FASALI NA FARKO

 

Ma'anar Makoma Da Tasirin Imani Da Ita

 Bahasi Na Farko: Ma'anar Makoma.

Makoma A Yare: Duk wani abin da ke komawa gare shi. Shi masdari ne na fi’ilin ada ya'udu, audan, Audatan da kuma ma'adan; wato ya koma gare shi, Allah Maxaukaki Na cewa:

﴿ ßóãóÇ ÈóÏóÃóßõãú ÊóÚõæÏõæäó ,

"…Kamar yadda Ya fara halittarku kuke komawa([1])".

Mafari wanda ake komawa gare shi: Na daga cikin siffofin Allah Ta’ala, saboda Allah Maxaukakin Sarki Shi ne Ya fari halitta, sannan Ya kashe su sannan kuma Ya dawo musu da rayuwa Ranar Qiyama. Allah Maxaukaki Na cewa:

 ﴿ æóåõæó ÇáøóÐöí íóÈúÏóÃõ ÇáúÎóáúÞó Ëõãøó íõÚöíÏõåõ æóåõæó Ãóåúæóäõ Úóáóíúå ö  

“Kuma Shi ne Wanda Ya fara halitta, sa’an nan Ya sake ta, kuma sakewarta ta fi sauqi a gare Shi…([2]).

Makoma A Isxilahi (a Ilmi): Ita ce samuwa ta biyu ta jikkuna da dawo da su bayan mutuwa da dagargajewarsu([3]).

Har ila yau kuma ana fassara ta da komawa zuwa ga samuwa (rayuwa) bayan gushewa, ko kuma komawa (haxuwar) vangarori na jiki bayan rarrabuwansu, komawa zuwa ga rayuwa bayan mutuwa, ko kuma komawar ruhi zuwa ga jiki bayan rabuwa da shi([4]). Wannan dai ita ce fassarar da aka tafi a kai, amma an sami savani kan ko komawar ta ruhi ce kaxai ko kuma har da jiki. Malaman falsafa sun tafi a kan cewa dawowa ta ruhi ce kawai saboda riqo da qa'idarsu mai cewa: Dukkan abin da ya gushe ba ya dawowa. Suna masu cewa tun da dai jikkuna sukan gushe bayan mutuwa, to ba zai yiwu su dawo ba. Saboda haka sun xauka cewa makoma (tashin qiyama) da dukkan abubuwan da suka ta'allaqa da ita, sun shafi ruhi kaxain da ba ya gushewa.

Su kuma masu cewa makoma ta shafi jiki, wato jama’ar musulmi bai xaya, waxanda suka haxa da malaman aqida da na fiqihu da hadisi da kuma sufaye, sun yi amanna da dawowar jikkuna ranar tashin qiyama, kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki Ya faxi.

To sai dai kuma akwai savani tsakanin waxannan malamai kan makomar ruhi bayan mutuwa, inda suka rabu kashi biyu, saboda savanin da suka samu wajen fassarar ma'anar ruhi: Kashin farko daga cikinsu suna ganin cewa ruhi wani jiki ne mai gudana a jiki kamar gudanar wuta a cikin gawayi ko kuma ruwa cikin fure. Don haka makomar jiki da ruhi a wajensu ita ce makoma ta jiki (wato za a komo da jiki ne). Xaya vangaren kuma, wanda ya haxa da da dama daga cikin ma'abuta hikima da malaman aqida da arifai, yana ganin cewa ruhi mujarradi ne (wato ba jiki ba ne) kuma yana dawowa cikin jiki bayan tayarwa. Don haka makoma a wajensu ta jiki ce kuma ta ruhi ce. Saboda haka ne maganganu kan makoma suka rabu zuwa kashi uku: ta ruhi, ta jiki da kuma ta jiki da ruhi lokaci guda([5]).

 

Bahasi Na Biyu: Tasirin Imani Ga Makoma:

Kafin bayani kan tasirin imani da kuma yarda da makoma, yana da kyau mu san cewa Allah Maxaukakin Sarki bai wajabta mana yin imani da ranar lahira da abubuwan da ke cikinta na tsananin hisabi da bayyanar sakamakon ayyuka ba a matsayin wata hanyar tsawatarwa kan aikata sharri da munanan ayyuka a nan duniya da kuma kwaxaitarwa ga ayyukan alheri da shiriya kaxai ba. A’a Ya wajabta shi ne saboda ranar lahira wani tabbataccen al’amari ne mai samuwa na haqiqa, kuma saboda cewa imani da makoma imani ne da wani tabbataccen lamari da kuma miqa wuya ga hukumcin da ba makawa gare shi. Allah Maxaukakin Sarki na cewa:

﴿ æÞÇá ÇáÐøóíäó ßóÝóÑõæÇ áÇó ÊóÃúÊöíäóÇ ÇáÓøóÇÚóÉõ Þõáú Èóáóì æóÑóÈøöí áóÊóÃúÊöíäøóßõãú ÚóÇáöãö ÇáúÛóíúÈö áÇóíóÚúÒõÈõ Úóäúåõ ãöËúÞóÇáõ ÐóÑøóÉò Ýí ÇáÓøóãóÇæóÇÊö æÇáÃóÑúÖö æáÇó ÃóÕúÛóÑõ ãöäú ÐÇáößó æáÇó ÃóßúÈóÑõ ÅáÇøó Ýí ßöÊóÇÈò ãøõÈöíäò

"Kuma waxanda suka kafirta suka ce, "Sa'a ba za ta zo mana ba". Ka ce, "Kayya! Na rantse da Ubangijina, lalle, za ta zo muku". Masanin gaibi, gwargwadon zarra ba ta nisanta daga gare Shi a cikin sammai, kuma ba ta nisanta a cikin qasa, kuma babu mafi qaranci daga wancan kuma babu mafi girma face yana a cikin Littafi bayyananne”([6]).

Amma abin da ke biye da imani da makoma, na daga tsayuwa akan iyakokin shari'a da kiyaye hukumce-hukumcenta – da abubuwan da suke biyo baya masu amfanar mutum da al'ummar da yake ciki, ta vangaren kula da kyawawan xabi'u ko kuma ta vangare gina kai ko kuma kyautata xabi’un qwarai ta yadda za su kai ga kamala– wani reshe ne na wancan tushe da kuma abubuwan da ya haifar wanda ke nuna mana kaxan daga cikin hikimar Ubangiji wajen farlanta jiga-jigan aqida da hukumce-hukumce, tare da amfanin da waxannan abubuwa suke da shi ga xan'Adam duniya da lahira da kuma gudummawarsu wajen tsara rayuwar xan’Adam mafi kyan tsari. Bari mu kawo kaxan daga cikin irin waxannan tasirin:

 

Na Farko: Tasirin Makoma A Vangaren Xabi'a:

A fili yake cewa buqatar mutum ta shiriya na daga cikin abubuwan da suka wajabta aiko Annabawa kuma hakan ya yi daidai da hikimar da Ubangiji Ya gudanar wajen halitta shi. To sai dai ba za a iya tsayar da asasin wannan shiriya ba matuqar dai ba a haxa ta da wani qarfi mai zartarwa ba, wanda zai tilastawa mutum bin hikimar, don wannan koyarwa da hukumce-hukumce na Ubangiji su fita daga da'irar nazari zuwa ga fagen aiki, sai su jagoranci mutum zuwa ga shiriya ba tare da ya sava ko ya kauce hanya ba. Idan aka rasa wannan qarfi, to waxannan koyarwa da hukumce-hukumce suna matsayin wa'azi kawai mara wata ma'ana cikin haqiqanin rayuwa kuma mara tasiri cikin halaye da xabi'un xan'Adam.

Idan har muka xauka cewa dokokin horo na tsarin dokar xan’Adam – da suka haxa da xauri, kisa, kora da dai sauransu – za su iya sanya wa mutum linzami su sa shi bin tafarki da gudanar da gyara da shiriya, to kuwa da mun yi kuskure, don kuwa haqiqa ta tabbatar da rashin nasarar hakan wajen kawo qarshen tushen sharri da fasadi, da lamunin rayuwa ta sa’ada da kamala da kuma tsaro, wa xaixaiku ne ko wa al’umma baki xaya.

Wannan haka yake, saboda idan har waxannan dokoki sun yi nasara wajen kare wuce gona da iri da ashararanci cikin al'umma, ta hanyar mafi tsaurin azaba, to a vangare guda kuma sun kasa magance bauxewar ma’abuta shugabanci, don kuwa sun gaza wajen fuskantar ‘yan kama-karya da suke wasa da dukiyoyin al'umma da take haqqoqinsu suna masu fakewa da irin waxannan dokoki da suke ba su kariyada tsaro

Sannan kuma irin waxannan hanyoyi na zahiri da ke tasiri cikin halaye da xabi'un mutum, da suka haxa da dokokin horo da gwamnatocin yawa-yawan qasashe suke sanyawa, suna da alaqa ta qut da qut da qarfin hukuma da haibar masu iko da kuma kyautata hanyoyin zartarwa. A duk lokacin da wata gwamnati ta rasa irin wannan matsayi, fasadi kuma ya samu gindin zama a cikinta, babu makawa waxannan dokoki za su rasa duk wata qima da suke da ita, za su kasance ba su da wata haiba ko mutumci a idanun al'umma.

Idan ma har da za mu xauka waxannan dokoki za su yi nasara wajen kawo qarshen laifuffukan talakawa da shuwagabanni, tare da samuwar doka mai tabbatar da wanzuwar waxannan gwamnatoci da cibiyoyinsu, to ai akwai wasu wuraren da idanuwan masu kula da dokokin gwamnatin ba za su iya isa gare su ba. Daga cikinsu har da nau’in laifuffukan da ba a saba da irinsu ba, waxanda suka samo asali daga son zuciya da ruxin Shaixan, la'ananne.

 ﴿ æóíõÑöíÏõ ÇáÔøóíúØóÇäõ Ãóä íõÖöáøóåõãú ÖóáÇóáÇð ÈóÚöíÏÇð

“Kuma Shaixan yana neman ya vatar da su, vatarwa mai nisa ne([7])".

﴿ Åäø ÇáÔøóíúØÇäó ßóÇä ááÅöäúÓóÇäö ÚóÏõæÇøð ãõÈöíäðÇ

“Lalle ne Shaixan ya kasance ga mutum, maqiyi bayyananne([8]).

Idan kuma aka ce: mai yiyuwa ne mulhidi (maras addini wanda bai yi imani da samuwar Ubangiji ba) ya kasance na gari, sai dai wannan nagarta tasa ta zahiri ce, ba ta kai zuci ba, saboda nagarta ce da ta samo asali daga kunyar idon mutanen da ake tare da su ko kuma tsoron mahukunta. Idan da waxannan abubuwa za su kau, ba zai yi tsantsainiqas ko kunyan wuce gona da iri kan mutane ko dukiya da dai sauransu ba, don kuwa idan son zuciya ya mallake rai, to zai juya shi zuwa ga aikata duk wani mugun abu. To ina nagarta ga mutumin da yake ganin kansa a matsayin dabba mai qarewa?

Don haka, ana iya cewa a lokuta da dama dokokin da qasashen duniya, ciki kuwa har da manyan qasashen da suka ci gaba, suke kafawa, sun nuna gazawarsu wajen shiryar da xabi'un mutum, tsara rayuwarsa da kuma isar da shi zuwa ga manufarsa ta xan'Adamtaka bisa tabbatattun asasi da za su shiryar da mutum da al'ummar da yake ciki zuwa ga sa'adar duniya da ta lahira.

Daga abin da ya gabata za mu iya fahimtar cewa abubuwan da suke cikin nafs (ran) xan'Adam da suke cikin asalin samuwa da lamirinsa, su ne qarfin da ke juya halaye da xabi'unsa na fili da na voye. Hakan kuwa ya samo asali ne daga irin qarfin da ruhi yake da shi na shiryar da ma'abucinsa, sai dai samar wa ruhi xin iko kan jikin mutum abu ne da ke da wahalan gaske idan ba ga wanda ya yi imani da dawwamar rai ba, don kuwa wannan aqida ta kan haifar da wani irin yanayi da zai sanya mutum aikata ayyukan alheri saboda tsammanin sakamakon lahira da kuma guje wa sha'awace-sha'awace da soyace-soyacen zuciya da kuma nesantar muggan laifuka da zunubai saboda tsoron uqubar lahira.

Hakan kuwa saboda mai yiyuwa ne lamirin xan'Adam shi kaxansa ya iya sukar ma'abucinsa idan ya aikata laifi amma ba zai iya azabtar da shi ba, kuma mai yiyuwa ne ya zarge shi kan aikata munkarin, amma ba ya horonsa. Mai yiyuwa ne kuma ya kasance mai nasiha da wa'azi, amma kuma ba mai shiryarwa ba, domin lamirin xan’Adam ba shi da katavus gaba ga son zuciya a duniyar vata da kaucewa tafarki. A lokuta da dama ma ya kan yi galaba a kansa, a irin wannan lokaci xan'Adam ya kan aikata duk abin da yake so yana mai fakewa da cewa idanuwan mutane ba sa ganinsa.

Idan har dokokin qasa da al'adun al'umma sun kasance wani qangi da ke taqaita mutum daga waje, sannan kuma lamirinsa ya kasance masa qangi da ke kange shi daga ciki da za su tsara halaye da mu'amalarsa gwargwadon, to haqiqa imani da Allah da ranar lahira suna haxa waxannan biyun da kuma wucewa gabansu. Saboda su waxannan abubuwa biyu (imani da Allah da ranar lahira) su kan sanya wa mutum shu'urin jin akwai wani mai sanya ido a kansa da ba zai iya tsere masa ba don kuwa yana kewaye da komai, sannan kuma yana kusa da shi fiye da jijiyar wuya, sannan kuma ya san abin da ke voye da wanda aka bayyana, kuma zai yi hisabi a kan dukkanin aiki babba da qarami. Wannan ya kan sa mutum ya ji cewa akwai wani nauyi a kansa yana mai tsoron azabar Ubangiji Maxaukakin Sarki ko da kuwa yana wani waje ne da idanuwan mutane ba sa kansa ko kuma dokar qasa ba za ta iya isa gare shi ba, don kuwa ya san cewa babu yadda zai iya tsera wa hukumcin Allah da ikonSa.

An ruwaito daga Imam Ali bn Husain Zainul Abidin (a.s) cewa wani mutum ya zo wajensa ya ce: "Ni mutum ne mai savo, ba na iya daurewa in bar shi, saboda haka ka mini wa'azi", sai Imam ya ce masa: "Ka aikata abubuwa guda biyar, sannan ka aikata duk savon da kake so: Na farko dai: Ka da ka ci arziqin Allah, sai ka aikata abin da kake so, na biyu ka fice daga ikon Allah, sai ka aikata abin da kake so, na uku: ka zavi wani wajen da ba Ya ganinka, sai ka aikata zunubin da kake so, na huxu: idan mala'ikan mutuwa ya zo xaukan ranka ka hana shi, sai ka aikata zunubin da kake so, na biyar kuwa shi ne: idan Maliku zai shigar da kai wuta ka qi shiga, sai ka aikata zunubin da kake so([9])".

Mumini dai ya yi imani da cewa dukkan komai na qarqashin iko da mulkin Allah Maxaukakin Sarki ne, kuma yana ganin dukkan ayyukan xan'Adam da kuma dukkanin abubuwan da ya voye, da kuma cewa waxannan ayyuka su kaxai ne masu mutum tun da ga ranar mutuwarsa har tashinsa a ranar hisabi sannan kuma su za su kasance ma'aunin sakamako mai kyau ko kuma akasin haka. Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: "Abubuwa uku ne suke raka mutum (idan ya mutu): iyalai, dukiya da ayyukansa, biyu za su dawo su bar shi, guda ne kawai zai zauna tare da shi. Iyalai da dukiyarsa za su dawo su bar shi tare da ayyukansa([10])".

Daga malizimtar imani da ranar lahira akwai: imani da cewa xan'Adam zai amsa tambaya kan abin da ya aikata lokacin da za a gabatar da shi a gaban Ubangiji ranar hisabi, inda za a tambaye shi kan abin da ya aikata, alheri ko sharri, na bayyane da na voye, daga nan sai a yi masa sakamako, gwargwadon abin da ya aikata, Allah na cewa:

 ﴿ æóáÇó ÊóßúÓöÈõ ßõáøõ äóÝúÓò ÅöáÇøó ÚóáóíúåóÇ æóáÇó ÊóÒöÑõ æóÇÒöÑóÉñ æöÒúÑó ÃõÎúÑóì ,

"Kuma wani rai ba ya yin tsirfa face domin kansa, kuma mai xaukar nauyi, ba ya xaukar nauyin wani..([11])", sannan kuma Yana cewa:

 ﴿ ßõáøõ äóÝúÓò ÈöãóÇ ßóÓóÈóÊú ÑóåöíäóÉñ

"Kowane rai ga abin da ya aikata jingina ce([12])".

Don haka, ayyuka su ne ma'aunin xaukaka ko kuma wulaqantar mutum, kuma asasin kusantar rahamar Ubangiji ko kuma nesantarta, don a wannan lokacin, muqami ko nasabar mutum ba su da wani amfani, kamar yadda dukiya ko 'ya'ya ma suke, Allah Maxaukaki na cewa:

﴿ ÝóÅöÐóÇ äõÝöÎó Ýöí ÇáÕøõæÑö ÝóáÇ ÃóäÓóÇÈó Èóíúäóåõãú íóæúãóÆöÐò æóáÇ íóÊóÓóÇÁáõæäó ! Ýóãóä ËóÞõáóÊú ãóæóÇÒöíäõåõ ÝóÃõæúáóÆößó åõãõ ÇáúãõÝúáöÍõæäó ! æóãóäú ÎóÝøóÊú ãóæóÇÒöíäõåõ ÝóÃõæúáóÆößó ÇáøóÐöíäó ÎóÓöÑõæÇ ÃóäÝõÓóåõãú Ýöí Ìóåóäøóãó ÎóÇáöÏõæäó ([13])

"Sa'an nan idan an yi busa a cikin qaho, to, babu dangantakoki a tsakaninsu a ranar nan, kuma ba za su tambayi junansu ba. To, waxanda sikelinsu ya yi nauyi, to, waxanan su ne masu babban rabo. Kuma waxanda sikelinsu ya yi sauqi, to, waxannan ne waxanda suka yi hasarar rayukansu suna madawwama a cikin (wutan) Jahannama". Sannan kuma Maxaukakin Sarki Yana cewa:

 ﴿ áóä ÊõÛúäöíó Úóäúåõãú ÃóãúæóÇáõåõãú æóáÇó ÃóæúáÇóÏõåõã ãøöäó Çááøåö ÔóíúÆðÇ

"Dukiyoyinsu ko xiyansu ba za su wadatar musu da kome ba daga Allah ([14])",har ila yau Yana cewa:

  ﴿ æóãóÇ íõÛúäöí Úóäúåõ ãóÇáõåõ ÅöÐóÇ ÊóÑóÏøóì,

 "Kuma dukiyarsa ba ta wadatar masa da kome ba, a lokacin da ya gangara (a wuta)([15])", haka nan Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: "Allah ba Ya duba surarku, hakan nan dukiyarku, face dai Yana dubi ne zuwa ga zuciya da ayyukanku([16])".

Wannan sashen abin da wajibi ne kowani mumini ya yi imani da su qarqashin imani da ranar lahira. Ta hakan zai iya haifar da zuhudu (gudun duniya) cikin rayuwarsa ta duniya, tsantsaini da kuma nesantar abubuwan da Allah Ya haramta, su kan sa mutum taraddudi a duk lokacin da ya so aikata savo don haka sai ya nesanci aikatawa saboda imanin da yake da shi da ranar hisabi da kuma jin cewa akwai wani Mai sanya ido a kansa ba tare da sauraron wata doka ko iko ba.

Don haka, imani da ranar lahira wani qarfi mai tasirin gaske ne na daidaita xabi'un mutum wanda daga qarshe ya kan yi tasiri a rayuwa ta al'ummance. Saboda hakan ya kan sa mutum musulmi ya yi riqo da Littafin Allah Maxaukakin Sarki, Sunnar Ma'aiki (s.aw.a) da kuma adalcin Allah da zai tsara lamurran al'umma, ya kare haqqin duk wani mai haqqi, kamar yadda kuma zai haifar da yanayi mai qarfi na shu'uri da jin nauyi (mas'uliyya) kan duk wani aikin da yake yi, da tsarkake kansa daga take haqqoqin sauran mutane da kuma tsantsainin da zai hana shi wuce gona da iri kan mutane. Amirul Muminina Ali (a.s) yana cewa: "Mafi munin guzurin ranar lahira shi ne zaluntar bayi([17])". Sannan yana cewa: "Bai yi imani da ranar lahira ba, duk wanda bai ji nauyin zaluntar bayi ba([18])", haka nan yana cewa: "Wallahi in kwana bisa qayar Sa’adan ba barci ko kuma kora ni cikin qangi shi ya fi soyuwa a gare ni da in sadu da Allah da Manzon Allah ranar lahira alhali ina mai zaluntar bayi ko kuma ina mai qwacen wani abu daga tarkacen abin duniya. Ta ya ya zan zalunci wani saboda ran da take tafe cikin gaggawa zuwa ga qarewa, wanda kuwa zaman shi cikin qasa zai yi tsawo?!.([19])".

Addinin Musulunci yana jaddada cewa mafi alherin abin da mutum zai tafi da shi lahira shi ne taqawa (tsoron Allah), hakan na iya shiga tsakanin mutum da yaxuwar fasadi da ha'inci zai kuma taimaka wajen tabbatar da tushen gyaran alumma da daidaito a cikinta.

Su ma a vangarensu, Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun kasance masu kwaxaitar da al'umma zuwa ga wannan mahanga. An ruwaito Imam Abu Ja'afar al-Baqir (a.s) yana cewa: "Amirul Muminina ya kasance idan ya jagoranci al'umma sallar lisha a garin Kufa ya kan xaga muryarsa har sau uku don kowa ya ji sai ya ce: Ya ku mutane, ku shirya, Allah Ya yi muku rahama, haqiqa an kira ku zuwa ga tafiya, mene ne amfanin zama a duniya bayan kira zuwa ga tafiya? Ku shirya, Allah Ya yi muku rahama, ku tafi (wannan tafiya) da mafi girman guzurin da kuke da shi, shi ne kuwa taqawa…([20])".

Imani da ranar lahira babban abu ne mai sa mutum ya kiyaye haqqoqin 'yan'Adam da mu'amala ta qwarai, da ta xoru bisa asasin adalci, gaskiya da amana. Allah Maxaukakin Sarki na cewa:

﴿ æóíúáñ áøöáúãõØóÝøöÝöíäó !ÇáøóÐöíäó ÅöÐóÇ ÇßúÊóÇáõæÇú Úóáóì ÇáäøóÇÓö íóÓúÊóæúÝõæäó ! æóÅöÐóÇ ßóÇáõæåõãú Ãóæ æøóÒóäõæåõãú íõÎúÓöÑõæäó ! ÃóáÇ íóÙõäøõ ÃõæáóÆößó Ãóäøóåõã ãøóÈúÚõæËõæäó ! áöíóæúãò ÚóÙöíãò([21])

"Azaba ta tabbata ga masu tauyewa wurin ciniki (tauye ma'auni da mudu da makamantansu. Waxanda idan suka yi awu (ciniki) daga wajen mutane sai su nemi a cika musu (haqqinsu). Kana yayin da za su aunar musu, da mudu ko da sikeli, sai su tauye. Ashe waxannan ba su tsammanin cewa za a tayar da su. A wata rana mai girma?

Musulunci yana jaddada cewa yayin da mutum ya bar duniya, babu abin da zai bi shi face abu mai yaxuwa kamar zuriya ta gari, kyakkyawan aikin da ya bari ake aiki da shi da kuma ayyukan alherin da ya aikata.

Imam Sadiq (a.s) yana cewa: "Babu wani lada da zai bi mutum bayan mutuwarsa in ban da waxannan abubuwa uku: sadakar da ya ba da a lokacin rayuwarsa, sannan ta ci gaba bayan mutuwarsa, ko kuma wata sunna (aiki) da ya qirqiro kuma aka ci gaba da aiki da ita bayan mutuwarsa, ko kuma xa salihin da ke masa addu'a([22]). Wannan hadisi yana kiran musulmi ne da ya yi tunanin kafa tushen alheri da gyara cikin al'umma da samar da zuriya ta gari wacce alherinta zai kasance tare da shi hatta bayan rasuwarsa.

Don haka, ana iya qirga imani da ranar lahira da hisabin da za a yi a ranar a matsayin xaya daga cikin muhimman tushen aqida da suke da tasirin gaske wajen tsara rayuwar al'ummar musulmi da shiryar da su zuwa ga cimma manufarsu ta 'yan'Adamtaka bisa asasi mai qarfi. Waxannan tushen aqida sun fi kowace irin doka ta xan'Adam da take qoqarin fuskantar duk wani rashin tsari da fasadi, kisa da sace-sace da suka zamanto ruwan dare a mafi yawan qasashen duniya waxanda suka ci gaba da kuma masu tasowa.

Dukkan waxannan abubuwa ne suka sanya da dama daga cikin mutanen da ba su ma yi imani da addini da kuma ranar lahira ba kamar su Kant da Voltaire suke bayyana cewar babu wani abin da ya dace ya sanya ido kan mutum da shiryar da halayensa zuwa ga tafarkin gaskiya da adalci a dukkan yanayi in ban da aqidar imani da ranar lahira([23]).

 

Na Biyu: Tasirin Makoma Kan Ran Xan’Adam:

Haqiqa imani da Allah da kuma ranar lahira wani babban makami da kuma lamuni ne ga xan'Adam don kuwa yana ba wa mutum iko da daman tsayin daka wajen fuskantar son zuciya da abubuwan da suke yaudarar xan'Adam a duniya. Hakan kuwa saboda da dama daga cikin waxanda ba su yi imani da ranar lahira ba amma sun yi imani da cewa mutuwa ita ce qarshen rayuwa, ba su da wani abin da zai kare su daga son zuciya da abkawa cikin vata da munanan ayyuka.

Shi kuwa wanda ya yi imani da ranar lahira yana xaukan duniya ne a matsayin wata makaranta ta shiri da kuma tara ilmi da falaloli don isa ga kamala, gaskiya da kuma samun kyakkyawar rayuwa a duniya ta har abada. A kan samu hakan ne ta hanyar tsarkake kai daga aikata savo da kwaxaitar da shi zuwa ga ma'anar xaukaka da adalci da samun kamala da kwanciyar hankali:

﴿ íóÇ ÃóíøóÊõåóÇ ÇáäøóÝúÓõ ÇáúãõØúãóÆöäøóÉõ ! ÇÑúÌöÚöí Åöáóì ÑóÈøößö ÑóÇÖöíóÉð ãøóÑúÖöíøóÉð ! ÝóÇÏúÎõáöí Ýöí ÚöÈóÇÏöí ! æóÇÏúÎõáöí ÌóäøóÊöí ([24])

"Ya kai rai mai nitsuwa! Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhali kana mai yarda abar yardarwa. Saboda haka, ka shiga cikin bayiNa. Kuma ka shiga AljannaTa".

Mutum ba zai bixi hakan ba sai domin imaninsa da ranar lahira, inda zai ga sakamakon aikin da yayi, in alheri, alheri, in sharri, sharri. Mutum zai samu iko a kan zuciyarsa ne saboda qarfin imanin da ya dasa qaunar xaukaka, kyawawan xabi'u da kamala a zuciyarsa wanda za su ba shi cikakkiyar kariya daga aikata zunubai da za su sanya shi nadama da xaukan babban nauyin ranar hisabi.

Haka nan imani da ranar lahira ba wai kawai kariya ce daga aikata munanan ayyuka ba wani abu ne ma da ke kwantar da hankali da tsugunar da abubuwan da suke tura mutum zuwa ga savo, kuma shi ne yake sanya fatar alheri marar iyaka ta yadda burin xan'Adam zai isa ga abin da yake son cimmawa, wato kamala, kuma ta haka mutum zai zamanto ma'abucin xaukaka. Ba wai don yana tsoron azaba ko kuma yana fatan samun sakamako mai kyau ba, a'a sai dai don kawai yana samun jin daxin kasancewa na gari sama da daxin ayyukan qasqanci, don haka sai ya bauta wa Allah ba wai saboda tsoro ko kwaxayin (lada ba), face dai don kawai yana ganin Allah a matsayin Wanda ya cancanci a bauta masa. Amirul Muminina (a.s) yana cewa: "Ya Allah! Ina bauta maKa ne ba don tsoron azabarKa ba, ba kuma don kwaxayin ladanKa ba, face dai kawai don na san Ka cancanci bauta ne, shi yasa nake bauta maKa([25])". Wannan shi ne ibadar 'yantattun bayi ma'abuta xaukaka da imani.

Su kuwa waxanda ba su yi imani da ranar lahira ba, waxanda ba sa fatan saduwa da Ubangiji, sai suka amince da rayuwar duniya da dogara da ita, don haka sai sha'auce-sha'auce suka yi galaba a kansu, son zuciyarsu suka wuce gaba, sai suka lalata rayukansu, ba abin da suke yi in banda rige-rige wajen neman abin duniya mai gushewa, ba don komai ba sai saboda hakan shi ne hanyarsu ta samun jin daxi da annashuwa kafin mutuwa, wacce suke ganinta a matsayin qarewa ta gaba xaya, ta riske su.

Don haka ne za ka gansu a ko da yaushe cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali saboda tsoron kada abin hannunsu ya qare kafin mutuwa ko kuma saboda tsoron kada su mutu ba su sami hanyoyin jin daxi da annashuwa ba. Hakan ya kan sa su cikin baqin ciki daga lokacin da suka fuskanci kome kashin rashin nasara a rayuwa, rayuwarsu ta yi qunci da wahala irin ta duniya da ba za su sami wani lada ko riba ba saboda ita. Saboda haka duniya sai ta yi musu baqi, wani lokaci ma har su kashe kansu, wai don su guje wa wannan yanayi mai sosa rai da ya same su, ba don komai suka shiga wannan hali ba sai saboda sun kasance makafi ne da ba sa gani, duniya ta makantar da su daga ganin tafarkin gaskiya, alheri da kamala.

Amirul Muminina (a.s) yana cewa: "Haqiqa duniya ita ce qololuwar ganin makaho (wanda zuciyarsa ta makance), ba ya ganin komai koma bayanta, shi kuwa mai gani, ganinsa ya qetare ta, don yana da masaniyar cewa akwai wani gidan bayanta, don haka mai gani yana gudunta, shi kuwa makahon yana nufarta, mai gani yana tara guzuri a cikinta (don ranar gobe) shi kuwa makaho yana tara guzuri ne dominta([26])".

Shi kuwa mumini, savanin haka, ya yi imani da cewa nasara ba wai kawai ta taqaita ne ga wannan duniya da abin cikinta mai qarewa ba, ya yi imanin cewa abin da ke wajen Allah shi ne mafi alheri kana kuma dawwamamme

 ﴿ æóãóÇ ÃõæÊöíÊõã ãøöä ÔóíúÁò ÝóãóÊóÇÚõ ÇáúÍóíóÇÉö ÇáÏøõäúíóÇ æóÒöíäóÊõåóÇ æóãóÇ ÚöäÏó Çááøóåö ÎóíúÑñ æóÃóÈúÞóì([27])

"Kuma abin da aka ba ku daga kome, to, jin daxin rayuwar duniya ne da qawarta. Kuma abin da ke wurin Allah, shi ne mafi alheri kuma mafi wanzuwa…". Hakan ya kan qara masa tsayawa qyam wajen fuskantar duk wata wahala ta wannan duniya, ba ya tava yarda ya miqa kai ko kuma ya faxa tarkon damuwa da fargaba don duniya, a’a ya kan tarbiyyantar da zuciyarsa da haquri da tunatar da ita tsayuwa gaban Allah Maxaukaki ranar lahira yana mai fatan samun jin daxi na har abada. Amirul Muminina (a.s) yana cewa: "Ku yawaita tunanin mutuwa da ranar fitarku daga kaburbura, da kuma tsayuwarku a gaban Allah Maxaukaki, sai musibu su sauqaqa muku([28])".

Saboda haka, (imani da) makoma aqida ce da take tabbatar da nasarar xan'Adam da juyar da akalarsa zuwa ga xaukaka da kamala, don kuwa nasara a gobe qiyama ta dogara ne da irin falala da kyawawan xabi'un da mutum ya samu a duniya da kuma daidaita qarfin sha’awa da na fushi, ba gazawa da wuce gona da iri. Da kuma bin tafarkin da zai kai shi ga samun xaukaka da kuma nesantar duk wani nau'i na qasqanci da suka haxa da qasqanci na duniya da na lahira. Hakan ne zai share masa hanyar isa ga cika da kamala.

Duk da irin qarfi na ci gaban zamani da qere-qeren da xan'Adam ya samu, ya gaza wajen samun damar mallakan zuciyar xan'Adam da juya ta zuwa ga kamalar da ake buqata, ya gaza wajen dakatar da abubuwan da suke kawo vata da kaucewa tafarki da qasashe da al'ummomi da dama suke fama da su.

Irin waxannan matsaloli da xan'Adam yake fama da su sun sanya qasashen duniya musamman waxanda suka ci gaba gabatar da dukkan hanyoyin da za su iya wajen ganin an shawo kan damuwa da zaman xar-xar xin da suke fama da ita, sai dai sun gagara cimma manufa, don haka al'ummominsu suka ci gaba da zama cikin irin wannan yanayi na damuwa da fargaba.

Abin da kawai ya saura shi ne aqidar imani da ranar lahira, don kuwa ita ce kawai qarfi guda da zai iya tsarkake rayuka ya kare su daga kaucewa tafarki. Ita ce kawai garkuwar da za ta iya kare mutum daga hare-haren son zuciya, don isa ga nasara ta har abada. Don kuwa ita ce kawai abin dogara wajen gina maxaukakiyar rai da kuma al'umma tsarkakakkiya.


 

 

([1]) . Suratul A'araf; 7:29.

([2]) . Suratur Rum 30:27, sannan mai son qarin bayani kan ma’anar lugga yana iya komawa ga Lisan al-Arab –Ud- 3/315, Mufradat al-Qur’an na Ragib – ud - :351, Misbah al-Munir na Al-Qayyumi – ada-2:101, Mu’ujam Maqayis al-Lugga na Ibn Faris – ud – 4:181.

([3]) . Babul Hadi Ashara na Fadhil al-Miqdad: shafi na 86.

([4]) . Sharhul Maqasid na al-Taftazani, juzu'i na 5, shafi na 82.

([5]) . Al-Mabda' wa al-Ma'ad na Sadruddin al-Shirazi,shafi na 374 -375, Haqqul Yaqin na Abdullah Shibr, juzu'i na 2, shafi na 36-38.

([6]). Suratus Saba'; 34:3.

([7]) . Suratun Nisa'; 4:60.

([8]) . Suratul Isra': 17: 53.

([9]) . Jami al-Akhbar na Sabzawari: 359/1001, Mu'assasar Aalulbait Qum Iran, Bihar al-Anwar na Majlisi 78:126/7.

([10]) . Kanzul Ummal na Muttaqi al-Hindi 15:690, Mu'assasar Risala – Beirut.

([11]).Suratul An'am; 6:164.

([12]) . Suratul Muddathir; 74:38.

([13]) . Suratul Muminin; 23: 101-103

([14]) . Suratu Al Imrana; 3: 10 da 116 da Suratul Mujadala; 58:17.

([15]) . Suratul Lail; 92:11.

([16]) . Tafsir al-Razi 22:135 Dar al-Ihya al-Turath al-Arabi – Beirut.

([17]) . Nahjul Balagah/Subhi al-Salih: 507 – hikima ta 221.

([18]) . Gurar al-Hikam na al-Amdi, 2: 364/409.

([19]) . Nahjul Balagah/Subhi al-Salih: 346 – huxuba ta 224.

([20]) . Amali na Mufid: 198/32 – Mu'utamar Sheik al-Mufid- Qum.

([21]) . Suratul Muxaffifin; 83: 1-5.

([22]) . Al-Tahzib na Tusi 9:233/3– Dar al-Kutub al-Islamiyya–Tehran.

([23]) . Al-Adillat al-Jaliyya fi Sharh al-Fusul al-Nasiriyya na Abdullah Ni'imat: 194 – Dar al-Fikr al-Lubnani.

([24]) . Suratul Fajr; 89:27-30.

([25]) . Bihar al-Anwar na Majlisi; 41/14/4

([26]) . Nahjul Balagah, huxuba ta 133.

([27]) . Suratul Qasas; 28: 60.

([28]) . Al-Khisal na Saduq: 616 – hadisi na 400.

 

عنوان الکتاب