|
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Maxaukakin Sarki, tsira da amincinSa su tabbata ga wanda babu wani Annabi bayansa tare da tsarkakan Iyalan gidansa masu albarka da zavavvun sahabbansa da masu binsu da alheri har zuwa tashin qiyama….. Bayan haka…. Makoma (ranar qiyama) na daga cikin tabbatattun jiga-jigan aqida, ba wai a Musulunci kaxai ba, hatta ma a sauran saukakkun addinai. Makoma dai jigo ne da ke gwame da tauhidi (kaxaita Ubangiji) da annabci domin ba da gaskiya ga Allah da ManzanninSa da Littafansa dole ne ya haifar da imani da shi, saboda haka makoma mai biyowa ne (lazim) ga yarda da kiraye-kirayen Annabawa masu cike da tabbatattun nassosi waxanda ke tabbatar da shi. Sannan kuma shi mai biyo yarda da alqawarin Allah na sakayya da narkon azaba ne; waxanda su kuma masu biyo xora nauyi (taklif) ne da adalcin Ubangiji da kasancewar rayuwa tana da manufa, wanda ke savawa yin aiki kara zube (abath), abin da ba a samun sa cikin adalci da hikimar Ubangiji. Alqur’ani ya tabbatar da wannan biyowa cikin ayoyi da dama, mafi bayyana shi ne faxinSa Ta’ala cewa: ﴿ ÃóÝóÍóÓöÈúÊõãú ÃóäøóãóÇ ÎóáóÞúäóÇßõãú ÚóÈóËðÇ æóÃóäøóßõãú ÅöáóíúäóÇ áÇó ÊõÑúÌóÚõæä ó﴾ “Shin, to, kun yi zaton cewa Mun halitta ku ne da wasa, kuma lalle ku, zuwa gare Mu, ba za ku komo ba? (Suratul Mu’minun 23:115). Alal haqiqa, tsawon tarihi, an yi ta samun mutane daban-daban da ke bijiro da tambayoyi marasa sarqaqiya kan wannan aqida, suna masu shakku kanta da kuma yarda da ita duk kuwa da bayyanar da take da shi. Waxannan tambayoyi sun danganci batun yiyuwar sake dawo da jikin mutum ne bayan lalacewarsa cikin qasa har ya zama qwayoyi tarwatsattsu…. To sai dai kuma tun zamanin saukar da wahayi, Alqur'ani mai girma ya magance wannan shakku ta hanyar gabatar da hujjoji na zahiri (hissiya) da qwaqwalwa za ta iya yarda da shi, kamar cikin faxinSa Maxaukakin Sarki cewa: ﴿ æóÖóÑóÈó áóäóÇ ãóËóáÇð æóäóÓöíó ÎóáúÞóåõ ÞóÇáó ãóäú íõÍúíöí ÇáúÚöÙóÇãó æóåöíó Ñóãöíãñ ! Þõáú íõÍúíöíåóÇ ÇáøóÐöí ÃóäÔóÃóåóÇ Ãóæøóáó ãóÑøóÉò æóåõæó Èößõáøö ÎóáúÞò Úóáöíãñ ﴾ “Kuma ya buga Mana wani misali, kuma ya manta da halittarsa, ya ce, ‘wane n eke rayar da qasusuwa alhali kuwa suna rududdugaggu?’ Ka ce, ‘Wanda ya qaga halittarsu a farkon lokaci, Shi ke rayar da su, kuma Shi, game da kowace halitta, Mai ilmi ne”. (Suratu Yasin; 36: 78-79) Bugu da qari Allah Maxaukaki Ya nuna wa xan'Adam rayayyun misalai na wannan rayarwa da kuma sake tayarwa bayan mutuwa da lalacewa, hakan ya zo da yawa cikin qissoshin Annabawan Bani Isra'ila waxanda aka san al’ummominsu da taurin kai da rashin amfani da hankali. Baicin waxannan tambayoyi marasa sarqaqiya, wasu tambayoyin irin na masana falsafa sun bijiro wa wannan batu na makoma kai har ma da yadda za ta faru bayan imani da ita da kuma tabbatar da ita da hujjojin falsafa. Tambayoyin nasu sun kasance kan haqiqanin rai da dangartakarsa da jiki, da kuma cewa shin rai shi ma zai qare ne bayan mutuwa kana ya dawo? Shin hujjojin falsafa da na shari’a suna nuni zuwa ga dawowar jikkuna ne ko sun taqaita ga dawowar rayuka ta yarda sakayya da uquba za su ta’allaqa da rai ne ban da jiki, da dai sauran tambayoyi kan batutuwa filla-filla waxanda suka danganci waxancan mas’aloli. A ra’ayin masana falsafa musulmi, ita mutuwa tana aukawa jiki ne ba ruhi (rai) ba, kuma rayuka suna da mazauninsu zuwa ranar qiyama, yayin da za su dawowa jikuna. Wannan kuwa ana kiransa dawowan (makoman) jiki, sai jikuna su sanya waxannan rayuka saboda rayuwar su ta har abada. Wancan rayuwa madawwamiya ta lahira tana da matakai masu tsawo waxanda ayoyin Alqur’ani mai girma da sunna tsarkaka suka shata iyakokinsu. Daga barzahu, zuwa hura qah, sai tashi, sai hisabi, sai sikeli (mizani), sai siraxi sannan daga qarshe sai Aljanna ko wuta. Ana kiran waxannan dogayen matakai fagagen alqiyama. Wannan littafi zai mana bayanin manufar makoma, hujjojinta, haqiqaninta da matakanta a wani balaguro na ruhi, abin buqata matuqa a gare mu.
Markaz al-Risala. GABATARWADukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, mafificin tsira da mafi cikan amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Muhammad al-Mustafa (s.a.w.a) tare da Alayensa tsarkaka, masu shiryarwa kuma masu daraja….bayan haka... Haqiqa imani da makoma xaya ne daga cikin jiga-jigan aqidar Musulunci waxanda suke tabbatattu ne cikin Alqur'ani mai girma da kuma Sunnar Ma'aiki (s.a.w.a), baya ga tabbatar da hakan da hankali yake yi da kuma rayuwar lahira. Tun farko dai, dukkan saukakkun shari’o’i sun haxu a kan kafa wannan tushe na aqida, kamar yadda kuma Annabawa da Manzanni suka sha xawainiya da wahalhalu qalubale masu yawa wajen tabbatar da wannan aqida cikin zukatan al'ummominsu. Lalle tunani kan yadda aka halicci sama da qasa da kuma irin yadda aka halicci abubuwan da suke cikinsu tare da lura da wannan cikakken tsari wanda sassansa ke dacewa da juna, zai kai mu ga yin imani da cewa Wanda ya fari qasa da saman, mai iko ne Ya sake rayar da halittu a karo na biyu kamar yadda Ya haliccesu daga babu a karon farko. Saboda wanda yake da qarfin farar da wani abu, to kuwa sake dawo da shi yafi sauqi a gare shi. ﴿ Ãóæóáóãú íóÑóæúÇ Ãóäøó Çááåó ÇáøóÐöí ÎóáóÞó ÇáÓøóãÇæóÇÊö æóÇáÇúóóÑúÖó æóáóãú íóÚúíó ÈöÎóáúÞöåöäøó ÈöÞóÇÏöÑò Úóáóì Ãóä íõÍúíöíó ÇáúãóæúÊóì ﴾ "Shin, kuma basu gani ba cewa, 'Lalle Allah, Wanda Ya halitta sammai da qasa, kuma bai kasa ga halittarsu ba, Mai ikon yi ne a kan rayar da matattu?([1])", kamar yadda Amirul Muminina Ali (a.s) ya tabbatar da hakan cikin faxinsa cewa: "Ina mamakin mai inkarin sake tayarwa gobe qiyama,alhali kuwa ya yi imani da halittar farko([2])!". Don haka, mutuwa, wannan mai tahowa da za ta riske mu kamar yadda ta riski waxanda suka gabace mu, ba wai qarewa ce ba mai kawo qarshen labarin halittar xan'Adam, wanda shi ne halifan Allah da aka xora wa nauyin bauta da biyayya ga Allah Shi kaxai da tabbatar da alheri da gaskiya a bayan qasa. A’a a aqidar Musulunci, mutuwa wani mataki ne daga matakan duniya ta gaba (lahira), duniyar tabbata da wanzuwa, duniyar Aljanna da wuta, inda mutane za su tabbata daidai da ayyukan da suka aikata ﴿ ßõáøõ äóÝúÓò ÈöãóÇ ßóÓóÈóÊú ÑóåöíäóÉ ﴾ "Kowane rai jingina ne ga abin da ya aikata([3])" , imma dai ni'ima ta har abada ko kuma azaba madawwamiya. Gidan lahira inda adalcin Ubangiji Maxaukakin Sarki da alqawarinSa za su bayyana, shi ne gidan bayar da sakamakon abin da aka aikata a wannan duniya, gidan jarrabawa… Don haka, imani da cewa Allah Maxaukakin Sarki Zai tayar da mutane bayan mutuwa, a ranar lahira, a ranar da aka yi alqawarinta, inda za a saka wa mai biyayya da azabtar da mai savo, na daga cikin abubuwan da suke sa mutum ya samu galaba kan sha'auce-sha'auce da son zuciya. Hakan ya kan zame masa wata garkuwa daga kusantar zunubi da sanya samuwarsa samuwa ta mutumci da xaukaka. Sai ka ga yana qoqarin aiwatar da abin da yake alheri da ayyuka na qwarai da kuma kamala dangane da kan kansa, iyalansa da kuma al'ummar da ya ke rayuwa cikinta domin ya shiryawa abin da yake zuwa bayan mutuwa na daga tsanani zaman kabari da kuma na hisabi. Haqiqa imani da makoma (ranar lahira) ta wata fuska kuma, ya kan raya fatar da ke tattare da xan'Adam game da rayuwa ta gaba, da ke nuni da adalci da gaskiyar alqawari da narkon Ubangiji. Sai ya sa mutane su qara qaimi wajen kafa halaye na gari da kuma addini a rayuwarsu, tare da yin haquri da wahalhalun da za su bijiro musu wajen gyara da kira zuwa ga gaskiya da adalci. A wannan xan qaramin littafi, za mu yi qarin haske ne kan wannan batu cikin babi guda huxu, inda za mu dubi ma'anar makoma da tasirin imani da ita, dalilan da suke tabbatar da ita da kuma wajibcinta, bayani kan haqiqaninta, amsa tambayoyi da shakku da masu inkarinta suke kawo wa, zango-zangon makoma kamar su mutuwa da rayuwar barzahu, alamun ranar tashin qiyama da fagagenta da dai sauransu. Muna roqon Allah da Ya nesanta mu daga fushinsa Ya kuma sanya mu cikin rahama da afuwarsa. |
||