GAME DA

RAYUWAR FATIMATUZ – ZAHRA (A.S.)

 

HASKE MABAYYANI

 

วแไๆั วแาวๅั

 

Kamar dama tana jin abinda matan Makka suka yi wa mahaifiyarta na kauracewa da suka yi mata... bama haka ba, hatta makusanta ma sun zama basu zuwa wurinta ballantana su tambayi halin da take ciki.. saboda haka sai ta saura ita kadai a gidanta… babu mai debe mata kewa idan Manzon Allah ya zan ya fita waje… haka yake, jinjirar nan na jin abinda ya faru da mahaifiyarta a sanadiyyar auren Manzon Allah(S.A.W.A.) da mahaifiyarta ta yi, don ganin wannan ne wannan jinjira tun tana ciki ta ga cewa lallai ne ta debe kewa wa mahaifiyarta… sai khadija ta yi murmushi don farin ciki saboda hirar da ta ji jinjirar nan ke yi da ita, ta yi murna sosai wadda bata taba yin irinta ba, lokacin da ta saura ita kadai…

Khadija…! Da wa kike magana?

Manzon Allah(S.A.W.A.) yayi wannan tambaya wa Khadija a halin yana mamaki sosai yayin da ya ga tana motsi da bakinta kamar tana magana da wani ne a gaba gareta… ga kuma farin ciki ya lullube ta…

Sai ta ce wa Manzon Allah(S.A.W.A.) Ya ma aikin Allah… jinjirin dake cikina ne ke magana da ni, ni kuma nake sauraron irin dadin maganarta…

A daidai wannan lokaci sai Mala`ika Jibrilu(A.S.) ya sauko… yayi magana da taushin murya a kunnen Manzon Allah(S.A.W.A.), maganar da ta sa Ma`aiki yayi murmushi don farin ciki daga bisani kuma ya je wajen Khadija domin ya gaya mata maganar Jibrilu(A.S.) ya ce mata: Khadija ai wannan jinjirin dake magana da ke `ya na ce… halitta ce mai tsarki kuma abar tsarkakewa… hakika Allah Ta`ala ya umarce ni da in sanya mata suna Fatima…Kuma Allah zai sanya Imamai daga zuriyarta wanda mutane za su shiryu ta hanyarsu…

Wannan magana ta sa farin-cikin Khadija ya kara yawa, murna kuma ta lullube ta gaba daya, daga bisani kuma sai wannan murna ta zama ta maye gurbin kaurace mata da matan Makka suka yi…

Alamun haihuwa sun bayyana ga Khadija… saidai kuma har yanzu ita Kadai ce babu wata mace kusa da ita, don haka sai ta aika wa makusatanta daga cikin matan Makka… ta zuba ido tana jira har amsarsu ta zo mata, ga abinda suka ce mata: Ke Khadija kin saba mana, kin ki karban maganarmu… har kika auri wannan matalauci wanda bai da dukiya… saboda haka ba zamu taba zuwa gurinki ba…

Khadija sai ta yi bakin-ciki matuka sabili da irin wannan amsa ta matan Makka … a yayin da khadija ke zaune cikin wannan hali sai ga wasu mata hudu sun shiga wurinta… Suna kama da matan kuraishawa… sai daya daga cikinsu ta ce: Khadija… kada ki yi bakin-ciki, hakika Allah Ta`ala Ya turo mu, mu zo gurinki, don mu taimaka miki…

Wannan mace da ta yi magana ita ce Asiya bint Muzahim… tare da ita kuwa akwai: Maryamu bint Imrana, da Sarah matar Annabi Ibrahim(A.S.) da kuma Safra`u yar Annabi Shuaibu(A.S.)… sai dukkansu suka zauna a gefenta… Suka kuma aiwatar da abinda ya kamata dangane da haihuwa, har aka haifi Fatimatu(A.S.) tsarkakka abar tsarkakewa kamar yadda Manzon Allah(S.A.W.A.) ya fada… daya daga cikinsu sai ta dauki Fatima… ta yi mata wanka da ruwan.

Al-Kausara, sannan ta share mata jiki… sa annan sai ta fitar da Kyallaye biyu farare, wanda farinsu ya fi na madara sannan kanshinsu ya fi na al miski da anbar… Sai ta kunshe ta a cikin daya ta kuma rufe kanta da dayan…

Sai ta jujjuya ta ko zata yi magana… ilai kuwa sai Fatima ta yi kalmar shahada tana mai cewa: Na yi shaida babu wani abin bauta da gaskiya face Allah… Kuma na yi shaida mahaifina Muhammad Manzon Allah ne… na kuma yi shaida cewa Aliyu shine shugaban wasiyyai (wato wadanda aka yi wasicci da su)… Kuma na yi shaida cewa `ya `yana sune shugabannin jikoki…

Daga nan sai Fatima ta yi sallama wa kowace daga cikin wadannan matan hudu kuma ta kira kowace da sunanta, su kuwa sai suka juyo suka yi mata murmushi… bayan haka sai suka koma sammai… bayan Khadija ta dau `yarta cikin farin ciki da murna, ta dora ta kan cinya ta ba ta nono…

Ba da dadewa ba sai aka yi lakabi wa Fatima da Az-Zahra…wato (mai haske)… domin kasa ta yi haske da haihuwarta, kuma hamada ta yi haske, duwatsu da tuddai suma sun yi haske… Mala`iku kuma suka sauko daga sama a yayin nan suka baza fikafikansu gabas da yamma ga su sun ji kawa na koli… mutanen Makka kuwa sai suka zan cikin lullubi na haske…

Manzon Allah(S.A.W.A.) ya shiga wajen Khadija yana murna yana farin- ciki yana ce mata: Khadija kada ki yi bakin ciki don matan Makka sun kaurace maki… Kuma ba su zo gurinki ba…

Domin kuwa yanzu haka ga matan hurul ini ina gani suna saukowa daga sama sun sha turare ga kuma haske na haskakowa daga gare su, ga kuma kanshi na tasowa daga gare su wanda mutan Makka za su yi farin ciki dominsa… sai suka yi sallama, suka kuma kyautata sallamar, sannan suka yi gaisuwa isasshe… Allah Ta`ala Ya turo su ne domin su yi hidima wa Khadija da `yarta Fatimatuz-Zahra(A.S.), wannan kenan bayan lamari ya zamana cewa suma kansu Hurul ini sun yi farin ciki da wannan haihuwa, sannan ma`abuta sama sashensu sai bushara suke yi ma sashe a sanadiyyar haihuwar Fatimatuz Zahra(A.S.), domin kuwa a yayin wannan haihuwa sai Mala`iku suka ga sama ta yi wani haske sosai wanda mala`ikun basu taba ganin irinsa ba…

Shekaru suka shude… Fatimatuz Zahra (A.S.) tana dada girma cikin sauri ba kamar na sauran yara ba… a a saurin girmanta ya saba ma abinda aka sani na al`ada… har aka zo wannan rana, ranar da Manzon Allah(S.A.W.A.) yake zaune a masallaci tare da sahabbansa, da kuma sayyidina Aliyu bin Abi Talib(A.S.), sai ga wani malaika ya sauko daga sama a cikin sifa wadda Manzon Allah(S.A.W.A.) bai saba gani ba, domin Maaiki ya zaci cewa Mala`ika Jibrilu ne,… sai Manzon Allah yayi nufin ya tashi ya sumbaci kan mala`ikan sai mala`ikan ya ce masa: a a Ahmadu[1] ai kai a wajen Allah ka fi dukan ma abuta Sammai da ma abuta Kassai baki daya…

Daga nan sai mala`ikan ya tashi yana sumbantar kan Manzon Allah(S.A.W.A.) da hannunsa… ana cikin haka sai Manzon Allah ya ce masa: Masoyina Jibrilu… yaya yau na gan ka a cikin sifar da baka saba saukowa a ciki ba…?

Sai mala`ikan ya ce masa: ai ni ba Jibrilu bane… Saidai ni mala`ika ne da ake kira na Mahmud… Kuma a tsakanin kafaduna an rubuta…

Kalmomin shahada, wato an rubuta cewa: Babu wani abin bauta da gaskiya face Allah… Kuma Muhammadu manzonsa ne…

A daidai wannan lokaci sai Mala`ika Jibrilu ya sauko daga sama da shi da Mika`ilu da lsrafilu tare da wasu malaiku da suka taho tare da su, shi kuwa mala`ika Mahmud sai ya ce wa Manzon Allah(S.A.W.A.): Allah ya aiko ni ne domin in aurar da haske ga haske… sai Ma`aiki(S.A.W.A.) ya ce masa: su wanene haske biyun… Sai Mala`ika Mahmud ya ce masa: wato in aurar da Fatima ga Aliyu(A.S.)…

Daga nan sai Ma aiki ya juya wajen Sayyidina Ali ya ce masa: hakika na aurar da ita gare ka a bisa abinda Allah Ta`ala ya aurar maka da ita tun a sama ta bakwai… don haka matarka ce… Sa annan sai Manzon Allah(S.A.W.A.) ya juya wajen Mahmud ya ce masa: wannan rubutu da aka yi a tsakanin kafadunka, tun da wane lokaci aka yi shi…?

Sai Mahmud ya ce masa: an rubuta shi tun kafin Allah Ta`ala Ya halicci Annabi Adamu da shekaru 2000…

Bayan haka sai Jibrilu ya mika wani kofi wa Manzon Allah(S.A.W.A.) a cikinsa akwai turaren aljanna, ya mika masa yana cewa: Ya masoyina ya Mahammadu ka umarci Fatima ta shafa turaren nan a kanta da jikinta…

Sai ya zamanto a duk lokacin da Fatima ta shafa turaren a kanta ko jikinta, sai mutanen Madina sun ji kanshinsa…

Fatimatuz-Zahra(A.S.) ta kasance kullum ta kan shagaltu da yin ibada… wata rana cikin dare yayin da take cikin ibadarta… ashe danta Hasan yana lura da ita a lokacin da take Sallolinta, take ruku`I da sujjada a wurin Sallarta, yana dai lura da ita har zuwa lokacin da ya ji ta fara addu`a sai ya ji tana yin addu`a wa dukkan makwabtan dake kewayensu maza da matansu da kuma yara… ta yi ta ibadarta har alfijir ya keto, Imam Hasan dai yana ta lura da ita, kai ka ce wani abu yake jira daga wurinta… Shin kana jin menene Imam Hasan yake jira daga mahaifiyarsa Fatimatuz-Zahra…?

To da Fatimatuz Zahra(A.S.) ta kare ibadarta da addu`o`inta… sai Imam Hasan yayi gaggawa ya tambaye ta, ya ce mata: Mama yaya ke ba ki yi addu`a wa kanki ba kamar yadda kika yi wa wasu…

Sai Fatimatuz-Zahra(A.S.) ta amsa wa danta ta ce: Ya da na… farko makwabta… Sannan sai a yi na gida…

Haka `yar Ma`aiki, tsokar Manzon Allah(S.A.W.A.) ta kasance take bada muhimmanci ga lamurran musulmai, kuma take neman alheri…

da arziki wa dukan musulmai, amma ina, ai Ma aiki(S.A.W.A.) bai dade da wafati ba sai, nau`I nau`I na masifu suka balbaleta, kuma aka zalunce ta aka kuma cutar da ita sosai, ba kuwa wani bane ya aikata wannan da ita face hukumar lokacin… don haka sai rayuwarta ta zama cikin bakin ciki da kunan zuci har zuwa lokacin da ta yi wafati a wannan hali na zaluntarta da aka yi, tana mai hakuri akan abinda aka yi mata kuma tana jiran sakayyar Allah… a cikin irin wannan hali ta tarar da mahaifinta Manzon Allah(S.A.W.A.) tana mai kai kara gare shi dangane da abinda ya shafi zaluntarta da aka yi gami kuma da cutar da ita da aka yi, bayan wafatinta sai aka binne ta cikin dare, ba a san kabarinta ba, wannan kuwa shine zalunci na kin kari.

Fatimatuz-Zahra ita ce wadda Manzo(S.A.W.A.) ya kira ta da Cewa “Ummu abiha” wato tamkar uwa take ga mahaifinta… Saidai ya ishi Zahra(A.S.) dangane da zaluntarta, abinda manzon Allah(S.A.W.A.) ya fada inda yake cewa:

“Fatima tsoka ce daga gare ni, wanda ya cutar da ita, ya cutar da ni”.

 


[1] Sunan Manzon Allah(S.A.W.A.) a sama Ahmad a kasa kuma Muhammad.

عنوان الکتاب