FASALI NA HUXU

 

 

ZANGO-ZANGO NA TASHIN QIYAMA

bullet

BAHASI NA FARKO: Mutuwa da Tsananinta

bullet

BAHASI NA BIYU: Barzahu Da Azabar Da Ke Ciki

bullet

BAHASI NA UKU: Sharuxxan Qiyama

bullet

BAHASI NA HUDU: Abubuwan Da Za Su Faru Ranar Qiyama

bullet

BAHASI NA BIYAR: Yan Aljanna Da  Yan Wuta


 

ZANGO-ZANGO NA TASHIN QIYAMA

 

Daga mutuwa zuwa lokacin haxuwa da Ubangiji, xanAdam zai tsallake wasu matakai masu wahala da firgitarwa. Wahalar ta kai wahala da za a iya kwatantata da mutuwa duk da irin wahala da firgitan dake tattare da ita (mutuwa), za a ga cewa ba a bakin komai take ba.

Imam Sadiq (a.s) yana cewa: Tsakanin duniya da lahira akwai shingaye guda dubu, mafi sauqinsu ita ce mutuwa([1]).

Abin dake biye, taqaitaccen bayani ne cikin bahasi biyar kan matakan da mutum ke tsallakewa a hanyarsa ta zuwa lokacin da za a tashe shi:

 

 

Bahasi Na Farko: Mutuwa da Tsananinta:

 

Mutuwa ita ce masaukin farko na isa ga tashin qiyama, sannan kuma zangon farko ta tayarwar lahira. Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Mutuwa qiyama ce, idan xayanku ya mutu qiyamarsa ta tashi, inda zai ga abin da yake da shi na alheri ko sharri([2]). Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Mutuwa qofa ce ta lahira([3]).

Abin nufi da mutuwa shi ne karvar rai da katse alaqarsa da jiki, ko kuma tashi daga rayuwar duniya zuwa ga rayuwar lahira, wanda hakan na daga cikin ayyukan Ubangiji. Allah Maxaukakin Sarki na cewa:

     ﴿

Shi ne Wanda ke rayarwa kuma Yana kashewa. To, idan Ya hukumta wani alamari, to, Yana cewa kawai gare shi, ka kasance, sai ya kasance([4]).

 Allah Maxaukakin Sarki Ya xora nauyin xaukan rai kan Malaikan mutuwa da zai xauki rai da umarninSa

﴿  

Ka ce, Malaikin mutuwa wanda aka wakkala a gare ku, shi ne ke karvar rayukanku. Sannan zuwa ga Ubangijin-ku ake mayar da ku([5]).

Ya kan xaukaka wasu daga Malaikun da ke zartar da umarninSa, sai ayyukansu ya zama kamar aikinSa

﴿

Har idan mutuwa ta je wa xayanku, sai manzanninMu su karvi ransa, alhali su, ba su yin sakaci([6]),

 Allah Maxaukakin Sarki ne ke karvan rayuka ta hannun malaikan mutuwa

﴿

Allah ne ke karvar rayuka a lokacin mutuwarsu([7]).  

Don haka ne cikin wani hadisi Imam Sadiq (a.s) yake cewa: Allah Maxaukakin Sarki Ya kan sanya wa Malaikan mutuwa mataimaka daga cikin Malaiku, suna xaukan rayuka kamar yadda sufeto janar na yan sanda yake da mataimaka cikin mutane, masu gudanar da ayyukansa, Malaiku suna karvar rayukan mutane sannan Malaikan mutuwa ya karvesu daga gare su ya haxa da waxanda ya zare da kansa. Daga bisani sai Allah Taala Ya karvi rayukan daga hannun Malaikan mutuwa([8]).

 

Wahalhalun Mutuwa:

 

 Mutuwa lamari ne mai tsoratarwa dake kawo qarshen rayuwar mutum a duniya, da ake ganinta a matsayin wata hanya da babu makawa sai an isa gare ta:

﴿

Ka ce, Lalle mutuwar nan da kuke gudunta, to, lalle ita mai haxuwa da ku ce saan nan kuma ana mayar da ku zuwa ga Masanin fake da bayyane, domin Ya ba ku labari ga abin da kuka kasance kuna aikatawa([9]).

Ayoyi da hadisai masu yawa sun yi bayani kan siffofin mutuwa da ababen firgitarwa dake tattare da ita. Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Mutuwa tana da abin tsoron da tsananinsa ya wuce siffantawa kuma hankulan mutanen duniya sun yi kaxan su fahimce shi([10]). Yanzu bari mu kawo wasu daga cikin waxannan ababen firgita cikin Alqurani mai girma da hadisai:

 

1- Gargara:

 Shi ne zuwan Malaikan mutuwa ko mataimakansa na daga Malaikun rahama ko na azaba don xaukan ran mutumin da ya kawo gargara. Wannan yanayi ne mai firgitarwa saboda irin tsoro da damuwar da take shiga zuciyar wanda ke halin gargara a lokacin da ya ga Malaika. Imam Zainul Abidin (a.s) yana cewa: Mafi tsananin lokuta ga xanAdam uku ne: Lokacin da ya ga Malaikan mutuwa, lokacin da za a tayar da shi daga kabari da kuma lokacin da zai tsaya gaba ga Allah Maxaukakin Sarki, ko dai zuwa aljanna ko kuma zuwa wuta([11]).

Firgicin lokacin gargara ya bambanta daga mutum zuwa mutum, tsanani ko sauqinsa gwargwardon halayya da ayyukan mutum ne. Muminai suna cikin farin ciki da annashuwa yayin da suke gamuwa da Malaiku, saboda nasara ta har abada da suka samu. Allah Taala Na cewa:

 ﴿    

Waxanda malaiku suke karvar rayukansu suna masu jin daxin rai, malaikun suna cewa Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa([12]),

 babu wani bambanci na lokaci tsakanin mutuwarsu da busharar niima saboda babu axafi tsakanin jumlolin biyu, wato mutuwa ce tare da busharar niima.

Wasu ayoyin kuma suna magana kan azaba da halin firgita da kafirai da azzalumai za su fuskanta sakamakon damuwar zuciyar da suke tare da ita saboda tsoron azaba. Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

﴿ !

Kuma da ka gani, a lokacin da malaiku suke karvar rayukan waxanda suka kafirta, suna dukar fuskokinsu da xuwawunsu, kuma suna cewa: Ku xanxani azabar Gobara. Wancan saboda abin da hannayenku suka gabatar ne([13]).

 

2- Mayen Mutuwa:

 Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

 ﴿   

Kuma mayen mutuwa ya je da gaskiya. Wannan shi ne abin da ka kasance daga gare shi kana bijirewa([14]).

 Abin nufi da mayen mutuwa, shi ne damuwar da take rufe mutumin da ya kai gargara na daga firgicin mutuwa, nutsewa cikin xacin mutuwa da zafinta da kasancewa da zai yi cikin tsananin zafi da wahala, maqura da wahalar fitar rai([15])

Manzon Allah (s.a.w.a) na cewa: mafi sauqin fizgar rai, yana a matsayin sara xari da takobi([16]). Ana iya ganin alamar wannan magagi da wahala mai tsanani na fitar rai a harshen mutumin da ya kai gargara, ganinsa da fuskansa, fatan bakinsa na karkarwa, numfashinsa na hauhawa, da canjin launin fatarsa, da mutuwar gavovinsa a hankali a hankali lokacin da tafin qafarsa zai yi sanyi, sai cinyansa, maye bayan maye, damuwa bayan damuwa, har lokacin da rai zai zo maqoshi, sai ganinsa ya yanke daga duniya, yankewar da babu komowa:

﴿ !   !   !   !

To, don me idan rai ya kai ga maqoshi? (kusa da mutuwa). Alhali kuwa ku, a lokacin nan, kuna kallo. Kuma Mu ne mafi kusanta gare shi daga ku, to, amma ku ba ku gani. To don me in dai kun kasance ba waxanda za a yi wa sakamako ba? Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance masu gaskiya([17]). Hakan tare da yanayin damuwa da mutumin da ya kawo gargarar yake fuskanta tun farko.

Yayin da yake siffanta wannan yanayi, Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Magagin mutuwa da baqin cikin kuvucewar (duniya) sun rufe su, sai gavovinsu suka yi rauni launukansu suka sauya, daga nan sai mutuwa ta qara shigarsu, ta raba su da qarfinsa na magana duk kuwa da cewa yana tsakanin danginsa, yana kallo da idanuwansa, yana ji da kunnuwansa, alhali yana cikin hankalinsa, yana tunanin yadda ya sarrafa rayuwarsa da kuma kan me ya qarar da lokacinsa! .. daga nan zai ciji yatsansa yana mai nadama kan abin da aka bayyanar masa na ayyukansa lokacin mutuwarsa. Zai qyamaci abubuwan da yake hanqoron samunsu lokacin rayuwarsa, zai yi burin da ma a ce wanda ke masa hassada da qoqarin hana shi samunsu ya yi nasara da samunsu! Haka mutuwa za ta ci gaba da kusato shi da shiga jikinsa har kunnensa ma ya kasance kamar harshensa (ba ya aiki), sai ya kasance cikin iyalansa ba ya magana da harshensa, ba ya ji da kunnuwansa, zai ci gaba da kallon fuskokinsu kawai, yana kallon motsin harsunansu amma ba ya jin abin da suke faxi. Daga nan sai mutuwa ta ci gaba da matsawa kusa da shi, sai a xauke ganinsa kamar yadda aka xauke jinsa, sai ruhi ya fice daga jikinsa, sai ya zamanto gawa tsakanin iyalansa, za su ji kaxaitaka daga gare shi, sai su nesance shi. Ba zai kasance tare da masu juyayi ba kamar yadda ba zai iya amsa wa mai kira ba. Daga nan sai su xauke shi zuwa wani xan qarami waje cikin qasa, su miqa shi ga ayyukansa, shi kenan sai su katse ziyartarsa([18]).

Daga cikin abubuwan da suke sauqaqa irin wannan mummunan hali na firgita da damuwa su ne wasu kyawawan ayyuka irinsu sada zumunci da bin iyaye, saboda abin aka ruwaito daga Imam Sadiq (a.s) inda yake cewa: Wanda yake son a sauqaqa masa mayen mutuwa, to ya kasance mai sada zumunci ga danginsa, kuma mai bin iyayensa.([19]).

 

3- Xaukan Rai:

 Ruwaya ta bayyana cewa tsanani ko sauqin xaukan (fitar) rai yana bambanta tsakanin mutane gwargwadon xabiu da ayyukansu. Muminan da imani ya ratsa zukatansu, waxanda suka kame gavavunsu daga muggan ayyuka, kuma suke farin cikin gamuwa da Ubangijinsu, Malaikun rahama za su xauki rayukansu cikin sauqi da tausasawa. Su kuwa kafirai waxanda duniya ta ruxe su da ababen ruxinta, suka nutse cikin fajirci da muggan ayyuka da kau da kai ga barin gamuwa da Allah, Malaikun azaba za su xauki rayukansu cikin tsanani da yanayi mai muni.

Imam Abu Jaafar al-Baqir (a.s) yana cewa: Alamar mumini, idan mutuwa tazo masa fuskarsa takan yi haske (fari) sama da launinsa, goshinsa ya kan yi zufa, ya gudana daga idonsa kamar hawaye, hakan ya kan zamanto alamar fitar rai. Shi kuwa kafiri ransa ya kan fita ne ta bakinsa kamar kumfar bakin raqumi.([20]).

Sai dai ruwayoyi sun nuna cewa waxannan ba dole ne su kasance a koda yaushe ba. Don kuwa ba wai duk wata wahala yayin mutuwa ne take nufin azaba ba, kamar yadda ba dukkan sauqi yayin mutuwa ne ya ke nufin sakamako mai kyau ba. Mai yiyuwa wahala ga mumini ta kasance kaffara ga zunubansa, kamar yadda sauqi ga kafiri yana iya kasancewa sakamako ne na ayyukan alherin da ya aikata([21]). An tambayi Imam Sadiq (a.s) cewa: Ya ya muke ganin kafiri na samun sauqi wajen cire rai, ana xaukan ransa alhali yana magana da dariya, kamar yadda ake samun hakan ma wajen mumini. Sannan kuma akwai muminai da kafirai da suke shiga cikin wahala yayin fitan rai? Sai ya ce: Sauqi ga mumini (ba wai wani abu ba ne) face gaggauta sakamakon (alheri) gare shi ne, wahala kuma tsarkakewa ce gare shi daga zunubi, don ya koma lahira tsabtatacce, don cancantar sakamako na har abada, ba tare da wani abu ya hana hakan ba. Sauqi ga kafiri kuwa (ba komai ba ne) face sakamako ne ga ayyukansa na alheri a duniya, don ya koma lahira ba shi da komai face abin da zai tabbatar masa da azaba. Tsanani ga kafiri mafarin azabar Allah ne bayan qarewar kyawawan ayyukansa. Saboda Allah adali ne ba Ya zalunci([22]).

 

4- Shiga Rayuwar Lahira:

Lokacin da mutum ya xandani xacin mutuwa, rai ya kama hanyar fita, a lokacin abubuwan da ba su fito masa fili ba lokacin rayuwarsa za su fito masa, kamar yadda abubuwa suke fitowa fili ga mutumin da ya tashi daga barci waxanda a da suka vuya masa lokacin yana barci, Mutane suna cikin barci ne, sukan farka ne kawai bayan mutuwarsu, su ga abin da waxanda suke raye basu gani ba. Allah Maxaukaki Na cewa:

   ﴿

(Sai a ce masa), Lalle ne, haqiqa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, saboda haka ganinka a yau, mai kaifi ne([23]),

 daga cikin abubuwan da mutum ya kan fuskanta yayin mutuwa, kamar yadda aka ruwaito cikin hadisai, har da:

 

a) Makomarsa a Aljanna ko wuta:

 Manzon Allah (s.a.w.a) na cewa: Idan xayanku ya mutu za a nuna masa makomarsa, idan xan aljanna ne, to aljanna, idan kuma xan wuta ne, to wuta, za a ce masa: Wannan ita ce makomarka har lokacin da Allah Zai tura ka cikinta ranar lahira([24]).

Amirul Muminina (a.s) cikin wasiqarsa ga Muhammad bn Abubakar yayin da ya naxa shi gwamnan Masar, yana cewa: Babu wani mutum daga cikin mutane da rai zai fita daga jikinsa face har sai ya san wani gida daga gidaje biyun nan zai shiga, aljanna ko wuta, shin maqiyin Allah ne ko masoyinSa. Idan masoyin Allah ne za a buxe masa qofofin aljanna, a buxe masa hanyoyinta, inda zai ga abubuwan da Allah Ya tanadar masa cikinta, zai rabu da duk wani aiki, an kuma xauke masa duk wani nauyi. Idan kuwa maqiyin Allah ne, za a buxe masa qofofin wuta, za a buxe masa hanyoyinta, ya ga abin da Allah Ya tanadar masa, ya fuskanci duk wahala dake ciki, ba shi da wani farin ciki. Dukkan hakan ya kan faru ne yayin mutuwa, daga nan zai ga yaqini([25]).

 

b) Misaltuwan Dukiya, Yaya da Ayyuka:

 Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Idan mutum ya iso ga ranarsa ta qarshe a duniya, wacce ita ce ta farko a lahira, za a nuna masa dukiyarsa, yayansa da aikinsa. Zai dubi dukiyarsa ya ce: Wallahi na kasance mai nuna kwaxayi kan ki matuqa, to me kika tanadar min? Sai ta ce masa: Ka sayi likkafaninka da ni. Sai ya ci gaba da cewa: Sai ya juya wajen yayansa ya ce: Wallahi na kasance mai qaunarku iyakacin qauna, kuma ina ba ku kariya iyakacin kariya, me kuka tanadar min? Sai su ce: Za mu raka ka zuwa kabarinka da rufe ka. Sai ya dubi aikinsa ya ce: Wallahi ka kasance abu mai nauyi gare ni, ni na kasance mai qasqantar da kai gare ka, me ka tanadar min? Sai ya ce: Zan kasance maka abokin zaman cikin kabari da ranar da za a tashe ka, har a gabatar da ni da kai gaban Ubangijinka([26]).

 

c) Ganin Annabi da Imamai (a.s):

  Sheikh al-Mufid yana cewa: Wannan lamari ne da Shia Imamiyya suka tafi a kai, an samo hadisai daga Imam Baqir da Sadiq (a.s), kamar yadda kuma aka ruwaito daga Amirul Muminina (a.s) cikin wasu baitukan waqe yana ce ma Harith al-Hamdani:

 

Ya Harith Hamdani duk wanda ya mutu zai ganni

Mumini ne ko munafuki a baya

Ya sanni da kansa kuma na sanshi

Shi kansa da sunansa da abin da ya aikata.

 

Ibn Abil Hadid ya kawo baitukan waqe shida daga cikinta yayin da Amirul Muminina (a.s) yake cewa: Ku da kun ga abin da waxanda suka mutu suka gani da kun yi raki da kuma kun firgice, da kuma kun ji kun bi. Sai dai abin da suka gani a shamake yake gare ku, kuma nan kusa za a kawar da shamakin.

Ibn Abil Hadid na cewa: Mai yiyuwa ne yana nufin abin da yake faxi game da kansa, cewa mutum ba ya mutuwa har sai ya ganshi a gabansa.

Daga nan sai ya kafa hujjar ingancin hakan da cewa: Wannan ba abin inkari ba ne, in har da gaske ya faxi hakan ga kansa. Cikin Alqurani akwai abin da ke nuni da cewa wani daga cikin maabuta littafi ba ya mutuwa har sai ya gaskata Isa xan Maryama (a.s) wato faxinSa Taala:

  ﴿   

Kuma babu kowa daga Mutanen Littafi, face lalle yana imani da shi a gabanin mutuwarsa, kuma a Ranar Qiyama yana kasancewa mai shaida, a kansu([27]).

 Da dama daga cikin malaman tafsiri suna cewa: Maanar hakan shi ne cewa: duk wani bayahude da sauran maabuta littafi da suka gabata, kafin mutuwarsa, lokacin da ya kai gargara, zai ga al-Masihu (a.s) a gabansa, wanda bai yi imani da shi ba a lokacin da yake mukallafi sai ya yi yanzu([28]).

To sai dai ba a wajabta mana sanin yadda ganin zai kasance da kuma yin bincike kan hakan ba. Imani dashi da sauran batutuwan gaibi irinsa ya wadatar saboda sun zo cikin ingantattun ruwayoyi daga gare su (a.s).

 

 

BAHASI NA BIYU: BARZAHU DA AZABAR DA KE CIKI:

 

Maanar Barzahu:

 Barzahu Cikin Lugga: Shamaki tsakanin abubuwa biyu([29]), wata duniya ce dake tsakanin mutuwa da qiyama, ana niimta mamaci ko azabtar da shi har lokacin tashin qiyama([30]). Allah Maxaukaki Na cewa:

 ﴿

Alhali kuwa a baya gare su akwai wani shamaki (barzakh) har ranar da za a tayar da su([31]).

 Wannan aya a fili tana nuni da samuwar wata rayuwa ta tsakiya tsakanin rayuwar duniya da ta lahira.

Kan tafsirin ayar, Imam Sadiq (a.s) yana cewa: Barzahu: (na nufin) kabari inda ake saka wa mutum ko kuma azabtar da shi tsakanin duniya da lahira([32]).

 

Wahalhalun Barzahu:

 Kamar yadda muka sani, rayuwar lahira ta kan fara ne daga mutuwa, ta mutuwa ne ake haihuwar mutum a rayuwar lahira. Bayan wahalhalun mutuwa sai kuma yanayin rayuwar kabari, kamar haka:

 

1- Azabar Kabari da Duhunsa:

 Kabari dai gida ne mai firgitarwa daga cikin gidajen dake hanyar zuwa tashin qiyama, inda za a bisne mamaci cikin qaramin rami mai duhu ba tare da kowa ba in ba malaikan rahama ko na azaba ba, sannan ba tare da wani abokin zama ba in ba ayyukan da ya aikata ba.

Amirul Muminina (a.s), cikin wasiqar da ya aike wa mutanen Masar, yana cewa: Ya ku bayin Allah, abin da ke bayan mutuwa ga wanda ba a gafarta masa ba yafi mutuwa tsanani; don haka ku tsoraci matsin kabari da duhu da kaxaitakansa. A kowace rana kabari ya kan ce: Ni ne gidan baqunta, ni gidan qasa (turvaya) ne, ni gida ne na tsoro, ni gidan tsutsa da .([33]).

A nan ne mutum ya kan koma cikin qasa, daga xan gida zuwa baqo, daga haske zuwa duhu, daga walwalar rayuwa da jin daxi zuwa matsin kabari da tashin hankalin dake cikinsa. Alamarsa za ta katse, ambatonsa zai gushe, siffa za ta canza, jiki zai yi rauni sannan gavovi su yayyanke.

Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Sau nawa qasa take cin mutum mai maxaukakin jiki, mai kyakkyawan launi alhali kuwa a duniya yana cikin wadata da jin daxi da girmamawa. Ya kan sa ran komawa ga jin daxi a lokacin baqin ciki, idan kuwa wata musiba ta same shi ya kan yi gaggawa wajen neman yayewarta yana rowar walwalarsa, yana qanqamo da wasanninsa.([34]).

2- Matsin Cikin Kabari: Ya zo cikin ruwaya cewa mamaci ya kan fuskanci matsi cikin kabari, qasa za ta matse shi har naman jikinsa tarwatse, da markaxewar kwanya hakan zai kasance ne sakamakon annamimanci da muggan xabia da muamala ga dangi, da yawan magana da rashin kula da tsarki. Da wuya ake samun wanda zai tsira in ba wanda ya cika sharaxin imani ba da kuma kai wa daraja ta kamala.

Abu Basir na cewa: Na ce wa Abu Abdillah: Shin akwai mai tsere wa matsewar kabari? Sai ya ce: Muna neman tsarin Allah daga ita. Kaxan ne masu tsira daga matsewar kabari([35]).

Akwai wata ruwaya da ke nuni da wahalan kabarin da sahabin nan Saad bn Muaz ya fuskanta, kamar yadda ya zo cikin ruwayar cewa lokacin da aka xauko shi kan makara, Malaiku suna raka shi zuwa kabari, Manzon Allah (s.a.w.a) na biye da shi ba tare da takalmi ko mayafi ba har ya bisne shi a kabari, sai mahaifiyar Saad ta ce: Ya Saad, barkanka da aljanna. Sai Manzo (s.a.w.a) ya ce: Ya Umma Saad, dakata kada ki xorawa Ubangijinki wani aiki, don kuwa Saad yana fuskantar matsin qasa. Yayin da aka tambaye shi dalilin hakan, sai ya ce: Haqiqa ya kasance mai munana muamalarsa ga iyalansa([36]).

Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Matsin cikin kabari ga mumini kaffara ce gare shi kan wasan da yayi da niima[37].

 

3- Tambayar Munkar da Nakir:

 A duniyar barzahu Allah Maxaukakin Sarki zai saukar da Malaiku guda biyu ga mamaci yayin da yake kabari, su ne kuwa Munkar da Nakir, inda za su tambaye shi kan Ubangijin da ya kasance yana bautawa, da addinin da ya kasance yana bi, da Annabin da aka aiko masa, da littafin ya kasance yana karantawa, da Imamin da ya kasance yana bi, da yadda ya gudanar da rayuwarsa, da yadda ya samo dukiyarsa da yadda ya kashe ta. Idan ya amsa daidai, sai su tarbe shi da faraa, da masa bushara da aljanna da yardar Ubangiji, su faxaxa masa kabarinsa. Idan kuwa yayi karkarwa wajen amsa ko kuma bai amsa daidai ba, ko kuma bai san ma abin da zai faxi ba, Malaiku za su yi masa bushara da ruwan zafi da wuta.

Ingantattun ruwayoyi daga Maaiki (s.a.w.a) da Ahlulbaiti (a.s) da kuma ittifaqin musulmi([38]) sun tabbatar da hakan ta yadda har ya zamanto daga cikin laluran addini.

Imam Sadiq (a.s) yana cewa: Wanda ya yi inkarin abubuwa uku, ba ya daga cikin Shianmu: miiraji, tambayar cikin kabari da kuma ceto([39]).

 

4- Azaba da kuma Niimar Kabari:

 Shi ne azaba ko kuma kyakkyawan sakamako da ake samu a barzahu, wanda lamari ne da babu kokwanto cikin yiyuwarsa. Ayoyin Alqurani da hadisan Maaiki da Ahlulbaiti (a.s) sun tabbatar da hakan, kamar yadda dukkan musulmi, na farko da na baya sun tafi kan hakan([40]).

 

Dalilai Daga Alqurani:

 Akwai ayoyin Alqurani da dama da suka yi ishara ga azabar kabari ko kuma niimar da ke cikinsa, a baya mun kawo wasu daga cikinsu, yanzu kuma ga wasu biyu daga ciki:

1- Faxin Allah Taala dangane da mutanen Firauna:

﴿  !

Kuma mummunar azaba ta tabbata ga mutanen Firauna. Wuta, ana gitta su a kanta, safe da maraice, kuma a ranar da Saa take tsayuwa, ana cewa: Ku shigar da mutanen Firauna a mafi tsananin azaba([41]).

 Wannan aya ce da a sarari take magana kan wannan batu, saboda axafi da wa yana tabbatar da bambancin abu da abin da aka yi wa axafin kansa. Da farko an ambaci cewa za a gabatar da su ga wuta safiya da marece, sannan sai aka haxa shi da abin da zai faru ranar lahira. Don haka aka amabaci na farko da gabatar da su (gittawa), na biyun kuma da shigarwa([42]).

An ruwaito Imam Sadiq (a.s) kan tafsirin ayar yana cewa: Idan ana azabtar da su cikin wuta ne da safiya da marece, to kenan tsakanin waxannan lokuta suna cikin niima. Aa, haka ya kan faru ne a barzahu kafin ranar tashin qiyama, ashe ba ku ji faxinsa Maxaukaki cewa: Kuma a ranar da Saa take tsayuwa, ana cewa: Ku shigar da mutanen Firauna a mafi tsananin azaba ba?([43]).

 2- Faxin Allah Maxaukakin Sarki cewa:

﴿

Kuma wanda ya bijire daga ambatonNa, to, lalle ne rayuwa mai qunci ta tabbata a gare shi, kuma Muna tayar da shi a Ranar Qiyama yana makaho([44]).

 Da dama daga cikin malaman tafisiri suna cewa:maanar rayuwa mai wahala shi ne azabar kabari da hasara a rayuwar barzahu. Saboda ambaton tayarwa da aka yi kana aka haxa ta da wawun, wanda hakan na tabbatar da bambanci. Ba yadda za a fassara hakan da mummunan yanayi a duniya, don kuwa da dama daga cikin kafirai sun fi muminai jin daxi a duniya, ba tare da wahala ba([45]).

Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Ku sani cewar maanar rayuwa mai qunci da ta zo cikin faxinSa Maxaukaki ﴿, ita ce azabar kabari([46]).

 

Dalilai Daga Sunna:

 Akwai ruwayoyi da dama daga vangarorin nan biyu (na musulmi)([47]) da suka tabbatar da batun azaba ko sakamako mai kyau a kabari, da kuma qarin bayani kan hakan. A baya yayin bayani kan tajarrudin ruhi, mun kawo wasu daga cikinsu, to sai dai duk da haka bari mu qara da wasu guda uku:

1-     Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Kabari, ko dai rami ne daga ramukan wuta ko kuma dausayi daga dausayan Aljanna([48]).

2-     Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Za a tura tinnin[49] guda casain da tara kan kafiri, su yayyaga namansa, su kakkarya qasusuwansa. Za su ci gaba da zuwa masa har ranar da za a tashe shi. Da guda daga cikin waxannan halittu zai hura qasa, to da babu wani abin da zai sake tsirowa har abada.([50]).

3-     An ruwaito Imam Ali bn Husain Zainul Abidin (a.s) game da faxin Allah:

 ([51]) ﴿ 

 yana cewa:

Shi ne kabari, suna da wata rayuwa mai tsanani a cikinsa. Na rantse da Allah (kabari) dausayi ne daga dausayan aljanna ko kuma rami daga ramukan wuta([52]).

Shakku: Akwai wasu batutuwa da shubuhohi da suke tasowa kan azabar kabari ko kuma niimar da ke cikinsa, da dama daga cikinsu suna tasowa ne kan yadda hakan zai kasance. Sai dai yana da kyau a fahimci cewa ba a wajabta mana kutsawa cikin neman bayani dalla-dalla kan hakan ba, abin da aka buqace mu mu yi shi ne imani da shi a yanayi na gaba xaya da imani da samuwa da kuma yiyuwar hakan, da tabbatarsa ta hanyar kalaman Maasumai (a.s). Haka lamarin yake kan dukkanin alamurran gaibi, don lamurra ne na duniyar malakuti, da hankulanmu ba za su riske su ba balle mariskanmu na zahiriYanzu bari mu kawo muhimmai daga cikin waxannan shubuhohi kan rayuwar barzahu, da kuma amsa su ta hanyar dogaro da ayoyi da hadisai.

1- Idan jiki shi ne hanyar isar azaba ga ruhi, to ya ya za a azabtar da ruhi ko niimtar da shi alhali kuwa ya bar jiki, ya lalace?

Amsa: Ruwayoyi sun tabbatar da cewa Allah Maxaukakin Sarki Yana rayar da mutum bayan mutuwarsa don yi masa tambayoyi, haka rayuwarsa za ta ci gaba, ko niima idan ya cancanci hakan ku kuma azaba idan hakan ya cancanta. Za a yi hakan ko dai ta hanyar rayar da jikinsa na duniya ko kuma haxa ruhinsa ga wani jiki na duniyar misali([53]). Yanzu bari mu yi bayanin dukkan alamurran biyu tare da hujjojinsu daga hadisai.

 

Na Farko: Rayar da Jiki Na Duniya:

Wato Allah Taala Yana dawo da ruhi zuwa ga jikin mamaci cikin kabarinsa, kamar yadda zahirin da dama daga cikin hadisai yake nunawa. Daga cikinsu akwai ruwayar da aka ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Akan dawo da ruhinsa ga jikinsa, daga nan Malaiku guda biyu za su zo su zaunar da shi([54]).

Sannan an ruwaito Abi Jaafar al-Baqir (a.s) yana cewa: Idan mutum ya shiga kabarinsa, za a dawo masa da ruhinsa cikin jikinsa, Malaiku (biyu) za su taho don masa tambayoyi([55]).

Daga Abu Abdillah al-Sadiq (a.s) yana cewa: Daga nan Malaikun kabari (biyu), waxanda su ne Munkar da Nakir, za su shigo masa, su tashe shi kuma su mayar masa da ruhi([56]).

Saboda haka ne aka ce: Rayuwar kabari, rayuwa ce ta barzahu, babu wata alamar rayuwa in banda wahala ko jin daxi, wato dawowar ruhi ga jiki na wani yanayi ne mai rauni, don kuwa Allah Ya kan dawo wa mamaci da wani nau'i na rayuwa gwargwadon yadda zai iya jin zafin azaba ko kuma jin daxin niimar da aka tanadar masa([57]).

 

Na Biyu: Haxuwa da Jiki Irin Na Misal:

 Ya zo cikin ruwaya cewa Allah Maxaukakin Sarki Yana zaunar da ruhi cikin wani jiki na misal a duniyar barzahu kamar jiki na duniya don tambaya da sakamako mai kyau ko azaba har tashin qiyama. Daga nan sai ya koma jikinsa kamar yadda da yake([58]).

Abu Basir yana cewa: Na tambayi Abu Abdillah (a.s) game da ruhin muminai, sai ya ce: A aljanna za su kasance da siffar jikinsu, ta yadda da za ka gan shi da ka ce ai wane ne wannan([59]).

An ruwaito daga Yunus bn Zabiyan cewa: Wata rana ina zaune wajen Abu Abdillah (a.s) sai ya ce: Me mutane suke faxi ne kan ruhin muminai? Sai na ce: Suna cewa zai kasance tamkar qundun korayen tsuntsaye cikin fitila qarqashin alarshi. Sai ya ce: Subhanallah! Martabar mumini a wajen Allah ta wuce Ya sanya ruhinsa cikin abincin tsuntsaye. Ya Yunus! Idan Allah Ya karvi ruhin mumini zai mai da shi wata sura tamkar surar da mutum yake da ita a duniya, suna ci suna sha. Inda da wani zai kusato shi zai gane shi da siffar da yake da ita a duniya([60]).

A wani hadisin kuma, an ruwaito shi (a.s) yana cewa: Martabar mumini a wajen Allah ta wuce qundun tsuntsu, face dai cikin jikkuna kamar tasu([61]). Akwai ma wasu hadisan na daban da suke tabbatar da abin da muka ambata([62]).

Bisa ga abin da ya gabata, abin nufi da rayuwar kabari cikin yawa-yawan ruwayoyi shi ne samarwa ta biyu da za a yi wa mutum a duniyar barzahu inda ruhi zai taallaqa da jiki irin na misal. Da wannan ne ake iya fahimtar dukkan abubuwan da suka zo cikin ayoyi da hadisai kan batun tajarrudin ruhi, niima da azabar kabari, faxi ko takura kabari, motsi da tashin ruhi da kuma ziyarar mamata ga iyalansu da sauransu.

 

Ilmi Na Tabbatar da Samuwar Jikin Misal:

 Gwajegwajen malaman kiran ruhi sun tabbatar da samuwar jikkuna na misal, kamar yadda masu wannan raayi suke cewa mutuwa a kan kanta ba komai ba ce face tashi daga yanayi na jiki na zahiri zuwa wani yanayin jiki mai matuqar taushi. Sannan kuma sun yi imanin cewa ruhi na da wani jiki tattausa don haka qa'idojin da ke aiki bisa jiki na zahiri ba su aiki a kansa([63]).

 

Shin Wannan Tanasukh al-Batil ([64])ne?

Mai yiyuwa ne wasu su yi zaton cewa faxin cewa ruhi zai shiga wata sura bayan ya fita daga jiki wani nau'i ne na tanasukh al-batil, to amma ba haka lamarin yake ba, saboda babban dalilin kore tanasukh dalili ne na addini da kuma abin da musulmi suka tafi a kai. Da dama daga cikin musulmi da malaman aqida da hadisi sun yi amanna da batun jiki irin na misal, kamar yadda hadisan Imamai (a.s) suka tabbatar. Wanda suka yi amanna da tanasukh sun kafirta ne saboda inkarin tayarwa (ranar qiyama), sakamako mai kyau ko kuma azaba, da kuma imanin da suka yi na sassake sheqa da rai ke yi cikin jikkunan wannan duniya, da kuma inkarin tayarwa (ranar lahira) da suka yi, haka nan da inkarin Mahalicci da Annabawa da kuma faxuwar takalifi da dai sauran zantukansu na wauta([65]).

2- Shubuha ta biyu a wannan vangare ita ce ya ya azabar kabari da niimar da ke ciki za su kasance alhali tukuna ba aljanna ba wuta?

Amsa: Ayoyi da hadisan da muka kawo dake tabbatar da azabar kabari suna nuni da samuwar aljanna da wuta da kuma cewa su halittattu ne, kamar yadda faxin Imam Sadiq (a.s) yayin da aka tambaye shi kan ruhin muminai: (Suna) cikin xakuna a aljanna suna ci daga abincinta da kuma sha daga abin shanta([66]), yake nuni da hakan.

A wani wajen yana cewa: Haqiqa ruhin kafirai suna wutan Jahannama..([67]).

Sheikh al-Saduq (r.a) yana cewa: Mun yi imani ne cewa aljanna da wuta halittu ne guda biyu, da kuma cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya shiga aljanna sannan kuma an nuna masa wuta lokacin da ya yi miiraji, da kuma cewa babu wanda zai fita daga duniya face sai ya ga makomarsa a aljanna ko kuma a wuta([68]).

Nasir al-Tusi yana cewa: Nassi (Alqur'ani da hadisi) na tabbatar da cewa an halicci aljanna da wuta kuma yanzu haka akwai su. Duk wani ra'ayi savanin haka tawili ne. Allamah, cikin sharhinsa, ya yi bayani kan savanin da aka samu kan hakan inda yake cewa: Akwai savani tsakanin mutane kan shin an halicci aljanna da wuta ko kuma aa, wasu sun tafi kan raayin farko, shi ne kuwa abin da Abi Ali ya tafi a kai, amma Abu Hashim da al-Qadhi sun tafi kan cewa ba a halicce su ba.

Masu raayin farko suna kafa hujja ne da faxin Allah na cewa:

 ﴿

"An tanadar da ita ga masu tsoron Allah([69])"

 da kuma

 ﴿

An tanadar da ita ga kafirai([70])

da

 ﴿

 

Ya Adamu, ka zauna, kai da matarka a Aljanna([71])

da

 ﴿

A inda taken, nan Aljannar makoma take([72]),

 aljannar makoma ita ce gidan sakamako, to wannan ya nuna cewa an halicce ta tana sama.

Shi kuwa Abu Hashim yana kafa hujja ne da faxin Allah cewa:

 ﴿

Kowani abu mai halaka ne face yardarSa([73]).

 Da ace an halicci Aljanna da dole ne ta halaka, wannan kuwa ba zai yiyu ba saboda faxinSa Maxaukakin Sarki:

 ﴿

Abincinta yana madawwami([74]).

Allamah ya amsa masa da cewa: Dawwamar abincin (aljanna) yana nuni ne da dawwamar halittan irin wannan abincin, saboda abincin Aljanna ya kan qare yayin da aka ci sai dai kawai Allah Maxaukaki Zai sake halittan irinsa ne. Halaka na nufin fita daga dairar amfani, babu shakka idan mukallafai suka qare Aljanna za ta tashi daga dairar amfani, za ta saura halakakkiya da wannan maana([75]).

 

 

BAHASI NA UKU: SHARUXXAN QIYAMA

 

Maanarta Ta Lugga: Jam'i ne sharaxi, abin da Allamah ya ke nufi shi ne: sharuxxan qiyama: alamomin da suke nuni da samuwarta. An ruwaito Ibn Abbas dangane da alamominta yana cewa: Allah Maxaukakin Sarki na cewa:

 ﴿

To, shin, suna jiran (wani abu)? Face Saa ta je musu bisa abke, domin lalle sharuxxanta sun zo. To, ya ya tunawarsu take, idan har ta je musu([76]). Wannan aya tana nuni da wasu abubuwa biyu na ranar qiyama:

Na Farko: Shi ne cewa za ta zo ne (wa mutane) ba zata, wato kwatsam, kamar yadda yake cikin Faxin Allah cewa:

 ﴿

Ba za ta zo muku ba face kwatsam([77]),

 hakan na nuni da cewa Allah ne kaxai Ya san lokacin faruwarta

﴿

Ka ce: Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Babu mai bayyana ta ga lokacinta face Shi([78]).

Na Biyu: Idan alamun qiyama suka fara bayyana, to a wannan lokacin imani ba za ta yi amfani ba, kamar yadda Allah Maxaukaki cikin Alqur'ani mai girma yake cewa:

 ﴿

Ranar da wasu daga ayoyin Ubangijinka za su zo ba wani rai da imaninsa zai amfane shi idan da can bai ba da gaskiya ba, ko bai aikata wani abu na alheri ba([79]), a lokacin ba za a karvi tuba ba, kamar yadda imani da xaa ba sa amfanarwa saboda gushewar takalifi.

Nauointa: Bisa abubuwan da suka zo cikin Alqurani da hadisai, ana iya raba alamomin qiyama zuwa kashi biyu:

Na Farko: Sun shafi xabiun mutane a qarshen zamani da suka haxa da fitinu da yaqe-yaqe. Hadisai sun siffanta wannan zamani ko dai ta hanyar muamalar mutane ko kuma ababen da suke samunsu.

Daga cikin waxannan hadisai har da abin da Ibn Abbas (r.a) ya ruwaito daga Maaiki (s.a.w.a) cewa: Daga cikin alamar qiyama (har da): tozarta salla, bin son zuciya, xaukaka maabuta dukiya, sayar da addini don duniya, a wannan lokacin zuciyar mumini za ta narke a cikinsa kamar yadda gishiri ke narkewa idan ya haxu da ruwa saboda yana ganin munkari amma ba za a iya canza shi ba([80]).

Har ila yau Manzo (s.a.w.a) yana cewa: Idan alummata ta aikata wasu abubuwa sha biyar, bala'i zai faxa mata, sai aka ce: Ya Manzon Allah! Waxanne abubuwa kenan, sai ya ce: Idan dukiya (ta qasa) ta zamanto mallakan wasu (yan tsiraru suna yin yadda suka ga dama da hana raunana amfanuwa da ita), amana kuma ta zamanto ganima, zakka ta zamanto tamkar tara, mutum ya kasance mai biyayya ga matarsa tare da savawa (rashin biyayya) mahaifiyarsa, mafi qasqancin alumma ya zama shugaba, amma alumma suna girmama shi don tsoron sharrinsa, da xaga muryoyi a masallatai, da sanya alhariri, da riqe mata masu waqa kuma suke kaxa goge, sannan na qarshen wannan al'umma na la'antar na farkonta. To sai a saurari jar guguwa ko haxiyewar qasa ko shafewa([81]).

Na Biyu: Abubuwan da za su auku ga qasa, daga cikinsu akwai:

1- Fitar dabba: Allah Maxaukakin Sarki na cewa:

﴿

Kuma idan lokacin da aka alqawarta musu ya cika, to za mu fito musu da wata dabba daga qasa da za ta riqa faxa musu cewa: Lalle mutane sun kasance game da ayoyinMu, ba su yin imanin yaqini([82]).

2- Bayyanar Imam al-Mahdi (a.s): Akwai hadisai da yawan gaske da suke tabbatar da bayyanarsa (a.s) kafin tashin qiyama, sai dai hadisin da ya fi shahara shi ne faxinsa (s.a.w.a) cewa: Qiyama ba za ta tashi ba, har sai wani mutum daga zuriyata (ko kuma daga cikin iyalan gidana) ya fito da zai cika duniya da adalci kamar yadda ta cika da zalunci da qiyayya([83]).

3- Saukowar Isa xan Maryama, an fassara hakan da faxin Allah:

 ﴿

Haqiqa kuma shi alama ce ta zuwan Alqiyama, kada ku yi shakka game da ita; kuma ku bi Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya([84]).

 Da dama daga cikin malaman tafsiri sun tafi a kan cewa wannan aya tana magana ne kan saukowar (bayyanar) Annabi Isa xan Maryama (a.s) a qarshen zamani([85]).

4- Bayyanar Yaajuju wa Maajuju([86]): Allah Na cewa:

﴿ !

Har sai lokacin da aka buxe Yajuju da Majuju, su kuwa za su gangaro ne ta kowane tudu. Kuma alqawarin gaskiya ya gabato, sai ga shi idanuwan waxanda suka kafirta sun yi zuru-zuru([87]).

5- Hayaqi Bayyananne, Allah Maxaukakin Sarki na cewa:

  !﴿

Saboda haka, ka dakata, ranar da sama za ta zo da hayaqi bayyananne. Yana rufe mutane. Wannan wata azaba ce mai raxaxi([88]).

 Yazo cikin hadisi cewa hayaqin zai cika tsakanin gabas da yamma, zai yi kwanaki da darare arbain([89]).

6- Akwai wasu alamomi masu yawa da aka ambace su cikin hadisai da suka haxa da: wutar da za ta fito daga gololon Adan ta kora mutane zuwa wurin taron qiyama, ba za ta bar kowa a baya ba, za ta sauka tare da mutane idan suka sauka, ta tashi da su idan suka tashi, fitar rana daga inda take faxuwa da kusufai guda uku: kusufi daga gabas, kusufi daga yammaci da kusufin da zai faru a Jazirar Larabawa, da bayyanar Dujjal([90]), ciwon shan Inna zai yaxu haka nan mutuwar ba zata, ruwan sama zai zo ba a lokacinsa ba([91]), baqar iska za ta bayyana([92]).

 

 

BAHASI NA HUDU: ABUBUWAN DA ZA SU FARU RANAR QIYAMA

 

Al-Qiyama: Ranar tayarwa, da halittu za su tashi gaban Ubangiji.

An tambayi Manzon Allah (s.a.w.a) kan dalilin sanya wa wannan rana sunan ranar qiyama sai ya ce: Saboda a ranar ne halittu za su tsaya don hisabi([93]).

Ranar qiyama tana da sunaye daban-daban kamar yadda suka zo cikin Alqurani mai girma, kamar Al-Azifa (makusanciya), Al-Haqqa (kiran gaskiya), Al-Qaria (mai qwanqwasar zukata), Al-Xamat al-Kubra (uwar musifu mafi girma), Al-Waqia (mai aukuwa), Al-Sakha (mai tsawa), Al-Saa (saa lokaci -), Yawmul jam (ranar taruwa), Yawm al-Tagabun (ranar kamunga), al-Yawm al-Mawud (ranar da aka yi alqawarin zuwanta), al-Yawm al-Mashhud (rana abin halarta), Yawm al-Talaqi (ranar haxuwa), Yawm al-Tanadi (ranar kiran juna), Yawm al-Hisab (ranar hisabi), Yawm al-Fasl (ranar rarrabewa), Yawm al-Hasrati (ranar nadama) da kuma Yawm al-Waid (ranar tseratarwa).

Ranar qiyama na daga cikin wurare masu tsanani da wahala ga xanAdam saboda irin wahalhalu da abubuwan firgitarwa da doguwar tsayuwa dake tattare da ita, Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

﴿ !

Ya ku mutane! Ku ji tsoron Ubangijinku. Haqiqa girgizar (ranar) qiyama abu ne mai girma. Ranar da za ku ganta (don tsananin firgita) kowace mai shayarwa za ta manta da abin da ta shayar, kuma kowace mai ciki ta zubar da cikinta, ka ga kuma mutane suna tangaxi (maye) alhali kuwa ba bugaggu ba ne, sai dai azabar Allah ce mai tsanani([94]).

Amirul Muminina (a.s) yana cewa: "Ko wani abu a duniya jinsa ya fi girma bisa ga ganinsa, ko wani abu a lahira kuma ganinsa ya fi jinsa. To ji ya wadatar da ku daga ganin, labari kuma daga shi gaibin([95]).

Zango-zangon qiyama suna da yawa, saointa suna da tsawo, matsayanta sun bambanta, Imam Sadiq (a.s) yana cewa: Ku yi hisabi wa kanku kafin a yi muku hisabi, don qiyama tana da matakai hamsin, kowani mataki na da kimanin shekaru dubu, daga nan sai ya karanto faxin Allah:

  ﴿

Malaiku tare da Ruhi (Jibrilu) suke hawa zuwa gare Shi a cikin wata rana (wadda) gwargwadonta yake daidai da shekaru dubu hamsin([96]).

Yanzu bari mu kawo irin waxannan abubuwa da za su faru tun daga hura qaho har lokacin da za a yi kira don hisabi, imma dai zuwa ga Aljanna ko kuma wuta.

 

1- Busawar Macewa Ko Tsawar Mutuwa:

 Allah Ta'ala Na cewa:

﴿

Kuma aka busa qaho, sai duk abin da yake cikin sammai da abin da ke cikin qassai ya halaka sai wanda Allah Ya so([97]), da faxinsa:

﴿ !

Ba su jiran (kome) face wata tsawa guda, za ta kama su, alhali kuma suna yin husuma. Ba za su iya yin wasiyya ba, kuma ba za su iya komawa zuwa ga iyalansu ba([98]).

Ya zo cikin tafsiri cewa al-sur yana nufin qahon da za a hura cikinsa, wasu kuma sun ce jam'i ne na sura don Allah Maxaukaki Zai sanya wa bayi surarsu (siffansu) cikin kabari kamar yadda ya yi yayin da suke cikin mahaifan uwayensu, daga nan sai ya hura musu ruhi kamar yadda Ya hura musu cikin mahaifan uwayensu([99]).

Sai dai zahirin ayoyi da hadisai yana nuni ne da maanar farko, an ruwaito cikin wasu hadisai masu yawa cewa Allah Maxaukakin Sarki Ya halicci Israfilu (malaika mai busa qaho) tare da (wani) qaho da ke da baki biyu: xaya a vangaren gabashi, xayan kuma a yammaci, yana riqe da shi, yana jiran umarnin Ubangiji, idan Ya masa umarni, sai ya busa([100]).

Daga cikin abubuwan da za su faru bayan busa qaho, (har da): babu wani mai rai a sama ko qasa da zai saura face ya mutu, babu wata alama ta rayuwa da za ta saura face sai abin da Allah Maxaukakin Sarki Ya so (ta rayu):

 ﴿

Babu abin bautawa face Shi. Kowane abu mai halaka ne face yardarSa. Shi ne da hukumci kuma zuwa gare shi ake mayar da ku([101]).

Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Bayan qarewar duniya, Allah Maxaukakin Sarki Shi ne kaxai wanzajje kamar yadda Yake kafin Ya fareta; ba tare da lokaci ko bigire ko zamani ba. A yayin wannan, dukan ajali da lokaci da shekaru da sa'oi sun gushe. Babu komai sai Allah, Makaxaici, Mabuwayi, kuma gare Shi ne makomar dukkan al'amura([102]).

 

2- Sauyawar Tsarin Duniya:

 Rayuwa a lahira, samarwa ce ta biyu da za ta faru a sabon tsari da za ta sami siffar dawwama, kuma za ta qumshi imma dai niima ta Aljanna ko kuma azaba ta wuta (Allah Ya tsare mu), dukkan hakan za su faru ne bayan gushewar tsarin duniya da ya ginu kan gushewa; Allah Maxaukaki Na cewa:

  ﴿

Ranar da za a sake qasa ba (wannan) qasar ba, da kuma sammai (ba waxannan sammai ba. Halittu) kuma suka fito (daga cikin qasa) a gaban Allah Makaxaici, Mai rinjaye([103]).

Allah Maxaukakin Sarki, cikin ayoyi da dama, yayi bayani kan wannan sauyi da zai faru a sammai da qassai, da ke nuni da sauyin..

Yayin da yake siffanta wannan rana, Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Rana ce mai gintsewa, mai murtukewa, ranar da sharrinta ya kasance mai tartsatsi, firgici da tsoron dake cikin wannan rana na firgita (hatta) Malaikun da ba su da zunubi([104]).

 

3- Busa Qahon Tayarwa ko Tsawar Tayarwa:

  Shi ne busa qahon da za a tayar da dukkanin halittu a ranar lahira, Allah Maxaukakin Sarki na cewa:

﴿ ! !

Kuma aka yi busa a cikin qaho, to, sai ga su, daga kaburbura zuwa ga Ubangijinsu, suna ta gudu. Suka ce: Ya bonenmu! Wane ne ya tayar da mu daga barcinmu? Wannan shi ne abin da Mai rahama ya yi waadi da shi, kuma Manzanni sun yi gaskiya. Ba ta kasance ba face wata tsawa ce guda, sai ga su duka, suna abin halartarwa a gare Mu([105]).

Kuma Allah Maxaukakin Sarki na cewa:

﴿ !

Kuma aka hura cikin qaho. Wancan yinin qyacewar ce fa. Kuma kowane rai ya zo, tare da shi akwai mai kora da mai shaida([106]).

Amirul Muminina (a.s) na cewa: Qasa ba ta tsagewa ga wani ranar qiyama, face sai wasu Malaiku biyu suna riqe da hannayensa suna cewa ka amsa kiran Ubangiji Mabuwayi([107]).

Za su amsa wa mai kira bayan qasa ta tsage musu, suna masu gaggawa zuwa matsaya, suna maqasqanta ga idanuwansu, wulaqanci ya rufe, tamkar farin da suka bazu ko kuma yayan fari masu watsuwa. Allah na cewa:

﴿ !

Ranar da suke fitowa daga kaburbura da gaugawa, kamar su, zuwa ga wata kafaffiyar (tura), suke yin gaggawa. Maqasqanta ga idanunsu, wani walaqanci yana rufe su. Wannan shi ne yinin da aka yi musu alqawarinsa([108]).

 

4- Tarawa:

Abin nufi a nan shi ne taro dukkan halittu ranar tashin qiyama lokacin da za a tara su gaba xaya babu wanda za a bari. Allah Maxaukakin Sarki na cewa:

  ﴿

 Kuma Mu tara su har ba Mu bar kowa ba daga gare su([109]).

 Wannan taruwa kuwa zai haxa har da namun daji da na gida da kuma tsuntsaye saboda faxinSa Maxaukaki:

  ﴿

Kuma idan dabbobin daji aka tattara su([110]),

 da kuma faxinSa:

﴿

Kuma babu wata dabba a cikin qasa, kuma babu wani tsuntsu wanda yake tashi da fukafukinsa, face alumma ne misalanku. Ba mu yi sakaci barin kome ba a cikin Littafi, saan nan kuma zuwa ga Ubangijinsu ake tara su([111]).

Taron ranar qiyama na daga cikin matakan da ke firgita zukata har su iso zuwa maqogwaro, yayin da za a kora halittu zuwa filin taruwa a ranar mai firgitarwa (ranar qiyama) kamar yadda Ubangijinsu Ya halittu su tun farko, huntaye marasa takalma, alhali zufa ta rufe su saboda quncin wajen.

Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Wannan rana ce da Allah Zai tattaro (mutanen) farko da na qarshe a cikinta don hisabi da kuma sakamakon ayyuka, suna tsattsaye cikin qasqantar da kai, alhali zufa duk ta rufe su, qasa kuwa tana jijjiga su. Wanda ke cikin mafi kyaun yanayi shi ne wanda ya sama wa qafafunsa wajen tsayuwa, ya kuma sami yadda zai yi numfashi([112]).

Imam Sadiq (a.s) yana cewa: Misalin mutane a ranar qiyama, idan suka tsaya a gaban Ubangijin talikai, tamkar kibiya ne cikin kwari, ba shi da wani abu a doron qasa in ba inda zai sanya qafafunsa ba, kamar kibiya cikin kwari, ba za ta iya motsawa zuwa nan ko can ba([113]).

Za a gabatar da mutane a gaban Ubangijinsu sahu-sahu don hukumci, ba tare da wani fifiko na nasaba ko dukiya ko muqami ko matsayi ba, za a gabatar da kowa babu wani da zai iya vuya

  ﴿

A ranar nan za a bijira ku (domin hisabi), babu wani rai, mai voyewa, daga cikinku, wanda zai iya voyewa([114]).

 Abin da ke voye zai ba da shaida, sannan abin da aka yi a voye zai fito fili

  ﴿

Ranar da ake jarraba-war asirai([115]),

 duk wani aiki ko kuma aqida da aka voye za ta bayyana

  ﴿

Ranar da suke bayyanannu, babu wani abu daga gare su wanda yake iya voyuwa ga Allah([116]).

Taruwa don hisabi ta kan bambanta gwargwadon ayyukan mutane na bayyane, inda za a tayar da masu taqawa cikin xaukaka

﴿

A ranar da Muka tara masu taqawa zuwa ga Mai rahama suna baqin girma([117]),

 alhali fuskokinsu na cike da alamun farin ciki da annashuwa

  !﴿

Wasu fuskoki, a ranar nan, masu haske ne. Masu dariya ne, masu bushara([118]),

 saboda abin da aka tanada musu na lada da nasara, suna da wani irin haske da annuri da ke bambance su daga sauran mutanen da ke wajen (a tsaye)

  ﴿

Ranar da za ka ga muminai maza da muminai mata, haskensu na tafiya a gaba gare su, da kuma dama gare su([119]).

Su kuwa mujirimai na daga kafirai da mushirikai da jagororinsu na daga shaixanu za a tayar da su ne a gurfane:

  ﴿

To, muna rantsuwa da Ubangijinka, lalle ne, Muna tayar da su da kuma shaixanun, saan nan, kuma, lalle Muna halartar da su a gefen Jahannama suna gurfane([120]),

 tare da abin da suke bautawa baicin Allah Maxaukakin Sarki:

     ﴿

Kuma ranar da Yake tara su da abin da suke bauta wa, baicin Allah([121]),

 za su bambanta da sauran mutanen da ke wajen saboda baqaqen fuskokinsu da mummunan yanayin da suke ciki:

  !﴿  

Wasu fuskoki, a ranar nan, akwai qura a kansu. Baqi zai rufe su([122]).

 Za a ja su akan fuskokinsu zuwa wutan Jahannama ba suna masu yanke qauna:

  ﴿

Kuma Muna taru a Ranar Qiyama a kan fuskokinsu, suna makafi, kuma bebaye da kurame([123]).

 

5- Kotun Ubangiji:

 Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

﴿ !

Kuma qasa ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littafi, kuma aka zo da Annabawa da masu shaida, kuma aka yi hukumci a tsakaninsu, da gaskiya, alhali kuwa, su, ba za a zalunce su ba. Kuma aka cika wa kowane rai abin da ya aikata. Kuma (Allah) Shi ne Mafi sani game da abin da suke aikatawa([124]). Wannan ita ce kotun Ubangiji da ba ta yi kama da ta duniya ba a komai, saboda alqalinta Ya san yaudarar idanuwa da abin da qiraza suke voyewa, shaidunta kuma Annabawa ne da Manzanni, da gavovin wanda ake tuhuma da ayyukansa da aka gabatar a gabansa da kuma takardun da aka rubuta ayyukansa da ba sa barin babba ko qarami face sun rubuta shi. To ya ya za a yi wanda ake tuhuman ya musanta abin da ake tuhumarsa da shi alhali ga ayyuka an gabato da su, an baza takardu, ga shaidu a tsaye sannan gavovi kuma suna magana?!

Yanzu bari mu yi qarin bayani kan wasu daga cikin ababen da za su gudana a wannan kotu na daga tambayoyi, hisabi da shaidu, kamar haka:

 

Na Farko: Tambaya:

 Za a gudanar da ita ne a kan dukkan halittu saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki cewa:

! ﴿

To, rantsuwa da Ubangijinka! Haqiqa, Muna tambayar su gaba xaya. Daga abin da suka kasance suna aikatawa([125])

 da kuma faxinSa:

  ﴿

Saan nan lalle ne Muna tambayar waxanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Muna tambayar Manzannin([126]),

 wato kan addini, amma zunubi kuwa ba a tambaya kansa face ga wanda za a masa hisabi, duk wanda za a masa hisabi kuma to abin azabtarwa ne ko da kuwa da doguwar tsayuwa ce([127]).

A wannan lokaci, za a tambayi gavovin kamar yadda aka ruwaito daga Imam Sadiq (a.s) dangane da faxin Allah Taala:

﴿

Lalle ne ji da gani da zuciya, dukkan waxancan, za su kasance abin tambaya([128]),

 inda yake cewa: Za a tambayi ji kan abin da ya ji, gani kuma kan abin da ya gani, zuciya kuma kan abin da ke qulle cikinta([129]).

Waxannan tambayoyi za su shafi xanAdam gaba xayansa da aqidar da yake riqe da ita. An ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a) cewa: Qafar bawa ba ta gusawa ranar tashin qiyama har sai an masa tambayoyi guda huxu: dangane da rayuwarsa, yadda ya gudanar da ita, dangane da jikinsa yadda ya sarrafa shi, dangane da dukiyarsa yadda ya samo ta da yadda ya kashe ta, da kuma dangane da qaunarmu Ahlulbaiti([130]).

Abin nufin da Ahlulbaitin da za a tambayi mutane dangane da qaunarsu su ne waxanda nassi ya tabbatar da ismarsu (tsarkinsu) cikin faxin Allah Maxaukakin Sarki cewa:

  ﴿

Haqiqa Allah Na nufin ya tafiyar da qazamta ne daga gare ku Ya ku mutanen Babban Gida (Ahlulbaiti) ya tsarkake ku tsarkakewa([131]),

 su ne waxanda Manzon Allah (s.a.w.a) ya tafi da su don yin mubahala (qalubalen tsinuwa) da nasaran Najran yana mai dogaro da faxin Allah Maxaukakin Sarki cewa:

﴿

To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: Ku zo mu kirayi yayanmu da yayanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, saan nan kuma mu qanqantar da kai, saan nan kuma mu sanya laanar Allah a kan maqaryata([132]), (Ahlulbaitin) su ne Manzon Allah (s.a.w.a), Ali, Fatima, Hasan da Husain (a.s) da sauran maasumai guda tara daga cikinsu, su kaxai banda wasunsu.

Lalle za a tambayi mutum kan qaunar Ahlulbaiti (a.s) ne saboda Allah Ya farlanta qaunarsu a kan halittu cikin faxinSa:

  ﴿

Ka ce: Ba ni tambayarku wata lada a kansa, face dai soyayya ga makusanta([133]),

 a matsayin wani tushen aqida dake nuni da tsananin riqo da Musulunci da asalin aqidarsa. Manzon Allah (s.a.w.a) ma ya jaddada hakan cikin hadisansa masu yawa, daga cikin har da faxinsa (s.a.w.a) cewa:

,

Ku so Allah saboda abin da Ya ciyar da ku na daga niimominSa, ku so ni saboda son Allah, kana kuma ku so Ahlubaitina saboda so na([134]).

Sai dai abin da ke da kyau a fahimta shi ne cewa ba wai kawai qauna da so ne za a tambaya ba, a'a har da xaa da biyayya gare su (a.s) a matsayinsu na wasiyyai maasumai sannan jagororin alumma bayan Maaiki (s.a.w.a). An ruwaito Manzo (s.a.w.a), kan ayar nan ta:   

 ﴿ ,

Kuma ku tsayar da su, lalle su, waxanda ake yi wa tambaya ne([135]),

 yana cewa: Wato kan wilayar Aliyu bn Abi Talib([136]).

 

Na Biyu: Hisabi:

 Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

  ﴿ *  

Lalle ne, zuwa gare Mu komowarsu take. Saan nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisabi([137]).

 Hisabi: na nufin binciken ayyuka da ba da sakamako kansu, da kuma tsayar da bawa don amsa abin da ya aikata, da inkarin munanan ayyukan da ya aikata, da kuma gode masa kan kyawawa, za a yi muamala da shi gwargwadon abin da ya cancance shi([138]).

Allah Maxaukakin Sarki Zai yi magana da bayinSa, na farkonsu da na qarshensu, ne da kalma guda yayin hisabi, kowa zai ji abin da ya shafe shi, ta yadda zai xauka da shi kawai ake yi banda waninsa, Magana ba ta shagaltar da Allah ga barin wata maganar. Zai gama wannan hisabi ne cikin saa guda daga irin saoin duniya([139]).

Dangane da faxinSa Taala:

  ﴿,

Allah Mai gaggawar sakamako da yawa ne([140]),

 ruwayoyi na nuni da cewa Allah Zai yi hisabi ga dukkan halittu ne cikin kyaftawar ido, a wata ruwayar kuma gwargwadon tatsar akuya[141].

An ruwaito Imam Sadiq (a.s) dangane da faxin Allah Taala cewa:

﴿

, A cikin yini wanda gwargwadonsa, shekara dudu hamsin ne([142]),

yana cewa: Da wani baicin Allah ne zai yi hisabi, da an xauki shekaru dubu hamsin kafin a gama, amma Allah Maxaukakin Sarki Zai gama shi cikin saa guda([143]).

An tambayi Amirul Muminina (a.s): Ya ya Allah Zai yi hisabi wa halittu duk kuwa da yawansu? Sai ya ce: Kamar yadda Ya arzurta su duk da yawansu, sai aka ce: Ta ya ya zai yi musu hisabi alhali ba sa ganinSa? Sai ya ce: kamar yadda Ya ke arzurta su alhali ba sa ganinSa([144]).

An ruwaito Imam Baqir (a.s) yana cewa: Abu na farko da za a yi wa bawa hisabi kansa shi ne salla, idan ta karvu za a karvi sauran (ayyukansa)([145]).

Babu wanda zai tsira daga wahalhalun ranar hisabi face wanda ya yi hisabi wa kansa tun a duniya, ya auna ayyuka da maganganunsa da mizanin sharia. Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Ya ku bayin Allah! Ku auna kanku kafin a auna ku, ku yi wa (kanku) hisabi tun kafin a yi muku hisabi, ku numfasa kafin shaqewa, ku miqa wuya kafin fizgar korawa([146]).

 

Na Uku: Shaidu:

 Shaidu suna daga cikin abubuwa masu firgitarwa da ban tsoro a ranar qiyama, saboda mutum zai fuskanci waxansu da ba a iya musanta shaidarsu. Ba abin da zai rage masa face 'karvar laifi' da kuskuren da ya aikata. Waxannan shaidu sun haxa da:

 

a) Allah Maxaukaki:

 Shi ne Maxaukakin da kome ke qarqashin ilminsa, sannan kuma Yana ganin kome, Yana ganin bawa a yayin da vuya, Ya san abin da ya voye, Shi Ya fi kusanci  gare shi daga lakar jannayensa. Allah na cewa:

   ﴿,

Kuma ba ku aikata wani aiki ba, face Mun kasance Halarce([147]).

Sannan kuma Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

  ﴿

.Wata ganawa ta mutum uku ba za ta kasance ba face Allah Shi ne na huxu xinta, kuma babu ta mutum biyar face Shi ne na shida xinta, kuma babu abin da ya kasa wannan kuma babu abin da yake mafi yawa face Shi Yana tare da su duk inda suka kasance, saan nan Ya ba su labari game da abin da suka aikata a Ranar Qiyama. Lalle Allah Masani ne ga dukkan kome([148]).

Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Ku ji tsoron sava wa Allah a voye, don kuwa mai shaidan shi ne kuma alqalin([149]).

 

b) Annabawa da Wasiyyai:

 Alqurani mai girma ya tabbatar da cewa Allah Maxaukakin Sarki Zai sanya kowani Annabi ya zamanto shaida a kan alummarsa Ranar Qiyama, Manzonmu (s.a.w.a) shi ne zai kasance shaida kan alummarsa, Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

  ﴿,

 To, ya ya, idan Mun zo da shaidu daga dukkan alumma, kuma Muka zo da kai a kan waxannan, kana mai shaida([150]).

Haka nan cikin faxin Allah Maxaukakin Sarki cewa:

  ﴿,

Kuma a ranar da Muke tayar da shaidu a cikin kowace alumma, a kansu daga kawunansu, kuma Muka zo da kai kana mai bayar da shaida akan waxannan([151]),

Ya yi bayanin cewa Ranar Qiyama Zai tayar da wani shaida cikin kowace alumma, su ne kuwa Annabawa da adilan kowani zamani inda za su  yi shaida kan mutane cikin ayyukan da suka aikata([152]).

Wannan aya tana nuni da wajibcin samun wani mutum cikin kowace alumma da maganarsa za ta kasance hujja ce a kan mutanen zamaninsa, wanda kuma adali ne a wajen Allah Maxaukaki. Wannan ita ce aqidar al-Jabba'i da mafi yawan masu aqidar Adalcin Ubangiji, kuma shi ne abin da Imamiyya suka tafi a kai, duk da cewa sun sava da su dangane da ko waye ne wannan hujjan (adilin)([153]).

A fili yake cewa ba dukkan alumma ne suka siffantu da zavi da adalci ba, da kuma kasancewa shaida akan mutane, don kuwa akwai da yawa da halayensu ba su vuya ba. Saboda haka wannan siffa ta wani sashe ne, waxanda kuma da su ake magana a nan.

Al-Ayashi ya naqalto Imam Sadiq (a.s), kan ayar:

       ﴿,

 Kuma kamar  wancan, Muka sanya ku alumma matsakaiciya domin ku kasance masu bayar da shaida a kan mutane kuma manzo ya kasance mai shaida a kanku([154]),

 yana cewa: Idan har kana zaton Allah, cikin wannan aya, Na nufin dukkan maabuta alqibla masu kaxaita Allah ne, ya ya mutumin da ba a karvan shaidarsa kan sa'i guda na dabino, amma Allah Ya kira shi shaida Ranar Qiyama, Ya kuma karve ta a gaban illahirin alummomin da suka gabata? Ko da wasa! Ba haka Allah Ya ke nufi ba, Yana nufin alummar da kiran Annabi Ibrahim (a.s) (wato: Kun kasance mafi alherin alumma da aka fitar ga mutane([155])) ya tabbata a gare su, su ne alumma matsakaiciya, su ne kuma mafi alherin alumma da aka fitar ga mutane([156]).

Imam Baqir (a.s) yana cewa: Mu ne alumma matsakaiciyya, mu ne shaidun Allah a kan bayinSa, sannan kuma hujjojinSa a bayan qasarSa([157]).

 

c) Malaiku:

Allah Maxaukakin Sarki Ya sanya wa kowani mutum wasu Malaiku da za su kasance tare da shi suna rubuta dukkanin ayyukansa, Allah Na cewa:

﴿  !

A lokacin da masu haxuwa biyu suke haxuwa daga dama kuma daga hagu akwai wani (Malaika) zaunanne. Ba ya lafazi da wata magana face a liqe da shi akwai mai tsaro halartacce([158]).

 Lokacin da aka gabatar da bawa don hisabi Malaiku za su ba da shaida kansa kan ayyukan da ya aikata a duniya na alheri ko sharri, Allah Na cewa:

   ! ﴿

Kuma aka hura a cikin qaho. Wancan yinin tsoratarwa ne fa. Kuma kowane rai ya zo, tare da shi akwai mai kora  da mai shaida([159]).

Amirul Muminina (a.s) na cewa: Mai korawa wanda zai kora shi zuwa wajen taruwa (don hisabi), da mai shaida wanda zai ba da shaida kan ayyukansa([160]).

 

d) Gavovi:

 A wasu matakan hisabi Allah Zai rufe bakunan mutane, sai hannaye da sauran gavovi ne za su ba da shaida kan abin da suka aikata, Allah Taala Na cewa:

    ﴿

A ranar da harsunansu, da hannayensu, da qafafunsu, suke bayar da shaida a kansu, game da abin da suka kasance suna aikatawa([161]).

Abin nufi da shaida shi ne shaidar da gavovi za su bayar kan munanan ayyuka da zunubi gwargwadon shaidar da ta dace da su. Harshe shi ne zai ba da shaida kan savon da ya shafi zance irin su qazafi, qarya, giba (cin nama) da makamantan hakan, abubuwan da suka shafi ayyuka kuwa kamar sata, tafiya saboda aikata annamimanci da makamantansu, sauran gavovi ne za su ba da shaida kansu([162]).

 

e) Littafin Ayyuka:

 A baya mun faxi cewa dukkan ayyuka da kalaman xanAdam akan rubuta su cikin litattafa da ke wajen wasu Malaiku masu tsaron su:

   ! !  ﴿

Lalle ne, a kanku, haqiqa akwai matsara. Masu daraja, marubuta. Suna sanin abin da kuke aikatawa([163]).

 A ranar tashin Qiyama za a gabatar da takardun ayyuka, Allah Maxaukaki Zai fitar wa kowace alumma littafin da zai ambaci dukkanin maganganunta da kuma bayyanar da haqiqanin ayyukanta, Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

﴿ !

Kuma za ka ga kowace alumma tana gurfane, kowace alumma ana kiran ta zuwa ga littafinta. (A ce musu) A yau ana saka muku da abin da kuka kasance kuna aikatawa. Wannan littafinMu ne, yana yin magana a kanku da gaskiya. Lalle Mu, Mun kasance Muna sauya rubutun tamkar abin da kuka kasance kuna aikatawa([164]).

Littafin kowani mutum, da ba ya barin qarami ballantana babba sai ya lissafo shi, zai bayyana masa, Allah Zai sanya mutum ya kasance mai hisabi wa kansa kuma alqali, Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

﴿ !

Kuma kowane mutum Mun lazimta masa abin rekodinsa a cikin wuyansa, kuma Mu fitar masa a Ranar Qiyama da littafi wanda zai haxu da shi buxaxxe. Karanta Littafinka. Ranka ya isa ya zama mai hisabi a kanka a yau([165]).

Mujiriman kafirai da mushirikai za su tsorata saboda abin da ke cikin waxannan litattafa na bincike da lissafin gaskiya  mai tsanani da babu kuskure cikinsa:

﴿

Kuma aka aza littafin ayyuka, sai ka ga masu laifi suna masu jin tsoro daga abin da ke cikinsa, kuma suna cewa, Kaitonmu! Mene ne ga wannan littafi, ba ya barin qarami kuma ba ya barin babba, face ya qididdige shi?([166]).

 

f) - Bayyanar Ayyuka ko kuma Xaukarsu Siffan Jiki:

 Allah Taala Na cewa:

   ﴿

A ranar nan, mutane za su fito daban-daban domin nuna musu ayyukansu([167]).

 Sannan kuma Allah Taala Na cewa:

﴿

A ranar da kowane rai yake samun abin da ya aikata daga alheri, a halarce, da kuma abin da ya aikata daga sharri, alhali yana gurin, da dai lalle a ce akwai fage mai nisa a tsakaninsa da abin da ya aikata na sharri([168]).

Saboda haka a rayuwar lahira ayyuka za su kasance shaida a kan mutum, sai dai an samu savani tsakanin malaman tafsiri kan yanayin da za a gabatar da su. Wasu sun tafi kan cewa za a gabatar da sakamakon ayyukan ne, wato ko dai lada ko kuma uquba. Wasu kuma suna ganin cewa za a gabatar da littafin ayyuka ne da abin da ke cikinsa na kyawawan ayyuka ko munana, domin su ayyuka aradh([169]) ne, aradh kuma abu ne mai gushewa([170]), wasu kuma suka ce za a yi hakan ne ta hanyar gabatar da su su kansu, saboda gabato da su xin yana nuni da cewa ayyuka suna nan kuma ana tsare su daga salwanta, sai dai sun vuya mana ne a wannan duniya, kuma Allah Maxaukakin Sarki Zai halarto da su ga bayinSa Ranar Qiyama. Don haka ne aka ce: Littafin aiki na qumshe ne da asalin ayyukan da aka aikata([171]).

Saboda haka, gabatar da ayyuka kamar yadda suke na nuni da cewa suna nan kuma ana ajiye da su ne ta hanyar gaibi wacee ta ma xara xaukar hotonsu balle rubutasu cikin littafi, da kuma gabatar da su ga bawa Ranar Qiyama ya gansu yadda suke, ka san kuwa babu wata hujja da ta wuce ido (gani).

 

6- Sikeli (Maauni):

 Abin da ake auna abubuwa, ko kuma magwaji da ake gane gwargwadon girman abu. Daga cikin abubuwan da za su faru a Ranar Qiyama har da sanya sikelin gaskiya don bambance maabuta xaa da imani daga maabuta savo da tawaye, Allah Na cewa:

﴿

Kuma Muna aza maaunan adalci ga Ranar Qiyama, saboda haka ba a zaluntar raid a kome. Kuma ko da ya kasance nauyin qwaya daga komayya ne sai Mun zo da ita. Kuma Mun isa zama Masu hisabi([172]).

A ranar tashin Qiyama ba za a sanya sikeli ga kafirai da mushirikai ba, za a vata ayyukansu ne kawai, sannan a tura su zuwa wutan Jahannama qungiya-qungiya:

             ﴿

Waxancan ne waxanda suka kafirta da ayoyin Ubangijinsu, da kuma haxuwa da Shi, sai ayyukansu suka vaci. Saboda haka ba za Mu tsayar musu da awu ba a Ranar Qiyama([173]).

An ruwaito Imam Aliyu bn Husain Zainul Abidin (a.s) cikin wani hadisi yana cewa: Ku sani Ya ku bayin Allah! Ba za a sanya wa maabuta shirka sikeli ba, ba za a baje musu litattafan (ayyuka) ba, abin da za a yi kawai shi ne a tura su zuwa Jahannama ne qungiya-qungiya, don kuwa sanya sikeli da baje litattafa na maabuta Musulunci ne. Don haka ku ji tsoron Allah Ya ku bayin Allah([174]).

Babu savani tsakanin alumma kan asalin sikeli saboda Alqurani da hadisan Maasumai (a.s) sun tabbatar da shi, savanin da aka samu shi ne dangane da haqiqaninsa da kuma maanarsa. Akwai raayoyi  daban-daban, waxansunsu sun dogara da hadisai, kan hakan. Mafi muhimmanci daga cikinsu, su ne:

Na Farko: Shi ne cewa sikelin Ranar Qiyama tamkar na duniya ne, kowani sikeli na da harshe da tafuka biyu, da za a auna ayyukan bayi na alheri ko sharri, suna masu riqo da gundarin kalmar sikeli. To sai dai sun sami savani kan abin da za a aunan, shin ayyukan mutum ne za a auna ko kuma litattafan ayyukan ko kuma wani abu daban; bisa maganganu daban-daban([175]).

Na Biyu: Sikeli kinaya ce ta adalci a Ranar Qiyama, wato babu wanda za a zalunta. Maanar ajiye sikelii (da aka ce) shi ne aiwatar da adalci, waxanda ayyukansu na qwarai suka yi rinjaye, to su ne maabuta rabo, waxanda kuma munanan ayyukansu suka yi rinjaye saboda qaranci kyawawa, to su ne waxanda suka yi hasara([176]).

Wata ruwaya da aka ruwaito daga Imam Sadiq (a.s) tana qarfafa wannan raayi lokacin da wani Zindiqi ya tambaye shi: ashe ba za a auna ayyuka ba? Sai ya ce masa: Aa, ai ayyuka ba jiki ba ne, su siffar abin da suka aikata ne. Wanda ya jahilci adadin abu kuma bai san nauyinsa ko sakwaikwayarsa ba, shi yake buqatar auna shi. Amma ai babu abin da ya vuya ga Allah.

Sai ya ce: to me ake nufi da sikeli? Sai Imam (a.s) ya ce: Adalci, sai ya ce: to mene maanarsa cikin littafinSa

   ﴿

To wanda sikelansa suka yi nauyi([177]),

 sai ya ce masa: Wanda ayyukansa suka yi rinjaye([178]).

Na Uku: Sikeli na nufin hisabi, rinjaye ko rashin rinjayen sikeli kinaya ce ga qaranci ko girman hisabin, saboda abin da aka ruwaito daga Amirul Muminina Ali (a.s) inda yake cewa: Maanar faxinSa

 ﴿

da kuma

﴿

shi ne qarancin hisabi da yawansa, mutane sun bambanta a wannan rana. Daga cikinsu akwai wanda za a masa hisabi mai sauqi ya koma zuwa ga iyalansa yana mai farin ciki, akwai kuma waxanda za su shiga Aljanna ba tare da hisabi ba, don ba su kutsa cikin alamurran duniya ba, saboda hisabi yana kan waxanda suka shigeta a nan ne. Akwai kuma wanda za a masa hisabi kan komai, babba da qarami, za a wuce da shi zuwa ga azaba mai tsanani, daga cikinsu akwai jagororin vata da kafirci, to waxannan ba za a tsayar musu da sikeli ba, ba za a kula da su ba don su ma ba su kula da umarni da haninSa (Allah) ba, za su dawwama cikin wuta, wuta za ta qona fuskokinsu, za su kasance a cikinta tamkar masu yagaggun levva([179]).

Na Huxu: Maauna: (su ne) Annabawa da wasiyyai, saboda abin da aka ruwaito daga Imam Sadiq (a.s) kan faxin Allah Taala:

 ﴿

Kuma Muna aza maaunan adalci ga Ranar Qiyama([180]),

 inda ya ce: Al-Mawazin (maauna) su ne: Annabawa da wasiyyai([181]), su ne (a.s) maaunin da za a iya gane gaskiya da adalci, rinjayen ayyuka kuwa ya kan samu gwargwadon imani da tafarkinsu, so da kuma biyayya gare su da kuma koyi da shiriyarsu.

Waxannan dai su ne muhimman raayoyi da kuma ruwayoyin da suka zo kan maanar sikeli, wataqila suna daga cikin misdaqinsa ne. To sai dai ba a wajabta mana imani da zurfafa bayani kan yanayinsa ba, abin da ke wajibi shi ne imani da samuwar sikeli ba tare da mun kutsa cikin neman qarin bayani kansa ba.

 

7- Siraxi:

A luggance siraxi na nufin tafarki ko kuma bayyananniyar hanya, Allah Na cewa:

   ﴿

Ka shiryar da mu madaidaiciyar hanya.

Siraxi xaya ne daga cikin zango-zangon ranar lahira. Shi ne kuwa wata gada da za a girka kan Jahannama kuma dole ne dukkan halittu su wuce ta kanta. Kaurinsa kamar gashi, kaifinsa kuwa kamar takobi. Yan Aljanna za su wuce shi ba tare da wani tsoro ko fargaba ba, su kuwa kafirai za su wuce kansa ne a matsayin azaba gare su da kuma qarin tsoro da firgita, duk wanda ya iso makomarsa cikin wuta sai ya faxo daga siraxin cikinta([182]).

Akwai bambancin sauri kan siraxi gwargwadon ayyukan da mutum ya aikata a nan duniya, muminai za su qetare shi tamkar walqiya mai sauri, su kuwa kafirai tun takun farko za su fara karkarwar faxawa cikin wuta. Imam Sadiq (a.s) yana cewa: Mutane sukan ketare siraxi xabaqa-xabaqa. Shi siraxi ya kasa gashi kauri, kuma yafi takobi kaifi, daga cikin mutane akwai wanda zai ketare shi tamkar walqiya mai qeftawa, akwai kuma wanda zai qetare shi tamkar gudun doki, akwai kuma mai qetare shi da rarrafe, akwai kuma wanda zai qetare da tafiya, akwai kuma wanda zai qetare shi yana liqewa masa, mai yiyuwa ne wuta ta yagi rabonta ta bar saura([183]).

Wasu sun ce: Siraxi a lahira misali ne dake nuni da tafarkin da mutum ya kasance a kai a duniya, duk wanda ya bi miqaqqen tafarki a nan duniya, ba zai yi nauyi a kan siraxin lahira ba don haka sai ya samu tsira. Shi kuwa wanda ya kauce wa miqaqqen tafarki a nan duniya, ya nauyaya bayansa da munanan ayyuka da savo, zai fara karkarwa da zaran ya xora kafarsa ta farko a kan siraxin([184]).

Imam Sadiq (a.s), yayin da yake bayani kan maanar siraxi, yana cewa: Shi tafarki ne zuwa ga sanin Allah Maxaukakin Sarki, siraxi ya kasu gida biyu: siraxi a duniya da siraxi a lahira. Amma shi siraxi na duniya shi ne Imamin da aka wajabta xaa gare shi. Duk wanda ya san shi a duniya ya kuma yi riqo da tafarkinsa, zai qetare siraxin da ke lahira da aka shimfixa shi a kan Jahannama. Wanda kuwa bai sanshi ba a duniya, qafafunsa za su zame a kan siraxi ranar lahira, ya faxa cikin wutar Jahannama([185]).

Wani hadisin Maaiki (s.a.w.a) ma yana tabbatar da hakan, inda yake cewa: Idan ranar lahira ta zo, aka girka siraxi kan Jahannama, babu wanda zai tsira sai wanda ke da takardar (daga) Aliyu bn Abi Talib tare da shi([186]).

Tafarkin Imamai (a.s) shi ne hanyarsu bayyananniya, wato miqewa da daidaito wajen qaunarsu, da kuma riqo da tafarki matsakaici wanda yake tsakanin taqaitawa da wuce gona da iri wato gazawa da guluwi. Irin wannan qauna ita ce aka yi mana umarni da ita da kuma riqo da ita har mu sadu da Allah Maxaukakin Sarki.

Imam Hasan Askari (a.s) yana cewa: Madaidaiciyar hanya (siratul mustaqim) ta kasu kashi biyu: Hanya (siraxi) a duniya da kuma hanya a lahira. Amma hanyar (siratul mustaqim ) duniya ita ce abin da qasa da guluwi da kuma sama da taqaitawa (rage qaunar Imamai (a.s) saboda qiyayya da sauransu)  da kuma miqewa ba tare da karkata zuwa ga vata ba, ita kuwa hanyar lahira ita ce hanyar muminai zuwa ga Aljanna, wacce take a miqe ba tare da karkata zuwa ga wuta ba, ko kuma zuwa ga wani wajen da ba aljanna ba([187]).

 

Shingayen da ke kan Siraxi:

 Siraxi na daga cikin wurare masu firgitarwa saboda wasu shingayen dake tattare da shi da dole ne a qetare su. Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Ku sani cewa dole ne ku qetare ta kan siraxi, inda taku suke karkarwa, qafafu ke zamewa, sannan kuma ga firgita da hatsari kan kowani taku...([188]).

Sheikh Saduq (r.a) na cewa: Akan siraxi akwai wasu wajajen (shingen) wahala da ake kiransu da sunayen umurce-umurcen sharia da haninta kamar su salla, zakka, sada zumunci, amana da kuma wilaya, don wanda ya gaza wajen ba wa kowani guda daga cikin waxannan abubuwa haqqinsa, to za a tsare shi a wajen inda za a tambaye shi haqqin Allah, idan ya samu kuvuta daga wajen albarkacin wani aikin alheri da ya aikata ko kuma wata rahama da ya samu, to sai ya wuce zuwa shinge na gaba. Haka zai ci gaba har sai ya kai ga gidan dawwama, inda zai rayu rayuwa da babu mutuwa cikinta, ya samu rayuwa cikin nasara da babu tavewa cikinta har abada. Idan kuwa bai samu damar wucewa ba, sai qafarsa ta zame a wajen wannan shingen, ya faxa cikin wutan Jahannama([189]).

Sheikh Mufid (r.a) yana cewa: waxannan shingaye: suna nufin ayyukan wajibi da tambayoyin da za a yi kansu, da bincike kansu, ba wai abin nufi shi ne wasu tsaunuka da za a qetare ba, aa ayyuka ne da aka kamantasu da shinge da wahalhalu. Sai aka siffanta wahalhalun da mutum zai fuskanta kafin ya kuvuta daga kura-kuransa dangane da xaa wa Allah da shingayen da za a sha fama wajen qetare su. Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

   ! !   ﴿

To don me ne bai shiga aqaba ba. Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake ce wa aqaba? Ita ce fansar wuyan bawa([190]).

 A nan Allah Maxaukakin Sarki Ya ambaci ayyukan da ya xora wa bayinSa da sunan Aqaba, yana mai misaltasu da shinge da duwatsu saboda wahalhalun da mutum ya kan fuskanta wajen aikata su kamar yadda yake wahala yayin da yake son tsallake shinge ko kuma hawa dutse.

Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Lalle a gabanku akwai kangewa mai tsanani da zango-zango masu firgitarwa da babu makawa sai kun wuce ta wurin, kun tsaya a wurin, imma dai ku samu tsira saboda rahamar Ubangiji ko kuma ku faxa wata halaka da babu sauran gyara abin da Imam (a.s) yake nufi da kangewa shi ne yanda mutum zai kuvuta daga laifukansa([191]).

 

 

BAHASI NA BIYAR: YAN ALJANNA DA YAN WUTA

Bayan hisabi da siraxi da sikeli, za a tura mutane zuwa ga makomarsu ta har abada, ko dai zuwa ga niimar Aljanna ko kuma zuwa ga azabar wutar Jahannama.

 

Na Farko: Siffar Aljanna, Mutanen Cikinta Da Kuma Niimar Da Ke Cikinta:

Siffar Aljanna:

 Gida ne da Allah Maxaukaki ya tanadar ga wanda ya sanShi da kuma bauta maSa na daga masu tsoron Allah, muminai da salihan bayi, niimar da ke cikinta kuwa ta har abada ne da ba ta da qarshe ko qarewa. Ita Aljanna gida ne na dawwama, zaman lafiya (jin daxi), babu mutuwa a cikinta, babu wahala, babu ciwo ko kuma wata annoba, babu gushewa, babu baqin ciki, babu buqata ko talauci cikinta. Ita gida ne na wadata da nasara (saada), gidan zama da karama, wahala ba ta shafan mutanen cikinta haka nan wata gajiya ba ta shafansu, a cikinta suna da ababen da ransu ke marmari kuma idanuwa su ke jin daxi, alhali suna masu dawwama a cikinta. Ita gida ne da mutanen cikinsa ke maqwabtaka da Ubangiji da waliyai da masoyanSa, maabuta karimcinSa([192]).

 

Yan Aljanna:

!  ﴿

Waxannan su ne magada. Waxanda suke gadon (Aljannar) Firdausi, su a cikinta madawwama ne([193]).

Alqurani mai girma ya siffanta masu samun nasarar shiga cikin niima da mulki mai girma (aljanna) da cewa su ne waxanda suka yi imani da kuma aikata ayyukan qwarai, waxanda suka ji tsoron Ubangijinsu, waxanda suka yi imani da Allah da ManzonSa, suka yi xaa wa Allah da ManzonSa, waxanda suka yi haquri saboda Allah da neman yardarSa, suka tsai da salla, suka ciyar daga abin da Allah Ya arzurtasu a bayyane ko a voye, waxanda su ne siddiqai da shahidai, waxanda suka nemi shiriyar Ubangiji, waxanda suka yi imani, suka yi hijira suka yi jihadi saboda Allah, waxanda suka ji tsoron matsayin Ubangijinsu suna hana kansu bin son zuciyarsu, waxanda suka ce Allah ne Ubangijinmu sannan suka tsaya qyam, waxanda suka yi hijira don Allah kana aka kashe su ko kuma suka mutu, kuma bayin Allah mukhlisai, waxanda suka yi imani da ayoyin Allah alhali suna musulmai, da waxanda suka biyo bayansu na daga iyaye, mataye da zuriyarsu muminai, da kowani mai komawa ga Allah mai tsare (umarninSa), wanda ya ji tsoron Mai rahama (Allah) a voye, ya zo da tsarkakakkiyar zuciya([194]).

Yayin da yake siffanta abin da yan Aljanna suka aikata a nan duniya, ta hanyar faxin Allah Maxaukakin Sarki:

  ﴿

Kuma aka kora waxanda suka bi Ubangjinsu da taqawa zuwa Aljanna, jamaa-jamaa([195]),

Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Sun tsira daga azaba, zargin aikata laifi ya yanke an nesanta su daga wuta. Makomarsu za ta kasance cikin kwanciyar hankali sannan kuma za su amince da makomarsu. Waxannan su ne mutanen da ayyukansu a duniya suka kasance tsarkaka, idanuwansu suka kasance masu zubar da hawaye, dararensu a duniya suka kasance (tamkar) rana saboda tsoron Allah da neman gafara, ranakunsu kuma suka kasance kamar darare saboda kaxaitaka. Don haka, Allah Ya sanya Aljanna ta kasance musu makoma sannan kuma lada don saka musu alhali sun kasance mafi dacewa da ita, kuma maabutanta cikin mulki na har abada da niima dawwamammiya([196]).

 

Rabe-Raben 'Yan Aljanna:

Sheikh Mufid ya bayyana cewar mazauna cikin Aljanna sun kasu kashi uku, su ne:

1-     Wanda aikinsa ya kasance don Allah kawai, wannan zai shige ta cikin aminci daga azabar Allah.

2-     Wanda ya haxa kyawawan ayyuka tare da munana, yana mai jinkirta neman gafara, sai mutuwa ta riske shi kafin hakan alhali yana cikin tsoron uquba wanda ake gaggautata da wanda ake jinkirtawa, ko kuma wanda ake gaggautawan ban da wanda ake jinkirtawa, ya shiga Aljanna bayan afuwa ko kuma uquba.

3-     Wanda Allah Ya sanya su cikinta ba tare sun aikata wani aiki a duniya ba, su ne yara na dindindin, waxanda Allah Taala Ya tanade su don hidima ga yan Aljanna a matsayin lada ga masu aiki. Hidimar  ta su ba za ta kasance wahala gare su ba saboda xabi'ar da aka halicce su da ita kenan([197]).

 

Siffar Niimar Aljanna:

An qawata Aljanna da nauoi daban-daban na jin daxi da niimomi, mazaunan cikinta kuwa suna da dawwamammiyar niima da farin ciki, suna da dukkanin abubuwan da suke so ko kuma suke marmarinsa a cikinta. Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

  ﴿

A cikinsu akwai abin da rayuka ke marmari kuma idanu su ji daxi([198]),

 sannan Yana cewa:

  ﴿

Suna da abin da suke so a cikinta, kuma tare da Mu akwai qarin niima([199]).

Kalmomi ba za su iya siffanta abubuwan da ke cikin Aljanna ba, akwai kuma abubuwan da mutum bai ma tava jinsu ba waxanda Allah Maxaukakin Sarki Ya tanadar wa bayinSa masu taqawa. Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

﴿

Saboda haka wani rai bai san abin da aka voye musu ba,  na sanyin idanu, domin sakamako ga abin da suka kasance suna aikatawa([200]).

A cikin hadisin Qudsi: Allah Taala na cewa: Na tanadar wa bayiNa salihai abin da idanuwa ba su tava gani ba, kuma kunne bai tava ji ba sannan kuma ba su tava zuwa ga zuciyar xanAdam ba([201]).

 

Jin Daxin Da Ake Jinsu:

 Ladar yan Aljanna sun haxa da ababen ci da na sha, da ababen kallo da kuma aure da abubuwan da suke iya riska waxanda  bisa xabi'a suna karkata zuwa gare su kuma suna samun biyan buqata tare da su([202]).

Ga wasu daga cikin waxannan ababen jin daxi dake cikin Aljanna kamar yadda Alqurani mai girma ya yi bayaninsu:

 

1- Ababen Ci Da Sha:

An arzurta yan Aljanna da arziqi mai yawan gaske ba tare da hisabi ba, da kuma wadataccen abinci da abin sha da zuciya ke marmari ba tare da ya qare ba. Sannan kuma ga yayan itatuwa daban-daban sai wanda suka zava, ba sa yankewa kuma ba a hana xibansu, inuwansu na kusa da kansu, an hore musu nunannun yayan itatuwan([203]).

Har ila yau a cikinta suna da ababen sha masu tsarki, za a shayar da su giyar da aka rufe da al-miski, ba ta sa ciwon kai, ba ta gusar da hankali. Bat a sa yasassar magana kuma babu jin nauyin zunubi, za a zagaya musu da kofi cike da ita fara sol maabuciya daxi, an haxa ta da nauoi daban-daban na kayayyakin qamshi kamar su kafur da zanjabil (citta mai yatsu). A cikinta (aljanna) akwai qoramu da idanuwan ruwa masu yawa, akwai qoramun ruwa waxanda ba gurvata gare shi, da qoramun nono da xanxanonsu bai sauya ba, da qoramun giya masu daxi ga masu sha, da kuma qoramu na tacecciyar zuma, za su sha daga idanuwan ruwa masu daxi kamar tasnim da salsabil. Za a ce musu: ku ci ku sha, madalla da abin da kuke aikatawa([204]).

 

2- Tufafi da Ababen Ado:

 A Aljanna za a tufatar da muminai da tufafi kore na mafi xaukakan hariri da siliki daga alharini mai taushin gaske da mai walqiya, ana qawata su a cikinsu, da waxansu mundaye na zinari da luu-luu da azurfa([205]).

 

3- Morar Ababen Kallo:

 Yan Aljanna za su mori ababen kallo masu jan hankula suna kishingixe bisa karagu da aka sanya su gavar qoramu masu gudu qarqashin inuwa dawwamamma. Ba sa ganin rana a cikinta ko kuma jaura (sanyi mai cutarwa, suna kallon shinfixaxxen ruwa da idanuwan ruwa masu gudanya, da lambunan dabino da inabi da rummani, itatuwa xanyu shataf da 'ya'yansu suke reto([206]).

 

4- Morar Fadojinta:

 Muminai za su shiga Aljanna mai faxin gaske da faxinta kamar sammai da qassai, an bubbuxe qofofinsu gare su, Malaiku suna gadinsu cikin shirin tarbansu, suna da darajoji mabambanta, xaya kan xaya gwargwadon kyan ayyukan da mutum ya aikata, cikin fadoji da xakunan Aljanna. Akwai wuraren zama masu kyau madawwama da xakuna da aka gina wasu xakunan a samansu, qoramu suna gudana a qarqashinsu, an shimfixe su da shimfixu masu kyau, cikinsu alhariri mai walqiya ne, suna gishingixe kan manyan fululluka suna masu fuskantar juna, ana kewayawa a kansu da akussa na zinariya da kwanuka na azurfa da kofuna da shantula da hinjalai cike da ababen da marmarinsu([207]).

 

5- Yara Madawwama:

 Yan Aljanna za su mori hidima maras yankewa da wasu yara da Allah Ya halicce su da matuqar kyau ga ado mai xauke hankali. Allah Na cewa:

﴿  

Kuma wasu yara samarin dindindin na kewayawa a kansu, idan ka gan su, za ka zaci su luu-luu ne wanda aka watsa([208]).

 

6- Mata da Hurrul Ini:

Yan Aljanna suna da tsarkakan mata na daga hurul in (masu fararen idanuwa matayen Aljanna) da aka tsare cikin haimomi. Allah Ya sanya su masu tsananin son mazajensu, masu taqaita ganinsu gare su kawai ban da wasunsu, cikakku tsarar juna a shekaru, budurwai babu wani mutum ko aljanni da ya xebe musu budurcinsu, maabuta kyau, tamkar yaqutu da murjani ko kuma kamar luu-luun da aka voye([209]).

 

Jin Daxi Na Ruhi:

 Baya ga waxannan abubuwa na jin daxi (da aka ambata a baya), yan Aljanna za su sami jin daxi na ruhi, wanda shi ne yardar Allah da gafara da rahamarSa gare su, da kuma farin cikin da za su ji sakamakon tarbar da Malaiku suka yi musu, da abubuwan da aka tanadar musu na har abada, da kuma samun aminci daga tsoron azaba da baqin ciki da dukkan wani wargi da qarya da hassada da qiyayya([210]).

 

 

Na Biyu: Siffar Wuta, Yan Wuta Da Kuma Azabobin Dake Cikinta:

Siffar Wuta:

 Wuta ita ce gidan wulaqanci, gidan xaukan fansa akan kafirai da masu savo. Alqurani mai girma ya siffantata da cewa ita kurkuku ce, da ke kewaye da kafirai, akwai shamaku kewaye da ita, kuma ita abar rufewa ce, cikin ginshiqai miqaqqu tana da inuwa mai rassa uku sai dai ba inuwa ce mai wadatarwa ba daga tsananin zafin wuta da balbalinta ba, kuma makamashinta mutane da duwatsu ne, qishirwar cikinta ba ta qarewa,  duk lokacin da wutar ta lafa sai ta qara tsanani, Malaiku masu tsanani ne ke gadinta waxanda aka ba su wakilcin gudanar da azaba, ba sa sava wa umarnin da Allah Ya yi musu, kuma suna aikata abin da aka umarce su, tana da qofofi bakwai, kowace qofa na da nata azabar da aka tanada([211]).

Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Jahannama tana da qofofi bakwai xaya na kan xayana qasa ita ce Jahannama, a samanta akwai Lazza, a samanta kuma akwai Huxama, a samanta akwai Saqara, a samanta akwai Jahim, a samanta akwai Sair, a samanta kuma akwai Hawiya.

A wata ruwayar kuma: Ta qasanta ita ce Hawiya, ta samanta kuma Jahannama([212]).

Yayin da yake siffanta ta (wuta) yana cewa: Ku ji tsoron wutar da qarqashinta ke da nisa, zafinta kuma yake da tsanani, azabarta kuwa sabuwa ce, gidan da babu rahama a cikinsa, baa jin kira a cikinsa sannan kuma ba a yaye baqin ciki([213]).

 

Yan Wuta:

 Allah Maxaukakin Sarki Na cewa:

﴿   

Waxannan su ne waxanda suka sayi vata da shiriya, kuma azaba da gafara. To, me ya yi haqurinsu a kan Wuta([214]).

Yazo cikin ayoyi da yawa cewa an tanadi wuta ne ga waxanda suka kafirta sannan kuma suka zamanto masu toshiya ga tafarkin Allah suka kuma mutu alhali suna kafirai, da kuma mushirikai waxanda suka qirqiri kishiya ga Allah, da munafukai, da masu girman kai, da azzalumai, da xawagitai, da masu qaryata Allah da ManzanninSa, da masu sava wa Allah da ManzonSa, suka juya wa Allah baya, suka qetare haddodinSa, suka yi girman kai daga bauta maSa, suka kange mutane daga tafarkinSa, suka juya baya daga ambaton Allah, ba sa fatan saduwa da Shi, da masu qaryata Ranar Lahira, waxanda suka yarda da rayuwar duniya da qawace-qawacenta da fifitata a kan Lahira, da wanda ya yi tsiwurwurin mugun abu, kuma laifinsa ya kewaye shi, da wanda ya yi ridda daga addininsa ya mutu kafiri, da wanda ke cin dukiyar mutane ba bisa haqqi ba, ko kuma yake cin dukiyar marayu bisa zalunci, da kuma wanda ya kashe mumini da gangan, da waxanda ke tara zinare da azurfa kuma ba sa ciyar da su bisa tafarkin Allah, da shugabannin zalunci da vata, da masu barin (wulaqanta) salla([215]).

Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Haqiqa na ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: A ranar lahira za a zo da azzalumin shugaba ba shi da mataimaki ko mai gabatar da uzurinsa, sai a jefa shi cikin Jahannama, zai dinga juyawa a cikinta kamar yadda dutsen niqa ke juyawa, daga nan sai a xaure shi a qarqashinta([216]).

Har ila yau daga gare shi (a.s) yayin da yake waazi ga sahabbansa yana cewa: Ku riqi salla kuma ku kiyaye ta, ku yawaita ta (yin salla), sannan ku nemi kusanci (ga Allah) ta hanyarta, don ita ta kasance a kan muminai farilla mai qayyadaddun lokuta([217]), ashe ba ku ji amsar yan wuta ba lokacin da aka tambaye su Me ya shigar da ku cikin Saqara? Suka ce, Ba mu kasance muna a cikin masu salla ba([218])?.

 

Masu Dawwama Cikinta: Babu masu dawwama cikin wuta face maabuta kafirci da shirka, amma maabuta zunubi daga cikin masu kaxaita Allah, za a fitar da su saboda rahamar (Allah) da za ta shafe su ko kuma ceton da za su samu (daga wajen wasu bayin Allah)([219]).

Imam Musa bn Jaafar al-Kazim (a.s) yana cewa: Ba wanda zai dawwama cikin wuta face maabuta kafirci da musantawa, da maabuta vata da shirka([220]).

 

Azabar Wuta: Yan wuta za su fuskanci nauoi daban-daban na azabar jiki da ta ruhi, Allah Maxaukakin Sarki Ya siffanta azabarta da cewa mai tsanani da wahala ce. Lokacin da za a tunkuxa qeyar yan wuta qungiya-qungiya zuwa wuta, za su gamu da Malaikun azaba:

Ku shiga ta qofofin wuta kuna masu dawwama cikinta, tir da makomar maabuta girman kai. Sannan wutar tana jiransu tun daga waje mai nisa, idan ta hango su za ta yi fushi da ruri kamar namijin zakin da ya ga abin da yake son kamawa daga nesa.

Za a buxe musu qofofin, za a kira su a cikinta tare da shaixanu da ababen da suka kasance suna bauta musu savanin Ubangiji, sai su kasance tsakuwar Jahannama kuma makamashin Saira. Idan an jefa su a cikinta, sai su ji daga gare ta wata qara tana tafasa, tana kusa tatssage domin fushi, sai wutanta ta qaru, sai ta qara ci, tarsatsinta ya watsu, harshenta ya tashi sama, alhali suna cikinta, cinsu daga cikinta ne, haka shansu da tufafinsu, ita ce gadon kwanansu ita ce kuma rufinsu, suna rufuwa da zafinta suna shimfixa shi, su yi ta yin makyarkyata a tsakankanin xabaqoqinta, azaba tana shafarsu daga samansu da kuma qasan tafin qafafunsu, cikin yankuna na wuta da kuma riguna na kwalta, za ta qona fuskokinsu, fuskarsu ta yi baqa qirin.

Za su kasance cikin wannan azaba har abada, mutuwa za ta zo musu da kowani waje amma su ba masu mutuwa ba ne, ba za a musu rangwami daga azabarta ba, kuma ba za jinkirta musu ba, duk lokacin da fatunsu suka nuna sai a sauya musu da waxansu don a sabunta musu azaba, kuma duk lokacin da suke son fita saboda wahala sai a mayar da su cikinta, a ce musu: ku xanxani azaba mai quna.

Sannan su suna xaure ne cikin sarqoqi a wuyansu, an tattara su a waje mai qunci, sannan a ja su da fuskokinsu cikin zafin (wuta), a kama kwarkaxarsu da sawayensu, sannan ana babbaka su cikin wuta, za a farfasa goshinansu da gwalmomin duka na baqin qarfe. Azabar iska mai zafi tana jiransu, da itaciyar zaqqum, da ruwan zafin da ake zubo shi daga saman kawukansu, abin da ke cikinsu da fatarsu ya narke.

Idan sun nemi taimako saboda tsananin qishirwan (da suke fama da ita), sai a kawo musu xauki da ruwan xiwan (qurji) suna kurvarsa amma da qyar suke haxiye shi, ko kuma a kawo musu tafashasshen ruwa da zai yayyanka hanjinsu, ko kuma da wani ruwa kamar narkakkiyar dalma, yana toye fuskoki yana tafasa a cikin ciki kamar tafasar ruwa, ba za su xanxani wani sanyi ko kuma abin sha ba face tafasasshen ruwa da ruvavven jini, haka duk da kuwa za su sha shi tamkar shan raquma masu jin qishirwa.

Idan kuwa sun buqaci abinci saboda tsananin yunwa, sai a ciyar da su abinci mai shaqewa da aka girka shi daga ruwan gyambo da (itaciyar) zaqqum, wacce ta ke tsirowa daga qarqashin (wutar) Jahim, gundarta ('ya'yanta) kamar kawukan  Shaixanu ne, duk da hakan kuwa za su ci, suna masu cika cikinsu da shi. Daga nan su sha daga ruwa mai zafin gaske.

Za su yi ta zabga kuwwa tsakankanin xabaqoqinta saboda tsananin azaba, alhali (wutar) tana tafasar abin tafasawa. Sai numfashi, kuka, ihu da husumarsu da tsinuwarsu su qaru, amma ina ba za a saurare su ba([221]).

Yayin da yake siffanta azabarta (wuta), Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Amma maabuta savon, (Allah) Zai sanya su cikin mafi munin gida, zai xaure hannayensu da wuyayensu, za a haxa kwarkwadarsu da sawayensu, sannan a tufatar da su da riguna na kwalta da yankuna daga wuta, cikin azaba da zafinta ya tsananta, da kuma qofar da aka rufe ta akan maabutanta, cikin wutan da ke cike da ihu da kuka da harshen wuta mai tashi da kuma muryoyi masu ban tsoro. Maabutanta ba za su fita daga cikinta ba sannan kuma ba fansar fursunanta haka nan kuma ba za a tsinka sarqoqinta ba. Babu wani wa'adi ga wannan gida ballanta ya qare, sannan kuma ba wani ajali ga mutanenta ballantana ya kai qarshensa([222]).

 

Azabarta ta Ruhi: Alqurani mai girma ya yi bayanin kan yanayi daban-daban na azabar, da suka haxa da: jin hasara, zargin kai, baqin ciki, tsoro da firgita. Azzalumai za su yi ihun nadama, nadama rashin samun Aljanna da niimominta, da kuma nadama rashin saduwa da Ubangiji da samun yardarSa, yanke qauna daga rahama da gafarar Ubangiji zai dinga damunsu. Sai qasqanci da wulaqanci su rufe su yayin da ake wucewa da su cikin wuta suna kallo da gefen ido a voye([223]).

Lokacin da aka gabatar da su ga wuta suka ga azabarta qeqe da qeqe, zuciyarsu za ta karaya saboda tsananin nadama, sai su bayyanar da barrantansu ga manya da shugabanninsu, nan take sai fata ta dinga zuwa masu, suna cewa:

﴿

Kaitonmu, saboda rashin biyayyarmu ga Allah da rashin biyayyarmu ga Manzo([224]),

 kowani guda daga cikinsu zai ce:

                  ﴿

Kaitona, da na gabatar (da aikin qwarai) domin rayuwata([225]),

  ﴿

Ya kaitona! (da ace dai) ban riqi wane masoyi ba!([226]).

To me amfanin nadama alhali suna cikin Ranar Mai Wahala.

Suna ihu da baqin cikin hasara kan abin da suka aikata a duniya, don haka za su buqaci dawowa cikinta, don su aikata ayyukan qwarai su kasance cikin muminai. Za su xaga murya su ce:

 ﴿

Saboda haka da lalle muna da (damar) komawa, domin mu kasance daga muminai([227]),

 za su xaga sautinsu da yin ihun cewa:

﴿

Ya Ubangijinmu! Ka fitar da mu, mu aikata aiki mai kyau, wanin wanda muka kasance muna aikatawa([228]).

Amma ina wannan fata ta su ba ta wuce kawalweniya ba, saboda a halin yanzu suna duniyar sakamako ne, duniyar da biyayya da komawa ga Allah da nadama ba su amfani. Da da gaske suke da tun suna duniyar aiki sun koma ga Allah da neman gafararSa Maxaukakin Sarki 

    ﴿

Kuma da an mayar da su, lalle da sun koma ga abin da aka hana su daga barinsa. Kuma lalle ne su, haqiqa, maqaryata ne([229]).

Daga nan sai a amsa musu:

﴿

To ku xanxani azaba saboda abin da kuka kasance kuna yi na kafirci[230],

 sai a ce musu:

  ﴿

Ku tafi (da wulaqanci) a cikinta. Kada ku yi mini magana([231]).

 Wannan yana qara musu yankewar zuciya da jin cewa sun yi hasara da kuma yankewar qaunar rahama da gafara, ta haka za su isa Jahannama suna a matsayin abin zargi, abin korewa.

Abin da zai qara sosa musu rai shi ne gatsen da Malaiku za su yi musu daga shigowarsu wuta. Allah Na cewa:

  ﴿

Koda yaushe aka jefa wani vangaren jamaa a cikinta, matsaranta na tambayar su da cewa Wani mai gargaxi bai je muku ba?,

 sai su amsa, suna iqirari, da cewa:

﴿ !  !

E, lalle wani mai gargaxi ya je mana, sai muka qaryata shi, muka ce: Allah bai saukar da kome ba, ba ku cikin kome sai vata babba. Kuma suka ce, Da mun zamo muna saurare, ko muna da hankali, da ba mu kasance a cikin yan Sair ba. Wato suka yi iqirari da laifinsu. Allah Ya laani yan Sair!([232]).

Lokacin da suka yanke qauna, sai su ce wa mai gadin wuta:

  ﴿

Ya Maliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana,

 sai ya ce musu:

  ﴿

Lalle ku mazauna ne (a cikinta)([233])

Allah Ya tsare mu gaba xaya daga sharrin Jahim da firgicin Ranar Qiyama, Ya arzurta mu da rahamarSa da ta mamaye kome, da ceton AnnabinSa Zavavve da tsarkakan Iyalan gidansa, tsira da amincin Allah su tabbata gare su.

 


([1]) . Man La Yahdhuruhul Faqih na Saduq 1:80/362 Darul Kutub al-Islamiyya Beirut.

([2]) . Kanzul Ummal na Muttaqi al-Hindi 15:548/42123.

([3]) . Gurar al-Hikam na al-Amdi 1:23/371.

([4]) . Suratu Ghafir 40:68.

([5]) . Suratus Sajda: 32:11.

([6]) . Suratul Anam 6:61.

([7]) . Suratuz Zumar 39:42.

([8]) . Man La Yahdhuruhul Faqih na Saduq 1:82/371.

([9]) . Suratul Jumaa 62:8.

([10]) . Nahjul Balaga Huxuba ta 221.

([11]) . Al-Khisal na Saduq:119/108, Bihar al-Anwar 6:159/19.

([12]) . Suratul Nahl 16:32.

([13]) . Suratul Anfal: 8:50-51, sannan a duba Suratun Nahl 16:28-29 da Suratu Muhammad 47:28.

([14]) . Suratu Qaf:50:19.

([15]) . Nahjul Balaga, huxuba ta 83.

([16]) . Kanzul Ummal na Muttaqi al-Hindi 15:569/42208.

([17]) . Suratul Waqia 56:83-87

([18]) . Nahjul Balaga, huxuba ta 109.

([19]) . Amali na Tusi: 432/967.

([20]) . Man La Yahdhurulhul Faqih na Saduq 1:81/366, Al-Kafi na Kulayni 3:134/11.

([21]) . Dubi Tashih al-Iitiqad na Sheikh Al-Mufid:95.

([22]) . Maanil Akhbar na Saduq: 287/1, Ilal al-Shara'i'i na Saduq: 1:248 babi na 235/hadisi na 2, al-Aqaid na Saduq: 54.

([23]) . Suratu Qaf: 50:22.

([24]) . Musnad Ahmad 2:51 Darul Fikr Beirut, Ihya al-Ulum na Gazali 5:316 Dar al-Waayi Halab da Kanzul Ummal na Muttaqi al-Hindi 15:641/42529.

([25]) . Al-Amali na Mufid 263-264.

([26]) . Man la Yahdhuruhul Faqih na Saduq 1:82-83/373, al-Kafi na Kulayni 3:231/1. Akwai cikakken bayani cikin manyan litattafa, ba buqatar mu faxaxa.

([27]) . Suratun Nisa: 4:159.

([28]) . Sharh Ibn Abil Hadid 1:299-300 (huxuba ta 20)

([29]) . Lisan al-Arab na Ibn Manzur Barzakh 3:8.

([30]) . Tafsir al-Mizan na Tabataba'i 1:349.

([31]) . Suratul Muminun 23:100

([32]) . Tafsir al-Qummi 1:19, Bihar al-Anwar na Majlisi 6:218/12.

([33]). Amali na Tusi: 28/31, Bihar al-Anwar 6:218/13.

([34]) . Nahjul Balaga Huduba ta 221.

([35]) . Al-Kafi na Kulayni 3:236/6.

([36]) . Ilal al-Shara'i: 309/4, Amali na Saduq: 468/623, Amali na Tusi: 427/955.

([37]) . Thawabul Aamal na Saduq: 197 Manshurat al-Razi Qum, Ilal al-Shara'i na Saduq 309/3, Amali na Saduq: 632/845.

([38]) . Dubi littafin Al-Kafi na Kulayni 3:232/1 da 237/7 da 238/10 da kuma 239/12, Al-Iitiqadat na Saduq: 58, Tashih al-I;itiqadat na Mufid: 99-100, Sharh al-Mawaqif na al-Jarjani 8:317-320.

([39]) . Amali na Saduq: 370/464.

([40]) .  Dubi Kashful Murad na Allamah Hilli: 452, Masail al-Sarwiyyah na Mufid:62- masala ta 5, Al-Arbain na al-Baha'i:283 da 487, Haqq al-Yaqin na Abdullah Shibr 2:68.

([41]) . Suratu Ghafir 40:45-46.

([42]) . Dubi Tafsir al-Mizan na Tabataba'i: 17:335

([43]) . Majmaul Bayan na Tabrisi 8:818.

([44]) . Suratu Taha: 20:124.

([45]) . Al-Arbain na Al-Baha'i:488.

([46]) . Sharh Ibn Abil Hadid 6:69 Darul Ihya al-Kutub al-Arabiyya Masar, Amali na Tusi: 28/31.

([47]) . Dubi al-Kafi na Kulayni 3:231, 244-245 da 253/10, Al-Mahasin na al-Barqi:174-178 Dar al-Kitab al-Islamiyya Qum, Bihar al-Anwar na Majlisi 6:202 babi na 8, Sunan al-Nisa'i 4:97-108 Kitab al-Janaiz Darul Kutub al-Arabi Beirut, Kanzul Ummal na Mutttaqi al-Hindi 15:638 da sauransu.

([48]) . Sunan al-Tirmidhi 4:640/24-60 Kitab Siffat al-Qiyama Darul Ihya al-Turath al-Arabi Beirut, Ihya Ulum al-Din na Gazali 5:316.

([49]) . Wata dabba ce mai kama da babban maciji.

([50]) . Amali na Tusi:28/31.

([51]) . Suratul Muminun 23:100

([52]) . Al-Khisal na Saduq: 120/108.

([53]) . Abin da ake nufi da duniyar misali shi ne wurin da jiki na zahiri ba shi da wani tasiri amma duk haraka tana gudana tamkar da wannan jikin. Alal misali abin da yake faruwa a mafarki.

([54]) . Al-Durrul Mansur na Suyuti 5:28.

([55]) . Al-Kafi na Kulayni 3:234/3.

([56]) . Kamar na sama 3:239/12

([57]) . Al-Arbain na Al-Baha'i:492

([58]) . Awail al-Maqalat na Mufid: 77, Tashihul Iitiqadat na Mufid: 88-89, Masail al-Sarwiyya na Mufid: 63-64 masala ta 5, Al-Arbain na al-Baha'i:504.

([59]) . Al-Tahzib na Tusi 1:466/172.

([60]) . Kamar na sama, 1:466/171. Al-Kafi na Kulayni 3:245/6.

([61]) . Al-Kafi na Kulayni 3:244/1.

([62]) . Dubi Al-Kafi na Kulayni 3:244/3 da 245/7.

([63]) . Dairat Maarif al-Qarn al-Ishirin na Wajdi 4:375.

([64]) . Tanasukh: shi ne aqidar da ke cewa idan mutum ya mutu ransa zai shiga wani jikin wato ana iya sake haihuwarsa cikin wani jiki ban da nasa kuma ya sake rayuwarsa nan duniya.

([65]) . Haqq al-Yaqin na Abdullah Shibr 2:50, al-Arbain na al-Baha'i 505, Bihar al-Anwar  6:271 da 278.

([66]) . Al-Kafi na Kulayni 3:244/4.

([67]) . Kamar na sama, 3:245/2.

([68]) . Al-Iitiqadat na Saduq: 79.

([69]) . Suratu Aali Imran:3:133.

([70]) . Suratul Baqara 2:24.

([71]) . Suratul Baqara 2:35.

([72]) . Suratun Najm: 53:15.

([73]) . Suratul Qasas: 28:88

([74]) . Suratur Raad:13:35.

([75]) . Kashful Murad na Allamah Hilli: 453. sannan kuma a duba Sharh al-Mawaqif na al-Jarjani 8:301-303.

([76]) . Lisan al-Arab na Ibn Manzur sharx 7: 329-330, Majmaul Bayan na Tabrisi 9:154, Tafsir al-Mizan na Tabataba'i 18:236, ayar kuma tana cikin Suratu Muhammad:47:18.

([77]) . Suratul Aaraf: 7:187.

([78]) . Suratul Aaraf: 7:187.

([79]) . Suratul Anam: 6:158.

([80]) . Tafsir al-Qummi 2:303, Bihar al-Anwar 6:306/6.

([81]) . Al-Khisal na Saduq: 500/1da 2.

([82]) . Suratun Naml: 27:82, mai son qarin bayani yana iya duba littafin al-Rajah na Markaz al-Risala: 27-32.

([83]) . Musnad Ahmad 3:36, Sahih ibn Habban 8:290/6284, Al-Mustadrak ala al-Sahihain 4:557.

([84]) . Suratuz Zukhruf 43:61.

([85]) . Mualim al-Tanzil na al-Bagwi 5:105 Dar al-Fikr Beirut -, al-Kasshaf na Zamakhshari 4:26, Tafsir al-Razi 27:222, Tafsir al-Qurxabi 16:105 Dar al-Ihya Turath al-Arabi Beirut, Tafsir Abi al-Saad 8:52 Dar Ihya Turath al-Arabi Beirut.

([86]) . Al-Khisal na Saduq:13/431, al-Durrul Mansur na Suyuti 6:380.

([87]) . Suratul Anbiya 21:96-97.

([88]) . Suratud Dukhan 44:10-11.

([89]) . Tafsir al-Tabari 25:68 Dar al-Maarifa Beirut.

([90]) . Al-Khisal na Saduq: 13/431, Durrul Mansur na Suyuti 6:380, Musnad na Ahmad 2:201, Jami al-Usul na Ibn Athir 11:87.

([91]) . Tafsir al-Qummi 2:304 da 306.

([92]) . Bihar al-Anwar 6: 315/24.

([93]) . Ilal al-Shara'ii na Saduq: 470.

([94]) . Suratul Hajj 22:1-2.

([95]) . Nahjul Balaga, Huxuba ta 114.

([96]) . Suratul Maarij 70:4.

([97]) . Suratuz Zumar 39:68.

([98]) . Suratu Yasin 36:49-50.

([99]) . Majmaul Bayan na Tabrisi 6:766.

([100]) . Dubi Tafsir al-Qummi 2:257, Bihar al-Anwar 6:324/2.

([101]) . Suratul Qasas 28:88.

([102]) . Nahjul Balaga, huxuba ta 186.

([103]) . Suratu Ibrahim 14:48.

([104]) . Amali na Tusi: 28/31.

([105]) . Suratu Yasin 36:51-53.

([106]) . Suratu Qaf: 50:20-21.

([107]) . Amali na Saduq 497/681.

([108]) . Suratul Maarij 70:43-44.

([109]) . Suratul Kahf 18:47.

([110]) . Suratut Takwir 81:5.

([111]) . Suratul Anam 6:38.

([112]) . Nahjul Balaga, huxuba ta 102.

([113]) . Al-Kafi na Kulayni 8:143/110.

([114]) . Suratul Haqqa 69:18.

([115]) . Suratux Xariq 86:9.

([116]) . Suratul Ghafir 40:16.

([117]) . Suratu Maryam; 19:85.

([118]) . Suratu Abasa 80:38-39.

([119]) . Suratul Hadid 57:12.

([120]) . Suratu Maryam 19:68.

([121]) . Suratul Furqan 25:17.

([122]) . Suratu Abasa 80:40-41.

([123]) . Suratul Isra: 17:97.

([124]) . Suratuz Zumar 39:69-70.

([125]) . Suratul Hijr 15:92-93.

([126]) . Suratul Aarafi 7:6.

([127]) . Al-Iitiqadat na Saduq: 74.

([128]) . Suratul Isra 17:36.

([129]) . Tafsir al-Iyashi 2:292/75.

([130]) . Al-Khisal na Saduq: 253/125. Amali na Tusi: 593/1237, al-Muujam al-Kabir na Tabarani 11:83/11177 Dar al-Ihya Turath al-Arabi Beirut, Majma al-Zawaid na Haithami 10:346 Dar Kutub al-Arabi Beirut.

([131]) . Suratul Ahzab 33:33.

([132]) . Suratu AlImrana 3:61.

([133]) . Suratush Shura 42:23.

([134]) . Sunan al-Tirmidhi 5:664/3789 Dar Ihya al-Turath al-Arabi Beirut, Hulyat al-Awliya/ Abu Naim 3:211 Dar al-Kutub al-Arabi Beirut, Tarikh al-Bagdadi na Al-Khadib 4:159 Dar al-Kutub al-Ilmiyya Beirut, Usud al-Gabah na Ibn Athir 2:13 Dar Ihya Turath al-Arabi Beirut, al-Mustadrak na Hakim 4:150 ya inganta hadisin Dar al-Maarifa Beirut.

([135]) . Suratus Saffat 37:24.

([136]) . Uyun Akhbar al-Ridha na Saduq:1:313/86, Maanil Akhbar na Saduq 67/7, al-Sawaiq al-Muhriqa na al-Haitami:149 Babi na 11 fasali na 1 yana cewa: Dailami ma ya fitar da shi, Amali na Tusi:290/564, Tafsir al-Habri:312/60 Muassasat Al al-Bait (a.s) Qum, al-Manaqib na Ibn Shahr Ashub 2:152 Dar al-Adhwa Beirut, Manaqib Aliyu bn Abi Talib (a.s) na Khawarizmi: 195 da kuma Tazkirat al-Khawas na Sibt Ibn Jawzi:17.

([137]) . Suratul Ghashiya 88:25-26.

([138]) . Tashih al-I;itiqad na Mufid:113

([140]) . Suratul Baqara 2:202.

([141]) . Tafsir Majma al-Bayan na Tabrisi 2:531.

([142]) . Suratul Miiraj 70:4.

([143]) . Tafsir Majma al-Bayan na Tabrisi 10:531.

([144]) . Nahjul Balaga, hikima ta 300.

([145]) . Al-Kafi na Kulayni 3:268/4, al-Tahzib na Tusi 2:239/946.

([146]) . Nahjul Balaga, huxuba ta 90.

([147]) . Suratu Yunus 10:61.

([148]) . Suratul Mujadala 58:7.

([149]) . Nahjul Balaga, hikima ta 324.

([150]) . Suratun Nisa 4:41.

([151]) . Suratun Nahl 16:89.

([152]) . Majmaul Bayan na Tabrisi 6:584.

([153]) . Majmaul Bayan na Tabrisi 6:586.

([154]) . Suratul Baqara 2:143.

([155]) . Suratu AlImrana 3:110.

([156]) . Tafsir al-Ayashi 1:63/114.

([157]) . Al-Kafi na Kulayni 1:146/2 da 147/4, Basair al-Darajat na Al-Saffar: 183/11 da 102/3 Muassasat al-Alami Tehran da Tafsir al-Ayashi 1:62/110.

([158]) . Suratu Qaf 50:17-18.

([159]) . Suratu Qaf 50:20-21.

([160]) . Nahjul Balaga, huxuba ta 85.

([161]) . Suratun Nur 24:24.

([162]) . Tafsir al-Mizan na Sayyid Tabataba'i 15:94.

([163]) . Suratul Infixar 82:10-12.

([164]) . Suratul Jathiya 45:28-29.

([165]) . Suratul Isra 17:13-14.

([166]) . Suratul Kahf 18:49.

([167]) . Suratuz Zalzala 99:6.

([168]) . Suratu AlImrana:3:30.

([169]) . Aradh shi ne abin da ba shi da zati, kamar launi ko tsawo, wato, samuwarsa yake buqatar wani abin da zai dogara da shi.

([170]) . Majmaul Bayan na Tabrisi 2:732, da Tafsir al-Razi 8:16.

([171]) . Dubi Tafsir al-Mizan na Tabataba'i 3:156 da 13:55.

([172]) . Suratul Anbiya 21:47.

([173]) . Suratul Kahf 18:105.

([174]) . Al-Kafi 8:75/29, Al-Amali na Saduq:598/822 Muassasat al-Biisat birnin Qum.

([175]) . Dubi littafin Kashful Murad na Allamah Hilli: 453, Tafsir al-Mizan na Tabataba'i 8:14, Haqqul Yaqin na Abdullah Shibr 2:109.

([176]) . Dubi Tashih al-Iitiqadat na Mufid: 114 da Tafsir al-Mizan na Tabataba'i 8:12-13.

([177]) . Suratul Aaraf 7:8.

([178]) . Al-Ihtijaj na Tabrisi: 351.

([179]) . Al-Ihtijaj na Tabrisi: 244.

([180]) . Suratul Anbiya 21:47.

([181]) . Al-Kafi na Kulayni 1:347/36, Maanil Akhbar na Saduq: 31/1 da kuma al-Iitiqadat na Saduq:74.

([182]) . Kashful Murad na Allamah Hilli:453.

([183]) . Al-Amali na Saduq: 242/257 da Tafsir al-Qummi 1:29.

([184]) . Ihya Ulum al-Din na Gazali 5:363.

([185]) . Maanil Akhbar na Saduq 32:1.

([186]) . Sawaiq al-Muhriqa na Ibn Hajr: 149, Manaqib Aliyu bn Abi Talib na Ibn al-Magazili 242/289, Faraid al-Simtain na al-Juwaini 1:289/228 da Al-Amali na Tusi:290/564.

([187]) . Maanil Akhbar na Saduq 33:4.

([188]) . Nahjul Balagah, huxuba ta 83.

([189]) . Al-Iitiqadat na Saduq: 71-72.

([190]) . Suratul Balad 90:11-13.

([191]) . Tashihih al-Iitiqad na Mufid: 112-113.

([192]) . Al-Iitiqadat na Saduq: 76, Tashih al-Iitiqad na Mufid:116.

([193]) . Suratul Muminun 23:10-11.

([194]) . Dubi: Suratul Baqara 2:25 da 38, Suratu AlImrana 3:198, Suratun Nisa: 4:13 da 69, Suratut Tauba 9:20, Suratur Raad 13:22-24, Suratu Taha 20:75, Suratul Hajji 22:58, Suratus Saffat 37:40, Suratu Ghafir 40:8, Suratuz Zukhruf 43:69, Suratul Ahqaf 46: Ê Ç13-14, Suratul Fathi 48:17, Suratu Qaf 50:31-33, Suratut Tur 52:21, Suratul Hadid 57:21, Suratun Naziati 79:40

([195]) . Suratuz Zumar 39:73.

([196]) . Nahjul Balaga, huxuba ta 190.

([197]) . Tashih al-Iitiqad na Mufid: 116-117.

([198]) . Suratuz Zukhruf 43:71.

([199]) . Suratu Qaf 50:35.

([200]) . Suratus Sajda 32:17.

([201]) . Kanzul Ummal na Muttaqi al-Hindi 15:778/43069, Bihar al-Anwar na Majilsi 8:191/168.

([202]) . Tashih al-Iitiqad na Mufid:117.

([203]) . Dubi: Suratur Raad 13:35, Suratul Hajji: 22:50, Suratu Yasin 36:57, Suratu Sad 38:54, Suratu Ghafir 40:40, Suratu Fussilat 41:31, Suratu Muhammad 47:15, Suratux Xur 52:22, Suratur Rahman 55:52, Suratul Waqiyya 56:21da 28-33, Suratud Dahri 76:14 da kuma Suratul Mursalat 77:42.

([204]) . Dubi: Suratus Saffat: 37:45-47, Suratu Muhammad 47:15, Suratux Xur 52:19 da 23, Suratul Waqia 56:17-19, Suratul Insan 76:5-6 da 17-18 da 21, Suratul Murasalat 77:43, Suratul Muxaffifin 83:25-28.

([205]) . Dubi: Suratul Hajji 22:23, Suratul Kahf 18:31, Suratu Fatir 35:33, Suratud Dukhan 44:53 da Suratud Dahr 76:12 da 21.

([206]) . Dubi: Suratur Raad 13:35, Suratu Yasin 36:56, Suratur Rahman 55:68, Suratul Waqia 55:30, Suratud Dahr 76:13, Suratul Mursalat 77:41 da Suratun Nabai 78:32.

([207]) . Dubi: Suratu AlImrana 3:133, Suratul Anfal 8:4, Suratut Tauba 9:72, Suratul Muuminun 21:103, Suratul Ankabuti 29:58, Suratus Saffat 37:43-44, Suratu Sad 38:50-51, Suratuz Zumar 39:20, Suratuz Zukhruf 43:71, Suratux Xur 52:20, Suratur Rahma 55:54, Suratul Waqia 56:15-18 da 34, Suratus Saf  61:12, Suratud Dahr 12:14-16 da Suratul Gashiya 88:10-16.

([208]) . Suratul Insan (Dahr) 76:19.

([209]) . Dubi: Suratu Yasin 36:56, Suratus Saffat 37:48-49, Suratu Sad 38:52, Suratud Dukhan 44:54, Suratux Xur 52:20, Suratur Rahma 55:56-58 da 72, Suratul Waqia 56:22-23 da 35-37 da Surarun Naba'i 78:33.

([210]) . Dubi Suratu AlImrana 3:15 da 136, Suratut Tauba 9:72, Suratul Hijr 15:47-48, Suratu Maryam 19:62, Suratu Fatir 35:34-35, SuratuYasin 36:55, Suratuz Zumar 39:73, Suratud Dukhan 44:56, Suratu Muhammad 47:15, Suratux Xur 52:18, Suratul Mujadala 58:22, Suratun Naba'i 78:35 da Suratul Gashiya 88:11.

([211]) . Dubi: Suratul Baqara 2:24, Suratut Tauba 9:49, Suratul Hijr 15:43-44, Suratul Isra 17:8 da 97, Suratul Kahf 18:29, Suratut Tahrim 66:6, Suratul Mursalat 77:30-31 da Suratul Humaza 104:8-9.

([212]) . Majmaul Bayan na Tabrisi 6:519.

([213]) . Nahjul Balaga, wasiqa ta 27.

([214]) . Suratul Baqara 2:175.

([215]) . Dubi: Suratul Baqara 2:81 da 86 da 161-162 da 217, Suratun Nisa 4:10 da 14 da 56 da 93 da 145, Suratut Tauba 9:34 da 63, Suratu Yunus 10:7-8 da 52, Suratu Hud 11:15-16, Suratun Nahl 16:85, Suratul Kahf 18:102-106, Suratu Taha 20:74 da 124-127, Suratul Furqan 25:11, Suratus Sajda 32:12-14, Suratuz Zumar 39:60 da 71-72, Suratu Ghafir 40:60 da 70-72, Suratu Qaf 50:24-26, Suratul Jinni 72:17 da 23, Suratul Mudassir 74:41-46 da Suratun Naziat 79:37-39.

([216]) . Nahjul Balaga, huxuba ta 164.

([217]) . Suratun Nisa 4:103.

([218]) . Nahjul Balaga, huxuba ta 199, ayar kuma tana cikin Suratul Muddathir 74:42-43.

([219]) . AlIitiqadat na Saduq:77.

([220]) . Al-Tauhid na Saduq 407/6 bugun Jamaat al-Mudarrisin Qum.

([221]) . Dubi: Suratul Baqara 2:90 da 104 da 114, da 164, Suratun Nisa 4:56, Suratul Anam 6:70, Suratul Aaraf 7:41, Suratu Ibrahim 14:16-17 da 49-50, Suratul Kahf 18:29, Suratu Taha 20:74, Suratul Anbiya 21:98-100, Suratul Hajj 22:19-22, Suratul Muminun 23:104, Suratul Furqan 25:12-14, Suratul Ankabut 29:54-55, Suratul Ahzab 33:64-68, Suratu Fatir 35:36-37, Suratus Saffat 37:62-68, Suratu Sad 38:55-64, Suratuz Zumar 39:71, Suratu Gafir 40:70-76, Suratud Dukhan 44:43-55, Suratu Muhammad 47:15, Suratux Xur 52:13-16, Suratul Qamar 54:47-48, Suratur Rahman 55:41-44, Suratul Waqia 56:41-44 da 51-56, Suratul Mulk 67:5-11, Suratul Haqqa 69:31-37, Suratul Muzammil 73:12-13, Suratud Dahr 76:4, Suratul Mursalat 77:30-33, Suratun Naba 78:21-30, Suratul Lail 92:14-16 da Suratul Humaza 104:4-9.

([222]) . Nahjul Balaga, huxuba ta 109.

([223]) . Dubi: Suratul Baqara 2:161 da 166-167, Suratul Anam 6:27-31 da 124, Suratul Aaraf 7:53, Suratu Ibrahim 14:44, Suratul Isra 17:18 da 39, Suratul Muminun 23:103-108, Suratush Shuara 26:95-102, Suratul Ankabut 29:23, Suratul Ahzab 33:66-68, Suratus Saba 34:33, Suratu Fatir 35:36-37, Suratuz Zumar 39:71, Suratu Gafir 40:73-76, Suratush Shura 42:45, Suratuz Zukhruf 43:77, Suratul Mulk 65:17 da Suratul Muxaffifin 83:15-17.

([224]) . Suratul Ahzab 33:66.

([225]) . Suratul Fajr 89:24.

([226]) . Suratul Furqan 25:28.

([227]) . Suratush Shuara 26:102.

([228]) . Suratu Faxir 35:37.

([229]) . Suratul Anam 6:28.

([231]) . Suratul Muminun 23:108.

([232]) . Suratul Mulk 67:8-11.

([233]) . Suratuz Zukhruf 43:77. Bisa laakari da cewa bahasin qarshe galibi ya qunshi bayani kan siffofi wuta da Aljanna ne daga muka ciro daga Alqurani mai girma, don haka muke ganin ya kamata mu kawo masdarorin hadisai ma ga wanda ke son qarin bayani kan niimomin da ke Aljanna da kuma azabobin da ke wuta. Don haka mai so yana iya komawa ga: Bihar al-Anwar na Majlisi 8:116-222 da 329-380 da Ihya Ulum al-Din na Gazali 5:385-392 da 374-381.

 

عنوان الکتاب