|
GAME DA RAYUWAR IMAM SADIK (A.S.) |
||
|
ALAMUN TAMBAYA
ΚΣΗζα
Da na Hamidu ya zamanto yana kallo na, yayin ni kuma ina karanta wani littafi dangane da Imam Jafar bin Muhammad As-Sadik(A.S.), Sai nan da nan!! - Baba na ina so na yi magana da kai . - Haka dana Hamidu ya ce mani Sai na ga ya tashi daga inda yake zaune ya zo kusa da ni . Sai na ce masa alhali ina kallon fuskarsa mara laifi:- game da me kake so kayi magana ya Hamidu? Hakika wata tambaya ta zo mini a raina yayin da nake tunanin Sunan Imam Jafar bin Muhammad As-Sadik(A.S.) akan bangon littafin nan Sai na ce masa, bayan na rufe littafin na dora shi akan tebur da ke gabana, na ce masa bismilla - Menene ya sa aka kira mazhabar mu mazhabar Jafari? - An dangata ta ne ga Imam Jafar bin Muhammad As-Sadik(A.S.). - To menene ya sa aka danganta mazhabar mu ga Imam Jafar bin Muhammad As-Sadik(A.S.), amma ba a dangantata ga wani ba daga cikin Imamai(A.S.)? Na duba fuskar da na Hamidu alhali farin ciki mai tsanani ya lullube ni saboda ganin irin wannan mai da hankali da yayi ga wadannan lamurra muhimmai sai na amsa masa da girmamawa da soyyaya domin in karfafa shi kan ci gaba da magianar sa Wannan ya zama haka ne domin a zamanin Imam Sadik mazhabobi da dama sun bayyana wanda aka danganta su ga wadanda suka assasa su da lakabobin su kamar mazhabar Malikiyya ta Malik bin Anas da mazhabar Hanbaliyya ta Ahmad bin Hanbal da mazhabar Hanafiyya ta Abu Hanifa da mazhabar Shafiiyya ta ShafiI to saboda a bambance tsakanin mazhabarmu da wadannan, don haka aka san ta da mazhabar Jaafari wanda aka dangantata ga wani Imami daga zuriyar Manzo(S.A.W.A) Imamin da yayi zamani da bayyanar wadannan mazhabobi, wato shine Imam Jaafar bin Muhammad As-Sadik(A.S.). Saidai kuma ya mahaifina, mu mun San cewa Imaman zuriyar Annabi Muhammad(S.A.W.A.) su maasumai ne, tsarkakku kuma wasu ayoyin Al-Kurani mai girma sun bayyana haka a sarari da kuma hadisan Manzo(S.A.W.A), to daga wadannan zamu san cewa Ahlul Bait(A.S.) su suka fi cancantar Imamamanci daga wasunsu to me Imam yayi dangane da wadannan mazhabobi? - Imam Sadik(A.S.) ya aiwatar da wajibin sa da kuma abinda ya rataya a wuyan sa na ilimi, a tsakiyar wadannan mazhabobi, a matsayinsa na Imami, kuma malami, dada masani na koli, wanda babu wani malami maabucin sani da yayi daidai da shi, hakika ya kasance tudu ne mai tsawo, kuma mai daukaka wanda ba kamarsa, ya bubbugo da ilmi, ya kuma yada ilimi da maarifa ga malaman zamaninsa To ya zamanto asasi ne na ilimi da akidoji matabbata wanda ginin musulunci ya kafu akai, kuma ilimin sa da dabi unsa sun yadu a nahiyoyi yaya ba zai zama haka ba alhali ilimin sa daga Manzo(S.A.W.A.) yake, kuma aikinsa ci gaba ne ga sakon Manzo(S.A.W.A.), to don haka ya aiwatar da wajibansa a shariá, a matsayinsa na Imami wanda ya wajaba ya yada sharia, ya kuma kare akidojinta kuma ya bata gudummawa, ta wannan bangaren a zamanin mahaifinsa Imam Muhammad Al-Bakir(A.S.) yayin da ya assasa Jamiΰr Ahlul Bait(A.S.), a masallacin Annabi sai ya bi diddigen mahaifinsa, suka yada ilmi da maΰrifa tsakanin malaman fikihu, da masu tafsiri da malaman hadisi, da kuma manema ilimi da ke zuwa wurinsu tawaga tawaga domin su nemi ilimi daga wannan mabubbuga ta taceccen ilimi hakika shugabannin sauran mazhabobi sun yi ikrari da hakkin Ahlul Bait(A.S.) kuma suna daukaka su Ga shugaban mazhabar ShafiIyya Imam Muhammad bin Idris ya tsara waka inda ya ambaci hakkinsu(A.S.) yana cewa: «Ya Ahlu Baitin Manzon Allah sonku, Farillane daga Allah da ya saukar a AlKurani, Daukakan lamarinku ya isa ace kune duk Wanda bai yi muku salati ba bai da salla». Sai Hamidu ya ce yana mai tsananin farin ciki: Hakika haka yake ya mahaifina ?! Don haka babu wani mutum da zai jahilci darajar Ahlul Bait(A.S.) Kuma wani abu ne ya faru a zamanin Imam Ja`far As-Sadik(A.S.) ? Haka kuma zamanin Imam Sadik(A.S.), a yayin ne daular Banu Umayya ta fadi wato Banu Abbas suka yi galaba a Kanta To ta yaya Banu Abbas suka yi suka ture daular Banu Umayya ? Hakan ya faru ne saboda sabubba guda biyu Na Farko: Shine cewa Banu Abbas sun san irin abinda ke zukatan mutane na kiyayya da fushi da kuma kin Banu Umayya, a sanadiyyar irin wahalhalun da mutane suka sha a hanun Banu Umayya na zalunci da tursasawa da kashe-kashe da balaóí wanda wanna lamari ya isa ya sa mutane su yaki Banu Umayya idan da yaki zai taso Abu na Biyu: Shine cewa yayin da yaki ya zo Sai Banu Abbas suka yi sanarwa cewa su basu yi wannan aiki ba, face don neman yardan Manzon Allah(S.A.W.A.) wato ta hanyar mayar da halifanci ga Ahlu Baitin Manzo(S.A.W.A.) to da yake Ahlul Bait sun kasance sune kan gaba kuma sune suke jagoranci, sannan sun zama take wanda mutane ke san ji to don haka sai aka soma yakar Banu Umayya da sunan Ahlul Bait(A.S.), kuma Imam Ja`far As-Sadik(A.S.) ya zamana yana sane da duk abinda ke faruwa saboda haka ya fadakar da shiΰrsa domin kada su bi irin wadannan take-take na rashin gaskiya wanda aka yi su domin yaudara kuma ya bayyana musu irin sakamakon da wadannan abubuwa zasu kai gare shi to bayan yaki ya kare, Banu Abbas sun yi nasara kuma suka kafa Daularsu, sai gaskiyar Imam Sadik(A.S.) ta bayyana ga kowa a sarari, bayan Ahlul Bait(A.S.) da shiΰrsu a yayin nan sun zama ana zaluntarsu ana tursasa musu a karkashin daular Banu Abbas har wani daga cikin mawaka ya tsara waka inda yake cewa: «Kaico, Ina ma da zaluncin Banu Marwan ya dauwama a garemu Kuma kaico ina ma da adalcin Banu Abbas ya zan yana wuta». A wannan lokaci sai idanun Hamidu suka cika da hawaye sai kuka yayi galaba a kansa sai na kama shi na kusato shi da kirjina na fara share masa hawaye ina cewa: Me yasa kake kuka ya kai da na... Sai maganganu suka fito bakinsa tare da hawaye: yana cewa: baka san yawan bege da nake yi ba, baba ina ma da ace na yi zamani da Imamai daga Ahli Baitin Manzon Allah(S.A.W.A.) in fanshe su da raina |
||