Tushen imani da ranar lahira ya ginu ne a kan wahayin Ubangiji da ya zo daga gare Shi Maxaukakin Sarki. Akwai ayoyin Alqur'ani mai girma da yawa da suka tabbatar da ita, kuma kusan ko wace sura ta Alqur'ani ta qumshi ayoyi da suka yi magana kan ranar lahira. Har ma ana cewa: adadin ayoyin da suka yi magana kan ranar lahira a fili ko kuma da ishara sun wuce dubu guda. Labarai da qissosin ranar lahira da Alqur'ani mai girma ya bayar sun zo ne a yanayi daban-daban. Dalilai daban-daban sun tabbatar da yiyuwa da kuma wajibcin tashin qiyama a matsayin xaya daga cikin shika-shikan aqida cikin dukkannin saukakkun addinai tare da yin raddi ga batutuwan da masu shakku kanta suke gabatarwa. Haka nan sun ba da labari kan mutuwa, tayarwa bayan mutuwa, hisabi da kuma siraxi, kamar yadda kuma suka siffanta yanayin muminai a gidan aljanna da irin abubuwan jin daxin da aka tanadar musu, da kuma yanayin mujirimai a Jahannama da irin azabobin da aka tanadar musu. Abin da ke biye taqaicen bayani ne kan muhimman batutuwan da Alqur'ani mai girma ya tavo kan ranar lahira da abubuwan da ta qunsa: 1- Ba wa ranar lahira matsayin jigo cikin aqida da kuma tabbatar da cewa tana daga cikin wajiban shika-shikan aqida, Allah Maxaukakin Sarki na cewa: ﴿ áøóíúÓó ÇáúÈöÑøó Ãóä ÊõæóáøõæÇú æõÌõæåóßõãú ÞöÈóáó ÇáúãóÔúÑöÞö æóÇáúãóÛúÑöÈö æóáóÜßöäøó ÇáúÈöÑøó ãóäú Âãóäó ÈöÇááøåö æóÇáúíóæúãö ÇáÂÎöÑö æóÇáúãóáÂÆößóÉö æóÇáúßöÊóÇÈö æóÇáäøóÈöíøöíäó ﴾[1] "Bai zama addini ba domin kun juyar da fuskokinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira da mala’iku da litattafan sama da annabawa”. Da kuma faxinSa Ta'ala: ﴿ ãóäú Âãóäó ÈöÇááøåö æóÇáúíóæúãö ÇáÂÎöÑö æÚóãöáó ÕóÇáöÍðÇ ÝóáÇó ÎóæúÝñ Úóáóíúåöãú ﴾[2] "Wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, kuma Ya aikata na qwarai, to, babu tsoro a kansu..". 2- Jaddada samuwar ranar lahira da kuma kasancewarsa lamarin da babu kokwanto cikinsa, Allah Na cewa: ﴿ ÑóÈøóäóÇ Åöäøóßó ÌóÇãöÚõ ÇáäøóÇÓö áöíóæúãò áÇøó ÑóíúÈó Ýöíåö Åöäøó Çááøåó áÇó íõÎúáöÝõ ÇáúãöíÚóÇÏó﴾[3] "Ya Ubangijinmu! Lalle ne Kai, Mai tara mutane ne domin wani yini wanda babu shakka a gare shi. Lalle ne Allah ba Ya sava alqawari". Sannan kuma Yana cewa: ﴿ Çááøåõ áÇ ÅöáóÜåó ÅöáÇøó åõæó áóíóÌúãóÚóäøóßõãú Åöáóì íóæúãö ÇáúÞöíóÇãóÉö áÇó ÑóíúÈó Ýöíåö æóãóäú ÃóÕúÏóÞõ ãöäó Çááøåö ÍóÏöíËðÇ ﴾[4] "Allah, babu abin bautawa face Shi. Lalle ne, haqiqa, Yana tara ku har zuwa ga Yinin Qiyama, babu shakka a cikinsa. Kuma wane ne mafi gaskiya daga Allah ga labari". Sannan kuma Allah Maxaukakin Sarki Na cewa: ﴿ æóÃóÞúÓóãõæÇú ÈöÇááøåö ÌóåúÏó ÃóíúãóÇäöåöãú áÇó íóÈúÚóËõ Çááøåõ ãóä íóãõæÊõ Èóáóì æóÚúÏðÇ Úóáóíúåö ÍóÞøðÇ æóáÜßöäøó ÃóßúËóÑó ÇáäøóÇÓö áÇó íóÚúáóãõæäó﴾[5] "Kuma suka rantse da Allah iyakar rantsuwarsu cewa Allah ba ya tayar da wanda yake mutuwa! Na'am, Yana tayarwa. Wa'adi ne Allah Ya yi a kanSa tabbatacce, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba", kuma yana cewa: ﴿ æóÞóÇáó ÇáøóÐöíäó ßóÝóÑõæÇ áÇó ÊóÃúÊöíäóÇ ÇáÓøóÇÚóÉõ Þõáú Èóáóì æóÑóÈøöí áóÊóÃúÊöíóäøóßõãú ﴾[6] "Kuma waxanda suka kafirta suka ce: 'Sa'a ba za ta zo mana ba' Ka ce; 'Kayya! Na rantse da Ubangijina, lalle za ta zo muku". 3- Tabbatar yiyuwar tashin qiyama da tada mamata ta hanyar da ba ta xaukan wani tawili, ta hanyar kafa misali da dawo da wasu mutane ko kuma al'ummomi ko dabbobi cikin al'ummomin da suka wuce zuwa duniya bayan mutuwarsu, inda suka sake rayuwa har lokacin da Allah Ya sake xaukar ransu. Hakan kuwa ya faru a lokuta da wurare daban-daban don kore duk wasu shakku yiyuwar dawo da mutum da kuma tabbatar da ikon Ubangiji Maxaukakin Sarki kan makoma. Ga kaxan daga cikin misalan hakan[7]: a - Rayar da wasu al'umma daga cikin Bani Isra'ila: Allah Maxaukakin Sarki na cewa: ﴿ Ãóáóãú ÊóÑó Åöáóì ÇáøóÐöíäó ÎóÑóÌõæÇú ãöä ÏöíóÇÑöåöãú æóåõãú ÃõáõæÝñ ÍóÐóÑó ÇáúãóæúÊö ÝóÞóÇáó áóåõãõ Çááøåõ ãõæÊõæÇú Ëõãøó ÃóÍúíóÇåõãú Åöäøó Çááøåó áóÐõæ ÝóÖúáò Úóáóì ÇáäøóÇÓö æóáóÜßöäøó ÃóßúËóÑó ÇáäøóÇÓö áÇó íóÔúßõÑõæäó ﴾[8] "Shin, ba ka gain ba, zuwa ga waxanda suka fita daga gidajensu, alhali kuwa su dubbai ne, domin tsoron mutuwa? Sai Allah Ya ce musu: "Ku mutu", sa'an nan kuma Ya rayar da su, lalle ne Allah, haqiqa, Ma'abucin falala a kan mutane ne, kuma amma mafi yawan mutane ba su godewa". b – Rayar da xaya daga cikin Annabawan Bani Isra'ila, Allah Maxaukakin Sarki Na cewa: ﴿ Ãóæú ßóÇáøóÐöí ãóÑøó Úóáóì ÞóÑúíóÉò æóåöíó ÎóÇæöíóÉñ Úóáóì ÚõÑõæÔöåóÇ ÞóÇáó Ãóäøóìó íõÍúíöÜí åóÜóÐöåö Çááøåõ ÈóÚúÏó ãóæúÊöåóÇ ÝóÃóãóÇÊóåõ Çááøåõ ãöÆóÉó ÚóÇãò Ëõãøó ÈóÚóËóåõ ÞóÇáó ßóãú áóÈöËúÊó ÞóÇáó áóÈöËúÊõ íóæúãðÇ Ãóæú ÈóÚúÖó íóæúãò ÞóÇáó Èóá áøóÈöËúÊó ãöÆóÉó ÚóÇãò ÝóÇäÙõÑú Åöáóì ØóÚóÇãößó æóÔóÑóÇÈößó áóãú íóÊóÓóäøóåú æóÇäÙõÑú Åöáóì ÍöãóÇÑößó æóáöäóÌúÚóáóßó ÂíóÉð áøöáäøóÇÓö æóÇäÙõÑú Åöáóì ÇáÚöÙóÇãö ßóíúÝó äõäÔöÒõåóÇ Ëõãøó äóßúÓõæåóÇ áóÍúãðÇ ÝóáóãøóÇ ÊóÈóíøóäó áóåõ ÞóÇáó ÃóÚúáóãõ Ãóäøó Çááøåó Úóáóì ßõáøö ÔóíúÁò ÞóÏöíÑñ﴾[9] "Ko kuwa wanda ya shuxe a kan wata alqarya, alhali kuwa tana wofintacciya a kan gidajen resunanta. Ya ce; 'Ya ya Allah zai rayar da wannan a bayan mutuwarta', sai Allah Ya matar da shi, shekara xari, sa'an nan kuma Ya tayar da shi. Ya ce: 'Nawa ka zauna? Ya ce; "Na zauna yini guda ko kuwa rabin yini'. Ya ce: 'A'a, ka zauna shekara xari." To, ka duba zuwa ga abincinka, da abin shaka kowannensu bai sake ba, kuma ka duba zuwa ga jakinka, kuma domin Mu sanya ka wata aya ga mutane. Kuma ka duba zuwa ga qasusuwa yadda Muke motsar da su, sa'an nan kuma Mu tufatar da su da nama'. To, a lokacin da abin ya bayyana a gare shi, ya ce: 'Ina sanin cewa lalle Allah a kan dukkan kome Mai ikon yi ne". c – Rayar da mutane saba'in daga cikin al'ummar Annabi Musa a.s, Allah Maxaukakin Sarki na cewa: ﴿æóÅöÐú ÞõáúÊõãú íóÇ ãõæÓóì áóä äøõÄúãöäó áóßó ÍóÊøóì äóÑóì Çááøóåó ÌóåúÑóÉð ÝóÃóÎóÐóÊúßõãõ ÇáÕøóÇÚöÞóÉõ æóÃóäÊõãú ÊóäÙõÑõæäó ! Ëõãøó ÈóÚóËúäóÇßõã ãøöä ÈóÚúÏö ãóæúÊößõãú áóÚóáøóßõãú ÊóÔúßõÑõæäó﴾[10] "Kuma a lokacin da kuka ce: "Ya Musa! Ba za mu yi imani ba dominka, sai mun ga Allah bayyane", saboda haka tsawar nan ta kamu ku, alhali kuwa kuna kallo. Sa'an nan kuma Muka tayar da ku daga bayan mutuwarku, tsammaninku, kuna godewa". d – Rayar da wanda aka kashe daga Bani Isra'ila: Allah Maxaukakin Sarki na cewa: ﴿æóÅöÐú ÞóÊóáúÊõãú äóÝúÓÇð ÝóÇÏøóÇÑóÃúÊõãú ÝöíåóÇ æóÇááøåõ ãõÎúÑöÌñ ãøóÇ ßõäÊõãú ÊóßúÊõãõæäó ! ÝóÞõáúäóÇ ÇÖúÑöÈõæåõ ÈöÈóÚúÖöåóÇ ßóÐóáößó íõÍúíöí Çááøåõ ÇáúãóæúÊóì æóíõÑöíßõãú ÂíóÇÊöåö áóÚóáøóßõãú ÊóÚúÞöáõæäó﴾[11] "Kuma a lokacin da kuka yi kisan kai, kuka dinga tunkuxa wa juna laifi a cikinsa, kuma Allah Mai fitar da abin da kuka kasance kuna voyewa ne. Sai Muka ce: "Ku doke shi da wani sashenta'. Kamar wancan ne Allah Yake rayar da matattu, kuma Ya nuna muku ayoyinSa, tsammaninku, kuna hankalta". e – Rayar da tsuntsaye ga Annabi Ibrahim a.s da izinin Allah Maxaukaki, Allah Yana cewa: ﴿æóÅöÐú ÞóÇáó ÅöÈúÑóÇåöíãõ ÑóÈøö ÃóÑöäöí ßóíúÝó ÊõÍúíöÜí ÇáúãóæúÊóì ÞóÇáó Ãóæóáóãú ÊõÄúãöä ÞóÇáó Èóáóì æóáóÜßöä áøöíóØúãóÆöäøó ÞóáúÈöí ÞóÇáó ÝóÎõÐú ÃóÑúÈóÚóÉð ãøöäó ÇáØøóíúÑö ÝóÕõÑúåõäøó Åöáóíúßó Ëõãøó ÇÌúÚóáú Úóáóì ßõáøö ÌóÈóáò ãøöäúåõäøó ÌõÒúÁðÇ Ëõãøó ÇÏúÚõåõäøó íóÃúÊöíäóßó ÓóÚúíðÇ æóÇÚúáóãú Ãóäøó Çááøåó ÚóÒöíÒñ Íóßöíãñ﴾[12] "Kuma a lokacin da Ibrahim ya ce: "Ya Ubangijina! Ka nuna min yadda Kake rayar da matattu". Ya ce: "Shin, kuma ba ka yi imani ba?", ya ce: "A'a!, amma domin zuciyata, ta natsu". Ya ce: "To ka riqi huxu daga tsuntsaye, ka karkatar da su zuwa gare ka, ka yanka su, sa'an nan kuma ka sanya juzu'i daga gare su a kan kowane dutse, sa'an nan kuma ka kira su, za su zo maka gudane. Kuma ka sani cewa lalle Allah Mabuwayi ne, Masani". 4- Bayanin Alqur'ani mai girma cewa xaya daga cikin muhimman ayyukan Annabawa a.s shi ne gargaxin mutane dangane da ranar da za a tayar da su gobe qiyama. Allah Maxaukakin Sarki Yana cewa: ﴿ íóÇ ãóÚúÔóÑó ÇáúÌöäøö æóÇáÅöäÓö Ãóáóãú íóÃúÊößõãú ÑõÓõáñ ãøöäßõãú íóÞõÕøõæäó Úóáóíúßõãú ÂíóÇÊöí æóíõäÐöÑõæäóßõãú áöÞóÇÁ íóæúãößõãú åóÜÐóÇ ÞóÇáõæÇú ÔóåöÏúäóÇ Úóáóì ÃóäÝõÓöäóÇ æóÛóÑøóÊúåõãõ ÇáúÍóíóÇÉõ ÇáÏøõäúíóÇ æóÔóåöÏõæÇú Úóáóì ÃóäÝõÓöåöãú Ãóäøóåõãú ßóÇäõæÇú ßóÇÝöÑöíäó﴾[13] "Ya jama'ar aljannu da mutane! Shin, manzanni daga gare ku ba su je muku ba, suna labarta ayoyiNa a kanku, kuma suna yi muku gargaxin haxuwa da wannan yini naku ba? Suka ce: "Mun yi shaida a kan kawunanmu", Kuma rayuwar duniya ta ruxe su. Kuma suka yi shaida a kan kawunansu cewa, lalle ne su, sun kasance kafirai". Sannan kuma Allah Maxaukakin Na cewa: ﴿ æóÓöíÞó ÇáøóÐöíäó ßóÝóÑõæÇ Åöáóì Ìóåóäøóãó ÒõãóÑðÇ ÍóÊøóì ÅöÐóÇ ÌóÇÄõæåóÇ ÝõÊöÍóÊú ÃóÈúæóÇÈõåóÇ æóÞóÇáó áóåõãú ÎóÒóäóÊõåóÇ Ãóáóãú íóÃúÊößõãú ÑõÓõáñ ãøöäßõãú íóÊúáõæäó Úóáóíúßõãú ÂíóÇÊö ÑóÈøößõãú æóíõäÐöÑõæäóßõãú áöÞóÇÁ íóæúãößõãú åóÐóÇ ÞóÇáõæÇ Èóáóì æóáóßöäú ÍóÞøóÊú ßóáöãóÉõ ÇáúÚóÐóÇÈö Úóáóì ÇáúßóÇÝöÑöíäó﴾[14] "Kuma aka kora waxanda suka kafirta zuwa Jahannama, jama'a-jama'a, har a lokacin da suka je mata, sai aka buxc qofofinta, kuma matsaranta suka ce musu; 'Ashe waxansu manzanni, daga cikinku ba su je muku ba, suna karanta ayoyin Ubangijinku a kanku kuma suna yi muku gargaxin gamuwa da yininku wannan ba? Suka ce: "Na'am" kuma amma kalmar azaba ita ce ta wajaba a kan kafirai". Gargaxin da ake magana a nan dai bai taqaita ga wata al'umma ban da wata ba. 5- Jaddadawan Alqur'ani mai girma kan samuwar aqidar tashin qiyama cikin sauran saukakkun addinan da suka gabaci Musulunci. Yayin da Yake magana kan jawabin Annabi Nuhu a.s ga al'ummarsa. Allah Ta’ala Na cewa: ﴿ Ëõãøó íõÚöíÏõßõãú ÝöíåóÇ æóíõÎúÑöÌõßõãú ÅöÎúÑóÇÌÇð !æóÇááåõ ÃóäÈóÊóßõã ãöäó ÇáÇúóóÑúÖö äóÈóÇÊÇð ﴾ [15] “Kuma Allah Ya tsirar da ku daga qasa kamar ganye tsirarwa. Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa". Dangane da sha'anin Annabi Musa kuwa, Yana cewa: ﴿ Ëõãøó ÂÊóíúäóÇ ãõæÓóì ÇáúßöÊóÇÈó ÊóãóÇãðÇ Úóáóì ÇáøóÐöíó ÃóÍúÓóäó æóÊóÝúÕöíáÇð áøößõáøö ÔóíúÁò æóåõÏðì æóÑóÍúãóÉð áøóÚóáøóåõã ÈöáöÞóÇÁ ÑóÈøöåöãú íõÄúãöäõæäó ﴾[16] "Sa'an nan kuma Mun bai wa Musa Littafi, yana cikakke bisa ga wanda ya kyautata hukumcin Allah da rarrabewa, daki-daki, ga kowane abu, da shiriya da rahama, tsammaninsu, suna yin imani da haxuwa da Ubangijinsu". Sannan, yayin da yake hakaito sukan da Musa a.s ya yi wa Fir'auna da fadawansa, Allah Maxaukaki Na cewa: [17]﴿Åöäøöí ÚõÐúÊõ ÈöÑóÈøöí æóÑóÈøößõã ãøöä ßõáøö ãõÊóßóÈøöÑò áÇó íõÄúãöäõ Èöíóæúãö ÇáúÍöÓóÇÈö﴾ "Lalle ni, na nemi tsari da Ubangijina kuma Ubangijinku, daga dukkan makangari, wanda ba ya imani da ranar hisabi". Haka nan Allah Maxaukakin Sarki, yayin da yake tunasar da Annabi Isa a.s ranar lahira, Yana cewa: ﴿ÅöÐú ÞóÇáó Çááøåõ íóÇ ÚöíÓóì Åöäøöí ãõÊóæóÝøöíßó æóÑóÇÝöÚõßó Åöáóíøó æóãõØóåøöÑõßó ãöäó ÇáøóÐöíäó ßóÝóÑõæÇú æóÌóÇÚöáõ ÇáøóÐöíäó ÇÊøóÈóÚõæßó ÝóæúÞó ÇáøóÐöíäó ßóÝóÑõæÇú Åöáóì íóæúãö ÇáúÞöíóÇãóÉö Ëõãøó Åöáóíøó ãóÑúÌöÚõßõãú ÝóÃóÍúßõãõ Èóíúäóßõãú ÝöíãóÇ ßõäÊõãú Ýöíåö ÊóÎúÊóáöÝõæäó﴾[18] "A lokacin da Ubangiji Ya ce: "Ya Isa! Lalle Ni Mai karvar ranka ne, kuma Mai xauke ka ne zuwa gare Ni, kuma Mai tsarkake ka daga waxanda suka kafirta, kuma Mai sanya waxanda suka bi ka a bisa waxanda suka kafirta, har Ranar Qiyama. Sa'an nan kuma zuwa gare Ni makomarku take, sa'an nan In yi hukumci a tsakaninku, a cikin abin da kuka kasance kuna sava wa juna". 6 – Alqur'ani mai girma, cikin ayoyi da yawa, ya bayyana cewa Allah Ta’ala Ya wakilta wasu Mala'iku wajen rubuta ayyuka da zantukan bayi cikin wani littafi da ba ya barin babba ko qarami. Allah Ta’ala Na cewa: ﴿ÅöäøóÇ äóÍúäõ äõÍúíöí ÇáúãóæúÊóì æóäóßúÊõÈõ ãóÇ ÞóÏøóãõæÇ æóÂËóÇÑóåõãú æóßõáøó ÔóíúÁò ÃÍúÕóíúäóÇåõ Ýöí ÅöãóÇãò ãõÈöíäò﴾[19] "Lalle Mu, Mu ne ke rayar da matattu kuma Mu rubuta abin da suka gabatar, da gurabunsu, kuma kowane abu Mun qididdige shi, a cikin babban Littafi Mabayyani". Kuma Yana cewa: ﴿ Ãóãú íóÍúÓóÈõæäó ÃóäøóÇ áÇó äóÓúãóÚõ ÓöÑøóåõãú æóäóÌúæóÇåõã Èóáóì æóÑõÓõáõäóÇ áóÏóíúåöãú íóßúÊõÈõæäó﴾[20] "Ko suna zaton lalle Mu, ba Mu jin asirinsu da ganawarsu? Na'am! Kuma manzanninMu na tare da su suna rubutawa". Sannan Allah Maxaukaki Na cewa: ﴿ æóáóÞóÏú ÎóáóÞúäóÇ ÇáÅöäÓóÇäó æóäóÚúáóãõ ãóÇ ÊõæóÓúæöÓõ Èöåö äóÝúÓõåõ æóäóÍúäõ ÃóÞúÑóÈõ Åöáóíúåö ãöäú ÍóÈúáö ÇáúæóÑöíÏö ! ÅöÐú íóÊóáóÞøóì ÇáúãõÊóáóÞøöíóÇäö Úóäö Çáúíóãöíäö æóÚóäö ÇáÔøöãóÇáö ÞóÚöíÏñ ! ãóÇ íóáúÝöÙõ ãöä Þóæúáò ÅöáÇøó áóÏóíúåö ÑóÞöíÈñ ÚóÊöíÏñ﴾[21] "Kuma lalle ne, haqiqa, Mun halitta mutum, kuma Mun san abin da ransa ke yin waswsi da shi, kuma Mu ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar jannayensa. A lokacin da masu haxuwa biyu suke haxuwa daga dama, kuma daga hagu akwai wani Mala'ika zaunanne. Ba ya lafazi da wata magana face a liqe da shi akwai mai tsaro halartacce". A wasu guraren, ayoyin Alqur'ani suna bayyana cewa akan gabatar da takardun ayyukan mutane gare su lokacin da aka zo da su don hisabi, sai a ce musu: ﴿Çáúíóæúãó ÊõÌúÒóæúäó ãóÇ ßõäÊõãú ÊóÚúãóáõæäó ! åóÐóÇ ßöÊóÇÈõäóÇ íóäØöÞõ Úóáóíúßõã ÈöÇáúÍóÞøö ÅöäøóÇ ßõäøóÇ äóÓúÊóäÓöÎõ ãóÇ ßõäÊõãú ÊóÚúãóáõæäó﴾[22] "…A wannan rana ne za a saka muku abin da kuka kasance kuna aikatawa a duniya. Wannan littafinmu ne yana yin magana da ku da gaskiya, haqiqa Mu mun kasance Muna rubuta abin da kuka kasance kuna aikatawa". Daga nan sai ximuwa da damuwa ta kama mujirimai saboda abubuwan da suke cikin waxannan littafa, Allah Maxaukakin Sarki Yana cewa: ﴿æóæõÖöÚó ÇáúßöÊóÇÈõ ÝóÊóÑóì ÇáúãõÌúÑöãöíäó ãõÔúÝöÞöíäó ãöãøóÇ Ýöíåö æóíóÞõæáõæäó íóÇ æóíúáóÊóäóÇ ãóÇáö åóÐóÇ ÇáúßöÊóÇÈö áÇó íõÛóÇÏöÑõ ÕóÛöíÑóÉð æóáÇó ßóÈöíÑóÉð ÅöáÇøó ÃóÍúÕóÇåóÇ æóæóÌóÏõæÇ ãóÇ ÚóãöáõæÇ ÍóÇÖöÑðÇ æóáóÇ íóÙúáöãõ ÑóÈøõßó ÃóÍóÏðÇ﴾[23] "Aka kuma sanya littafin ayyukansu sannan sai ka ga masu laifi cikin damuwa saboda abin da yake cikinsa, suna kuma cewa: "Kaiconmu, me ya sami wannan littafin, bay a barin aiki qarami balle babba sai ya rubuce shi, suka kuma sami duk abubuwan da suka aikata an zo da su. Ubangijinka kuwa ba Ya zaluntar kowa". A fili waxannan ayoyi sun tabbatar da samuwar littattafan da ake rubuta ayyukan mutane da kuma samuwar ranar sakamako da za a gabatar wa kowa abubuwan da aka rubuta na ayyukan da ya aikata a duniya, babba ne ko qarami. 7 – Akwai kuma ayoyi masu yawa da suke raddi ga masu inkarin ranar lahira da kuma bayyana cewa waxannan mutane ba su da komai kashin dalili na inkarin wannan batu, ba abin da suke da shi in ba zato ba kuma zato haqiqa ba ya wadatar da komai a kan gaskiya. Allah Ta'ala na cewa: ﴿æóÞóÇáõæÇ ãóÇ åöíó ÅöáÇøó ÍóíóÇÊõäóÇ ÇáÏøõäúíóÇ äóãõæÊõ æóäóÍúíóÇ æóãóÇ íõåúáößõäóÇ ÅöáÇøó ÇáÏøóåúÑõ æóãóÇ áóåõã ÈöÐóáößó ãöäú Úöáúãò Åöäú åõãú ÅöáÇøó íóÙõäøõæäó﴾[24] "Suka kuma ce: "Ai ita ba wata aba ba ce, face rayuwarmu ta duniya, za mu mutu mu kuma sake rayuwa ba kuwa wani mai hallakar da mu sai zamani, alhali kuwa ba su da wani sani game da wannan, ba abin da suke yi sai zato". A wani wajen kuma Yana cewa: ﴿æóãóÇ áóåõã Èöåö ãöäú Úöáúãò Åöä íóÊøóÈöÚõæäó ÅöáÇøó ÇáÙøóäøó æóÅöäøó ÇáÙøóäøó áÇó íõÛúäöí ãöäó ÇáúÍóÞøö ÔóíúÆðÇ﴾[25] "Kuma ba su da wani ilmi game da shi, baa bin da suke bi sai zato, kuma zato haqiqa ba ya wadatar da komai a kan gaskiya". A wani wajen kuma, Allah Yana qalubalantarsu da su kawo dalilin inkarin nasu. Allah Ta’ala Yana cewa: ﴿ Þõáú åóÇÊõæÇ ÈõÑúåóÇäóßõãú Åöä ßõäÊõãú ÕóÇÏöÞöíäó﴾[26] "Ka ce da su: "Ku kawo dalilanku inda kun kasance masu gaskiya". Ba komai suke da shi ba face qananan shakku da damuwa[27]. Alqur'ani mai girma ya ba su amsoshi masu gamsarwa, wasu daga ciki hujjoji ne na hankali da ke tabbatar da wajibcin makoma lahira da cika alqawarin Allah, kamar faxinsa Maxaukakin Sarki cewa: ﴿æóÖóÑóÈó áóäóÇ ãóËóáðÇ æóäóÓöíó ÎóáúÞóåõ ÞóÇáó ãóäú íõÍúíöí ÇáúÚöÙóÇãó æóåöíó Ñóãöíãñ ! Þõáú íõÍúíöíåóÇ ÇáøóÐöí ÃóäÔóÃóåóÇ Ãóæøóáó ãóÑøóÉò æóåõæó Èößõáøö ÎóáúÞò Úóáöíãñ﴾[28] "Kuma ya buga mana wani misali, kuma ya manta da halittarsa, ya ce: "Wane ne ke rayar da qasusuwa alhali kuwa suna rududdugaggu?. Ka ce, 'Wanda Ya qaga halittarsu a farkon lokaci, Shi ke rayar da su, kuma Shi, game da kowace halitta, Mai ilmi ne".
Na Biyu: Cikin HadisaiAkwai hadisan Ma'aiki s.a.w.a da Ahlulbaiti a.s da yawa da suka yi magana kan ranar lahira da abubuwan da ta qunsa na tayar da mutane, hisabi, ni’ima ko kuma azaba gwargwadon yadda Alqur'ani mai girma ya yi bayani ko kuma ma a ce da qarin bayani. A nan za mu ambato wasu hadisan da suke tabbatar da ranar lahira da kuma abubuwan da za su faru. Manzon Allah s.a.w.a yana cewa: "Ya 'ya'yan Abdul Mutallib…..Na rantse da Wanda Ya aiko ni da gaskiya za ku mutu kamar yadda kuke barci, kuma za a tayar da ku kamar yadda kuke farkawa daga barci. Bayan mutuwa babu wani gida face Aljanna ko wuta, halittar dukkan halittu da tayar da su a wajen Allah Maxaukaki tamkar halittar rai guda ne da tayar da shi, Allah Ta'ala Na cewa: ﴿ãøóÇ ÎóáúÞõßõãú æóáÇó ÈóÚúËõßõãú ÅöáÇøó ßóäóÝúÓò æóÇÍöÏóÉò﴾[29]. Sannan kuma yana cewa: "Bawa ba zai yi imani ba har sai ya yi imani da abubuwa guda huxu: Har sai ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaxai ba Shi da abokin tarayya, sannan ni Manzon Allah ne da Ya aiko ni da gaskiya, har sai ya yi imani da tayarwa bayan mutuwa, sannan kuma har sai ya yi imani da qaddara[30]". Amirul Muminina Ali a.s yana cewa: "Har lokacin da dukkan abubuwan da aka rubuta suka zo qarshe, al'amurra suka isa ga inda aka nufe su da isa, aka sadar da halittar qarshe da ta farko sannan umarnin Allah na sabonta halittarSa ya zo. Sannan sai Ya motsa sama da tsattsagata, Ya kuma girgiza qasa, Ya tunvuko duwatsu da tarwatsa su, sai su bugi juna saboda haibarSa da tsoron girmanSa. Yayin da Ya fitar da waxanda ke cikinta, daga nan Ya sake sabonta su bayan sun dagargaje, Ya taro su bayan sun rarrabu. Daga nan sai Ya rarraba su don yi musu tambayoyi kan ayyukan da suka voye. Sai Ya raba su gida biyu: Ya saka wa xaya da alheri Ya kuma azabtar da guda[31]". Haka nan yayin da yake siffanta ranar lahira, yana cewa: "A wannan rana, Allah Zai tara na farko da na qarshe don hisabi da sakamako ga ayyukan da suka aikata suna masu qan-qan da kai, suna tsaye alhali gumi na karyo musu, qasa kuma tana girgiza a qasa da su, wanda yanayinsa yafi kyau shi ne wanda ya sama wa qafafunsa wajen tsayawa, sannan kuma ya samu wajen numfasawa mai faxi[32]". Imam Aliyu bn Husain Zainul Abidin a.s yana cewa: "Lalle abin da mamaki mutum ya yi shakku kan Allah alhali yana ganin halittun Ubangiji, abin da mamaki yadda mutum zai yi inkarin mutuwa alhali a kullum yana ganin ana mutuwa, abin da mamaki yadda mutum zai yi inkarin tayar da mamaci a lahira alhali yana ganin halittarta farko halittan mutum, abin da mamaki ga wanda yake gina gidan da zai rushe ba da jimawa ba duniya alhali ya fita sha'anin gidan zama na har abada[33]".
Na Uku: Al-Ijma:Imani da ranar lahira aqida ce da dukkan musulmi suka yi imani da ita ba tare da wani savani ba. Dukkansu suna ganin imani da ranar lahira a matsayin lalura na addini da dole ne dukkan musulmi ya yi imani da shi, wanda kuwa ya yi inkarin hakan ya fita daga cikinsu. Idan muka duba za mu ga cewa kalmar da musulmi suke maimaitawa a kullum ta 'maliki yaumiddin' tana nuni da imaninsu na samuwar rayuwa bayan mutuwa, don haka wannan batu ne da suka haxu a kansa. Dukkan addinai da shari'oi sun tafi a kan samuwar wata rayuwa bayan mutuwa, savanin da kawai ake da shi shi ne dangane da yadda hakan zai faru. A baya mun kawo bayanai kan ma'anar tashin qiyama a isxilahi na addini, abin da muke son yi a nan ba shi ne gudanar da bincike na ilmi cikin waxannan maganganu da fitar da wanda ya dace ba. Abin da za mu ba shi muhimmanci shi ne tabbatar da asalin fikirar tashin qiyaman, wanda shi ne dawo da mutum bayan mutuwa zuwa ga rayuwa ta biyu, ko ma dai ta ya ya ne, inda za a saka wa mutum kan ayyukan da ya aikata, in alheri, alheri, in sharri, sharri. Wannan lamari ne da dukkan musulmi suka haxu a kai, don abu ne mai yiyuwa a hankalce, kuma hakan ya faru bisa nassin Alqur'ani da sauran saukakkun Littafa.
Na Huxu: Dalili Na Hankali:Da dama daga cikin malaman falsafa da na aqida sun kafa hujja ta hankali tsantsa a kan tabbatar ranar qiyama da wajibcin hakan, kamar yadda a cikin Alqur'ani mai girma akwai dalilai masu yawa, na hankali da waxanda ake saninsu daga zuciya wujdani da suke tabbatar da haqiqanin makoma da rayuwa bayan mutuwa, a matsayin raddi ga masu inkarin tashin qiyama da kuma tabbatar faruwar hakan. Abin da ke biye wasu ne daga cikin irin waxannan dalilai:
Na Farko: Dalili Na Tamka:Allamah Hilli yana cewa: 'Wata duniya tamkar wannan duniya ta mu mai yiyuwar samuwa mumkin ce, domin ita wannan duniya kanta mai yiyuwar samuwa ce; kuma tamka daidai yake da tamka a wajen hukumci. Saboda haka, tun da dai wannan duniya mai yiyuwar samuwa ce, to wajibi ne a yi wa xayar ma hukumcin yiyuwar samuwa[34]". Akwai wasu misalai kan hakan da Alqur'ani mai girma ya kawo da ke nuni da kama da daidaito tsakanin rayawa a duniya da kuma a gobe qiyama ta nau'i guda biyu: Na farko: Daidaito ko kama na samuwar farko wato daga rashi da samuwa ta lahira. Na biyu: kama da ke akwai tsakanin rayar da qasa bayan mutuwarta da kuma rayarwa a lahira. Hankali yana hukumci da cewa tamka daidai take da tamkarta wajen hukumci, don haka muna iya fahimtar cewa mai ikon samara da rayuwa ta farko zai iya samar da wata rayuwa ta biyu, don kuwa abubuwa ne guda biyu da suke tamkar juna. Nau’in Farko Na Tamka: Abin nufi a nan shi ne kafa hujjar makoma tashin qiyama ta hanyar mafari halittar farko ta hanyar tamkar da suke da ita. Alqur'ani mai girma ya tabbatar da yiyuwar tashin qiyama ta hanyar tabbatar da tamkar hakan, ta hanyar kwatanta samar da mutum a wannan duniya bayan ya kasance babu shi – kamar halittar Annabi Adamu a.s ba tare da uwa ko uba ba – da kuma dawo da shi bayan mutuwa da lalacewa. Allah Maxaukakin Sarki Na cewa: ﴿íóÇ ÃóíøõåóÇ ÇáäøóÇÓõ Åöä ßõäÊõãú Ýöí ÑóíúÈò ãøöäó ÇáúÈóÚúËö ÝóÅöäøóÇ ÎóáóÞúäóÇßõã ãøöä ÊõÑóÇÈò Ëõãøó ãöä äøõØúÝóÉò Ëõãøó ãöäú ÚóáóÞóÉò Ëõãøó ãöä ãøõÖúÛóÉò ãøõÎóáøóÞóÉò æóÛóíúÑö ãõÎóáøóÞóÉò áøöäõÈóíøöäó áóßõãú æóäõÞöÑøõ Ýöí ÇáÃóÑúÍóÇãö ãóÇ äóÔóÇÁ Åöáóì ÃóÌóáò ãøõÓóãøðì Ëõãøó äõÎúÑöÌõßõãú ØöÝúáðÇ Ëõãøó áöÊóÈúáõÛõæÇ ÃóÔõÏøóßõãú æóãöäßõã ãøóä íõÊóæóÝøóì æóãöäßõã ãøóä íõÑóÏøõ Åöáóì ÃóÑúÐóáö ÇáúÚõãõÑö áößóíúáóÇ íóÚúáóãó ãöä ÈóÚúÏö Úöáúãò ÔóíúÆðÇ﴾ "Ya ku mutane! Idan kun zamanto cikin kokwanton tashi, to haqiqa Mu Muka halicce ku daga qasa, sannan daga maniyyi, sannan daga gudan jini, sannan daga tsoka, mai cikakkiyar halitta da kuma wadda ba cikakkiya ba, don Mu bayyanar muku ikonMu. Kuma muna tabbatar da abin da Muke so a cikin mahaifa har zuwa wani lokaci qayyadajje, sannan kuma Mu fito da ku kuna jarirai, sannan kuma don ku kai cikakken qarfinku; daga cikinku akwai wanda za a karvi ransa, akwai kuma wanda za a bari har zuwa mafi qasqantar rayuwa don ya kai ga halin da ba zai san komai ba bayan kuwa da can ya sani", har zuwa faxin Allah Maxaukakin Sarki cikin Alqur’ani cewa: ﴿Ðóáößó ÈöÃóäøó Çááøóåó åõæó ÇáúÍóÞøõ æóÃóäøóåõ íõÍúíöí ÇáúãóæúÊóì æóÃóäøóåõ Úóáóì ßõáøö ÔóíúÁò ÞóÏöíÑñ﴾, "Wannan kuwa saboda Allah Shi ne Gaskiya, kuma lalle Shi ne yake raya matattu, kuma haqiqa Mai iko ne a kan komai"[35]. Saboda haka mutum ya kasance ba komai ba, sai Allah Ya samar da shi daga turvaya, Ya fitar da shi daga rashi zuwa samuwa, daga nan Ya arzurta shi da hankali da fahimta, Ya sanya shi a mafi kyaun halitta. Don haka babu kokwanto cikin ta da shi bayan mutuwa da ragwargwajewar gavovinsa domin kuwa hakan tamkar halittarsa a duniyan nan ne bayan da babu shi; don hukumcin abubuwan da suke tamka guda ne, hankali ba ya bambantawa tsakanin abubuwan da suke dadai, kai yana ma xaukar samuwar xaya daga cikinsu dalili ne a kan yiyuwar samun xayan. Daxin daxawa, ai samuwar farko ita tafi ban mamaki. Allah Ta'ala Yana cewa: ﴿ æóåõæó ÇáøóÐöí íóÈúÏóÃõ ÇáúÎóáúÞó Ëõãøó íõÚöíÏõåõ æóåõæó Ãóåúæóäõ Úóáóíúåö æóáóåõ ÇáúãóËóáõ ÇáÃóÚúáóì Ýöí ÇáÓøóãóÇæóÇÊö æóÇáúÃóÑúÖö ﴾[36] "Shi ne wanda Ya ke farar da halittu, sannan Ya mayar da su bayan mutuwa. Yin hakan kuwa shi ne ya fi sauqi a gare Shi, kuma Yana da sifa maxaukakiya a cikin sammai da qassai". A nan dukkan ayoyin da suke daidaita tsakanin mafari da makoma tashin qiyama wajen hukumci suna tabbatar da wannan hujja, kamar faxin Allah Maxaukaki cewa: [37] ﴿ Çááøóåõ íóÈúÏóÃõ ÇáúÎóáúÞó Ëõãøó íõÚöíÏõåõ Ëõãøó Åöáóíúåö ÊõÑúÌóÚõæäó ﴾ "Allah ne Yake farar halitta sannan Ya mayar da ita bayan mutuwa sannan kuma gare Shi za a komar da ku", da kuma faxinSa: [38] ﴿ÝóÓóíóÞõæáõæäó ãóä íõÚöíÏõäóÇ Þõáö ÇáøóÐöí ÝóØóÑóßõãú Ãóæøóáó ãóÑøóÉò﴾ "Sannan za su ce: "To wa zai dawo da mu bayan mun rududduge? Ka ce dasu: "Wanda Ya halicce ku tun farko", da faxinSa Ta’ala: [39]﴿ßóãóÇ ÈóÏóÃúäóÇ Ãóæøóáó ÎóáúÞò äøõÚöíÏõåõ æóÚúÏðÇ ÚóáóíúäóÇ ÅöäøóÇ ßõäøóÇ ÝóÇÚöáöíäó﴾ "Kamar yadda Muka qagi halitta da farko haka za Mu mai da ita. Wannan alqawari ne da Muka xauka. Haqiqa Mun kasance Masu aikata haka". Nau’i Na Biyu Na Tamka: Alqur'ani mai girma, cikin ayoyi masu yawa[40] ya tabbatar da ranar qiyama ta hanyar xaukar abubuwa biyu a matsayin tamkar juna wato rayarwar da ake ji da ganinta, ita ce rayar da qasa bayan mutuwarta, da tsirowar tsiro daga qasar da dawowar rayuwarsu bayan dakatar da ita lokacin sanyi, da kuma rayar da matattu ranar qiyama. Allah Maxaukaki Sarki Na cewa: ﴿ ÝóÇäÙõÑú Åöáóì ÂËóÇÑö ÑóÍúãóÊö Çááøóåö ßóíúÝó íõÍúíöí ÇáÃóÑúÖó ÈóÚúÏó ãóæúÊöåóÇ Åöäøó Ðóáößó áóãõÍúíöí ÇáúãóæúÊóì æóåõæó Úóáóì ßõáøö ÔóíúÁò ÞóÏöíÑñ﴾[41] "Sannan ka yi dubi zuwa ga guraban rahamar Allah yadda Yake raya qasa bayan qeqashewarta. Haqiqa wannan lallai Mai raya matattu ne, kuma Mai iko ne a kan komai", kuma Yana cewa: ﴿æóåõæó ÇáøóÐöí íõÑúÓöáõ ÇáÑøöíóÇÍó ÈõÔúÑðÇ Èóíúäó íóÏóíú ÑóÍúãóÊöåö ÍóÊøóì ÅöÐóÇ ÃóÞóáøóÊú ÓóÍóÇÈðÇ ËöÞóÇáÇð ÓõÞúäóÇåõ áöÈóáóÏò ãøóíøöÊò ÝóÃóäÒóáúäóÇ Èöåö ÇáúãóÇÁ ÝóÃóÎúÑóÌúäóÇ Èöåö ãöä ßõáøö ÇáËøóãóÑóÇÊö ßóÐóáößó äõÎúÑöÌõ ÇáúãæúÊóì áóÚóáøóßõãú ÊóÐóßøóÑõæäó﴾[42] "Shi ne kuma Yake aiko muku da iska mai albishir tare da rahamarSa, har dai lokacin da ta xauko girgije mai nauyi da ruwa sai Mu shayar da gari qeqasasshe da shi, sai Mu saukar masa da ruwa, sannan Mu fitar da dukkan 'ya'yan itace daga gare shi. Kamar haka Muke fito da matattu don ko kwa wa'azantu". Wannan aya da ma wacce ta gabace ta suna qoqarin kiran hankali wanda ya yarda da cewa hukumcin abubuwan da suke tamkar juna, guda ne, wato idan har rayar da qasa bayan mutuwa ya tabbata ba abin da zai hana abkuwar hakan a kan xan'Adam bayan mutuwarsa da ma rayayyu. Allamah Sayyid Tabataba'i na cewa: "Manufar faxin Allah Maxaukaki ﴿Åöäøó Ðóáößó áóãõÍúíöí ÇáúãóæúÊóì﴾ ita ce nuni zuwa ga tamka da ke cikin rayar da matacciyar qasa da kuma rayar da mamaci, don kuwa a cikinsu akwai mutuwa, wato kawar da rayuwa daga wani abin da aka kiyaye shi, da rayuwa wato sake dawo da wannan abu da aka kawar. Haqiqa rayarwa ta faru ga qasa da tsirai da kuma rayuwar xan'Adam da dai sauran abubuwa masu rai, ga shi kuma hukumcin tamka xaya ne. To idan har rayarwa tana iya yiyuwa a kan wasu daga cikin waxannan tamka, wato qasa da tsirai to ya halalta a kan sauran[43]". Alqur'ani mai girma ya yi ishara da abin da ke kusato da wannan ma'ana, shi ne kuwa cewa halittan xan'Adam tamkar na tsirrai ne, haka nan sake raya shi, Allah Ta'ala Na cewa: ﴿æóÇááøóåõ ÃóäÈóÊóßõã ãøöäó ÇáÃóÑúÖö äóÈóÇÊðÇ * Ëõãøó íõÚöíÏõßõãú ÝöíåóÇ æóíõÎúÑöÌõßõãú ÅöÎúÑóÇÌðÇ﴾[44] "Kuma Allah Ya tsirar da ku daga qasa kamar ganye tsirarwa. Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa".
Na Biyu: Dalili Na QuduraBisa la'akari da cewa qudurar Mahalicci da ba ta da iyaka, sai mu ce ta shafi dukkan komai daidai wadaida ba tare da bambanci kan abu mai wahala da mai sauqi ba. Ana iya fahimtar hakan cikin faxinSa Allah Maxaukakin Sarki: ﴿Åöäøó Çááøóå Úóáóì ßõáøö ÔóíúÁò ÞóÏöíÑñ﴾, wato “Allah mai qarfi ne a kan dukkan komai”. Ayoyin Alqur'ani da yawa sun yi ishara da hanyoyi biyu na tabbatar da tashin qiyama ta hanyar ambaton quduran Ubangiji da kuma kasancewarta mara iyaka: Hanya Ta Farko: Cikin ayoyi da yawa[45] Allah Maxaukakin Sarki Ya bayyana qudurarsa kan tayarwa a ranar lahira bayan ambaton mafari samuwa ta farko, wanda hakan za nuna cewa duk wanda ke da qarfin samar da abu daga rashi, yana da qarfin dawo da shi bayana lalacewarsa, Allah Maxaukakin Sarki na cewa: ﴿Ãóæóáóãú íóÑóæúÇ ßóíúÝó íõÈúÏöÆõ Çááøóåõ ÇáúÎóáúÞó Ëõãøó íõÚöíÏõåõ Åöäøó Ðóáößó Úóáóì Çááøóåö íóÓöíÑñ ! Þõáú ÓöíÑõæÇ Ýöí ÇáÃóÑúÖö ÝóÇäÙõÑõæÇ ßóíúÝó ÈóÏóÃó ÇáúÎóáúÞó Ëõãøó Çááøóåõ íõäÔöÆõ ÇáäøóÔúÃóÉó ÇáúÂÎöÑóÉó Åöäøó Çááøóåó Úóáóì ßõáøö ÔóíúÁò ÞóÏöíÑñ﴾[46] "Yanzu ba su ga yadda Allah Yake farar halitta ba, sannan Shi ne kuma Zai mayar da ita? Haqiqa wannan mai sauqi ne a wurin Allah. Ka ce: "Ku yi tafiya a bayan qasa sannan ku duba ku ga yadda Allah Ya farar da halittu. Sannan Allah ne Zai sake samar da su samawar qarshe. Haqiqa Allah Mai iko ne a kan komai". Waxannan ayoyi biyu su na kwaxaitar da xan'Adam ne da ya yi dubi cikin lamarin halittar farko, domin ta hanyar hankalinsa ya fahimci Wanda Ya halicce ta Ya kuma tsara. Wannan rukunin farko ne na kafa hujja kan tashin qiyama da qudurar Ubangiji mara iyaka. Alqur'ani ya sake jaddada wannan rukunin cikin wasu ayoyin na daban. Allah Na cewa: ﴿ ÃóáÇó íóÚúáóãõ ãóäú ÎóáóÞó æóåõæó ÇááøóØöíÝõ ÇáúÎóÈöíÑõ﴾[47] "Ashe, Wanda Ya yi halitta ba zai iya saninta ba, alhali kuwa Shi Mai tausasawa ne, kuma Masani ne", har ila yau Yana cewa: ﴿ äóÍúäõ ÎóáóÞúäóÇßõãú Ýóáóæúáà ÊõÕóÏøöÞõæäó ﴾[48] "Mu ne Muka halicce ku saboda me ba kwa gaskatawa", har zuwa inda Ya ke cewa: ﴿æóáóÞóÏú ÚóáöãúÊõãõ ÇáäøóÔúÃóÉó ÇáÇõæáóì Ýóáóæúáà ÊóÐßøóÑõæäó﴾[49] "Haqiqa kuma ku kun san farkon halittarku, don me ba kwa wa'azantuwa". Abu ne da yake a fili cewa xan'Adam ya san samuwarsa ta farko, ya kuma fahimci cewa Wanda Ya samar da shi, Ya zava masa siffofin da yake da su, Ya tsara masa al'amarinsa, Shi ne Allah Maxaukakin Sarki da Ya halicci dukkan komai, Allah Maxaukakin Sarki na cewa: [50]﴿Þõáú åóáú ãöä ÔõÑóßóÂÆößõã ãøóä íóÈúÏóÃõ ÇáúÎóáúÞó Ëõãøó íõÚöíÏõåõ﴾ "Ka ce da su: "Shin daga cikin gumakanku ko akwai wanda yake qaga halitta, sannan ya mai da ita?", sannan Yana cewa: ﴿ßóíúÝó ÊóßúÝõÑõæäó ÈöÇááøóåö æóßõäÊõãú ÃóãúæóÇÊÇð ÝóÃóÍúíóÇßõãú Ëõãøó íõãöíÊõßõãú Ëõãøó íõÍúíöíßõãú Ëõãøó Åöáóíúåö ÊõÑúÌóÚõæäó﴾[51] "Ku mutane qa qa kuke kafircewa da Allah, alhali kuwa kun kasance rasassu sannan Ya samar da ku, sannan kuma zai kashe ku sannan Ya sake raya ku, sannan kuma wurinSa za a komar da ku". Daga abin da ya gabata mun fahimci cewa qarfin quduran Ubangiji Maxaukakin Sarki da ba shi da iyaka na rayarwa a karon farko da na biyu xaya ne babu wani bambanci, babu wata gazawa ta kowani vangare, Allah Yana cewa: [52]﴿ÃóÝóÚóíöíäóÇ ÈöÇáúÎóáúÞö ÇáÇæøóáö Èóáú åõãú Ýöí áóÈúÓò ãøöäú ÎóáúÞò ÌóÏöíÏò﴾ "Shin Mun gaza ne da halittar farko? Ba haka ba ne, su dai suna cikin ximuwa ne game da sake sabuwar halitta", kamar yadda Yake cewa: ﴿ãøóÇ ÎóáúÞõßõãú æóáÇó ÈóÚúËõßõãú ÅöáÇøó ßóäóÝúÓò æóÇÍöÏóÉò﴾[53] "Halittarku da tayar da ku bai wuce tamkar na rai guda ba", don haka babu wani abu da yafi wani sauqi ko wahala a wajen Allah Maxaukakin Sarki. Haqiqa cikin hakan akwai hujja mai qarfi da zai sanya mutum imani da ranar lahira da yarda da ita. Hanya Ta Biyu: Allah Maxaukakin Sarki Ya bayyana qudurursa ta tayarwa a ranar qiyama a jere da ambaton halittar sammai da qassai. Allah Maxaukaki Yana cewa: ﴿ æóÞóÇáõæÇú ÃóÆöÐóÇ ßõäøóÇ ÚöÙóÇãðÇ æóÑõÝóÇÊðÇ ÃóÅöäøóÇ áóãóÈúÚõæËõæäó ÎóáúÞðÇ ÌóÏöíÏðÇ ! Ãóæóáóãú íóÑóæúÇú Ãóäøó Çááøåó ÇáøóÐöí ÎóáóÞó ÇáÓøóãóÇæóÇÊö æóÇáÃóÑúÖó ÞóÇÏöÑñ Úóáóì Ãóä íóÎúáõÞó ãöËúáóåõãú﴾[54] "…suka kuma ce: "Yanzu idan muka zama qasusuwa kuma rududdugaggu bayan mutuwa, yanzu ashe kuwa za a tashe mu mu koma sabuwar halitta? Yanzu ba sa ganin cewa Allah Wanda Ya halicci sammai da qassai Mai iko ne a kan Ya halicci irinsu?", sannan Yana cewa: ﴿ ÃóæóáóíúÓó ÇáøóÐöí ÎóáóÞó ÇáÓøóãóÇæóÇÊö æóÇáÃóÑúÖó ÈöÞóÇÏöÑò Úóáóì Ãóäú íóÎúáõÞó ãöËúáóåõã Èóáóì æóåõæó ÇáúÎóáÇøóÞõ ÇáúÚóáöíãõ ! ÅöäøóãóÇ ÃóãúÑõåõ ÅöÐóÇ ÃóÑóÇÏó ÔóíúÆðÇ Ãóäú íóÞõæáó áóåõ ßõäú Ýóíóßõæäõ ﴾[55] "Yanzu Wanda Ya halicci sammai da qassai ba zai samu ikon halitta irinsu ba? Ai tabbas zai iya, kuma Shi ne Mai yawan halittu Masani. UmarninSa kawai idan Ya yi nufin wani abu sai Ya ce da shi: "Ka samu, sai ya samu", kuma yana cewa: ﴿ Ãóæóáóãú íóÑóæúÇ Ãóäøó Çááøóåó ÇáøóÐöí ÎóáóÞó ÇáÓøóãóÇæóÇÊö æóÇáÃóÑúÖó æóáóãú íóÚúíó ÈöÎóáúÞöåöäøó ÈöÞóÇÏöÑò Úóáóì Ãóäú íõÍúíöíó ÇáúãóæúÊóì Èóáóì Åöäøóåõ Úóáóì ßõáøö ÔóíúÁò ÞóÏöíÑñ ﴾[56] "Shin ba sa ganin cewa haqiqa Allah Wanda Ya halicci sammai da qassai bai kuma gaji ba wajen halittarsu Mai iko ne kan Ya raya matattu ba? Ba haka ba ne, haqiqa Shi Mai iko ne a bisa dukkan komai". Tunani kan halittun sammai da qassai zai kai mu ga imani da lahira, don kuwa Wanda Ya halicci sama da qasa – da dukkan abubuwan da ke cikinsu na mamaki – ya ya za a ce ba zai iya sake halittan xan'Adam a ranar lahira ba? Ai halittan mutum nesa ba kusa ba tafi sauqi a kan halittan sammai da qassai. Allah Ta’ala Na cewa: ﴿áóÎóáúÞõ ÇáÓøóãóÇæóÇÊö æóÇáÇÑúÖö ÃóßúÈóÑõ ãöäú ÎóáúÞö ÇáäøóÇÓö æóáóßöäøó ÃóßúËóÑó ÇáäøóÇÓö áÇó íóÚúáóãõæäó﴾[57] "Ba shakka halittar sammai da qassai ta fi girma a kan halittar mutane, sai dai kuma yawancin mutane ba su sani ba". A wani wajen kuma Allah Maxaukaki Na cewa: ﴿ÃóÃóäÊõãú ÃóÔóÏøõ ÎóáúÞðÇ Ãóãö ÇáÓøóãóÇÁ ÈóäóÇåóÇ ! ÑóÝóÚó ÓóãúßóåóÇ ÝóÓóæøóÇåóÇ ! æóÃóÛúØóÔó áóíúáóåóÇ æóÃóÎúÑóÌó ÖõÍóÇåóÇ ! æóÇáÃóÑúÖó ÈóÚúÏó Ðóáößó ÏóÍóÇåóÇ﴾[58] "Yanzu ku ne kuka fi qarfin halitta ko kuwa sama ce? Shi fa Ya gina ta. Ya xaukaka rufinta sannan Ya daidaita ta. Ya duhuntar da darenta Ya kuma fitar da hasken hantsinta. Qasa kuma bayan hakan Ya shimfixa ta". Akwai kuma wasu ayoyin Alqur'ani mai girma da suka zo don ruguza abubuwan da wasu mutane suka yi riqo da su wajen nesantar da aqidar tashin qiyama: ﴿æóÞóÇáõæÇú ÃóÆöÐóÇ ßõäøóÇ ÚöÙóÇãðÇ æóÑõÝóÇÊðÇ ÃóÅöäøóÇ áóãóÈúÚõæËõæäó ÎóáúÞðÇ ÌóÏöíÏðÇ﴾ "Kuma suka ce: "Shin, idan mun kasance qasusuwa da niqaqqun gavavuwa, an ya kuwa za a tashe mu da sabuwar halitta?", sai Allah Maxaukakin Sarki Ya mayar musu da martini Yana mai tunatar da su qarfinsa maras iyaka: ﴿Þõá ßõæäõæÇú ÍöÌóÇÑóÉð Ãóæú ÍóÏöíÏðÇ* Ãóæú ÎóáúÞðÇ ãøöãøóÇ íóßúÈõÑõ Ýöí ÕõÏõæÑößõãú﴾[59] "Ka ce da su: "Ku zama dutse ko baqin qarfe. Ko kuwa wata halitta daga abin da yake da girma a cikin qirazanku". A nan Allah Ya yi musu umarni ne na wofantar da su da cewa su zamanto dutse ko qarfe ko kuma duk wani abin da suke ganin mayar da shi mutum zai zamanto wahala sama da mayar da niqaqqun gavavuwa ko qasa zuwa mutum, su kasance duk abin da suke son zama, Allah Zai sake mayar musu da halittarsu bayan tashisu ranar qiyama. Daga wannan muna iya fahimtar cewa babu wani abin da ya isa ya keta qudurar Ubangiji a duk lokacin da take son gudanar da aikinta na sabunta halitta, shin daga qasusuwa ne ko kuma gavavun da suke gama lalacewa ko dutse ko qarfe ko waninsu[60].
Na Uku: Dalili Na HikimaHaqiqa Allah Ta'ala Mai hikima ne cikin ayyukanSa, dukkan abin da Ya fito daga gare Shi yana qumshe da hikima. Duniya da dukkan abubuwan mamakin da ke cikinta tana tafiya ne bisa hikima da manufa, kamar yadda dukkanin dokokin shari'a suna komawa ga tafarkin hikima da ya sava wa wasa da wargi. Allah Na cewa: [61]﴿ÃóÝóÍóÓöÈúÊõãú ÃóäøóãóÇ ÎóáóÞúäóÇßõãú ÚóÈóËðÇ æóÃóäøóßõãú ÅöáóíúäóÇ áÇó ÊõÑúÌóÚõæäó﴾ "Ko kuna tsammani ne cewa Mun halicce ku ne don wasa, kuma ko ba za a dawo da ku gare Mu ba?", sannan Yana cewa: ﴿æóãóÇ ÎóáóÞúäóÇ ÇáÓøóãóÇÁ æóÇáÃóÑúÖó æóãóÇ ÈóíúäóåõãóÇ ÈóÇØöáÇð Ðóáößó Ùóäøõ ÇáøóÐöíäó ßóÝóÑõæÇ Ýóæóíúáñ áøöáøóÐöíäó ßóÝóÑõæÇ ãöäó ÇáäøóÇÑö﴾[62] "Kuma ba Mu halicci sammai da qassai da abin da ke tsakaninsu a banza ba. Wannan shi ne zaton waxanda suka kafirce, saboda haka tsananin azabar wuta ta tabbata ga waxanda suka kafirce", sannan Allah Ta'ala Na cewa: ﴿ÃóíóÍúÓóÈõ ÇáÅöäÓóÇäõ Ãóä íõÊúÑóßó ÓõÏðì﴾[63] "Yanzu mutum yana tsammanin za a bar shi haka sakaka?". Ana iya kawo siffar wannan hujja ta hanyar qiyasi da ya qumshi rukunai guda biyu: Na Farko: Allah Maxaukakin Sarki ma'abucin hikima ne. Na biyu: Duk wani ma'abucin hikima ba ya aikata wani abu saboda wasa, don haka Allah Maxaukaki ba Ya aikata abu domin wargi ko wasa ba tare da dalili ba. Idan da a ce babu makoma tashin qiyama ga mutum to da halittarsa ta zamanto wargi kawai, ga shi kuwa bisa hikima ta Ubangiji, Allah ba Ya aikata wargi, don haka dole ne xan'Adam ya sami makoma a ranar qiyama saboda hikimar Ubangiji. Da a ce mutum ya kan qare ne da mutuwa ba tare da cewa za a ta da shi saboda wata rayuwa, ko aljanna ko wuta, ba, to da halittarsa a wannan duniya ta kasance wasa da wargi, don kuwa kowani irin aiki ba ya iya fita daga matsayin wasa da wargi har sai ya kasance yana da wata manufar da hankali ke karvanta. Hakan zai samu ne ta hanyar makoma tashin qiyama kaxai, don kuwa idan har rayuwar mutum ta kan zo qarshe ne bayan mutuwa, kenan babu wata manufa ga halittar xan'Adam da ta wuce wannan rayuwa ta duniya mai iyaka da ke cike da matsaloli, fitina, bala'oi da sauran nau'oi na damuwa. Sannan hakan na nuna cewa kenan Allah Ya taqaita ne kawai da samarwa da kashewa, sannan samarwa da kashewa ba tare da wata manufa ba. Wannan kuma lamari ne da mutum mai hankali ba zai aikata ba, ina ga Mahalicci, Mai hikima?!! Haqiqa Allah Maxaukaki Ya xaukaka ga barin wannan. Don haka, dole ne a samu wata duniya ta daban da za ta cimma manufar halittan, hakan kuwa ita ce duniyar dawwama, Allah Maxaukakin Sarki Na cewa: ﴿æóãóÇ åóÐöåö ÇáúÍóíóÇÉõ ÇáÏøõäúíóÇ ÅöáÇ áóåúæñ æóáóÚöÈñ æóÅöäøó ÇáÏøóÇÑó ÇáÇÎöÑóÉó áóåöíó ÇáúÍóíóæóÇäõ áóæú ßóÇäõæÇ íóÚúáóãõæäó﴾[64] "Kuma wannan rayuwar duniyar ba komai ba ce face nishaxi da wasa, kuma haqiqa rayuwar gidan lahira ita ce rayuwa, in da sun kasance sun sani". A nan wasu ayoyin Alqur'ani sun tabbatar da cewa halittan duniya cikin hikima shi ne yake tabbatar da samuwar ranar lahira, Allah Maxaukakin Sarki Na cewa: ﴿Ãóæóáóãú íóÊóÝóßøóÑõæÇ Ýöí ÃóäÝõÓöåöãú ãóÇ ÎóáóÞó Çááøóåõ ÇáÓøóãóÇæóÇÊö æóÇáÃóÑúÖó æóãóÇ ÈóíúäóåõãóÇ ÅöáÇøó ÈöÇáúÍóÞøö æóÃóÌóáò ãøõÓóãøðì æóÅöäøó ßóËöíÑÇð ãøöäó ÇáäøóÇÓö ÈöáöÞóÇÁ ÑóÈøöåöãú áóßóÇÝöÑõæäó﴾[65] "Yanzu ba su yi tunani a kan kansu ba? Allah bai halicci sammai da qassai da abin da ke tsakaninsu ba sai a kan gaskiya da kuma zuwa lokaci qayyadajje. Haqiqa mafi yawan mutane masu kafircewa ne da haxuwa da Ubangijinsu". Sannan kuma Maxaukaki Yana cewa: ﴿æóãóÇ ÎóáóÞúäóÇ ÇáÓøóãóÇæóÇÊö æóÇáÃóÑúÖó æóãóÇ ÈóíúäóåõãóÇ áÇÚöÈöíäó ! ãóÇ ÎóáóÞúäóÇåõãóÇ ÅöáÇ ÈöÇáúÍóÞøö æóáóßöäøó ÃóßúËóÑóåõãú áÇ íóÚúáóãõæäó ! Åöäøó íóæúãó ÇáúÝóÕúáö ãöíÞóÇÊõåõãú ÃóÌúãóÚöíäó﴾[66]
"Ba Mu kuma halicci sammai da qassai da abin ke tsakaninsu ba don wasa ba shiririta ba. Ba Mu halicce su ba sai don gaskiya, sai dai kuma yawancinsu ba su, sani ba. Haqiqa ranar rabewa shi ne lokacinsu baki xaya"
Na Huxu: Dalili Na Adalci
A fili yake cewa Allah Maxaukakin Sarki Ya sanya rayuwar duniya a matsayin jarrabawa ga xan'Adam, don kuwa Ya ba shi abubuwan da suke tura mutum zuwa ga alheri da kuma waxanda suke tura shi zuwa ga sharri don wannan jarrabawa ta cika. A daidai wannan lokaci kuma sai Ya ba shi hankalin da zai bambance tsakanin alheri gaskiya da sharri qarya, Ya aiko masa da Annabawa don su bayyanar masa da tafarkin gaskiya da na qarya. Bayan haka sai Ya xora masa nauyin bin tafarkin gaskiya da kuma nesantar na qarya da vata, Ya kuma ba shi damar zavi don ya cancanci sakamako mai kyau in ya aikata mai kyau ko azaba in ya aikata mummuna. Allah Na cewa: [67]﴿ÇáøóÐöí ÎóáóÞó ÇáúãóæúÊó æóÇáúÍóíóÇÉó áöíóÈúáõæóßõãú Ãóíøõßõãú ÃóÍúÓóäõ ÚóãóáÇð﴾ "Wanda Ya halicci mutuwa da rayuwa don Ya jarraba ku, Ya ga waye a cikinku ya fi kyakkyawan aiki", sannan kuma Yana cewa: [68]﴿æóÈóáóæúäóÇåõãú ÈöÇáúÍóÓóäóÇÊö æóÇáÓøóíøöÆóÇÊö﴾ "Muka kuma jarrabe su da daxaxan abubuwa da wahalhalu". A wani wajen, Allah Na cewa: ﴿æóäóÈúáõæßõã ÈöÇáÔøóÑøö æóÇáúÎóíúÑö ÝöÊúäóÉð æóÅöáóíúäóÇ ÊõÑúÌóÚõæäó﴾[69] "Muna kuwa jarrabarku da fitinar sharri da ta alheri, kuma gare Mu ne za a dawo da ku". Don haka, haqiqanin rayuwar duniya da dukkanin abin da ta qumsa na abubuwa masu warwarar juna; jin daxi da wahala, lafiya da cuta, arziqi da talauci, rungumar masharranta da yin watsi da mutanen kirki, dukkansu jarrabawa ne ga xan'Adam babu wani abu daga waxannan da zai dace da abin sakawa. To da yake kallafa wa mutum wani aiki yana wajabta saka masa, saboda haka ranar lahira wajibi ne don a saka wa wanda ya aikata alheri, sannan a azabtar da wanda ya sava, idan kuwa ha baka ba, to babu wata fa'ida ga taklifi, da kuma ya zamanto wasa da wargi kenan. Dangane da hakan Fadhil al-Miqdad na cewa: "Da a ce ranar lahira ba gaskiya ba ce to da taklifi ya zamanto mummunan abu, don kuwa taklifi wahala ce da ta cancanci sakayya, wahala ba tare da sakayya ba kuwa zalunci ne. Yana da kyau a fahimci cewa ba dole ne sakayyar ta zo a lokacin da ake aikin ba, don haka dole ne a samu wani waje wata duniya da mutum zai samu wannan sakamako na ayyukan da ya aikata. In kuwa ba haka ba, taklifi ya zamanto zalunci kenan. Wannan kuma abu ne mai muni da Allah Ya tsarkaka daga gare shi[70]".
Nasir al-Tusi cikin Ithbat Wujub al-Ma'ad yana cewa: "Wajibcin cika alqawari da hikima yana tabbatar da wajibcin tayarwa bayan mutuwa". Allamah Hilli cikin Sharhinsa na cewa: "Allah Maxaukakin Sarki ya yi alqawarin sakayya da kuma narkon azaba ga mukallafai, don haka dole ne a dawo da mutum don cika wannan alqawari na sakamako ko azaba da Ya yi[71]. Domin kuwa a fili yake cewa mutane ba za su iya samun lada ko azabar da ta dace da ayyukansu ba cikin xan wannan qaramin lokaci; misali mutanen kirkin da suka gudanar da dukkan rayuwarsu wajen ibada, yaxa kyawawan ayyuka a bayan qasa, suka jure wa wahalhalun da suke kan wannan tafarki, babu wata hukuma a faxin duniyan nan da za ta iya biyansu ladan wannan aiki nasu. Kamar yadda mujiriman da suka aikata muggan laifuffuka wajen cutar mutane, sannan kuma suka sami ni'imomi da jin daxin duniya sama da sauran mutane, mai yiyuwa ne ba za su shiga hannun mahukunta ba, ko da ma sun shigan hukumcin da za a yanke musu ba zai yi daidai da irin munin ayyukansu ba, don haka za a qyale da dama daga cikin muggan ayyukansu ba tare da an hukumta su ba, don haka babu wata hukuma a faxin duniyan nan da za ta iya qwato dukkan haqqoqin jama'a da suka take. Idan har aka ce rayuwar mutum tana qarewa ne da zarar ya mutu, wato azzalumai da waxanda aka zalunta, mutanen kirki da na banza dukkansu za su qare ne cikin qaburburansu ba tare da an saka wa mutanen kirki da kuma azabtar da na banza ba, to lalle hakan ya sava wa alqawarin adalcin Ubangiji Maxaukaki da ke bambance vangarorin biyu wajen makoma sakamako mai kyau da kuma azaba mai tsanani. Da yake ba za a iya samun hakan a wannan duniyan ba, ya zama dole a samu ranar lahira don tabbatar da adalcin Ubangiji a aikace da kuma cika wannan alqawarin gaskiya na Ubangiji na saka wa Annabawa, waliyai, shahidai da salihan bayinSa da kuma xaukan fansa a kan azzalumai da mujirimai. Ayoyin Alqur'ani mai girma sun yi bayani kan wannan dalili ta hanyoyi biyu: Ta Farko: Jaddadawa kan bambancin dake tsakanin mai savo da mai biyayya a ranar lahira don tabbatar da sakamako mai kyau ko kuma azaba, wanda hakan shi ne ma'anar adalcin Ubangiji. Allah Ta'ala Na cewa: ﴿Åöáóíúåö ãóÑúÌöÚõßõãú ÌóãöíÚðÇ æóÚúÏó Çááøåö ÍóÞøðÇ Åöäøóåõ íóÈúÏóÃõ ÇáúÎóáúÞó Ëõãøó íõÚöíÏõåõ áöíóÌúÒöíó ÇáøóÐöíäó ÂãóäõæÇú æóÚóãöáõæÇú ÇáÕøóÇáöÍóÇÊö ÈöÇáúÞöÓúØö æóÇáøóÐöíäó ßóÝóÑõæÇú áóåõãú ÔóÑóÇÈñ ãøöäú Íóãöíãò æóÚóÐóÇÈñ Ãóáöíãñ ÈöãóÇ ßóÇäõæÇú íóßúÝõÑõæäó﴾[72] "Zuwa gare Shi ne makomarku take gaba xaya, alqawarin Allah gaskiya ne, haqiqa Shi ne Yake farar da halitta sannan Ya mai da ita ranar lahira don Ya saka wa waxanda suka ba da gaskiya suka kuma yi aiki na gari da adalci; waxanda suka kafirce kuwa suna da abin sha mai quna da kuma azaba mai raxaxi saboda abin da suka kasance suna kafircewa da shi", kuma Yana cewa: ﴿ÝóÃóãøóÇ ãóä ØóÛóì ! æóÂËóÑó ÇáúÍóíóÇÉó ÇáÏøõäúíóÇ ! ÝóÅöäøó ÇáúÌóÍöíãó åöíó ÇáúãóÃúæóì !æóÃóãøóÇ ãóäú ÎóÇÝó ãóÞóÇãó ÑóÈøöåö æóäóåóì ÇáäøóÝúÓó Úóäö Çáúåóæóì !ÝóÅöäøó ÇáúÌóäøóÉó åöíó ÇáúãóÃúæóì﴾[73] "To a wannan lokaci duk wanda ya yi xagawa. Ya kuma zavi rayuwar duniya. To haqiqa jahima ita ce makoma. Amma duk wanda kuma ya ji tsoron tsayuwa gaban Ubangijinsa. Ya kuma hana zuciya bin abin da take so. To haqiqa Aljanna ita ce makoma". Ta Biyu: Inkarin cewa vangare biyu daidai suke. Allah na cewa: [74]﴿ÃóÝóãóä ßóÇäó ãõÄúãöäðÇ ßóãóä ßóÇäó ÝóÇÓöÞðÇ áÇó íóÓúÊóæõæäó﴾ "Yanzu wanda ya zamanto mumini ya zama kamar wanda ya kasance fasiqi? Ai ba za su zama daidai ba", kuma Yana cewa: ﴿Ãóãú äóÌúÚóáõ ÇáøóÐöíäó ÂãóäõæÇ æóÚóãöáõæÇ ÇáÕøóÇáöÍóÇÊö ßóÇáúãõÝúÓöÏöíäó Ýöí ÇáÃóÑúÖö Ãóãú äóÌúÚóáõ ÇáúãõÊøóÞöíäó ßóÇáúÝõÌøóÇÑö﴾[75] "Shin za mu mayar da waxanda suke ba da gaskiya suka yi ayyuka nagari kamar masu varna a bayan qasa, ko kuma za mu mayar da masu tsoron Allah kamar lalatattu?. Kamar yadda kuma a wani wajen Yake cewa: ﴿Ãðãú ÍóÓöÈó ÇáøóÐöíäó ÇÌúÊóÑóÍõæÇ ÇáÓøóíøöÆóÇÊö Ãøä äøóÌúÚóáóåõãú ßóÇáøóÐöíäó ÂãóäõæÇ æóÚóãöáõæÇ ÇáÕøóÇáöÍóÇÊö ÓóæóÇÁ ãøóÍúíóÇåõã æóãóãóÇÊõåõãú ÓóÇÁ ãóÇ íóÍúßõãõæäó﴾[76] "Ko kuwa waxanda suka aikata munanan ayyuka suna tsammanin za Mu sanya su ne kamar waxanda suka ba da gaskiya suka kuma yi kyawawan ayyuka? Su zama xaya cikin rayuwarsu da mutuwarsu! idan haka suke zato to tir da abin da suke hukumtawa". Yana kuwa cewa: ﴿Åöäøó áöáúãõÊøóÞöíäó ÚöäÏó ÑóÈøöåöãú ÌóäøóÇÊö ÇáäøóÚöíãö ! ÃóÝóäóÌúÚóáõ ÇáúãõÓúáöãöíäó ßóÇáúãõÌúÑöãöíäó ! ãóÇ áóßõãú ßóíúÝó ÊóÍúßõãõæäó﴾[77] "Haqiqa masu tsoron Allah suna da aljannonin ni'ima a wajen Ubangijinsu. Yanzu za Mu sanya musulmi kamar kangararru? Me ya sa me ku ne, ya ya kuka yi irin wannan hukumci". [1] . Suratul Baqara; 2:177. [2] . Suratul Ma'ida; 5:69. [3] . Suratu Al Imrana; 3:9. [4] . Suratun Nisa'i; 4:87. [5] .Suratun Nahl; 16:38 [6] . Suratus Saba'; 34:3. [7] . Za mu taqaita ne kawai da ambaton ayoyin da suka yi Magana kan wannan batu, mai karatu yana iya komawa ga littafin Al-Raj'ah da wannan cibiya ta buga shafi na 18 zuwa 26 don ganin hadisan da suka zo cikin tafsirin waxannan ayoyi. [8] . Suratul Baqara; 2:243. [9] . Suratul Baqara; 2:259. [10] . Suratul Baqara; 2:55-56. [11] . Suratul Baqara; 2:72-73. [12] . Suratul Baqara; 2:260. [13] . Suratul An'am; 6:130. [14] . Suratuz Zumar; 39:71. [15] . Suratu Nuh; 71:17-18. [16] . Suratul An'am: 6:154. [17] . Suratu Ghafir: 40:27. [18]. Suratu Al Imrana; 3:55. [19] . Suratu Yasin; 36:12. [20] . Suratuz Zukhruf; 43:80 [21] . Suratu Qaf; 50:16-18, sannan kuma a duba Suratu Yunus; 10:21, da Suratul Isra' 17:14 da Suratul Qamar 45:52 da 53 da kuma Suratul Infixar 82:10-12. [22] . Suratul Jasiyya; 45:28-29. [23] . Suratul Kahfi; 18:49. [24] Suratul Jasiyya; 45:24. [25] . Suratun Najm; 53:28. [26] . Suratul Naml; 27:64. [27] . A nan gaba za mu ambato wasu shakku da ake gabatarwa da kuma raddinsu a fasali na uku. [28] . Suratu Yasin; 36:78-79. [29] . Al'I'itiqad na Saduq: 64, Bihar al-Anwar na Majlisi 7:47/31 da 103/13, ayar kuma tana cikin Suratu Luqman: 31:28. [30] . Bihar al-Anwar 7:40/11. [31] . Littafin Nahjul Balagah huxuba ta 109. [32] . Nahjul Balagah huxuba ta 102. [33] . Biharul Anwar 7:42/14, da Haqqul Yaqin na Abdullah Shibr 2:54. [34] . Kashful Murad na Allamah Hilli: 424. [35] . Suratul Hajj; 22:5-6. [36] . Suratur Rum 30:27. [37] . Suratur Rum 30:11 [38] . Suratul Isra': 17:51. [39] . Suratul Anbiya'; 21:104. [40] . Dubi Suratur Rum 30:19, al-Fatir 35:9, al-Fusilat 41:39, al-Zukhruf 43:11 da al-Kaf 50:11. [41] . Suratur Rum: 30:50. [42] . Suratul A’araf: 7:57. [43] . Tafsir al-Mizan na Allamah Tabataba'i, Mu'assasar al-A'alami 16:203 da 17:21. [44] . Suratu Nuh; 71:17-18. [45] . Dubi Suratu Yunus; 10:4 da 34, Suratul Naml: 27:64, Suratur Rum; 30:11, Suratu Nuh; 71:17-18 da Suratul Buruj 85:13. [46] . Suratul Ankabut; 29:19-20. [47] . Suratul Mulk 67:14. [48] . Suratul Waqi'a; 56:57. [49] . Suratul Waqi'a; 56:62. [50] . Suratu Yunus; 10:34. [51] . Suratul Baqara; 2:28. [52] . Suratu Qaf; 50:15 [53] . Suratu Luqman; 31:28. [54] . Suratul Isra'; 17: 98-99. [55] . Suratu Yasin; 36:81-82. [56] . Suratul Ahqaf; 46:33. [57] . Suratu Ghafir; 40:58. [58] . Suratun Nazi'at; 79:28:30. [59] . Suratul Isra': 17:49-51. [60] . Dubi Al-Mizan na Allamah Tabataba'i 13:116. [61] . Suratul Muminun; 23:115. [62] . Suratu Sad; 38:27. [63] . Suratul Qiyama; 75:36. [64] . Suratul Ankabuti; 29:64. [65] . Suratur Rum; 30:8. [66] . Suratud Dukkhan; 44:38-40. [67] . Suratul Mulk; 67:2. [68] . Suratul A'araf; 7:168. [69] . Suratul Anbiya': 21:35. [70] . Al-Na'fi' Yawm al-Hashr fi Sharh Bab al-Hadi Ashar na Fadhil Miqdad: 86-87 da makamancin hakan cikin Manahij al-Yaqin fi Usul al-Din: 337 Tahqiqin Muhammad Ridha al-Ansari. [71]. Kashf al-Murad fi Sharh Tajrid al-I'itiqad / Allama Hilli: 431. [72] . Suratu Yunus; 10:4. [73] . Suratun Nazi'at; 79:37-41. [74] . Suratus Sajda; 32:18. [75] . Suratu Sad; 38:28. [76] . Suratul Jathiya; 45:21. [77] . Suratul Qalam; 68:34-36. |
||||||||||||||||||||||||