|
GAME DA RAYUWAR IMAM BAKIR (A.S.) |
||
|
SAFARA A CIKIN LITTAFI
ÑÍáÉ ÚÈÑ ßÊÇÈ
Ina cikin karanta wani littafi… yayin da nake bubbude shafinsa… sai na ji kamar ina shiga wani dadadden gari ne, wanda ga alamu gari ne na musulmi… domin kuwa da yawa daga mutanen dake wucewa gaba gare ni suna sanye ne da tufafi na musulunci… to saidai kuma akwai wasu alamu da suka saba ma wannan, domin kuwa ina ganin wasu mutanen da suke wucewa gaba gareni suna maye, suna tafiya suna tangadi… ga kuma daga muryarsu da suke yi suna kyalkyalewa da dariya, ga shi suna yin wasu irin zantuttuka da basu dace a fade su a wuraren taro ba, suna zance ne akan mata suna kuma sifanta jikinsu da kyawunsu… ina kuma jin kade-kade daga wurare daban-daban… ina cikin wannan tafiya tawa sai na ga wani saurayi dake sanye da tufafi na musulunci yana tahowa ta inda nake… koda na lura da shi sai na ga alamun cewa saurayi ne mai ladabi mai dabi`u na gari…
koda ya matso kusa da ni sai na yi masa sallama… da jin sallamata sai ya tsaya yayi murmushi ya amsa sallamata sannan ya ce: ya dan uwana na ga kamar kai bako ne, yanayin tufafin da ka sa na nuna haka… Sai na ce masa: E haka ne… amma kada ka damu da haka ina so ne in tambaye ka dangane da wannan gari… domin ni na ga shi wannan gari yanayin ginin gidajensa da irin tufafin mutanensa na nuna kamar gari ne na musulunci… amma a daidai wannan lokaci kuma na ga wasu alamu da basu dace da musulunci ba shin menene ya sanya haka…? Sai nan da nan na ga yaro na bakin ciki, sai ga hawaye na zubo masa yana kuma cewa: Ai wannan aikin Banu Umayya ne… su Banu Umayya sun halatta ma kansu duk abinda suka ga dam, saboda ganin hukuma tasu ce Sai ni kuwa na ce: Banu Umayya dai…? Wai shin har yanzu suna kan mulki…? Yaro sai ya fara share hawayensa sannan ya ce mini: ka san su ne? Sai na ce: na san ababe da dama dangane da su a yayin da nake karanta tarihin Ahlul Bait(A.S.)… Yace mini: Ya dan uwana ai yanzu muna zamanin Imamancin Imam Bakir(A.S.) ne… amma ga Banu Umayya har yanzu suna nan suna tabka munanan aiyuka iri-iri a ko`ina suna masu bayyana fasikanci da alfasha a gidajensu da wuraren tarurrukansu da kuma duk inda suka je… Sai saurayin nan ya sake fashewa da kuka… Sai kuka ya hana shi ci gaba da maganarsa… nima sai na yi bakin ciki sosai ganin irin halin da yake ciki… sai na fara zance domin in dan kawo masa sauki… na ce masa: dan uwana ka yi hakuri… Sai ya ce: Ya kai danuwana hakika abinda yake gudana a gidajen wadannan mutane, abin bakin ciki ne matuka, ga shi kuma har yayi tasiri akan sauran musulmai, don haka suma suka wayi gari suna aikata dukkan munanan aiyuka… suna neman dukkan abubuwa na son… zuciya da kuma abubuwan yaudara na duniya… to me muka iya…? Hakika shugabannin Banu Umayya sun bi hanyoyi daban-daban na zalunci da azaba da matsin lamba domin su gina daularsu da mulkinsu… don haka suka kashe marasa laifi da masu kawo gyara… suka kuma yi almubazaranci da dukiyar musulmi ba don komai ba sai domin kare mulkinsu da bin son zuciyarsu… hakika shi`ar Ahlul Bait… da kuma zuriyar Imam Ali(A.S.) sune wadanda wannan bakar siyasa ta fi cutar da su, ba kuwa don komai ba sai don su Ahlul Bait suna da irin daukaka na ilimi da kuma halaye na kwarai da yasa mutane ke karkata zuwa gare su, kuma har ila yau saboda su Ahlul Bait suna da sifofin yin Khalifancin Manzon Allah(S.A.W.A.)…
Na ce masa: ni na san cewa Banu Umayya sun kai intaha na bin hanyoyin rashin tausayi wajen matsin lamba wa Ahlul Bait(A.S.) da su da shi`arsu… kuma Banu Umayya sun wuce misali wajen zubar da jini da yaudarar mutane ta hanyar kudi har ya zamanto rayuwa ta cika da zalunci da barna… Mutane kuwa har yanzu suna nan suna ci gaba da rashin taimakonsu ga Ahlul Bait(A.S.) a daidai wannan lokaci da Banu Umayya ke matsa lamba wa Ahlul Bait, alhali su Ahlul Bait manufarsu ita ce su kawar da zalunci daga masu rauni da kuma miskinai, su kuma tserar da musulunci daga wannan irin makoma da yake masa barazana, matsawar su wadannan shugabanni suka ci gaba da zaluncinsu… hakika abubuwa sun canja, kuma yanayin tunani ma an canja shi, wato dai abubuwa daban-daban na al ummar musulmi, sun canja, tun daga abinda ya shafi akidarsu da tunaninsu da kuma abinda ya shafi sauran lamurra na rayuwa… sai wasu irin tunani da akidu suka bulla, wanda a tare da irin wadannan akidu da tunani babu komai face kafirci da musanta Allah Ta`ala, kuma dukkan wadannan ababe da suka shafi al ummar musulmi sun ci gaba da aukuwa har suka zamanto suna yin barazana wa asasin akidar musulunci… wadanka kuma suko zo da irin wadannan… tunani suka kuma yi musu shimfida, mutane ne wadanda babu abin da ya hada su da musulunci sai kawai suka kirkiro akidu suka kuma sanya musulmai suna dauke da su… To a dangane da irin wadannan hadarori dake barazana wa tunanin musulmi, wane irin mataki Imam Bakir(A.S.) ya dauka…? Domin na karanta a tarihin Imam Bakir(A.S.) cewa shine Imami a bayan Imamancin babansa Imam Zainul Abidin Ali bin Husain(A.S.)… Kuma shi Imam Bakir ya tsere wa dukan sauran `yan uwansa a ilimi da zuhudu da daukaka, kuma ya fi dukan sauran yan uwansa kyakkyyawan ambato… ya kuma fi sauran yan uwan nasa daraja da falala a wajen dukan musulmai shi`a da sunna… Abinda ya bayyana daga Imam Bakir(A.S.) na ilimi da ruwayoyi da tafsiri da kuma sauran fannoni, bai bayyana haka ba a wajen sauran `ya `yan Imam Hasan da Husain, don haka ne aka yi wa Imam Bakir(A.S.) lakabi da Al-Bakir saboda fito da ilimi da yayi wato zurfafawa da yayi a cikinsa har ya san dukan tushensa da asasin sa… to sabili da kasancewar Imam Bakir Imami daga cikin Imamai goma sha biyu shi ya sa na tambaye ka irin wajibinsa da ya aiwatar a irin wannan hali da al`ummar musulmi ta shiga ciki… Sai ya amsa ya ce: a cikin irin wannan yanayi dake cike da sabani na akidoji sai Imam Bakir(A.S.) ya ga cewa maslahar musulunci na tilasta masa da ya mai da hankalinsa wajen kare akidar musulunci da kuma yada koyarwarsa… Sai kuwa dubban mutane suka zagaye shi, domin neman ilimi da kuma ruwaito hadisai daga gareshi… mutane daban-daban, shi`a da wadanda ba shi`a ba… Imam Bakir(A.S.) kuma sai ya rika zama da su yana koya musu karatu a masallacin Madina… wannan darussa da Imam Bakir(A.S.) yayi ta koyarwa a wannan wuri, an kira shi tamkar karatu ne a jami`a, saboda kasancewar ta ta taro mutane daruruwa daga sassa daban-daban wadanda suka zo neman ilimin fikihu da hadisi da tafsiri da falsafa da lugga da sauransu daga fannonin ilimi iri-iri… Kuma garuruwa irinsu kufa da Basra da Wasit da Hijaz sun aika da zababbun `ya `yansu zuwa ga wannan jami`ar … wanda daha nan zasv zama manyan malaman hadisai da kuma manyan maruwaita… Sai na ce masa: wanene mai mulkin Banu Umayya a wannan zamani naku…? Sai ya ce: Abdul Malik bin Marwan shine yanzu yake mulki… koda yake shi wannan mai mulki da farko ya so ya rage matsin-lamba ga zuriyar Imam Ali(A.S.) a zahiri ta yadda ba zai aikata irin abinda magabatansa suka aikata ba… har ya rubuta takarda zuwa ga gwamnansa a Hijaz ya ce masa: “Ka nesatar da zubar da jinin zuriyar Abu Talib daga gare ni” mu kuwa da muka ji haka sai muka dauka cewa ya gano irin fushi da kuma rashin jin dadi da siyasar Muawiya da dansa Yazid ya haifar ne… wanda daga bisani ya jawo yunkuri da bore a wurare daban-daban cikin al ummar musulmi… amma abinda ya bayyana daga baya shine cewa ashe dama shi Abdul Malik bin Marwan yana da wani abokin hamayya ne a Hijaz wanda ake kira Ibnu Zubair… wanda shi wannan abokin hamayyar nasa ya so ya mamaye wurare da suka shafi kamar Irak da kuma wasu gurare… to bayan Abdul Malik ya samu yayi galaba kan wannan abokin hamayyar nasa… sai ya rubuta takarda zuwa ga gwamnoninsa ya umarce su da su kuntata wa shi`ar Ahlul Bait, kada su sassauta musu ko su ji tausayinsu… sannan ya umarci Hajjaj da ya je Iraq ya zama gwamna a can, ya ce masa:”Ka yi yaudara domin ka kashe su, saboda na samu labarin abin da bana so daga gare su… kuma idan ka isa garin Kufa… ka aikata wa mutanenta irin abin da zai zama darasi wa mutanen Basra” bayan haka kuma ya ci gaba da sa ido a kowane motsi da ake yi… Sai na ce masa: Na karanta tarihin Hajjaj sai na tarar cewa abinda Hajjaj ya aikata da Imaman Ahlul Bait(A.S.) da su da shi`arsu, babu abinda ya kai shi muni cikin dukan wahalhalun Ahlul Bait da tarihi ya rubuta… musamman abinda ya aikata da shi`ar Ahlul Bait da suke Irak… tun da shi Hajjaj yana bin umarnin Abdul Malik bin Marwan ne, wato kenan da umarninsa ne Hajjaj ya aikata abin da ya aikata… - Wannan daidai yake… - Ya dan uwana akwai wani abin da ya dame ni, abin kuwa shine cewa… Abdul Malik bin Marwan yayin da ya ga wata takardar kudi wanda ke dauke da wata alama wadda aka yi ta da harshen Rumanci… sai ya bada umarni a fassara zuwa larabci… Koda aka fassara sai ya tarar ma anar ita ce “Uba… Da… da Ruhi mai tsarki” wannan abu sai ya fusata shi.. Don haka sai ya rubuta takarda zuwa ga dan`uwansa dake gwamna a Masar wato Abdul Aziz bin Marwan… ya umarce shi da ya bata wannan alamar da aka sa akan takardar kudin… daga bisani ya ce masa: ya sa masu buga takardun Kudi su yi alama da surar Al-Kur`ani… haka kuma ya rubuta wa gwamnoninsa dake sauran gurare ya umarce su da su bata takardun da aka yi masu alama ta Rum… Kuma su yi ukuba ga duk wanda aka sake samunsa da wannan kudi bayan hani da aka yi… su yi masa bulala su kuma daure shi na tsawon lokaci…! Sai ya ce na gane manufarka ya dan uwana… ai akwai da yawa daga cikin mutane wadanda suke damuwa da zahirin musulunci amma ba hakikaninsa ko badininsa ba… to Abdul Malik bin Marwan yana daya daga cikin irin wadannan mutane… Kuma duk da Cewa shugaban Rum yayi kokari ya ga ya hana Abdul Malik wannan abu… amma Abdul Malik bai nuna wani sassauci akai ba. Daga karshe sai shugaban Rum yayi barazana wa Abdul Malik da cewa zai buga Kudi, dinari da dirhami Kuma alamar da zai sanya akansu ita ce zagin Annabi(S.A.W.A.)… to menene ya sa kasa kamar Rum zata shiga al`amarin wata kasa daban, har ma abin da ya shafi kudin da ita wannan kasa ke mu amala da shi…? - Wannan kuwa ya faru ne saboda kasarmu bata da nata kudin na kanta wanda take ma`amala da shi… dukan dinari da dirhami gaba daya dama kasar Rum ita ce take buga su a Masar… to tun da ita kasa ce ta kirista don haka suke sa alama ta kirista… To anan ne sai Abdul Malik ya samu kansa cikin halin kaka nikai… ya rasa mafita cikin wannan barazana da aka yi masa… sai ya shawarci wadanda ke kewayensa, amma bai samu mafita ba… daga karshe sai aka yi masa ishara da cewa ya nemi shawarar Imam Bakir(A.S.)… koda ya shawarci Imam Bakir(A.S.) sai Imam ya ce masa: yayi amfani da iya gwargwadon zinari da azurfa da ake da su a cikin kasa, ya buga kudi da su kuma ya sanya alama irin ta musulunci akansu… daga bisani ya sanya masa tsari wanda yake ba zai taba yiwuwa a samu a yi wasa da farashin dinari da dirhamin ba… - Wannan haka yake… to tun daga lokacin muma muka zamanto muna da namu kudin da muke mu amala da shi a cikin kasa. - To saidai yaya aka yi Imam Bakir(A.S.) ya taimaki wannan shugaba azzalumi wato Abdul Malik bin Marwan - har ma ya fitar da shi daga cikin wannan hali na kaka nikai… ya kuma warware masa wannan matsala wanda ta kusa ta kawo karshensa…? - Ai amsar wannan tambaya, mai sauki ce… bata bukatar wani tunani akanta… dalili kuwa shine… kowane Imami Maasumi, ya kan sanya maslahar musulunci sama da dukan abubuwa… don haka yayin da Imam Bakir (A.S.) ya tarar cewa maslahar musulunci a nan ita ce a taimaka wa Abdul Malik bin Marwan dangane da lamarin buga kudi… sai nan da nan Imam ya aikata haka… ba kuma don shi Abdul Malik ba, a a saboda amfanin musulunci da musulmai… Bayan haka sai saurayi yayi murmushi da kyau sannan ya ce: kana da wasu tambayoyin ne…? Sai na ce masa… na gode maka dan uwana da wannan kokari da ka yi… Allah ya kiyaye ka… mu huta lafiya… Bayan mun yi ban kwana da saurayi… sai na rufe littafin da dama ke gaba gare ni… kai ka ce dama mafarki nake… |
||