|
GAME DA RAYUWAR IMAM SAJJAD (A.S.) |
||
|
YUNKURI NA HAWAYE
ΛζΡΙ ΗαΟγζΪ
Na kasance ina zaune ni kadai ina duban abubuwan da suka faru a tarihi sai na tarar tarihi ya daga lullubinsa, daya bayan daya sai ga ni nan na samu kaina ina shiga wani bene wanda yanayin gininsa ya sha bamban da gine-ginen wannan zamani sai na tsaya ina mamakin abinda na gani gaba gareni wato mutane ne wadanda suke sanye da tufafi na musulunci amma sai daga muryoyinsu suke yi suna kyalkyala dariya ga kuma kofunan giya nan sai sha suke suna mika ma junansu, a wannan wuri kuma sai kade-kade ke tasowa ga kuma mata nan sai juyawa suke suna rawa suna kada jiki saidai kuma ana cikin wannan hali na kyalkyalewa da dariya da kuma kade-kade da raye-raye sai kuma ga wata murya tana kuka tana nishi sai kuwa na fito domin na ga wanda yake kuka daga bisani in san musabbabin kukansa anan ne fa sai na ga wani dattijo na tafiya a gefen hanya kusa da ni, yana yin magana da taushin murya yana cewa tir da ku Banu Umayya, kaicon ku wane irin zamani ne wannan wanda fandare wa addini ya mamaye shi ga kuma rashin ladabi, da rashin dabi`u na gari duk sun watsu ko`ina wane irin zamani ne wannan wanda mahukunta azzalumai ke mulkinsa ga su basu san komai a addini ba face suna basu kuma san komai daga gaskiya ba face hoto har ma mutum ya sami kansa a wannan zamani a tsakiyar yakoki masu tsanani wadanda kungiyoyi da jam`iyyun siyasa da na zamantakewa masu fakewa da musulunci suke ta yin su mafi karancin makirci da kuma lalacewa dake cikin wannan zamani, shine cewa mutum musulmi yanzu bai da tsarkin niyya babu tsarkin ruhi babu tsabtar batini ayyukan riya sun yi yawa ga kuma munafunci ya yadu a tsakanin mutane anan kenan wajibin mutum mumini mai kula da addini, dole ya zan ya kara nauyi akansa ni kuwa sai na je wajen wannan tsoho nace masa: malam yi hakuri ban gane abinda nake gani ba a gaba gare ni ! Domin kuwa na ga wasu mutane na sanye da tufafi na musulunci saidai kuma abin takaici irin ayyukan da suke aikatawa ya zan tamkar suna raye ne a zamanin jahiliyya Nan ne fa sai dattijo ya fashe da kuka yana cewa: kenan kai baka jin labarin Banu Umayya ? Sai yayi shiru na dan lokaci yana kallona sannan sai ya ce: da na kamar kai kana raye ne cikin wani zamani ba namu zamanin ba ?! Sai na yi murmushi na ce masa: ba komai gareka idan ka kasa amsa tambayata amma zaka iya gaya mini shin wane mutum ne wannan da yake ta kuka, wanda kukansa da nishinsa ya game gari ? Sai ya ce: da na wancan mutumin ai shine Imam Ali bin Husain As-Sajjad(A.S.) Kuma tun lokacin da aka yi yakin Karbala yake akan irin wannan hali na kuka da bakin ciki Sai na fada cikin ta`ajjubi: na ce: shin Imam Sajjad(A.S.) zai kare rayuwarsa ne da kuka saboda musibar da ta shafi Babansa Imam Husain(A.S.)ύ ? To menene wajibin Imam dangane da irin wadannan abubuwa dake faruwa a matsayinsa na Imami maasumi wanda wajibin kare sakon Annabi Muhammadu kakansa(S.A.W.A.), ya rataya a wuyansa. Anan ne sai na ji dattijon nan ya daga muryarsa yana ce mani: ba haka bane ya dana! Wajibi ne ya zan baka yi wani shakka ba kan wajibin Imam Sajjad(A.S.) domin kuwa babu wanda yake iya kamanta dukan abinda ya zo a sakon Manzon Allah(A.S.) face Ahlu Baitinsa(A.S.) sune asasin sakon addinin musulunci, kuma a gidansu ne wahayi ke sauka, wurinsu ne mala`iku ke kaiwa da komowa, da su ne Allah Yayi budi kuma da su zai rufe ya da na ka sani cewa kukan Imam Sajjad(A.S.) ba saboda abinda aka yi wa mahaifinsa Imam Husain da shi da sahabbansa da mutan gidanas a ranar goma ga watan Muharram bane a a, kukansa yana yin sa ne domin ya tuna wa mutane muhimmancin sabubban da suka janyo har Imam Husain(A.S.) yayi irin wannan sadaukarwa mai girma wanda daga karshe ta jawo shahadarsa, da shahadar `ya `yansa da `yan uwansa da `ya `yan yan`uwansa da sahabbansa, sannan aka kame matansa a matsayin fursunonin yaki, wanda a wannan yunkuri da Imam Husain(A.S.) yayi, manufarsa ita ce ya raya zuciyar bil Adama, ya kuma wayar da kan dukan kwakwalwa mai tunani saboda haka kukan Imam Sajjad a matsayin abu ne da ke kammala yunkurin da mahaifinsa(A.S.) yayi, Imam Sajjad yana nufin ya farkad da zukatan mutane ne ya kuma motsa tausayinsu daga bisani ya tunatar da su kan abinda mahaifinsa Imam Husain(A.S.) ya gabatar, bayan Banu Umayya sun zama suna kiran mutane zuwa ga guraren wasanni da guraren rawa da kade-kade, da shan giya ga shi mutane kuma suna karkata zuwa ga wadannan abubuwa, sun mance abinda Imam Husain(A.S.) ya sadaukar da kansa dominsa saboda ya kare addinin mutane sabili da haka ne Imam Sajjad(A.S.) ya ga cewa wajibi ne akansa ya gyara abinda Banu Umayya suka bata shi daga sakon kakansa Manzon Allah(S.A.W.A.), kuma da haka yayi nufi ne ya kammala hanyar da mahaifinsa Imam Husain shugaban shahidai ya fara don haka kukansa da yake yi dangane da musiba mai girma da ta faru ranar 10 ga watan Muharram manufarsa ita ce ya tunatar da mutane game da wannan musiba mai kona zuciya wanda ta hanyarta ne babansa Imam Husain(A.S.) ya kare asasin addinin musulunci- da haka kuma Imam Husain(A.S.) ya sanar da al`umar musulmai yadda zasu kare addini da yadda zasu sadaukantar da kansu domin addini domin kuwa daukakarsu na tattare da kare addini, hakanan darajarsu da kuma lahirarsu dukansu na tattare da addini- don haka Imam Sajjad(A.S.) duk inda yake hatta lokacin da ya tafi kasuwa ya tarar mahauci ya yanka rago misali Sai ya tambaye shi cewa shin ya shayar da ragon ruwa kafin ya yanka shi ko kuwa sai mahaucin ya bashi amsa ya ce: ai ba na yanka rago face sai bayan na shayas da shi ruwa a nan ne sai Imam Sajjad(A.S.) ya kalli taron jama`a ya ce musu: Ku duba hatta rago ma ba a yanka shi har sai an shayar da shi ruwa amma mahaifina Imam Husain an kashe shi da kishirwa ba a ba shi ruwa ya sha ba Manufar Imam Sajjad a nan ita ce ya bayyana wa mutane irin halin kekasan zuci wanda Imam Husain(A.S.) yayi shahada a ciki, da shi da wadanda ke tare da shi daga sahabbansa da mutanen gidansa. Akwai kuma wata hanyar da Imam Sajjad ke amfani da ita domin ya bayyana wa mutane hakikanin abinda ke gudana a kewayensu yana ce musu:idan kun ga mutum, maganarsa da dabi`unsa sun yi kyau kuma yana yin tawali`u daidai gwargwado a ayyukansa, to ku lura da shi sannu-sannu, kada ya rude ku, domin akwai da yawa daga mutane wandanda suka kuma gaza samun duniya, suka kuma gaza samun haramun saboda rauninsu da gazawarsu da kuma tsoronsu, amma sai suka fake da addini suka zama suna yaudarar mutane da zahirinsu, irinsu kuwa da zarar ya samu damar aikata haramun sai ka ga ya jefa kansa ciki kuma idan kuka ga mutum ya kame kansa daga kudin haram to shima ku lura da shi a hankali, kada ya rude ku domin kuwa sha`awar mutane ta kasu iri-iri sau da yawa zaka ga wasu sun ki aikata wani aiki na haramun koda ya yawaita, amma a wani bari kuma sai ya dora wa ransa wata mummunan aiki, ka ga ya aikata haramun daga ta nan don haka kada mutum ya rude ku har sai kun ga karfin kwakwalwarsa da dalilinsa domin zaka samu wani ya bar dukan wadannan aiyukan amma ba saboda wani dalili ingantacce na hankali ba sai ya zamana a binda zai aikata na barna saboda jahilicinsa, ya fi abinda zai gyara shi da irin wannan kwakwalwa tasa . Idan kuma kun samu cewa yana da cikakken hankali da kuma kwakwalwa mai kyau to nan ma kada ya rude ku har sai kun duba kun ga shin ya kan fifita son zuciyarsa akan hankalinsa ne ko kuwa ya kan kaddamar da hankalinsa (kwakwalwarsa) akan son zuciyarsa sannan yaya kwadayinsa yake ga son mulki na karya, reman sa yake ko kuwa gudunsa yake yi sa boda akwai daga cikin mutane wanda ya kan bar duniya saboda neman duniya sai su ga cewa dadin mulki na karya shi ya fi musu akan shugabancin kudi da shugabancin ni `imomi na halal don haka sai ya bar kudin haram saboda neman mulki da sarauta idan aka ce masa: ka ji tsoron Allah sai girman kai ta debe shi ya aikata laifi to wutar jahannama ta ishe shi, kuma wannan makwanci yayi muni zaka samu yana fadi- tashi babu hankali cikin aikinsa, son sarautarsa da mulkinsa ya zan yana jansa zuwa ga zalunci da dagawa sai ya halatta abinda Allah Ya haramta, ya kuma haramta abinda Allah Ya halatta bai damu da abinda ya tsere masa ba daga addininsa, matsawar mulkinsa da sarautarsa tana nan babu abinda ya taba ta. Wato dai Imam Sajjad(A.S.) da ya ga cewa yanayin da ake ciki bai dace da ayi yunkuri na soji ba sai ya bi wata hanya domin ya wayar da kan mutane ya kuma kawo gyara a al`umma domin ya nuna musu wajibinsu na fuskantar hukuncin Banu Umayya, bayan ya samu ya kawar da ababen da suka yi lullubi wa siyasarsu da su Daga nan sai fuskar dattijo ta yi haske saboda farin ciki yana kuma ce ma ni: lallai dama wannan shine abinda na so in yi maka bayaninsa- cikin wannan maganata da na yi maka Ashe kenan Imam Sajjad, yayi nufi ne ya fadada alakar mutane da Ahlul Bait(A.S.) ya kuma karfafa alakar shi`a masu biyayya ga Ahlul Bait tsakaninsu da zutiyar Manzon Allah(S.A.W.A.) ta hanyar motsa tausayinsu da zukatarsu daga bisani kuma ya nuna musu soyayya ta hakika wato soyayyar Ahlul Bait a aikace, alabashi daga ta nan ya samu ya karfafa matsayin mutane wajen kare sakon kakansa Manzon Allah(S.A.W.A.), bayan ya samu ya samar da mutane masana wadanda suke da tunani irin na musulunci tsintsa olomin su jagoranci lamarin akidar mutane da abinda ya shafi tunaninsu don haka ne ya zamanato a kowane lokaci sai Imam Sajjad ya zan yana shirya majalisin ta aziyya a gidansa saboda ambaton Imam Husain(A.S.) shi da mutan gidansa da sahabbansa ya saura cikin zukatan al`umma Akwai kuma har ila yau wata hanya da Imam Sajjad(A.S.) ya bi wajen fadakar da mutane, wannan hanyar kuwa ita ce hanyar addua- domin ita addu`a tana da fuskoki biyu tana da fuskar ibada, tana kuma da fuska ta zamantakewar jama`a, wannan fuska kuwa ta saje ta yi daidai da lamarin kawo gyara da Imam Sajjad(A.S.) yake yi. Wadannan addu`o`I na Imam Sajjad suna karfafa mu a ruhinmu da kuma a mu amalarmu da jama`a ta hanyoyi daban-daban domin kuwa bayan ta koya mana yadda zamu daukaka Allah da yadda zamu tsarkake shi, da kuma yadda zamu yi munajatinsa mu koma gare shi, mu kuma tuba gare shi-sai ga shi tana kuma koya mana yadda zamu yi biyayya ga iyaye tana mana bayanin hakkokin uba akan dan sa da hakkokin da akan mahaifi da hakkin makwabta da hakkin kowane musulmi akan dan`uwansa musulmi cikin dukan lamurra Imam Sajjad ya zabi gidansa da kuma masallacin Annabi, domin su zama wurare masu albarka wadda zai yi amfani da su domin yada ilimi na addinin musulunci kuma da sannu zai yi tarbiyya wa mutane a wannan makaranta tasa, mutane wadanda zasu shugabanci lamarin ilimi kuma al`ummu zasu dogara akansu To bayan wannan dattijo ya kare maganarsa, sai na yi masa murmushi, sa annan na ce: na gode maka sosai dattijo hakika ka yi mini bayani mai kayatarwa dangane da hanyar gyara da Imam Sajjad(A.S.) ya dauka Wannan `yar tafiya tawa da na yi ta a cikin abubuwan tarihi, tafiya ce mai dadi sai na ji kamar nima na rayu a wancan zamani Bayan haka sai na ci gaba da bin lamurran tarihi, a cikin littafan tarihi da aka rubuta su, ina kuma tambayar kaina: Shin Imam Ali bin Husain As-Sajjad ya ci nasara kuwa a wannan aiki nasa ? Hakika domin kuwa bayan nan sai ga Imam Sajjad(A.S.) ya wayar da kan jama`a masu yawa sosai bayan sun ga iliminsa da ibadarsa sai suka karkata zuwa gare shi, hakannan bayan hakurinsa da kawaicinsa da cika idon mutane, karamcin sa da kyauta yinsa kuma ya mamaye zukatar su sai aka wayi gari kowa sai neman saduwa da Imam Sajjad(A.S.) yake yi wanda yayi arziki a cikinsu shine wanda ya sami ganinsa ya kuma ji zancensa wannan abu sai ya zamana Banu Umayya basu ji dadinsa ba rashin dadi na intaha musamman ma Walid bin Abdul Malik, domin wannan mugun mutum shine ya fi dukan sauran mutane hasada wa Imam Sajjad, a nan ne fa sai Walid ya zan yana cewa: ai ni Walidu ba ni da hutu, matsawar Ali bin Husain na raye a duniya Ba a kuwa dade ba, ran nan sai aka ji Imam Sajjad - Ali bin Husain yana mike-mike akan gadonsa guba ta kama jikinsa sai tsananin ciwo yake ji me ya faru kuwa ai wannan mugun mutum Walidu bin Abdul Malik shine ya aikata wannan mummunan aiki shine ya nemi wani ya sa guba wa Imam Sajjad Koda mutane suka yi gaggawa zuwa ga Imam Sajjad(A.S.) domin su duba halinsa, sai suka same shi yana addu`a, yana rokon Allah, yana yabonsa, yana masa godiya a daidai lokacin kuma yana fama da ciwo mai tsanani Imam Sajjad ya saura cikin wannan hali na tsawon kwanaki bayan haka yayi shahada a ranar 25 ga watanMuharram mai alfarma a shekara ta 95 bayan hijira a yayin nan yana da shekara 57 a duniya |
||