GAME DA

RAYUWAR IMAM ALI (A.S.)

 

 UMARNI DAGA ALLAH

 

ΓγΡ γδ Ηααε

 

Bayan ayar Alkurani dake cewa “Kuma ka yi gargadi ga danginka mafiya kusaci”[1] ta sauko wa manzon Allah(S.A.W.A.) sai ya zamanto wajen mutum arba`in daga kabilun larabawa sun zo domin su saurari maganar Ma`aiki(S.A.W.A.).

Yayin da Ma`aiki ke ce musu: ni ina kiranku zuwa ga kalmoni biyu masu sauki a harshe… masu nauyi a ma`auni… Zaku mallaki larabawa da wadanda ba larabawa ba da su, kuma al ummu za su karkato zuwa gareku, dada za ku shiga aljanna saboda wadannan kalmomi kuma ku kubuta daga wuta… Kalmomin kuwa sune: shaidar cewa babu wani abin bauta da gaskiya face Allah ni kuma manzonsa ne… to duk wanda ya amsa mani zuwa ga wannan al’amari… Kuma ya taimake ni akai domin mu tsayar da shi… ya zama dan uwana, kuma ya zama wanda zan yi wasicci da shi, kuma ya zama mataimakina, magajina kuma halifana a bayana…

 Manzon Allah(S.A.W.A.) ya ci gaba da maimaita wannan magana amma bai ji amsa daga wani ba, face mutum guda dake zaune a tsakaninsu…

Koda yake shine mafi karancin shekaru a tsakaninsu… saidai kuma duk lokacin da ya ji maganar Ma`aki(S.A.W.A.) sai ka ga ya mike tsaye cikin nitsuwa ya ce: Ni ya ma aikin Allah zan taimake ka kan wannan al amari…

Sai Manzon Allah(S.A.W.A.) ya umarce shi da ya zauna…

Sa annan sai Ma`aki ya sake maimaita maganarsa ga mutanen da suka halarci taron…

Ya shugabana ya Ma`akin Allah shin kana sauraron wani ne kuma bayan wannan saurayi,…

Ai kai ka fi kowa saninsa..?

Ba shi bane ka zabe shi tsakanin `yan uwansa domin ya zo ya rayu da kai a yayin nan yana da shekara shida Kawai? Ka zamar da shi karkashin lurarka da tarbiyyarka, kuma ka shayar da shi daga idaniyar ruwan iliminka, ka kasance kana kusato shi jikinka, kuma kana tauna abinci ka sa masa a bakinsa… idan ba shi ba wanene ya san lokacin da kake zuwa kogon Hira yana ganin ka amma sauran basu ganin ka…?! Shin akwai wani saurayi ne da ya ji kanshin annabci idan ba shi ba kuma ya ga hasken wahayi tun yana dan kankani…?! Kuma ya sami ilimi daga gareka, har ya tambaye ka a wata rana yana mai cewa: Ya Manzon Allah wace kara ce wannan? Bayan ya ji wata kara ta zo kunnensa…

Sai ka ce masa: Wannan shedan kenan, hakika ya yanke kauna daga ibadarsa… lallai kai kana jin abinda nake ji, kuma kana ganin abinda nake gani… saidai kai ba annabi bane…

Kai mataimaki ne.

Shin akwai wani idan ba shi ba ya Manzon Allah… alhali shine ya ga irin halayen karfafa ruhi da ka yi ta shiga daban-daban a yayin da kake zuwa kogon Hira… har ya sakankance da Komai dukkaninsa, tun kafin ma ka kira shi zuwa ga addinin musulunci…? Wannan saurayi kuwa ba wani bane face Aliyu bin Abi Talib(A.S.) wanda jahiliyya bata shafe shi da komai ba daga gare ta, kuma bai yarda da ita ba, hakika ya kasance yana sauraron kira da zaka yi ya kuma ga tafarkin ka, sai ya gaskata ka, ya kuma sakankance, har ya ce:

Manzon Allah(S.A.W.A.) ya sanar da ni babi dubu na ilimi, kuma kowane babi zai kasu zuwa babi dubu…

To bayan Aliyu ya tashi shi kadai cikin wannan taron ya amsa maganar Manzon Allah(S.A.W.A.), daga karshe sai Manzon Allah(S.A.W.A.) ya ce masa: Ka zauna, kaine dan`uwana kuma kaine wanda zan yi wasicci da shi, kuma kai ne mataimaki na, kaine kuma magajina da Khalifana a baya na…

Sai Kabilun suka tashi daga taron alhali suna ce wa Abu Talib tare da izgili: Muna taya ka murna don ka shiga addinin dan dan`uwanka, ga shi kuma ya sanya danka ya zama shugaba a kanka…

Shin akwai wani saurayi ne banda Aliyu bin Abi Talib wanda Allah Ta`ala ya daukaka fuskarsa da abinda bai girmama fuskar wani mutum da shi ba,… wannan kuwa ya faru ne yayin da Allah Ta`ala Ya bude Dakin Ka`aba wa mahaifiyar Aliyu wato Fatima bint Asad… ta shiga domin ta haife shi a dakin kaaba … sai kuwa ta haife mai kyan fuska, da tsabtarsa, ga kuma farin ciki… Sai Allah Ya ciyar da ita `ya `yan itacen aljanna tun tana nan duniya... Kuma aka kira ta cewa: Ya ke Fatima ki sa masa suna Ali…

Hakika ni na tsago sunansa daga sunana (wato A`ali daga Ali) kuma na yi masa tarbiya da tarbiyaNa, na Kuma Sanar da shi ilimi mai zurfi… to aljanna tana ga wanda ya so shi yayi masa biyayya…Kuma azaba ta tabbata ga wanda ya ki shi ya saba masa…

Ya Ma`akin Allah dukkan ababen nan da Allah ya sanya su tare da Aliyu tun daga haihuwarsa a dakin Ka`aba har ya zuwa lokacin da ka fara kira, hakika Allah ya sanya sune ba don komai ba sai domin ya zama shine Khalifarka kuma mataimakin ka…

Shekaru suka ci gaba da shudewa daya bayan daya… har aka zo kan ranar da aka yi alkawarinta… ya mamakin wannan rana, a wannan rana ya kasance ana Zafi mai tsanani Sosai… Kuma a lokacin ga dubban ayarin mahajjata suna dawowa daga aikin hajji tare da Manzon Allah(S.A.W.A.), kafafunsu sun zamanto suna kuna saboda tsananin zafin yashi… ga kuma zafin rana dake kone fuskokinsu a cikin hamada… banda wannan ga kuma abinda suke ta tunaninsa a cikin zukatansu… domin kuwa Manzon Allah(S.A.W.A.) ya dan nuno musu alamar cewa wannan aikin hajji da yayi shine hajjinsa na karshe, ya kuwa nuna musu wannan alama ce tun kafin su gama aikin hajji…

Ayarin mahajjata dai ya ci gaba da tafiya har aka zo wani guri wanda hanyoyin mahajjata suka rarrabu daga wurin… wanda kuma ake kira “Gadir Khum”… sai mutane suka ji wata murya tana kiran su, tana kuma neman su da su dakata.. da jin haka kuwa sai taron mahajjata suka waiga domin su ji dalilin wannan abu… Kuma shin menene ya faru a daidai wannan lokaci kuma a irin wannan yanayi?…

Ga kuma wasu mutane nan da nan har sun fara shirye-shiryen kafa tantuna domin su gyara wurin ya zama ya dace…

Mutane dai suna ta tambayar dalilin wannan lamari, watakila basu ma san cewa umarni ne ya zo wa Ma`aiki ba, domin ya tara mutane a daidai wannan lokaci, kuma abu ne wanda Allah madaukakin sarki ya aiko Mala`ika Jibrilu da shi, ya saukar wa Annabi (S.A.W.A.) yana mai ce masa:

“Ya kai Manzo ka isar da abinda aka saukar maka daga Ubangijinka, kuma idan ba ka aikata ba, to ba ka isar da sakonsa ba kuma Allah Yana kare ka daga mutane…”

Surar Ma`ida aya ta 67.

Sa annan sai aka yi kiran Sallar azahar… sai Manzon Allah(S.A.W.A.) yayi salla tare da wannan jama`a mai tarin yawa, a wannan rana wadda a sanadiyyar tsananin Zafinta sai ka ga mutane sun sanya sashen tufafinsu a kansu wani sashen kuma a karkashin kafafunsu.

Da Manzon Allah(S.A.W.A.) ya idar da salla sai ya tashi ya fuskanci mutane domin yayi musu jawabi, ya hau kan dan minbari da aka shirya, ya kuma daga muryarsa yadda jama`a za su ji yana cewa: Godiya ta tabbata ga Allah, muna neman taimakonsa, mun yi imani da shi kuma gare shi muke dogaro… Kuma muna neman tsari da Allah daga sharrin kawunanmu da munananan ayyukanmu… Wanda ya batar babu mai shiryadda shi, kuma wanda ya shiryas babu mai batar da shi… Ya ku mutane!

Hakika Allah Masani ya ba ni labari cewa wani annabi ba ya rayuwa face misalin rabin shekarun annabin da ya gabace shi… Kuma hakika na kusa a kira ni in amsa, kuma ni abin tambaya ne, kuma za a tambaye ku, to me za ku ce?

Suka ce: mun yi shaida cewa hakika ka isar da sako kuma ka yi jihadi (kokari) matuka, ka kuma yi nashia, Allah ya saka maka da alheri…

Sai ya ce musu: Shin kun yi shaida cewa babu wani abin bauta da gaskiya face Allah kuma Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne… sannan kun yi shaida cewa Aljannar Allah gaskiya ce, kuma wuta gaskiya ce, kuma kun yi shaida cewa mutuwa gaskiya ce tashin kabari ma gaskiya ne, shin kun yi shaida cewa ranar lahira tana zuwa babu Kokwanto a cikinta kuma Allah zai ta da matattu…?

Suka ce mun yi shaidar haka…

Sa annan sai ya ce: Allah kai ne shaida… ya ku mutane! Hakika Allah Mai jibintar al amurana ne, ni kuma majibincin lamuran muminai… Kuma ni ne nake da fifiko akan muminai fiye da kawunansu…

Daga nan sai ya kama hanun Imam Ali(A.S.) ya daga sama har aka ga hammatarsu, sannan ya daga muryarsa ya ce wa mutane: Wanda na zama majibincin al`amuransa to wannan Aliyu majibincin lamuransa ne ya Allah ka so wanda ya so shi kuma ka yi gaba da wanda yayi gaba da shi… Kuma ka taimaki wanda ya taimake shi, ka ki taimakon wanda ya ki taimakonsa, kuma ka zamar da gaskiya tare da shi duk inda ya juya… Ya ku mutane! Ni na riga ku… Kuma ku za ku taho wurina a tabki… tabki wanda fadinsa ya kai daga Basra (a Iraq) har zuwa San`aa (a Yemen)… a tabkin akwai kofuna gwargwadon yawan taurari, wadanda su wadannan kofuna na a zurfa ne… Saboda haka ku duba yanda zaku rike nauyaya biyu a baya na… hakika zan tambaye ku dangane da su yayin da kuka zo tabki… Abu na farko daga wadannan nauyaya biyu shine littafin Allah Ta`ala, shine mafi girma daga nauyayan biyu, kuma gefensa daya

yana wajen Allah Ta`ala, daya gefen kuma yana hanunku… Ku yi riko gare shi har abada ba zaku bata ba… abu na biyu daga nauyaya biyun shine itrana wato Ahlu Baitina…Kuma hakika Allah Masani mai tausasawa ya ba ni labari cewa ba zasu taba rabuwa ba har abada har su riske ni a tabki… don haka kada ku shige gabansu ku halaka… Kuma kada ku ki bin su, nan ma ku halaka… to wanda ya halarci wannan jawabi a cikin ku, ya isar da maganar zuwa ga wanda bai halarta ba…

Wannan wuri da Ma`aki yayi jawabi wato Gadir Khum, a wannan lokaci Gadir Khum ya ga wani irin lamari mai armashi wanda dan Adam ba zai manta ba… domin kuwa wannan sako na Ma`aiki ya zo ne a daidai lokacin da ma`aiki yake amfani da lafuzza na bankwana, da haka wannan magana ta shiga jikin al`umma, ta kuma shiga cikin tunaninta da zuciyarta… nan take mutane suka taho wajen Imam Ali suna ta yi masa mubaya`a… Sai Halifa Abu Bakr da Umar bin Khattab suka je wurin Manzon Allah(S.A.W.A.) suka ce masa: shin wannan lamari daga gareka ne ko daga Allah…?

Sai Manzon Allah(S.A.W.A.) ya ce: Shin wannan abu zai yiwu ya zama ba da umarnin Allah ba?…

Daga nan sai Umar bin Khattab ya zo gurin Amirul Muminin Ali(A.S.) ya yi masa sallama ya ce: Aminci ya tabbata a gareka ya shugaban muminai, ina yi maka murna ya Ali… domin kuwa ka zama majibincin lamarina da ni da kowane mumini da mimina… Halifa Abu Bakr shima sai ya aikata kamar yadda Halifa Umar ya aikata, ya kuma fadi abinda ya fada a gaban wannan taron jama`a mai yawa…

Saidai kuma duk da abinda ya auku a Gadir Khum dangane da wannan mubaya`a da kuma takidi da Manzon Allah(S.A.W.A.) yayi na cewa Khalifancin Sayyidina Ali umarni ne daga Allah amma ba wai Ma`aiki ne ya bawa Sayyidina Ali domin kusancinsa da shi ba, dun haka, Ma`aiki ya riga ya san abinda zai faru bayan rasuwarsa, sai ga Ma`aiki(S.A.W.A.) wata rana cikin dare ya kira Aliyu tare da wasu jama`a daga sahabbai… ya fita da su zuwa Baki`a… a yayin nan ya zamana ya ga irin yadda rashin lafiyarsa ya tsananta yana kuma ganin kusacin ajalinsa. Sai ya tsaya tsakanin kaburbura yana mayar da magana ga muminai da suke kwance a wannan wuri, yana cewa: Aminci ya tabbata a gareku ya ma abuta kaburbura, ku yi murna da halin da kuke ciki wanda shi ya fi muku abinda mutane dake raye ke ciki, domin kuwa yanzu haka fitinu sun kusa su zo, tamkar yankin dare mai duhu dayansu bayan daya…

Sannan sai Manzoin Allah(S.A.W.A.) ya nema masu gafarar Allah na tsawon lokaci… ya kuma sanar da mutane muminai da suka taho tare da shi makabartar da cewa, ajalinsa yayi kusa…

Ma`aiki(S.A.W.A.) dama can ya bada umarni da a shiryo rundunar yaki wato yayi umarni da a yi shirin fita yaki sannan sai ya sanya shaihunnan muhajirai da Ansar a cikin rundunar, wato kamar su Halifa Abu Bakr da Umar bin Khattab da Usman bin Affan da sauransu… sannan ya sanya shugabancin rundunar a hanun sahabi matashi wato Usama bin Zaid bin Harisata… Saidai a daidai lokacin da Manzon Allah(S.A.W.A.) yake fama da tsananin rashin lafiyarsa, sai Halifa Abu Bakr da Umar da Usman suka kawo uzuri domin kada su bi wannan runduna ta yaki da Usama ke shugabanta… wannan kenan, alhali a daidai wannan lokaci Ma`aiki yayi magana kan wanda ba su bi wanna runduna ba, yana mai cewa:

La`anar Allah ta tabbata ga wanda bai bi rundunar Usama ba…! uzuri da suka kawo shine cewa su ba zasu iya rabuwa da Ma`aiki a cikin irin wannan hali na tsananin rashin lafiya da yake ciki ba… amma kuma yayin da ran Ma`aiki(S.A.W.A.) mai tsarki ya fita alhali Aliyu bin Abi Talib(A.S.) na rike da shi…

Sai wadannan mutanen uku dukkansu suka fita suka bar lamarin Manzon Allah(S.A.W.A.), suka nufi sakifatu Bani Sa`ida, domin su yi taro a can daga bisani su nada wanda zai zama Khalifar Manzon Allah(S.A.W.A.) wajen jagoranci ga al`umma… da wannan aiki da suka aikata sai suka zan tamkar wanda ya jahilci maganar Manzon Allah(S.A.W.A.) da duk jawabin da yayi a Gadir Khum, inda aka yi mubaya`a wa Sayyidina Ali, lamarin da ba wani dadewa yayi ba a lokacin, to haka ne suka tabbatar da cewa sun saba wa waccan mubaya`a da aka yi a Gadir Khum… to ya ishe mu, mu tuna da abinda Ma`aiki(S.A.W.A.) ya ce dangane da Aliyu inda yake cewa babu mai son ka face mumini… babu kuma mai kin ka face munafuki…

Can a sakifa sai Umar yayi gaggawa yayi mubaya`a wa Abu Bakr ya Kuma nemi sauran mutane dake wurin da su yi masa mubaya`a… labari sai ya kai wajen Amirul Muminin Aliyu(A.S.) saboda irin surutu da kuma yawan muryoyin jama`a da yayi ta tashi bayan sun fito daga sakifa sun nufi masallacin Annabi…a halin suna tafe da Halifa Abu Bakr suna masa gara tamkar na amarya, a daidai lokacin da…

Imam Ali(A.S.) da sauran Ahlul Bait sun kasance sun shagaltu da shirya Manzon Allah(S.A.W.A.) wato abinda ya shafi yi masa wanka da sa masa likkafani da yi masa salla da kuma binne shi… to saboda rashin amincewar Sayyidina Aliyu(A.S.) da wannan abinda ya gudana a sakifa jim kadan bayan rasuwar Manzon Allah(S.A.W.A.), don haka sai ya ci gaba da yin imani da cewa halifanci dai hakkinsa ne kamar yadda Manzo ya bayyana a Gadir Khum, ya kuma ci gaba da kare musulunci da musulmai, yana mai warware manya-manyan matsaloli da suke tinkarar musulunci da musulmai yana kuma mai jure wahalhalu, yana mai hakuri, har zuwa lokacin da mafi sharrin halitta duka, wato Abdurrahman bin Muljam ya sare shi da wuka a kansa ya lullube shi da jini, wannan sara kuwa ta faru ne a daren sha tara ga watan Ramalana a Shekara ta 41 bayan hijira, da wannan ne kuma al ummar musulmi suka saura cikin bakin ciki na har abada domin jim kadan bayan haka Imam Ali ya bar duniya.

 


[1] Suratu Shu`ara sura ta 26 aya ta 214.

 

عنوان الکتاب