GAME DA

RAYUWAR IMAM HASAN (A.S.)

 

KIRA ZUWA GA JIHADI

 

ΟΪζΙ ααΜεΗΟ

 

Ban san me zan ce muku ba…? Kuma ban san abinda zan sifanta ku da shi ba…? Domin kuwa idan aka ce mutum to ba wai jikinsa da tsokarsa da jininsa bane ake nufi, a a abin nufi da mutum shine dabi`u da kuma ma`ana da Allah Yayi nufi ga mutum… tun lokacin da Allah Ya halicce shi har ya sanya shi a gurbi madaukaki wanda ke tattare da mutunci da daukaka… mutum shine shugaban dukan halittun Allah a Kassai amma da sharadin idan ya kyautata tunani da abinda Allah Ya ba shi, wannan abinda Allah Ya ba shi shine kwakwalwa da kuma hankali, domin kuwa shine abinda yayin da Allah Ya halicce shi, sai ya umarce shi da ya zo sai ya zo, ya kuma umarce shi da ya juya sai ya juya, daga nan sai Allah Ta`ala Ya ce masa: Na rantse da girmana da daukakana… da kai ne zan bada ladan aiki, kuma da kai ne zan yi ukuba ga wanda ya saba mani…

To ya ku mutane, idan dai hakkan da hanklinku da kuma kwakwalwarku ne kuka yi Imani da Allah da Manzonsa da littafansa kuma kun shaida da haka…to ni yanzu zan yi muku tambaya da wannan kwakwalwa da ya zama sanadin imaninku, tambayar kuwa ita ce shin mecece ma`anar ayar nan da Allah Ta`ala Yake cewa:”Ka ce ba ni tambayar ku wani lada a kai face dai soyayya ga makusata” Surar Shura aya ta 23.

Kuma mecece ma`anar ayar nan da Allah Ta`ala Ya ce:”hakika abinda Allah Ya yi nufi kadai shine ya tafiyar da kazanta daga gare ku, ya ku mutan gida (Ahlul Bait), kuma Ya tsarkake Ku tsarkakewa.”

Surar ahzab aya ta 33.

Sannan shin ina ma`anar wasiyyar da Manzo(S.A.W.A.) yayi muku a Gadir Khum inda kuka yi mubaya`a…? Shin Manzo(S.A.W.A.) bai ce bane Hakika ni mai bari cikinku nauyaya biyu ne: Littafin Allah da itrana wato Ahlu Baitina wanda idan kuka rike su Su biyun ba zaku bata a baya na ba har abada…”

Zuciyata ta kusa ta ta rabe biyu Saboda bakin ciki… wai shin Imam Hasan ba yana daya daga cikin Ahlu Baitin Annabi ba…? Kuma yana daya daga cikin wadanda nassin ayoyin Alkur`ani ya sauka akan su…?

Shin ba yana daya daga cikin wadanda Manzon Allah(S.A.W.A.) yayi muku wasicci da su ba…? To ina kwakwalenku da hankulanku suke yayain da Imaminku Imam Hasan bin Ali(A.S.) ya kira ku, bayan Banu Umayya sun kai hari wajejen Irak ya ce muku: Hakika Allah Ta`ala ya wajabta jihadi ga bayinsa sai ya kira shi “wahala” Sannan sai ya ce wa masu jihadi:

“Ku yi hakuri hakika Allah Yana tare da masu hakuri” Don haka ya ku mutane ku sani cewa ba zaku sami abinda kuke so ba face sai kun yi hakuri a kan abinda kuke ki…

To ku fita zuwa sansanin yaki dake Nukhaila… mu ga abinda hali zai yi, kuma ku gani, mu kuma zuba ido kuma ku zuba ido…

Shin Imamanci ba asali bane daga ususin addini…? Shin biyayya ga Imami ba biyayya bane ga Manzon Allah, biyayya ga Manzon Allah kuma biyayya ce ga Allah…? To a ina kwakwalenku suke yayin da Imamin ku Imam Hasan(A.S.) ya umarce ku da fita zuwa sansanin yaki dake Nukhaila…?! Wai shin wani abu ke gudana cikin zukatanku, yake kuma wasa da fahimatarku da tunaninku…?

Yaya aka yi hankulanku da kwakwalenku suka gaza fahimtar tsegungumi da farfagandar Muawiya… har kuka gafala, Kuka yi sakaci, daga bisani kuma umarnin Imaminku wanda ya zan Imami na gaskiya, kuka kasa aiwatar da shi, saboda haka kiranku da yayi zuwa ga jihadi da tafiya wajen yaki, ya zan bai karbu ba a gurinku… wasu irin kwakwale ne wadannan, da suka mika wuya ga kudin Banu Umayya a maimakon su tashi su kare gaskiya…?

Ana tsakiyar wannan lamari sai wani dan haske ya bulla wanda ya canja rashin taimakon Imam Hasan(A.S.) zuwa ga sa rai da kauna a jikin wasu mutanen da ke kewayen sa, wadannan mutane kuwa sune Adiy bin Hatam… da Kais bin Saad… da Maakil bin Kais… da Ziyad bin Saasaa at-tamimi… domin su wadannan mutane sun nuna cika alkawarinsu da tsarkin niyyarsu ga Imaminsu Imam Hasan(A.S.), sai suka yi masa mubaya`a… sannan suka dau alkawarin zasu zage damtse su taimaka wa gaskiya kuma su yi fito na fito da zalunci da kuma fitina… daga nan sai suka daga muryoyinsu a gaban taron jama`a da suka ki taimakon Imam Hasan, suka zarge su, suka yi tir da su, daga bisani suka kira su domin su tashi su aiwatar da wajibinsu na shari`a…

Sai Imam Hasan(A.S.) yayi murna da wadannan mutane ya kuma yaba musu akan wannan irin matsayi nasu wato matsayi na gaskiya da suka dauka, ya ce masu: Kun yi gaskiya… Allah Yayi muku rahama… Ko dama can na san ku da tsarkin niyya… da cika alkawari… da soyayya ingantacciya… Allah Ya saka muku da alheri…

Wata kila mutane sun komo ga taimakawa gaskiya… Kuma sun yarda su kare addinin musulunci… Kuma dama abinda Imam Hasan(A.S.) yake fatan zasu yi Kenan.. sai nan da nan Imam Hasan ya fara tsare tsaren yadda za a jagoranci rundunonin mayaka… sai ya zabi dan baffansa Ubaidulla bin Abbas ya shugabanci rundunonin… ya aika `yar wata jama`ar mayaka tare da shi domin ta, zama ja-gaba ga sauran rundunonin ya kuma yi masa magana kamar haka ya ce: Ya dan baffana zan aika mayaka dubu goma sha biyu tare da kai a cikinsu akwai jarumai masu yaki kan dawakai, akwai kuma makaranta sanannu na garuruwa, wanda kowane daya daga cikin wadannan karfi ne ga bataliya, to ka je da su, ka kyautata ma amalarka da su,ka sake musu fuska, ka yi musu tawali`u, ka kusatar da su a wajen zamanka, domin sune sauran amintattun Amirul muminin(A.S.), ka bi da su gabar Furat sannan ka ci gaba da tafiya har ka je inda za ku yi gaba da gaba da rundunar Muawiya… idan ka isa garesu to ka tsaya nan har lokacin da na zo, domin kuwa ina nan biye da kai ba da dadewa ba, kuma ka aiko mani da labarinku a kullum, kada ka yaki rundunar Muawiya har sai sun yake ka, idan ya yake ka, ka yake shi… idan kuma ya zamana an yi maka rauni, to kais bin Sa`ad ya shugabanci rundunar, idan shima aka yi masa rauni, to Saiid bin Kais ya maye gurbinsa a shugabancin mayaka…

Yayin da bangarorin mayaka kowannensu ya kama wuri a inda ake kira “Maskan” kusa da kogin Dujail a Irak, a yayin nan Imam Hasan(A.S.) ya kamo hanya shi kuma da sauran mayakan sai ya yada zango a inda ake kira Mazlam Sabat, kusa da garin Mada`in…

Ya ku mutane, yanzu zan tambaye ku… shin wai kwakwalenku ne suka sa kuka kuka taro kanku har kuka shirya runduna a sansanin Nukhaila…? Ko kuma dai maganganun zargi wanda Adiy bin Hatam da sauransu suka yi muku, wato maganganu da mutane masu basira suka fuskance ku da su…? Ai lallai abubuwa sun bayyana a gare ku a fili, alhali ga ku nan kuna tafiya kamar ba za ku yi tafiyar ba, ga zukatarku da niyyar ku duk sun yi rauni, rarrabuwa da kasala duk ya lullube ku shin baku san cewa kuna sabon Allah bane a irin wannan hali da kuke aikatawa, baicin ga Muawiya da ya bayyana sabon Allah da yake yi a fili… amma rundunarsa tanai masa biyayya…

Saidai kuma duk da haka, ai saida lamari ya faskara, dan hasken da da Imam Hasan(A.S.) ya sa rai sai ya zamanto babu shi, ya mamakin irin wannan abu da ya auku, ya kuma canja lamurra gaba daya suka komo yanda ba a zata ba… domin kuwa shugaban runduna sai ya zamana ransa na karkata ga dukiya, ya kumo gaza mallakan kansa a yayin da aka rude shi da kudi cikin duhun dare… koda aka wayi gari rundunar Imam Hasan(A.S.) suna jiran shugabansu ya zo yayi musu limanci a sallar asuba sai aka tarar ya gudu ya koma wajen Muawiya.

Da haka ne Muawiya ya ga cewa hanyar da ta fi kusa domin ya sa Imam Hasan yayi masa mubaya`a ita ce yada karairai da kuma yin farfaganda na son kai a tsakanin mutane da kuma mayakan Imam Hasan(A.S.), da kuma baza kudi domin ya saye zukatar mutane da kwakwalensu… to bayan Ubaidullah bin Abbas shugaban rundunar Imam Hasan ya koma gurin Muawiya… sai mai shelar Muawiya ya daga murya ya ce wa mayakan Imam Hasan(A.S.): Ai ga shugabanku nan a gurinmu ya riga yayi mubaya`a… to akan menene kuma za ku kashe kanku…?

Muawiya ya ci gaba da mugun nufinsa… sai ya rubuta takarda zuwa ga wasu shugabannin kufa yana musu alkawarin dukiya, yana kuma kwadaitar da su mukami, aka kuwa samu wasunsu suka yarda da haka, suma suka rubuta masa suna nemanda yayi haka da gaggawa, suka kara da cewa ya taho nan ya same su, sun yi alkawarin za su sallama masa Imam Hasan(A.S.) ko kuma su kashe shi… Imam Hasan(A.S.) sai ya samu labarin haka don haka sai ya zama koda salla zai je yana sanye da sulken sa…

To bayan wadannan abubuwa da suka faru, sai ya zamanto Imam Hasan(A.S.) bai da wani zabi face abu biyu, imma dai shi da Ahlu baitinsa da masu basira cikin sahabbansa, su ci gaba da yaki da Muawiya, su fuskance shi na dan lokaci kadan sannan bayan haka Muawiya ya sami biyan bukatarsa,… Ko kuma Imam Hasan yayi mubaya`a wa Muawiya domin ya kare asasin musulunci daga karkata, ya kuma kare jama`ar shi`a daga halaka, musulunci kuma ya zan ba a samu an shafe shi ba ballantana a sake komawa ga jahiliyya kamar yadda da ake… don haka Imam Hasan(A.S.) ya ga cewa ya zame masa dole yayi sulhu da Muawiya…

alabashi ya sami lokaci domin ya yi kira zuwa ga addini, ya kuma karantar da mutane ya shiryar da su,… la alla zukatarsu su amsa wannan ilimi su kuma yi aiki da shi… amma kuma shin Muawiya zai wadatu da kujerar mulki ita kadai kuwa…? Ya kuma bar sake-sake da mugun nufi da yake yi… dada ya kuma bar rudin mutane da satar kwakwalensu…? Ko kuwa zai ci gaba da bin mummunar hanyarsa domin ya ga ya kashe Imam Hasan(A.S.) jikan Annabi…?

Ai kuwa, Muawiya bai natsa ba, har sai da ya sanya guba wa Imam Hasan(A.S.) ta hanyar daya daga matan Imam Hasan wacce ake kira Ja`ada bint Ash`as, bayan shi Muawiya ya kwadaitar da ita abubuwa da yawa idan har ta iya aiwatar da wannan abu…

Da haka ne Muawiya ya warware sulhu da alkawura da yayi tsakaninsa da Imam Hasan(A.S.) jikan Manzon Allah(S.A.W.A.), bayan wannan ne Muawiya ya yaye lullubi na karshe wanda ya dade yana ta neman buya a bayansa lullubin da yayi ta kokarin nuna wa mutane ta hanyarsa cewa a zahiri shi mai kare musulunci ne…

عنوان الکتاب