihya al-Turath al-Arabi – Beirut, Bihar al-Anwar 61: 1-150, Da'irat Ma'arif al-Qarn al-Ishirin na Muhammad Farid Wajdi 4: 340-346 – Dar al-Fikr – Beirut.

([4]) . Suratul Isra': 17:85

([5]) . Dubi: Tafsir al-Razi 21: 38, Ruhul Ma'ani na Al-Allusi, 15: 152, Majma'ul Bayan na al-Tabrisi 6: 675 – Dar al-Ma'arifa – Beirut da Almizan na Tabataba'i 13: 199.

([6]) . Majma'ul Bayan na al-Tabrisi 6: 674 da Ruhul Ma'ani na Al-Allusi, 15: 152.

(¯). Malakutu wata duniya ce maxaukakiya sama da duniya ta zahiri.

([7]) . Tafsir al-Iyashi 2: 317/163 – Al-Maktab al-Ilmiyya al-Islamiyya – Tehran.

([8]) . Suratu Yasin: 36: 82-83.

([9]) . Suratul Qamar; 54: 50.

([10]) . Dubi Tafsir Almizan na Allamah Tabataba'i 1: 351 da 12:206 da 13:196-198.

([11]) . Al-Kasshaf na Zamakshari 2:690 da Majma'ul Bayan na Tabarisi 6: 675.

([12]) Tafsir al-Razi 21: 38 da Majma'ul Bayan na Tabarisi 6: 675.

([13]) . Suratul Hijr, 15: 29.

([14]) . Suratul Anbiya 21: 91.

([15]) .  Suratun Nisa' 4: 171.

([16]) . Dubi: Tashih al-I'itiqad na al-Mufid: 32, Mufradat na Ragib – qarqashin kalmar ruh-: 205, Ruhul Ma'ani na al-Allusi 15: 156 da kuma wannan aya ta take cikin Suratul Hajj: 22: 26.

([17]) . Suratu Maryam 19: 17.

([18]) . Tafsir al-Qummi 2: 48 – Dar al-Kitab – Birnin Qum – Iran.

([19]) . Suratush Shu'ara': 26: 193.

([20]) . Suratun Nahl 16:102.

([21]) . Tafsir al-Qummi 1: 390.

([22]) . Tafsir al-Mizan na Tabataba'i 14:36.

([23]) . Suratun Naba’ 79:38.

([24]) . Suratul Qadr: 97:4.

([25]) . Basa'ir al-Darajat na al-Saffar: 484/4 Mu'assasat al-A'alami – Tehran.

([26]) . Tafsir al-Qummi 2:402.

([27]) . Suratush Shura 42:52.

([28]) . Al-Kafi na al-Kulaini 1: 214/1.

([29]) . Suratul Mujadala 58:22.

([30]) . Al-Kafi na al-Kulaini 2:12/1 da 13/5.

([31]) . Al-Kafi na Al-Kulaini 2:213/11.

([32]) . Qurbul Asnad na al-Humairi 17 – Maktabat Nainawa – Tehran.

([33]) . Tafsir al-Mizan na Tabataba'i 19:197 ayar kuma tana cikin Suratul An'am 6:122 ne.

([34]) . Suratun Nahl 16:2.

([35]) . Suratu Ghafir 40:15.

([36]) . Tafsirul Qummi 1:382.

([37]) . Tafsir al-Razi 21: 38, sannan kuma a duba ma'anar ruhi cikin: Al-Anba Bima Fi Kalimat al-Qur'an min Adhwa na al-Karbasi 3:110-113 –Madba'at al-Adab – Najaf, da kuma Mufradat al-Ragib –ruh-: 2:455 –Nafs- 6:233.

([38]) . Al-Arba’in na Al- Baha'i: 499 – Jama’at a;Mudarrisin - Qum

([39]) . Tafsir al-Mizan na Tabataba'i 1:364, al-Ma’ad na Mutahari: 224 Mu’assasat Umm al-Qurah.

([40]) . Tafsir al-Mizan na Tabataba'i 1:350.

([41]) . Al-Maddiyun (Masu Aqidar Maddiyya): Aqidar Maddiyya ita ce aqidar masu ganin cewa babu wani abu samamme wanda ba madda ba. Madda shi ne abin da yake da jiki yake da nauyi da kuma xaukar wuri. Masu wannan aqida suna inkarin dukkan gaibi da ruhi da sauransu.

([42]) Dubi: Bihar al-Anwar 61:73-77 daga Sharh al-Mawaqif wa al-Saha’if al-Ilahiyya.

([43]) . Dubi: Da’irat Ma’arif al-Qarn al-Ishrin na Wajdi 4:330 da Al-Adillat al-Jaliyya fi Sharh al-Fusul al-Nasiriyya na Abdullah Ni’ima: 178.

([44]) . Al-Adillat al-Jaliyya fi Sharh al-Fusul al-Nasiriyya na Abdullah Ni’ima: 184-185.

([45]) . Dubi: Tafsir al-Razi 21:52-53, Tafsir al-Mizan na Tabataba'i: 1:365-370 da Da’irat al-Ma’arif al-Qarn al-Ishirin na Wajdi 4:332 da Tafsir Al-Amsal 9:105-107 – Mu’assasat al-Bi’itha – Beirut.

([46]) . Al-Ma’ad na Mutahhari:168-169 Mu’assasat Ummul Qurah da Ruhul Ma’ani na Al-Alusi 15:157 da Da’irat ma’arif al-Qarn al-Ishrin na Wajdi 4:324-327.

([47]) . Da’irat ma’arif al-Qarn al-Ishrin na Wajdi 4:327.

([48]) . Al-I’itiqad na Saduq: 50, ayar kuwa tana cikin Suratul Muminun 23:14.

([49]) . Al-I’itiqad na Saduq: 47.

([50]) . Kashful Murad fi Sharh Tajrid al-I’itiqad: 195.

([51]) . Dubi Al-Masa’il al-Sarwiyya na Sheikh Mufid: 59, Al-Arba’in na Al-Baha'i: 499-500, Bihar al-Anwar 61:13 da 75-76, da Tafsir al-Razi 21:45, Ruhul Ma’ani na Alusi 15:156, Da’irat Ma’arif al-Qarn al-Ishrin na Wajdi 4:338.

([52]) . Haqqun Yaqin na Abdullah Shibr 2:48.

([53]) . Dubi: Al-Ma’ad na shahid Mutahari: 169-170 da Falsafatuna na Shahid Sadr: 335 Dar al-Ta’arif – Beirut.

([54]) . Suratul Baqara 2:154.

([55]) . Suratu Al Imrana 3:169.

([56]) . Suratul Fajr 89:27-30.

([57]) . Al-Mizan na Tabataba'i: 1:350 da Tafsir al-Razi 21:40-41.

([58]) . Suratu Ghafir 40:45-46.

([59]) . Suratu Nuh 71:25.

([60]) . Dubi: Tafsir al-Razi 21:42.

([61]) . Suratul Muminun 23:12-14.

([62]) . Tafsir al-Razi 21:51 da Tafsir al-Mizan na Tabataba'i 1:352.

([63]) . Suratuz Zumar 39:42.

([64]) . Majma’ul Bayan na Tabrisi 8:781.

([65]) . Al-Kasshaf na Mugniyya 6:419 Dar al-Ilm lilmalayin- Beirut.

([66]) . Suratul Isra’ 17:85.

([67]) . Suratu Yasin 36:82.

([68]) . Tafsir al-Mizan na Tabataba'i 1:351-352.

([69]) . Tashih al-I’itiqad na Mufid: 91-92 Mu’utamar Sheikh al-Mufid.

([70]) . Siratun Nabawiyya na Ibn Hisham 2:292.

([71]) . Tafsir al-Razi 21:41.

([72]) . Tashih al-I’itiqad na Mufid: 93.

([73]) . Al-Kafi na Kulayni 3:243/1.

([74]) . Al-Kafi na Kulayni 3:244/4.

([75]) . Al-Kafi na Kulayni 3:245/1

([76]) . Nahjul Balaga, hikima ta 205.

([77]) . Da’irat Ma’arif al-Qarn al-Ishirin na Wajdi 4:377-378.

([78]) . Dubi: Usul al-Aqa’id fil Islam na Mujtaba Musawi Lari 4:89 da 92-94 da Al-Hayat ba’ad al-Maut na Ridha al-Muxawwuf al-Samawi: 297-315 Dar al-Zahra Beirut da Da’irat Ma’arif al-Qarn al-Ishrin na Wajdi 4:365-400 da 10:400-409.

([79]) . Suratun Nur; 24:24.

([80]) . Suratu Ibrahim; 14:48 da 51.

([81]) . Suratul Qiyama; 75:3-4.

([82]) . Suratu Yasin; 36:78-79.

([83]) . Suratu Yasin; 36:51-54.

([84]) . Suratu Taha; 20:55.

([85]) . Suratu Yasin; 36:65.

([86]) . Suratul Fusilat; 41:20.

([87]) . Suratul Baqara; 2:73 da 259-260 da Suratul Kahf; 18:21-25.

([88]) . Suratul Waqi'a; 56:15-23.

([89]) . Suratun Nisa’; 4:56.

([90]) . Nahjul Balagah, huxuba ta 83.

([91]) . Al-Amali na Saduq: 243/258, Haqqul Yaqin na Abdullah Shibr 2:54 da Bihar al-Anwar na Majlisi 7:33/1 daga Al-Amali da 7: 39/8 daga Tafsir Aliyu bn Ibrahim.

([92]) . Al-Asfar na Sadr al-Muta'allihin 9:165, Al-Mabda' wal Ma'ad na Sadr al-Muta'allihin 375.

([93]) . Haqqun Yaqin na Abdullah Shibr 2:38-39.

([94]) . Al’Ihtijaj na Tabrisi: 350.

([95]) . Al-Asfar na Sadr al-Muta'allihin 9:165, Sharh Mawaqif na al-Jarjani 8:298-300.

([96]) . Dubi: Al-Adhawiya fi Ma'ad na Ibn Sina: 126 Mu'assat al-Jam'iyya Beirut.

([97]) . Tuhafat al-Falsafa na Al-Ghazali: 235-253.

([98]) . Al-Shafi al-Ilahiyat na Ibn Sina 423 Al-Qahira, Bihar al-Anwar Na Majlisi 7:50.

([99]) . Ibn Sina wa Mazhabihi fi al-nafs na Fathullah Khalifa: 117 Beirut 1974.

([100]) . Bihar al-Anwar na Majlisi 7:52.

([101]) . Suratus Saba’: 34:7-8

([102]) . Suratul Jathiya 45:24.

([103]) . Suratul Qiyama 75:5-6.

([104]) . Suratul Mu’minun 23: 33-38.

([105]) . Suratun Nahl 16:22.

([106]) . Suratul Muminina 23:81-83.

([107]) . Suratun Nazi’at 79:10-12.

([108]) . Suratul Isra': 17:49 da 98.

([109]) . Suratul Sajda 32:10.

([110]) . Suratul Sajja 32:11.

([111]). Tafsir al-Mizan an Tabataba'i 11:299

([112]) . Suratul Ra'ad: 13:5.

([113]) . Suratul Isra':17:10.

([114]) . Suratul Muxaffifin 83:10-12.

([115]) . Suratu Yasin, 36:79.

([116]) . Suratu Qaf: 50: 3-4.

([117]) . Suratu Taha: 20: 51-52.

([118]) . Nahjul Balaga, huxuba ta 83.

([119]) . Suratul Baqara: 2:260

([120]) . Tafsir al-Qummi 1:91.

([121]) . Bihar al-Anwar na Majlisi 7:37.

([122]). Sharh al-Mawaqif na Al-Jarjani 8: 296, Al-Mabda’ wal Ma’ad na Sadruddeen Shirazi: 376.

([123]) . Kashful Murad na Allamah: 431-432.

([124]) . Dubi Sharh al-Mawaqif na al-Jarjani 8:289-293, Adillat al-Jaliya fi sharh al-Fusul al-Nasiriyya na Abdullah Ni’imat:212-213.

([125]).  Al-Kafi na Kulayni 3:251/2, Bihar 7:43/21.

([126]) . Al-Mabda’ wa al-Ma’ad na Mulla Sadra: 376.

عنوان الکتاب