|
MAFIFICIN ANNABAWA MUHAMMADU (SAWA) |
||
|
Babban lakabinasa: mustafa Alkunyarsa: abul kasim wato baban kasimu,khairul bariyya: mafificin haliftu, nabiyur rahma (annabin rahama), sahibul malhama, muhallilu,t tayyibat (mai halatta kyawawa),khatamun nabiyin (Cikamakin annabawa), rasulul hammadin (Ma’aikin masu godiya), ramatan Lil Alamin: Rahama ga halittu, ka’idul Garril Muhajjalin: Abdullah; Bawan Allah, Khiyaratullah; Zababben Allah, Sayyidul Mursalin : Shugaban Manzanni, Imamul Muttakin; Jagoran Masu Takawa, Habibullah: Masoyin Allah, Safiyallah; Zabin Allah, Ni’imatullah; Ni’imar allah, Sahibulliwa; Ma’abucin Tuta, Ibinul Fawatim; Dan Fatimomi, Abdul Mu’ayyed; Bawa Abin Taimako, Nabiyul Muhazzab; Annabi Mai Tsari, safiyul Mukarrab; Zababbe Abin Kusatarwa, Habibul Muntakhab; Abin so Zababbe, Aminul Muntakhab; Amini Zababbe, Sahibul Haudha wal kausar; Ma’abucin Tabki da Alkausara, Khairul Bashar; Mafificin Mutane, Almurtadha Lil ilmi; Abin yarda ga Ilimi, Muharramul Khaba’is; Mai haramta kazanta, Miftahul Jannati; Mabudin Aljanna, Da’awatu Ibrahim; Addu’ar Annabi Ibrahim, Bushra Isa; Busharar Annabi Isa. Mahaifinsa: Abdullah Mahaifiyarsa: Amina bintu Wahab Ranar Haihuwarsa: Ranar Juma’a da Safe 17 ga watan Rabi’u Awwal Gurin Haihuwarsa: Garin Makka Mai Alfarma Shekarar Haihawarsa: shekrar giwaye zamanin mulkin Adalin sarki Anusharawan shekara ta 622 miladiyya. Ranar wafatinsa: Ranar Lahadi 28 gawatan Safar kafin magariba. Shekararsa: Sittin da Uku. Dalilin Rasuwarsa: Guba da aka sa masa a abincinsa. Gurin Kabarinsa: Garin madina Adadin ‘ya’ yansa: 7, uku mza hudu mata. Mazan sun e: 1) Kasimu 2) Abdullah wanda ake yi wa lakabi da Attahir, mai tsarki, da kuma Attayyib kyakkyawa. Mahaifiyarsu it aceKhadija, 3) Ibrahim Mahaifiyarsa it ace Mariya. ‘Ya’ya mata kuma su ne: 1) Zainab, 2) Rukayya, 3) Ummu Kulsum, 4) Fatima. Adadin Matansa:15 Hatiminsa: Kalmar Shahada. |
||