|
GAME DA RAYUWAR IMAM HUSAIN (A.S.) |
||
|
KUMA SAI LOKACI YAYI
ζΝΗδ ΗαζήΚ
Yayi dogon numfashi yayin da yake kan kujerar mulki bayan mutuwar baban sa, ya ci gaba yana magana cikin murna yana cewa: yanzu na zama mai mulki Saidai kuma ba a dade ba sai wannan tunani ya fado masa, sai ya ji kamar wata murya na ce masa: ai yanzu lokaci yayi da asirinku zai tonu, kuma a yaye lullubi daga fuskarku sai ya gyara zama ya ce: wani lullubi? Lullubin da babanka ya matsa domin ya ga cewa ba a yaye shi ba, wannan lullubi da ya rufa dukan aiyukansa da shi, ya kuma samu ta haka har ya gudanar da siyasarsa a kan kwakwalen mutane hakika yayi matukar kokarinsa domin wannan lullubin ya saura da kyanasa, domin da haka ne ya shar anta dukan abinda yake yi a fuskar jama`a wato ya nuna musu cewa shari`ar musulunci bata saba da abinda yake yi ba Sai Yazid ya fara jin tsoro bayan ya ji wannan magana, amma kuma sai yayi kokarin magance lamarin yana mai cewa: ai nima hakan zan yi zan ci gaba da kare wannan lullubin, kamar yadda babana ya aikata domin nima in rufe siyasa ta da shi Sai ya ji kamar wannan muryar ta kyalkyala dariya, tana mai cewa: Kai din kuwa ? Shin wanene bai san Yazid bin Muawiya ba mashayin giya wanda a kullum babu abinda yake sha`awa tamkar kiwon birai da tsuntsaye da kuma kafa tarurrukan wasanni da na kade-kade wace irin al`ummar musulmi ce zata yadda da rayuwar jahiliyya a karkashin tutar musulunci bama haka ba ai babanka ya kunyata kansa yayin da yayi wasicci da ka zama Khalifarsa alhali, wannan Khalifanci hakkin Imam Husain(A.S.) ne idan za a bi gaskiya. Yazidu sai ya sunkuyar da kansa ya shiga wani tunani mai zurfi daga nan sai ya daga kansa yana cewa: zan rubuta takarda zuwa ga gwamna na dake Madina, domin ya tilasta Husain yayi mani mubaya`a, ai lallai ya wajaba a matsa lamba wa Husain har sai yai mani mubaya`a Ni kuma me ya hada ni da Husain dan Fatimatuz Zahra ? Walid yayi wannan magana ne lokacin da ya samu wasikar Yazid bin Muawiya a daidai wannan lokaci sai wani mutum dake kusa da Walid ya kyalkyala dariya, wannan mutum wato mugun mutum da yayi dariya shine Marwan binil Hakam Sai Walid ya kura ido wa Marwan sa annan ya ce masa; ai ba na zaton Husain zai yadda yayi mubaya`a wa Yazid. Marwan sai ya ce masa: ni na san har abada Husain ba zai amsa maka yin mubaya`a wa Yazid ba kuma baya ganin cewa ya wajaba yayi biyayya wa Yazid Marwan yayi shiru na dan lokaci kadan sannan sai ya ci gaba da zancensa, yayin nan bakin halinsa da muguntarsa ta bayyana a fuskarsa, ya ce: da ni ne a matsayinka ai bama zan yi wani zance wa Imam Husain ba koda kuwa kalma daya, sare wuyansa zan yi tun kafin ya san cewa Muawiya ya mutu Wannan magana ta Marwan ta girmama matuka a zuciyar Walid Sai ya sunkuyar da kansa yana kuka cikin karkarta murya, yana kuma magana cikin rashin jin dadi yana cewa: dama ba a haifi Walidu ba, dama Walidu bai zama abin ambato ba Marwan yana nan yana lura da kukan da Walid yake yi, yana kuma sauraron magaganunsa sai ya fara masa magana cikin taushin murya yana cewa: Ya kai gwamna kada ka ji tsoro saboda abinda na gaya maka domin a hakika zuriyar Ali bin Abi Talib makiyanmu ne tun ba yau ba, kuma har yanzu kiyayyar bata kare ba idan har baka magance lamarin Husain ba to girmanka da darajarka zata fadi a wajen shugaba Yazidu Sai Walid yayi tsawa wa Marwan cikin tsananin fushi, ya ce masa: kaitonka, rabu da ni da irin wannan magana ta ka ka kyautata zance kan Husain dan Fatimatuz-Zahra domin shine kadai wanda ya saura cikin `ya `yan Annabawa Daga nan sai Walid bin Utba ya aika domin a kira Imam Husain(A.S.) dama can Imam Husain ya san abinda ya sa Walid ya aika a kira shi sabili da Imam ya gani cikin mafarki kamar Muawiya yayi dungure, wuta kuma tana ci a cikin gidansa sai ya san cewa Muawiya ya mutu kenan saboda haka Walidu a yanzu yana neman Imam Husain yayi mubaya`a wa Yazidu kenan Imam Husain(A.S.) yayi wanka sannan yayi salla raka`a biyu daga nan sai ya roki Allah abinda yake so, bayan haka sai ya aika domin a kira masa yaransa da bayinsa da maabuta gidansa ya kuma sanar da su halin da yake ciki, ya ce musu: kowane dayan ku ya dau takobinsa a karkashin tufafinsa yayi shirin sara, kuma ku jira nan a kofar wannan mutumi (wato gwamna) ni kuma zan shiga in yi magana da shi idan kun ji na daga muryata ina magana da su kuma kuka ji na kira ku Ya zuriyar Manzo to ku shiga da karfi ba tare da izini ba ku cire takubanku amma kada ku yi gaggawa idan kuwa kuka ga abinda kuke tsoro, to ku yi amfani da takubbanku Kuma ku kashe wanda ya nemi kashe ni Imam Husain(A.S.) sai ya fito daga gidansa a tare da shi kuwa ga mutum talatin daga mutanen gidansa da bayinsa da jama`arsa sai ya tsayar da su a kofar Walid ya ce musu: Ku kiyaye abinda na gaya muku kada ku ketare shi Kuma ina fatan in fito gare ku lami lafiya in sha Allah Sai ya shiga wajen Walid yayi masa Sallama sannan ya ce: Yaya gwamna ya wayi gari yau ? Kuma yaya lafiyarsa? Sai Walidu bin Utba ya mayar masa da amsa mai kyau sannan ya kusato shi, ya zaunar da shi kusa da shi shi kuwa Marwan, wannan mugun mutum, yana kallonsu Sai Imam Husain(A.S.) ya tambayi Walidu dangane da lamarin Muawiya, kai ka ce Imam bai san komai ba game da lamarinsa, ya ce wa Walid shin kun sami wani labari kuwa a kan Muawiya? Domin rashin lafiyarsa yanzun haka ta yi tsawo to yaya ya kara ji ? Walidu yayi ajiyar zuci sannan ya ce wa Imam Husain(A.S.): Ya Abu Abdillah ai Muawiya ya rasu Sai Imam Husain(A.S.) ya ce wa Walidu Inna lillahi wa inna ilaihi raji una hakika daga Allah muke, kuma gare shi zamu koma to amma ina dalilin kirana da ka yi ? Sai Walidu ya amsa: ya ce na kira ka ne domin mubaya`a wanda mutane suka hadu akanta Sai Imam Husain ya ce: ya kai gwamna hakika mutum kamata baya yin mubaya`arsa a asirce kamata yayi ace mubaya`a ta a fili na yi ta, a cikin jama`a saboda haka gobe idan ka kira mutane zuwa ga yin mubaya`a to muma sai ka kira mu tare da su Sai Walidu ya ce masa: Hakika ka yi magana, kuma ka kyautata zance, dama can haka nake zaton zaka yi. Anan ne fa sai Marwan binil Hakam ya tashi yayi tsawa wa Walidu ya ce masa: ya kai gwamna idan har ya rabu da kai yanzu alhali bai yi mubaya`a ba, to hakika ba kuma zaka sake samun iko akansa ba don haka ka tsare shi nan wurinka, kada ka barshi ya fita har sai yayi mubaya`a idan kuwa bai yi ba, to ka sare wuyansa Imam Husain(A.S.) sai ya ce wa Marwan kaiton ka ya kai wulakantacce nine kake bada umarni a sare wuyana Wallahi ka yi karya, kuma ka lalace Na yi rantsuwa da Allah idan har wani mahaluki ya nemi yin haka, to sai na shayar da kasa jininsa in ka ga damar haka to ka nemi sarar wuyana idan da gaske kake Daga nan sai Imam Husain ya je gurin Walidu ya ce masa: Ya kai gwamna mu Ahlu baitin Annabi ne kuma mu asasi ne na sakon addinin musulunci Kuma Mala`iku a gidanmu suke sauka garemu rahama take sauka da mu ne Allah yayi budi kuma da mu ne Ya rufe Yazidu kuwa mutum ne fasiki mashayin giya mai kashe rai, kuma mai bayyana fasikanci a fili don haka mutum iri na baya mubaya`a ga irinsa zamu wayi gari kuma ku wayi gari za kuma mu gani, kuma ku ga cewa wanene ya fi cancantar ayi masa mubaya`a kuma wanene ya fi cancantar halifanci, tsakanin ni da ku Wanda da suka tsaye a kofe suka ji muryar Imam Husain(A.S.) ta yi sama sai suka yi nufin su shigo nan wurin da takubbansu ba izini amma kafin su yi haka sai kawai suka ga Imam Husain(A.S.) ya fito gurinsu saannan sai ya umarce su da su koma gidajensu Bayan an yi haka sai Marwan ya zargi gwamna da irin wannan mataki nasa, ya ce: Ya kai gwamma, hakika ka saba abinda na gaya maka, har ka bar Husain ya fice daga gurinka to ka sani cewa zai yake ku da kai da Yazidu Sai Walidu ya ce masa: kaitonka, cewa ka yi fa in kashe Husain ai idan kuwa na kashe shi to addini na da duniyata duk sun halaka Wallahi bana so in mallaki duniya koda kuwa dukkaninta ne gabashinta da yammacinta a bakin kashe Husain dan Fatimatuz Zahra Kuma bana Zaton wani mahaluki zai je ga Allah ranar gobe kiyama a halin ya zubar da jinin Husain face ma`auninsa ya zan bai da nauyi a gurin Allah, kuma Allah ba zai kalle shi ba, ba kuma zai tsarkake shi ba, sannan kuma Allah zai yi masa azaba mai tsanani Kashegari sai hanya ta hada Imam Husain(A.S.) da Marwan binil Hakam, sai Marwan ya nemi cewa Imam Husain ya tsaya, saannan sai ya ce masa: Ya Abu Abdillah ni ina shiryar da kai zuwa ga yin mubaya`a wa Yazid domin yin haka shi ya fi maka a addininka da kuma duniyarka da Imam Husain(A.S.) ya ji haka, sai ya ce:Inna lillahi wa inna ilaihi rajiuna idan dai an jarabci al`umma da shugabancin shugaba kamar Yazid, ai babu musulunci kenan (wato dai saidai a yi ban kwana da irin wannan musulunci) Marwan har kai ne zaka ce kana shiryar da ni zuwa ga yin mubaya`a wa Yazid alhali Yazidu mutum ne fasiki ? Hakika ka fadi magana fandararriya Kuma mai batarwa amma ba zan ga laifinka ba domin kuwa kai ne la`ananne wanda Manzon Allah(S.A.W.A.) ya la`ance ka a yayin nan kana cikin tsatson babanka Hakam binil As Wanda kuwa Manzon Allah(S.A.W.A.) ya la`ance shi ba za a zarge shi ba idan an ga yayi kira domin a zo a yi mubaya`a wa Yazid je ka ban wuri ya makiyin Allah domin mu Ahlu Baitin Manzon Allah ne gaskiya yana tare da mu, yana gudana a harsunanmu hakika na ji kakana Manzon Allah(S.A.W.A.) yana cewa: Halifanci ya haramta wa zuriyar Abu Sufyan sakakku (wandanda Manzo ya sau su bayan Fatahin Makka) `ya `yan sakakku to idan kun ga Mu`awiya akan minbarina, ku tsaga cikinsa kuma hakkan mutan Madina sun gan shi akan minbarin Manzon Allah(S.A.W.A.) amma basu aikata abinda aka umarce su da shi ba don haka Allah ya jarabce su da dansa Yazid Da Marwan ya ji wannan magana sai yayi magana cikin fushi sosai, ya ce: Wallahi ba zan barka ba har sai ka yi mubaya`a wa Yazid tilas domin ku zuriyar Ali bin Abi Talib gabar ku da kiyayyarku ga zuriyar Abu Sufyan ta cika yawa, a sabili da haka ya dace suma su yi adawa da ku Sai Husain(A.S.) ya ce masa: ja ka bani wuri domin kai najasa ne ni kuwa ina daga Ahlu Baiti ne masu tsarki wanda Allah Ya sauKar da aya akan mu: hakika abinda Allah Yayi nufi kadai shine ya tafiyar da kazanta daga gare ku, ya ku Ahlul Baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa surar Ahzab aya ta 33. Sai Marwan ya sunkuyar da kansa bai sake furta wata kalma ba daga nan sai Imam Husain(A.S.) ya ce masa: ina maka bushara ya kai lalatacce da cewa zaka sadu da dukan abinda kake ki daga Manzon Allah(S.A.W.A.) rarnar da ka koma ga Allah Ta`ala yayin da kakana (manzon Allah) zai tambaye ka game da hakkina Marwan sai ya tafi wajen Walid ya ba shi labarin abinda Imam Husain ya ce, Walidu kuwa sai ya aika da mutum talatin domin su nemo Imam Husain(A.S.) saidai su wadannan mutum talatin sai suka gaza samun iko akan Imam Husain(A.S.) Daga nan sai Walidu ya rubuta takarda zuwa ga Yazidu ya kuma ba shi labari kan lamarin Husain(A.S.), cewa baya ganin zai yi biyayya ga Yazid, bai kuma ganin zai yi masa mubaya`a Bayan takardar Walidu ta isa ga Yazidu sai Yazid yayi fushi, fushi mai tsanani daga bisani ya rubuta wata takardar wa Walid, yana neman cewa Walid ya kashe Imam Husain bin Ali(A.S.), kuma idan har Walidu yayi haka to zai samu kyauta mai girma Sai wannan abu ya girmama a gurin Walid sosai sosai, yana cewa: Wallahi Allah ba zai tarar da ni a halin na kashe Husain dan Manzon Allah(S.A.W.A.) ba koda kuwa Yazid ya ba ni duniya da abinda ke cikinta Imam Husain(A.S.) cikin dare sai ya tafi kabarin kakansa Manzon Allah(S.A.W.A.) yayi salla a can yayin da ya idar da sallarsa sai ya shiga yin addu `a yana cewa: Ya Allah wannan kabarin Annabinka Annabi Muhammad(S.A.W.A.) ne, ni kuma dan diyar Annabinka ne hakika ka kuwa san lamarin da ya faru gare ni Ya Allah hakika ni mai son aiki mai kyau ne kuma ina kin mummunan aiki ina rokon ka ya maabucin girma da daukaka, saboda hakkin wannan kabari da wanda ke cikinsa Ka zaba mani daga wannan lamari nawa, abinda yardarka ke ciki Kuma yardar Manzonka ke ciki da kuma muminai Daga nan sai ya saura a nan yana ta kuka har alfijir yayi kusan ketowa sai ya sanya kansa akan kabarin, barci kuma ya dauke shi na dan lokaci kankani Sai ya ga Manzon Allah(S.A.W.A.) a cikin wannan barci da yayi, ya zo gurinsa a tare da Maaikin Allah ga bataliya nan na Mala`iku, sai Manzon Allah(S.A.W.A.) ya rungume shi, sannan ya sumbace shi a goshinsa daga nan sai ya ce masa: masoyina ya Husain tamkar ina ganin ka ba da dadewa ba an lullube ka cikin jininka Ka yi shahada a kasar Karbala a hanun wata jama`a daga wannan al`umma kana mai neman ruwa, kana kuma jin kishirwa amma baza a baka ruwa ka sha ba masoyina Ya Husain hakika mahaifiyar ka da mahaifinka da dan uwanka sun taho zuwa gare ni yanzu haka suna tsananin begenka kuma hakika kana da darajoji a aljanna wadda ba zaka same su ba face ta hanyar shahada don haka lokaci yayi, lokacin da Imam Husain ya dade yana sauraro tun lokacin da yake yaro, wannan kuwa ya bayyana gare shi ne yayin da ya je wajen mahaifiyarsa Fatimatuz Zahra(A.S.) ya tambaye ta tare da bakin ciki mai tsanani: ya ce mata: Ya Ummana menene ya sa kakana Manzon Allah(S.A.W.A.) yake sumbata na a wuyana amma ba a bakina ba ? Kuma menene ya sa idan ya sumbace ni a wuya sai in ga hawaye sun zubo masa ? A yayin nan da Imam Husain(A.S.) ya tambayi mahaifiyarsa Fatimatuz Zahra, sai ita kuma ta tafi wajen babanta Manzon Allah(S.A.W.A.) ta tambaye shi Sai Maaiki(S.A.W.A.) ya bata labarin abinda zai faru da danta Imam Husain(A.S.) Malaika Jibrilu ne ya sauko, sai ya bawa Manzon Allah(S.A.W.A.) wata kwalaba a cikin kwalbar akwai turbayan Karbala sannan ya bada labari wa Maaikin Allah cewa za a kashe Imam Husain(A.S.) a Karbala kuma lokacin shahadarsa wannan turbaya zata zama jini A lokacin sai Maaikin Allah ya dauki wannan kwalbar da turbayar da ke ciki ya bada su a matsayin amana a wajen Uwar muminai wato Ummu Salama, ya kuma sanar da ita abinda zai faru da turbayar dangane kuma da lamarin Imam Husain(A.S.)! Bayan Imam Husain ya ga haka sai yayi shiri zai fita daga Madina, yayi wasiyya wa dan uwansa Muhammad bin Hanafiyya kafin fitarsa, ya ce masa: Ni na kudura aniyar fita zuwa Makka na kuma yi shirin haka da ni da `yan uwana da `ya `yan dan uwana da shi`ata wanda lamarinsu shine lamarina kuma ra`ayinsu shine raayina amma kuma kai ya dan uwana, ya wajaba ka saura a Madina domin ka zama mai gane mani abinda suke kullawa Kuma kada ka boye mani wani abu daga lamurransu Umar muminai Ummu Salama ta samu labarin lamarin Imam Husain(A.S.), sai ta tuna da wani abu wanda dama can amana ce a gurinta tun tsawon shekaru da suka wuce abin kuwa shine kwalbar da turbaya ke ciki, wanda Manzon Allah(S.A.W.A.) ya ajiye a matsayin amana a wajenta don haka sai ta aika wa Imam Husain(A.S.) tana bashi labari, ta ce masa: Ni ina maka tunatarwa ya dana, kada ka fita don kuwa Manzon Allah(S.A.W.A.) ya ce mani za a kashe dana Husain a Irak kuma ya ba ni kwalba da turbaya a ciki sannan ya umarce ni da in kiyaye ta in kuma rika lura da abinda ke ciki Imam Husain(A.S.) sai ya aika mata da cewa: Ya Umma wallahi za a kashe ni babu makawa ina za a samu maguda daga abinda Allah Ya kaddara ? Ai babu wata makawa daga mutuwa Kuma hakika ni na fi sanin wurin da ranar da kuma sa ar da za a kashe ni na san gurin da za a kashe ni na kuma san gurin da za a binne ni, na san wadannan abubuwa tamkar irin sanin da na yi maki idan kin ga dama sai in nuna maki inda za a bisne ni da inda za a binne wadanda zasu yi shahada tare da ni Sai ta zo gurinsa ta ce masa ina son ka nuna mini Sai Imam Husain ya karanta Ismul Aazamu sai kasa ta yi kasa-kasa har ya nuna mata inda za a binne shi da inda za a binne wadanda zasu yi shahada tare da shi sa annan sai ya bata turbaya dan kadan, sai ta gwama ta da wanda ke wajenta a cikin kwalbar daga nan sai ya ce mata: za a kashe ni a ranar Ashura shine kuma ranar goma ga watan Muharram, shahadata zata zama a wannan rana bayan sallar azahar aminci ya tabbata a gareki ya Umma Allah Ya yarda da ke, da yardar mu a gareki Bayan haka sai Imam Husain(A.S.) ya tara sahabbansa wadanda suka yi shirin fita tare da shi zuwa Irak ya ba kowane daya daga cikinsu dinari goma, da rukumi Da zai dauki kayansa da guzurinsa akai sannan yayi dawafi a dakin Allah, ya kuma yi sa`ayi tsakanin safa da Marwa bayan wannan ne kuma sai yayi shirin fita, sai ya dora `ya `yansa mata da `yan uwansa mata akan ababen hawa ya fita daga Makka a ranar talata ranar tarwiya wato ranar takwas ga watan zul Hijja a yayin nan tare da shi akwai mutum 82 daga shi`arsa da `yantattun bayinsa da mutan gidansa ya fita daga Makka, ya nufi Irak kuma yana sane da cewa ba wani amfani na kyale-kyalen duniya bane zai samu a jikin wannan yunkuri nasa a a bil hasali ma zai yi shahada da shi da `ya `yansa da sahabbansa da `yan uwansa kuma yana sane da cewa za a kame matansa tamkar fursunonin yaki to ta yaya Imam Husain zai iya rayar da sakon Annabi Muhammad da irin wannan abinda zai faru da shi ? Ai lallai sai da haka domin kuwa irin halin da al`ummar musulmi ta shiga ciki a lokacin, ya zamanto yana bukatar irin wannan yunkuri na shahadar Imam Husin(A.S.) domin a samu a raya ruhin jihadi a tsakanin al`ummar musulmai kuma ya zamanto an yi sadaukarwa na koli wanda babu kamarta domin aga an kare asasin wannan addini daga bisani ya zama haske, abin koyi ga dukan masu yunkuri, yayin da kare addini ya wajaba gare su koda kuwa hanyar kariyar ta zan da wahala ko kuma alamun nasara a zahiri sun gushe saboda haka ne Imam Husain(A.S.) ya fadi dalilin fitarsa jihadi zuwa kasar Karbala da maganganu da suka saura a tarihi har abada, yana cewa:hakika ni ban fita don girman kai ko kuma don alfahari ba, ban kuma fita domin in yi barna ko in yi zalunci ba saidai ni na fito ne domin neman gyara a al`ummar kakana Manzon Allah(S.A.W.A.). A ranar goma ga watan Muharram kuwa wato ranar Ashura a fagen yaki nan a Karbala, Imam Husain(A.S.) ya fuskanci abubuwa iri-iri, ya ga musiba da rashin kyauta yi, wanda tarihi bai taba ganin irinsa ba mata da yara da suke cikin tantuna sun kusa su mutu saboda tsananin kishirwa suma neman koda digon ruwa su samu su sha a fagen yaki kuwa dan uwansa Abul Fadlil Abbas yayi shahada nan a bakin gabar kogin Furat yayin da yake kokarin debo ruwa saboda mata da yara su samu susha ya yi shahada a halin hannayen sa biyu duka an yanke su ga kuma babban dansa Aliyul Akbar yayi shahada da shi da Kasim dan Imam Hasan, dukansu sun yi shahada, sahabbansa da suka zabi su zauna tare da shi dukansu suma sun yi shahada, abinda ya fi wadannan duka kona rai, shine yin shahada da Abdullah dan Imam Husain yayi domin kuwa shi Abdullah bai fi yan watanni ba a duniya da haihuwarsa, yaro ne dan kankani mai shan nono koda nonon mahaifiyarsa Rabab ya kafe, sai Imam Husain(A.S.) ya dauko shi, ya tsaya da yaron a hanunsa ya fuskanci makiya yana ce masu: Ku da ni kuke yaki, ni kuma ina yakar ku to shi kuma wannan dan yaro dake jin tsananin kishirwa, menene zunubinsa ? Ku karbe shi ku da kanku ku shayar da shi ruwa koda kurbi amma amsar da suka ba Imam Husain ita ce harbo kifiya da wani maras imani daga cikinsu ya yi ana Kiransa Harmala bin Kahil, ya harbo kifiya daidai wuyan dan wannan yaro sai ya yayyanke jijiyoyinsa ya raba shi da ransa Ya ku mutane shin wace irin zuciya ko kwakwalwa ce zata iya tsayin daka a gaban irin wannan musiba ? Amma duk da irin wadannan musibu da dacin hali da suka shafi Imam Husain(A.S.), kuma suka nemi kashe masa karfinsa, duk da haka gami kuma da tsananin kishirwa da ya sanya harshensa ya zan tamkar busasshen itace Sai ga Imam Husain(A.S.) ya ciro takobinsa ya nufi inda abokan gaba suke, ya kai musu hari, yayi ta kai musu hare-hare gwanin gani ana cikin haka sai wani daga cikinsu ya jefe shi da dutse a goshinsa, abinda ya janyo jini na zuba kan idanunsa da fuskarsa a yayin da yake kokarin share jini, sai wani daga cikinsu ya harbe shi da kibiya mai baki uku sai kibiya ta ratsa zuciyar Imam Husain(A.S.) sai ga jini na ta tunkundowa da yawa daga nan ne Imam(A.S.) ya zan fuskarsa da gemunsa duk jini ya baje su, yana mai cewa:Abinda ya faru gare ni ya zan da sauki, tun da Allah Yana gani haka zan kasance har in tarar da kakana Manzon Allah(S.A.W.A.)ύ ina lullube cikin jinina in ce masa: ai wani da wani ne suka kashe ni A wannan rana wato ranar goma ga watan Muharram, Uwar muminai, Ummu Salama ta zamana tana kura ido ga wannan kwalbar turbayar, ga kuma bakin ciki da take ciki tana cikin haka, sai kawai ta ga turbayar ta zamo jini ja zur Imam Husain yayi shahada lallai, domin ya raya sakon Annabi Muhammad, ta irin wannan hanya mai kona rai, hanya wadda zata motsa zukatan al`ummar musulmai, hanya ce wanda ke kunshe da bakin ciki, bakin cikin da ke lullube ran mumini, daga bisani ya iza shi zuwa ga yunkuri domin neman daukakarsa hanya ce wadda ke tada wani sabon haske a zukata da suka mace, irin haske wanda bai wucewa duk tsawon shekaru, duk tsawon zamani Don haka yakin Karbala bai zama abin bakin kiki mai shudewa ba, alabashi a ce ya faru ne a wani yanki na tarihi kadai Ko kusa abinda ke akwai shine cewa, wannan cikakkiyar sura ce ta jayayya wadda ke tsakanin gaskiya da kuma bata, sura ce kamila wadda take raye, kuma ita ce cibiyar tarihin musulunci domin kuwa idan ba don ita ba da tarihin musulunci ya mace, wannan wata murya ce wadda ke tasowa a kullum daga yan adamtaka, daga mutuntakar bil adam a duk lokacin da kuwa tarihi ya yaye lullubinsa, sai jikin Imam Husain dake cikin jini ya bayyana a gaba ga duniya baki daya, a ga shimr bin zil Jaushan wannan la anannen yana zaune shi kuma a kan Imam Husain yana yanke kan Imam Husain(A.S.) a gefen shimr kuma ga sauran mutane, wanda daga cikinsu waninsu ya dauke rawaninsa wani kuma yana dauke takobinsa, wani kuma tufafin Imam Husain yake daukewa ga wani nan shi Kuma yana kokarin cire zoben Imam Husain amma ya gaza cirewa, sai ya dauko takobi ya sare `yar yatsar Imam Husain wai saboda ya mallaki zoben alal hakika mutum sai ya rasa ta cewa, mutum sai ya dimauce, ya rasa na yi, shin wannan zai Kalla, ko kuwa abinda ke bayan wannan, shin wani abu ne bayan jikin Imam Husain ? Idan ba tantunansa ba tantunan da matansa da yaransa suka fake a ciki ai wadannan tantunan kuwa fa aka cinna musu wuta, makiya suka cinna wa tantuna wuta, sai mata da yara suka fita suna kuwwa suna kuka, suka fito a firgice suna neman hanyar tsere wa wutar da ta kama tantuna suna cikin wannan hali ne fa, sai kuma dawakan makiya suka zagaye su Da haka ne surori biyu suka hade, suka zan guda daya ta wani bari, duniya su ga matan Imam Husain(A.S.) da `ya `yansa an zamar da su kamammun yaki, ana kora su zuwa fadar Yazid bin Muawiya, a wani bari kuma ga kawuna nan an sanya su a bakin masu, wato kan Imam Husain(A.S.) da kawunan mutan gidansa da sahabbansa wadannan sahabbai wanda haskensu ya haskaka hanya wa bil adama, ya kuma raya ma`anar sadaukarwa domin taimakon gaskiya, da taimakon addini. |
||