|
GAME DA RAYUWAR IMAM KAZIM (A.S.) |
||
|
LABARI DAGA KOGIN DAJLA
ΝίΗνΙ νΡζνεΗ δεΡ ΟΜαΙ
Ina cikin tafiya a gabar kogin Dijla a kasar Irak ina lura da yanda ruwan yake sai na ji kamar ruwan na ce mani in tsaya a daidai wani wuri a bakin Kogin sai ya fara bani labari, labari wanda ko da can ya bada shi ga mutanen da suka gabata ya kuma motsa zukatarsu nan da nan sai zuciyata ta yi kamar ta rabe biyu hawaye kuma sai kwarara yake a kumatu na, na kasa mallakar kaina sai ga ni ina daga muryata ina cewa: shin wanene a cikinku bai san kogin Dijla ba ? Wannan kogi da ya raba birnin Bagadaza kashi biyu shin kun taba tsayawa a gabarsa kun ga zuban hawayensa? Shin kun saurare shi da zukatarku da hankulanku ? Hakika tun shekara ta 183 bayan hijira wannan kogin ke ta bada labarinsa wa mutane , labari mai kona rai wanda birnin Bagadaza bata taba jin irinsa ba saboda haka ne ya saura tare da wannan kogi, kai ka ce jiya ne abin ya faru, a lokacin da wannan abu ya faru, tankar a wannan lokaci Birnin Bagadaza bata ga ketowan rana ba, wato kamar rana ta dushe a Bagadaza a ranar, zukatan shi`ar zuriyar Manzon Allah(S.A.W.A.) kuwa kamar an kyekketa, a wannan rana sama ta yi kukan jini, birnin Bagadaza sai cewa take: Wallahi kun yi karya da kuka ce ni gari ne mai aminci wani aminci ne a tare da wannan gari alhali a kulli yaumin zaluncin Banu Abbas da rashin adalcinsu sai gudana yake a cikina ga kuma irin kisan kai da kuma barna da suke yi ? Har lamari ya kai ga yau kuma zuriyar Manzon Allah(S.A.W.A.) aka kashe a nan, aka lullube shi cikin bakin tufafi aka aza kan gada sai kuma neman yin wasu tuhumce-tuhumce na karya ake shin wane irin jahilci ne ke tare da ku ? Kuma wane irin gaba ne ya sanya zukatarku suka kekashe suka zan tamkar duwatsu ? Sai kuka yanke wannan reshe daga itaciyar Annabicin Manzon Allah(S.A.W.A.) wannan reshe dake tamkar turare wanda ke cike da kanshi bayan kun kashe shi sai kuka yada gawarsa akan gada a Bagadaza Ashe haka kaskantattun rayuka ke aikatawa idan ashararancinsu ya yi galaba a kansu ko kuma zuga da tsegumi yayi musu galaba ba don komai ba, wai domin a samu kusaci zuwa ga shugabanni azzalumai ta hanyar kuntata wa masu kira zuwa ga shiriya a kuma zubar da jininsu shin wadannan mutane sun tambayi kansu kuwa dangane da abinda suke aikatawa na zalunci da matsin lamba a dalilin me suke aikata haka shin don neman mukami ne na jabu ko kuwa don jin dadi dan kadan mai karewa, wanda ransu ta gwada musu, irin wannan rai batacciya, wulakantacciya, kaskantacciya wanda take neman ta biya bukata ga wasu, domin su yarda da ita Ina cikin share hawayena sai na daga ido na kalli mutane dake kewaye na, sai na ga saboda tsananin kuwa da suke yi, kamar hawaye ya tona rami ne a kumatunsu ga kuma zukatarsu tamkar ta rabe biyu kai ka ce suna ganin abinda ya faru tun waccan lokacin ne a gaba gare su sai wani tsoho daga cikinsu ya taho gurina-gemunsa duk ya jika da hawaye, yana min magana cikin kuka sai ya ce mani: da na hakika tarihi ya bamu labarin irin zaluncin da shugabanni sukai ta yi wa Ahlu Baitin Manzon Allah(S.A.W.A.) da kuma kin Imamancinsu da Khalifancinsu da suke yi Koda yake Imam Musa Al-Kazim(A.S.) ya ga sa ido mai tsanani daga gurin hukumar lokacin, ya kuma zauna a fursunoni daban daban a lokacin to saidai kuma duk da haka, Imam Kazim ya kasance yana ci gaba da aiwatar da sakon iyayensa wato sakon yada ilimin addinin musulunci da yada hadisai da kuma dabi`u na kwarai ya kuma kasance yana kare musulunci yana kuma lura da musulmai mafi karancin abin da aka fada dangane da shi, shine cewa idan ya bada jakar kudi ga fakiri to fakirin ya zama mai arziki kenan, talauci bai kuma sanin inda yake Ya kai wannan tsoho! Ai wajibi ne ya zan haka ? Shin ko ba shi Imami ma`asumi bane daga zuriyar Manzon Allah(S.A.W.A.) ? Shin ko ba shi bane biyayya gare shi ta wajaba akan musulmi- don haka ne wannan masarauci daga Banu Abbas wato Harun Ar-rashid yake fushi da shi wannan ne kuma ya sanya Harun Rashid yake ta tunanin hanyar da zai kashe shi, musamman idan ya ji yadda mutane suke zagaye Imam Kazim(A.S.) domin su yi masa tambaya kan lamuran addini, su kuma nemi ilimi a wajensa, ga kuma ba shi zakka da Khumusi da mutane ke yi wani abinda ya kara munana lamarin shine cewa daya daga cikin mutanen dake kusa da Imam Kazim(A.S.) shine ya kai tseguminsa wajen Haruna Rashid ba kuwa don komai ba sai don kwadayin duniya da son duniya da kuma hadamarsa akanta, don haka ya je ya tsaya a gaban Harun Rashid domin ya gaya masa duk sirrin Imam Musa Kazim, wanda jin haka ya sa Harun Rashid ya ji tsoro matuka akan mulkinsa don haka sai ya sa a zo masa da Imam Kazim ya sa shi a fursuna Daga nan sai na yi shiru sai tsoho ya juya gurin mutane ya ce musu: Shin kun san abin da Harun Rashid ya gaya wa Imam Musa bin Ja`afar Al-Kazim(A.S.) ? Harun Rashid cewa yayi wa Imam Kazim:ta yaya kuka halatta mutane su danganta ku ga Manzon Allah har suna ce maku `ya `yan Annabi alhali ku `ya `yan Aliyu ne shi mutum ai ga babansa ake danganta shi ba ga mahaifiyarsa ba ? Shin Haruna Rashid bai ga ayar Al Kur`ani bane, inda Allah Ta`ala Yake cewa:To wanda yayi jayayya da kai a cikinsa, bayan abinda ya zo maka daga ilimi, to ka ce: ku zo mu kira `ya `yanmu da `ya `yanku da matanmu da matanku, da kanmu da kanku, sa annan mu kankantar da kai mu sanya la anar Allah akan makaryata surar Ali Imran aya ta 61. Kuma hakika musulmi dukaninsu sun yi ittifaki kan cewa Manzon Allah(S.A.W.A.) ya kira Aliyu da Fatima da Hasan da Husain(A.S.) a wannan lokaci Aliyu sai ya zama shine Kanmu a wannan ayar, Fatima ta zan ita ce matanmu a ayar, sannan Hasan da Husain suka zan sune `ya `yan Annabi To me zai sa Haruna Rashid ya tambayi Imam Kazim(A.S.) wannan tambaya ? Shin saboda jahilci ne ko kuma yana so ya ki yarda da lamarin Allah ne ? Nan ne fa sai daya daga cikin mutanen dake wajen ya ce: to menene Haruna Rashid ya aikata bayan haka ? Sai tsoho ya amsa masa ya ce: Haruna Rashid ya sanya Imam yana shiga fursuna bayan fursuna sannan daga karshe ya sa shi a fursuna a Bagadaza a wannan fursuna na Bagadaza ne aka ba wa Imam wani kwano da dabino mai guba a ciki sai Imam ya ci wannan dabino shi kenan ya soma mike-mike saboda tsananin ciwo ya saura cikin haka na tsawon kwana uku yana fama da yayyanke hanjin cikinsa da guba yayi har ya bar duniya Bayan haka sai na ga tsoho ya nufi ta inda kabarin Imam Musa Kazim(A.S.) yake, mutanen dake wurin suma sai suka bi bayansa nima sai na bi su, bayan na gane cewa zasu je ziyartar kabarin Imam Musa bin Ja`afar(A.S.) ne. |
||