|
GAME DA RAYUWAR IMAM ASKARI (A.S.) |
||
|
TARTSATSIN HASKEN ILIMI
ÔÚÇÚ Úáã ËÇÞÈ
Khalifan Banu Abbas wato Muutamad yana zaune sai ya fara karkarwa… Sai yayi gaggawa ya tafi wajen Imam Hasan bin Ali Al-Askari(A.S.)… me ya faru haka har Khalifa ya fita da irin wannan gaggawa daga tsakanin matansa da kuyanginsa… ya fita daga wannan gagarumin bene nasa wanda tarihi bai taba ganin irinsa ba… ga kuma mutum-mutumi na zinari daya kawata fadarsa da su wannan fada da aka lullube ganuwarta da makuba da duwatsu masu tsada… Khalifa ya fice ya wuce masu gadinsa dukaninsu yana mai gaggawa … mutane kuwa sai kura ido suke yi… ya ci gaba da tafiyarsa, ya wuce musakai akan hanya da kuma mutanen da aka zalunta da wadanda ke fama da yunwa… Khalifa baka san wadannan mutane bane…? Ko kuwa idanunka bai kai jikinsu bane wanda yagaggun tufafinsu ya gaza suturcesu? Wadannan fa aikinka ne ya Khalifa… kaitonku ya Banu Abbas, hakika zaluncinku yayi yawa… da dukiyar wadannan talakawan kuke gina benayenku… kuke kuma tara zinari da kyale-kiyale iri-iri… har kuna raya tarurrukanku da kade-kade da raye-raye da giya da kuma nau`I daban-daban na alfasha… alhali ga mutane nan sai ramewa suke ta yi saboda yunwa…
jikinsu kuma sai sandarewa yake saboda sanyi… lokacin zafi kuma haka suke kuna a cikin zafin rana saboda rashin matsuguni… Irin wannan fita ta gaggawa da Muutamad yayi, kuma a halin yana firgice, ya sa mutane na ta tambaya… ko shin me ya janyo haka…? Sai wani mutum daga mutanen Khalifa Muutamad ya ce: ai Khalifa ya tafi fursuna ne gurin Imam Hasan Al-Askari(A.S.)… Sai daya daga cikin mutane ya ce: menene wannan lalatacce ke nema da Imam Askari(A.S.)…? Shin sa shi a fursuna da yayi da kuma hana shi saduwa da shi`arsa da Khalifa yayi bai ishi Khalifa bane…? Me yake nema kuma da Imam bayan ya riga da ya kuntata wa Imam ya matsa masa lamba, bai Ko tausaya masa ba… ya Kuma sa Imam cikin kuncin rayuwa matsananc ya … Ko kuma yana nufin ya kashe Imam ne…? dayansu ya tambaya Wani kuma ya ce: ai babu mamaki… domin kuwa akwai labari da ya yadu a tsakanin mutane cewa akwai wani Imami da zai fito daga tsatson Imam Hasan Askari(A.S.) wanda zai cika wannan kasa da adalci da daidaito… bayan an riga an cika ta da zalunci da ji`irci… Sai mutumin yayi ajiyar zuci sannan ya ce: ashe akwai wani zalunci da ja`irci fiye da wanda muke ciki a yanzu…? Koda Khalifa ya zo wajen Imam Askari sai ya ce masa: Ya dan Manzon Allah ka ceci al`ummar kakanka… sannan ya ci gaba da cewa: tun tsawon lokaci gari ke fama da fari mai tsanani saboda rashin saukar ruwan sama… sai na yi umarni da a fita a yi rokon ruwa, a kuma kankantar da kai ga Allah ko ma sami ruwan sama… sai muka aikata haka na tsawon kwana uku amma ko digon ruwa bai sauko mana ba… ba a jima ba sai muka ga wata jama`a ta nasara (kirista) sun zo rokon ruwa, a tare da su akwai wani malaminsu… daga hanun malamin nan sama ke da wuya sai kawai muka ga girgije ya taso sai ga shi za a yi ruwa… wanda wannan lamari ya sa wasu musulmai cikin kokwanto dangane da addininsu… wata jama`a kuma ta yi ridda… don haka na rude, ban san abin da zan aikata ba… sai Imam Askari(A.S.) ya ce: ka bar su gobe su sake fitowa… in Allah ya yarda zan kawar da kokwanton… Sai Khalifa Muutamad yayi farin ciki sosai… nan take ya bada umarni a saki Imam Askari(A.S.)… sai Imam ya nemi a saki sahabbansa tare da shi… Muutamad sai ya amsa ba bata lokaci… Kashegari sai ga tarin jama`a sun zagaye wannan malami banasare suna mamaki sosai… ya kuma daga hannayen sa zuwa sama, sai ga shi girgije ya fara taruwa… a daidai wannan lokaci sai aka ji muryar Imam Askari(A.S.) yana bada umarnin cewa a kame hannayen wannan malami banasare tun kafin ruwa ya sauko… mutane kuwa sai mamakin abinda ke faruwa suke yi… suna kuma tambayar cewa ko menene ke faruwa…? Ana cikin haka sai wasu suka ce: ku duba ku ga… Imam Askari(A.S.) ya karbe wani abu daga hanun wannan malami banasare…!! Khalifa Muutamad sai ya taho gurin Imam Hasan Al-Askari(A.S.) yana tambayarsa ya ce wa Imam Askari(A.S.): menene ka karbe daga hannunsa…? Sai Imam Askari(A.S.) ya daga muryarsa yadda sauran mutane zasu ji… ya ce wannan kashin wani Annabi ne wannan malami banasare ya samu daga wasu kaburbura… Mutane kuma kowannensu hankalinsa ya koma wajen Imam Askari(A.S.) sun kura masa ido sun kashe kunne suna sauraron Imam yayin da yake bayani… Imam ya ci gaba da magana… har ya ce: matsawar an yaye kashin wani Annabi a karkashin sammai, to sai kuwa sama ta sauko da ruwa… Anan ne fa sai duk mutane suka daga muryarsu suna salati ga Annabi da Ahlu Baitinsa… suka koma suna cewa: Karya ta kare… kokwanto kuma ya kau… masu tsubbu basu isa su motsa ba a gaban Ali Baitin Manzon Allah(S.A.W.A.)…! |
||